Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

try, yanzu abinda zaki yi, ki nemo mana wanda zai yi mana aikin nan".

Sai a lokacin itama Ayush ta saki murmushi tace, "I have someone to do the work for us."

⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

            "Kai Aboki na, kasan kuwa cewa wannan Babe ɗin taka zata yi aure?" Cewar Dr. Sabo dake zaune gaban table ɗin Dr. Sa'id yana juyawa a kujeran

Ɗago kai Dr. Sa'id yayi daga rubutun da yake yi, ya bi sa da kallo yana cewa, "wa kenan?"

"Oh you don't know? I'm surprised. I mean Dr. Ɗahira Mana, duk a tunani na kai zaka yi wuf da ita wlh, amma fa kayi rashin Sa'a wlh da ka bari ta suɓuce maka duk da Nasan halin ka". Dr. Sabo ya ƙare maganar yana dariyan shaƙiyanci

Sosai maganar ta bugi zuciyar Dr. Sa'id, cikin wani irin yanayi yace, "Please are you serious or joking?"

"Haba wlh da gaske nake yi, her cousin will also marry Dr. Usman, magana ma har ta baza ko ina a Hospital ɗin nan".

Shiru Dr. Sa'id yayi

Dr. Sabo yace, "yanzu haka ma two weeks ya rage Ina ga bikin, but wlh ina maka jaje da rashin samun ta, duk a tunani na tuni kun rigada kun daidaita, aure kawai ya rage, ashe ba haka ba".

Ajiyan zuciya Dr. Sa'id ya saki, kana ya dube sa yace, "ba abinda ke raina ba kenan, in fact ma ban taɓa tunanin auren ta ba, sabida kasan halin matata, baza ta taɓa yarda na sake aure ba, but Ni dama da wata manufa nake son ta, Amma kuma ga shi ina ga Ina son rasa dama ta".

Dariya Dr. Sabo yayi yace, "well Dama nasan abunda zaka ce kenan, but ban taɓa tunanin itama tana ɗaya daga cikin irin ƴan matan ka da zaka yi wannan rayuwan da ita ba, duba da yanda ita ba halin ta kenan ba, ashe dai kana nan kana target ɗin ta ne".

Murmushi Dr. Sa'id yayi yana shafa sajen sa yace, "yarinyan ce ta wuce tunani na wlh, kallon farko da nayi mata nayi tunanin bazan sha wahala wajen samun ta a hannu ta zama nawa ba, but duk yanda na so tafi ƙarfi na, uhmmm yarinyan tayi ne Dr. That's why nake son duk yanda za'a yi na ƙulla alaƙa da ita, koda kuwa bata saba ba, nayi alƙawarin sai na cika buri na akan ta, sai na maishe ta nawa, a kaina zata san daɗin rayuwa. Kuma auren ta ba yana nufin zan kasa cika burina bane". Sai yayi shiru yana ɗago da kansa daga jikin kujeran, ya ɗaura hannayen sa biyu saman table ɗin yana ɗan buga wa yace, "yanzu ma aka soma, wlh idan har na cika Dr. Sa'id Khan mayen Mata, sai na ɗanɗana yarinyan nan, domin hankali na bazai taɓa kwanciya ba sai na ganni tare da ita a kan gado ɗaya. Har yanzu ta kasa barin ruhi na ya samu sukuni, ta shiga rayuwata da yawa".

Murmushi Dr. Sabo yayi yace, "tirƙashi akwai aiki kenan Dr.".

Murmushi kawai Dr. Sa'id yayi, sai kuma yace, "baza ka gane bane. Let's stop talking now, I will call her now nayi mata murna, yanzu sabon salon zai fara".

⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

        Biki nata ƙarato wa, inda tuni an soma shirye-shirye ko ta wani ɓangare

Gefe ɗaya kuma Ɗahira har yanzu fama take yi da kanta, domin a tsaitsaye take rame wa sabida zullumi, ko yaushe ba ta jin daɗin jikin ta, yau ciwo gobe lafiya

Duk yanda Aunty Amarya tayi don ta kwantar mata da hankali, amma abun ya citura, ta kasa cire damuwa a ranta, gaba ɗaya ta rame sosai, sai haske da ta ƙara da girman idanu a waje, dama ba auki ne da ita ba, kamar ta karye take jin ta tsaban siranta, yanzu kuwa har tafi Da sirance wa

Har yanzu kuma bata koma bakin aikin ta ba, dole Abbu ya hana ta koma wa, tunda har yanzu ba ishashshen lafiya ne da ita ba, tarigada ta saka abun a ranta yana ta cutar da ita.

         ********

       Gefe ɗaya kuma Usman shima yana cikin tashin hankali, musamman da yaga auren yana ta ƙarato wa, tabbatan dole sai an yi, shiyasa gaba ɗaya ya shiga  damuwa tsantsa, ko abinci ba ya ci duk ya hana kansa sukuni, gaba ɗaya ma ya dena zama a gida, sai dare yake dawowa. duk yanda Hajiya tayi don ta samu ta kwantar masa da hankali, ya ƙi sauraron ta, shiyasa kullum ranan duniya sake jin tsanar Ɗahira take yi, ga shi ko gayya taƙi yi, ba ta shirin komi na bikin, duk yanda kuwa ta so da cin zaƙin bikin ɗan ta mafi soyuwa a ranta. A ganin ta baza ta iya taron biki tana murna ba, ɗan ta kuma yana cikin damuwa, ga shi Big Dady ko bi ta kansu ba ya yi, ya bar su ya zira musu ido daga ita har shi Usman ɗin, kuma ya hana su sake zuwar mishi da zancen.

                  ⚫⚫⚫

           *ONE WEEK AGO*

      Yau ma kamar kullum yana zaune a Office ɗin sa, ya haɗa kansa da table yana ta faman tunani, dama nan ne wajen zaman sa koda yaushe, tun safe idan ya zo ya rufe kansa a Office ɗin, sai dare yake koma wa gida.

    Nocking ɗin da aka yi masa, shi yasa ya buɗe jajayen idanun sa da suka kumbura ainun sabida rashin barci, da kuma ɓacin rai, be motsa ba har sai da yaga me Nocking ɗin ya dame sa, tsaki yaja yana ɗago kansa yabi ƙofan da kallo, gaba ɗaya fuskar sa ta gama haɗe wa tayi jazur sabida tsantsan damuwa, da gani kasan ba a cikin mood ɗin sa yake ba

Lumshe idanu yayi yana buɗe baki a hankali ya ba da iznin shigo wa, sai dai babu yanda za'a yi aji sa, dole ba don ya so ba ya sake ɗaga murya ya ba da iznin shigo wa

Wani staff ne ya shigo ciki, tare da gaishe sa cikin girmamawa

Sai dai yanda kasan kamar dutse haka Usman yayi banza da shi, illa rikitattun idanun sa da ya kafa masa

Duk ya ruɗe ɗan saurayin sabida Mayun idanun sa da ke kallon sa, ya matso yana miƙa masa envelope, sannan ya sanar masa, "wani ne yace a ba shi"

Be ce masa komi ba, yayi masa alamun ya ajiye masa

Ajiye masa yayi a saman table kamar yanda ya ba shi umarni, kafin ya fice da sauri

Da kallo Usman ya bi envelope ɗin da shi, yana mamakin mene ne a ciki? Da Kuma wanda ya aiko?

Tsaki yaja yana sake gyara zaman sa kan kujeran, ya saka white hand ɗin sa ya ɗauka ya soma buɗe wa, hotuna ne ya zaro guda biyar

Hoton farko dake saman sai da ya ɗauke numfashi na wucin gadi sabida munin hoton, Ɗahira ce kwance tsirara da wani ƙaton gardi suna manne da juna babu kaya suna aikata masha'a

Saurin lumshe idanun sa yayi yana jin wani tashin zuciya na son kama shi, take a nan ya saki sauran hotunan zuwa ƙasa ba tare da ya gani ba, sosai zuciyar sa take tafarfasa da abinda ya gani

"Yanzu wannan sheɗaniyar yarinyan karuwa, ita ce su Kaka za su aura min?" Yayi maganar a maƙoshi yana jin tamkar ya haɗiya zuciya ya mutu tsaban baƙin ciki

Hoton yabi da kallo daga ƙasa, sai yayi saurin kawar da kansa saboda ganin sauran da suka ninka wanda ya gani muni, kifa kansa kawai yayi a saman table ɗin yana riƙe da kansa dake faman sara masa, tuni idanun sa sun juye sun sake zama ja sabida tsaban ɓacin rai, a fili ya furta, "na tsane ki sosai fiye da komi dake duniyar nan! dama tun ba yau ba na rigada nayi tunanin hakan a Raina". Sai yaja dogon tsaki yana tunanin yanda zai yi, "anya bazai ɗau hotunan ya nuna wa iyayen sa ba, wataƙil ma ya samu damar tsere wa auren?" Zuciyar sa ta raya masa hakan

Take kuwa ya saka hannu ya kwaso hotunan, ya mayar dasu cikin envelope ɗin, miƙe wa yayi tare da wayan sa a hannu da keey ɗin motan sa ya bar Office ɗin.

⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

         Tana kwance a saman gadon ta tayi samɓal da ƙafafuwan ta, sai ta kifa cikin ta ta tusa kanta ƙasan pilow, a hankali take fitar da numfashi ɗai-ɗai.

        Fadila ce ta turo ƙofan ta shigo da sallama a bakin ta, da kallo tabi Ɗahiran dashi har taƙariso bakin gadon tana zama tace, "Sister lafiya dai?"

Ɗahira da taji muryan Fadila tamkar daga sama, domin mugun tunani ta afka da gaba ɗaya ma ba ta cikin duniyar mu, da sauri ta zaro kanta dake ƙasan pilow tabi Fadila da kallo da manyan idanuwan ta da suka gama sauya kala suka yi jazur tamkar tayi kuka, ga shi sun faɗa sosai, hakan yasa idanuwan suka sake fito wa waje suka yi ƙwala-ƙwala

Nan da nan Fadila ta ruɗe da ganin ta a haka, tace,"lafiya Sis? what's going on? What's wrong with you looking at your eyes have changed color?"

Murmushin ƙarfin hali Ɗahira take yi, ta tashi zaune tana kallon ta da kyau, kafin tace, "nothing Sis, yaushe kika zo?"

"Ya zaki ce min babu komi? Kin kuwa ga yanda kika koma? Ciwo kika yi ne ko wani abun ke damun ki?" Fadila ta sake faɗa tana ƙare mata kallo, ganin yanda ta ƙara ƙarmashe wa sabida tsaban rama har ƙasusuwa ake gani ta wuyan ta

Stil dai murmushin tayi mata tace, "ciwo nayi Sister".

"Amma shi ne baki sanar dani ba, babu wanda ya kira Ni ya faɗa min? tun yaushe kike ciwon ne da kika rame haka?"

Ɗahira dariya tayi me bayyana haƙora, wanda idan ka kalla kasan cewa na dole ne, tace, "kin sauya ƴar uwa, yau ke ce kike jero min waɗannan tambayoyin?"

Hararan ta Fadila tayi tace, "Seriously, it's not a joke. I'm asking you ciwon meye kika yi ya mayar dake haka?"

"Hmmm ciwo ne kawai, zazzaɓi".

Kallon ta Fadila tayi, sai tace, "ko dai kan maganar auren ki ne? Of course there is something going on. nayi mamakin jin cewa an haɗa ki da Ya Fodio, na kira wayan ki duk ba ta shiga, meyasa Sister kika yarda da auren nan tunda kin san ba kya son shi? In fact ma ba kwa shiri ke dashi?"

Shiru Ɗahira tayi bata ce komi ba

Fadila ta sake cewa, "I know wannan raman yana da nasaba da auren ki, ban ji daɗi ba gaskiya yanda na ganki haka.."

Shigowar Fadil ne yasa Fadila yin shiru, duk kan su suka bi shi da kallo har ya ƙariso ciki

Hannayen sa biyu cikin aljihun wandon sa yake kallon su yace, "Aunty Ɗahira Kaka na neman ki". Sai kuma ya mayar da idanun sa kan Fadila yana dariyan tsokanan da zai mata yace, "ke kuma nan kika yo daga zuwa? ga shi can mijin ki na bilayin neman ki, ashe ke kin zo nan kin maƙale, halan kewar ɗakin kika.."

Bugun da ta kai masa ne, yasa shi guduwa ba tare da ya ƙarisa zancen nasa ba, sai da ya kai bakin ƙofan ɗakin yana dariya yace, "to ki dai fito ga shi can yana neman ki cwhengum ɗin naki, sai kace ba yanzu kuka rabu ba".

"Fadil ba ka da kunya ko?" Cewar Ɗahira tana murmushin zancen sa

"Ki ƙyale sa, zan gyara masa zama wlh kafin in tafi, ai kasan hali na?" Fadila ta faɗa tana tsare sa da idanu fuska a kirne

Be sake cewa komi ba ya fice da sauri, don yasan yayi tsokana, gwara ya fece tun kafin ta kama shi

Ɗahira tace, "ga shi har an kira Ni ba mu gaisa ba, bari in dawo sai mu gaisa".

"Ok Nima Ina Nan zuwa wajen Kakan yanzu ai". Cewar Fadila tana tashi tsaye

Tare suka fita daga ɗakin.
[23/09, 9:23 pm] OumƊahira نفيسة: 💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTOR'S*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱


*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA'IL LAWAL_




*بسم الله الرحمن الرحيم*


*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA'S FAMILY*_

*HADHISI *
_Aisha (may Allah be pleased with her) was quoted as saying, "The Messenger of Allah (may peace be upon him) married her when she was six years old, and she was nine years old with him, and Allah took her life when she was eighteen years old." Reported by Muslim._

.




*EPISODE Thirty Seven*

K.B ne da Aunty Amarya a Parlour'n zaune, ita kuma Umma tana kichen tana shirya abincin ranan da bata kammala ba

"Ƙanwa ta ashe kina ciki kin maƙale ina ta tambayar ki?" Cewar K.B yana kallon Ɗahira da suka ƙariso wajen tare da Fadila

Dariya tayi tace, "Yayana anya baka neme Ni ba dai, Tunda ai Mama ta san ina ɗaki".

"Aff to ai yanzu ne na soma maganar taki".

"To magana ta fito fili kenan". Tafaɗa tana dariya

Zama Fadila tayi gefen sa, don ita Aunty Amarya har ta tashi ta shige ɗaki ma

Gaishe sa Ɗahira tayi

Ya amsa yana cewa, "wai ƙanwa ta ciwo kika yi kika rame haka? Ko dai zullumin auren ne?" Yayi maganar cikin barkwanci

Murmushi kawai tayi

While Fadila tace, "Nima haka na gani yaya, wai ciwo tayi".

Tashi Ɗahira tayi tace, "bari dai inje in dawo Kaka na kira na sai muyi magana, I have something to talk to you about. yaushe Shamsiyya zata zo ne?"

Taɓe baki yayi yace, "to ki dai kira mijin ta ki tambaye sa, amma bani ba, tunda Ni ga nawa tazo".

Dariya kawai tayi ta wuce ta bar su nan. Ta san halin K.B idan ta biye mishi babu inda zata je

Part ɗin Kaka ta wuce kai tsaye, tana shiga ɗakin sa da sallama

Ya amsa mata yana zaune kan gadon sa yana duba wani ƙaton littafi na addini

"Taho Mata ta". Yayi maganar yana kallon ta da murmushi a kyakykyawar face ɗin sa

Taho wa tayi ta zauna gefen sa tace, "Kakus nayi kewar ka". Ta ƙare maganar da jan gemun sa

"Me too My wife, bayan ma yanzu kin dena nema na, har sai na aika a kira ki kike zuwa, yanzu kenan idan kinyi auren ma haka zaki guje Ni ko?"

"Eyya Kaka wlh No, I will never run away from you, idan ba ka a rayuwa ta ai kamar babu Ni ce". Tayi maganar tana langaɓe kai

"To amma ciwo kika sake yi ne bani da labari, naga duk kin sake rame wa ne sosai?".

"kai Kakus, sai dai idanun ka ne suka gane maka haka, amma ai dama can haka nake". Tayi maganar tana dariya

"Anya ba zullumin rabuwa dani kike yi ba?"

Dariya sosai wannan karon take yi

Shima yana taya ta, sai kuma yace, "faɗa min gaskiya Ɗahira, do you want this marriage or not?"

Kallon sa tayi tana tsayar da dariyan, sai kuma ta yafa wa fuskar ta murmushi tace, "Kaka idan ma ba na son auren ai bazan ƙi muku biyayya ba, kana tunanin zan watsa muku ƙasa a ido ne? Never. Ba na fatan wannan ranan tazo".

Murmushin jin daɗi yayi, sosai yaji daɗin kalaman ta, amma sai yace, "Mata ta a kan farin cikin ki babu abinda bazan iya ba, ko yau ake ɗaura auren ku kika ce baki so, to zan dakatar dashi, Na san yanda kuke da Fodio, ko kaɗan jinin ku be haɗu ba, tabbas nasan sai kinyi haƙuri dashi kafin komi ya daidaita, amma kuma hakan da nayi shi ne naga ya dace, wannan hanyar ce kaɗai zai sa ku dawo kuna shiri, domin ba na son nan gaba bayan ba na raye iyali na kansu ya rabu, zan so tun ina da rai inga kun shirya kan ku, kun dawo kuna ƙaunar junan ku, wannan shi ne burina, domin ba na jin daɗin yanda tun kina ƙarama yake nuna miki tsana".

Hannayen sa ta riƙo, idanun ta cike da hawaye, tace, "wlh Kaka zan yi muku biyayya ko waye kuka kawo min a matsayin miji, bare kuma ɗan uwa na. Na rigada na ɗaukar maka alƙawari da kai da iyaye na zan yi zaman auren nan da zuciya ɗaya, fata na kawai Allah ya bani ikon yin biyayya a gare ku da miji na".

Tafin da Fadila take yi ne yasa suka juyo suna kallon ta, "oh ka ga masoyan asali? an haɗa kai ana ta ƙus-ƙus". Tayi maganar cikin sigan tsokana, duk da kuwa sai da ta gama jin abinda suke cewa ta shigo

Kaka yace, "Miskila kin fi mahaukaci ban haushi saukar yaushe?"

Dariya tayi tana zama kan drowern gadon tace, "yanzun nan babu daɗe wa Alh. Kaka, ya gida? na same ku lafiya?"

Yana murmushi ya amsa mata da cewa, "alhmadulillah.. Ina Kakan nawa, shi dai ya kawo ki ko?"

"Shi ya kawo Ni, yana waje tare da Ya Baffa".

"Masha Allah, ya wajen su Rabi'atu (Hajiya Ikram) komi lafiya?"

"Lafiya lau Kaka, suna gaishe ka da kyau-da kyau, sai jibi za su zo su".

A lokacin ne shima K.B ya shigo, nan suka shantake gaba ɗaya ana ta hira da Kaka, har Ɗahira da ba jin daɗin jikin ta take yi ba, sai dai ta saki jiki sosai tana ta saka musu baki, daga ƙarshe K.B ne ya soma tafiya, tunda dama yau ne zai koma, sai ranan biki ya dawo

Su ma daga baya fitowa suka yi, Fadila ta wuce sashin Hajja don ta gaishe su, ita kuma Ɗahira tayi Part ɗin su

A Hanya suka haɗu da Usman yana taho wa, tunda ta gansa gaban ta yayi muguwar sara wa, tayi saurin kawar da kai daga kallon sa, rabon da ta gansa tun ranan da aka ce za'a haɗa su aure, sai yanzu

Shima dai tunda ya ganta yayi matuƙar ɗaure fuska, zuciyar sa na wani irin tafarfasa saboda ganin ta da yayi

Suna zuwa dai-dai juna yace da ita, "ta biyo sa".

Sarai Ɗahira taji me yace, duk da kuwa babu wanda zai ce yayi magana, sabida yanda yayi maganar a ciki, kuma kansa na kallon hanya babu wanda zai ce da ita yake yi, ita kuwa taci gaba da tafiya tana jin ƙirjin ta na bugawa da sauri-da sauri

Ji tayi kawai an jawo ta baya an haɗa ta da bango, wanda sai da yasa ta saki ƙara saboda buguwan da ƙashin ta yayi, zaro idanu kawai tayi tana kallon sa kamar zuciyar ta zata faso ƙirjin ta ta fito tsaban tsoro

"Ni nake kiran ki kike banza dani?" Yayi maganar a zuciye tamkar zai kai mata bugu

Runtse ido tayi da sauri jikin ta na rawa

Cikin ɗacin rai yace, "shashashan yarinya ballagaza, sauran maza, tun wuri ma ki je ki ce baki son auren nan, idan ba haka ba wlh sai na halaka ki kika shigo gida na, na tsane ki ba na ƙaunar ki! kuma bazan taɓa son ki ba, ƴar iska kawai".

Yanda ta ƙwalalo masa idanun ta dake zubar da hawaye, ji yake yi kamar ya saka hannu ya ƙwaƙulo su, sai dai dauriya da yake yi sabida ba ƙaramin jin tsanar ta yake yi ba. saurin janye hannun sa daga riƙe mata kafaɗa yayi, yana matsawa da sauri tare da tofar da yawu, ciki-ciki yace, "ƙazamiya.. wai a rasa ma wanda za'a aura min sai sauran maza irin ki? tirrr dake". Ya buga mata wani banzan kallo ya wuce da sauri

Zame wa tayi a nan ta haɗa kanta da ƙafafun ta ta soma kuka, kuka me taɓa zuciya, har wani rawa jikin ta yake yi, kalaman sa ne suke yawo a cikin kunnen ta, "me yake nufi kenan? Bayan tsanar da yayi mata yanzu kuma kallon ta yake yi ƴar iska? Har da kiran ta ƙazamiya. Karuwa?"

"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un". Take faɗi kawai, while zuciyar ta tamkar ta fashe tsaban takaici

Da sauri ta ɗago kanta tana share hawayen fuskar ta, tuna wa da tayi a hanya take, kuma kowa zai iya ganin ta idan bata tashi ba. Miƙe wa tayi tana sake share hawayen ta, ta nufi Part ɗin su zuciyar ta cinkushe da baƙin ciki, har wani jiri-jiri take gani a hanya, Allah yasa babu kowa a parlour'n, sai tayi saurin shige wa ɗakin su, Toilet ta shige ta rufe kanta tasha kukan ta ma'ishi, sannan ta wanko fuskar ta tare da ɗauro alwala ta fito

Tana tayar da Sallah Fadila ta shigo ɗakin, dama kiran ta ta shigo yi don su ci abinci, tunda taga tana sallah sai ta koma.




⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

Ɗakin sa ya wuce kai tsaye, ya faɗa kan gadon sa yana me lumshe ido, shi kaɗai yasan me yake ji a duniyar nan, da ba don kalaman Dadyn sa da yake tunawa ba, wlh da tuni sun neme sa sun rasa ya bar ƙasan, sai dai ya rigada yace masa, "muddin be bari an yi auren nan lafiya an gama lafiya ba, to wlh sai yayi dana-sani a rayuwan sa, domin wlh sai yayi mugun saɓa masa".


Dogon tsaki yaja yana miƙe wa zaune, ya ɗauki envelope ɗin da ya ajiye sa saman drowern gadon sa tun dawowar sa, ciro wa yayi ya hau yaga hotunan ɗaya bayan ɗaya, zuciyar sa na ci gaba da tafarfasa tamkar zata ƙone, ko wani daƙiƙa sake jin tsanar Ɗahira yake yi, wanda ko ada be ji makamancin irin sa ba, a yanzu kuwa ji yake yi da za'a ba shi wuƙa ya yanka ta, sai yayi mata gutsi-gutsi yayi filla-filla da naman jikin ta

Yana gama wa ya kwashe ya zuba a basket ɗin dake bayan ƙofan sa, ya shige Toilet don yin alwala.





⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

A hankali gida ya soma cika da mutane, sabida ƙaratowar biki, ƴan uwan Aunty Amarya duk sun cika Part ɗin su tun ana saura kwana uku biki, dayake itama ƴar dangi ne babu laifi duk sun zo

Duk wani shiri da ake yi na Amare Ɗahira bata a ciki, su Fadila da su Firdausi, da sauran ƴan matan Familyn su suke yin komi, ita dai tana ɗaki sai dai ta ƙule taƙi fitowa, gaba ɗaya ma ba jin daɗin jikin ta take yi ba, saboda zazzaɓi da take fama da shi, shiyasa babu wanda ya takura mata, gyaran jiki ma tace "ba ta so" dole aka ƙyale ta, daƙyar ta bari ana gobe bikin aka yi mata saloon da lalle.

Washe gari 27 April 2021. Aka shaida ɗaurin auren *DR. USMAN NOOR AL'AMEEN* tare da Amaryan sa *DR. NAFEESAT AL'AMEEN AL'AMEEN (ƊAHIRA).* bikin da ya tara dubbannin jama'a, sai mu ce masha Allah

Daƙyar Usman ya halarci ɗaurin auren nan, ana gama wa aka neme sa aka rasa, dama be gayyaci kowa ba, bare abokan sa ma ba ƴan nan bane, sai dai wasu sun ji labari kuma sun halarta, sai dai shi be ma gansu ba ya arce.

Ana ta neman Ango an rasa, haka dai aka gama gaishe-gaishe ƴan uwa da abokan arziƙi aka soma watse wa.

Cikin gida ma ana ta shagulgulan biki, babu abinda za'a yi a bikin, tunda daga Amaryan har Angon babu me halarta, Ɗahira na fama da kanta, tunda tun sanda aka ɗaura auren jikin ta ya rikice, dole aka ɗaura mata drip aka yi mata alluran barci don zuciyar ta ya huta, dayake Abbu ne ya duba ta shiyasa ya gane damuwa ce kawai da yayi mata yawa

Lokacin da ta tashi har ɗakin ya shiga, ya zauna daga shi sai ita, yayi mata nasiha me ratsa zuciya, kuma ya roƙe ta "ta dena saka damuwa a ranta, ta riƙe auren ta da amana, tayi biyayyan aure", nasiha sosai yayi mata wanda take ta faman kuka.

An rigada an shirya mata Part ɗin ta ya tsaru, dayake duk na gida ne, Big Dady da Abba suka ɗau nauyin yin mata komi, an shirya mata ɗakin ta irin na ƴan gata, komi sai dai ace Masha Allah.


Zuwa dare aka kai ta ɗakin auren ta, wanda tasha kuka ba Ni da kuka ba, aka watse aka bar ta ita kaɗai tunda baza a kwanan mata ba.

Sai da Big Dady ya kira wayan Usman ya shaida masa "muddin be kwana a gida ba tare da matan sa ba, sai ya saɓa masa". Kuma ya basa umarnin yayi maza-maza ya dawo gare ta.





*******

Be dawo gidan ba, sai ƙarfe 01:00am. Na dare. Lokacin tuni Ɗahira tayi barci abin ta, bayan ta gama kwankwaɗan kukan ta son ranta, wanda ya haddasa mata zazzafan zazzaɓi, daƙyar ma barcin ya kwashe ta tana ƙudundune a kan gadon ta.





.









_to nan ake yin ta fa, ya zaman Ɗahira da Usman zai kaya? Wani irin zama za su yi a rayuwan auren su? Hmm ku dai gyara zama kawai Ni dai abinda zan ce muku kenan, yanzu

Please Login or Register in order to submit comment