Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ce komi ba, yana fita ta kwanta tana lumshe idanun ta tare da ci gaba da tsiyayar da hawaye

Yau wani irin baƙar rana ce a rayuwan ta da tazo mata? Ba ta jin zata iya kai wa zuwa anjima a yanda take ji, taya ma zata iya rayuwan aure da mutumin da tafi tsana a rayuwan ta? Sannan shima ya tsane ta fiye da kowa? Taya?

"Ya ilahi! Wannan wani irin mummunan ƙaddara ce ta zo min? God I beg you! If I am asleep, O God, wake me up quickly." Ta ƙare maganar tana me fashewa da kuka, kukan da ke fitowa can cikin zuciyar ta, tare da saka mata raɗaɗi me zafi, babu wanda zai iya gane halin da take ciki, sai wanda ya tsinci kansa a irin wannan yanayin, tamkar dai ranta zai fita take ji sabida tsaban ƙunci da baƙin cikin dake tattare da ita.




⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

           "I'm so happy Hajja wlh, Ni wannan haɗin da aka yi yayi min dai-dai, domin kuwa ta hakan ne Ɗahira zata ɗanɗani wulaƙanci a rayuwan ta, Ni na tabbata babu ta yanda za'a yi Ya Usman ya ƙaunace ta, I know Kare ma sai ya fi ta daraja a gidan shi". Shakira ta ƙarisa maganar nata cike da farin ciki da ya nuna a fuskar ta

Cikin ɓacin rai Hajja ta kalle ta tace, "dalla rufe min baki, kin san kuwa abinda zai faru a wannan auren da kike murna? To bari kiji muddin ina numfashi sai na wargaza auren nan, Ni da nake neman hanyar da zan fitar da uwar ta gaba ɗaya a gidan, a'a sake neman gindin zama suke yi a gidan, tun farko a raina ke nayi Wa sha'awar auren Usman, amma hakan be faru ba.."

"Ni kuma Hajja?" Shakira ta faɗa tana me ƙwalalo ido waje tare da dafe ƙirji

Dogon tsaki Hajja taja tana cewa, "meye kuma haka?"

"Yo Hajja do you know what you are talking about? Ni fa kike wa fatan rayuwa da wancan miskilin mara mutunci? Ina sam.. Allah ya kyauta wlh, gwara ma da Allah yasa nayi aure na; ba Ni ce aka haɗa Ni dashi ba".

Tashi Hajja tayi fuuu ta wuce ta bar Part ɗin, don sosai Shakiran ta ɓata mata rai

Ita kuwa Shakira taɓe baki tayi tana gyara zaman ta tace, "lallai kam Hajja ban san ba kya so na ba sai yanzu, ina Ni ina auren wannan mutumin? Kenan in ƙarike rayuwa ta a cikin uƙuba da rashin jin daɗin Rayuwa? Ina sam".  Sai kuma ta kwashe da dariya tana cewa, "ai wlh haɗin nan ya min daɗi, uhmmm ina tausaya miki Ɗahira, kin shiga bakin mayunwacin zaki, me fitar dake kuma ban ganshi ba, haka zaki dauwama kina me dana-sani a rayuwan ki".




             ⚫⚫⚫

          Direct Hajja part ɗin Hajiya ta wuce, can kuwa ta gan su zaune da Yusra ran su duk a ɓace, musamman ma Yusra da take ta zagin Ɗahiran, tana aibata ta, sannan a cewar ta, "sam bazai yiwu Ɗahira ta auri Yayan ta ba, duk hanyar da zata bi sai tabi don ganin ta hana wannan auren".

         Shigowar Hajja a dai-dai lokacin ne Aunty Zainab ta fito daga ɗakin Hajiya take ce mata, "ke wace iriyan sakarya ce? Do you know what you are saying? Ɗahiran ƴar uwan ki kike aibata ta? Wai shin Yusra me ta tare miki ne da kike tsanar ta?"

Turo baki Yusra tayi tace, "wlh Aunty baki san halin wannan munafukar bane, sam na tsane ta sabida ko kaɗan ba ta da hali me kyau.."

"Will you shut up your mouth?" Aunty Zainab ta daka mata tsawa

Hajja tace, "to ai gaskiyar ta ta faɗa, shin ke baki san kitumurmuran da A'isha da ɗiyar ta suke ƙulla wa ɗan uwan ku bane? Wlh muddin kuka sake ya aure ta tabbas sai A'isha ta shanye shi".

"Haba Hajja wai don Allah me bayin Allan nan suka tare muku ne duk kuka bi kuka tsane su?What is wrong with this marriage? Ke kanki kin san Aunty Amarya ba mayya bace bare ta shanye shi, kawai kin ɗaura mata karan tsana kuna ta aibata su".

Wannan karon Hajiya ce tayi magana da cewa, "Zainab, shut up before I hurt you. Shashashan Yarinya ana faɗa miki Gaskiya kina kare su, to Ni sam ko da babu abinda za su yi masa, ban amince da wannan auren ba, sabida ba na son shi da ita".

Kallon mahaifiyar nata kawai Aunty Zainab take yi, sosai ranta ya ɓaci da irin wannan abubuwan da take ji yau a gidan su, "wannan wani irin tsana ce? Mene ne aibun su da ake ganin laifin su? Kai sam bazai yiwu ba, baza ta zira ido ta ga gidan su na ƙoƙarin rabewan kai ba, dole ne ta sanar da Dady". Juyawa tayi ta shige ɗakin Hajiyan, ta sumfuci Jinior dake barci ta goya shi, ta ɗauki gyalen ta da jakan ta ta fito, bata bi ta kansu ba ta wuce ta bar gidan.

        Ita kuwa Hajja zama tayi tana ta ƙara ingiza Hajiya a kan "lallai-lallai kar ta yarda da wannan auren, kar ta soma ayi wa ɗan ta auren dole tunda shima ba ya so".


Nan ake yin ta fa.. chakwakiya.





⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

           Shi kuwa Usman tsaban ɓacin rai da jin maganar nan, yana fita daga General parlor barin gidan yayi, tuƙi kawai yake yi ya rasa ina zai je sai faman huci yake yi, yayi tafiya me nisa kafin ya tsaya yana gangarawa gefen titi, a zuciye ya buga sitiyarin motan yana cewa, "impossible.. I will never marry this girl, I hate her! I hate her so Much! zan iya kashe ta ma idan har na ganta a gida na".


Gaba ɗaya idanun sa sun kaɗa sun yi jazur, tamkar zai haɗiya zuciya sabida ɓacin rai, jijiyoyin kansa sun fito raɗo-raɗo, haka ya kama gashin kansa ya matse yana me kiran sunan Kaka, sai kuma ya matse bakin sa cikin amon muryan sa yace, "wlh muddin kuka haɗa auren nan sai na kashe muku ita, gaba ɗaya sai kun yi dana-sanin haɗa Ni aure da ita". Ya ƙare maganar da dukan sitiyarin motan da mugun ƙarfi yana ihu, sai kuma ya kifa kansa saman motan yana me sakin numfarfashi, cikin slow voice yace, "I hate her! Then I will killed her".







.



.

_Hmm akwai jan aiki fa.. kuna ganin su Kaka ba su yi ganganci ba? Wani irin hali Ɗahira zata shiga? Shin maƙiyan ta suna yin nasara kuwa?_
[23/09, 9:21 pm] OumƊahira نفيسة: 💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTOR'S*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱


*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA'IL LAWAL_




*بسم الله الرحمن الرحيم*



*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA'S FAMILY*_

.



        *EPISODE Thirty Five*

         Usman be dawo gidan ba sai dare, yana shigowa parlor ya tarar da Hajiya na zaune tana tsimayen shigowar sa, domin kuwa a lokacin wajen ƙarfe 12:00pm ne na dare

Yana shigowa tayi zumbur ɗin zuwa wajen sa, cikin tashin hankali tace, "Ina ka je ne tun ɗazu ina buga wayan ka ban samu ba?"

Kallon ta kawai yake yi amma be ce komi ba, gaba ɗaya ransa a ɓace yake har yanzu, zuciyar sa gaba ɗaya ba ta masa daɗi, shiyasa ma ko kaɗan bazai iya buɗe bakin sa ba, bare yayi magana

Zata sake yin magana, sai suka ji muryan Big Dady yana cewa, "Ka dawo?"

Gaba ɗaya kallon sa suke yi kamar yanda ya kafe su da ido, yana tsaye a bakin ƙofar ɗakin sa

Shiru Usman yayi yana me kawar da kai daga kallon sa

"Dama kai nake jira, daga ke har shi a gidan nan zan yi mummunan saɓa muku, muddin kuka ce za ku ja da maganar auren nan, duk abinda kike faɗa min a kan a janye auren nan, to wlh muddin ina numfashi sai an yi sa, sakaran banza sakaran hofi, kuma wlh idan har baka dena nuna wa Daughter irin tsanar nan ba, Ni da kai ne a gidan nan, zan ga uban da tayi maka ka tsane ta". Yana ƙare maganar ya juya ya shige ɗakin sa

Usman be bari ya ƙara Socond ɗaya ba shima ya wuce ɗakin sa da sassarfa, yana jin Hajiya na kiran sa amma ina sam ya ƙi waigo wa

Itama cikin ɓacin rai ta nufi ɗakin Dadyn, tana shiga ta tarar da shi zaune gefen gado yana shirin kwanciya, ta ƙarisa wajen sa tana cewa, "wai me kake nufi da zaka saɓa mana a kan maganar nan? Ina ce yaron nan ba ya ƙaunar yarinyan? Kowa yasan da cewa jinin su be haɗu ba a gidan nan, kuma kafi kowa sani, amma sabida tada zaune tsaye ake son tauye wa ɗana haƙƙin sa, Ni fa bazan goyi bayan gaskiya ko ƙarya ba, Ni ɗana kawai na sani, abinda yake so shi nake so, tunda ya nuna ba ya son haɗin nan, kun hana sa ya faɗi ra'ayin sa, amma ai fuskar sa ta nuna muku ba ya so, to wlh bazai yiwu ba, a kan ɗana babu abinda bazan yi ba".

"Wato kina so ki nuna min wuyan ki ya isa yanka Asiya? Har Ni kike tsayawa a gaba na a kan wannan maganar kike son gaya min magana ko? To kar ki fasa, ki je kiyi duk abinda za ki yi, amma aure ne babu fashi, tunda kuka nuna ba ku son auren nan, to yanzu ne na ɗau ɗammaran sai ya aure ta, wlh bari kiji ko bayan raina bazan taɓa yafe wa ba muddin Usman be auri Ɗahira ba, idan kin ga ba'a yi ba kuwa, to ɗayan biyu ne, ko Allah ne be yi nufin matar sa ba ce, ko kuma Baba ne ya hana, shi ne kawai zan iya bin umarnin sa a duniyar nan, kuma ki ɓace ki bani wuri kar ki sake tanka wa tun kafin raina ya ɓaci".

Dole Hajiya ba don ta so ba ta juya ta wuce ɗakin ta, amma a ranta ta ɗau alwashin muddin ɗanta ba ya son auren nan, to itama baza ta taɓa son Ɗahira ba, sai ta muzguna wa rayuwan ta.




                   ⚫⚫⚫

       A wannan dare a cikin Usman da Ɗahira babu wanda yayi barcin farin ciki, zan iya cewa gaba ɗayan su a zaune suka kwana.

          Washe gari ma Ɗahira da zazzafan zazzaɓi ta tashi, sosai hankalin Aunty Amarya ya tashi, gani take yi wani abu zai sami ɗiyar ta, tunda ta san halin ta, abu kaɗan ke ɗaga mata hankali ya fitar da ita cikin kamannin ta. Tasa Abbu tayi gaba tana kuka a kan "ya taimaka a warware auren nan, tunda dai Ɗahira ba ta so, be kamata su yi wa ɗiyar su auren dole ba". Gaba ɗaya tarikice wa Abbu ya rasa yanda zai yi da ita, dole ya fito ya barta cikin ɗakin ya nufi ɗakin Ɗahira

Tana kwance ta ƙudundune cikin bargo sai rawan sanyi take yi, tun daga bakin ƙofa yana jin yanda haƙoran ta suke karkarwa

"Ya subhanallah.." Abbu ya faɗa yana zama bakin gadon, gaba ɗaya ya ruɗe da yanda ya ganta

Cikin sauri ya yaye bargon yana cewa, "Mamana kina jina?"

A lokacin ne ta buɗe idanun ta da suka kaɗa suka yi jazur ta sauke kan su daga Abbu har Aunty Amarya da ta shigo ɗakin a yanzu, sai hawaye take yi

Kallon sa Aunty Amarya tayi tace, "Abbun Zulaiha don Allah ka taimaki ɗiya ta, kana ganin yanda take yi ko? Shikenan ka ga zan rasa ta?" Tana maganar ne duk a rikice

Shi kansa Abbu tsaban tausayin Ɗahira ce ya kama shi, yace da Aunty Amarya "ta taimaka mata ta shirya ta su tafi asibiti, don be kamata su zauna a gida ba," sannan ya tashi ya fice.

          Kai tsaye asibiti suka wuce har da Aunty Amarya, inda tuni Umma ta je ta shafa wa mutanen gida halin da ake ciki, daga Hajja har Hajiya babu wanda ya damu, ita Hajiya ma ko a jikin ta, domin ta ɗanta take yi, tunda ya shige ɗaki a daren jiya ya ƙi fitowa, juyin duniya ta buga masa ƙofa ya buɗe amma ya ƙi, Usman da kwai kafaffiyan zuciya, idan yace ba ya son abu ba ya so ne kawai, idan kuma aka matsa mishi tabbas rayuka ne za su ɓaci.





              ⚫⚫⚫

          Hajja kuwa shiri ma tayi ta wuce gidan ƙawar ta Hajiya Sa'ima.

"Ya na ganki duk a firgice ƙawata? Lafiya dai me ke faruwa?" Cewar Hajiya Sa'ima tana kallon Hajja da ta buga tagumi

"Hmm Ina fa lafiya? Wlh baƙin ciki ne yake son kashe ni a kan A'isha".

Dariya Hajiya Sa'ima tayi tace, "wai ke kam har yanzu baza ki bar baiwar Allan nan ta huta ba? Ina ce yanzu Safiyya tayi auren ta har da yaran ta, kuma ke kanki kin fi kowa sanin tana jin daɗi a gidan mijin ta, to mene ne dole sai ta auri Mijin A'ishah?"

Hajja tace, "baza ki gane ba, wlh duk wanda yaci dani tuwo miya yasha, hankali na bazai taɓa kwanciya ba har sai na ƙuntata wa A'isha, sai na ɗaiɗaita ta sannan hankali na zai kwanta, buri na kawai yanzu in ga tabar gidan nan. Ba ma wannan ba, yanzu ta ɗiyar ta nake yi, kin san cewa yanzu za'a haɗa auren su da Usman?"

"Haba dai?" Cewar Hajiya Sa'ima tana kallon ta

"Wlh kuwa, ai tuni iyayen sun haɗa auren nan, kuma kin san halin Kaka, shi ya tsara wannan abun, sannan tunda yace za'a yi to tabbas sai anyi, tunda Ƴaƴan sa baza suyi masa musu ba, abinda yake so shi suke so".

Cike da baƙin cikin jin zancen Hajiya Sa'aima tace, "to shi Usman ɗin yana son ta ne dama?"

Dayake itama tana wa ɗiyar ta kamun Usman, burin ta kenan ɗiyar ta ta shiga gidan, shiyasa maganar be mata daɗi ba

"Ki bari dai, Usman ba ya son ta, haka Hajiya ba ta son auren, tunda duk yanda zan yi nayi don ganin naga ta tsane ta, kuma buri na ya cika, yanzu abinda nake so shi ne tsayar da auren nan, ba zan taɓa bari ayi auren nan ba, gwara taje ta auri wani a waje hankali na zai fi kwanciya, da ace ta auri ɗan gida, hakan na nufin wata rana A'isha da ɗiyar ta...". Sai tayi shiru saboda baƙin cikin abinda take son ƙarisawa

"Kin kawo kuka gidan da ya dace, ai tun farko abinda ya kamata kiyi kenan, ina da hanyar da zan taimaka miki wajen raba auren nan, akwai wani Malami a can hayin mu, wlh an bani labarin sa aikin sa kamar yankan wuƙa ne, ai kawai wajen sa zamu je ayi wa tufkar hanci".

"Hajja tace, "ke Ni ban ƙi aje wajen duk wanda za'a je ba, koda Boka ne, in dai buri na zai cika, idan ba Allah ya tsare Ni ba, da tuni a kan ɗana baƙar ƙaddarar nan zata faɗa, da tuni Baffa zata aura".

"Ke dan Allah?" Cewar Hajiya Sa'ima tana ƙwalalo ido waje

"Wlh kuwa, ke dai bari, A'isha gaba ɗaya ta gama siye ƴan gidan nan, asirin nata kuma so tayi ta mallake min ɗana, ɗiyar ta ta aure sa, amma sai da nayi da gaske sannan Baffa ya bar zancen, har yanzu kuma ba wai dena son ta yayi ba, sun rigada sun ba shi a ruwa ya sha".

"Jar uba..! To wlh zama be kama ki ba Fatu, tashi mu je kawai, ai wani kissa duk da zaki yi yanzu bazai yi aiki ba, tunda itama a tsaye take, watarana ma yanda kike son ganin ta fice a gidan, ke zata fitar wlh, ai yanzu kai ya waye sai ana yi ana neman taimako wajen malamai".


Hajiya Sa'ima tana yafa gyalen ta, suka fito suka hau motan Hajja Fatu suka bar gidan, suka nufi gidan Malam.





⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

               Yanda jikin Ɗahira yayi tsanani, dole aka bata gado

Su Big Dady duk hankalin su ya tashi da wannan ciwon na Ɗahira, sai dai babu wanda yayi yunƙurin sanar wa Kaka, kuma sai da suka kira gida suka yi musu gargaɗi

Duk kawaicin Aunty Amarya sai da tayi ta sharan hawaye a gaban su Big Dady, sosai hankalin ta ya tashi, musamman yanda wajen awanni biyu da kawo Ɗahira amma babu ci gaba, jikin ta sosai yayi zafi, suman da tayi kuwa babu iyaka, daƙyar aka samu numfashin ta ya dawo aka sanya mata oxygen, sannan aka saka mata ƙarin ruwa, zazzaɓin ne yayi mata mummunan kamu.





⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

         Su Hajja sun isa gidan Malam, inda suka samu ganin sa, sannan suka sanar masa abinda suke buƙata
Hajja ta so tace a hana auren ne, sai kuma taga idan tayi haka bata ci riba ba, sai tace a ƙara rura wutar ƙiyayyar da Usman yake yiwa Ɗahira, bayan an yi auren yayi mata sakin wulaƙanci tare da wulaƙanta rayuwan ta, sannan tana son itama Aunty Amarya tabar gidan, ayi mata saki kamar yanda za'a yi wa ɗiyar ta

Duk kuɗin da Malam ya buƙata, haka Hajja ta lale ta bashi, tunda tana da su, kuɗi ba matsala bace wurin ta, burin ta kawai haƙan ta ta cinma ruwa..




         ***** **** **********

            Su Big Dady ba su san takamaiman abinda ke damun Ɗahira ba, tunda daga Abbu har Aunty Amarya babu wanda ya faɗa musu, shi da kansa ma Abbun yayi mata gwaje-gwaje, inda ya gano damuwa ce ya haifar mata da wannan mugun zazzaɓin, kasancewar ta me raunin zuciya, wanda nan da nan damuwa yake kwantar da ita.

              Sai da aka kwana biyu, lokacin har Ɗahira tana iya gane mutane, saboda zafin zazzaɓin ya sauka sosai, sannan ne aka sanar wa Kaka

Duk da haka sai da ya tashi hankalin sa matuƙa, sosai yake ƙaunar Ɗahira a cikin jikokin sa, shiyasa ko ya ya ne abu ya same ta, sai ya shiga tashin hankali matsananci

Yanda yaga jikin nata kuma da sauƙi, sai yaji ɗan dama-dama a zuciyar sa, ya tambaye su Abbu "ciwon me take yi?"

Abbu yace, "zazzaɓi ne kawai".

Da haka aka ci gaba da kula da Ɗahira, kwanan ta biyar ta ƙara aka sallame ta. Koda suka dawo gida, daga Aunty Amarya har Abbu babu wanda yake barin ta ta zauna ita kaɗai, zaunar da ita Abbu yayi yayi mata nasiha sosai, wanda sosai ya ratsa jikin ta ainun, har tana jin zata iya yin musu biyayya, koda kuwa waye suka kawo gare ta, sai da Abbu ya sake yiwa Aunty Amarya kashedi, ta dena barin ta tana zama a ɗaki tana yin tunani, hakan zai saka damuwar nata yariƙa yawa har ya haifar mata da matsala, kuma ya hana ta zuwa aiki gaba ɗaya, yace "sai ta warke sosai"

Shiyasa koda yaushe tana ɗakin Aunty Amarya suna hira, ko tayi ta mata nasiha tana faɗa mata tayi ta roƙon Allah, idan Usman ba alkhairi bane a rayuwan ta, wlh Allah maji roƙon Bawa ne, kuma yana jin ta zai amsa mata

Da haka ne Ɗahira take samun sauƙi a cikin ranta, kasancewar ba ta zama ita kaɗai bare ta samu halin yin tunanin dake addabar ruhin ta, wuni suna tare da Aunty Amarya, ko aiki take yi sai ta kira ta ta taya ta, ko kuma Aunty Amarya tace mata "ta fito Parlour su zauna da Fadil su yi hira ko kallo," dayake Fadil me surutu ne shiyasa yake addabar ta da surutun shi, ko bata so sai ta biye mishi, yayi ta saka ta magana, hakan yasa kaso mafi yawa cikin damuwar ta take gushe wa

Yanzu sallan dare shi ne abun yin ta, koda yaushe tana kai kukan ta wajen Allah ne, da zaran aka ce dare yayi, to bata da sukuni, damuwar ta gaba ɗaya zai dawo mata, ta dinga kuka kenan tana ibada tana kai kukan ta wajen rabbi, Wanda shi ne kawai zai fid da ita a halin da take ciki, a kuma kullum ranan duniya sake jin tsanar Usman take yi a ranta, tana sake jin tabbas idan ta aure sa tamkar ta gama rayuwar farin ciki ne a rayuwar ta. Amma kuma babu yanda zata yi tunda auren nasa shi ne ƙadddaran ta, baza ta iya bijire wa iyayen ta ba, haka Allah ya so.





⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

           Fannin Baffa kuwa, al'amarin sa yayi ƙamari, duk yanda ya so ya cire Ɗahira a cikin ransa ya gaza, damuwa sosai yake ciki, dole ya koma shan giyan sa, don gani yake yi wannan hanyar ne kaɗai zai bi don samun sukunin zuciya, kullum ranan duniya sai yaje mashaya ya sha, ko kuma ya siyo ya zuba a ɗakin sa ya ɓoye, idan dare yayi ya rufe ƙofan sa ya sha yayi tatul ya kwanta barci

Hakan sai ya soma saka Sa'adatu a cikin ƙunci, domin ko kaɗan yanzu Baffa ba ya da lokacin ta, ta rasa yanda zata yi, har ƙaran sa ta kai wajen Hajja, amma duk faɗan da Hajja tayi masa be fasa ba, yanzu ta kansa kawai yake yi, sai yaga dama yake kula Sa'adatu, shiyasa duk auren ma ya soma fita ranta, tunda yanzu be da time ɗin ta, da zaran dare yayi zai rufe ƙofan shi ya barta, kuma har yanzu bata san yana shaye-shaye ba.
[23/09, 9:22 pm] OumƊahira نفيسة: 💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
              *FAMILY DOCTOR'S*
                         🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
   *NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱


*MALLAKAR:*
                 _NAFISAT ISMA'IL LAWAL_




*بسم الله الرحمن الرحيم*


*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA'S FAMILY*_

_Wannan shafin naki ne Shugaba adila, *SAFNA ALIYU JAWABI* Allah yaja da ranki ya kare ki daga sharrin maƙiya, Allah yasa kifi haka Amin ya allah._ 🙏

.

        *EPISODE Thirty Six*

         Lokacin da Ayush ta samu labarin maganar auren Usman da Ɗahira, hankalin ta idan yayi dubu, to, ya tashi, domin gani take yi tabbas idan har Usman Ɗahira zai aura, to ta rasa shi, domin babu ta yanda za'a yi Usman ya saki Ɗahira ya aure ta, ya ma za'a yi a haɗa su? Ɗahira tafi ta komi da komi, kyawu, nasaba, kuɗi, da komi ma Ɗahira tafi ta, ko kaɗan bata kama ƙafan kyawun Ɗahira ba, class da komi tafi ta, tasan babu namijin da zai samu kamar Ɗahira ya so ya rabu da ita, dole hankalin Ayush yayi matsanancin tashi, ta samu Safra da maganar ta sanar mata komi

Dariya kawai Safra tayi tace, "yanzu mene ne zai baki tsoro Ayush? Ni kam zan so ganin Lucky Babe ɗin nan da har ta samu the Handsome Guy ɗin ki, ina ga itama ta haɗu gaskiya tunda har ya zaɓe ta matsayin mata".

Ayush wayan ta ta ɗauka, ta lalubo pic ɗin Ɗahira, wanda suka ɗauka tun waliman da aka yi musu da za su fara aiki, ta nuna wa Safra tana cewa, "Look, kema kin san tunda a family ɗin su ta fito dole zata haɗu, wlh yarinyan nan muddin ta aure sa na rasa shi".

Sosai Safra ta yaba da kyawun Ɗahira, bata taɓa tunanin zata ganta haka ba, babu abinda ya ƙara tafiya da hankalin ta ya shagaltar da ita irin Sky Green eyes ɗin ta, baki kawai ta riƙe tana faman faɗin, "Wow!". Sai kuma ta kalli Ayush tace, "Truly the girl is Very Very beautiful! She is very close, ta burge Ni". Ta ƙare maganar da shafa fuskar wayan tana murmushi. Sai kuma ta sake kallon Ayush tace, "amma kina ganin haɗa su aka yi? Ba soyayya suke yi ba?"

"I don't know". Ayush tafaɗa fuska cike da damuwa

Murmushi Safra tayi tace, "tabbas wannan sai aikin Malam, ba na tunanin Usman zai taɓa son ki idan har yana tare da wannan kyakykyawar yarinyan, abu ɗaya kawai zamu yi yanzu, kamar yanda na sanar miki, dole mu san yanda zamu yi mu ɓata ta wajen sa, i mean sharri da tuggu shi ne nasaran mu, duk hanyar da zamu bi sai mun raba su dole".

"But how? Bayan kin san ƴar uwan sa ce, kuma ya san halin ta". Ayush ta sake faɗar haka har a time ɗin zuciyar ta cinkushe da damuwa

Killer smaller Safra ta saki, kafin tace, "Let's

Please Login or Register in order to submit comment