Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

can I tell you? Shakira, kin san Buri na shi ne In ga ranan da za'a ce mun fi kowa a wannan familyn, I want to see the future of the  *AL'AMEEN FAMILY HOSPITAL* back under us. wannan dalilin ne yasaka na saka wa Baffa sunan Kakan ku, kuma dalilin ne yasaka na matsa wa Abban ku yabar Ni na koma makaranta na zama Likita, I know that one day my dream will come true. "

Shakira looked at her mother and said, "Hajja, how do you think this hospital will be ours alone? Kar ki manta fa Familyn mu babba ne kuma kowa yana da gado idan har Kaka akace ya mutu, sannan taya kike tunanin sunan Ya Baffa zai taimaka mana don samun Asibitin nan?"

Hajja Fatu smiled and said, "Hmm, I know what I am thinking. Please keep your eyes peeled. Insha'Allah sai mahaifin ku ya gaji asibitin nan, sai mun fi kowa fice a cikin asibitin nan, sannan sunan Baffa da na saka don ina so ne nan gaba koda bayan ran Kaka ya zamana shi ke juya Hospital ɗin, ma'ana kowa yayi tunanin sunan ɗana ne sannan a manta da kakan ku, Ni a ganina hakan zai yi sauƙin zama namu".

Shiru Shakira tayi tana kallon ta sai kuma ta kwashe da dariya

Hajja Fatu dake faman kallon ta baki hangame tace, "Ke ban son iskanci! Why are you laughing like that?"

Wlh Hajja you laughed at me, wai taya ma kike tunanin Jika zai mallaki Hospital ɗin Kaka idan har don kin saka sunan sa? Bayan kin san da cewa ABBU ma sunan Kakan yaci, to ki faɗa min da ɗa da jika wanne mutane za su yi tunanin Hospital nashi ne?"

"Hmm ai fata nake yi sannan cewa nayi ina so kowa ya ɗauka cewa Al'ameen ɗina ne aka saka, kin ga Ni da Abban ku da ke da Baffa duk muna aiki a cikin asibitin, don haka nake so nan gaba asibitin ya zamto na mu, ke dai kawai ki mayar da hankalin ki da zaran akace kun soma aiki, duk abinda baki fahimta ba kizo waje na ki sanar dani kinji?"

Gyaɗa kanta Shakira tayi tana kallon uwar nata

"Now call me Baffa and we will talk to him."

"Ok".

Tashi Shakira tayi ta nufi corridor'n da zai sada ta da ɗakin Yayan nata.

        *****
      The next morning gidan Doctor Al'ameen sosai ya cika da mutane ƴan uwa, Hajiya Ikram da Hajiya LAILA har sun iso da iyalan su, haka ma su Aunty Zainab da Aunty Zulaiha, nan da nan gidan ya rincaɓe da hayaniya sai shirye-shiryen abubuwan da za'a yi suke yi.

........ ....... ....... ....... ....

   Baƙar Mota ce ta sanyo kai cikin ƙaton gidan da ya tsaru iya tsaruwa, kai da gani kasan mamallakin gidan ba ƙaramin hamshaƙin me kuɗi bane, sosai gidan yake da girma da yalwa Two upstairs ne, idan ka shiga haraban gidan yana da yalwa sosai wanda aƙalla zai cinye motoci kusan ashirin, sai kuma Part ɗin masu aiki da akayi daban, da akwai Garden a ta bayan gidan tare da abubuwan more rayuwa, the home of Doctor Al'ameen and his family.

Motar na packing wata mata da a ƙalla baza ta wuce 45years ba ta fito, sai kuma wata matashiyar budurwa da shekarun ta ba zai fi 25years ba itama ta fito, tana sanye ne da wani Abaya green colour Wanda a gefe da gefen rigan an sanya ratsin blue, sai kwalliyan Flower da akayi da stone masu matuƙar ƙyalƙyali daga sama har ƙasa, tayi Rolling kanta da ɗankwalin Abayan da ya kasance Blue, sai ta saka wani ɗan siririn farin glass Wanda ya ƙara fito da zallan kyawun ta da kwarjinin ta; tare da fito da manyan idanuwan ta da ƙwayan idanun suka kasance sky Green, kallo ɗaya idan kayi mata zaka san da cewa ba ƙaramar mugun haɗuwa tayi ba, fara ce sosai tana da kyawun fuska tare da ƙira me kyau, sai dai ta kasance siririya ce sosai kuma matsakaiciya, kana kallon ta kasan cewa za tayi yanga ne da yawa, don ko maganar ta da tafiyan ta idan tayi zaka san cewa Nature ɗinta ne hakan

Matar kallon drever'n da ya fito cikin motan tayi tace, "Ali where are you doing now?"

"I will go to the hospital because Alhaji said, 'If I drop you off, he will sent me.'"Ali said respectfully.

Gyaɗa kanta tayi kana tace, "ok go, idan ka dawo I'll sent you later".

"To Hajiya".

Daga haka juyawa tayi ta nufi cikin gidan, Matashiyar yarinyan itama tabi bayan ta. koda suka shiga ciki Direct Part ɗin su suka nufa, lokacin da suka shiga cikin ɗan madaidaicin parlour'n su da sallama a bakin su

Fadila ce zaune tana kallo ta'amsa musu

"Welcome Aunty"  Fadilan saying

"Yauwa Fadila, ke kaɗai ce zaune?" Aunty Amarya tace hakan cike da fara'a tana kallon ta

Fadila ta bata amsa da "Eh su Umma na General parlour".

"Ok mu ma ai bamu shiga cikin gidan ba nan muka taho, bari in shiga ɗaki in yaso sai in shiga can mu gaisa".

"Toh aunty".

Wuce wa ɗakin ta Aunty Amarya tayi

ita dama tuni Ɗahira ta wuce tasu ɗakin wanda ya kasance tasu tare da Fadila, tana shiga ta'ajiye Jakan dake hannun ta ta zauna gefen gadon ta, zare ɗankwalin da tayi Rolling a kanta tayi ta'ajiye tana bin gadon ta kwanta, kanta na kallon sama yayin da ta ƙure Cilling ɗin ɗakin da kallo, ta ɗan jima ahaka kafin ta sauke ajiyan zuciya tana lumshe kyawawan idanuwan ta, sai kuma ta buɗe ta tashi zaune tana zare Glass ɗin idanun ta ta miƙe ta nufi gaban Looking glass ta buɗe Locker ta'adana, darect Sif ɗin kayan ta tanufa ta ciro wasu riga da wando na Pakistan Milk and Red colour ta zube su saman gado, kayan jikin ta ta soma cire wa kafin ta ɗaura towel ajikin ta tashige toilet, wanka tayi ta ɗauro alwala ta fito, sai da ta shafa Lotions ajikin ta kafin ta saka kayan ta ɗaura Hijab tayi sallan asar da ta wuce su tun a hanya, bayan ta gama ne ta nufi wajen Looking glass ta zauna tana kallon kanta a madubi, tagumi ta zuba still tana ci gaba da kallon kanta

Fadila ce ta shigo ɗakin idanunta ya sauka akanta, sai ta taɓe baki tana ƙarisawa wajen ta tace, "Are you all right?"

Sai a lokacin Ɗahira ta ɗago kanta tana kallon ta, sai kuma takau da kan tare da faɗin "me kika gani?"

Fadila batace komi ba ta juya ta tafi, dama wayan ta tazo ɗauka, tana ɗauka ta fice a ɗakin, wannan shi ne halin su su duk ka biyun basu cika kula juna ba duk da duk kan su suna da ƙyaliya, But kasancewar Iyayen su suna kishi shiyasaka su ma suke taya su a junan su, ga dai shi ɗaki ɗaya suke kwana amma sai su wuni su hantse ba wacce zata kula ƴar uwanta, ba me shiga harkar ɗaya sai sun ga dama, ita dama Ɗahira ƴar ba ruwanta ne, bata cika shiga shirgin da ba nata ba, bata da son hayaniya amma tana da fara'a da kirki, komi tana yin abinta ne cikin class, sai dai alokaci ɗaya baza ka taɓa fahimtar halin ta ba sai ka zauna da ita, Fadila ma haka sai dai wani lokacin tana da yawan wulaƙanci a ɗabi'a, domin miskilancin ta yayi yawa don in bata ga dama ba ko kai uban waye baza ta kula ka ba sai taga dama.

Ɗahira cire tagumin tayi ta soma shafe Baby face ɗin ta da kayan makeup, ita gwanar son gayu ne duk sanda zaka ganta bata rabo da kwalliya, Light makeup tayi wanda ya ɗau fuskarta sosai ya ƙara fito da zallan kyawunta, ba maganar wasa ba Ɗahira tana ɗaya daga cikin kyawawan gidan, duk a cikin ƴan matan gidan zan iya cewa tafi su kyau duk da suna matuƙar kama, sai dai ita yanayinta da komi nata ya banbanta da nasu

Buɗe Lockern tayi ta ciro Glass ɗin ta tasanya Wanda ya zame mata ɗabi'a ko yaushe idan zaka ganta tana tare dashi, sai ta miƙe ta nufi gaban gadon ta taɗau wayan ta ƙirar IPhone 11+, takalmin ta kawai ta sanya ta fito batare da ta yafa komi ajikin ta ba baya ga ɗankwali da ta sanya ta rufe tulin gashinta, tana fitowa parlor ta hangi Fadila zaune har yanzu, sai dai wannan lokacin wayan ta take dubawa, ɗakin Mahaifiyar ta tawuce, tana shiga babu kowa hakan yasa ta fito ta doshi cikin gidan, sai da ta wuce wani dogon corridor kafin ta buɗe wani ƙofa ta shige, ahankali ta soma taka Step tana sauko wa sai gata cikin wani kyakkyawan parlour ƙarami, sai tabi ta wani ƙofan ta fito babban parlor'n gidan da ya kasance cike da mutane kowa sai harkan gaban sa yake yi, tana isa ta gaishe dasu sannan ta wuce wajen ƴan matan dake can gefe zaune, zama tayi gefen Shakira da Salma (ƴa ga Hajiya LAILA),

Shakira CE ta soma cewa, "Now I ask Aunty Amarya where are you? She told me kina Sashin ku ai".

Ɗahira She smiled and said,  "na tsaya wanka ne".

Fiddausi da ta kasance ƙanwar Salma tace, "to ya Naga hannayen  ki rabbana suna dukan cinya, ina tsaraban tamu?".

Kallon ta Ɗahira tayi tace, "What are you eating na baka na zuba? Let me rest for a while, sai ki zo ki taya ni kwance jakan".

Gaba ɗaya wajen su kayi dariya ban da Yusra dake faman latsa wayan ta ko ɗago kai bata yi ba

Shakira tace, "kin ji ƙyale wannan yarinyan bata da hankali, ke da akaje Duba marar lafiya kike zancen tsaraba?"

Ɗage gira Fiddausi tayi tace, "to kuma akace idan anje baza'a yi tsaraba ba? Nasan da cewa waɗannan tsofaffin baza su barta haka ba sai sun haɗo ta da abin lasawa".

Shamsiyya (ƴa ga Hajiya Ikram) tace, "ƙwarai kuwa Fido sai dai idan mu baza'a bamu ba, don naga tunda ta shigo Shakira take ƙifƙifta mata idanu".

Salati Shakira ta saki tana rufe bakin ta tare da zaro idanu, sai suka saki dariya suna shewa, wasu suce "eh su ma sun gani" wasu kuma suce "kai Shamsiyya banda ƙarya".

Dogon tsaki Yusra taja ta miƙe ta wuce abin ta, yayinda duk kan su suka bi ta da idanu kana Salma tace, "Oh, that juju girl, what's wrong with her?"

Dawo da idanun ta Ɗahira tayi gare su tana murmusawa tace, "Ni kun ga tafiya na bari inje in miƙa gaisuwata ga Kaka tunda naga ban ganshi anan ba".

Tafa hannu Fiddausi tayi tace, "ai Kaka yau sai dai yayi haƙuri mun hana sa fitowa, cewa yayi bazai iya da surutun mu ba ya shige ciki ya kwanta".

Tashi Ɗahira tayi tana faɗin "ai gwara haka kar ku ƙara masa damuwa".

Daga haka ta wuce batare da ta kula su da sukayi mata caaa ba.
[29/08, 1:29 pm] OumƊahira نفيسة: 💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*DOCTOR'S FAMILY*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱


*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA'IL LAWAL_




*بسم الله الرحمن الرحيم*



*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuDahirah*👈

*\F.W.A📚/*

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA'S FAMILY*_

*NATSUWA A SALLAH*
_Manzon Allah mai tsira da aminci, ya ce, "sallah ba kome ba ce illa miƙa wuya da tawali'u..." Kuma ya ƙara da cewa, "Bawa bai samun ladan sallar sa sai gwargwadon abinda ya hankalta daga sallar." Watau, gwargwadon natsuwar mutum cikin sallah gwargwadon darajar da yake samu gun Allah. Don haka ne ma ma'aikin Allah ya ce, "Allah ba ya juya wa Bawa baya yana cikin sallah matuƙar bai waiwaya ba; idan ya waiwaya kuwa, sai Allah ya bijire masa."_
_Babu abin da yake kawo waiwayo cikin sallah kuwa sai gafalar Bawa da muƙamin Ubangijin sa, watau ya zama tamkar wanda ya tsaya yana ganawa da Ubangijin sa alhali zuciyar sa tana shagale da wani abin dabam. A kan wannan matsala ne Allah yake ce wa Manzon sa, da al'ummar sa ma, a cikin suratul A'ARAF aya ta 205:_
_"Kada ka kasance daga gafalallu."_
_In muka lura sai mu ga cewa ta ya ya kuwa gafalalle zai iya tunawa da muƙamin Ubangijin sa yana cikin wannan hali na rashin kula har wani abin tsoro ya auku? Bugu da ƙari, daman can ga shi Allah ya yi umarni a cikin suratul Ɗ.H., aya ta 14 da cewa:_
_"Kuma ka tsayar da Sallah domin tuna Ni"._
_In mutum ya Yi haka, ana fata ya rabban ta._
   _Allah yasa mu dace._

.

*EPISODE four*

    Babban haraban asibitin cike yake da mutane bila adadin, mutane ne kamar tsaki kama daga yara manya masu kuɗi da manyan likitoci duk an gayyace su, har ta da gwamna Malam Nasiru El Rufa'i sai da aka gayyace shi wajen, komi ana yinsa ne akan tsari gunun sha'awa

Ɗahira, Shakira, Yusra da Fadila can na hango su wajen zaman su daban, sosai su kayi kyau cikin shigan su na material fari ƙal da akayi masa ɗige-ɗigen Coffee colour, ɗinkin doguwan riga akayi musu fitted, sai suka yane kan su da Goldeen Veil tare da sanya Hill shoes shima Golden, sosai su kayi matuƙar kyau kamar ka sace su ka gudu sai faman haskawa suke yi kamar taurari

Nan akayi ta gabatar da komi cikin girma da arziƙi, daga ƙarshe aka gabatar dasu a matsiyin waɗanda ake taya murna tare da sauran sabbin ma'aikata da za'a ɗiba.

      Wata kyakykyawar Farar mota ce ta shigo haraban asibitin, a hankali motar take tafiya har zuwa inda sauran motocin suke fake, tsawon mintuna 5 kafin aka buɗe motan ya zuro kyawawan ƙafafun sa kana ya fito a hankali yana rufe motan, kyakykyawar saurayi ne da aƙalla bazai wuce 32yrs ba, fari ne tarrr kamar kalatsa shi jini ya fito don har wani ɗaukan idanu yake yi, yana sanye da Milk ɗin riga me gajeren hannu da ya matse sa sosai, sai Blue Jeans tare da sanya Combat a ƙafafun sa shima blue, yana da yalwan gashin kai kwantacce baƙi siɗik tare da ɗan siririn sajen sa, Kallo ɗaya idan kayi wa Guy ɗin zaka tabbatar da ya haɗu ne tako ina, *USMAN NOOR AL'AMEEN* kenan, *(The Younger Doctor)* yaro kyakykyawa me Izza da Son nuna shi wani ne, ma'aboci Son gayu da son hutu

A hankali ya taka ya soma tafiya cike da taƙama ya nufi inda su Big Dady suke.

Har aka gama taron sannan kowa ya soma tafiya gida, sai yamma duk yawancin ƴan uwa suka soma watsewa sai gidan ya rage daga ƴaƴan Kaka sai jikokin shi suka rage waɗanda basu tafi ba, su ma ɗin a gobe duk za su watse su tafi

Washe gari ƙarfe 05:00pm. Na Yamma gaba ɗaya a halin gidan sun hallara a babban parlour bisa umarnin Kaka

Ɗahira ce tafito daga Part ɗin su don ita bata riga ta tafi ba, tana sanye da doguwar rigan atamfa kalan ja da ratsin Milk da ruwan ƙwai, rigan iyakan ta ƙwaurin ƙafafuwan ta kuma sosai tayi mata kyau ta sake fito da tsantsan kyawunta da kwarjinin ta, sai tayi Rolling da ɗan ƙaramin Veil da iyakan sa kafaɗun ta, Slippers ne a ƙafanta tana tafiya tana latsa waya, hira take yi da freinds ɗinta na Facebook sai faman doka murmushi take yi, gab da ta iso ƙofan da zata sada ta da General parlour taji tayi karo da mutum wanda hakan yasaka wayan ta ya zame ya faɗi ƙasa, a hankali ta ɗago kanta tana kallon sa

haka zalika shima ɗin dai-dai da sanda ya sauke nashi idanun cikin ƙwayan idanuwanta da yafi tsana cikin rayuwan sa

kallon sa kawai take yi babu ko ƙyafta idon

While shi kuma ya ɗaure fuska tamau yaja jikin sa ya wuce, gab da zai buɗe ƙofa ya tsinkayi zazzaƙan muryan ta tana cewa

"Ba ka ganin kayar min da waya ne?"

Cak ya tsaya yana juyowa ya kalle ta da tsananin mamaki da ya nuna a face ɗin sa, ita kuwa a lokacin kallon wayan nata da ya fashe take yi cike da tsananin baƙin ciki sannan ta ɗago kyawawan idanun ta tana kallon sa itama fuskarta a ɗaure

A hankali ya tako ya'iso gaban ta still yana ci gaba da kallon ta, duk da ya daɗe be ganta ba kuma tayi masa girma ainun but be yi tunanin cewa ta kai matsayin da har za tayi masa irin wannan maganar ba, shiru yayi yana ƙare mata kallo yayinda itama ɗin shi take kallo batare da ko alaman tsoro ya nuna a fuskarta ba, abinda ya ƙara ba shi matuƙar mamaki kenan, domin yasan ada babu wanda tafi tsoro sama dashi, idan har zata gan shi ko za taji sunan sa tsoro ne da fargaba suke kawo mata cafka, ko kaɗan bata haɗa hanya dashi bare magana ya haɗa su, duk inda akwai shi to ta haramta wa kanta wurin har sanda zai bar wajen

Kuma hakan ya samo asali ne tun sanda ta tashi da wayon ta take matuƙar tsoron sa, ba don komi ba sai tsananin azaban da yake gana mata da tsanar da yake nuna mata afili ko a ɓoye, shi kuwa tun sanda aka haife ta ya haɗa idanu da ita shikenan yaji ya matuƙar tsanar ta, ba don komi ba sai don ƙwayar idanun ta da ya kalla, sabida idan har zai kalle ta sai yaji faɗuwar gaba me tsanani tare da tsoro wanda hakan ne ya saka mishi muguwan tsanar ta cikin ran sa, sosai cikin ƙwayar idanun ta da suka kasance sky green suke bashi tsoro da fargaba, hakan yasa tun tana ƙarama ko ɗaukan ta ba ya yi, da zaran ya ganta duka ne abinda ke haɗa shi da ita, har zuwa kuwa girman ta da ta gane shi ɗin mugu ne, koda laifi sukayi ƴan gidan gaba ɗaya, to ita yake kamawa ya fanshe kaf dukan da zai yi musu akan ta, ko agaban waye babu wanda zai iya hana sa, kuma koda an hana sa sai ya san yanda yayi ya haɗu da ita ya gana mata azaba, Ɗahira ta tashi cikin tsoron sa matuƙa wanda ya haddasa mata tsanar sa fiye da wanda yake mata, kwata-kwata bata ƙaunar sa bata ƙaunar ganin sa koda jin sunan sa ne, ta saka wa kanta shi ɗin maƙiyin ta ne wanda babu wadda tafi tsana a duniya sama dashi

Wajen shekara 9-10years kenan babu shi a ƙasan, yana can ƙasar Turkey yana aiki acan, tun sanda ya tafi karatu ya zauna can sai dai yazo gaishe su, Ɗahira ta dena jin tsoron sa ne don kawai daɗewan da tayi ba ta ganin shi, and sai kuma girma da yazo mata, yanzu baza ta taɓa juran abinda yayi mata a baya ba, domin ita tana ganin ta wuce matsayin da zata zauna wani banza wanda ba iyayen ta ba ya duke ta bare har taji tsoron sa.

      Sauke kansa yayi kan wayan yana kallo, sai kuma ya mayar da idanun sa kanta yana sake ɗaure fuska ya ɗaga ƙafan sa ɗaya ya ɗaura saman wayan ya soma murje ta da ƙaton takalmin sa da ya kasance tamkar irin na sojoji, babu abinda ake ji sai sautin ƙaran fashewan wayan

Ita kuwa Ɗahira sauke idanun ta kan ƙafan sa tayi tana kallon wayan yayinda taji hawaye sun ciko mata idanu sabida tsananin baƙin ciki da yazo mata iya wuya, still ɗago kanta tayi tana kallon sa cike da zallan tsana da ya nuna a cikin ƙwayan idanun nata

shi kuma hawayen da ya gani a idanun nata shi ya saka shi jin wani farin ciki tare da sanyi a ransa, magana ce a bakin sa yake son faɗa mata amma girman kai da Izza sun hana sa buɗe bakin, illa juyawa da yayi ya nufi ƙofa ya buɗe ya shige

Ƙaran rufe ƙofan ne ya saka ta ƙyafta idanun ta wanda hakan ne yasa hawayen ta daman zubowa suka sauka kan kuncin ta, ahankali ta sake mayar da idanun ta kan wayanta da ya gama murƙushe ta duk screan ɗin ya farfashe babu kyan gani, wasu zafafan hawayen ne suka soma sintiri a face ɗin ta, tayi saurin saka hannu ta soma sharewa domin baza ta bama kanta daman nuna raunin ta kan shi ba, dole ne ta nuna masa yanzu ba irin da bane, dole ta nuna masa ba ta tsoron sa, kuma duk abinda yayi mata BASHI ne ya ɗauka dole sai ya biya, don haka ɗaukan wayan tayi ta nufi ciki itama da sauri.

_To fa nan ake yinta, bari muga me zai faru?_

_kar ku manta ku suburbuɗo min Comments ta hakan ne zai bani daman ƙara muku yawan Page._

Plz
*Share and Vote.*
[29/08, 1:29 pm] OumƊahira نفيسة: 💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
             *DOCTOR'S FAMILY*
                         🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
  *NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱


*MALLAKAR:*
                 _NAFISAT ISMA'IL LAWAL_




*بسم الله الرحمن الرحيم*


*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuDahirah*👈

         *\F.W.A📚/*

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA'S FAMILY*_

.

        *EPISODE Five*

Da shigan ta darect wajen Kaka ta nufa, ta sami waje kan hannun kujeran dake kusa da Wheel chair ɗin sa ta zauna tana sauke kai ƙasa

"Matata lafiya wa ya taɓa min ke?"

Abinda ya saka yayi mata tambayar ya santa idan har tazo wuri dole sai ta tsokane shi, ƙa'ida ne sai taja masa gemu kafin ta nemi wurin zama

Ɗago kanta tayi tana kallon sa sai kuma ta soma wurwurga idanun ta tana kallon mutanen wurin da duk suka nutsu suna kallon ta, a kan Usman dake zaune kusa da Abbun ta ta sauke idanu, yayin da shi kuwa wayan sa yake latsawa ko sanin Allah yayi ruwanta be yi ba

"Tell me my wife. I can't calm down idan ban san abin da ke damun ki ba?"

Dawo da idanun ta kan Kaka tayi cike da marairaice fuska tace, "Kaka Ya Usman ne ya fasa min waya, kuma ya saka ƙafa ya tattaka shi da gangar".

Kaka salati yayi yana kallon wayan dake hannun ta kana ya mayar da idanun sa kan Usman da har yanzu yaƙi ya ɗago kansa duk da yana jin abinda ake yi, shi har a lakocin mamakin yarinyan yake yi ainun, "yaushe har ta samu ƙwarin gwiwar da har zata kawo ƙarar sa? Lallai yarinyan nan dole ya koya mata hankali".

"Fodio, why did you break my wife's phone?"

Shiru yayi batare da ya ɗago kan sa ba, kuma be dena latsa wayan ba

"Kai ba magana ake maka ba? Are you crazy? Uban meyasa ka fasa mata waya? Ka dawo kenan zaka soma takura mata ko?" Big Dady yayi maganar a zafafe yana kallon sa

Sai a lokacin ne Usman ya ɗago kai fuskar nan a ɗaure yana kallon su, sai dai be iya cewa komi ba

Abba yace, "miƙo wayan mu gani uwata".

Miƙa masa wayan tayi, ya'amsa yana juyawa sai ya ɗago yana kallon ta yace, "Agarin ya yafasa miki wayan?"

"Mun yi karo ne shine ya faɗi, da nayi masa magana shi ne ya dawo ya tattaka min da takalmin sa".

"It's your fault, why did you talk to him then? Stop following her shit please". Abbu yayi maganar yana amsan wayan daga hannun Abba and put it aside

Big Dady said, "why doesn't she talk and break her phone?"

Sai kuma ya mayar da kallon sa ga Usman ɗin yace, "Make sure you buy her her phone and pay for it, idan ba haka ba zan mummunan saɓa maka kana jina ko?"

Gyaɗa kan sa kawai Usman yayi yana kallon Ɗahira da kanta ke ƙasa, kawai tunani yake yi a ransa abinda zai yi mata idan har ta shigo hannun sa

Kaka ne yace, "ya isa haka Lawal (Noor), karka ɗau abinda zafi haka mana, yanzu mu mayar da hankali kan abinda ya tara mu. Alhmadulillah and Allah show us this time to see my grandchildren finish their studies and become doctors now, don haka na tara ku in sanar muku da Albishir da na tanadar muku".

Murmushi yayi yana kallon su ɗaya bayan ɗaya kana yaci gaba da cewa, "Zuwa nan da Sunday motocin ku da na siya muku za su iso sai kowa ya zaɓi wanda yake so, wannan shi ne kyauta na a gare ku, sannan ina jan hankalin ku ku mayar da hankali wajen aikin ku, abinda ya kai ku shi za kuyi ba na son wasa,
May God help you all. May God bless you."

Duk ka parlour'n suka amsa da ameen ban da Usman da har yanzu latsa wayan sa yake yi, nan ɗaya bayan ɗaya suka yi ta mishi godiya kana

Please Login or Register in order to submit comment