Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya kalli Usman yace

"Kai kuma Fodio, the opportunity I have given you is enough. dole ne ka dawo Nigeria kaci gaba da aiki a asibitin mu, domin baza mu zira idanu ace kana can kana ma Nasara aiki suna ƙaruwa mu nan ka bar mu haka ba".

Usman da ya ɗago kansa yana kallon Kaka, a karo na farko yace, "wai Kaka meyasaka kake son takura min ne? I don't want to work here. I want to.."

Be dire maganar ba Big Dady ya daka masa tsawa, hakan yasaka shi yin shiru yana kawar da kai still fuskan sa ba walwala

"Umarni ake baka ba shawara ba ka ajiye aiki ka dawo nan kaci gaba, karka sake mu ƙara ja'inja da kai". Big Dady ya faɗi maganar da kakkausar murya

Murmushi Kaka yayi yace, "ka bar shi nace Lawal; ba na son kana nuna masa zafi, ai ba cewa yayi bazai dawo ba, abi shi a sannu, kowa zai iya tafiya. idan kuma da me magana ko ƙorafi akan wani abu sai yayi magana".

Kafin Kaka ya rufe baki Usman yayi saurin tashi ya fice, haka sauran ma su kayi ta tatashi suna ficewa ya rage daga Kaka sai su Big Dady


               *****

      Hajja Fatu ce ta shigo parlour'n Hajiya da sallama

Hajiya wacce ke zaune a parlour ta'amsa mata sallaman sannan tayi mata maraba

Zama Hajja Fatu tayi tana kallon Hajiya da murmushi a face ɗin ta tace, "Oh ashe haka abu ya faru? Na zo miki jajen abinda Ɗahira tayi wa Usman ne, gaskiya bata kyauta ba".

Hajiya tace, "Haka ne. amma shima da laifin sa ai, da be taka mata wayan ba baza ta kawo ƙarar sa ba".

Ɗan taɓe baki Hajja Fatu tayi tace, "eh Haka ne kamar yanda ki kace, amma abinda tayi ai be kamata ba, wannan ai kamar tana so ta haɗa Ɗa da uba ne, ko ba kya ganin yanda Mahaifin sa ya nuna fushi dashi? Kuma da ba haka yake nuna masa ba, don Ni kai na shaida ce wajen ƙaunar da yake masa, amma a kan ta ya rufe idanu ya suburbuɗa masa faɗa a gaban ƙannin sa, wannan abun ba yi bane, idan ma uwarta take zugo ta ai zamu gani".

Shiru Hajiya tayi tana sauraron maganganun Hajja Fatu, kuma da alamun sosai zancen yake shigan ta duba da yanda fuskarta ta sauya, domin abinda aka yi wa ɗan nata dama be mata daɗi ba, amma kuma maganganun Hajja ya sake saka ta taji haushi matuƙa

Ita kuwa Hajja Fatu ganin haka ya saka ta sakin wani shu'umin murmushi tana cewa, "Ai sai haƙuri amma dai na san yarinyan nan yanzu hure mata kunne ake yi, ada ai ba ta yin haka duk kuwa da cewa yana dukan ta, amma yanzu tunda ana son haɗa sa da ubansa ai an koya mata yanda zata riƙa kawo ƙarar sa, kin ga hakan zai sa Mahaifin sa ya riƙa fushi dashi".

Hajiya kallon Hajja Fatu tayi don da alamun kalaman nata sun gama ratsa ta sosai tace, "nima naga alamun haka Hajja, sai dai ko ma wa ya koya mata da duk abinda suke nufi da ɗana sai dai ya koma kan su, babu wanda ya'isa ya shiga tsakanin ɗana da mahaifin sa, dole ne ma in ja masa kunne babu ruwan sa da ita tun wuri ya fita harkan ta, ba na son abinda zai saka mu sami saɓani, domin akan ɗana babu abinda bazan iyaba, kowa ya san da cewa ina matuƙar ƙaunar sa; don zan iya yin komi akan sa".

Ajiyan zuciya Hajja Fatu ta saki tana kallon Hajiyan da alamun nuna damuwa a fuskarta tace, "gaskiya ne Hajiya, gwara dai ayi wa tufkan hanci tun kafin magana tasha banban, Allah ya kyauta gaba to, Ni bari in tashi na tafi".

"To shikenan Nagode sai nima na leƙo". Cewar Hajiya da murmushi a fuskarta

Tashi Hajja tayi ta nufi ƙofa ta fice tare da barin Hajiya cikin tunani. Tana fita ta saki wani shu'umin murmushi fuskarta cike da farin ciki, dama abinda take so kenan kuma tana ganin da alamu tarkon ta ya fara kamawa, taku ɗaya zuwa biyu tayi ta tsaya tana juyowa ta kalli ƙofar parlour'n Hajiya, a fili ta furta

"Now the game has started. If I am Hajja Fatu, I will open the heart of everyone in the house. I will make everyone hate you, A'ishah. tare da ƴarkin da kika ƙwallafa rai a kan ta, zan maye gurbin zuciyar kowa da ƙauna ta a ran shi, zaki san kin shigo cikin Familyn da ba na ki ba, mu zuba dani dake.."

"Hajja ke da wace ce zaku zuba? Me tayi miki?"

Da sauri Hajja ta juyo tana kallon ta, wani irin bugawa zuciyar ta tayi, nan da nan tsoro da fargaba ya ɗarsu a cikin zuciyarta har bata san sanda ta fiddo idanu waje ba suna kallon kallo..

.

_Hhhh to Fans shin wa kuke tunanin wacce Hajja ta gani haka har ta sorata ainun?_

_karku manta da Comments, domin comments ɗin ku shi ke saka na ƙara yawan post._
[29/08, 1:30 pm] OumƊahira نفيسة: 💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*DOCTOR'S FAMILY*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱


*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA'IL LAWAL_




*بسم الله الرحمن الرحيم*



*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuDahirah*👈

*\F.W.A📚/*

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA'S FAMILY*_

*TUNATARWA*
'''Manzon Allah mai tsira da aminci, ya yi mana bayani a kan sallah da abin da Bawa yake iya samu. Cewa ya yi, "Yana yiwuwa mutum ya kawo sallah ga baki ɗayan ta amma a ba shi lada wadda ba ta wuce sudusin ta ko ushurin ta ba." Abin da yasa haka kuwa shi ne  rashin nutsuwa cikin sallah.
   Allah yasa mu dace.'''

.

*EPISODE Six*

Murmushi Hajja Fatu ta ƙirƙiro cikin tsananin ruɗewa da son ɓoye halin da take ciki tace, "am..uhmm babu, auhm Ni da wata ƙawata ce da taci amana ta". Taƙarishe maganar tana sake sakin murmushi

Ɗahira kuwa kallon ta kawai take yi, domin kuwa duk abinda ta faɗa ta riga taji, sai dai tayi tsananin mamaki da al'ajabin abinda Hajja Fatu take faɗa akan Mahaifiyar ta da ita kanta. ita ma ɗin nuna mata tayi kamar bata ji maganar nata ba illa sakin murmushi da tayi tace, "But Hajja, why don't you forgive her? I don't see the point in keeping a person in mind."

Wani irin ajiyan zuciya Hajja Fatu ta saki jin cewa ta yarda da abinda ta faɗa mata, hakan na nufin bata ji maganar da tayi ba kenan, murmushi ta sake ƙirƙirowa tace, "ƴata baza ki gane zafin cin amana ba, amma tunda kin ce in yafe ai Ni me iya yafe mata ne, nima sai yanzu na gane hakan be da wani amfani muyi ta sa'insa akan abinda be kai ya kawo ba".

Sai kuma ta sauya akalan maganar da tambayarta "ina zaki je kika yo nan?"

Ɗahira said, "I will reply to Mamana's message,"

Gyaɗa kanta Hajja Fatu tayi tace, "ok".

Sannan ta juya ta tafi batare da ta sake furta komi ba

Ɗahira kuwa bin bayan ta tayi da kallo har sanda ta ƙule wa ganin ta, maganganun Hajjan ne suka dawo mata

"What does that mean?" Tafaɗa aranta tana sake zurfafa a tunani

Tabbas ta san akwai abinda Hajja ke shiryawa akan Mahaifiyar ta, sai dai kuma duk yanda za'a yi baza ta taɓa bari taci nasara ba, tun farko dama tasan Hajja Fatu ba ta ƙaunar Mahaifiyar ta, Kasancewar ita A'isha wato Aunty Amarya Asalin ta ƴar Soba ce a ƙaramar hukuman Zaria, karatu ya kawo ta Kaduna tana zaune wajen auntyn ta, to anan ne Mijinta Al'ameen ya ganta har ya'aure ta, tun sanda aka kawo ta gidan Hajja Fatu ta nuna ba ta ƙaunarta kuma take son nuna ita ɗin bare ce acikin su, sabida alokacin ƙanwarta dama ta daɗe tana ƙaunar Al'ameen wato Abbu, to hakan ya saka ta ɗau alwashin sai ta fid da Aunty Amarya a cikin gidan ko ta halin ƙaƙa, don a cewarta tunda ƙanwarta bata same shi ba duk a dalilinta, to, itama sai ta rasa shi

Numfashi Ɗahira ta sauke tana ɗauke kanta daga kallon Hanyan da Hajja Fatu tabi, ko kaɗan baza ta so ta faɗa wa Mahaifiyarta wannan maganar ba, domin ta san hankalin ta zai tashi matuƙa, sai dai zata dage da taya ta da addu'a duk wani wanda ke binta da sharri ya koma masa

takawa tayi ta shige Parlour'n Hajiya da sallama

Hajiya da har yanzu take zaune tana tunanin maganar Hajja Fatu, ta ɗago kanta tana bin Ɗahira da kallo, fuska babu walwala ta'amsa mata sallaman

Ita kuwa Ɗahira ƙarisowa tayi ta zauna a kujera tana kallon Hajiya tace, "Hajiya sannu da hutawa".

"Yauwa". Hajiya ta'amsa ataƙaice tana sake tamke fuska

Sosai Ɗahira tayi mamakin halin da Hajiya ta nuna mata, domin ta san ta mace ce me fara'a, kuma suna ɗasawa da ita ainun, tayi mamaki da ganin sauyawar fuskarta amma kuma sai ta dangana hakan da ko wani abun ne ke damunta, don ko kaɗan bata yi tunanin abinda ya faru ɗazu ba

"Hajiya dama Mama ce tace inzo in amsar mata saƙo".

Miƙe wa Hajiya tayi batare da ta tanka mata ba ta shige ɗaki, sai gata ta fito da leda ta miƙa mata

Amsa Ɗahira tayi cike da girmamawa ta tashi ta fice

Ita kuwa Hajiya rakata tayi da harara tana jan tsaki

Ɗahira da har ta fice sai da tajiyo sautin tsakin, hakan yasaka taja ta tsaya tana kallon ƙofar, nan take kuwa abinda ya faru ɗazu ya dawo mata kwanya "kenan Hajiya tana fushi da ita ne saboda abinda ya faru ɗazu?" Ta tambayi zuciyarta cike da mamaki, taɓe bakin ta kawai tayi tajuya tayi tafiyar ta, Part ɗin Hajja Fatu ta shige, babu kowa a parlour sai ta nufi ɗakin Shakira kanta tsaye, tana isa ta tura ƙofar ta shiga da sallama a bakin ta

Shakira dake zaune gaban mirror tana gyara kayan kwalliyan ta ta ɗago da kanta tana kallon ta, sai kuma ta saki murmushi tana cewa, "ƴan mata adon gari me aka kawo min ne?"

Ƙarisawa kusa da ita Ɗahira tayi tana jingina da bango tace, "a'a Ni babu abinda na kawo miki, amsa dai nazo yi, kin san yanzu wayata ta samu matsala shiyasa zaki haɗo min kan Littafaina in tafi dasu".

Dariya Shakira tayi tace, "kai wlh Ƴanmata yau kin bala'in burge Ni, ashe zaki iya kai ƙaran Ya Usman? Shin wai ina tsoron da kike mishi ya tafi?"

Taɓe baki Ɗahira tayi kana tace, "ai dama ɗan hakin da ka raina wataran shi ke tsole maka ido, kema da kanki kin faɗa da ba yanzu ba, Ɗahiran Da; da na yanzu sun sha banban".

Miƙe wa Shakira tayi tana sakin murmushi tace, "gaskiya ne ƴan mata, don yanzu ba lokacin Da damuke yara bane, yanzu mu ɗin DOCTORS ne manyan yara, kinga kuwa baza mu iya ɗaukan raini ba, wlh kin burge Ni amma Ni kam ba na tunanin zan iya fa".

"Dama ai ke matsoraciya ce, Ni dai ɗauko min in tafi Mama jira na take yi".

Drower Shakira ta buɗe ta soma kwaso mata Books ɗin tana cewa, "hmm baza ki gane bane, Ya Usman ya wuce gaban kwatance, wlh ko wacce mace idan har zata haɗu dashi sai dai ta kalle shi da idon soyayya amma ba faɗa ba, kwarjinin sa da kyawun sa tare da isa da izzar sa su kansu sun ishe ka, ina matuƙar shakkan Ya Usman kuma ba na son abinda zai haɗa ni dashi da har zai saka mu saka ƙafan wando ɗaya dashi, but ke kam nasan kashin ki ya bushe wlh don ba ƙyale ki zai yi ba, ya lafiyan Kura ma bare ace tayi hauka, uhmm ke dai kawai ki guji ranan haɗuwan ku".

Ɗahira takowa tayi tazo gaban ta ta soma kwashe Littafan tana zubawa a leda, batare da tabi ta maganarta ba tace, "Ni kin ga tafiya na ba ni da lokacin ku daga ke har shi ɗin".

Tajuya tayi ƙofa zata fice, dai-dai lokacin da Yusra ta turo ƙofan ta shigo suka kalli juna suka ɗauke kai sannan ko wacce ta wuce

ƙarisowa Yusra tayi kusa da Shakira dake zaune bakin gado; itama ta zauna gefen ta tana cewa, "wai ya maganar mu na zuwa shopping yaushe za mu je?"

Shakira tace, "ki bari a kawo mana Mota mana, kin ga sai muje aciki ko ya kika ce? Don Ni wlh bazan fita a tsohuwar mota ba, gwara muje muna tsole idanun Gayu"

Dariya Yusra tayi tana cewa, "shegiya inda ba'a ce za'a ba mu ba fa? ya za kiyi dole ki fita a ciki".

"Uhm baza ki gane bane amma dai gwara mu bari sai ranan Sunday ɗin muje, kin san har gidan su Marcy za muje ranan wlh".

Hannu Yusra ta bata suka kashe tana cewa, "gaskiya ne Tawan ai wlh yanzu ma kika tuna min da ita, ahh ai dole ne ma muje, kai wlh har kin sani na ƙosa ranan tazo, uhmm Allah ya kai mu har na hango irin wulaƙancin da zanyi".

Sai suka kwashe da dariya suna sake tafawa

Shakira tace, "kin san yanzu muka gama hiran ki da mutumiyar taki?"

"Wace kenan?" Yusra ta tambaye ta cike da rashin fahimta

"Wace kika sani ban da Ɗahira, Ni na rasa meyasaka ba ta ƙaunar ki duk sanda zamu zauna sai tayi maganar ki, abun mamakin ma yanda tayi ta zagin Ya Usman anan wajen, uhmm duk wai akan waya".

Ɗaure fuska Yusra tayi tace, "wlh yarinyan nan akwai ranan da zan cire mutunci mu goge raini, ni fa na gaji da kawo miñ ƙarar ta da kike yi a kaina tana zagi na, wlh zan je inji dalilin da ya saka take zagi na". Tana ƙarike maganar ta miƙe da ninyar tafiya

Shakira tayi saurin riƙe ta tana cewa, "ke kuma meye haka? Yau ta soma zagin ki da zaki damu? Wlh idan baki iya kama ɓarawo ba sai ya kama ki, yanzu idan kika je sai kice mata mene? ki bari duk ranan da kika kama ta tana maganar naki sai ki ɗau mataki amma ba yanzu ba, kuma menene na damuwa tunda gani ina faɗa miki komi?".

Yusra dake tsaye har yanzu kallon Shakira take yi har ta dire aya kana ta ɗaura da nata, "But wlh today I have to tell Hajiya everything, dama ina ɓoye mata ne ban son hankalin ta ya tashi". Daga haka ta juya ta fice fuuu kamar ana tura ta

Tana fita Shakira ta saki murmushi tana cewa, "Dama haka nake so gwara kije ki faɗa ma Hajiyar ki don ta ƙara ƙullatan ta, shegiya Ni wlh ba ƙaunar Ɗahiran nan nake yi ba, da wani idanu sai kace na fataken dare, kai ko a turawan ma bana tunanin akwai masu irin wannan idanun.."

Ƙaran buɗe ƙofarta shi ya katse mata maganar ta, tayi saurin juyawa tana kallon me shigowa, ganin Mahaifiyar ta ne ya saka ta sauke ajiyan zuciya har da dafe ƙirji

ƙarisowa wajen ta Hajja Fatu tayi tana kallon ta tace, "What happened to Yusra leaving here in a rage?"

Dariya Shakira ta kwashe dashi tana cewa, "me kuwa zai faru in ba zugo ta da nayi ita da Ɗahira ba, ai yau sosai na fusata ta don har maganar Ya Usman nayi mata, yanzun ma Mahaifiyar ta za taje ta sanar ma wa".

Sai kuma ta kuma kwashe wa da dariya tana cewa, "wlh da ma maganar ya koma kunnen Ya Usman inga yanda zai yi ƙulun kubura da ita".

Hajja Fatu itama dariyan tayi tace, "yauwa ɗiyar albarka ai gwara da kika zugo ta ɗin, idan ta sanar wa mahaifiyar ta na san yanzu gaba ta soma ita da A'isha, hmmm mu zuba yanzu ma aka soma".

Wannan shine halayyan Shakira da Mahaifiyar ta, ko ince ƙudurun su akan Ɗahira da Maman ta

Yusra da Ɗahira basu shiri tun farko; sakamakon zigin da Shakira take yi a tsakanin su batare da sun sani ba, ita Yusra akwai zafin kai da saurin fushi, tun farko dama ba wani shiri suke yi da Ɗahira ba, hakan yasaka Shakira ta samu dama take ƙara wa abun wuta, duk idan suka zauna tare da Yusra sai ta ce mata, "Ɗahira ta zage ta, ko tayi gulmanta", hakan yasaka Yusra ko magana ta dena ma Ɗahira kullum kallon ta da abun take yi, ita kuma Ɗahira dama ba me son shiga harkan da babu ruwan ta bane bare kuma idan ana mata wulaƙanci, don haka itama ɗin sai ta fita harkan ta a cewar ta "duk ranan da ta sauko ta dena ɗaga mata kai sai su ci gaba da mutunci" kuma dama Ɗahira tana ganin itace Babba babu yanda za'a yi ta zauna tana bin ƙanwar ta don kawai tana son su shirya tunda ta san bata yi mata komi ba, duk da su huɗun ba wani tazara ne a tsakanin su ba duk sa'annin juna ne, sai dai Ɗahira aka fara haifa yanzu haka shekarun ta 25years and Two Month, sai Shakira me shekaru 25years cif-cif, sai kuma Yusra me 24years and 8month, maraban su da Fadila kwana goma ne

Gaba ɗaya ahalin gidan halayyan su ɗaya ne na jijji da kai da nuna taƙama, sai dai na wasu ya fi na wasu ne musamman ma Usman da ya fi kowa a gidan, kuma hakan a jinin su yake.

.

_Hmm now the game has started because there is a lot cakwakiya  in this family, just go ahead and follow me and suburbuɗo me a comment to get more Post.
[29/08, 1:31 pm] OumƊahira نفيسة: 💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*DOCTOR'S FAMILY*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱


*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA'IL LAWAL_




*بسم الله الرحمن الرحيم*



*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuDahirah*👈

*\F.W.A📚/*

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA'S FAMILY*_

.

*EPISODE Seven*

Sallama tayi ta turo ƙofar ta shigo, Aunty Amarya dake zaune gefen gado ta'amsa mata tana kallon ta

ƙarisowa tayi ta zauna kusa da ita tare da miƙa mata ledan tana cewa, "Ga shi Mama".

Bata amsa ba tace da ita, "Where have you been waiting for me?"

Ɗahira tace, "na je wajen Shakira amsan Littafaina ne".

Gyaɗa kai kawai tayi tana ɗaukan ɗan kitt ɗin dake gaban ta ta miƙa mata tace, "ga shi Abbun ki ya ce in baki kyautar sa ne".

Saurin miƙa hannu Ɗahira tayi ta'amsa tana buɗe wa, murmushi ta saki ganin danƙareriyar sarƙan gwal kana ta kalli Maman nata tace, "ina Abbu ɗin?"

"Ya fita, Ni kuma ki riƙe wannan ledan da kika amso sai ki ɗinka".

Dariyan farin ciki Ɗahira ta saki kana tayi mata godiya tare da nuna murnan ta a fili, buɗe ledan tayi ta soma duba wa, atamfofi ne guda biyu masu kyan gaske sai kuma Material guda ɗaya

"Mama Nagode sosai Allah ya saka da alheri".

Murmushi Aunty Amarya tayi tana kallon tilon ƴartan cike da so da ƙauna tace, "ki dena godiya tunda ya zama dole ne mu yi miki".

Daga nan miƙe wa Ɗahira tayi zata fita, Aunty Amarya ta kira ta ta dawo, sake zama tayi inda ta tashi tana kallon Mamar nata

Ita kuwa cikin sauya fuska tace, "Meyasaka kika kai ƙarar Usman don ya fasa miki waya?"

Shiru Ɗahira tayi tana sunkuyar da kai ƙasa

" I don't want to hear it again, do I?"

Gyaɗa kanta tayi

"Tashi ki je Allah miki albarka".

Sai da ta'amsa da "ameen". Before leaving

Tana fita ɗakin su ta shiga

Fadila na kan gadon ta tana latsa waya sai faman doka murmushi take yi, idan za'a rantse ma bata san da shigowan ta ba

ita kuwa Direct wajen gadon ta ta nufa ta'ajiye kayan hannun ta, fiddo kayan tayi tana gani, har ta gama dubawan ta'adana sannan ta dawo ta zauna ta ciro Books ɗin ta zube su saman gadon

dai-dai lokacin ne Fadila ta ɗago kai ta kalle ta, nan idanunta suka faɗa kan NOVELS ɗin dake zube kan gado, da sauri ta'ajiye wayan ta tataso ta nufo wajen ta tana zama kan gadon;, ta saka hannu ta ɗauki ɗaya daga cikin litattafan, cikin farin ciki ta ɗago tana kallon Ɗahira tace, "Hey Sis Where did you get this book?"

Ɗahira da take riƙe da ɗaya daga cikin litattafan me suna *BARRISTER IBRAHIM KHALIL* tana dubawa ta bata amsa, "It's mine".

"Wayyo Allah wlh na daɗe ina neman Littafin *RAUDHAN* nan amma ban samu ba, Please ki ara min in karan ta, sosai nake son Littafan *JIKAR LAWAL GOMA* amma na rasa inda zan samu, ko da naje kasuwa nayi yawo but Allah be sa na samu ba".

Ajiye Littafin hannun ta tayi tana kallon ta tace, "Ni kam samun littafan ta ba ya min wuya, idan kina so sai ki bari adawo min da wayata in saka ki group ɗinta".

Murmushi Fadila tayi tace, "Thanks Sis, kai wlh har naji daɗi! na ƙosa naga ƙarshen abinda zai faru tsakanin *RAUDHA* da Captain Rayyan".

Miƙe wa Ɗahira tayi ta shige Toilet ta bar Fadila nan zaune har ta soma karanta NOVELS ɗin.

.

_If you need my Book so contact me on this Number 07065334256._

.

⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

    Tun sanda ya fito General parlour ya nufi part ɗin su, cikin ɗakin sa ya shiga ya rufo ƙofan, Direct gaban Royal Bed ɗin sa ya nufa ya zauna a bakin gadon, har a lokacin be saki fuskar sa ba sai dai baza ka iya gane a halin da yake ciki ba, ya jima ahaka yayi shiru yana tunani sannan daga baya ya miƙe ya soma haɗa kayan sa cikin trolly, bayan ya gama Toilet ya shiga be jima ba ya fito ya bar ɗakin, yana fito wa parlour ya tarda Hajiya zaune tana kallo, a hankali ya taka ya'iso wajen ta ya sami waje kan sofa ya zauna

Hajiya kallon sa tayi tace, "Dama kana ciki?"

Gyaɗa mata kai kawai yayi yana mayar da idanun sa kan t.v

kallon sa Hajiya take yi tana karantan yanayin sa, duk da ta san halin ɗan nata ba kasafai kake gane alƙibilan sa ba, kiran sunan sa tayi

hakan ya saka ya juyo yana kallon ta sai dai be amsa mata ba

"Ina son ka fita harkan yarinyan nan ba na son ko kaɗan wani abu ya sake haɗa ku, yanzu ba kamar Da bane".

Usman kallon ta yake yi a rashin fahimta, don be fahimci abinda take magana akai ba, sai dai kuma bazai iya buɗe baki ya tambaye ta ba

itama Hajiya ganin yayi shiru be ce komi ba; sai taci gaba da kallon ta don ta san ba amsa mata zai yi ba

sai da yaja lokaci a zaune a wajen be yi abinda ya kawo sa ba kafin daga bisani daƙyar ya buɗe baki yace,"I'm leaving".

Kallon sa tayi batare da ta gane me yake nufi ba

hakan ya saka ya kawar da kai yana ɗan motsa bakin sa

"Ina zaka je?" Ta tambaye sa don ita bata gane inda za shi ba

In a calm and proud voice he said, "Turkey".

Hajiya tace, "kamar ya zaka koma kai da kace sai kayi kwana biyu?"

Shiru yayi

"Are you talking quietly?"

"I have a job there."

Shiru tayi tana kallon sa, shi kuwa ya kau da kai don be san ma su haɗa idanu

"Shikenan amma ka bari sai gobe sai ka tafi, yau dai ka haƙura".

Be ce komi ba ya miƙe ya nufi ɗakin sa, yayinda ita kuma taraka sa da kallo tana mamakin irin halin sa

Shi kuwa yana shiga keey ɗin mota ya ɗauka ya fito ya zo ya wuce Hajiya still tana bin sa da kallo

parcking space ya nufa ya ɗau motar sa ya bar gidan.

⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

        *WASHE GARI*

Wajen ƙarfe 05:30pm. Na yamma Ɗahira na zaune saman gadon ta tana karatun Novel *(JARUMAI na Jikar Lawal Goma).*

Fadil ne ya shigo ɗakin kamar an hankaɗo shi ko sallama, wajen ta ya nufa yana dariya yace, "Aunty, are you still here?"

Kallon sa kawai take yi batare da ta furta komi ba

sai ya sake sakin dariya yana cewa, "Yaya Usman ne ya bani saƙo in baki shi ne naje ɗakin Kaka neman ki ashe kina nan kina faman karatun Novel, Wai me kuke karantawa aciki ne?" Yaƙarike maganar yana kai hannun sa kan littafin

Buge hannun sa tayi tana hararan sa tace, "kai ba na son iskanci; Yi abun da ya kawo ka ka ware".

Miƙa mata Leda yayi tare da wayan ta da aka farfasa yace, "ga kwaraɓaɓɓiyan wayan ki inji Kaka".

Bata ce komi ba ta'amsa tana ajiye wa taci gaba da karatun ta

shi kuma Fadil tsayawa yayi yaƙi tafiya yana kallon ta

Ɗago kyawawan idanuwan ta tayi ta maida kansa, "What's stopping me?"

"Aunty Ɗahira ki bani wannan wayan mana tunda kin ga kin samu wata".

"What are you talking about now?"  Ɗahira ta tambaye sa still tana kallon sa

Ɗan turo baki yayi yace, "ai gaskiya na faɗa ba kwaraɓaɓɓiyan ba ce?"

Hannu tasa da ninyan riƙo sa yayi

Please Login or Register in order to submit comment