Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

duba da kanka mana ai nasan kama san komai kawai rama mini ka ki yi, shi kenan yanzu ka dena sona shi ya sa ake cutar dani baka rama mini" Ta ƙarashe maganar tana sa kukan ƙarya."

"A a kar ki zubar da hawayenki abar ƙauna, yanzu kafin ki gama magana naga komai , ki rabu dasu zan koya mu su hankali ɗaya bayan ɗaya, ɗazu naga Namir a tare dake nu na bashi tsaronki na yi wata tafiya mai nisan gaske, zo nan kar ki yi fushi dani kinji abar ƙauna" Ya ƙarashe maganar yana rungume ta tare da bubbuga bayanta yana mata kalamai ma su daɗin sauraro.. Murmishi ta yi ta kuma shigewa jikinsa tana lumshe idanu. "Bobby yaushe za mu yi aure wai? Ta faɗa idanunta a lumshe..

Murmishi ya saki tare da shafa gashin kanta ya ce" To ai aure da kin shirya ko yanzu kawai mu yi ni a shirye nake ina so ki dawo inda nake muci gaba da rayuwarmu mai daɗi ki haifa mana yara masu kama dake, bana so na taɓa ki har sai mun ɗaura aure."

"Ke dan uwarki maza tashi ko yanzu in zuba miki ruwan sanyi.

Zabura Auta ta yi ta tashi sai kawai ta fashe da kuka, sake da baki Sauban ke kallon Auta ganin yadda take kuka kamar ya rabata da wani tsagin rayuwarta, zama ya yi akan gadon ya kamo hannunta ya ce" Buɗe idanunki Auta kina ta bacci ƙarfe biyar da rabi naga ba ki ce kin mana iyayin da ki ka saba ba ne, shi ya sa nace bari na leƙoki ko lafiya kike kuwa ashe kina nan kina bacci yau dai ba ki takura mana ba ki ce ba mu sallar La'asar ba, kinga yau kema kin za ma irinmu tun da ba ki yi sallar ba" Ya ƙarashe maganar yana mayar da eapis ɗinsa kunne ya miƙe ya fita daga ɗakin yabarta baki buɗe tana kallonsa jin abin da ya faɗa mata..

"Subhanallah! Ya furta jin zuciyarta na bugawa, da sauri ta sauko daga kan gadon tana mamakin abin da ta gani a mafarki, to waye shi wannan ɗin? Ta faɗa a fili yayinda ta shiga toilet ɗin. Bata jima ba ta fito ta tada salla tana gamawa ta yi addu'a kamar yadda ta saba amma duk sai taji jikinta ba daɗi bata jin karfin jikinta, miƙewa ta yi ta ɗauki Teddynta ta sumbata kana ta shiga wanka ganin lokaci na tafiya Mommy ta za ƙaraso a ko wani lokaci..

Tana shiga ta haɗa ruwa ta shiga ta Lumshe idanunta sosai mafarkin da ta yi ya tsaya mata a rai, photon wanda ta kira da Bobby take haskowa a idanun zuciyarta, haka dai ta yi wanka ta fito ta shirya ta sauka ƙasa ta zau na bata kula Sudas dake mata dariyar makarar da ta yi a salla..

Hon suak ji ana ta yi, da sauri Auta ta miƙe ta nufi ƙofa tana faɗin" Oyoyo Mommy.


Ɓata rai Fadila ta yi tana faɗin" Yanzu ƴar sa'idon nan ta dawo kuma ba dama ka yo abin da ranka yake so sai ta saka maka na mujiya tsuwww" Taja tsaki tana nufar ƙofar fita daga palon." Dariya Sudas ya yi yana rage volume ɗin TV da waƙa ke tashi ta turanci ya kalli Sauban ya ce" Ya dai kai kuma ka wani zau na ko ka dena zuwa taro Mommy ne?" Pilo ya ɗauka ya jefo masa yana nunasa da hannu ya ce" Babu ruwanka ɗan sa'ido ba dai ka ce aure za ka yi ba? To Mommy na hutawa zan antayo mata labari tun daga A har Z ba zan yi tsallake ba."

"Amma Wallahi da ka birgeni matuƙa bro, ka rashi mu fita kafin ta nemi inda muke..

Motar na yin parking direba ya fito da sauri ya buɗe mata ƙofar mota, wata kyakyawar mata ce ta hakimce akan kujera sanye take da doguwar rigar material pink haka ma mayafinta pink ne, matar za ta kai shekaru 48 zuwa da 49 fuskarta dauke da murmushi ta fito daga motar tana sauke ajiyar zuciya. A guje Auta ta iso gareta ita kuma ta ware mata hannaye ta rugume ta tana faɗin" Miss you so much my darling daughter ina matuƙar kewarku ba ki ɗaya, ina 'yan uwan naki suke?" Auta ta ɗago za ta yi magana sai ga Fadila ta su Sauban na biye da ita sun iso, sakin Auta ta yi Fadila ta iso tana kumbura baki ta rungume ta ta ce" Mommy damejo ni dai ban yi kewarki ba, ya Amurka?"

"Mi kike cewa Fadila?" Mommy ta faɗa tana ɗago da ita daga jikinta.

"Cewa na yi mun yi kewarki gidan shuru ba daɗi da ba ki kusa."

Murmishi kawai Mommy ta yi dan sarai taji mai ta faɗa, sakinta ta yi Sudas ya iso ya rungume ta yana cewa" Miss you Mom ya hanya?"
.
" Alhamdulillah my Son ina shi Daddyn naku yake? "Bai dawo ba. "To muje ciki..

Ciki suka shiga Auta na manne da Mommy suka shiga ɗakinta, sai ta taga ta shiga wanka kana ta fito tare da ɗauko wayar Mommy ta shiga kallon picture ɗin da ta yi a can Amurka..

Abinci mai rai da lafiya Kandeta haɗawa Mommy ta fito ta zau na akan darning, takaici ne ya kama Mommy ganin dukkansu waya suke dannaw wata ce kawai ki rungume ta Teddynta tana masa wasa,sosai ta yi mamakin ganin yadda Auta ta girma bata mata kukan data saba ba in har ta dawo daga tafiya ta yi ta binta duk inda ta yi banɗaki ne kawai bata binta, yanzu gashi ta dawo kuma sai taga canji daga welcome back ɗin data mata bata kuma kallon inda take ba. " E lalle su Autar tawa an soma za ma 'yan mata" Ta ƙarashe maganar tana murmishi..

"Ku ba za ku ci abinci ba je ko mai? Yamutsa fuska kowa ya yi sai kuma suka tashi suka isa kowa yaja kujera ya zau na, Auta ta janyo babban filet ta cika shi tam da shinkafa da miya ta nama manya-manya, ba mata lokacin ta dinga kamar wadda ta shekara bata samu irin wannan abincin ba..

Sake da baki Mommy ke kallon Auta. "Kici abincin a hankali mana Auta. Jinjina kai kawai ta yi, Fadila ta buga tsaki ta zubawa idanu . Mommy ta juyo dan ta yiwa Auta magana taga wayam kan darning ɗin, baki ta saki tana bin kwanukan da kallo Auta dake zau ne ta yi rashe- rashe tana mayar da numfashi sai zare ido take, cikin ya zama babban kamar mai shigar dan wata huɗu..

Innalillahi! Mommy Alkur'an Auta ta handime komai na kan darning ɗin, dama tun da ki ka tafi take yin wasu abubuwa, mun shiga uku mun lalace! Yanzu duk wannan abincin Auta kin dura shi a cikinki? Kuturu! Gaskiya gaban nan buhu guda za ake dafawa a gidan nan" Cewar Fadila tana tafa hannu..

Miƙewa Auta ta yi shuuu kamar wadda ake turawa suka ga tabar wajan ta yi sama..

Dariya Sudas ya yi ya ce" Auta fa ta haukace Mommy samo mata magani."

"Dole na nemo magani wannan wacce irin masifa ce haka da Magaribar nan? Innalillahi wa'inna ilaihin raju'un! Dama haka take yi wai tun da na tafi? Labari Fadila ta shiga bata tiryantiryan, tafa hannu kawai Mommy ke yi ta miƙe da sauri ta ɗauke mahafinta ta fice a gidan...


Bala mai shayi ƙarfe shadaya daidai ya tashi daga wajan sana'ar shi, sauri yake yi dan ya yi dare gashi gidan shi sai ya bi gindi wata makabarta hakan ya sa yake sauri dan dama matsoraci ne..

Yana zuwa saitin makabartar ko numfashi da kyar yake yi saboda tsoro, sai da ya wuce ya sauke ajiyar zuciya, ya zo gindin wata bishiyar mangwaro ya ji ana surutai sai mamaki ya kama shi yana tunanin wasu yara ne haka suke wasa har wannan lokacin..

"Kai baka isaba ni na rigaka zuwa da minti ɗaya.

"A a nine na rigaka lokacin da na yi nutso a tekun maliya saida na kai can kasa ina hutawa kafin ka zo, taya ma za ka ce ka rigani zuwa?

"To ai kaima lokacin da na isa bangon duniya na kudu sai da na yi hutun awa ɗaya, har sai da na soma bacci kana ka zo kaga ai na rigaka yanzu dai ni na riga amma ka ce wai ka rigani zuwa kasan tekun..

Rikice ne ya rikice kowa na cewa shi ya riga ɗan uwansa.

Jikin Bala shayi tana ya ɗauki rawa dan ya duba har haskawa ya yi jikin bishiyar amma baiga kowa ba a gurin, ji ya yi ana damke sai sautin dukan yake ji, giririf! Kawai yake ji kamar ana dukan ƙarfe.

Cikin Bala mai shayi ne ya bada kuuuuuu bai sna lokacin da ya saki futsari ba, runkuyawa ya yi zai cire takalmansa yaji an zabga masa mari ji kake gauuu.

Wata irin sufa Bala ya yi ya watso kwanar gidansa a guje yana faɗin" Dije! Dije! Dije masa buɗe mini ƙofa Dije kina ina?



_*One love masoya ina sonku irin sosai ɗin nan, ina matuƙar godiya a gareku yadda kuke mini fatan Alkhairi na gode Ubangiji ya barmu tare daku, da wanda nake gani da wanda ban gani ba masoyan ina Alfahari daku a duk inda kuke na fili dana ɓoye.*_



_*Taku har kullum Maman Nusaiba ce*_
[03/12, 21:49] Umma Amjad: _*🧟‍♀️ALJANAR GIDANMU 🧟‍♀️*_





Daga Alƙalamin

_Sarat Alƙasum (Maman Nusaiba)_



_🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION 📚_


*WhatsApp number.+966599791573*

بسم الله الرحمن الرحيم

0️⃣8️⃣


"Dije maza buɗe mini ƙofa ki taimaka Dije na, Innahu Sulaimanu ku kuke ganinmu ba mu muke ganinku ba Dije ki yiwa girman Allah ki buɗe mini ƙofa kar ki rasa haɗaddan mijinki Dije" Ya ƙarashe maganar yana ja da baya ya yi wata irin sufa ya buga ƙofar da ƙarfi gaske ya ci sa'a ta buɗe.. A firgice Dije ta fito daga banɗaki tana kallon Bala, ƙanƙance idanu Dije ta yi cikin masifa ta ce" Kan uban can! Bala waye ya baka izinin buga mini ƙofa kamar ka samu tabin hankali? Wai lafiya ma tun daga ƙofar gida naji kana kirana? Salon iska ta ɗauki sunana ko mayu ayi ta yawo dani aje a lika mini maita, to Wallahi ba ka isaba yau ba za ka kwanan mini akan gado ba kai ɗakin ma za ka kwana ba sai dai ka kwana a shagon shayin naka, ina jinka yau da zaka fita kana ce mini wai juya bana haihuwa,to ka yi da shegiya a gidan nan dan za kaga rashin mutumci yadda baka tunanin maza ka fitan mini a ɗaki ko yanzu na maka ɗan banzan duka a cikin daren nan" Ta ƙarashe maganar tana turashi bakin ƙofa."

"Innalillahi wa'inna ilaihin raju'un! Yake faɗa yana kallon Dije sake da baki, tun da yake da Dije bai taɓa jin ta tanka masa magana ba ko dukanta ya yi bata zuwa gidansu za ta yi haƙuri ta zau na, duk gurin da yake mata bata taɓa tanka masa akan hakan ba, kuɗin cefane sai ya yi wata bai bata ba kawai sai dai ya ce mata ta tafasa ruwa tasha shi ne abincinta, amma yau gashi Dije ce ke masa tsawa har tana cewa za ta masa duka. Anya kuwa ba wani ya zuga mini Dije na ba? Ya faɗa a bayyane..

Kafin ya yi wani yunkuri Dije ta ɗamko hannun shi tana aiko masa harara ta ce" Shin za ka fita ko saina lallasa ka a ɗakin nan?" "Don girman Dije na ki yi haƙuri gamo na yi a hanya shi ya sa, Aljannu fa naji suna muso a tsakanin su wai anje bango duniya da kudu,kuma k.. Bai ƙarasa ba aka ɗauke wutar ɗakin, hankali tashe ya lalibo Dije ya maƙale a jikinta kamar zai koma cikinta. "Kai ka sakeni dalla can so kake ka shiga cikina ko me? Ganin fa yaƙi sakinta ta taƙarƙare ta zuba masa dundu a gadon baya. Ba shiri ya saketa ya dawo bayan yana cewa" Shi kenan na shiga uku sun biyoni har g.. Marin da Dije takai masa ne ya hana shi ƙarasa maganar, dukansa ta shiga tako ina har da ƙafa take sakawa, cikin wata iriyar murya ta ce" Ni za ka yiwa wulaƙanci har kasa hannu kake dukana? Yau saina karya maka hannu da ƙafa."

Ihu Bala yake yana roƙon Dije da ta rabu dashi, ita kuwa sai ma ƙara kaimi take ganin dukan da hannu bai mata ba ta juya gefenta ta ɗauko muciya ta shiga zuba mi shi ita tana cewa" Gobe ma ka sake dukana za kaga mai zan yi maka a gidan nan, ni Ƙawar uwarka ce har ka ɗaga hannu ka dakeni?"


"Waiyo Allah jama'a a kawo ɗauki, Dije nine fa Bala ɗinki ki dena dukana na miki alƙawarin ba zan sake dukanki ba, Dije mijinki ne fa kar ki nakasa ni ki taimaka Dije. Dariya Dije ta yi taja da baya ta dunƙule hannu, Bala na ɗagowa ta kai masa naushi a hanci nan take ta fasa masa hancin. Ihu Bala ya kurma yana sa hannu ya riƙe hancinsa da yake jin kamar ba a jikinsa yake ba, cikin kuka ya ce" Dije kin fidda mini hancin fa, waiyo Dije anya kuwa Dije na ce wadda na sani ko dai an canja mini ita?" Iska ce taso a cikin ɗakin aka ɗauki Bala ana yin royal dashi a saman ɗaki, kallo ƙasa ya yi yaga Dije ce ta ɗaga shi da hannu ɗaya ta ɗaga shi take wurga shi a sama...

"Innalillahi! Dije kasheni za ki yi wai? Ki dawo hankalinki mana nine ba Bala ɗin ki fa.

Sai da ta jijjiga shi ya galabaita sumar da Bala ya yi tafi biyar a cikin wannan yanayin, wani irin juyi Dije ta yi da Bala ta sako shi kan gado tana yin dariya, mari ta zabga masa mai zafi hakan ya sa ya dawo daga sumar da ya yi, ihu ta kurma ya janyo bargo ya lulluɓa da fargo yana roƙon Dije ta dena dukansa. Dif yaji komai ya tsaya cak an dawo da wutar ɗakin, leƙo kansa ya yi yana fatan Dije kar ta kuma masa irin wannan damƙar, wayam ya gani ba kowa a cikin ɗakin mamaki da al'ajabi ta kama Bala, a sanyaye ya tashi daga kwanciyar da ya yi soma duba ko'ina amma bai ga alamar Dije ba. "Dije! Dije!

"Na'am Maigida ka dawo ashe? Wallahi ina ɗakinka ina yin sallar shafa'i da wutiri dan bacci naji yana neman ɗaukeni shi ya sa na tafi can da na gyara ma ɗakin sai na yi sallar, a a wai lafiya naga hancinka a fashe ko bugewa ka yi da wani abu ? Maigida ka yi shuru baka ce mini komai ba?. Bala da ya saki baki da hanci yana kallon Dije bai san lokacin data ƙaraso kusa da shi ba har sai da takai hannu ta dafa kafaɗar shi. Da sauri ta zabura ya ce" Waiyo Allah! Ki yi haƙuri Dije Wallahi ba zan sake dukanki ba."

Cike da tashin hankali Dije ta rungumi Mijin nata, addu'o'i ta shiga tofa masa a kunne tana shafa bayan shi kamar wani ƙaramin yaro, can taji ya shiga sauke ajiyar zuciya yana sumbatu, sosai Dije ta tashi hankalinta ganin Bala a cikin wannan yanayin, ɗago dashi ta yi cike da kulawa ta ce" Maigida wai lafiya kake kuwa?"

"Dije ki yafe mini dukan da ki ka mini ya isa haka ina jin ma kin targada mini ƙafa. "Riƙe hannun shi ta yi ta dube shi ta ce" Maigida yaushe kuma aka yi haka? Ni da kaina zan iya sa hannu na dakeka kamar ban san darajar aure ba? To duka ma nawa nake da har zan iya dukanka ka tsaya kana kallona, ka dawo hankalinka nifa ina ɗakinka ban shigo nan ba sai yanzu..

Da sauri ya kalleta zufa na tsatstsafo masa ta ko'ina, cikin shi ne ya bada kululuuu, miƙewa ya yi cike da tsoro ya ce" Dije zawo nake ji ki rakani yau naga rayuwa Dije ki taimaka karki sake dukana aradu na daku, Dije rakani rakani Dije" Ya ƙarashe maganar yaan riƙe cikin. Kafin Dije ta sauko daga kan gado Bala ya soma sakin zawo a jikinsa, da sauri ta kama hannun shi suka nufi banɗaki, suan shiga ta juya za ta fito ya yi saurin riƙe hannunta ya sa kuka kamar wani yaro ya ce" Dije na karki tafi ki barni Wallahi za ki iya rasani in ki ka tafi daga banɗakin nan." Dije ta rasa abin da yake mata daɗi ta tsaya tare da done hancinta jin wani mugun tsami na bugar mata hanci..

Ranar dai Bala kwana ya yi a bakin banɗaki warwas ya yi a ƙasa yana juyi, ganin abin na yi ne ya cire kayan jikin shi daga shi sai gajeran wando shi ma sai tsami yake, Dije ta rafka tagumi tana kallon Bala, jin bai dena sumbatun kar ta dake shi ba ta tashi ta ɗauko Alkur'ani ta shiga karantawa tana tofa masa a haka suka kwana....
______________

Mommy na fita daga gida gidan Malamin da yake koya mata karatu ta nufa tana kuka, ikon Allah ne kawai ya kai Mommy gidan Malam, tana zuwa ta durƙusa a gaban shi sai kuka take ta kasa ma yin magana..

Malam ya dubi Mommy cike da mamaki ya ce" Azima lafiya? Yaushe ma ki ka shigo ƙasar ne?"

"Baba ka taimakeni Auta na cikin wani hali ka zo muje kaga abin da take yi ,lafiya lau na barta amma na dawo na samu yarinya ta canja, labarin da Fadila ta bata ta zaiyanewa Malam..

"Subhanallah! Lalle lamarin nata kamar mai shafar aljannu yanzu kije gobe ki kawo ta nan inma sune za mu gani.

"Baba da ka zo yanzu dan ni Wallahi na tsorata da abin da na gani, abincin na kusan mutum 10 fa Auta ta cinye kuma duk cikin minti ɗaya yadda kasan iska haka ta cinye tass ta miƙe tabar mu baki buɗe, Baba ka zo muje don Allah kar wani abu ya sameta iafin safen nan ina jin tsoro..

"Ki kwantar da hankalinki Azima babu abin da zai sameta sai wamda ya rubuto mata a shafin ƙaddararta, ki dena jin tsoron komai in sha Allah zan je goben yanzu kinga dare ya yi maigidanki zai iya dawowa kuma kin san halinsa dai , ki kawo ta nan na mata addu'a ko ma mene ne za mu gani goben da izinin Allah..

Haka ya shiga kwantar mata da hankali yana nuna mata duk abin da yafu da Auta sufa dama can rubutacce ne a shafin ƙaddararta dole sai ya faru , ka ba su da ikon da za su canja mata ƙaddararta Allah ne kaɗai zai iya canja mata ƙaddara ba dai mutum ba.. Jiki a sanyaye Mommy ta tashi ta nufo gida cike da damuwa..

Yau tun da sassafe Auta ita ta tayar da Mommy daga bacci tana kukan wai zazzaɓi take ji, hakan ya sa Mommy ta shiryata tsab suka fito palo suka zau na, Kande ta iso ta kalli Auta ta ce" Autarmu ya dai naga kina kuka? Ko yunwa kike ji na kawo miki abinci?" Fashewa da kuka ta yi ta miƙe tare da riƙe cikinta tana kallon Kande ta ce" Anty Kande ki zuba mini abinci dayawa yunwa sosai naje zan ci kaɗan tun da ina jin zazzaɓi kinga jiya har kaina ciwo ya yi ki kawo mini nan kinji Anty" Ta ƙarashe maganar tana zaman 'yan bori akan carpet." Murmishi kawai Kande ta yi ta juya ta nufi kicthen ɗin, Auta ta kalli Mommy ta ce" Mommy bayana ciwo yake ina za ki kaina a bani magani?" Zuba mata idanu Mommy ta yi duk ta kasa gane kan yarinyar, da farko ta ce zazzaɓi dazu kuma ta ce cikinta yanzu kuma ta ce bayanta, kamo hannunta ta yi ta janyota jikinta ta rungume tare da bubbuga bayanta tana mata sannu a haka Kande ta kawo mata soyayyan kwai da bred haɗe da shayi mai kauri ta aje mata a gaban Mommy ta ce" Autarmu tashi na kawo miki abincin kici ko."

Da sauri ta sauka daga jikin Mommy ta sauko ƙasa, ganin abin da ke gabanta ta ɓata fuska kamar za ta yi kuka ta ce" Wannan dan yakushen abincin kamar wata almajira ni dai gaskiya ki kawo mini goman wannan indai har ba rowa za ki mini ba yau" Ta ƙarashe maganar tana cuno baki gaba tare da aikawa Sudas harara da ya shigo yana fito tafiyar ma yana yi yana rawa har ya iso gurinsu.." Shuru Kande ta yi ita kanta wannan cin abincin na Auta yana bata mamaki, ji ta yi tasa kuka tana faɗin aje ayo mata wani, juyowa Kande ta yi za ta mata magana taga ba komai a kwanon ta cinye tass ta miƙe ƙafa tana kukan a ƙaro mata, da sauri Kande ta ɗauke kwanon ta wuce kitchen..

"Allahuna ajurni fi musibati wa'akalifili khairan minha! Lahaula wala kuwwata illa billahil aliyun azim! Ubangiji ka bawa yarinyar nan lafiya wannan wacce irin masifa ce haka muke cikinta? Cewar Mommy tana kallon Auta da take kuka bil hakƙi.. Sudas ya dubi Mommy ya ce" Mommy ki dena damuwa za ta dena yanzu dai kuje Asibitin a lafiyart a gani, kinga daga nan sai asan abin yi." "Ba dole na damu ba Sudas yarinya gaba ɗaya ta canja komai nata ya canja Kamar ba Afra ta ba da na sani a baya.. Kande ta soye mata kwai guda 12 ta ɗauko wani bred ɗin da shayin ta kawo mata, da sauri ta amsa ta shiga ci tana jinjina kai , kafin minti ɗaya tuni ta cinye ta miƙe tana gyatsa ta nufi banɗakin palon ta wanke hannunta kana ta fito, kallon Mommy ta yi ta ce" Mommy muje asibitin kinga har yanzu cikin nawa bai dena ciwo ba muje a dubani" Ta ƙarashe maganar tana kamo hannun Mommy dake zau ne ta saki ba ki tana kallon ikon Allah."

Ba shiri Mommy ta miƙe suka bar gidan.

Daret wajan Malam ta nufa da ita, tun a hanya ta yi bacci hakan ya yiwa Mommy daɗi ta yi saurin ƙarasawa gidan Malam. Sai da isa kana ta tasheta , da ƙyar ta tashi tana miƙa suka nufi ciki, sake da baki Auta ke kallon gidan har suka isa inda Malam yake zau ne a wata ruwa. Barka da zuwa ya musu kana suka shiga ita dai Auta na bin Mommy da kallo, za ma suka yi suka gaisa kana Mommy ta ce" Malam gata nan na kawo ta." Kallon Auta Malam ya yi yana nazartata da kyau, addu'a ya yi a ciki ruwa ya miƙawa Auta ya ce tasha, kamar ba za ta amsa ba sai kuma ta amsa tana yatsina fuska ta sha kaɗan ta aje gefe tana hura hanci..

Karatu Malam ya soma yi yana yi yana mata tofi, yafi minti 20 yana karatu amma shuru ko gizo Auta bata yi ba sai ma wasa zoben hannunta take yi, abin ya bawa Malam mamaki ya tsayar da karatun ya dubi Mommy ya ce" Gaskiya Azima babu komai a jikin yarinyar nan, in ma tana da su to ƙila sai an ɓata mata rai ne suke zuwa, yanzu dai ba komai a jikinta inda akwai da tuni sun yi magana a Karatun da na yi yanzu, abin yi kawai zan ke mata rubutun addu'o'in kariya daga shedanun aljannu da duk wani abin cutarwa sai take sha tana shafe jikinta da shi.."

Jinjina Mommy ta yi ranta jiki a sanyaye ta masa sallama suka dawo gida. Mommy na zuwa ta shirya ta fito dan tana da meeting a office ɗin su, a palo ta samu Daddy Fadila na gefe tana

1 Comments On ALJANAR GIDANMU
avatar
taskar

1 year ago

Reply

Good

Please Login or Register in order to submit comment