You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
ce babu ruwana".
Taɓe baki yayi yace, "jaaa can da Allah! Ki ɗauki ƴar ki ki wuce kin ji, duk kin cika min kunne da surutu".
"Shikenan Kaka, kora ta kake yi ko? Babu damuwa ai, dani kake zancen wlh". Cewar Aunty Zulaihan tana ƙarisa wa ta ɗauki Ilham tana saɓa ta a baya
Dama sun saba irin haka sosai, kusan a jikokin gidan, Kaka da Aunty Zulaiha sun fi wasan jika da Kaka, idan suka haɗu waje ɗaya bakin ɗayan su ba ya shiru.
Tashi Ɗahira tayi, tace wa Kakan "zata je ta raka ta". Sannan suka fice tare.
⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫
*WASHE GARI*
*12:30pm.*
Shigowar motan Usman ɗin cikin asibitin, yasa Ayush buɗe motan Safra tana leƙa wa, sai kuma ta juyo ga Safran dake latsa waya tace da ita, "Ga shinan ya shigo".
Ɗago kai Safra tayi, tana bin waje da kallo tana faɗin, "ina yake?"
"Wannan motan". Ayush ta nuna mata motan Usman da ya ƙariso kusa da na su ya tsaya
Da ido Safra tabi motan da kallo, shi kansa motan ba ƙaramin burge ta yayi ba, bare kuma sanda tayi tozali da mamallakin Motan, hohoho ai da sauri ta buɗe motan ta fito tana sake ƙare masa kallo
Itama Ayush fitowan tayi tana bin sa da kallo tamkar zata cinye sa, a duk socond ɗaya ƙaunar sa na ƙara ruruwa a zuciyar ta, sosai yayi mata kyau tare da ƙara mata kwarjini fiye da kullum, yana sanye cikin ƙananan kaya ne, wanda koda yaushe shigan da ya saba yi kenan, sai ƙyalli yake yi, kai da gani kasan hutu da jin daɗi ya zauna masa, kuma duk wanda ya kalle sa ya san cewa ba ƙaramin haɗaɗɗen Guy bane, sosai yake da son gayu fiye da tunanin mutum, shiyasa yake fita daban duk inda ya shiga, yana zama tamkar wani tauraro me haska waje, bare shi Fari ne, ga kyawu na ban mamaki.
Duk abun nan be ma san suna yi ba, tafiyan sa kawai yake yi ya shige cikin Hospital ɗin, fuskar sa kamar dai yanda take babu fara'a, illa kwarjini da take dashi, wanda idan ka kalle sa dole ne fuskar tasa ta burge ka, duk da kuwa babu ko ɗigon annuri, amma kwarjinin sa shi yake ƙara masa kyau.
"Gaskiya Ayush dole ne ki haukace saboda wannan Guy ɗin, Ni kaina ba ƙaramin tafiya da imani na yayi ba a kallon farko duk da Maza ba sa burge Ni, bare ke da kika saba ganin sa kullum". Cewar Safra tana kallon Ayush ɗin
Numfashi Ayush taja, kafin tace, "hmm yanzu kin yarda da Ni Ko?"
"Ƙwarai kuwa.. shiga mota mu je, ina da hanyar da za mu ɓullo masa, idan ya san wata ai be san wata ba, na saba haɗuwa da irin waɗannan guy ɗin masu murɗaɗɗen hali, kuma mun ci galaba a kansu". Ta yi maganar tana taunan cwhengum
Murmushi Ayush tayi, kafin suka koma cikin motan, Safra taja suka bar Hospital ɗin.
.
_Ko Me Za su shirya? 🤔 Muna dai biye da su ai._
[23/09, 9:19 pm] OumƊahira نفيسة: 💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTOR'S*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA'IL LAWAL_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA'S FAMILY*_
*NASIHA*
_Muna iya lura cewa ga al'ada in an Kira talaka zuwa fadar sarki yakan gyara fuska, ya yi ado don ya sami kyakkyawar maraba daga Sarki. To, in haka ne, ina ga in ya tashi zuwa tsayuwa gaban Ubangijin sa? Bawan da aka neme shi ya zo gaban Ubangiji, Sarkin sarakuna, mamallakin mamallaka, lalle kam ya fi kamata ya gyara kansa saboda wannan muhimmin muƙami. Ya kamata ya gyara kansa ta tsarkake tufafin sa da jikin sa, ya fito cikin kama mafi kyawu, kamar dai yadda aka umurci musulmi duka a cikin suratul A'ARAF, aya ta 31:_
_"ya ɗiyan Adam! Ku riƙi ƙawar ku a wurin ko wane masallaci"_
_Allah yasa mu dace._
.
*EPISODE Thirty Three*
"Kina da kuɗi a tare da ke? Domin kai tsaye wajen Malami na za mu wuce".
Kallon ta Ayush tayi, sai kuma ta girgiza mata kai alamun "A'a" kafin tace, "Malami kuma Safra? Wanne irin Malami? Me kuma zamu yi a can?"
Dariya tayi still tana taunan cwhengum ɗin ta tace, "neman biyan buƙata mana Ƙawata, Ai dole sai da haka, don wlh bari kiji, irin waɗannan Guy ɗin ba naki bane, kee wlh bazan yi kaffara ba, idan har kika ce ta haka zaki jawo hankalin sa, babu taimakon Malamai, to, zaki dauwama baki yi aure ba, domin wlh sai kin ruɓe a gidan ku. Yanzu dai za mu wuce wajen Malam, inyaso zan ranta miki kuɗi idan muka dawo ki bani".
Ayush dai ta kasa cewa komi illa kallon titi da take yi, tana me tunani a zuciyar ta, "anya wannan hanyar da ta ɓullo wa kanta me ɓulle wa ne? Domin tasha jin yanda mutanen da suke zuwa wurin boka suke ƙare wa, to amma dogon burin ta fa? Hakan na nufin muddin bata nemi taimako wajen su ba, to, har abada baza ta taɓa auren Usman ba?..".
Kai tsaye hanyar Zaria suka nufa, sun kusa shiga Zarian, sai suka karya kwana suka bi wata hanya, tafiya miƙaƙƙa suka yi a cikin hanyar me kama da jeji, domin ko kaɗan babu gida gaba bare baya. Sun yi tafiya sosai kafin suka soma hango ƙauyaku, inda suka sauka a wani ƙaramin gida da aka zagaye shi da kara, sai bukka da aka yi su da yawa a wajen, shiga suka yi gidan, inda Ayush sai kalle-kalle take yi tana biye da Safra dake tafiyan ta kai tsaye, ba tare da wata fargaba ba, ga duk kan alamu ta saba da zuwa
A bakin wani bukka dogo suka dakata, inda Safra ta hau faɗin, "an gaishe ka Malam, an gaishe ka Malam".
Daga ciki dariya ne ya biyo baya, inda yace, "Hajjaju Safra da baƙuwar ta, maraba da zuwa, za ku iya shigo wa".
Shiga Safra tayi, inda Ayush ke biye da ita
Yana da faɗi cikin bukkan, babban mutum ne fari sol yake zaune a gaban wani ƙaton ƙwarya baƙi, yana ɗaure da zanin atamfa a jikin sa yayi tamkar yanda ƴan Saudiya suke yi idan za su yi aikin hajji, sai gashin kansa me yawan gaske tamkar na mace, ya zubo masa har kafaɗun shi
Da kallo ya bi su dashi har suka zauna, kafin yace, "an sanar min da zuwan ku tun kuna hanya, kuma na san abinda ya kawo ku".
Ayush ce kawai tayi mamaki da kalaman sa, ban da Safra da ba yau ta soma zuwa ba
Kallon Ayush ɗin yayi yana faɗin, "yanzu me kike so ayi masa?"
Kallon Safra tayi, itama kuma ta gyaɗa mata kai alamun "ta sanar masa"
"Malam ina ƙaunar sa matuƙa, kuma so nake yi a saka mishi ƙauna ta yaji duk duniya babu wanda yake so face Ni, ina son ya zo min da buƙatar auren sa".
Tsare ta da ido yayi tamkar be san me take cewa ba
Sai ta kalli Safra a tsorace, sabida ba ƙaramin tsoro jajayen idanun sa suke bata ba, musamman da ya ƙure ta da su tamkar zai cinye ta
Hannun ta Safra ta kama tana son kwantar mata da hankali
Muryan sa suka ji yana cewa, "kee yarinya! Idan har aka zo nan ba a shigo min da tsoro, tun wuri ki dena jin tsoro na, idan ba haka ba, to zan saka miki wasi-wasi a zuciya, kuma duk abinda zan miki baza ki taɓa ganin dai-dai ba".
Da sauri Ayush ta gyara zaman ta tana cewa, "kayi haƙuri, bazan sake ba".
"Da yafi miki". Ya faɗa yana taɓa hannun sa a cikin ruwan dake gaban sa cikin ƙwarya, zane ya soma yi na ɗan mintoci, kafin ya ɗago yana kallon ta yace, "leƙo nan".
Matso wa tayi ta tura kanta ta yanda zata ga cikin ƙwaryan, Usman ta gani zaune a Office ɗin sa, yana shingiɗe a kan kujera idanun sa a rufe, kujeran na faman juya sa
"Wannan shi ne ko?"
Da sauri ta gyaɗa masa kai tana faɗin, "eh shi ne Malam".
Ci gaba yayi da zanen sa na ɗan wani lokaci, kafin ya ɗago yana duban su yace, "kina da rabon auren sa, sai dai a nan gaba, domin na ga gagarumar matsala tana kunno wa daga dangin sa, suna shirin aura masa ƴar uwan sa nan ba da jima wa ba. Kuma na duba duk yanda za'a yi, babu ta yanda za'a hana auren nan, dole ne sai ya aure ta".
"Malam kana nufin dai sai ya auri wata kafin ya aure ta?"
"Eh haka nake nufi".
"Amma meye mafita Malam?". Safra ta sake tambayar sa
Numfashi yaja kafin yace, "wannan yarinyan ƙaddaran sa ce, kuma dole ne sai ya aure ta babu yanda za'a yi, bazan iya muku aiki ba yanzu har sai sanda aka yi auren nasu, sannan ku dawo akwai abin yi, a nan ne nake da daman raba su ke kuma ki shiga, in har ba haka ba kuwa, babu ta yanda zaki aure sa tana cikin gidan sa". Ya ƙare maganar da nuna Ayush da duk ta gama firgita da jin abinda yake faɗa
"Yanzu Malam babu abinda zaka iya yi a kai? Ya kamata kayi wani abun, domin mun san zaka iya ne".
Cikin amon muryan sa yace, "babu abinda zan iya a kai yanzu, duk abinda kuke so ku dawo bayan auren su, a nan ne zan iya muku komi, ku tashi ku tafi".
Da sauri suka tashi sabida jin tsawan da ya danƙara musu, suka fice suka nufi motan su, hawa suka yi suka bar wajen, babu me magana cikin su har sanda suka fito bakin titi
Da damuwa a fuskar ta tsantsa Ayush tace, "yanzu ya za mu yi? Ga shi mun zo wajen Malamin, memakon samun mafita, sai faɗa min abinda ya ɗaga min hankali yayi, kuma ya ƙi mana aikin".
Numfashi Safra taja kafin tace, "ke a naki tunanin, wace ce yarinyan da kike ganin za'a haɗa su aure?"
"No bazan taɓa sanin hakan ba gaskiya, domin Familyn su babba ne, kinga babu ta yanda zan yi in gane wacce zai aura, kuma kwanan nan duk ƙannin sa suka yi aure na cikin gidan su, illa mutum ɗaya ce wacce yanzu tana gida bata yi aure ba, ban san kuma meyasa ba".
Murmushi Safra tayi tace, "tabbas ina ji a jiki na, ita ce za'a haɗa su aure, sai dai baza mu fara aiki a kan hakan ba, har sai mun tabbatar da maganar Malam, kar ki damu idan sun san wata basu san wata ba, tunda Malam ya gaza wannan aiki, uhmmm makircin mu shi ne zai yi aiki a nan".
"I don't understand?" Ayush asked looking at her
"I mean. duk ta hanyar da za mu bi don hana yiwuwar hakan za mu yi, domin cin ma burin mu, ke dai kawai ki tabbatar kin samo yarinyan ko wace ce, a nan ne zan tabbatar miki da shirin mu a gaba, inyaso sai mu koma ga Malam ya saka mishi ƙaunar ki a zuciya".
⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫
*AFTER TWO WEEKS*
Gaba ɗaya ahalin gidan suna zaune a babban Parlourn gidan, yau har da Aunty Zulaiha da Aunty Zainab duk sun samu zuwa taron Familyn da suke gabatar wa a duk ƙarshen wata, haka ma Shakira da Yusra duk sun hallara, har Sa'adatu tana a cikin parlour'n, kasancewar itama yanzu ta zama ƴar gida
Abba ya soma buɗe taro da addu'a, inda Kaka ya bi su bayan ɗaya yana jin matsalolin su, tare da tambayar zaman nasu a gidajen mazajen su. sai da komi ya nitsa kafin ya kira sunan Usman
Usman dake zaune a gefen Baffa kan two seater, ya amsa mishi yana me ɗago kai ya kalle sa
"Ina muka kwana a zancen mu na auren ka?"
Dama ya san kwanan zancen, duk da an kwana biyu ba'a tayar da maganar ba, shiyasa ya sake ɗaure fuska, cike da isa yace, "har yanzu ban samu wacce tayi dai-dai da ra'ayi na ba Kaka, Ni a gani na gwara a dena zancen aure na yanzu, because I'm not ready to do it now."
Big Dady ne yayi ninyan magana, sai Kaka ya katse masa hanzari da faɗin, "to shikenan, tunda baka shirya ba, ai mu mun shirya aurar da kai yanzu". Sai ya juya ga Ɗahira yace, "What about the My wife? Are you still silent?"
Gyaɗa masa kai tayi kanta a ƙasa tana wasa da kwalliyan rigan ta
"To duk wani dama da Yakamata mu baku mun rigada mun baku, tunda har yanzu baku samo abokan zaman ku ba, mun yanke shawara Ni da iyayen ku, Kai Usman, da ke Ɗahira, za mu haɗa ku aure a tsakanin ku, ina fata dai..."
Zumbur Usman yayi ya miƙe yana dakatar da Kaka da faɗin, "haba Kaka! What are you saying? Dani da wa zaka haɗa aure?"
"Dan uban ka With you and your younger sister Ɗahira". Cewar Big Dady yana tsare Usman ɗin da kallo
Huci Usman ɗin ya soma, kafin yace, "It is not possible at all. You must change your mind soon. I will never marry this girl." Yana gama faɗa yayi hanya zai fice
Big Dady yace dashi, "Wlh if you go out, ranka zai ɓaci, come back and sit down, ka dawo nace ka zauna ko baka ji bane?"
Lumshe idanun sa yayi yana dakata wa daga inda yake, dunƙule hannun sa yayi yana faman huci, kafin kuma ya juya a zuciye ya dawo inda yake da zama ya koma ya zauna, gaba ɗaya fuskar sa ta haɗe tayi murtik, jira kawai yake yi ya amayar da abinda ke cikin sa.
Hannun ta da Kaka ya riƙo, shi ya dawo da ita hayyacin ta, ta ɗago kai tana kallon sa da idanun ta da suke zubar hawaye tun soma jin zancen Kaka
Hannun ta ya sake riƙe wa ƙam yana faɗin, "Nafeesa mene ne ya saka ki Kuka?"
Kasa magana tayi illa kallon sa da take yi, sai da taji saukar muryan Abbun ta ne kafin ta sake ƙifta ido tana mayar da idanun wajen sa, jin abinda yake cewa ya tabbatar mata ba mafarki take yi ba
"Sakarci ne irin nata, amma in ba sakarci ba meye na kuka a wannan maganar?" Ya ƙare maganar yana balla mata harara
Gaba ɗaya mutanen wajen, idan ka ɗauke Sa'adatu da tayi murnan jin zancen nan, sai kuma su Abba da su sun san da maganar, amma babu wanda haɗin nan yayi masa daɗi, musamman Hajja da take jin tamkar ta shaƙe Kaka da maganar ya fito daga bakin sa, baƙin cikin ta ma har ya fi na Hajiya da take uwar Usman ɗin
Ita kanta Aunty Amarya bata san meyasa ba, sam ta ji zuciyar ta ta karye da wannan haɗin, tana ji a ranta tabbas ɗiyar ta zata shiga wani hali a kan wannan auren, tamkar dai wani abu zai same ta, "shin sun manta da cewa Ɗahira da Usman ba sa shiri ne suke son haɗa su aure?" Tayi wa kanta tambayar a cikin ranta..
Muryan Big Dady ne duk ya dawo da kowa hayyacin sa, yace dasu, "mun tsayar da ranan auren nan da wata ɗaya me zuwa, don haka ban yarda ko inji ko in gani wani ya yi maganar akasin abinda muka faɗa ba, sai kowa ya soma shiri tun yanzu, za ku iya tafiya".
Baffa ne ya riga kowa tashi ya bar parlour'n yana me riƙe da kansa
Da sauri Sa'adatu ta miƙe tabi bayan sa zuciyar ta fari karrr, ko ba komi tana gani an kawo mata ƙarshen matsalan ta
Ɗaya bayan ɗaya kowa ke tashi ya bar parlour'n, ban da Usman da Ɗahira da suke zaune tamkar an dasa su a wajen
Ganin haka yasa Aunty Amarya da zata wuce, ta nufi wajen ta ta ɗago ta, tare da riƙe mata hannu suka bar parlour'n
Shi kuwa Usman yana zaune ya haɗa kai da hannayen sa yana faman huci, gaba ɗaya idanun sa sun kaɗa sun yi jazur
Babu wanda ya kula shi a cikin su Abba, har sai da kowa ya watse, inda Abba ya gungura Kaka zuwa ɗakin sa, Big Dady na biye da su a baya yana amsa waya
While Abbu na zaune be tashi ba, sai da ya ga kowa ya bar parlour'n kafin ya miƙe ya iso gaban Usman, hannu ya saka ya dafa sa yana me kiran sunan sa
Ɗago jajayen idanun sa da har sun tara hawaye yayi, ya kai duban sa ga Abbu yana me taune haƙoran sa da ƙarfi, take jijiyoyin kansa suka fito raɗo-raɗo
Shi kansa Abbu jikin sa sai da yayi sanyi da yanayin da ya gansa, be iya ce masa komi ba illa kallon sa da yake yi
Hakan yasa Usman ya ɗauke idanun sa, yana miƙewa tsaye ya doshi ƙofa ya bar parlour'n
Da kallo Abbu ya bi shi da shi har ya fice, a ransa yana ayyana "shin wani irin tsana ne me ƙarfi da Usman yake yi wa ƴar sa? Anya baza su yi kuskure ba idan suka haɗa su Aure?" Babu me ba shi amsa, dole ya saki ajiyan zuciya ya juya ya nufi ɗakin Kaka ransa duk babu daɗi.
.
_too chakwakiya ... now the game will start ... Just follow me to hear how it will go ... Don't forget your comments it will make me more typing._
[23/09, 9:20 pm] OumƊahira نفيسة: 💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTOR'S*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA'IL LAWAL_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA'S FAMILY*_
*TUNATARWA*
'''Manzon Allah ya ce mana, "tsabta kam ita ce rabin imani kuma ita ce mabuɗin Sallah. Abu na farko da ake buƙata kafin a shiga sallah shi ne tsarki, tsabta ta zuciya da jiki, ta tufafi da kuma wurin yin sallar.
Sallah ibada ce ta ruhu, kuma a cikin ta ne Bawa yake ganawa da Ubangijin sa, yake tsayawa a natse a gaban sa yana yabo yana godiya, yana roƙon Allah ya shiryar da shi bisa ga tafarki madaidaici. Saboda haka bai kamata Bawa ya shiga wannan ganawa ba sai bayan ya shirya kansa da kyau, ya tsarkake jikin sa da tufar sa da wurin sallar sa. Zai yi alwala in ƙaramin tsarki ya kama shi; in kuwa babban tsarki ne sai ya yi wanka don kuwa ta haka ne zai haɗa tsarkin jiki da na zuciya a lokacin ganawar sa da Ubangiji.
Allah yasa mu dace.'''
.
*EPISODE Thirty Four*
Direct Aunty Amarya ɗakin ta ta wuce da Ɗahira, suna shiga ta zaunar da ita kan kujera tana kiran sunan ta
Sai dai ga duk kan alamu Ɗahira tayi nisa a duniyar mu ba ta jin ta. Sai da ta saka hannu ta riƙo mata kai tana shafa mata fuska, kafin taja numfashi tana ware idanun ta da suka sauya launi a kan ta
Ita kanta Aunty Amarya ta tsorata da yanayin kallon da take mata, shiyasa tayi saurin cewa, "Ɗahira Are you all right?" Ta ƙare maganar tana ɗan ƙara girgiza ta
Sai kawai gani tayi ta ƙame alamun ta sume idanun ta a buɗe, sosai hankalin Aunty Amarya ya tashi, babu shiri ta hau girgiza ta tana hawaye cike da ruɗu, sai kuma ta miƙe zata yi waje, har ta kai bakin ƙofa ta sake dawowa tayi cikin Toilet, domin tana ganin be kamata a san halin da ɗiyar ta take ciki ba, musamman yanda ta san ba ita kaɗai bace a sashin, yanzu sai aje ana yamaɗiɗi da maganar kuma ta daban
Ruwa ta ɗibo ta zo ta shafa mata a fuska, sai da tayi haka sau uku kafin Ɗahira ta farka, sai dai tana buɗe ido tayi arba da fuskar mahaifiyar ta sai ta fashe da kuka, nan da nan Aunty Amarya ta sake ruɗe wa, tayi saurin ajiye Cup ɗin hannun ta a ƙasa tana tambayar ta "what's going on?"
Cikin kuka Ɗahira tace, "Mama don girman Allah kiyi min rai! idan har ba mafarki nake yi ba, ki taimake Ni ki je ki cewa su Abbu ba na son Ya Usman, wlh Mama Mutuwa zan yi idan na aure sa, Mama ba ya ƙauna ta ko kaɗan, Ni ba na son sa wlh bazan iya auren sa ba, ki taimaka min Mama, ki ce musu kar su haɗa mu, sam-sam ba mu dace ba Mama". Sosai take kuka har da majinu
Riƙe ta Aunty Amarya tayi cike da tsantsan tausayin ta, cikin sanyin murya tace, "I don't know what to say to you Ɗahira, amma abinda zai fito daga baki na be wuce haƙuri zan baki ba, kiyi haƙuri ki ɗauki ƙaddaran ki, tunda iyayen ki sun rigada sun yanke wannan hukuncin; ki daure kiyi musu biyayya kinji?"
Girgiza kanta ta soma yi tana ci gaba da zubar da hawaye, tace, "Mama ko kin manta da waye za'a haɗa aure na? Aure fa za'a haɗa Ni dashi, Yaya Usman da ya tsane Ni tun ina tsumman goyo na, yanzu shi ne zan aura a matsayin miji na? Please Mom help me I can't marry him, I like Yaya Baffa .. "
Shigowar Abbu da sallaman sa, shi ya hana Aunty Amarya jin ƙarisan zancen nata, bare kuma dama tana kuka ne tana maganar, hakan yasa ba lallai ka fahimta ba. kallon sa kawai take yi bayan da ta amsa mishi sallaman nasa
Zuwa yayi ya zauna a kan hannun kujeran, inda suka saka Ɗahira a tsakiya dake faman kuka sosai, ta haɗa kanta da gwiwa tana ta rerewa, hannu yasa ya ɗago kanta yana kallon ta cike da tausayin ta yace, "Mama na, please stop crying. Stop kinji.. alfarma zan roƙa wajen ki, duk da na san ba kya son Usman, Amma Ina son ki amshi maganar nan hannu bibbiyu, kiyi mana biyayya kinji? Mu iyayen ki muka ga dacewan haɗa ku, abinda mun daɗe muna fatan haɗa zumunci, duk da bamu so mu yi wa ɗayan ku tilas ba, amma kuma ga shi mun aiwatar a kan ku, sakamakon rashin kawo naku zaɓin da baku yi ba, mu a ganin mu wannan haɗin da muka yi shi zai kawo daidaito a tsakanin ku, hakan ne ya ƙara bamu ƙwarin gwiwa, don Allah ɗiya ta ki daure ki amshi wannan haɗin da muka yi muku, ba na son ko kaɗan wani abu ya fito daga gare ki da sunan ɓata shirin iyayen ki kinji?"
Tsamm Aunty Amarya ta miƙe tayi hanyar waje tana me share hawayen tausayin ɗiyar ta, "kenan babu shakka dole sai an yi auren nan? Tana ji tana gani dole za'a ɗaura wa ɗiyar ta ƙwalli ɗaya wanda ba ta so" ba ma wannan ne matsalan ba, mutumin da ya fi tsanar ta da kowa shi zata aura, to taya zata ji daɗin rayuwa? gaskiya wannan abun da cutar wa ga ɗiyar ta
Da kallo Abbu ya bi ta dashi har ta fice, shi kansa ƙarfin hali yake yi domin babu yanda zai iya, wannan shawaran ba shi ne ya bayar ba, shi dai kawai ya bayar da yardan shi ne don biyayya ga mahaifin sa, amma yana ganin tabbas wannan haɗin akwai cuta wa ɗiyar sa, da yana da halin da zai samo mata wani, da tuni ya samo mata kafin hakan ta faru..
Numfashi yaja yana saka hannu ya ɗago kan Ɗahira da har yanzu take ta sharɓan kuka, kallon ta yake yi cike da tausayin ta yace, "yanzu shin Nafeesa ba mu isa kiyi mana biyayya bane?"
Ɗago jajayen idanun ta tayi tana kallon sa, cikin dauriya da cije kukan ta ta girgiza masa kai, sai dai tana son yin magana amma ta kasa
"But why don't you accept the destiny God has chosen for you? Why not accept your parents' choice?"
Shiru tayi tana shashsheƙan kuka, sai kuma daƙyar ta iya buɗe baki tace, "Abbu.. na.. na amin ce.. zan.. yi muku biya..yya".
Yace, "Alhamdulillah, this is what I want to hear from you, insha Allahu baza kiyi dana-sani ba, kuma ko yaushe ke ce a sama in Allah ya yarda, albarkacin biyayyan nan da zaki yi mana, Allah zai daidaita tsakanin ku, zaku yi alfahari da junan ku, Allah ya miki albarka kinji? Share hawayen ki". Ya ƙare maganar yana saka yatsun sa yana share mata
Itama hannun ta ta saka tana share wa
Yace da ita, "yanzu ga yi can ana kiran sallah, ki tashi ki je kiyi kinji? Kar kuma in dawo inga kina kukan nan kinji Mamana? ki sanya dangana a ranki".
Ɗaga masa kai kawai tayi har ya fita bata