Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

1❤️💛💚💜💙
Lokacine...
❤️💛💙💜💚


® zuwairat (ummumaryam)


1️⃣

Free page

Alhamdulillah...

Dedicated to my anty...

Cikin wata falo dake dauke da wasu Manyan mata akwatuna né na lefe akalla guda goma, sai budewa ake Ana yaba irin Kayan da aka zuba cikin akwatin,
"Oh wannan yaran da kashin arziki suke...ji wannan Kayan kaman bazaa mutu ba..." Inji wata middle age woman, wata mata ce ta sauko face dinta dauke da medical glasses ta saki murmushi for a second sai kuma ta daure face, da gani itace matar gidan but  am surprised why face dinta ke daure haka while wayanda ke duba lefe sai faman tofa albarkacin bakinsu suke, gefe daya ta koma ta zauna Tana latsa phone din hannunta Tana lumshe idanuwa, daya daga cikin matan da suke duba lefe ta Mike , da ganin matar kasan she's her sister, dafa shoulder dinta tayi tace
"Wai sister meye haka?..Dan Allah ki saki ranki pls ...kar a gane something is wrong with you.." Matar ta fada mata hannunta kan shoulder din matar gidan, idanuwa matar Ta lumshe tace
"Hmmmm wa ke bai San something is wrong ba?... Duk Wanda yasan ni yasan family din nan yasan something is wrong..." Matar Bata karasa ba ta Dora hannu kan lips dinta,
"Dan Allah ki bar cewa something is wrong...ki tuna wacce aka kawo lefenta ma is your daughter...me zata  ji if you show you're not happy..." Ta fada mata cikin lallashi, matar gidan Dan Dora Kai Tana a hannunta sai hawaye, idanuwa sister dinta ta zaro yana cewa
"Pls ki Bari mana...pls ki Bari...nasan nan cikin mu babu bakuwarki amma pls me Aisha zataji.,she will feels you love Maryam more than her..." Matar ta fada cikin lallashi, sauran matan dake kallon lefe mikewa sukayi suka dawo kan matar dake kuka suka fara yi mata fada,
"Wai meye haka?.. Ke bakisan kaddara bane?... Duk sanda aka zo biki gidan nan sai kinyi wa mutane hauka...bakisan komai sai Allah ya yarda ba.." Wata babban mace Tafada mata cikin tsananin fada, ahankali matar dake kuka ta daga Kai ta kalli babban matar tace
"Yaya bazaki gane ba...mami wuya take sha a hannun kaka...Wallahi in har aka Kai mata wannan lefen ta gani sai tayi mata tas kaman ita ta Hana kanta mijin aure...Wallahi duk sanda ta ganta sai tayi mata gori..." Bata karasa ba yaya tace
"Dalla rufe mana baki... But taje tayi mata gorin mana..ai she's her granddaughter..kuma Banda abinki gori har wani Abu né?... Yanzu kin zauna kina hawaye in mami ta shigo ta tarda ki haka sai tazo kuy tare kenan?... " yaya ta fada mata, cikin kuka matar gidan tace
"Wallahi yaya na gaji...nan da wata biyu zan aurar da autata while yayarsu Tana zaune...Wallahi Sam bani da kwanciyar hankali har sai ranar mami ta bar gabana..." Matar ta fada cikin kuka, cikin rarrashinta wata yace
"Sister kiyi hakuri mana...kindai San babu irin kokarin da bamuyi kan almaranta ba...kullum cikin Rokan Allah muke kan wannan alamarin...sai mu jira muga ikon Allah..." Matar ta fada mata, shuru mai kuka Tayi amma tears basu daina fitowa ba, ba komai take tunani ba Illah first daughter dinta, her happiness her joy her pride, Tana mugun kaunar ta with her life, su biyar ta Haifa, the first born itace Maryam amma Ana kiranta da mami, she's 32 Yanzu, followed by yazid Wanda Yanzu he's 29 then asiya 26 Tay aure da yaranta biyu, sai Fatima 23 itama tayi aure da 1 child sa auta Aisha wacce is 21 one itace zatayi aure Yanzu amma ita first born din har yau bata yi aure ba, kome dai anyi, anyi sadaka, anyi adua anyi komai amma still shuru, bawai mazan basu Sonta ba, amma da Anzo wajen aure sai komai ya watse.  Horn akayi Kofar gidan matar dake kuka tayi saurin cewa
"Itace..." Tafada Tana mikewa da sauri, hanyar upstairs tayi da sauri while masu kallon lefe suka koma kallon lefen kaman nothing happened,

A bakin gate kam wata black Jaguar ce tsaye wata fara yarinya na zaune ciki Tana latsa horn, daga gefen ta kam bag dinta né sai farar riga irin ta doctors, face dinta dauke da glasses Dan siriri, face dinta look so beautiful and innocent, gaban goshinta kwance yake da wasu kananun gashi,  ganin tayi horn har sau uku ba'a bude ba yasa tayi relaxing cikin motar Tana cewa
" I know you heard my horn...ko me kake yi ka gama kazo ka bude..." Tafada cikin wani irin sexy voice, Tana lumshe idanuwan ta dake kama da na Mai Jin bacci, bayan kaman minti daya taga an bude gate din, Mai gadi né ke tura gate din kanshi daure da towel alaman daga wanka ya fito, Tana ganin an bude ta tada motar ta ta shigo ciki Tana tuki ahankali, Mai gadi ya dawo saitin glass din motar yace
"Hajiya kiyi hakuri Ina wanka né..." Yafada yana dariya, Dan murmushi ta saki Wanda yasa gefen cheek dinta lotsewa, wajen jerin cars ta samu available space tayi parking motar ta, bude motar tayi ta fiddo wasu Vincci slippers ta ajiye kasa Sannan ta zira legs dinta ciki ta fito rike da bag dinta, Maigadi dake maida gate ya kalleta tare dacewa
"Sannu da zuwa Doctor..." Ya fada mata yana kame mata kaman yanda ya sama as usual, kallon shi Tayi ta saki yar dariya before saying
"Ka bar wannan fadancin ban rago komai ba yau..." Tafada cikin dariya zolaya, Maigadin marairacewa yayi kaman zaiyi mata kuka yace
"Ai ba komai Doctor...da akwai gobe..." Yafada yana tale baki kaman zaiyi kuka, dariya Tayi tare da girgiza Kai  Dan koma bayan motar ta bude ta dauko wata Leda ta mika mashi, Da gudu middle aged man din yazo ya amsa yana cewa
"Anty na Allah ya biya maki bukatunki na alkhairi...Allah ya ya baki duk abinda kikeso duniya da lahira..." Yafada yana yaga ledar da hakorasa, dariya tayi tace
"Ameen..." Tafada Tana  kama hanyar falo, Maigadi da saboda dadin da doctor ke kawo mashi kullum yasa ko anyi Abincin rana aka bashi bai ci sai har Doctor ta dawo yaga in bata kawo komai ba sai yaci ya samu wurin ya zauna ya ware suyar data sha cabbage da su carrot ya lumshe idanuwa yana shakan kamshin Nama ya dauko daya ya Kai baki yana santi. Dan juyowa tayi ta kalleshi ta saki murmushi Sannan ta hau stairs uku ta isa varender, kofa falon ta bude walking like a princess Don ko kadan babu hayaniya tattare daita, she looks so calm and peaceful until she steps into the falo, dukkan matan dake falon juyowa sukay suna kallon ta some wearing a smile while others a wearing a sympathetic look, itama murmushi ta saki idanuwanta kan jerin boxes dake falon, gabanta né yayi mugun faduwa data tuna yau né za'a kawo lefen Baby wato Aisha, nan take face dinta ya Chanza but she's trying to smile, karara abinda ke cikin ranta ya bayyana a face dinta,
"Mami har kin taso?.." Yaya elder sister din mom dinta ta fada, Dan murmushi ta sake saki Sannan tace
"Mommy Ina wuninku?.." Ta fada sounding calm, ni Kaina I was surprised danaji an kirata mami, alaman itace wacce mom dinta ke kuka kan she's 32 amma ba aure, Nikam she don't look 32 to me, duk da Tana da weight daidai and her height is average she look so beautiful and stunning,
"Lafiya lau " suka amsa mata suna kallon ta, ita kuma ahankali ta shigo tsakiyar falon Sannan tace
"Mommies kuna Jin dadin ku..." Tafada cikin zolaya trying to look normal even though Tana tunanin Yanzu her last baby sister will be married in the next two months leaving only her and her immediate younger brother,
"Ke dai ce Mai Jin dadi..." Inji daya daga cikin su, dariya tayi Tana kokarin maida tears dinta tace
"Bari in hau upstairs and freshen up...zan sauko Yanzu..." Tafada Tana Kama hanyar stairs,  basu ce komai ba sai tausayinta daya cika ransu saboda sunga  what she's trying to hide, Tana kaiwa stairs na uku  ta saki tears, kawai she just let them out freely like never before, da sauri ta wuce dakinta da gudu ta shige ta kulle kofa Sannan ta shiga bathroom ta zauna ta dinga kuka, kuka tayi like never before Don dukda Tana kuka almost every day because of her problems nayau yafi na kullum, she cried and cried and cried, she can believe her baby is getting married and, the baby she is eleven years older than, the baby da itace tamkar mom dinta saboda yanda take Sonta is getting married and still leaving her behind in their parents house
"Inna lillahi wa'ina ilaihi rajiun..." Tafada cikn matsanacin kuka,
"Ya rabbi meye laifina?... Ya rabbi why do you want me to be a laughing stock a cikin family...ya rabbi komeye laifina pls forgive me,,,this punishment is too heavy for me...ya rabbi ka garfata min..." Tafada crying very loud knowing too well that nobody will hear her cry, the bathroom has been a perfect pls to shed her sorrowful tears, kawai tunani take Yanzu in the next one year her baby sister will be a mother while she's here yet tobe married, sai da Tasha kukan ta ta koshi Sannan ta sakarwa  kanta ruwa ta fito daure da towel, wata karamar box ta dauko daga karkashin gado ta bude ta dauki pills Tasha, it's a pain reliever pills, duk yanda take Jin zafi a heart dinta data sha sai ta samu sauki, bayan ta sha ta koma bakin gado ta zauna duk gashnta a hargitse a face dinta, ahankali ta tura su baya ta Mike ta taka zuwa gaban mirror tayi tsaye Tana kallon kanta, ba yabon Kai ba tasan she's beautiful, she's so beautiful that she always thank Allah for making her this way, everything about her is moderate, ba'a ce mata short then you won't call her tall, her skin color is so silky radiant, Tasan the problem is not from how she looks, at times Tana ganin matan da ko Rabin kyauwunta basu dashi d cute hubbies dinsu sai tace
"I wish me..." Take fada cikin ranta, ahankali ta Dan Shafa bismid cream dinta Sannan ta saka doguwar rigar material ta saka ta Dan kwanta saboda kar a gane tayi kuka, she's so good in doing that, wato pretending nothing happened, pretending she's alright even when she's dying, Kara mikewa tayi ta je tayi unlocking door dinta Sannan ta kwanta, bayan kaman minti talatin da kwaciyanta aka Kira sallah asar, mikewa tayi feeling strong ta shiga bathroom tayi alwallah tafito tayi sallah tayi adua as usual Sannan ta tsaya gaban mirror ta karewa eyes dinta kallon ta tabbatar she looks alright Sannan ta fita kan babu komai, hanyar dakin mom dinta ta nufa tayi sallama Tana bude Kofar, mom dinta dake zaune kan praying mat looking weak ta daga Kai with a smile ta kalleta Sannan ta mika mata hannu Tana cewa
"My jewel har kin dawo?.." Ta tambayeta cikin so da kauna, ahankali ta taka ta zauna kusa da mom dinta ta Kama hannunta Tana cewa
"Yes mommy...Ina wuni?.." Ta gaisheta feeling so happy saboda duk yanda ranta ya bace in har zata gan mom dinta sai taji wasai, kullum tunanin is what will she have done without her mother, her mother never give up on her even for a minute, kullum she's behind her, kullum cikin petting dinta take, at times Tana tunanin kilan saboda situation dinta take mata haka saboda kar taji komai amma kuma in taga yanda mom dinta keyi da sauran yan gidan kasan love is in her blood, she so much loves her children,
"Yau kin dawo da wuri..hope you're alright..." Mom dinta ta tambayeta kaman  wata karamar baby,
"Mommy yau babu aiki da yawa...kuma Ai na Dan dade da shigowa...har nayi wanka nayi sallah..." Tafada hannunta cikin na mom dinta,
"Tou abinci fa?.." Ta tambayeta
"Mummy am not hun...." Bata Bari ta karasa ba tace
"Aa...muje...kici abinci..." Tafada mata Tana kokarin mikewa saboda kar taga tear dake taruwa idonta,
"Mum anjuma zanci...after magrub..." Tafada Tana jawo hannun mum dinta, komawa tayi ta zauna zata bude baki tayi magana akayi sallama tare da bude Kofar, yazid né ya shigo,
"Mommy and aunt...good evening..." Handsome cute guy din Yafada yana shigowa dakin, amsawa mom tayi wearing a lovely smile Sannan mami tace
"Sannu da dawowa..."
"Aunt ya akayi kika Rigani shigowa yau?..." Ya fada mata yana gefensu, he's the only boy and ya Saba da zama cikin mata, kome zaayi tare dashi ake zama ayi, three years ke tsakanin shi da mami amma he calls her aunt, the whole entire family dinsu suna da Wannan respect din ga junansu, ko one month mutum ya baka dole ka saya sunanshi ka kirashi da aunt, yaya, brother da sauransu, family dinsu is among the largest and richest a family a Kano state, daka ce mai waazi family an San su, Maza har so suke su yi aure a family din Don su samu garagbasa saboda yanda suke hada yaran su da angon goma ta arziki,
"Kawai babu aiki sosai a office...how was your day?.."
"Hectic...na dawo kuma Yanzu am going out again..."Yafada yana lumshe idanuwa cikin gajiya,
"zuwa Ina kuma?.." Mom dinshi Ta tambayeshi
"Suhail né zai dawo...yace dole ni zan daukoshi daga airport..." Idanuwa mom dinshi ta zaro Sannan tace
"Wai har ya gama karatun?.." Ta tambayeshi
"Eh Wallahi...ya gama..."
"Oh ikon Allah kaman jiya fa ya tafi...Alhamdulillah...saidai Yanzu ganinka sai ahankali tunda besty is back..." Mami Ta fada,
"Ai I can't wait to see him...dukda he's angry at me wai banzo Lagos na tarbeshi ba kafin mu taho tare..."  Yafada yana mikewa,
"Kaci abinci né?.." Mommy ta tambayeshi,
"Aa Bari in naje chan zanci..." Yafada Sannan ya bar dakin, bayanshi suka bi da kallo both wearing a smile.

Marigayj alhaji Muhammad Mai waazi is a great man of honor, yana da mata hudu inda ko wacce mata sai da ta haifi yara goma plus, family house dinshi is well known by prominent people saboda shi babban mutum né Mai halin kirki kafin ya bar duniya, kafin ya bar duniya babu abinda ya fadawa yara shi sai dai kar su kuskura su bar zumunci nor matter what, Sannan in ba dole ba bayason duk zuriar shi suyi nisa da juna, and Alhamdulillah dukda bai duniya yaranshi da suka rage su 37 basu bar zumunci ba Don duk end of the month sai anyi family meeting inda ko Ina kake an nor matter how busy you are dole kazo da family Dinka, except in Baka country din zai wuceka, duk matan alhaji Mai waazi sun rasu sauran daya tal wacce suke Kira da kaka, wato mahaifiyar dad dinsu mami, she's the youngest wife of alhaji Mai waazi, Yanzu she's the controller of the family affairs, ko fada akayi a family itace Mai sasantawa, Tana zaune né a makeken gidan alhaji Mai waazi, duk yaran  suna respecting dinta tunda bata juyawa kowa baya ba, she takes all as her own amma don't get in trouble with her, she's as hot as fire Don duk family meeting da za'a yi a gidan akeyi itace a head table, dukda She's old she knows how to handle duk Wanda yayi ba daidai ba hakan yasa duk tsoron yin laifi suke daga yaran har jikokin, duk family din zamansu is so sweet and suna supporting din juna sai dai matansu Wanda suka auro daga waje ke gulma da small talks Wanda ba'a rasawa a duk family.

A airport Karfe biyar jirgi ya iso daga Lagos, mutane suka sauko cikinsu har da wani saurayi Mai shegen kyau siriri dogo fari tas, rike da bag din puma, yana sanye da dark blue jean sai red polo Wanda ya amshi jikinshi kaman hauka, face dinshi dauke da glasses baki, tafiya yake cikin kwanciyar hankali, bayan ya fito daga cikin airport ya taho hannunshi daya rike da bag duk babe din data ganshi sai  ta sake kallon shi for the second time, wannan suhail kenan, the cutest of the waazi's family kaman yanda ake ce mashi, yazid dake zaune bayan motanshi na ganinshi saurin direwa daga bayan motar ya nufo shi, suhail na ganin shi ya wani kauda Kai kaman bai San da kowa ba wajen, dariya yazid yayi yasan he's angry at him
"Cutest meye haka Baka ganni bane?.." Yazid Yafada yana dariya, suhail cire glasses dinshi yayi ya kalleshi from head to toe Sannan yace
"Do I know you?.." Yafada yana rolling idanuwa kaman mace, dariya yazid ya sake yi yana cewa
"Wallahi Baka da mutunci...ko abinci banci ba ...direct daga offfice na wuto daukan ka shine kake yi min haka?." Bai Karasa suhail yaja tsoki before saying
"Do you think saying that will make me think am important to you?....you left me stranded in Lagos..." Yafada cikin wata husky and sexy voice, dariya yazid yayi before saying
"Wane irin I left you stranded...ai I never told you zanzo..." Bai karasa ba suhail ya katseshi dacewa
"You see?... Exactly why I said you don't fucking care about me...na bar kasar nan for the pass four fucking years and na dawo bazaka iya zuwa Lagos tarbata ba?.." Dariya yazid yayi da karfi saboda yanda yake cewa fuck this fuck that Sannan yace
"Allah kaka taji ka kana wannan fuck din sai kaci ubanka...Dalla give me your bag..." Yafada yana Jan bag din daga hannunshi, rungume juna sukayi suhail yayi mashi kiss a wuyanshi yazid yayi saurin janyewa yana cewa
" kazama Dan iska Wallahi...Dalla mu tafi gida..." Yafada yana bude mota, shigewa yayi shima suhail ya  shige tare da relaxing.
"Wallahi I miss you..." Inji suhail
"Anya ka kaini?.." Yazid ya amsa mashi. Suna cikin hirar nishadi suka iso gida, horn yayi a bakin Kofar aka bude mashi gate, mutane né sunfi su shabiyar a compound din , mostly yanmata né daga family dinsu wayandan suka San da zuwan shi sunzo yi mashi Sannu da zuwa, yana fita daga cikin mota suka tafi riiii saboda yi mashi Sannu da zuwa, kaman wani yaro yayi saurin komawa bayan yazid,da yazid yayi step shima sai yay step, hannu ya dinga daga masu yana cewa
"Ji wannan yaran sun zama manya...abun ba wahala..." Ya fada yana leko su, sai kallon shi suke suna yi mashi Sannu da zuwa
"Weird fellows..." Yafada under his breath while smiling at each and everyone of them,.


Share
2❤️💛💚💜💙
Lokacine
❤️💛💚💜💙




® zuwairat (ummumaryam)


2️⃣



Free page



Dedicated to my anty, lobi  you die


Haka ya dinga boyewa bayan yazid yana daga masu hannu yana murmushi while shi yazid yana dariya har suka isa falo, nan ma wasu families né zaune suna jiran shigowan shi, wata mata na gani Baka Mara tsawo sosai ta taho da saurin ta, da gudu suhail ya fada jikinta yana kissing face dinta, da sauri matar ta tureshi Tana goge face dinta Tana cewa
"Wallahi sai kaci ubanka..." Tafada but laughing dariya duk mutane dake falon sukayi yace
"Haba mommy shikenan haka zaki tarbeni?.." Yafada kaman zaiyi kuka, dariya Jin dadi ta saki ta mika mashi hannu alaman yazo, ahankali ya Kama mata hannu ya rungume ta,
"Mommy I miss you so much..." Yafada mata,
" Nima haka....ya kake ya hanya?.."
"Alhamdulillah mommy.." Ya fada mata wearing a lovely smile,  Dan juyawa matar Tayi taga yazid, nan take face dinta ya Chanza for a second Sannan kuma ta saki murmushi which is clear its not deep,
"Mommy Ina wuni?.." Yazid ya gaisheta
"lafiya..." Ta amsa mashi atakaice Sannan ta juya ga suhail tace
"Wai meyasa kaki azo daukanka?.. Wa ya daukoka?.." Ta tambayeshi kaman bata ga yazid rike da bag din suhail ba,
"Ai mommy besty ya dauko ni...wai Inna abba?.." Ya tambayeta,
"Bai dawo daga office ba..." Ta amsa mashi. Sauran family dake cikin falon gaisawa sukayi da suhail ya amsa masu looking so happy amma ko kadan bai son wannan never ending greetings,  bayan sun gama gaisawa ya shiga part dinshi tare da yazid yayi wanka sukaci abunci ya suka koshi Sannan ya kalli  yazid yace
"Muje gidansu humaira.." Mika yazid yayi yace
"Wallahi bacci nake ji..." Bai karasa ba suhail yace
"Aa babu wannan zancen..Dan Allah muje mudawo..I can't wait to see her...it's been a while,,,pls..." Ya rokeshi,  kaman yazid baiso ya Mike ya dauki mukullin motarshi suka fita zuwa gidansu humaira...humaira cousin dinsu ce, wato yar kanin baban yazid, daman dad din yazid da dad din suhail are not from the same mother, kowa da uwarshi amma dad dinsu daya, humaira is suhails love, suna kaunar juna sosai kaman they can't stay without each other, a family humicute ake kiranta saboda suhail, suhail yaso ya aureta kafin ya tafi karatu abroad amma she's just 16 lokacin, shi kuma 25, duk haukar da yayi dole ya hakura saboda family dinsu basu yarda su aurar da yarinyar da bata haura 18 ba, saboda hanashi aure da akayi yasa har yau yake Jin haushin kaka saboda itace tace bazaa yi ba wai dole subi doka,  bayan sun yi tafiya for like forty minutes yazid ya tsaya a wata gate yayi horn, Maigadi né ya bude ya shiga yayi packing suka fito, gidan na dauke da parts buda uku, babban ciki suka nufa, sallama sukayi falo suka shiga matar gidan da wasu family suna zaune
"Cute Yaushe ka dawo?.." Inji wata cikin mutanen falon,
"Yau...ban dade da dawowa ba..." Yafada cikin respect, basu dade da shigowa ba wata very pretty slim girls  dake sanyi da skirt da Riga na atampa ta sauko daga upstairs da sauri Tana cewa
"Yaya Sannu da dawowa..." Suhail daga  Kai

Please Login or Register in order to submit comment