Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

To shi wannan kuma waye shi? Kuma a ina zan ganshi a zahiri da nake mafarkin tsayin shekaru huɗu, da sauri ta miƙe ta kalli agogon ɗakinta taga ƙarfe 7:30pm salati take tana ambaton kalmar Astagafurullah ganin lokaci ya tafi bata yi sallar Magariba, jikin bango ta dinga bi har ta shiga banɗakin....
_________________________
Amra na zau ne tun da ta gama magana da Auta take nazarin maganarta Aliyu dake kusa da ita ya ce" Yaya Amra nifa na gaji da dakatar damu da kike yi akan ahalin yarinyar nan gaskiya, Yaya Amina za ta iso na jiyo ƙamshinta yau ɗin nan za mu yi duk abin da ya kamata sannan maganar mai bibiyar rayuwarta ina iya bakin ƙoƙarina amma har yau na kasa gano shi, tabbas wannan ko a ina yake mugun shu'umi ne na gasken gaske ace duk ƙarfinki ki ka kasa gano shi to taya ma ni zan gano shi yanzu d... "Ya isa Haidar! Ta faɗa da ƙarfi cikin irin wata murya dake nuna ranta yakai mataki na ƙarshe a ɓaci, tuni idanunta suka canja kala cikin wata irin murya ta ce" Zaki ka daina tunanin na hanaka yi wannan abun ina son ne na gano wanda yake tare da ita daga baya sai mu cika alƙawarin da muka ɗaukarwa iyayenmu." "Haba Yaya Amra taya za ki ce wai sai kin gano kana za mu cika alƙawarin da muka daukarwa iyayenmu shekaru da dama? Nidai in za kibi magana kawai mu fara cika da alƙawarin da muka ɗauka inyaso daga baya komai ba sai ayi, ko kin manta yadda girman alƙawari yake ne? " A a Zaki ban manta ba amma ku mini uziri ina so mu taimaki wadda ta nuna tausayawarta a garemu duk da bata san mu ko su waye ba, mu taimaki rayuwarta mu rabata da wannan ɓakin azzalumin da yake tare da ita." Aliyu ya koma suffar Zaki ya yi kururuwa ya yi wata irin sufa ya nufi kan Amra,ita kuwa ta tsaya tana kallonsa har yazo kusa da ita sai kuma ya yi baya ya kuma yin kukan Zakuna kana ya koma gefe yana huci, Amra ta matso kusa dashi ta sunkuya cikin tausasa murya ta ce" Zaki kada ka yi fushi da Amrar ka ka mini uziri ni ban halaka yin abin da kake so ba, idan za ku iya aiwatar da komai ba tare dani ba to ku yi har lokacin da zan gama bincikena na dawo cikinku ka yi haƙuri ɗan'uwana" Ta faɗa tana shafa kan shi." Sunkuya da kai Zaki ya yi hakan ya sa Amra ta fahimci ya ji maganarta ta miƙe ta fice a ɗakin..
_________________________

Hon yake ba kakkautawa kamar wanda ake neman rayuwar shi, a guje Maigadi ya fito daga banɗaki ya iso ya buɗe masa ƙofar jikinsa na rawa yana addu'a Allah ya sa kar a masa cin mutumci. Yana gama parking ya fito cikin sauri ya nufi Maigadi bai tsaya yin wani abu ba ya kife shi da zazzafan mari mai shiga jiki, cikin tsananin ɓacin rai ya ce" Saboda ka rainani ina ta hon amma kaƙi buɗe mini ƙofar kamar ka samu gidan tsohonka ko?" Maigadi ya durƙusa ya ce" Ka yi haƙuri Alhaji Wallahi cikina ne ya ɓaci shi ne na zaga banyan gida na shiga kenan naji hon ɗinka na farko amma ka mini afuwa." "Matsiyacin banza kawai ni za ka rainawa hankali to ka yi ta albashinka na wannan watan in kaga na baka kuɗi sai watan gaba .. Hankali Maigadi ya yi matuƙar tashi jin abin da Daddy ya faɗa ya dinga ba shi haƙuri kamar zai masa sujjada amma Daddy sai ma zaginsa da yake juya gefe yana faɗin" Kai Garbati! Garbati! .A guje Garbati ya iso gareshi jikinsa na rawa ya durƙusa ya ce" Sannu da zuwa Alhaji."

"Ba wannan na tambayeka ba da zan tafi mai na ce maka? Shuru ya yi yana nazari ya ɗago kai ya dubi Daddy ya ce" Alhaji ka ce na sare wancan shukar data fito a gefen fulawar can." "To ya aka yi yanzu kuma nake ganinta baka sareta ba? "Ayi haƙuri Alhaji ayyukan ne suka mini yawa yau sai bayan Isha'i na gama goge kayanka..
"Ok saboda ka rainani shi ya sa daka gama gagara baka sare ba ko? Garbati ya ƙara sunkuyar da kansa ya ce" Alhaji naga dare ya yi ne shi ya sa ban sare ba amma gobe In sha Allah da safe zan sare." Daddy ya watsa masa wani kallo kana ya ce" Yanzu ƙarfe nawa da kace dare ya yi?" Garbati ya duba agogon hannunsa ya ce" Ƙarfe 10:30pm yanzu."
"Gobe in na fito naga an sare an gyara gurin bana son komai inba fulawowin nan ba a harabar gidan nan, ka kiyaye dan zan ɗauki mataki mai tsauri in kana tsallake maganata.. Ajiyar zuciya Garbati ya sauke ya ce" To in sha Allah Alhaji." Tsaki Daddy ya yi kana ya wuce ciki yana ta masifa akan kin sare bishiyar dake jikin fulawar..

11pm Auta ta fito daga ɗakinta ta tarar da su Sudas zau ne suna bin baitin waka ita kuma Fadila tana gefe ta ƙurawa TV idanu tana kallo hannunta nade da bandeji, girgiza kai ta yi ta iso ta zau na ta ɗauki remote ta canja ta kawo wani shiri a wata tasha da ake yi kullum da dare daidai wannan lokacin..

Fadila ta ƙundumo wata kalar ashariya ta ƙundumawa Auta tana watsa mata harara ta ce" In ba ki mayar mini gurin da nake kallo ba saina wurga miki wannan takalmin dake kusa dani." Banza ta mata ta ci gaba da kallon ta sai ga Daddy ya iso palon yana faɗin" Ke kuma lafiya kike ɗaga murya? Ya ƙarashe maganar yana zama." "Daddy kana gani fa da ka shigo ina kallon wani shiri a MBC2 amma wannan yarinyar daga zuwanta ta canja mini gurin da nake kallo dan taga hannuna bai warke ba take mini rashin kunya." Haƙuri Daddy ya bata ya mayar da kanshi kan wata takarda dake gabansa hakan ya kuma baƙanta ran Fadila ta cika ta yi fam Sudas na mata dariya ta wurga masa takalmi ya cafe yana mata gwalo..

Hankalinta ta mayar ga kallon ganin yadda wata majiya take bin wata yarinya a tsakiyar daji, wani irin ihu yarinyar ke yi hakan ya sa Fadila ɗago da kanta har da su Sauban. Ana wuce gurin aka kawo gurin wani daji mai duhuwa sai wani irin kuka-kuka dake tashi, wani irin doguwa mace suka gani fuskarta babu ƙyan gani bakinta na zubar da jini mai haɗe da wani irin ruwa baƙi, hannuwanta dogaye har jan ƙasa suke ƙafarta sak ta Raƙumi. Jin sautin ya yi yawa ya sa Auta ta soma ƙoƙarin rage volume aka yi wani irin tsillata bayan kujera , hannu aka miƙo daga cikin TV aka nufi Sudas da ya ƙame kamar Soja na amsar horo a filin koyarwa ihu Fadila ta kurma bata san lokacin data haye kan cinyar Daddy ba...




_*Taku har kullum Maman Nusaiba ce.*_

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


1 Comments On ALJANAR GIDANMU
avatar
taskar

1 year ago

Reply

Good

Please Login or Register in order to submit comment