Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sosai a zuciya, har ta zubar da hawaye.



                ⚫⚫⚫⚫

           Kai tsaye gidan su suka nufa, Sa'adatu tariga shi isa, inda ta zauna a kan ɗaya daga cikin kujerun parlour'n ta tana faman karkaɗa ƙafa, sosai ta cika tayi maƙil tsaban kishi, ita ko kaɗan yanzu ba ta ƙaunar Baffa ya raɓi Ɗahira, gani take yi hakan zai saka mutanen gida su san me ke faruwa tsakanin su, kuma ta san ako yaushe za'a iya kawo mata ita a matsayin kishiya, tunda ita ɗin ƴar uwan sa ce, baza su yi la'akari da daɗewan auren ba ko rashin sa.

        Shigowar Baffa ne ya dawo da ita daga guntun tunanin da ta afka

Kallon ta yayi kamar yanda take kallon sa yace, "ke wai Sa'adatu wani irin baƙin kishi ne kike son ki shigo min da shi gida na? Wato rashin hankalin naki ya kai har ki shiga tsakani na da ƙanwa ta? A kan me zaki riƙa min haka? Ke fa baki isa ki hana Ni abinda nayi ninya ba, kuma idan Allah yace Ɗahira mata ta ce, wlh daga ke har wacce take ɗaure miki gindin baku isa ku hana ba".

Sai kawai yaga ta fashe masa da kuka, cikin kukan take cewa, "wlh tallahi kamar a kunnen Hajja, wato kana nufin Ni da ita ba mu isa mu hana ka kula wancan yarinyan ba ko? Kenan Hajja bata da mutunci a wajen ka? Da kake cewa kar na shiga tsakanin ka da Ƙanwar ka; ai ba Ni ce na raba ku ba, wlh na gaji da abinda kake min, tunda ba ka gani na da mutunci ƙarar ka zan kai". Tana ƙare zancen nata ta tashi fuuuu ta fice tana ci gaba da kukan ta

Direct cikin gidan ta nufa, inda ta wuce Part ɗin Hajja don Kai ƙaran sa.

         Ta bar sa nan tsaye da sakakken baki, sosai ransa ya ɓaci da abinda ta faɗa, "kenan shi be da ikon da zai mata faɗa, sai ta ɗibi ƙafafu ta kai shi ƙara wajen Mahaifiyar sa? Anya zai iya wannan auren kuwa?"




.






_to ba mu dai sani ba baffa. 🤷_
[10/09, 8:50 pm] OumƊahira نفيسة: 💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
              *FAMILY DOCTOR'S*
                         🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
   *NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
                 _NAFISAT ISMA'IL LAWAL_



*بسم الله الرحمن الرحيم*






*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA'S FAMILY*_

*TARIHIN FARILTA SALLAH*
'''An farilta sallolin nan biyar ne gabanin ƙaura, watau hijira, da shekara ɗaya da rabi. Sallah ce kaɗai ibadar da aka farilta ta a sama a daren Isra'e, kamar dai yadda aka ruwaito a hadisin nan na Anas. Da farko an umurce shi da Sallah guda hamsin ne; da sannu aka dinga rage su har suka zama biyar a bisa roƙon da shi Manzon ya yi wa Ubangijin sa. Da suka zama biyar, sai Allah ya ce masa su biyar ɗin nan, dai-dai suke da hamsin.
Malamai da yawa sun yi bayanin yadda sallar ma'aikin Allah, mai tsira da aminci, take gabanin Isra'en.
Wasu malaman sun ce, "Gabanin Isra'e, babu wata sallah wadda aka farilta sai sallar dare (Ƙiyamul lail) wadda aka umurci ma'aiki da yin ta ba da iyakataccen lokaci ko adadi ba, kamar yadda yake a suratul Muzzammil, ayoyi huɗu na farko:
"Ya wanda ya lulluɓe! Ka tsayu domin yin Sallah a cikin dare (duka) face kaɗan, rabin sa, ko ka rage abu kaɗan daga gare shi, ko ka ƙara kansa...
Ma'aikin Allah ya kasance yana yin sallar a kashi biyu cikin uku na dare ko a rabin sa ko kuma sulusin sa. Musulmi suka dinga yi tare da shi kamar shekara guda har suka gaji; daga nan sai Allah ya shafe ta don jin ƙan su.
An ruwaito cewa sallar da Musulmi suke yi gabanin tafiyar dare suna yin ta ne kafin faɗuwar rana da kafin ketowarta kamar yadda yake a sallah littafin Almanhalil Azb. Gabanin ƙaurar Annabi zuwa Madina raka'o'in sallah bibbiyu ne, bayan ƙaura ne suka zama hurhuɗu, illa magriba da ta kasance raka'a uku, ita kuma sallar subahi ta tsaya a kan biyu saboda dogon karatun da ake yi cikin ta. Buhari da Ahmad sun ruwaito daga Nana A'ishah cewa, "an farilta sallah raka'a bibbiyu, bayan ƙaura ne aka mai da ita raka'a hurhuɗu, amma an bar sallar tafiya a kan raka'a ne bibbiyu, sai sallar magriba ita ko da ma raka'a uku-uku ce."
Allah ya sa mu dace.'''

.

        *EPISODE Thirty One*

        Tunda Sa'adatu ta shiga parlour'n Hajja, ta tarar da ita zaune, sai ta ƙara volume ɗin kukan ta tana nufan kujera kusa da ita ta zauna

Kankace me Hankalin Hajja ya tashi, nan ta soma tambayan ta ba'asin kukan nata

Sa'adatu ta sanar mata da abinda ke faruwa, daga zuwa gaishe da Ɗahira Da Baffa ya matsa mata tayi, har maganganun da ya faɗa yanzu

"Lallai kam Baffa yana son Wasa Dani a gidan nan, amma bari miƙo min waya ta in Kira sa".

Tashi Sa'adatu tayi ta miƙo mata wayan daga kan Centre table, ta ba ta

Kiran sa tayi ta ba shi umarnin zuwa yanzu

Be daɗe ba kuwa sai ga shi ya shigo parlour'n da sallama

Tsaban tsiya ya ci ran Hajja, ko sallaman ma basu amsa ba, ta hau masa faɗa, ta inda take shiga ba ta nan take fita ba

Ganin abun yayi yawa, sai ya ce, "Hajja wai me tace miki ne da kike min irin wannan faɗan?"

"Uwar ka tace min, nace uwar ka tace min, wallahi tallahi Baffa ka fita ido na in rufe, idan ba haka ba zan mummunan saɓa maka a gidan nan, tunda kake baka taɓa gaya min magana ba, amma a kan wancan shegiyar yarinyan naga alamu kana so ka bijire min, to wlh kar in sake ganin ka raɓe ta, idan ba haka sai na.."

"Hayaniyar mene ne haka nake ji wai?" Cewar Abba da ya fito daga daƙi daga shi sai Singlet da dogon wando, da alamu dai barci yake yi Hajja ta tashe shi da hayaniyar ta

Daga Baffa har Sa'adatu duƙar da kansu suka yi, sun kasa cewa komi, sai Hajja ne da ta cika maƙil da fushi tana shirin magana

Ya katse ta da faɗin, "ya isa, ku tashi ku tafi gidan ku".

Tashi suka yi daga Baffan har Sa'adatu suka fice

Sannan ya juyo kan Hajjan yace, "wai ke Fatima me kike so ki zama ne? Me Baba na yayi miki da kike son hana sa kwanciyar hankali shi da matar sa? Duk abinda kike faɗa ina ji, wlh idan har baki fasa shiga sha'anin auren su ba, to watarana zaki ji kunya, kuma da kike son raba sa da ƴar uwan sa, kar in ji kar in gani, domin zan mummunan saɓa miki kema, wannan ai rashin hankali ne, tukuna ma me Uwata tayi miki ba kya ƙaunar ta?"

Shiru Hajja tayi don bata san me zata ce ba, shaf ta manta da yana ciki da tun farko bata ɗaga muryan ta yaji ta ba

Ƙwafa yayi kafin yace, "ki ci gaba kar ki fasa". Ya juya ya shige ɗaki

Sosai ran Hajja ya ƙara ɓaci, a ranta ta ɗau alƙawarin muddin tana numfashi sai ruwan sha ya gagari A'isha da ɗiyar ta.

⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

       Ranan Monday Ɗahira ta koma bakin aikin ta, saboda sosai jikin ta yayi sauƙi

Shima Baffa ranan ya koma, tunda sati biyu kenan da auren su

Nan hankalin Sa'adatu ya tashi matuƙa, domin gani take yi, Baffa ya koma bakin aiki ne duk sabida ya ga Ɗahira ta koma aikin ta, kuma tasan a can dole su riƙa haɗuwa, wannan abun duk ya dame ta, taje ta sanar wa Hajja

Hajja tace, "ta bar su, zata saka musu idanu, kuma zata yi wa Baffa gargaɗi sosai" domin ita kanta Hajja yanzu ba ta ƙaunar alaƙar Baffa da Ɗahira, hanya mafi sauƙi take son samu don raba su, sam ba ta ƙaunar su ci gaba da yanda suke kamar da, tunda yanzu a ganin ta yayi aure, hakan zai cuta wa Sa'adatu.

       Baiwar Allah Ɗahira, ko kaɗan ma bata san wainar da suke toya wa ba, babu ruwan ta, abinda ta saka a gaba shi take yi, a ranan ma da ta dawo aiki ta shirya zuwa gidan su Shakira, tunda ko sau ɗaya bata je ba, da biki bata da lafiya, kuma Aunty Amarya ne ma ta matsa mata taje ɗin, kar ace tana baƙin ciki ne mutanen gida su yi wani fassara daban, shiyasa yau da wuri ta tashi a aiki, zuwa ƙarfe ɗaya da rabi ta dawo

Wanka kawai tayi ta shirya cikin farin Less me ɗige-ɗigen baƙi, riga da skert aka yi mata, wanda yayi mata cif a jikin ta, ya kuma ƙara haska mata white skin ɗin ta, sai ta yafa baƙin gyale bayan tayi ɗaurin ɗan kwalin ta normal, sai dai fuskar nan ya sha make-up, sabida Ɗahira ba baya ba wajen son gayu, musamman na kwalliya, takalmi me tudu tayi amfani da shi fari, ta ɗau HangBag ɗin ta ta rataya ta fito

Umma ce kaɗai zaune a parlour'n

Tace mata, "Umma zan je gidan su Shakira ne".

Sai Umma ta wangale baki tace, "ahh to Masha Allah, yau kenan zaki leƙa su? To ki gaishe su".

Murmushi Ɗahira tayi tace, "insha Allah Umma za su ji". Tana gama faɗar haka ta shige ɗakin Maman ta

Taɓe baki Umma tayi tana kawar da kanta daga kallon bayan Ɗahiran, a ranta tace, "gulma ajali! ba ma asan me zaki je yi ba, Allah dai ya tsare min ɗiya ta ba a nan kusa take ba bare ace za'a je mata". Sai kuma ta miƙe ta nufi cikin gidan inda zata je kai wa Hajja rahoto.

     Ɗahira na shiga tace ma Aunty Amarya "ta shirya zata tafi".

Shi ne take tambayan ta "baza ta ci abinci bane?"

Tace mata "sai ta je can, zata ci a gidan su".

Daga haka Allah ya kiyaye hanya Aunty Amarya tayi mata, ta bata saƙon gaisuwa, sannan ta fito. Motar ta ta hau ta bar gidan.

            Gidan Yusra ta soma zuwa, tunda babu nisa da su, babu ƙarya gidan ta ya haɗu matuƙa, babba ne sosai tunda mijin ta yana da kuɗi sosai, Costume ne shi, ya taɓa aure kuma sun rabu da matar tuni, har ɗiya yana da ita, sai dai tana wajen Mahaifiyar sa ne

Horn tayi, me gadi ya leƙo, sai da ya zo wajen ta tayi masa bayanin kanta, kafin ya buɗe mata ta shiga ciki, tana yin parcking ta fito tayi cikin gidan

Tun daga haraban gidan komi ya burge Ɗahira, da ace ita baƙauyiya ce, ko ba su da shi a gidan su, da har zilalan yawu sai tayi lokacin da ta shiga parlour'n Yusra, sai dai kasancewar ta wayayyiya kuma masu shi, shiyasa sama-sama tayi ma komi kallo, a ranta kuma sosai komi ya bata sha'awa, tana ganin Yusra ta more da komi, domin tayi Sa'an muhalli.

        Fitowar wata babbar mace da kaya haɗin gambiza a jikin ta, ya tabbatar wa da Ɗahira ƴar aiki ce, a ranta tace, "su Yusra uwar son jiki! Har an soma ajiye ƴar aiki".

Matar iso wa wajen ta tayi, ta zuƙuna har ƙasa ta soma gaishe ta

Saurin yalwata fuskar ta da fara'a Ɗahira tayi, tace da ita, "don Allah Mama ki tashi, Ni Yakamata in gaishe ki ai ba ke ba".

Murmushi matar tayi tace, "ai babu damuwa ɗiyar albarka, idan na gaishe ki ma girman ki ne, don daga gani ke ƴar uwan matar gidan ce, kinga kuwa be kamata naƙi gaishe ki ba".

Itama Ɗahiran murmushi tayi tace, "amma ai kin girme Ni Mama, don Allah kar ki sake zuƙuna min kinji? Ki ɗauke Ni tamkar ɗiyar ki".

"To babu damuwa, insha Allahu. bari in Kira miki Hajiyan". Matar tafaɗa da fara'a, a ranta sosai taji ƙaunar Ɗahira sabida mutunta ta da tayi, har tana jin da ita ce Uwar gidan nata.

     Har tayi nisa kuma ta juyo ta tambayi Ɗahiran "wa zata ce mata ta zo?"

Ɗahira ta sanar mata da sunan ta

Ita kuma ta juya ta shiga ciki.

     Kamar shuɗewar mintuna biyar sai ga ta ta dawo, tace mata "ga ta nan zuwa"

"To Mama na gode". Ɗahira tafaɗa tana murmushi

Itama murmushin tayi tace, "babu damuwa ɗiyar albarka".

Daga nan juya wa tayi taje ta kawo mata Drinks kamar yanda ta saba tarban baƙi idan sun zo, sai dai na Ɗahira har da abinci ta sawo mata, tunda tana ganin ita ɗin ƴar uwanta ce, be kamata ta tarbe ta da Drinks kaɗai ba, kuma abincin na Mijin ne tayi masa cus-cus, tunda shi ya fi so kuma yace ayi masa. To ta ga bata rigada ta sauke sauran abincin ba, shiyasa ta ɗibo mata nashi.

      Matan tana barin wajen, sai ga Sulaiman ɗin ya fito, da fara'an sa ya zauna suka gaisa da Ɗahira, har yana tsokanar ta da "sai yau za su ga idon ta, gaba ɗaya ita tayi wuyan gani, dole sai an cike Form me tsada ake iya ganin ta, da biki ma ko ganin ta be yi ba"

Ɗahira na murmushi tace dashi, "Allah Sarki Yaya Sulaiman, wlh ciwo nayi shiyasa kwata-kwata ban fita waje ba, kayi haƙuri".

"Eyya Sorry! But ban ji labari ba ko kaɗan wlh, domin dai Yusra bata sanar min ba, ai da mun shiga mun gaishe ki, Allah ya ƙara lafiya, yasa kaffaran zunubai ne".

"Amin Amin Yaya Sulaiman, na gode sosai".

Murmushi yayi yace, "ki dena godiya Auntyn mu, mun rigada mun zama ɗaya Yanzu".

Murmushi kaɗai tayi ita dai

Yace, "sai fa kin yi haƙuri da wannan ƙanwar taki, tana shirya wa ne amma yanzu zata fito".

"A'a babu komi wlh".

"To bari in ɗan fita waje, zan haɗu da Maƙoci na ne, idan ta fito ki ce mata yanzu zan dawo".

Amsa mishi tayi cikin murmushin da ya zame mata jiki

Shi kuma ya tashi ya fice a Parlour'n

Ajiyan zuciya Ɗahira ta sauke, tana ɗauke kai daga hanyar da yabi, sai kuma ta kalli Centre table ɗin da me aiki ta shirya mata abinci da drinks, hannu ta sanya ta ɗauki Robbern fanta, ta buɗe ta tsiyaya a glass cup ta soma sha. Abu kamar wasa har tsawon mintuna 15 suka shuɗe babu Yusra babu dalilin ta, don haka ta zuba cus-cus ɗin ta soma ci, kasancewar sosai take jin yunwa

Tana cikin ci ne, sai Yusra ta fito cikin takun ta ɗai-ɗai tana faman taunan cwhingum

Da kallo Ɗahira tabi ta dashi tana mamakin ganin ta da Shimi da dogon wando, babu alamun dai shirya wa ne ya tsayar da ita, koda yake da ta tuna ba shiri suke yi ba, tasan komi zata iya mata, don haka ta tsayar da cin abincin da take yi tana kallon ta fuskar ta cike da fara'a, ganin yanda tayi mugun sauya mata, tamkar dai ba satin su biyu ne da aure ba, tabbas aure ni'ima ce, Allah yasa mu dace.

      Yusra dai tunda ta ƙariso wajen taga abincin da Ɗahira ke ci, sai ta sake ɗaure fuskar ta tamau fiye da yanda ta ɗaure, tana faman fiffizge kai tana taunan cwhengum ɗin ta har da su ƙas-ƙas-ƙas

Ɗahira ita ta soma mata magana, tare da gaishe ta cikin fara'a

Sai da ta zauna ta gama yamutsa fuskar ta kafin tace, "Lafiya. Dama ke ce?"

Murmushi Ɗahira tayi tace, "eh".

"Yayi to". Tafaɗa tana sake taɓe baki

Shiru ne ya biyo bayan maganar ta, don ita kanta Ɗahira bata san me zata ce ba, domin kawai yanda ta amshe ta ɗin, sai jikin ta duk yayi sanyi, tamkar ma ta ƙaro wulaƙanci ne, ga shi sai mata kallon banza take yi kamar dai ta ga kashi..

Numfashi taja sabida maganar Yusran da ya dawo da ita hayyacin ta

"Wai Husband ne yasa a kawo miki abincin nan?"

Shiru Ɗahira tayi tana kallon ta, don bata san me zata ce mata ba, tunda bata gane ma manufar ta ba

Guntun tsaki Yusran taja tana ɗaga murya ta soma kiran matar nan, "Marka.. Marka".

"Na'am yallaɓiya, gani". Cewar matar da ta fito da gudun ta

"Wa ya baki damar zuba mata abincin Husband?"

Shiru matar tayi tana zazzare ido, ta kalli Ɗahira ta kalli Yusran

Sai da ta daka mata tsawa da faɗin, "ba dake nake yi ba?"

"Kiyi haƙuri Ranki ya daɗe! Gani nayi ƴar uwan ki ce, shiyasa na zuba mata tunda yanzu na ɗaura sanwa, kuma zata..."

"Dalla rufe min baki". Ta katse ta da faɗar haka

Jiki a sanyaye matar tayi shiru tana sad da kanta ƙasa, zuciyar ta cike fal da mamakin uwar ɗakin nata

"Wlh duk sanda kika sake ɗaukar abincin Miji na kika ba ma wata, a mean ba ita ba ko waye ma, wlh ranki sai ya ɓaci! baza ki sake zamar min a gida ba, ba na haɗa Miji na da ko wani tarkace kina ji ko?" Tayi maganar cikin isa da gadara

"Eh naji ranki ya daɗe! amma wai da naga ita ɗin..."

"Shut up I say".

Gum Matar tayi jikin ta na rawa, sabida sosai tsawar ta ya shige ta

"Ki kwashe ki mayar min dashi kichen, idan kin girka wancan sai ki zubo mata".

"To". Matar ta amsa da sauri tana nufan Centre table ɗin, ta ɗauki Plate ɗin kacokan ta wuce kichen, zuciyar ta gaba ɗaya babu daɗi, sosai taji tausayin Ɗahira har tana sake waigo wa ta kalle ta da zata shiga kichen ɗin

Ɗahira na zaune dai tana kallon ikon Allah, har a ranta sosai da sosai abinda Yusra tayi mata ya bata mamaki da tsoro, "shin wani irin tsana ce take mata da har zata yi mummunan wulaƙanta ta haka? Tana a matsayin ƴar uwan ta?". Sosai ta danne ɓacin ranta da komi, cikin juriya ta ƙirƙiro murmushi kafin tace, "Allah ya huci zuciyar ki! wlh nima bansan abincin Mijin ki bane, da ban ci ba". Sai ta miƙe kafin taci gaba da faɗin, "Ni zan tafi, su Umma da Mama suna gaishe ki". Ta ƙare maganar da yin gaba ta nufi ƙofar fita

Taɓe baki Yusra tayi tana faman kaɗa ƙafa, a fili ta furta, "dama ba gayyar ki nake yi ba".

     Ɗahira na fita ta saka hannu ta share hawayen da suka zubo mata a fuska, ta saki wani irin numfashi tana jan majina, lumshe idanu tayi tana haɗiyar wani abu da ya tsaya mata a maƙoshi

"Lafiya Ɗahira? Why are you crying?" Cewar Sulaiman dake tsaye gaban ta ba tare da ta san da zuwan shi ba.
[10/09, 8:51 pm] OumƊahira نفيسة: 💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTOR'S*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA'IL LAWAL_



*بسم الله الرحمن الرحيم*





*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA'S FAMILY*_

               *HADHISI*
_An karbo dga Aisha Allah ya ƙara yarda agareta tace " Manzon Allah s.a.w ya aureta tana da shekara shidda,kuma yatare da ita tana da shekara Tara,kuma Allah ya karbi ransa tana er shekara sha takwas. Muslim ya ruwaito_

.

       *EPISODE Thirty Two*

         Ɗago kanta tayi tana kallon sa, sai tayi saurin ƙirƙirar murmushi tace, "No, I'm not crying, abu ne ya faɗa min a ido shiyasa".

Duk da be yarda ba, sai yace, "Eyya sorry! Amma dai ba tafiya zaki yi ba?"

"I'm going Yaya Sulaiman, har da gidan Shakira zan je, and Mama says" I'll be back soon ".

"To babu damuwa, ki gaida mutanen gidan don Allah".

"Insha Allah, they will".

Hannu yasa cikin aljihu ya fito da kuɗi yana faɗin, "amma shi ne Yusran bata zo ta taka miki ba?"

Bata ce mishi komi ba, tunda bata san me zata ce mishi ba

Sai ya miƙa mata kuɗin har 20k Yana faɗin, "ga shi babu yawa kiyi haƙuri".

Girgiza kanta tayi tace, "a'a wlh bazan amsa ba, ka bar shi Yaya Sulaiman". Tana faɗan hakan ta wuce sa ta bar wurin

Da kallo ya bi ta da shi har ta kai wajen motan ta, kafin yaja numfashi yana mayar da kuɗin cikin aljihun sa, ƙofan ya buɗe ya shiga ciki da sallama

Yusra dake zaune har yanzu a inda take, tana faman karkaɗa ƙafafu tana latsa waya, ɗago wa tayi tana amsa sallaman nasa idanun ta a kansa

Shi kuwa a kan Centre table ɗin ya sauke idanun sa, zuciyar sa sosai take ɗarsa masa tabbas Yusra ce tayi wa Ɗahira wani abun, domin ya san cewa Yusra ba ta shiri da ita, tunda sau nawa take faɗar magana a kanta, kuma sannan ba ta son ko kaɗan yayi maganar ta a waje, idan yayi kuma ta dinga kushe ta kenan

Kallon ta yayi yace, "meyasaka Ɗahira ta tafi tun yanzu?"

Taɓe baki tayi tace, "can ta matse mata nima ban sani ba".

Waro ido yayi kanta yana sake gasgata abinda ke ransa, sai kuma ya juya yana kwaɗa wa me aikin nasu kira. Tana fitowa ya tambaye ta "ina abincin nan da na ga Ɗahira tana ci? Yanzun nan daga fitan ta har kin kawar da Plate ɗin?"

Jiki na rawa matar tace, "wlh ranka ya daɗe! Uwar ɗaki na ce ta sanya Ni na ɗauka na mayar tunda abincin ka ne".

"Kina nufin tana zaune a nan ta saka ki kika ɗauke?"

Jiki a sanyaye ta duƙar da kanta ƙasa saboda uwar hararan da Yusra ta banka mata, ta amsa mishi da "eh. Amma a gafarce Ni yallaɓoi, ba laifi na ba.."

"Je ki abun ki Baaba".

Da sauri ta wuce ta koma kichen

Sai ya mayar da idanun sa kan Yusra dake ci gaba da karkaɗa ƙafafun ta, tamkar ma bata damu da abinda yake tambaya a kai ba, yace da ita, "Yusra wai Ni shin in tambaye ki? Ɗahira ba ƴar uwan ki bace?"

Ɗago kai tayi tana kallon sa, sai ta turo baki ta soma magana

Ya katse ta da faɗin, "amsa nake so".

"Ƴar uwata ce mana".

"Ok ƴar uwan taki ce ta zo gidan nan, kika wulaƙanta ta ko? Shin kin san kuwa abinda kike yi? Da kuka fa ta bar gidan nan".

Shiru tayi masa

Cike da ɓacin rai yace, "yayi miki kyau! ki ci gaba da abinda kike yi, Ni babu abinda ya shafe Ni, amma ki sani ranan da zaki yi nadama na nan zuwa". Yana gama faɗar maganan nasa yayi cikin ɗaki da sauri

Tsaki taja kafin ta miƙe tabi bayan sa.

⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

           Murza sitiyarin ɗin motan take yi zuciyarta na ƙuna, sosai take jin ƙunci da abinda Yusra tayi mata, numfashi kawai take sauke wa duk socond baƙin ciki na ƙara wanzuwa a zuciyar ta, nan da nan kanta ya soma mata ciwo sabida damuwa da tuno abinda tayi mata ya haifar mata, sosai take dana-sanin rashin amayar mata da ƙuncin da ta saka mata, sabida ta san ita zai cuta, amma kuma ta ga ita ta kawo kanta shiyasa be kamata ta biye mata har wani saɓani ya shiga tsakanin su ba, but she promised she would never see her again in her home.

Ta so koma wa gida, sai kuma ta ga be dace taƙi zuwa gidan Shakira ba, can ta wuce duk da bata san gidan ba, sabida kwatancen akwai wahala sosai in dai ba ka taɓa zuwa bane, dole ta kira Baffa ya sake mata kwatancen gidan kafin ta gane

Itama gidan nata babu laifi tunda ita kaɗai ce, amma kuma na Yusra yafi girma da haɗuwa, mijin ta Sahabi aiki yake yi a Companin wutar lantarki.

       Sanda ta shiga gidan da sallama, Shakira na zaune a Parlour tana cin abinci tana kallo, ganin ta yasa ta tashi da fara'an ta ta rungume ta

Murmushi Ɗahira tayi, cikin sanyin murya tace, "ƴar uwa nayi missing ɗin ki sosai da sosai".

Dariya Shakira tayi tace, "ai wlh baki kai Ni ba sister, tun sanda Hajja ta kira Ni tace kina nan zuwa na zauna a nan zaman jiran ki, meyasa ma kika fara zuwa wajen wancan mara mutuncin? Tunda kin san ba shiri kuke yi ba, Allah yasa dai ta amshe ki hannu bibbiyu bata miki wulaƙacin da ta saba ba, ba Ni nasha don Allah ya kuka kwashe?". Ta ƙare maganar har da gyara zaman ta tana zuba wa Ɗahira idanu

Shiru Ɗahira tayi, nan maganar da Fadila ta faɗa mata ya faɗo mata, hakan yasa ta saki murmushin yaƙe tace, "ke dai Shakira, daga zuwa baza ki bari na huta ba sai ki soma min gulman wata?".

Hannun ta ta watsa saman cinyoyin ta tana faɗin, "ai wlh ke dai bari Sister, na damu dake ne wlh, domin nasan halin Yusra yanda ta tsane ki, ruwan gidan ta ma baza

Please Login or Register in order to submit comment