Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bashi labarin abin da ya faru jiya har suka kasa gabatar da shagalin birthday ta, shi kuwa Daddy yana gefe yana mamaki har Mommy ta zau na tare da gaishe sa. Ɗago kai ya yi ya dubi Mommy ya ce" Ina Auta take ne? Yanzu Fadila ke faɗa mini abin da ya faru jiya." "Hmm meye bai faru ba Daddyn su yanzu haka wajan Malam na kaita ya mata addu'a ya kuma ce zaike mata tana sha tana shafawa a jiki mu gani ko za a dace ta dena abubuwan nan.. Daddy ya ce" Ni ma zan sa a haɗa mata magani sai mu gani, yanzu ke Fadila an jima birthday ne ko an fasa wannan shekarar?"

"Tab! Haba Daddy ai ba abin da zai hanani yin birthday na, ka dena faɗin haka kar ma Mommy ta samu damar hanani yin abin da nake so gashi na tattaro ƙawayena da friend na makaranta wanda muka yi Jami'a da su kuma kowa ya ce zai zo, kaga kenan ai ba zan fasa dan kar ajina ya zube a gurin su, in kuma kana so a rainani to sai ka yi ta faɗa Mommy tasa mini ido" Ta ƙarashe maganar tana haɗe rai. Murmishi kawai Mommy ta yi ita yanzu lamarin Fadila ya dena damunta saboda ubanta ke ɗaure mata gindi ta yi duk abin da takeso ba mai hanata, Daddy ya kamo hannunta ya ce" Ai dole ma ki yi na tura miki 500k ki samu ki yi komai na kece reni zanje gidan Yaya daga can zan wuce wani taro da ya taso kuma nine babban baƙo a gurin." Murmishi ta yi tare ta yi masa kiss a goshi ta ce" Love you so much my darling Daddyna ,ina ƙaunarka fiye da kowa a rayuwata a gidan nan kai kaɗai kake sona Wallahi dan haka duk abin da kakeso nima zan yi maka Daddyna bari naje zan yi waya da Mufy ta iso" Miƙewa ta yi da sauri ta nufi ɗakinta dukkan wani illahirin jikinta ana ganin komai hatta da pant din jikinta da bra duk ana ganinsu a bayyane, girgiza kai Mommy ta yi ta miƙe da sauri ta ce" Bye sweetheart idan Kande ta iso ka ce mata ta kula mini da Auta yanzu za ta tafi school da ta dawo ta kirani zan mata bayanin abin da za ta dafa mata." Tsaki Daddy yaja ya ce" Ke dai Wallahi Azima har yau kin kasa wayewa, kalleki za ki je babban meeting na manyan mutane ki ɗauki wani zunbulelan hijab ki zunbula kamar wata matar Liman ko Ustaz, kullum ke kanki a dubu yake ki yi ta yawo da hijabi ke wai bakya jin zafi ne? Ko ba ki ga yadda abokan aikin ki suke yi ba wayayyu masu aji da class ba irin ke ba mai kai a duhu, duniya ta canja zamani ya zo amma ke har yanzu kina nan da kanki irin na kifaye kin kasa wayewa ki ci lokacinki ki fita kina ƙamshi yadda duk wanda ya kalle ki zai yi sha'awar ƙara kallonki ya san ke ɗin matar Alhaji Shatima ce, tsuwww wani lokacin kamar mai hankali ashe amma minti ɗaya sai ki dawo riƙakkiyar mahaukaciyar kidahuma, Wallahi aure ma zan yi na auro ƴar bana bakwai mai wayewa ba irin ki ba aikin banza, kalleki gaki fara sol mai jiki da ƙyan diri ga gashi gaki doguwar mace kamar ke ki ka yi kanki ,amma duk sai kike kunshe jiki a cikin hijabi.. "Ko irin ɗaurin ɗan kwalin nan da ake a fito da gashi ya zuba baya yana channing duk ke ba ki iya ba gashi dai kinà da komai wanda mata masu class suke nema, ko ba ki ga har gashin doki suke sakawa ba?

Tun da ya soma magana Mommy ke tsaye tana kallon ikon Allah, ta inda ya shiga ba ta nan yake fita ba murmishi kawai ta yi ta dube shi sama da kasa ta ce" Ka gama ko da saura?"

Tsaki yaja ya ɗauki jaridar dake gaban shi ya ce" Malama rufe mana baki a gurin marar wayewa kawai."

"Hmm indai wannan ne wayewa ba zan yi ba, kai yanzu dan rashin sanin darajar matar sai na saka kaya masu matsewa na saka mayafi a kafaɗa, sannan na fito da gashina na fita haka dan baka da kishin matarka? To ba da ni ba aure kuma inka tashi ka auro 3 mu za ma 4 a gidan ni ba damuwata ba ce , Allah ya sa ka gane gaskiya Wallahi kaji kunya" Tana gama faɗin haka ta fice fuuu ranta a matuƙar ɓace."

Dariya Daddy ta yi ya ce" Mahaukaciya na san kishi ne kike dan na ambaci zan ƙaro aure, ni bani da lokacin ki mai hakin mutanen farko."

Da sauri take saukowa tare da faɗin" Daddy! Daddy! Please zan bika ka saukeni." Kallonta ya yi ganin yadda tasha riga da sket kayan sun amsheta fatar jikinta ta haska, murmishi ya yi ya ce" Ba hanya ɗaya za mu bi ba gaskiya Auta ki tafi Direba ya kaiki kawai ni sai na yi wanka zan tafi." Kumbura baki ta yi ta nufi ƙofar fita tana cewa" To ba ruwana dakai yau zan haɗu da Ƙawata ba zan dawo da wuri ba tun da Anty Fadila birthday za ta mana a cikin palo, wani lokacin sai na bar muku gidan nan dan na huta daku mutane kamar jikokin shedanu haba, kowa sai jin kiɗa kun mayar mana da gida kamar club to kun kaini bango saina bar muku gidan na huta da ganin kayan takaici" Haka ta dinga faɗa har ta iso bakin mota ta buɗe ta shiga. Direba dake kallonta ya ce" Auta kin tashi lafiya?" Murmishin yake ta yi ta ce" Alhamdulillah ya gida ya su Anty?" "Duk suna lafiya. Jan motar ya yi Maigadi ya buɗe musu ƙofa suka fita..

Suna zuwa saitin inda suke haduwa da Amra ta ce ya sauketa ya koma tun da gata ga makarantar za ta isa, ba yadda ya iya a sauketa ya dawo.. Shuru ta yi a gurin tana jiran Amra , can daga bayanta taji taku ta yi saurin juyawa suka haɗa idanu da Amra, da gudu ta isa gareta suka rungume juna cikin farinciki ta ce" Ƙawata na yi kewarki sosai kwana biyu ji na yi kamar mun shekara bamu haɗu ba." Amra ta ɗagota daga jikinta tana murmishi ta ce" Nima haka Ƙawata ya gida ina dai fatan Mommyn namu ta dawo ko? Ina kuma Yayanki Sudas?" Cikin zallar ƙaunarta Auta ta ce" Mommy ta dawo jiya Yaya Sudas kuma ai ranar da muka zo nan da dare ya dinga ihu ya ce wai fatalwa ce ta shigo masa ɗaki, kuma da mu ka shiga bamu ga kowa ba na ce ya rakoni ya ce indai school ba zai rakoni ba amma indai wajanki ne zai kawoni, ya ma ce na gaishe ki" Ta ƙarashe maganar tana dariya tunawa da ihun da Sudas ya dinga zundumawa a daren."

Dariya itama ta yi ta ce" E lalle ƙila ya yi gamo ne." Kama hannunta ta yi suna ƙoƙarin ficewa Auta ta juyo, waro idanu ta yi ta tsaya bakin na rawa ta ce" Amra ke kalli wata mai ciki ƙila bata da lafiya." Da sauri Amra ta juyo taga abin da Auta ta gani, da gudu suka isa gareta suna faɗin" Baiwar Allah sannu lafiya dai?"

Da ƙyar matar ta iya buɗe bakinta ta ce" Ku taimaka mini ku buɗe jakata ku ɗauko wayata ku kira layin mijina shine a sama ,ku faɗa masa halin da nake ciki." Da sauri Amra ta buɗe jakar ta fito da wayar ta dannawa mijin nata kira, har ya yi ringing ya gama ba a ɗauka ba, sake kira ta yi nan ba ba a ɗauka ba har ta katse ran Amra ya yi bala'in ɓaci ta kuma kira, sai da ta kusa tsinkewa kana aka ɗauka muryarsa taji yana faɗin" Haba Bintu wai ke wata irin mata ce kin fitar ma ba za ki rabu dani na huta ba, ba na baki naira dari ba na ce ki hau machine ko wani sabon salon iskanci kike ji da ki ka dameni da kira tun ɗazu? Ballagazar mace kawai na dawo daga kasuwa na kwanta ina hutawa ba za ki barni naji sanyi ba, ke bakya gane lokacin kiran mutum da lokacin da ba na kiran shi ba ki fita idona fa kin sanni ba sanin shanu ba dan miki rashin mutumci in ki ka dawo gidan nan , ina dalili ina mafari in banda nemawa kai fitina ina baccina mai daɗi sai kin tasheni meye haka? Nifa bani da mutumci kin sani kuma na kusa aure na huta dake dama dai ke kin sani ba sonki nake ba Baba ya matsa saina aureki, to dan haka kar ki takurani Wallahi kina dawowa na nakada miki mugun duka ba ruwana da cikin dake jikinki, in ba kwartanci ba ma ai nasan magani ki ka sa mini a cikin abinci har na kwanta dake cikin ya samu, kin san dai da kaina ba zan taɓa nemanki ba dan banga abin so a jikinki ba ƴar gidan mayu kawai, kuma daga yau I...

"Kai dalla can dakata! Amra ta faɗa ranta ya yi mugun ɓaci.

"Ke kuma daga ina ? Owo wato ke kike daure mata gindi take bijirewa duk dokokin dana shinfida mata ko? Lalle shi ne yanzu ki ka ɗauki wayarta ki ka kirani, to in asiri ne ma ku koma a sake muku wani bar ci ba...

"Kaga Malam bana son maganar banza matarka ce ke nakuɗa a tsakiyar titi ka zo ka kaita Asibiti, ki shiga hankalinka shashashan namiji kawai..

"A a fa yarinya karki zageni fa bani da mutumci nan da kike ganina zan miki rashin mutumci yadda bakya tunani...

"In ka sake magana saina karya maka wuya azzalumi macici" Tana gama faɗin haka ta kashe wayar ta dubi Auta ta ce" Kinga wannan mijin nata bashi da tausayi, mu tsayar da mota a kaita Asibiti."

Innalillahi wa'inna ilaihin raju'un! Shi ne abin da matar ke faɗa. "Sannu baiwar Allah yanzu za mu samu mota a kaiki Asibiti" Cewar Amra tana ɗagawa wata mota hannu. Tsayawa motar ta yi ta ce" Don Allah ka ɗaukar mana waccen matar zuwa Asibiti."

"To maza ku taimaka mata ta shigo. Da sauri ta dawo suka ɗaga matar har jini ya soma zuba a jikinta, da ƙyar suka sakata a motar suka juya za su tafi suak jiyo mai motar yana cewa" Kai yara ina za ku je ba Antynku ba ce za ku bar mini ita? Ki dawo mu tafi tare." Amra ta dubi Auta ta ce" Ki tafi school ɗin ni zan kaita Asibiti." "A a mu tafi tare gaskiya. To kawai ta ce suka shiga mai motar yaja suka bar gurin...

"Tun suka kama hanya Amra ke jan tsaki tana jinjina kai, lumshe idanu ta yi ta ce" Zaki kana ina ne?" Shuru ta yi da wani lokacin ta saki murmushi kana ta buɗe idanunta a lokacin sun iso Asibitin.

A hanzarce aka shiga da matar suka tsaya a bakin ƙofar ɗakin da aka shiga da ita, Amra nata zarya tana hura hanci idanunta sun yi jajur saboda ɓacin rai sosai kalaman mijin matar nan yake mata yawo a rai...


Bala mai shayi yau da ƙyar ya iso gurin sana'arsa, sai da ya buɗe komai ya ya zau na ana ciniki ana ta tambayarsa mene ne ya samu bakin shi haka?

"Ai jiya nake baku labari Garbati aljannu na gani a gindin b... Bai ƙarasa maganar ba ya yi arba da wani ƙatoton maciji ya tashi koshi a gefen shi, zabura Bala ya yi yayi sama sai gashi akan cinyar Garbati. "Waiyo gasu nan sun sake dawowa ku taimaka Garbati" Ya faɗa yana ƙara maƙalewa a jikin Garbati..

"Kai dalla Malam ka ɗagani" Cewar Garbati yana rintse idanu..

Bala juyo dan ya gani macijin nan yana nan ko kuwa ai kuwa ya yi arba da macijin yanzu sun zama biyu ma, suna haɗa idanu suka yo kanshi, ihu yasa ya yi wata irin sufa ya watsa da gudu a 380 ya hau hanya a guje....


Amra tsaye taga Auta ta yi bacci, zama ta yi a gefenta tana tarota dan kar ta faɗi ji ta yi saitin zuciyarta na bugawa sai murmushi take saki kuma baccin take. Idanu ta rufe ta dafa saitin zuciyar Auta, zuwa can ta yi saurin buɗe a zabura ta miƙe ta ce" Innalillahi wa'inna ilaihin raju'un! Auta k.....



_*Yau dai na yi muku dayawa ina bukatar comment da sharhi, in ku ka yi haka zan ke muku 2 fage a rana inhar kun bani haɗin kai ta hanyar comment da sharhi*_







_*Taku har kullum Maman Nusaiba ce*_
[05/12, 14:39] Umma Amjad: _*🧟‍♀️ALJANAR GIDANMU 🧟‍♀️*_



Daga Alƙalamin

_Sarat Alƙasum (Maman Nusaiba)_


_🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION 📚_


*Much love ƙauna masoya ina alfahari daku🫶🏻🫶🏻😘*

*بسم الله الرحمن الرحيم*

0️⃣9️⃣


Innalillahi wa'inna ilaihin raju'un! Auta k. Bata ƙarasa maganar ba sakamakon jin sautin muryar Doctor da ya fito yana mata magana ta yi saurin juyowa hankalinta a tashe ta ce" M.. Me ka ce Likita?" Murmishi ya sakar mata tare da gyara tsayuwar shi ya ce" Yarinya Antyn naku fa bata da jini sai kun saya ko kuma ku samo wanda za a ɗauka a jikinsa." Ya rabbi! Amra ta faɗa tana miƙewa tsaye, hannu biyu ta haɗe sai ga hawaye sharr³ ta ce" Likita ka taimakemu asa mata jinin nan na maka alƙawari in sha Allah zan kawo maka kuɗinka, mijin nata ne baya kusa ban san a ina zan samu kuɗin nan ba a yanzu ni ba ƴar garin nan ba ce ka taimaka kar ta rasa ranta ka dubi girman Allah ku saka mata jinin nan" Ta ƙarashe maganar tana goge hawaye." Ke yarinya karki raina mini hankali mana, taya ina miki maganar ki bada kuɗi kina maganar ba ki da kuɗi in ba za ki nemo ba ki bari Antyn naki ta rasu ku kuka yi asara bani ba kin gane?

Numfashi ta fesar ranta ta kai matakin ƙarshe a ɓaci, idanunta suka yi jajur tana zubar da hawaye lumshe idanu ta yi ta soma magana a cikin zuciyarta. "Ya rabbi! Ubangiji ka sassautawa wannan baiwar taka ta haihu lafiya, Allah ya sayayya mini zuciyata kar na nunawa yaron nan fushina, Aliyu kana ina ne? Ka zo yanzu ina son ganinka. Buɗe idanunta ta yi ta durƙusa a gabansa ta ce" Don Allah ka taimaki Antyna kar ta rasa ranta kaji."

"Tsuwww aikin banza kuma ai sai ki yi kinga ma tafiya ta ta mutu ma babu ruwana, ni za ki rainawa hankali har da wani kuka na iskanci? To ba zan taimaka ɗin ba" Ya ƙarashe maganar yana juyawa zai koma ɗakin.. "Nawa ne kuɗin? Kamar daga sama Amra taji murya mutumin. Dawowa Doctor ya yi yana dage hanci sai da ya sha ƙamshi kana ya ce" Dubu hamsin za ku biya har kuɗin maganinta bana ma tunanin za ta iya haihuwa da kanta, kawai abu mafi sauƙi ku biya 100k sai a mata aikin." Murmishi ya yi ya zaro 'yan rafa ɗaurin dubu dari ya miƙawa Doctor ya ce" Gashi a hanzarta a mata aikin, inma yafi haka zan biya ma matsala ba ne." Da sauri Doctor ya warci kuɗin a hannun shi yana washe baki ya ce" To ranka ya daɗe yanzu kuwa bari na wuce" Ya faɗa yana ficewa..

Jinjina kai Amra ta yi ta juyo ta kalli mutumci tana goge hawaye ta ce" Yaya na gode Allah ya saka da alkhairi ashe za mu sake haɗuwa?" Murmishin dai ya mata ya dawo ɗaya daga cikin kujerun ya zau na ya ce" Ai dama na ce miki za mu sake haɗuwa dake ya jikin Inna?" Itama murmishin ta yi ta zau na a kusa da Auta tare da ɗaura kanta akan cinyarta ta ce" Inna ta samu lafiya sosai gaskiya naji daɗi matuƙa ka zo a lokacin da nake buƙatar taimakonka, Allah ya saka da alkhairi bani da bakin maka gidoya kai ɗin mutumcin kirki ne." Jinjina kai kawai ya yi sai yakai kallon shi kan Auta dake ƙoƙarin tashi, zuba mata idanu ya yi har ta buɗe idanunta tana kallon Auta sai kuma ta miƙe zaune. "Amra ta haihu ne wai?" Kallonta kawai Amra ta yi ranta na tafasa ta rasa dawa za ta yi magana akan abin da ta gani a jikin Auta, "Amra lafiya dai kike kallona haka?"

"Ihum ba komai Auta naji kamar zazzaɓi ne a jikin naki ko? Cuno baki ta yi tana murza idanu ta ce" Amra yunwa nake ji ki bani abinci naci." Idanun Amra ne ya ciko da ruwan hawaye ta yi saurin mayarwa ta kama hannayenta ta ce" To Auta a ina zan samu abinci a Asibitin nan? Ki daure a jima Aliyu zai zo mana da abinci." Auta ta faɗa jikin Amra ta fashe da kuka tana a bata abinci ta ci, dan yadda take jin yunwar nan in har aka jima sai dai a ɗauki gawarta. Murmishi ya yi ya ce" Sorry sister bari nasa a kawo miki abincin dena kukan kinji." Ɗagowa ta yi tana kaon shi baki ta murguda masa ta kalli Amra ta ce" Wannan fa?" "Shi ya biya kudin da za a saka mata jini, dama na taɓa ganin shi kuma ya taimakeni.. Ajiyar zuciya ta sauke ta ce" To mun gode ka kawo mini abincin naci yunwa nake ji sosai." Waya ya yi ya ce a kawo abinci inda yake kana ya kashe kiran..

Suna nan zaune sai ga wani ma'aikacin restaurant ya kawo abincin, godiya ya masa tare da bashi kuɗin ya tafi, yana miƙa mata ta yi saurin karɓa ta gyara zama ta soma cin abincin da sauri-sauri. Yadda take cin abincin sai ya birge shi ya yi tagumi yana kallonta har lumshe idanu take.

Amra ma kallonta ta yi tana jinjina kai har ta ci ta ƙoshi ta bar sauran ɗan kaɗan tana mayar da numfashi, kallonsu ta yi sai kuma ta cuno baki ta ce" To ina ruwan yake?" Miƙa mata ya yi ta amsa ta sha, bayan ta gama ta yi hamdala kana ta juyo ga Amra da take kallon ɗakin da matar da take..

Suna nan gefe sai aka buɗe ƙofar, Doctor ta fito riƙe da jaririya ta nufosu Amra ta yi saurin tashi ta amshi yarinyar tana murna, itama Auta murna ta shiga suna hamdala. Amra ta ce" Likita ya jikin nata?"

"Lafiya lau take babu komai sai dai rashin kwarin jiki za ma ku iya ganinta ai." Godiya suka mata kana suka shiga ɗakin suka sameta kwance tana kallon gefe, zama Amra ta yi riƙe da jaririyar ta ce" Anty kinga ƴarki mai kyau." Murmishi ta yi tana taɓa jaririyar, "Yawwa Anty mijinki dai ya ki ɗaukan kira na kira yafi sau 20 bai ɗauka ba, yanzu ki mana kwatancen inda gidanki yake sai mu tafi mu kaiki gidan naki ko gidanku." Goge hawaye matar ta yi ta ce" Dama ba lalle ba ne ya ɗauki kiran tun da kin kira da farko ya dauka yana masifa, kawai gidanmu zan tafi na gaji da cin mutuncin da yake mini a zamana dashi."

Ajiyar zuciya Amra ta sauke ta ce" Ba komai Anty ya sunanki to?" "Sunana Hafsat. "To Anty ina ne Unguwar taku?
"A ƙofar Soro ne gidanmu. Jinjina kai Amra ta yi sai kuma ta ce" Wannan shi ne ya biya kuɗin da aka sa miki jini"Ta faɗa tana nuna shi ya yi tsaye bakin ƙofa." Godiya ta shiga masa har da hawayenta ya ce ba komai in an sallame su shi zai kaisu gida, Amra ta masa godiya sai ga Doctor ya shigo ya miƙawa wannan mutumin takarda ya ce" Idan kum fita ku bi hanyar hagu sai zai kaiku wani ɗaki anan za a baku magani Allah ya raya baby" Ya faɗa yana barin ɗakin tare ta jadadda musu da ruwan ya kare a kira shi ya cire sai su tafi..
Sai kusan ƙarfe 11 kana aka sallame su suka tafo zuwa gidan su Hafsat..

Suna zuwa gidan suka shiga Maman Hafsat ta tarbesu da Ƙanwarta, sai da suka zau na kana Amra ta musu bayanin komai, godiya Maman Hafsat ta yiwa su Amra ta sanya hijabi ta fito waje ta yiwa mutumin nan godiya tana saka masa albarka, shi kuma yana amsawa da amin kana ta juyo sai ga su Amra sun fito suka mata sallama.. "Haba yaran nan ya za ku tafi yanzu kuma ku zauna mana a jima. "A a Mama za mu wuce za mu dawo ko gobe ne mu ga Babyn" Cewar Amra tana shigar da Auta cikin motar, shiga itama ta yi suka bar ƙofar gidan Maman Hafsat na ɗaga musu hannu..

Daidai inda suka ɗauki matar nan ya aje su, godiya sosai suka masa ya buƙaci Auta ta basa number ta, ai kuwa ta kafe ta ce ita fa bata kula maza shekararta 14 fa ,da ƙyar Amra ta lallaɓa ta ta bashi number kana suka ya tafi..

Dariya Amra ta yi ganin yadda Auta ta yi kicinkicin da fuska, kamo hannunta ta yi ta ce" Ƙawata wai fushin nan dan kin bada number ki ne? To meye ƙila ma ba sonki yake ba sai kawai musha biki ba nan da wasu shekarun." "Nidai bana soyayya Mommy ta ce inyi karatuna kar na kula maza wasu yaudara garesu.. To naji yanzu dai kin yi latti zuwa makaranta kira Direba ya mayar dake gida.. To ta ce tana kumbura baki ta kira shi, suna zau ne a gindin wata bishiya sai gashi ya iso, sallama ta yiwa Amra ta shiga mota sai gida...

Amra na ganin sun wuce ta ɓace a wajan, bata bayyana a ko'ina ba sai a cikin wani daji mai bishiyoyi dayawa baka jin komai sai kukan tsintsaye da kukan kuraye da Zakuna, za ma ta yi akan bishiyar can sama ta ce" Aliyu kana ina wai?"

Wata guguwa ce ta karaɗe gindin bishiyar, Amra ta yi murmishi kawai har sai da guguwar ta lafa kana ya bayyana sanye da kayan yaƙi a jikinsa, gyara zama ya yi ya ce" Yaya Amra wai lafiya kike ta kwada mini kira? Kin san fa naje farauta ne haka na bari ganin kiran ya yi yawa me yake faruwa ne?" Ajiyar zuciya Amra ta sauke kana ta dubi Aliyu ta ce" Zaki akwai matsala babba." "Subhanallah! To me yake shirin faruwa ne? Ki faɗa mini ko akwai ta yadda zamu samu mafita."

"Zaki akwai wani a jikin Auta kuma ya daura soyayya da ita har ma yana mata maganar aure, na duba na kasa ganin fuskarsa sai dai kawai naga fuskar ta yi baƙi, bana so ya cutar da ita dan da alama bashi fa imani ya san tsakanin mutum da aljani babu soyayyar aure amma me ya sa ya canja ta? Zaki ya za mu shayo kan matsalar nan don Allah? Na yi iyakar dubana na kasa ganeshi bana ganin komai Aliyu ka yi wani mu gani mana" Ta ƙarashe maganar idanunta na canjawa." Hannayenta Aliyu ya riƙe cikin kwantar da hankali ya ce" Yaya Amra ki kwantar da hankalinki babu abin da zai faru da Ƙawarki in sha Allahu, bari na duba na gani ko ni zan ganshi, amma kuma Yaya Amra kema da kika fini ƙarfi ta ko wani ɓangare ba ki gani ba bare ni da ko rabin ƙarfinki ban kai, amma dai bari na duba sai muga abin

1 Comments On ALJANAR GIDANMU
avatar
taskar

1 year ago

Reply

Good

Please Login or Register in order to submit comment