Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya tanadar mata, yayi wa kansa alƙawari sai tayi dana-sanin rayuwan ta.

    Ita kuwa Ɗahira ko ci kanka bata ce masa ba har ya fice, domin wani irin baƙin ciki da zallan tsanar sa ke nuƙurƙusan ta, shiyasa baza ta iya tambayan sa ina zai kai mata waya ba.

     Ta jima a nan zaune tana kuka, gaba ɗaya ta fita hayyacin ta, har wajen ƙarfe 10:30pm. tana nan a haka, zazzaɓi me zafi ya rufe ta, dole ta rarrafa ta isa inda ta ajiye sauran maganin da tasaka a kawo mata jiya, ta ɗauka ta isa ga Fridge ta samu ruwa, sai dai bata sha ba sai da ta kora drinks ɗin da ta gani a ciki, domin ba ƙaramin yunwa take ji ba, ga shi mugun can ya rufe ta, tana tunanin wannan wani irin mugu ne da zai rufe ta a ɗaki? To me yake nufi da hakan? Shi ne bata sani ba.

     Tana gama shan maganin ta kwanta, sai dai ta kasa barci sai juye-juye take yi, daƙyar barci ɓarawo ya sace ta.

   

      Washe gari koda ta farka da safe, sabida yunwan dake cin ta ta nufi ƙofa don ta fita ta nemi abinci, amma sai taji ƙofar a garƙame, wani irin jijjiga ƙofan ta hau yi tana kiran sunan sa, nan da nan hawaye suka soma zuba a kyakykyawar fuskar ta da ta gama kumbura, ta sauya kamanni. dama ba ƙwarin jiki ne da ita ba, sai ta zube a nan ta hau rusa kuka, sosai take kuka tana kiran sunan sa ya zo ya buɗe ta.

      Amma Usman yana zaune a Parlour Yana jin ta be ko motsa ba, illa gyara kwanciyar sa da yayi ya ci gaba da latsa wayan sa, sai ma da yaji ta ishe shi sai ya kunna t.v ya ƙure ƙaran

Hakan ya tabbatar wa da Ɗahira yana nan zaune yana jin ta, wani irin kuka ta saki tana zame wa ta kwanta a wajen, ta ma rasa wani irin tunani zata yi, illa zuciyar ta dake ta faman zugi tamkar ta faso ƙirjin ta, "ashe ya shirya mata mugunta ne shiyasa ya ɗauke wayan ta, domin kar ma ta nemi wani ta waya"

Kukan ta tasha ta tashi zaune, shiru kawai tayi tana tunani hawaye na zubo mata, "me zata yi masa ta huce? Tana ga baza ta iya zaman auren nan ba, dole ne yau ta fita ta koma gida, dole ne kowa ya san halin da take ciki, da dai ta zauna a gidan sa ta gummaci a raba auren nan tun yanzu, ta matuƙar tsanar sa! kullum sake jin tsanar sa take yi a rai, domin ba shi da tausayi ko kaɗan.

        Miƙe wa tayi riƙe da cikin ta dake faman ciwo, ta nufi Fridge ta buɗe, drinks ta ɗauka tasha sosai, ta kwanta saman gado tana ta faman tsiyayar da hawaye.

    Wasa-wasa wunin ranan currr Usman ya ƙi buɗe ta, tun tana ɗaukar abun da wasa har taga ta kusa mutuwa saboda yunwa, domin bata da abun sha sai drinks, gaba ɗaya cikin ta ya gama ƙulle wa

Shi kuwa yana Parlour ko jirgau be yi ba, sallah kawai yake tayar dashi, duk wanda ya zo neman ta sai yace musu "tana barci". Har da masu zuwa ganin ɗaki ƴan cikin anguwa, da friends ɗin ta na wajen aiki, duk sai da Usman ya kora su, aka aiko Fadil da abinci, ya amsa ya rufe ƙofan, ya kuma je ya ajiye be ci ba be kai mata ba.

     A haka Ɗahira ta kwana a mawuyacin hali, ga yunwa ga zazzaɓin da koda yaushe yana jikin ta, sakamakon damuwa da kukan da take wuni yi.

    Da safe ta gwada buɗe ƙofan, sai taji ya buɗu, da sauri ta koma ta saka Hijab a saman kayan barcin ta ta fito da zumman zuwa gidan su ta faɗa wa iyayen ta komai, domin baza ta iya zama cikin uƙuba ba.


      Sai dai tana zuwa ƙofan Parlour ta ganshi a garƙame, lumshe idanuwan ta tayi hawaye na zubo mata, cikin muryan kuka tace, "Allah na roƙe ka, ka fitar dani daga hannun wannan azzalumin bawan naka". Sai ta fashe da kuka. Juyawa tayi ta koma kan kujera ta kwanta tana ta rera wa, sai da tayi ma'ishi wanda daƙyar ma take iya numfarfashi saboda yunwan dake cin ta. Tashi tayi ta nufi saman dainning ganin cololi an jera, sai dai tana buɗe wa tsami ya bugo ta, sabida abincin tun na jiya ne da aka aiko mata, juya wa tayi ta koma kichen, a wahalce ta gama girka indomie, a kichen ɗin ta zauna ta hau ci hannu baka hannu ƙwarya, duk jikin ta rawa yake yi, babu abinda take yi sai zubar da hawaye, gaba ɗaya tausayin kanta ya kama ta, "yanzu idan a haka zata ci gaba da rayuwa ya zata yi? Babu dole fa auren nan."

Sai da taji ta cika cikin ta fam kafin ta haƙura, tasha ruwa ta tashi ta fito, kan dainning ɗin ta nufa ta kwaso komi ta kai kichen, sai da tagama wanke gaba ɗaya cololin kafin ta wuce ɗaki, wanka tayi ta sauya kaya ta haye kan gado.

       Tun daga ranan haka Ɗahira take rayuwa, kullum tana gwada fita amma ina ƙofan rufe yake, ba ta da aikin yi sai dai ta kwanta tayi ta faman tunani, tun abun na damun ta har ta haƙura, ga shi ya raba ta da wayan ta bare ta kira Maman ta, gaba ɗaya tayi kewar su, kullum tana zaune cikin kaɗaici, ko kallo ba ta yi, sabida tun farko ma bata saba ɓata lokacin ta wajen kallo ba, ga shi ba ta sanin sanda Usman yake shigo wa da sanda yake fita, wataƙil ma ba a gidan yake kwana ba, shiyasa ta tashi tsaye wajen kai wa Allah kukan ta, shi ne ya jarabbe ta da wannan ƙaddararren auren, kuma shi ne zai fid da ita, domin bata da tsimi ko dabara, idan Allah yayi nufin Mijin ta me shiryuwa ne ya gane kuskuren sa, ita me iya biyayya ne ta zauna dashi kamar yanda iyayen ta suka zaɓa mata, amma muddin yaci gaba da wulaƙanta ta, to, dole ne zata sanar wa su Kaka a raba auren, domin baza ta iya zama ba.


         A haka har suka yi sati biyu da auren nan. A ranan da suka cika sati biyun ne, Usman ya koma aiki, har Office Big Dady ya Kira sa yace masa, "ya kamata ya bar matar sa taci gaba da zuwa aiki". Be ce masa komi ba illa gyaɗa masa kai da yayi

Sai da ya dawo Direct ya wuce wajen Kaka

Kaka na murnan ganin sa yana cewa, "ina ya baro matar nasa? ya hana ta zuwa ta gaishe shi tunda aka yi aure".

Taɓe baki yayi yace, "Ni Kaka zuwa nayi in sanar maka zamu tafi hutun amarci (Honeymoon) Ni da ita".
[23/09, 9:26 pm] OumƊahira نفيسة: 💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
              *FAMILY DOCTOR'S*
                         🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
   *NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱


*MALLAKAR:*
                 _NAFISAT ISMA'IL LAWAL_




*بسم الله الرحمن الرحيم*


*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA'S FAMILY*_

         *NATSUWA A SALLAH*
_Manzon Allah mai tsira da aminci, ya ce, "sallah ba kome ba ce illa miƙa wuya da tawali'u..." Kuma ya ƙara da cewa, "Bawa bai samun ladan sallar sa sai gwargwadon abinda ya hankalta daga sallar." Watau, gwargwadon natsuwar mutum cikin sallah gwargwadon darajar da yake samu gun Allah. Don haka ne ma ma'aikin Allah ya ce, "Allah ba ya juya wa Bawa baya yana cikin sallah matuƙar bai waiwaya ba; idan ya waiwaya kuwa, sai Allah ya bijire masa."_
_Babu abin da yake kawo waiwayo cikin sallah kuwa sai gafalar Bawa da muƙamin Ubangijin sa, watau ya zama tamkar wanda ya tsaya yana ganawa da Ubangijin sa alhali zuciyar sa tana shagale da wani abin dabam. A kan wannan matsala ne Allah yake ce wa Manzon sa, da al'ummar sa ma, a cikin suratul A'ARAF aya ta 205:_
_"Kada ka kasance daga gafalallu."_
_In muka lura sai mu ga cewa ta ya ya kuwa gafalalle zai iya tunawa da muƙamin Ubangijin sa yana cikin wannan hali na rashin kula har wani abin tsoro ya auku? Bugu da ƙari, daman can ga shi Allah ya yi umarni a cikin suratul Ɗ.H., aya ta 14 da cewa:_
_"Kuma ka tsayar da Sallah domin tuna Ni"._
_In mutum ya Yi haka, ana fata ya rabban ta._
   _Allah yasa mu dace._


.


        *EPISODE Forty*

     Washe baki Kaka yayi yace, "to to kai da Ɗahiran ce za ku tafi hutun?"

"Eh mana Kaka". Yayi maganar yana yatsina

"To Masha Allah Abu yayi daɗi, masha Allah". Kakan ya sake faɗa cike da farin ciki, domin ba kaɗan ba yaji daɗin hakan, tabbatan dai suna zaman lafiya. Sai kuma ya sake kallon Usman ɗin yace, "But when are you going? And what country are you planning to go to?"

"Tomorrow evening .. We will go to Turkey .. because can nake da gida.. na fi son zaman can". Yayi maganar tamkar ba ya so

"Masha Allah.. to Allah ya Kai ku lafiya, zan sanar da iyayen naka ko, ita kuma zuwa goben ya kamata tayi wa kowa sallama".

Tashi tsaye Usman yayi yana faman taɓe baki, kafin yace, "ai ba sai kace ba Kaka, she will come to greet you".

"Ja'irin yaro ka ganka ko? Kai dai ba'a yin abun arziƙi da kai Fodio". Cewar Kaka yana murmushi

Shi kuwa be ma bi ta kansa ba ya bar ɗakin. Kai tsaye Part ɗin iyayen shi ya wuce, babu kowa a Parlour, sai ya wuce ɗakin sa ya ɗauro alwala, da zai tafi masallaci ne suka ci karo da Hajiya, gaishe ta yayi ya wuce da sauri sabida har an gama kiran sallan magriba, kafin ya kai za su iya tayar wa.

    Sai bayan isha'i ya koma gidan su. Yana shiga parlour'n ya mayar da ƙofan ya rufe, kai tsaye ɗakin sa ya wuce ya yi shirin kwanciyar sa, zama yayi kan gado ya ɗauko Lapton ɗin sa yana dannawa, a haka har dare yayi nisa, sannan ya kwanta barci.

          Itama Ɗahira tuni tayi barcin ta, tunda babu abinda take yi sai kwanciya, iyakan tayi girki iya bakin ta ta cinye ta ɗauraye abun da ta ɓata ne, dayake ba shigo musu ake yi ba ko shara ba ta yi tunda babu inda yake ɓaci, ɗakin ta kawai take kakkaɓe wa ta share.






           *TOMORROW*

      Tana kwance a kan gadon ta tayi ɗai-ɗai, daga ita sai shimi fara da gajeren wandon sa shima fari, ta rufe gashin kanta da hula me raga-raga ja, babu abinda take yi sai tunanin ta yanda za'a yi ta koma aikin ta, zuwa yanzu ya kamata ta koma bakin aikin ta ko don ta riƙa ɗebe kewa, tunda babu abinda take yi yanzu a gidan.


      Buɗe ƙofan da aka yi yasa ta ɗago kanta tana aza manyan idanuwan ta a kansa, saurin kau da kai tayi daga kallon sa

While shima tunda ya shigo ya sauke ido a kanta, ya ɗauke kansa yana jan dogon tsaki tare da haɗe rai

Tsakin kamar a tsakar kanta yayi, itama sai taci magani zuciyar ta cike da baƙin cikin ganin sa

"Put on the Hijab and follow ME". Abin da ya faɗa kenan ya juya ya fice

Shiru tayi tana tunani, tamkar baza ta yi abinda yace ba, sai kuma ta tashi ta buɗe wardrobe ɗin ta ta zaro dogon Hijab maroon Colour, ta saka a jikin ta ta nufi ƙofa ta fice.

     Yana zaune a Parlour, ganin ta sai ya tashi ya nufi ƙofa ya fice

Bata yi wani tunani ba tabi bayan sa, a haka suka ƙarisa cikin gidan su

Kai tsaye Part ɗin Kaka suka wuce, inda suka same sa kamar ko yaushe yana zaune a kujeran sa yana karatun jarida

Ganin su ba ƙaramin farin ciki ne ya ɗarsu a zuciyar sa ba, nan da nan ya washe baki yana musu maraba

Tuni Ɗahira ta isa wajen sa ta rungume sa, sai ta fashe da kuka tsaban farin ciki, domin ji take yi tamkar an ciro ta a kurkuku yau ta sami sake

"A'a Mata ta ya haka? Ko duk kewar nawa ne da kika yi?"

Bata yi magana ba illa ɗago kai da tayi tana kallon sa

Sai ya sakar mata murmushi yana cewa, "kin ganki kuwa? Duk kin sauya gaba ɗaya kin rame, halan ciwo kika yi?"

Usman dake tsaye bakin ƙofa kamar an dasa shi, ya harɗe ƙafafu yana kallon su, yayi saurin cewa, "to ba dole ka ganta ta rame ba tunda ta rabu da hanjin rayuwan ta, ko rashin ganin ka zai saka ta rama, ga ta nan dai ku gaisa ka ba Ni ita zamu wuce".

Dariya Kaka yayi yace, "ban san sanda ka lalace ba Fodio". Sai kuma ya mayar da kallon sa kan ta yace, "to mata ta Ubangiji Allah ya kai ku lafiya ya dawo daku lafiya, abinda zan ce kawai ki kula da kanki kinji? Kuma ki yo min tsaraba sosai kar ki ce kin manta dani".

Kallon sa kawai take yi da mamaki, sai kuma ta buɗe baki da ninyan tambayar sa

Usman ya katse ta da faɗin, "tashi mu je, You are wasting my time".

"Kai dai ja'irin yaro ne Usman, tafiyan da ba yanzu za ku yi ba shi ne duk kabi ka ishe ta, ka bari mana mu gaisa sosai mana".

Shi Usman gani yake yi kamar zata iya ɓallo masa ruwa, shiyasa yayi saurin taho wa yaja hannun ta suka fice

Da sakakken baki kawai tabi sa tana kallon ikon Allah

Suna fita ya yi saurin sakin hannun ta kamar ya riƙe ƙaya, domin abinda yaji kamar ana jan sa da electronic, be kalle ta ba yace, "ki mai da hankali ki sanar da su game da zaman mu, wlh sai na ɓalla miki rayuwa biyu".

Idon ta ta waro kawai tana kallon sa, "to wannan ko dai ya samu taɓin hankali ne?" Tafaɗa a ranta tana me sake ƙwalalo idanu waje

Kallon ta yayi ganin kamar ba ta bin shi a baya, yanda idanun sa suka shige cikin nata sai yayi azaman ɗauke kai, domin ba kaɗan ba ya tsani su haɗa ido, wani irin faɗuwar gaba ne me haɗe da tsoro yake riskan sa a koda yaushe, shiyasa ya tsane ta sosai. Daure wa kawai yayi ya dalla mata harara, kamar zai yi magana sai kuma ya fasa ya juya yaci gaba da tafiya

Sai tabi bayan sa kawai tana kitsima abubuwa a ranta, sai kuma maganar Kaka ya dawo mata, "to ina za su je ne da Kaka yake musu addu'a?". Babu me ba ta amsa dole taci gaba da bin bayan sa. Part ɗin su taga sun bi, sai farin ciki tsantsa ya cika ta

Suna shiga suka ci karo da Aunty Amarya zaune a parlour'n ita kaɗai, babu kowa ma sashin, tunda Abbu yana Hospital, Fadil kuma yana school, sai Kuma Umma da ta tafi anguwa

Da gudu Ɗahira ta ƙarisa wajen Maman ta tana me kiran sunan ta tare da fashe wa da kuka

"A'a mene ne haka kuma? Wannan wani irin sakarci ne?" Aunty Amarya tayi maganar tana riƙe ta

In a tears, Ɗahira she said, "I miss you Mama! Miss U so Much."

Murmushi Aunty Amarya tayi, sai ta kalli Usman da ya samu wuri ya zauna har da harɗe ƙafafu yana latsa waya, tace, "ashe za ku yi tafiya? Ɗazu nake ji wajen Abbun su".

Sai lokacin ya ɗago kai ya kalle ta, guntun murmushi ya saki kafin ya bata amsa a taƙaici, yana me gaishe ta

Ta amsa cikin fara'a tare da sanya musu albarka, da musu fatan alheri

Ɗahira fa kanta ya gama ƙulle wa, "da wannan mutumin ne za su yi tafiya? To zuwa ina?" Wannan tambayoyin ne bata sani ba, duk da tana son tambaya sai kuma ta fasa. Tana ɗago kai suka haɗa ido dashi, ya sakar mata wani kallo da sai da gaban ta ya faɗi, da sauri ta ɗauke kai tana mayar wa wajen Maman ta

Aunty Amarya tace, "So take care of your self? May God protect you and bring you peace."

Daga ita har shi babu wanda ya amsa. Illa miƙe wa da yayi yace, "tashi mu je. Za mu tafi Mama".

"To madalla, a dai ta addu'a Allah ya tsare". Aunty Amarya tafaɗa cikin fara'a

Usman fa ya kasa ya tsare ya ƙi tafiya sai da Ɗahira, don shi gani yake yi kamar zata faɗa mata wani abun, shi kuma ba ya son kowa ya fahimci komi yanzu ba tare da ya wulaƙanta rayuwan ta ba, inyaso sai a saka shi ya sake ta da hujja, domin ya san muddin su Big Dady suka san wani abu, za su hana sa tafiya ko ina ne, sannan za su saka mishi ido, haka kuma zai ci gaba da zama da ita ba halin saki.

      Ɗahira ko jirgau bata yi ba don ba ta da ninyan tashi ma. Sai da Aunty Amarya tace mata, "ta tashi su tafi". Kafin ta miƙe cike da ƙunan zuci tabi bayan sa, tamkar ta koma ta sanar wa mahaifiyar ta halin da take ciki, sai kuma ta ga hakan be dace ba, gwara taci gaba da haƙuri, Allah shi zai mata maganin komi, da sannu Allah zai saka mata. Idan Allah yayi auren su ba daɗaɗɗe bane nan kusa za su rabu da yardan Allah

    Kai tsaye Part ɗin Hajiya suka wuce, inda suka tarar da ita a parlour

Da sauri Ɗahira ta duƙa har ƙasa ta gaishe ta

Tsaban takaici ma Hajiyan bata amsa ta ba, illa ɗaure fuska da tayi tana kallon Usman tace, "na ji wani zance wai za ku tafi Turkey yawon cin amarci? Har yaushe ta shanye ka da zaku tafi cin amarci da ita? Yaushe ka soma son ta ma?"

Usman be tanka ba, don be da ma alaman tankawan

Ɗahira kuwa tuni ta sad da kanta ƙasa tana maimaita kalaman Hajiyan tamkar karatu, domin ta kasa ma fahimtar me take nufi

Tsawan da Hajiyan ta daka wa Usman ne ya dawo da Ɗahira cikin tunanin ta, da sauri ta ɗago kai tana kallon Hajiyan

"Ke tashi ki wuce". Yayi maganar idanun sa a kan Ɗahira fuska babu walwala

Tana mayar da idanun ta kansa, ya ɗauke nashi idanun daga gare ta

Ta san babu da wanda zai yi sai da ita, don haka ta miƙe ta fice ta nufi hanyar gidan su.


     Kai tsaye ɗakin ta ta wuce ta zube saman gado, shiru tayi tana faman tunani, "ta fa kasa gane me mutanen gidan suke nufi, shin da gaske ne tafiya za su yi da shi ko kuma fahimta ne bata gama yi ba? Amma kuma ga abinda Mahaifiyar sa tace, ma'ana dai da ita yake son tafiya? Anya?" Sai kuma ta miƙe zaune kamar an zare mata laka, a ranta take tambayar kanta, "shin meyasa yake son yin tafiya da ita? Sai dai idan akwai abinda ya shirya yake son aiwatar wa a game da ita, idan ba haka ba mutumin da ya tsane ta ba zai taɓa tafiya da ita wani waje ba. Tabbas a cikin zuciyar ta ta kasa yarda babu komi a zuciyar Usman".

Shigowar sa cikin ɗakin ne yasa tabi shi da idanu

Fuska a ɗaure ba tare da ya kalle ta ba yace, "ki shirya kayan ki.. by 03:00 pm. We'll go". Da gama maganar nasa ya juya da ninyar fice wa

Amma sai tayi saurin cewa, "Where are we going? Ni fa I don't understand."

Be ce mata komi ba bare ya juyo, ya ficewar sa.

    Ɗahira ta jima a nan zaune bata iya tsinana komi ba, sai kuma daga baya da ta ga bata da sauran dabara sai ta miƙe ta soma shirya kayan ta a cikin ɗan ƙaramin akwati, ba wani kaya da yawa ta zuba ba tunda har yanzu bata tantance inda za su je ba, duk da ta ji su Kaka ɗazu sun faɗi yawon cin amarci, amma ta san yanda suke zaune shiyasa ma bata saka maganar a rai ba, ta san sai masoyan asali ke irin wannan tafiyan amma ba su ba.

    Bayan ta gama ta zare Hijab ɗin jikin ta, sannan ta sauya kaya zuwa Arabian gwon baƙa da kwalliyan stones, sosai rigan ta haska fatar ta ta ƙara mata kyau ainun, duk da sosai zaka ga raman da tayi matuƙa, amma kuma ta sake kyau saboda hutu da ta ɗan samu waɗannan satikan ba tare da ta taɓuka komi ba

Tana gama wa ta fito Parlour, zaman ta tayi tana jiran kuma next me zai ce tayi. har ƙarfe ukun ta gota be fito ba

Sai uku da rabi sannan ya fito cikin shirin sa, sosai yayi kyau kamar ka sace sa ka gudu, shigan dai da ya saba na ƙananan kaya shi yayi, wandon me ruwan ƙasa jeans, sai farar riga da aka yi harafin U a gaban rigan da coffee colour, kayan sun yi masa kyau sosai sun kuma haskaka skin ɗin sa, musamman ma da yayi amfani da coffee Cumbas sai ya ƙara haɗe wa, kansa ba hula sai kwantaccen gashin kansa baƙi siɗik da ya sha gyara har zuwa sajen sa suna shaining. Shima yana jaye da ƙaramar Trolly wanda tafi na Ɗahira ƙanƙanta, ba kaya ya zuba ba abubuwan buƙatar sa ne a ciki, irin su laptop da sauran su, saboda  yana da komi a can, kayan sawan sa ma na can daban ne

Jan Trollyn yayi ya nufi ƙofa zai fice

Ganin haka itama Ɗahira sai ta fito ta biyo shi, tana fita ta ganshi tsaye bakin ƙofan, sai tayi saurin jan Trollyn ta tayi gaba

Shi kuma komawa ciki yayi rai a haɗe ba tare da ya kalle ta ba, jin ƙai ya hana sa furta komi bare ya saka ta taje ta kashe kayan wutan gidan, ya gummaci shi yaje yayi da ya furta mata

Har ɗakin ta sai da yaje ya kashe komi na na'ura, sannan ya fito, ya rufe gidan ya nufi parcking space, inda Ɗahira ke tsaye tsakankanin motan ta da na shi; rana sai faman gasa ta take yi, dayake ba inuwa a wajen, sai faman jan tsaki take yi cike da takaicin sa, "don me ya saka ta ta fito sannan ya shanya ta a waje ya koma ciki? Miskilin mutumi kawai". Ta sake jan dogon tsaki tana ɗago kai, sai ta ganshi gab da ita yana taho wa, da sauri ta ɗauke kai daga kallon sa duk da shi ba ita yake kallo ba, amma sarai yaji tsakin da tayi, shiyasa ya sake tamke fuska kamar hadarin kaji, irin ba mutuncin nan

Boot ya buɗe ya saka Trolly ɗin sa, sannan ya bar shi a buɗe ya shige motar sa

Hakan yasa itama Ɗahira ta saka nata a ciki, sai ta rufe ta zo tayi tsaye a gefen motan tana tunanin inda zata shiga

Horn ya danna mata da ƙarfi, dole yasa ta buɗe gaba ta shige tayi zaman ta, shi kuma yaja motan yayi bakin Gate Yana sake cin magani, sai dai miskilanci ya hana sa tanka wa bare ya faɗa abinda ke ransa

Ita kuwa duk a takure take da ganin su waje ɗaya cikin mota, tunda hakan be taɓa faruwa ba

Haka zalika shima hakan yake ji, shiyasa ya ke tsula gudu shaf-shaf suka kai, don kawai ya ƙosa ta fice masa a mota.

    Suna kai wa airport wani abokin Usman ɗin ya zo ya tarbe su, shi Usman ɗin ya saka yayi musu komi da za su buƙata, ko passport da za'a yi wa Ɗahira sai dai ya samo picture ɗin ta a wayan Fadil.


        Jira kaɗan suka yi aka kira su, suka shiga jirgin. Kujeran su na side ɗin juna ne, ita tana ɓarayin dama a kujeran hanya, sai wata a gefen ta a lungu. Shi kuma yana gefen hagu ne a lungu, shima yana tare da mace ce a gefen nasa. A haka jirgin nasu ya tashi ba tare da magana ta sake shiga tsakanin su ba, tamkar ma dai ba tare suke ba, domin babu wanda zai ce ma suna da

Please Login or Register in order to submit comment