Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Singlet ɗin dake jikin sa, ya fito ya wuce ya shiga motar sa ya bar gidan, a cikin mota in banda tsaki da yake saki babu abinda yake yi, kaso mafi rinjaye na zuciyar sa yana ga Ɗahira, ya rasa meyasa zuciyar sa ta kasa nutsuwa da halin da ya saka ta, yana ji a jikin sa tabbas tana wani hali a sanadiyar Text ɗin da ya tura mata, amma ya zai yi? Bazai iya zuwa ya same ta ba, bazai iya jure ganin damuwa a kyakykyawar fuskar ta ba, ya gummaci ƙaurace mata har sanda komi zai dai-daita. Lumshe idanuwan sa yayi yana buɗe wa sai ga hawaye sun zubo masa a kunci, hannu ya saka ya share yana jan numfashi cike da takaicin Mahaifiyar sa, zuciyar sa sosai take mishi ƙunci fiye da tunanin mutum, yana ji a ransa bazai iya jure wa ba, bazai iya auren kowa ba face Ɗahira, dole ya sake yi wa mahaifiyar shi magana, ko zata iya tallafa wa rayuwar sa, Allah ya gani ba ya ƙaunar yarinyan nan da za'a liƙa masa, sannan kuma bazai iya zuwa ya tunkari wata ɗiya mace da sunan so ba, bare har ya iya auren ta, ita dai Ɗahiran da Hajja ba ta so ita zuciyar sa ke so..


      Be fasa tunanin sa ba har sanda ya dangana ga airport ɗin, tunda ya faka motan ya hange ta, sabida kasancewar ta doguwar mace, idan har ta tsaya cikin mutane nan da nan ake iya gane ta, ga ta fara kuma tana ƙara wa dana kanti

Ya ɓata lokaci cikin motan kafin yaja numfashi ya buɗe ya fito, yana hangen ta sai faman waige-waige take yi tana duba agogon dake ɗaure a tsintsiyan hannun ta. Lumshe idanu yayi ya sake buɗe wa a kanta, kamar bazai taka ya isa wajen ta ba, sai kuma ya daure cike da baƙin ciki ya nufe ta, fuskar sa babu ko alamun walwala

Sai da ya dangana ga inda take tsaye, sannan ne ta hange sa, ai nan ta saki murmushin da ya bayyana haƙoran ta, wanda da gani kasan tana cikin tsantsan farin ciki, kiran sunan sa tayi tun kafin ya ƙariso

Sai ya kau da kai yana sake ciccin magani, ya tsaya cak a wajen

Ɗaukar jakar ta tayi ta nufo sa tana sake washe baki, tana iso wa wajen sa ta soma gaishe sa cike da fara'a, amma yanda ya amsa mata ne sai walwalan ta ya ragu

"But yaya lafiya dai ko?" Tayi masa tambayar tana kallon sa

Be ce mata komi ba ya juya ya nufi motar sa

Sai ta tsaya kawai tana kallon sa baki sake, duk da ta san ba ya son ta amma ai suna mutunci sosai ba kamar yanda ya nuna mata haka ba, "so what's wrong with him?" Tayi wa kanta tambayar har yanzu tana tsaye a inda take. Sai da taji horn ɗin motan sa kafin ta ankara, taja akwatin ta ta nufi motan, buɗe bayan tayi ta saka akwatin kafin ta shiga gaban motan ya ja suka bar wajen.


          A cikin motan ma babu abinda yace mata, duk da kuwa ta sake tambayar sa abinda ke damun sa, amma yayi mata banza, har suka kai gidan ya sauke ta yaja motar sa ya bar gidan

Tsaye tayi a wajen tana bin motar har ya ɓace wa ganin ta, sai kuma jiki a sanyaye taja Trolly ɗin ta tayi cikin gidan, duk wanda ta gani a hanya gaishe sa take yi har ta isa Part ɗin Hajja Fatu

Sosai Hajja Fatu tayi murna da ganin ta, nan tayi ta nan-nan da ita har ta cika mata gaban ta da kayan ciye-ciye

Ruwa kawai ta ɗauka tasha, sannan ta kalli Hajja Fatu tace, "Hajja where is Shakira I didn't hear her movements?".

"Ai kuwa Shakira tana wajen Yusra, amma yanzu zaki ga ta zo tunda ta san an tafi ɗauko ki".

Gyaɗa kai Sa'adatu tayi, kafin ta sake cewa, "Hajja is something happened to Yaya Baffa? na ga tunda muka zo be ce min komi ba ne?"

Murmushin yaƙe Hajja tayi tace, "bar shi nan yanda kika ganshi, shi ya san me ke damun shi".

Langaɓe fuska tayi tace, "eyya Hajja taya zan bar shi bazan damu ba? kinga fa shi ɗin Yayana ne, wlh baki ga tunda muka biyo hanya duk na gama damuwa da halin da na ganshi, ko dai Ni ce ba ya son gani?".

Hajja tace, "Taya Zaki ce haka? Ina ruwan shi dake da zai ce ba ya son ganin ki? Kin San tunda nayi masa maganar bazai auri yarinyan da ya zaɓa bane, shi ne ya dena min magana, ko abinci ma ba ya ci a nan, ya dena walwala gaba ɗaya, Ni kuwa bazan yarda ya aure ta ba bayan ga ki kina son shi, muddin idan be kawo wacce yake so ba, to ke ce matar sa da yardan Allah kamar yanda muka tsara".

Washe baki Sa'adatu tayi, cike da farin ciki tace, "Allah ya amsa bakin ki Hajja ta. Amma to wace ce wacce ya ke so ɗin?".

"Kar ki damu ba sai kin san ta ba, don ba na son ma maganar tariƙa tsawo azo kuma a samu matsala, maganar ta faɗa kunnen wani".

"Haka ne Hajja, amma ai Yakamata ki sanar dani tun wuri, don wlh har na ji tsanar ta a raina, kinga kuwa gwara in santa in San yanda zan yi zama da ita koda watarana na ganta".

Taɓe baki Hajja Fatu tayi tace, "ai kin ma santa tunda ba wata ƴar nesa bace, Ɗahira ce ta nan gidan".

"What ..! But wlh Hajja I hate this girl so much, God forbid that you forbid her, Allah yasa gwara da kika hana, don wlh wannan yarinyan idan ta aure sa babu ke babu ɗanki, domin irin su ne masu raba uwa da ɗan ta, sai dai ki riƙa hangen sa daga nesa".

"Ai nima shi na gani, ya rasa wacce zai aura sai ita, ba ga shi ba muna gani a wajen uwar ta, yanda take juya Al'ameen, Bilkisu kuwa ta zama abun kallo kamar ba ita ce matar sa ta farko ba, sai abinda tace za'a yi, ke wlh in gaya miki duk iyayen nasu maza sun fi ƙaunar ta, idan har wani abu zai fito daga hannun su to ita suke ba ma wa, ko Kaka shima idan zai yi shawara da matan gidan ita yake kira, komi yace A'isha, uhmmm wlh abun yana baƙanta mini Rai, shiyasa na matuƙar tsanar ta sabida gaba ɗaya Kaka ya rage nuna min kula wa kamar baya, burina kawai ta bar gidan nan tunda Innar ku Safiyya bata aure sa ba, to nima bazan samu kwanciyar hankali ba har sai na kora ta ta bar gidan nan. Mu dai bar maganar nan ki ci abinci tukunna".

"Ok Hajja".  Sa'adatu tafaɗa tana saka hannu ta buɗe coolarn

Daga nan sauya hiran suka yi, inda Hajja take tambayan ta mutanen gida da basu gaisa ba.





⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

         Gaba ɗaya a kwanaki biyun nan da suka wuce Ɗahira ta sauya, ba komi ya sauya ta ba illa kewar masoyin ta, a kullum ranan duniya zata ɗau wayan ta sau babu adadi don ganin ko zata ga message ɗin sa, sai dai kuma har ranan ta wuce baza ta ga ko me kama da Numban sa ba, ta kasa haƙura har kiran Numban tayi, amma kuma a kashe ne kamar ko yaushe, duk ta rasa nutsuwar ta ta saka wa kanta tunani, kullum bata da aiki sai tunanin sa, idan ta je Office ma zama take yi tayi ta faman tuna sa, har mafarkin sa tana yi wai ga shi sun haɗu, tabbas sosai take son bawan Allan nan da ya guje ta, ta kasa cire sa a ranta ta saba da rashin sa, ga shi ya tafi ya bar ta koda sunan sa ne bata sani ba, illa kawai A.A.A. da ya rubuto mata a ƙarshen text message ɗin da yayi mata na ban kwana, kuma duk iya tunanin ta na ganin ta gano ma'anar A.A.A ɗin ta kasa, haka zata zauna ta saka wannan sunan ta saka wancan sunan don ganin ta ba shi suna, amma ko wanne ta saka sai ta ga be dace ba.

     Ga shi tana son tayi magana da Baffa, koda zai ba ta shawara ne, amma kuma ta kasa ganin sa shima, shi kaɗai ne wanda zata iya faɗa masa damuwar ta amma kuma duk idan taje office ɗin sa ba ta ganin sa, dole yau bayan ta shirya zata wuce aiki, sai ta fara wuce wa Part ɗin su ta duba sa, wataƙil akwai abinda ke damun sa ne ba ta ganin sa a Hospital, Tabbas tana ji a jikin ta ba ya zuwa ne, idan da yana zuwa dole zai neme ta.

       A time ɗin su Hajja Fatu duk sun tafi aiki, illa Sa'adatu dake zaune ita kaɗai a Part ɗin, tana Parlour ne tana Breakfast tana latsa wayan ta, sai ta jiyo sallaman Ɗahira da ta shigo parlour'n, ɗago kai tayi tana kallon ta, sai ta ɓata fuska tana kau da kanta

Ita kuwa Ɗahira fara'a ta saka a fuskar ta tana cewa, "ah ah yau Sa'ada ce a gidan na mu? Saukar yaushe ba mu da labari?"

Sa'adatu bata ɗago kai ba, sai tsaki da taja tana kai loman abinci

Hakan sai ya sanyayar wa da Ɗahira jiki, bata sake cewa komi ba tayi hanyar ɗakin Baffa

"So, Ma'am, where are you going?"


Juyo wa Ɗahira tayi tana kallon ta, hakan yasa suka haɗa ido

Sai Sa'adatu ta banka mata harara tace, "dama kin bar wahalar da kanki a kan Ya Baffa, domin kuwa shi ɗin nawa ne Ni kaɗai, ba'a yi macen da ta isa ta ƙwace min shi ba, don haka idan ma zaki nemi mijin ki a can wani wajen ki nema, domin dai Baffa nawa ne, nima kuma tashi ce".

Baki sake Ɗahira take bin ta da kallo, a haƙiƙanin gaskiya Sa'adatu ba wai haushi ta ba ta ba, illa dariya da maganar nata ya bata, wanda har sai da ta murmusa, a ganin ta in ba hauka ba, Taya ma zata ce ta zo wajen Baffa ne domin neman soyayyar sa, bacin ta san da cewa shi ɗin yayan ta ne, ko kaɗan bata taɓa kallon Baffa a matsayin wanda zata iya aure ba, ba wai don wani abu ba, a'a, sai dai tana mishi kallon wanda suka fito ciki ɗaya, duk yanda mutane suke fassara su bata taɓa koda kallon abun hakan ba, "to meyasa su suke wannan tunanin?" Ta tambayi kanta idanuwan ta akan Sa'adatu tamkar da ita take yi, sai dai yanda tayi maganar a hankali babu wanda zai iya ji bare ya bata amsa. Ajiyan zuciya ta sauke sannan ta juya taci gaba da tafiya zuwa ɗakin nasa, don a ganin ta ɓata lokaci ne ta zauna tana biye wa Sa'adatu, tasan ciwon kanta, duk da a girme dai baza ta girmi Sa'adatu ba, amma kuma za su yo sa'anni da juna.


         Tana zuwa ƙofar ɗakin ta cinma a rufe yake, bata yi ƙoƙarin buɗe wa ba duk da kuwa tana tare da keey ɗin ɗakin shi a cikin nata, tunda tasan shi dai ta zo nema ba wani abun ba, shiyasa ta juya ta wuce tabar Part ɗin baki ɗaya, ko kallon inda Sa'adatu take zaune ma bata yi ba. Motan ta ta hau ta wuce Hospital, tana isa ta fara zuwa Office ɗin Baffa, amma kuma babu shi sai dai Office ɗin a buɗe yake, kai tsaye lefter ta hau ta koma Office ɗin ta, ta soma duba Patients ɗin ta, tunda a time ɗin har sun soma zuwa.
[10/09, 8:45 pm] OumƊahira نفيسة: 💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
              *FAMILY DOCTOR'S*
                         🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
   *NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
                 _NAFISAT ISMA'IL LAWAL._



*بسم الله الرحمن الرحيم*






*HIKIMAR FARILTA SALLAH*
      '''An farilta sallah domin a cikin ta akwai godiya ga Mani'imcin sarki jalla Ta'ala, wanda yake shi ne macancancin godiya da yabo, kuma shi ne kaɗai muka keɓe shi da ruku'u da sujada. Ba wani mahaluki da ya dace da wannan. Idan wata masifa ta sami mutum yakan yi maza ya fake da Allah ta yin Sallah, kamar dai yadda Allah yayi umurni a cikin suratul Baƙara, aya ta 45 da cewa:
       "Kuma ku nemi taimako da yin haƙuri, da Sallah".
    Ganawar da bawa yake yi da Ubangijin sa a cikin Sallah ita ce bauta wadda take ƙarfafa zumunta tsakanin bawan da Ubangijin nasa. Ubangiji kuma yana yi wa bawan baiwar darajar samun kusanta da shi. Hikima ce kammalalliya da aka farilta sallah, don kuwa ta yin Sallah ne ake kankare wa bawa zunubai, muddin dai ya yi sallah yadda ake so.
     An ruwaito cewa annabawan da suka wuce, ko wannen su yana da Sallah da yake ibada da ita. Sallolin suna da lokatai biyar; asuba, azahar, la'asar, lokacin faɗuwar rana da na isha'i. Ashe za mu lura cewa Allah ya tara wa Annabi da al'umma tasa sallolin dukan annabawan da suka gabata.
    Allah ya sa mu dace.'''

.



        *EPISODE Twenty Six*

             *SUNDAY*
          Gaba ɗaya sun taru a General Parlour kamar yanda al'adan gidan yake, sai da suka gama raha da nishaɗin su, sannan Kaka ya soma magana da cewa, "Kai Fadil ki rawo Fodio tunda ya ƙi zuwa".

"To Kaka". Fadil ya amsa mishi da sauri yana tashi ya fita

Babu jima wa sai ga Fadil ya dawo, ya isar da saƙon zuwan Usman

Kamar mintuna biyar da shigowar sa ne, Usman ya shigo yana ciccin magani, fuskar nan ko alamun fara'a babu, babu wanda yayi masa magana sai Big Dady dake faman hararan sa, sai dai shi ɗin be ma san yana yi ba, tunda be kalli kowa ba, ya samu wuri ya zauna gefen Baffa, sannan ya gaishe su yana latsa wayan sa

Kowa ya amsa, banda Big Dady da hakan ya ƙular da shi, a fusace ya ce, "kai Usman wannan wani irin ɗabi'ar banza ce? Ina ce gaishe mu kake yi amma kanka a waya?"

Sai a lokacin Usman ya ɗago kansa, sai dai be ce komi ba, illa jikin sa da yayi sanyi ya zame hannayen sa daga wayan ya bar sa a saman cinyan sa

Zai sake magana Big Dady, sai Kaka ya tare shi da faɗin, "bar wannan maganar Noor, mu Yi abunda ya tara mu, kasan halin wannan yaron meyasa kake son ɗaukan zafi da shi ne?"

"Baba wlh abun Usman sake gaba yake yi ba baya ba, kamar shi har sai an zauna ana faɗa mishi dai-dai da wanda ba dai-dai ba? Nan ya bar mu muna zaman jiran sa tsawon lokaci, duk sabida shi aka ƙi cewa komi, amma kuma ya zo yana wani sabga daban bayan yasan da cewa magana me muhimmanci ne ya tara mu".

"Well enough to stop talking, ban san ka da wannan halin ba Noor Kar ka soma ka ji ko?" Kaka ya sake faɗa idanun sa kan Big Dady

Gyaɗa kansa yayi, kana yace, "to Baba Allah ya huci zuciyar ka".

Murmushi Kaka yayi, yayinda su Abba da Abbu suka amsa da "Ameen, sai haƙuri ai".

Kaka ya ce, "to ina jin ku, ya muka kwana a maganar yaran nan ne? tunda yau dama na ce zamu sake zama akan maganar".

Abba ne ya ce, "ai Baba duk na tambaye su kuma na ce su turo mun su, kuma sun zo mun yi musu tambayoyi da Yaya (Yana nufin Big Dady) sannan na bincika duk na gano inda yaran suke, har na saka ayi min bincike a kansu. Uwata kuma da Usman har yanzu ba su ce komi ba akan maganar, shi kuma Baffa ɗazu Mahaifiyar tashi take faɗa min Sa'adatu ta wurin ƙanwar ta Hajiya Amina yake so".

Kaka yace, "to Masha Allah Baba na". Sai ya mayar da kallon sa ga Ɗahira da ke gefen sa ya ce, "Matata har yanzu abokin takaran nawa be shirya bane da baki gabatar da shi wajen Iyayen naki ba?"

Shiru Ɗahira tayi kanta a ƙasa

Sai da Big Dady yace, "Daughter you're talking, are you okay? No problem?"

Bata ɗago kai ba tace, "Daddy, I don't have anyone to introduce me to."

"Baki da wanda zaki gabatar kuma?" Cewar Big Dady da Abba da suka haɗa maganar a tare

Sai kuma Big Dady ya ƙara da faɗin, "ko dai kin tsaya ruwan ido my Daughter? Amma maganar babu wanda zaki gabatar ai be taso ba".

Jikin ta a sanyaye tace ,"Daddy wlh da gaske nake yi, wanda muke soyyayya da shi ya ce "ya fasa aure na, sabida Mahaifiyar sa ta zaɓa mishi wacce zai aura".

Daga Aunty Amarya har Abbu da su Big Dady sai da jikin su yayi sanyi, haka zalika Kaka da yayi zugum yana kallon ta ya kasa furta komi

"Yanzu Uwata babu kuma wanda zaki iya gabatar wa ne?" Cewar Abba da yayi maganar a sanyaye

Gyaɗa kanta tayi, don haka kawai taji hawaye ya cika mata ido, a ganin ta abun da kunya a tara su a gaban jama'an gidan ace ta kawo zaɓin ta, amma kuma bata da shi, babu wanda zata iya nuna wa a matsayin gwanin ta, kamar ta ƙatuwar budurwa da ita, a ƙalla yanzu kaɗan ya rage ta cika 26 cif-cif...

Muryan Kaka ya katse mata tunanin ta, sai ta saka hannu tana share hawayen da ya zubo mata tana ci gaba da sauraron shi

Tambayan Usman yayi kamar yanda yayi mata

Usman ɗago kai yayi yana kallon kakan, fuska babu walwala a daƙile ya ce, "Babu".

"Meye kuma Babu?" Abba ya tambaye sa

"I mean har yanzu babu wacce nake so".

Shiru gaba ɗaya parlour'n ya ɗauka, ana jiran aji wani yayi magana a kan hakan, amma babu wanda ya iya cewa komi, har Kaka kuwa, kowa juya maganar nasa yake yi a mizanin hankalin sa

Kaka kallon Abbu yayi ya ce, "Takwara kun yi maganar da Yayar taku?" (Hajiya Ikram, Yana nufin akan Khabeer da ke son Fadila)

"Eh Baba, Yaya yayi maganar da ita".

Big Dady yace, "mun yi maganar, har mun tattauna da mijin ta, babu matsala tunda su ma a shirye suke, za'a haɗa gaba ɗaya dana Isma'il da Shamsiyya". (Sauran yaran Hajiya Ikram, su uku kenan zata aurar itama, har da K.B)

Gyaɗa kansa Kaka yayi yace, "Masha Allah gaskiya nayi farin ciki matuƙa, Allah ya sanya albarka gaba ɗaya".

"Ameen ameen". Suka amsa gaba ɗaya

"Yanzu duk abinda kuka ga ya dace sai ayi, kun san dai idan za'a saka ranan nace muku kar ya wuce wata ɗaya? Sai ayi komi a tsanake zuwa watanni biyu, na ƙara lokaci, a lokacin idan Fodio da Matata sun kawo nasu sai a haɗa baki ɗaya, don baza ayi babu su ba. Kai kuma Fodio kayi ƙoƙarin samo mata tun kafin Ni in zaɓa maka kana ji ko?" Kaka yayi maganar ta sigan barkwanci

Be ce komi ba kamar yanda kuwa babu wanda yayi tunanin zai ce.

     Daga nan dai aka bar zancen aka kama wani, inda waɗanda suke da abun yi suka bar wajen.

    Ɗahira bata wani tada hankalin ta ba akan maganar, ta bar wa Allah zaɓi, a ganin ta idan ta saka damuwa kanta zata cuta, tunda dama bata iya saka damuwa a ranta ba, da zaran ta saka, to shikenan ta dinga ciwo kenan, duk idan ka ga tana ciwo to tabbas da akwai abinda ke damun ta ne, ba ta iya jure wa damuwa ko kaɗan a ranta, bata da dauriyan hakan, domin zuciyar ta ba ta iya ɗauka, shiyasa ba ta shiga sabgar kowa idan har be shafe ta ba, sabida ta san matsalar kanta.

      Aunty Amarya har ɗaki ta kira ta, tayi mata nasiha akan hakan

Amma sai Ɗahira ta nuna mata babu komi, har da fara'an ta

Hakan ya kwantar wa da Aunty Amarya hankali matuƙa, ko babu komi taji daɗi a yanzu, tunda ta san dole ɗiyar ta zata shiga wani hali na rashin masoyi, tabbas rashin Masoyi abu ne me ciwo ga duk macen da ta isa aure amma babu ma nemi, sai dai Allah ya zaɓa mana mafi alkhairi.





          ⚫⚫⚫

     Fannin Usman ma, da dare Daddy ya Kira sa ya titsiye sa akan maganar, a cewar sa "ai wannan shirmen banza ne, shirmen hofi. Ta ya zai ce be da wacce yake so duk girman sa, shekara kusan 33 yana musu wasa da hankali". Tsiya-tsiya sosai Big Dady yayi masa, kuma ya ba shi umarnin "lallai-lallai ya kawo mata zuwa nan da lokacin da Kaka ya ce, idan ba haka ba, zai ɗau mummunan mataki a kansa"

Hajiya na zaune tana jin su, sai dai bata ce komi ba, tunda itama ai tana ƙaunar ganin ɗan nata yayi aure, shi ne babban ɗa a gidan, amma har yanzu be yi aure ba, duk da a ganin ta ai ba wani shekaru ne masu yawa da shi ba, amma ta yanda za'a ganshi da girma, ƙannin sa su ƙara ganin girman sa, ai sai idan yana da mata, itama zata so ta ga jikokin ta ta wajen shi, ai abun kunya ne ma ace yanzu Yusra zata yi aure shi be yi ba, sannan ga ɗaya ƙanwar sa can a ɗakin miji har da ɗan ta, shi ƙaton banza ya zauna.

     Shi kuwa Usman ko a jikin sa, tunda a ganin sa dai babu wanda ya isa yayi masa auren dole, don haka be tashi yin aure ba yanzu sai sanda yayi niyya, duk a cikin mata har yanzu be ga wacce tayi dai-dai da ra'ayin sa ba, yana da burin ra'ayin auren mace zaɓin shi da koda yaushe zuciyar sa take raya masa, kuma har yanzu be dace da kalan ta ba, don haka sai sanda ya same ta sannan ne zai yi aure, mata yanzu ba sa gaban sa, shiyasa ya ɗauki maganar Kaka ba ta da wata muhimmanci, bare shi rayuwan boko ya saka wa kansa, har yanzu gani yake yi be kai matakin da har zai iya ajiye mata ba, ɗawainiya ya hau kansa tun da ƙuruciyar sa ya tsufa da wuri.





            ⚫⚫⚫

     Baffa kuwa sosai ya shiga damuwa a wannan ranan, har kuka sai da ya sha ya ƙoshi, ya kuma gode wa Allah, ga shi yana ji yana gani zai bar zaɓin shi babu yanda ya iya, yana kallon wacce yake ƙauna bata da wanda zata iya gabatar wa face shi, amma kuma Mahaifiyar shi tayi masa iyaka da ita.

      Ya tuna sanda ya je har ɗakin ta yana kuka ya sake mata maganar "ta amince ya auri Ɗahira, in yaso duk wacce take so ya aura, shi wlh zai aure ta, koda kuwa mata huɗu zata haɗa masa, idan har da Ɗahira to ya amince".

Amma sai buɗan bakin Hajja tace, "kai Al'ameen ka ji Ni da kyau, Ni Ɗahiran ce ba na so ka aura, bazan taɓa haɗa tsatso da A'ishah ba, domin kuwa na tsane ta a raina, ban taɓa faɗa maka hakan ba, amma yanzu sabida maganar nan ka saka ina bayyana maka sirrin dake raina, to wlh idan har ka kuma sake tayar da maganar nan ma, ban yafe maka ba".

Kuka sosai Baffa ya fashe da shi, be iya furta komi ba sabida tsaban tashin hankali, wai yau Mahaifiyar sa ce take furta masa kalmar nan duk a sabida wani dalili nata mara tushe, ko a mafarki be taɓa tunanin akwai abinda zai iya bayyana wa mahaifiyar sa yana so ba, ta kasa mishi, sabida ya san tana ƙaunar sa, duk abinda yake so to itama tana so, hakan be taɓa faruwa ba, shiyasa yake ganin abun tamkar almara. ranan ya sha kuka kamar babu gobe, har zazzaɓi ya kwana da shi a ranan. Allah ya ɗaura masa ƙaunar Ɗahira kamar ransa, amma ga shi a lokaci ɗaya ya rasa ta, abinda be taɓa tunani ba ko da a mafarki, ya rigada ya saka wa ransa ita ɗin tashi ce, tunda be taɓa tunanin akwai wata matsalar da zai shiga tsakani ba, ko da ma akwai, to, sai dai a wajen Ɗahira, ita ma kuma be taɓa tunanin zata iya cewa ba

Please Login or Register in order to submit comment