Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da zamu iya akai." "Ka taimaka ai ba sai lalle sai ka kaini ƙarfi ba za yi abin da ni na ƙasa abin daga Allah ne ka taimaka nidai..

Jinjina kai Aliyu ya yi kana ya rufe idanun shi, can ya ce" Yaya Amra na ga ƙafarshi ki duba ƙila kema ki gani." Da sauri ta rufe idanunta Aliyu ya ce" Kama hannuna za ki iya gani ta hakan." To kawai ta ce ta riƙe hannun shi, ƙafar tasa ta gani a nade irin ta harde su ya zau na ƙafar tana sanye da takalmi, ran Amra ya kuma ɓaci ta ce" Aliyu tabbas ko ma waye wannan ya shamceni kuma ko a ina yake saina binciko shi in sha Allah" Ta ƙarashe maganar tana buɗe idanunta."

"Yaya Amra karki damu za mu gano shi amma tabbas yana matuƙar sonta sosai kin gani kalli nan" Ya faɗa yana shafa hannun shi ya ɗan miƙa mata. Amra ta gani tana cikin nishaɗi tana jikin wata fulawa sai shinshinawa take tana sakin murmishi , Jinjina kai ta yi ta ce" Mu koma gida so nake Amina ta iso mu ko ita za ta samo mana shi tun da ta fimu shiga duniya." To kawai ya ce suka ɓaci daga kan bishiya , basu bayyana a ko'ina ba sai a jikin wani dutse mai girman gaske suka shige ciki....
_________________________
Auta na zuwa gida ta samu Fadila tare da ƙawayenta suna ta gyare-gyare a falo, isowa ta yi gurinsu tana kallon yadda aka shirya kayan da za ayi shagali ga balon-balon nan kala kala an saka su a jikin bango abin sai ya birge Auta ta saki murmushi tana lumshe idanu , kallon Fadila ta yi ta ce" Anty a duba mini abinci yunwa nakeji banci komai ba yau ko ɗaya" Ta faɗa tana cuno baki." A fusace Fadila ta juyo ta dungure mata kai ta ce" To fitinanniya kin iso gidan ai kuma shi kenan ba dama mutum ya huta sai kin dameshi da yunwa kike ji, anya ma kuwa ke a cikinki kike zuba abincin? To ba zan iya wannan masifar taki ba ki wuce ki bani guri ko in lallasaki yanzu." "Mufy ta harari Auta ta ce" Ki fice mana a nan mai ɓakar zuciya anyo gadon Mommy banza, in kinga dama kije ki zuba abincin gashi can akan darning, idan kuma ba ki ga dama ba ki yi ta zama da yunwa karki kuskure mu yi baƙi ki iso inda muke ko ki faɗa mana maganar banza." Saɓa baki Auta ta yi tana shirin yin kuka Fadila ta yi saurin hankadata gaba ta faɗi tim ta shiga zaginta har da jan mata kunne sai da taji ta kwalla ihun azaba kana ta sake mata kunne, hannunta ta kama tana janta kiiii ta kawota kan darning ɗin ta damƙi wuyan rigarta ta ce" Tashi dan uwarki ga abincin nan, idan na sake ganin walkiyarki a palon nan sai na kakkarya miki ƙafafu ya" Tana gama faɗa ta saketa ta dawo inda Mufy ke tsaye tana yiwa Auta dariya har tana cewa Fadila ta zane Auta.. Haushi da ɓakin ciki suka rufe Auta ta fashe da kuka ta miƙe da gudu ta nufi ɗakinta, tana zuwa ta faɗa kan gado ta dinga kuka tana kiran sunan Mommy...
________________________
Yana zau ne kamar wanda aka tsikara ya miƙe tsaye ya nufi gindin wata doguwar bishiya, kamar biri nan da nan ya haye samar bishiyar ya samu guri ya zau na yana sakin murmishi, a hankali ya ce" Afra na na yi kewarki a ina kike? "Ya ƙarashe maganar yana shafa hannun shi sai gata ta bayyana a kan gado tana bacci, tsayawa ya yi da kyar yana kallon fuskar tata yaga hawaye kwance akan kuncinta har sun bushe, hankalin shi ne ya yi matuƙar tashi ya yi saurin rufe idanun shi yana faɗin" Abar ƙauna wani mai tsautsayi ne ya sa tsadaddan hawayenki ya zubo daga cikin idanunki? Ko ma waye zai karɓi hukuncin daga masoyiki Bobby. Buɗe idanun shi ya yi ya wura iska a jikin rishen bishiyar, abubuwa da ya faru a gidan tun daga shigowarta har kukanta duk ya gani, Jinjina kai kawai ya yi ranshi na ƙara tafasa ya ɓace a kan bishiyar. A cikin wani ɗaki mai kama da faɗa ya bayyana a bakin gado ya zau na yana huce ya ce" Namir ko mai kake ka aje ka iso ina neman ka."

Yana rufe baki wani haske ya haska ɗakin, zuwa can sai ga wani haɗaddan saurayi matashi mai fasalin larabawa ya yi tsaye a gaban shi, cike da girmamawa ya ce" Yaya gani da fatan dai ba wani abu bane yake faruwa ko?" "Mene ne ma bai faru ba Namir so nake duk wanda ya taɓa mini matata a masa yadda ba za moru ba, wai yau aka samu wanda ya dakar mini ita ya kuma sakata kuka da hawaye, na yi ƙoƙarin mu haɗu a baccinta amma naga bata cikin shauƙin da za mu iya haɗuwa, ni kuma yau ina buƙatarta a tare dani ina so mu kwanta a gadon nan nida matata bana so ko kuɗa ya taɓa mini ita bare mutum irinta, inaso ka yi duk abin da ya dace akan su ni zan lallaɓa Afra na shayo kanta bana son ganin ɓacin ranta ko da na minti ɗaya ne, kasan dai yadda nake ƙaunarta ba zan bar wani ya ɓat mata rai ba na barshi shi yana walwala a duniyar nan, kaje ka gargade su kara musu kunne ni in naje mai gaba ɗaya zan musu shi ya sa bana zuwa sai dai na tura ka" Ya ƙarashe maganar yana fesar da iska daga bakinsa.."

"An gama Yaya ka kwantar da hankalinka zan yi komai yadda ya dace, dama kasan dai makiyanmu ne wannan ahalin gidan ai , ina fa tunanin lokacin bayyanarmu ya yi wa ahalin gidan nan..

"Haka ne amma ba ko da wasa kar a taɓa mini matata, zan ɗauketa na kaita kullacaccen gidana inda za ta samu farinciki.. Jinjina kai kawai ya yi ya ɓace a ɗakin....
_________________________
Mijin Hafsat yaga shuru-shuru har la'asar ta yi amma bata dawo ba sai mamaki ya kama shi , kiran wayarta ya yi ringing biyu uku ta ɗauki kiran, a masifance ya ce" Ke dan tsabar kin raina mini hankali ki tafi gantalinki har Yamma ba ki dawo ba, yo ko gidanku ki ka wuce ai kin mini text ki faɗa mini, amma da yake ba a miki tarbiya a gudanku ba kin kwashi ƙafa kina gararanba a gari, dan kina kawai dao ki wulaƙantani ace bana baki abinci ko bana kula dake to ba zai yiyuba ba ki maza ki dawo ko ma ina ki ka tafi, kayana gasu nan ba ki wanke su ba ki ka tafi wani dan iskan ne zai wanke mini da ki ka bar mini su a zube kamar ba ki darajar tufafiba? Ki fita idona na rufe Hafsat, ko da yake dama ku 'yan zaɓin iyayen nan haka kuke da raina miji ya yi magana ku kai ƙaran shi wajan iyayensa ƙara."

Haka ya dinga masifa ta inda ya shiga ba ta dan yake fita ba..

Hafsat ta kalli Jaririyarta dake gabanta tana nono, wani ɓakin ciki ne ya rufe ta ta cire jaririyar daga shayarwar da take mata, gyara wayar ta yi ta ce" Maigida yanzu ni kake faɗawa wannan maganar? Ko da yake ai dama ka saba kai ko tausayina baka yi ga tsohon ciki ga aikin gidan har ma da wankin ka to ba zan yi ba, ji nake kiranka aka dinga yi kaƙi ɗauka daga karshe ma ka yiwa wadda ta kiraka rashin mutumci a lokacin da nake tsakanin rayuwa da mutuwa, idan kaga dama ka zo gidanmu na haihu ga ƴarka nan akan cinyata."

Zaro idanu ya yi sai kuma ta miƙe tsaye ya ce" Kuturu! To Alkur'an sai dai Baba ya yankawa ƴarki ragon suna ba dai ni ba, ni nace ki yi cikin ko nj nace ki haihu a wannan lokacin da bani da kuɗi sosai a hannuna, mata turo mini photo Yarinya na gani in bata yi kama dani ba kema kin san sauran bayanin, in ban da ke raguwa ce tashin farko ma ki haifo mini mace dan ki cika mini gida da haihuwar ɗiya mata, ba ba zai yiyuba daga wannan karki sake haifo mini mace duka maza nake so ƴar rainin hankali, na dai kusa yin aure na aure yar charas."

Murmushi mai ciwo Hafsat ta yi tana jinjina rashin mutumci irin na mijin nata, ta ce" Maigida kenan ai bani na bawa kaina haihuwar ba in kuma kasan kasuwar da ake sayo ɗa namiji kaje ka sayo namijin sai na bayar da wannan ɗin kyauta, kana musulmi amma ya shigo Muslimci yau ya fika sanin komai daga Allah ne, yanzu kai ko kunya kaba ji ba? Allah ya maka kyauta amma ka raina saboda mutulci irin na ɗan adam, Allah ya shiryeka" Tana gama faɗin haka ta kashe wayar saboda jaririyar na kuka ta mayar da ita ta ci gaba da shayar da ɗiyarta, Allah ya rabani da wannan ƙaddara" Ta faɗa tana goge hawaye.."

Iye! Lalle Hafsat wuyanki ya isa yanka, wato ni kike yabawa magana? Zan yi maganinki. Yana zau ne yana kallo aka kira Magariba aka yi salla bai motsa ba aka kira Isha'i nan ma bai tashi ba yana kallon wani Indian film..

Sallama yaji ana yi a ƙofar shigowa, tsaki yaja ya miƙe ya nufi ƙofar yana faɗin" Waye haka da daren nan ya zo muni gida yawo, to inma neman Hafsat ku ka zo bata nan tan can daga gantalin ta wuce gidansu acan ta haihu." Buɗe ƙofar ya yi ya leƙo yaga ba kowa wayam, tsaki ya kuma yi ya rufe kofar ya dawo ya ci gaba da kallo.. Zubar ruwa yaji daga kitchen abin ya bashi mamaki ya miƙe ya nufo kitchen ɗin, rufe pampon ya yi ya dawo ya zau na, faɗuwar kanuna ya dinga ji ta ko ina sai kuam dariya mai haɗe da kuka yake ji a palon, a 380 ya watso da gudu ya nufi ɗaki, kafin ya isa ƙofar ta rufe ji kake bamm...

Ƙaran tafiya ya dinga ji a bayanshi ya yi saurin juyowa, zabura ya yi ya kurma ihu ganin wani ƙaton kare baƙi narkeke da manyan manyan idanun shi jajaye ya nufo shi, ban san lokacin da ya saki futsari ba ya yi baya luuuu.....






_*Taku har kullum Maman Nusaiba*_
[06/12, 20:42] Umma Amjad: _*🧟‍♀️ALJANAR GIDANMU 🧟‍♀️*_


Daga Alƙalamin

_Sarat Alƙasum (Maman Nusaiba)_


_🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION 📚_

*بسم الله الرحمن الرحيم*

1️⃣0️⃣


Wani irin kurnani Karen ya dinga yi yana kusanto mijin Hafsat dake sheme a ƙasa ya yi warwas, yana ƙarasowa ya rikide ya dawo wata kyakywar matashiyar budurwa mai tsananin kyau kamar ita ta yi kanta. Dariya ta dinga yi wadda duk palon ya ɗauki amsakowar muryarta, hannu ta miƙa ta ɗamko wuyan mijin Hafsat tare da zabga masa lafiyayyen mari wanda ya yi sanadiyar dawowar numfashinsa daga suma. "Allahu akbar! Innalillahi wa'inna ilaihin raju'un! Na shiga uku ku gafarceni je. "In ka sake magana saina datse maka harshenka mugu azzalumi marar imani, kai har kana da bakin yin magana dama kasan Allah kenan? Kasan da ubangijin da ya halicceka ashe? Kenan kana tunawa da wanda ya halittoka amma ka kasa bin dokokinsa?

"Waiyo Allah! Na tuba nabi Allah na biku a rufa mini asiri please ba zan sake saɓawa Ubangiji na ba, na muku alƙawarin dena komai karku kasheni zan yi duk abin da kuka buƙata koma mene ne shi" Ya ƙarashe maganar yana zaro idanu waje kamar za su faɗo.. Hahahaha! Kowa ya tuba da wuya ba lada" Ta faɗa tana nuna shi da hannunta wanda yake dauke da zaƙo-zaƙon faracuna masu kaifi. Kwalalo idanu ya yi ganin hannuwanta na yin tsawo suna neman rufe mata fuska, a kidime ya ce" Ki taimaka ki barni da raina Mama karki kasheni banga ba matata Hafsatu mai hankali matar aljana. " A fusace ta kai masa naushi a gefen fuska, ihu ya kurma yana sakin zawo palon ya cika da tsami, hannunta ta ɗaga sama sai ga wata ƙwarya mai dauke da ruwa a cikinta yana turiri dariya ta shiga yi tana karkato ƙwaryar akan shi.

"N...Na... Natuba Mama ki taimaka karki kasheni zan miki d.. Bai ƙarasa ba ruwa ya soma kwarara tun daga kanshi har ƙasa, wani kalar azababben zafi yaji wanda yake iya cewa kamar fatar jikinsa tana ɗayewa, kururuwa yake yana birgima yana kiranta da Mama ita kuma tana dariya duk inda ya juya yana neman guduwa sai ya ganta a gaban shi ta bayyana, haka ta dinga zuba masa ruwan yana kurma ihu har ruwan ƙwaryar ya ƙare kana ƙwaryar ta ɓace daga hannunta.. Tsawa ta daka masa har sai da ya kuma sakin futsari a karo na barkatai. "Zau na a nan ɗan iska marar mutumci!

Yadda ta yi maganar ya kuma sa shi a duniyar tsoro mai tsanani, jikin shi na rawa ya zau na yana ƙanƙame jikin shi. Wani irin kallo ta watsa masa kana ta ce" Kai! Ya sunanka?" Baki na rawa ya ce" Sus... Suna. Tsawa ta kuma daka masa har sai da ya wutsila ya kifa zai faɗa kan wani ƙaton madubi tasa ƙafa ta kai mata masga a gadon baya ba shiri ya gyara zamansa ram. "Ina jikin maza ya sunan ka?

"Mama sunana Shu'aibu ne matata kuma sunanta Hafsat..

Jinjina kai ta yi ta ce" Mugu azzalumi matar taka ta kiraka a waya amma kaƙi ɗauka, bayan ka kira ma sai kawai ka yi ta faɗa mata magana marar daɗi dan ka rainata ko?" Da sauri ya ce" Wallahi Mama bazan sake ɓata mata rai ba na miki alƙawari gobe ma zanje gidan nasu da safe na dawo da ita ki yi haƙuri.. "Karka sake ce mini Mama. " To ba zan sake ba, kuma na.. Ji ya yi shuru ya yi saurin ɗago kansa yana bin inda ta zau na da kallo, wayam ba kowa a gurin ya yi saurin tashi yana waige waige , kafin ya yi wani motsi yaji TV na magana ya zabura ya kalli TV . Wani ƙungurmin daji ya gani a TV babu kowa sai bishiyoyi, wata yarinya ya gani zau ne a bakin wata rijiya sake tsakiyar dajin a cikin wani fili, kwalalo idanu ya yi yana ja da baya zai matsa yaga yarinyar ta ɗago da kanta sama tare da wage bakinta wani ƙatoton maciji ya fito daga bakinta ya dabaibayeta...

Innalillahi! Ya faɗa yana rintse idanu.

Hannu ta miƙo sai gashi a waje ta kuma ɗayan shima ya fito daga TV, kamar wata kifi haka ta fito daga jikin TV bakinta jini na malala tana wani irin kurgunki, wajan Shu'aibu ta nufo tare da macijiyar a hannnunta sai huci take.. Numfashin Shu'aibu ne ya ɗauke na wucin gadi yana ja da baya yana kuka tare da rokonta.. Tana isowa ta ɗaga macijin sama ta dawo kare ta jefawa Shu'aibu, Karen nan ya shiga yagon Shu'aibu yana keta masa riga ita kuma tana dariya ta koma gefe..

"Waiyo!Waiyo! Ki taimaka karki kasheni" Haka yake faɗa. Sai da karen nan ya masa jina-jina duk ya yage mata jiki kana ya ɓace bat. Da ƙyar Shu'aibu ke ɗaga hannun shi saboda azaba nadama kuwa ya yita tafi cikin kwando yana kiran sunan mamansa da Hafsat. Sake bayyana ta yi sai ta dawo a suffar namiji ƙaton gaske baƙi hannun shi ɗauke da bulala, ja baya Shu'aibu yake har ya ƙure jikin bango ya takure yana rufe fuskar shi da hannu, dukan shi ƙaton nan ya shiga yi baƙi ba gani shi kuma yana ihun neman ceto .

Sai da ya farfasa masa jiki kana ya barshi ya kuma ɗauke ruwan nan ya dinga zuba masa a jikinsa, wuliliya Shu'aibu ke yi yana kurma ihu duk inda ruwan nan ya zubo masa ji yake gara ma ayi ta dukanshi zaifi da ruwan nan mai zafi.. Sai da ya jera suma a jere tafi goma da ya suma za'a dinga zane shi har sai ya dawo daga sumar, ranar dai Shu'aibu ya bambance tsakanin aya da tsakuwa....
_________________________

Ihu ne yake tashi a cikin palon tare da kiɗa an ƙure sautin wakar, 'yan mata da samari suna ta tikar rawa wasu a zau ne wasu kuma na gefe..

Hon ake yi Maigadi ya fita a guje ya buɗe get jikinsa na rawa ya dinga faɗin" Barka da zuwa Hajiya sannu." Murmishi Mommy ta sakar masa kana ta fito cikin takunta irin na manyan hajiyoyi ta iso kusa da shi cikin sanyin murya ta ce" Baba sannu da gida, wannan kiɗan da yake tashi duk a gidan ne?" "Kwarai ma kuwa Hajiya ai in faɗa miki Fadila ce tare da abokanta suka shigo wai ta ce yau take yin birthday. Jinjina kai ta yi ranta a matuƙar ɓace ta wuce ciki tana cewa" Na gode Baba zan yi maganin ƴar iska."

Ko da ta shiga ba wanda yaji shugowarta, sosai ta kamu da tsananin mamaki da al'ajabi ganin Fadila tasha ado ta saka riga bakin guiwa wadda da ita da babu duk ɗaya ne, dan kana kallonta za ka hango pant ɗinta ta bra ɗinta wadda itama brar kusan na fulaninta rabi a waje suke. Innalillahi wa'inna ilaihin raju'un! Ta faɗa jikinta na ɓari, lalle abin gaba yake wato iskancin na Fadila ya wuce inda take tunani, wai yau ƴarta ce take gani namiji ya nanike mata yana bata cake a baki itama tana bashi? Kai wannan wani irin zamani ne Allah ya kawo mu ni Azima ?" Ta faɗa a bayyane. Da sauri ta isa gurin speaker ta cire soket ɗin saboda tsananin ɓacin rai har wani ɗaci take jin bakinta na mata..

Fadila dake gaban saurayinta jin an kashe kiɗan ta ce" Mufy bana son iskanci fa uban wa ya ce ki kashe mana muna cikin nishaɗin mu?" "Ubaki ne ya sa banza shashasha sakarya, ku kuma kafin na ƙirga uku ku ɓaci mini da gani a cikin palo ko kuma yanzu na sa a ɗaure mini ku, shashashun banza ƙattai da ku ko kunya bakwa ji ku shigo gidan aure gidan sunna ku kunna kiɗa, har da samun guri kuka zau na ku gaku 'yan zamani ko? Maza na ce kafin na juyo naga kun tafi!" Ta faɗa cikin matuƙar ɓacin rai yau ji take kamar ta shake Fadila yarinya bata san komai sai kiɗa da wulaƙanta mutane..

Fadila ta ɓata fuska tana kumbura baki tana magana ƙasa ƙasa cikin jin haushin an hana su jin daɗi, a masifance ta ce" Baby kar ku tafi ku tsaya ai sai da na faɗawa Daddyna zan kawo ku mu yi shagalin birthday na a nan kana mu ka zo, amma shi ne za ta wani hanamu kar wanda ya tafi." Sake da baki Mommy take kallonta dama tasan za a runa wai an saci zanan mahaukaciya, juyowa ta yi ta kuma musu gargadi tare da ɗaukan wayarta za ta kira police, amma ga mamakin ta ba wanda ya motsa sai ma Fadila data miƙe ta isa gurin speaker ta kunna tare da ƙure sauti ta iso gaban saurayinta ta kamo hannunsa suka soma takawa..

Bata ƙara tankawa ba ta wuce sama ranta ba daɗi, daret ɗakin Auta ta nufa tare da buɗewa tana faɗin" Autar Mommy kina ina ne?" Can ta hangota a tsakiyar makeken royal ɗin gadonta ta rufe kanta da pilo ta takure a guri ɗaya, da sauri ta isa gareta tare da ɗago ta ta ce" Auta lafiya dai kike? Me ya sameki? Yunwa kike ji?" Duk ta jero mata tambayoyi a jere tana ɗago da fuskarta." Zaro idanu ta yi tare da cewa" Subhanallah me zan gani haka Auta? Wannan ɗin mene ne a fuskarki?"

Auta ta fashe da kuka jin muryar mahaifiyarta cikin shashshekar kuka ta ce" Mommy ba Anty Fadila ba ce ta mareni ita da Ƙawarta wai dan na dawo daga school na ce ta zuba mini abinci Kande bata nan taje kasuwa, shi ne fa Mommy ta mareni itama Ƙawarta ta mareni" Ta ƙarashe maganar tana kuka sosai..

Lahaula wala kuwwata illah billah! Wai mai Fadila take son za ma ne ? Ki yi haƙuri kinji da Daddyn ki ya zo ki faɗa masa komai zai mata hukunci, kwanta naje na dauko miki abincin. "Na koshi bana so" Ta faɗa da wata kalar murya abin da ya sa Mommy saurin kallonta." "To shi kenan koma ki kwanta ni ma zan je na kulle ɗakina wannan kiɗan ya yi yawa kuma bani da damar hanata tun da ubanta ya daure mata gindi. Fita ta yi tare da janyo mata ƙofar ta wuce nata ɗakin ta kulle...

Su Fadila har ƙarfe tara na dare ba su tafi ba, ko da aka soma kiran sallar Magariba ba wanda ya kashe waƙar bare ma a kai ga yin salla, haka ma Isha'i duk suna rawa aka yi salla biyu.. Sai da su ka gaji dan kansu kana suka kashe kayan kiɗan, Fadila tasa Kande ta dafa mu su abinci kowa ya ci duk sun yi kaca-kaca da palon..

Suna zau ne suna kallo sai ga Daddy ya shigo gidan, da gudu Fadila ta isa gareshi ta faɗa jikinsa tana masa oyoyo. Murmishi ya yi cikin jin daɗi bai ma damu da shigar da ta yi ba ya ce" Daughter har an gama shagalin ba ku jirani ba?"

Murmishi ta yi kana ta kama hannun shi suka ƙaraso ta gabatar mi shi da kowanne daga cikin friend nata, shi ko sai washe baki yake yana cewa" Wow so beautiful."

Mommy ce ta fito cikin tsananin mamaki take kallonsu ganin ba su tafi ba, Hmm Allah dai ya shirya mana" Ta faɗa tare da kallon Daddy a dakile ta ce" Sannu da zuwa Daddyn su." Ido ɗaya ya kashe mata tare da ɗage mata gira ɗaya ya ce" Darling yau ba ko oyoyo ma na dawo ina son na ganku, ina Auta take?" Wani haushi ne ya turnike Mommy wai ta masa oyoyo a gaban futsararrun yaran nan dan shi ma ya zama sorry kawai, kwafa ta yi ta ce" Su 'yan birthday ɗin ko a nan za su kwana ne?"

"E a nan za su kwana wani abu ne in sun kwana a nan ɗin?" Daddy ya faɗa yana sakin murmishi tare da mayar da kallon shi ga TV.

Auta ce ta fito tana murza idanu tare da cewa" Mommyna Daddyn bai dawo ba ne?" Ta faɗa da wata iriyar murya wadda duk 'yan palon sai da suka juya suna kallon Auta.. "A a Auta kinfi na fari iye dama kina ɗaki shi ne ba ki ji na dawo ba?" Cewar Daddy yana miƙa mata hannu." Da hanzari ta iso tare da hayewa kan cinyar Daddy tana murmishi bata sake cewa komai ba illa haɗe rai da ta yi tana kallon kowannen su tana ɓata fuska. Daddy ka ce su tashi a palon nan a gyara kalli fa yadda suka masa ko tausayin Kande basa yi, yau fa sai da na tayata aiki kana ta gama baka ga yadda take shan wahala ba Daddy, ina so dama a ƙara mata 30 a cikin albashinta ya za ma dubu 40 saboda aikin gidan nan ya mata yawa sosai kaji Daddy" Ta faɗa tana mintsinin Mufy dake gefen Daddy ta ɗaya ɓangaren."

Da sauri Mufy ta kalli Auta sai kuma ta janye idanunta ta mayar kan TV tana jinjina irin dukan da za ta yiwa

1 Comments On ALJANAR GIDANMU
avatar
taskar

1 year ago

Reply

Good

Please Login or Register in order to submit comment