Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

magana da yaren da zanji dan Manzon Allah (S.A.W)Yayi Hani da idan mutane na zaune wasu daga ciki su sauya harshe zuwa wanda sauran basaji koda ba zaginsu zasuyi ba amma wanda baijin Yaren zai tsargu dan haka ku kula hegiya gantalelliya mai kaɗifiri�?.

Kai Yaya Abba ya gyaɗa cike da ladabi yace.
“Insha Allah zamu kiyaye�?.
Ita kuwa khausar baki ta taɓe aranta tace wannan tsohuwa ta fiye mita da takalan magana. Ta fara da fadin Manzon Allah a karshe kuma ta buge da masifa da cemin gantalelliya.

Azahiri kuwa sai ta saki fursakarta ta matsa kusa da yaya Abba tace.
“Ayyah Yaya Abba ka sammin wayarka zan kira Mommy na mugaisa�?.
Juyowa yayi ya kalleta tare da cewa.
“Ok ba matsala anjima zan baki sai Khadijah ta rakaki bishiyar ƙare zancen ka kuyi magana�?.
Cikin jin dadi tace.
“Toh shikenan Nagode�?.
Sallama yayi musu kana ya tafi.

Da yammaci Khausar na zaune adakali Dije kuma na shara suna hira sai da ta kammala sharan Khausar ta dube tace.
“Dije muje ki rakini wajen Yaya Abba in karɓi wayarsa�?.
Kai Dije ta gyaɗa da faɗin.
“Toh�?,sannan suka fice suna hira har suka isa.

Yaya Abba kuwa yana ganinsu ya miƙe tare da zuwa kusa dasu Idanunsa akan Khausar yace.
“Kinzo�?.
Kai ta gyaɗa alamar eh.
Yace.
“Ok mutafi nima zanje taya ƙanina Ibrahim ɗiban ƙwai�?.
Ɗan murmushi tayi tare da faɗin.
“Yaya Abba kaima kana aikin?�?.
“Sosai ma aikin gado ne ai duk da cewa ina shirin kammala degree na acikin Ɓadamaya bazai hana nayi aikin gadona ba�?.
Cewar Abba
Kai ta jinjina kana tace.
“Allah yataimaka�?.
Ya amsa da.
“Ameen�?.
Suna isa Gindin bishiyar Khausar ta juya ta kalli Dije tace.
“Dole sai na hau bishiyar network zai zo�?.
Dije ta girgiza kai tace.
“A'a ko kan duwatsun nan kika zauna zaki samu network inde ba'a cika ba abinda yasa wasu ke hawa bishiyar saboda kafin su zo duk an cika saman duwatsun idan kasamu ancika dole sai kan bishiyar�?.

Kai ta gyaɗa kafin ta ƙarasa ainihin inda ƙarƙashin bishiyar yake Sadik ta gani zaune yana waya.
Murmushi ta sakar masa tare da zama gefensa sannan ta sanya number Mommy. ringing ɗaya ana biyu Mommy tayi picking.

Ita kuwa khausar cike da zumuɗin jin Mommy tayi picking call ɗin tace.
“Mommy na�?.
Aɓangaren Mommy kuwa jin Muryar Khausar yasa ta saki murmushi mai sanyi kafin tace.
“Khausar�?.
Murmushi mai nuni da zallan farin ciki Khausar tayi tace.
“Na'am Mommy na nayi missing ɗinki�?.

“Nima nayi missing ɗinki Mamana�?.
Dariya Khausar tayi tace.
”Mommy Ina Raudat?,Ina Haiydar?, Ina Ramadan??�?.
Murmushi Mommy tayi tace.
“Duk suna lafiya�?.
Haiydar dake gefen Mommy yace.
“Gani nan Maman Fitina nayi missing ɗinki tunda kika tafi babu mai min faɗa babu wanda zai ce na renasa sannan babu mai nuna min iko da mulkin mallaka�?.

Dariya Khausar tayi tace.
“Hmmm ai nagane ɗan uwa ko ina nuna maka iko da mulkin mallaka gada nayi in faɗa maka na samu wacce ta cuna Ni komai da ƙa'ida akeyi ko kallo zakayi sai an maka tsarin kallon da zaka yiwa mutum shi�?.

Murmushi Haiydar yayi yace.
“Allah Hajja Nana ko?�?.
Dariya tayi tace.
“Ita dai fitinanniyar tsohuwa, tsohuwa sai Bala'i ba'a zaman lafiya da ita".

Mommy dake gefe ta amshi wayar da faɗin.
“Um,Um Khausar karfa ta jiki�?.
Murmushi Khausar tayi tace.
“Toh idan ta jini ma ya ta iya dani bare ma tana can gida mun barta tana gyaɗa kai muku ma munzo wajen bishiyar ƙare zancenka ne ko surutunka ne ohon musu!�?.

Haiydar ne yayi Dariya kasancewar wayar a speaker yake yana jin komai yace.
“Wani irin bishiya ne kuma ƙare zencen ka�?.

Ita kuwa khausar cewa tayi.
“Hmm garin fa basu da network sai wajen bishiya ɗaya suke zuwa yanzu ma haka wurin bishiyar nake�?.

Dariya Haiydar yayi yace.
“Ai dama kin iya ɗale-ɗalen bishiya kina nan kamar Biri�?.
Murmushi tayi sai kuma ta ɓata fuska tace.
Ni sa'arkace za kace ina tsalle kamar Biri??�?.

Murmushi tare da faɗin.
“Addah Khausar Sarkin son girma kiyi haƙuri to yar uwa�?.
sakin murmushi tayi kafin tace.
“Bawa Ramadan�?.
Miƙa masa Haiydar yayi.
Ramadan yace.
“Addah Khausi nayi kewarki�?.
Cike da ƙaunar ƙannen nata tace.
“Nima nayi kewarka ɗan ƙanina Insha Allah na kusa dawowa�?.
Amsar wayar Mommy tayi tace.
“Kin Kusa dawowa haka kukayi da Hajja Nana nan?�?.

fuska ta ya mutsa kana tace.
“Sai munyi da ita Mommy yau kwanana biyarfa ana shida nake idan nayi sati biyu zan dawo ai�?.
Mommy tayi murmushi tace.
“Tsakaninku de ni yanzu ba ruwana nima ba bari na tayi ba�?.
Dariya Khausar tayi tace.
“Ina Raudat? Su Ramadan na zuwa hadda ko?�?.

Kai Mommy ta gyaɗa tace.
“Ai Asma'u ma tazo tace malamai nata tambayarki sunce taya zakiyi tafiya baki sanar musu ba kodan ba boko ne sai hadda ne kawai wato?�?.

Girarta ta ɗan shafa da yatsarta manuniya kana tace.
“Hmmm ai kuwa na faɗawa Asma'u ta sanar musu wataƙil ta manta ne�?
“To ai yanzu kam sai in kin dawo.
Ki dai bi tsohuwar ahankali saboda ki samu tabarki ki dawo akan lokaci�?.
Cewar Mommy.
Itako Khausar kai ta gyaɗa kafin tace.
“Toh shikenan Mommy na zanyi duk yanda kika ce. Yawwa Mommy ki turo min Number Ummin Asma'u�?.
”Toh”Mommy tace sannan ta katse kiran.
Ita kuwa Khausar juyawa tayi tare da kallon yaya Abba dake tsaye ta langwaɓar da kai kafin tace.
“Ayyah Yaya Abba in ƙara Kiran wata ƙawata?�?.
Kai ya gyaɗa kana yace.
“Ki kira ba matsala�?.
“Toh�?,
tace tare da maida kallonta kan wayar da text ɗin Number ya shigo copy tayi tare da dearling.

Tana kira ringing ɗaya Ummi ta ɗauka.
Khausar tace.
“Ummina�?.
Murmushi Ummi tayi tace.
“A'a Khausar kece? Ya mutanen Ruga fatan kun same su lafiya?�?.

“Lafiya lau Ummi. Ina Asma'u�?. Cewar Khausar

“Gata nan tana tsifa�?. Ummi ta faɗa tare da miƙa wa Asma'u wayar.

Asma'u na amsar wayar ta maƙala akunnenta tare da ƙyalƙyalewa da dariya tace.
“Na sani�?.
Ita kuwa Khausar hararan wayar tayi jin Dariyar da Asma'u keyi tace.
“Kinsan me?�?.
Asma'u tace.
“Na sani tsoron Yah Moddibo kike yasa kika gudu kika tafi Rugar nan inba haka ba keda baki ƙaunar tafiyar nan amma daga arba dashi kika tafi Ruga�?.

Ƙwafa Khausar tayi tace.
“Ba dole in tafiba tunda kika kaini kafin in dawo wala Allah ya huce�?.
Cike da zolaya Asma'u tace.
“Wai ai Yah Moddibo baya mantuwa duk abinda aka masa".
Wara ido Khausar tayi sai kuma tace.
“Asma'u duk kece kika janyo min da baki kaini gidansu ba da haka bai faru ba wlh�?.

Asma'u kuwa murmushi ya subce mata kafin tace.
“Calm down wasa nake Miki shi idan abu ya wuce kwana uku ma wata ƙil mancewa�?.
Ita kuwa khausar jin haka yasa ta saki ajiyar zuciya da faɗin.
“Alhamdulillah". Sai kuma ta harari wayar tare da cewa.
“Au wata ƙil nema kenan�?.
Dariya Asma'u tayi kana tace.
“Yaushe zaki dawo?�?
Taɓe baki Khausar tayi tace.
“Waya sanma wannan tsohuwar wataƙila nan da sati biyu ko kuma sati ɗaya idan nayi sa'a tabarni in dawo anata wuceni ahadda ko?�?.

Da sauri Asma'u tace.
“Eh ana wuce ki kam�?.
Ita kuwa Khausar ɗan jim taui kafin tace.
“Insha Allah nima dai na kusa dawowa�?.
“Toh Allah yasa�?. Asma'u ta faɗa kana sukayi Sallama tare da katse kiran.

Kallon Khausar yaya Abba yayi yace.
“Koda kuna hutun ana baku hadda ne?�?.
Kai ta gyaɗa da faɗin.
“Eh Yaya Abba muna zuwa hadda�?.

“To ai babu matsala inde hadda ne ki riƙa zuwa wajen Babanmu yana ƙara miki ai zai baki hadda ki cigaba kada awuceki�?.
Cewar Abba.
Khausar kuwa cike da farin ciki tace.
“Toh shikenan Yaya Abba insha Allah kuwa�?.
Daga haka suka miƙe suka taho kai tsaye gidansu Abba suka nufa bakinsu ɗauke da Sallama suka shiga.

Kallon Dije da Ibrahim Yaya Abba yayi yace.
“Bari na rakata wajen Liman�?.
Kai suka gyaɗa sannan yayiwa Khausar jagora zuwa ɗakin Mahaifinsa bakinsu ɗauke da Sallama suka shiga ɗakin.
Ɗaki ne irin na bukka mai shatin kwabo baki ɗaya ɗakin kewaye yake da littattafan Addini kana da qura'anai bugu da ban bugun misira da warash.
Cike da ladibi Khausar ta gaishesa Amsawa yayi cikin sakin fuska kafin ya kalleta da murmushi yace.
“Matso mana�?.
Kai ta gyaɗa tare da Matsawa kusa dashi ta zauna akan buzunsa.
Yana murmushi yace.
“Lafiya? ko dai ƙaran Addata kika kawo?�?.

Murmushi tayi tace.
“Ni Meye ruwana da ita da zan kawo ƙaranta, dama karatune muna hadda Acan toh kuma na tsaya za'a iya wuceni�?.

Kai Ya jinjina kana yace.
“Wacce surah kuke?�?.
Anutse tace.
“Suratul Taubah muke munyi shafi huɗu zan tashi ashafi na biyar�?.
Cikin gamsuwa ya gyaɗa kai tare da faɗin.
“Karanta inda kukayi naji�?.
Gyara zamanta tayi tare da gyaɗa kai kana taja sassayan numfashi cikin zazzaƙan Muryanta tayi basmala kana ta fara rerewa karatun cike da jan Tajwidan Tartilan.
Kai Malam Liman ya jinjina da faɗin.
“Masha Allah�?.
Yaya Abba kuwa lumshe Idanunsa tun lokacin data fara karatu kana ya buɗe su alokacin da takai ƙarshen ayan yace.
“Masha Allah Allah ya baki zaƙin murya Hafiza�?.
Jin abinda yace.
Yasa Khausar sakin sakin ɗan guntun murmushi

Malam Liman ne yace.
“Masha Allah, yanzu dai kullum ki ringa zuwa irin wannan lokacin kina ɗauka darasin saboda maza basu fara zuwa ba, dalibai yara kuma sun tashi. kullum zan dinga baki awa ɗaya sai ki dinga zuwa ina ƙara miki sannan da wasu littattafan ma idan kunayi ki faɗa zan dinga ƙara miki�?.

Cikin daɗi tace.
“Toh ba matsala Insha Allah sannan munayin littafin Tajweed, Tauheed, Urasatul Nurul yaƙin, Nahwu, da kuma Mi'atu Hadith da dai sauransu�?.
Gyara zaman babbar rigarsa yayi tare da faɗin.
“Insha Allah zaku riƙa zuwa ina ƙara miki keda Dija da Ma'u tunda dama sunyi sauƙa�?.
Sannan ya buɗe kur'ani ya miƙa mata shi kuma ya shiga karanta mata akai yayin da yake bin ko wanne harafi yana basa haƙƙinsa saida yakai har ƙarshen shafin kafin ya dubeta yace.
“In mai-maita Miki?�?.
Kai ta girgiza alamar a'a tana jinjina baiwar ilimi da zaƙin murya da Allah ya masa.
Anutse yace.
“Ki hadda ce su kafin gobe sannan ki kawo min�?.
Khausar kuwa kai ta gyaɗa tace.
“Insha Allah zan dage Malam amman dai goben ma zan biya sai jibi a ƙara min ko?�?.
Murmushi yayi tare da cewa.
“La ba'as�?.
Miƙewa tayi Sannan tace.
“Zan tafi da Kur'anin�?.

“Toh�? ya cemata
Sannan suka fice bayan fitansu ta dubi Dije tace.
“Muje gidan garkuwan rugan ki�?.
Murmushi Dije tayi tace.
“Gidan Baffa Umaru�?.
Kai Khausar ta gyaɗa sannan suka nufi gidan Baffa Umaru.
Aƙofar gida suka samesa yana tare da baƙi,
Juyawa yayi ya kallesu kafin yace.
“Kushiga ciki ina zuwa".

Kai suka gyaɗa sannan suka shiga cikin gidan bakinsu ɗauke da Sallama,kallon cikin gidan Khausar tayi ko ina ashere fes-fes babu alamar datti ko ƙazanta.
Adama kuwa murmushi fuskarta ta faɗaɗa tace.
“Su Khausar ne sannun ku da zuwa�?.
Dije tace.
“Yawwa Goggo Adama ya gida�?.
Ta amsa da lafiya lau sannan ta miƙe ta kawo musu faten doya da ruwa arandan ƙasa mai sanyi.
Ita kuwa khausar murmushi tayi tana jinjina mutunci da karancin Goggo Adama atare sukaci kana suka gabatar da sallan Azahar sannan sukayi mata har zuwa lokacin Baffa Umaru bai shigo ba.

Bayan fitarsu agidan Baffa Umaru Khausar ta juya ta kalli Dije tace.
“Muje gidan Hajja Nana in ɗauki kayana�?.
Dije tace.
“Toh�?.
Sannan suka nufi gidan Hajja Nana ba suyi wani tafiya mai tsawo ba suka isa gidan, Atsakar gida suka tarar da Hajja Nana.

Harara Hajja Nana ta watsa mata tace.
“Ke kam Uwar gantali kina nan kina ta yawo bazan ganki ba bare in Zauna dake�?.
Fuska Khausar ta ɓata da faɗin.
“Wani irin gantali duk ba gidan ƙannenki da ‘ya‘yanki nake zuwa ba kuma ɗazun nan ina anan na tashi zaki ce amma yanzu zaki ce min gantali na tafi to nide gaskiya ba gantalalliya bace yawwa zaki wani cemin gantali ba gidan ƙannenki na tafi ba kuma saida na faɗa miki zamuje Bishiyar ƙare zancenka in kira Mommy na sannan yanzu ki wani cemin gantalalliya to nide wallahi ba gantalalliya bace�?.

Hajja Nana tace.
“Ke kam wace gantalalliya ce ma ta fiki?,In banda gantali me kika iya?".
Ita kuwa khausar juya manyan Idanunta dake lumshe kafin tace.
“Wallahi da abinda na iya�?.
Hajja Nana kuwa kai ta gyaɗa tace.
“ƙwarai da abinda kika iya fitsara ba gashi ma yanzu kina yi bayan shi babu wani abu da kika iya�?.

Khausar za tayi magana Dije tayi saurin riƙe hannunta cikin ƙasa da murya tace.
“Dan Allah kiyi shiru ki ƙyaleta�?.
Kai ta gyaɗawa Dije tare da tsuke bakinta.

Hajja Nana kuwa fuska ta tsuke Idanunta akan Khausar tace.
“Bari in samiki doka gidan Jauro da kike zuwa ki kwana bazan hanaki ba tunda kince kinfi farar kura tsoro.
Amma gobe ana sallar asuba na ganki anan dan zaki riƙa tayani aiki.

Baki Khausar ta taɓe da faɗin.
“Allah ya kaimu sannan bawai ana idar da Sallah bane zanzo saina yi Azkharul sabah da kuma karatuna�?.
Harara Hajja Nana ta watsa mata tace.
“Toh Al-huda-huda sarkin karatu�?.

Khausar kuwa baki ta taɓe tace.
“Koma de menene�?. Sannan ta juya ta shiga ɗaki ta dauko kayanta tana fitowa ne taji Hajja Nana na cewa Dije.
“Kar kice zaki koyi rashin kunyar wannan yarinyar".
Dije kam murmushi tayi ita kuwa khausar batare data tanka taba ta fice Dije tabi bayanta...

GEMBILA

Acan ɓangare Moddibo kuwa kwance yake akan makeken gadonsa daya sha shimfiɗa na Alfarma yayin da hannunsa biyu ke haɗa yana addu'ar bacci ya ɗauki kimanin minti goma kafin yasha fa addu'ar ya gyara kwanciyarsa yana mai lumshe idanunsa da haka bacci ya ɗauke sa can cikin baccinsa yaji wayarsa na ruri ya buɗe idanunsa kasancewar sa ba mutum ne mai nauyin bacci ba yasa hannu ya janyo wayar yana kallon screen ɗin Bahrain shine sunan dake ƙasan screen ɗin.

Picking Yayi tare da kai wayar kunnensa tare da sallama.
Amsawa Jalaludeen yayi da faɗin.
“Ya yatsun ƙafar naka sun warke ne!?�?.
Moddibo kuwa gyara kwanciyarsa yayi da faɗin.
“Jameel ya faɗa maka kenan?".
Jalaludeen yace.
“Kamar dai baka sanni ba sai Jameel ya faɗa min zan sani?�?.

Moddibo kuwa kwanciyar sa ya gyara kana yace.
“Eh ainaga kunyi waya ne bayan abin ya faru�?.
Jalaludeen yace.
“Wallahi Jameel bai faɗa min ba lokacin da abin yafaru ma ai ina nan�?.

Shi kuwa Moddibo kwanciyarsa ya gyada tare da faɗin.
“Hmmm yayi kyau ka kawo mana ziyara kenan�?.

“Eh nakawo muku ziyara Barka da jumma'a ai tare mukayi jam'in sallan jumma'a ma�?.

Sassayan numfashi Moddibo ya fesar kana yace.
“Mungode amma aiba mu gaisa ba".

Murmushi Jalaludeen yayi yace.
“Ai zamu gaisa sai kuma na samu abin kallo ana dramer Shiyasa ba mugaisa ba, na tafi shi Kam Jameel baima San nazo ba Dan ban faɗa masa ba�?.
Kai Moddibo ya jinjina kafin yace.
“Toh yayi kyau ya labarin mutanen England�?.
Jalaludeen yace.
“Duk suna nan lafiya�?.
Kana sukayi Sallama.
Kallon screen ɗin wayar Moddibo yayi Aransa yace Allah mai kyauta shi Jalaludeen jinsinsa da ban amma haka yake jin daɗin Mu'amala damu sannan babu cutarwa atsakaninmu da wannan tunani bacci ya ɗauke sa.

Acan Rugar Jauro yaya kuwa Washe gari da Asubah bayan Khausar ta idar da Sallah tayi Azkharul sabah da tagama ta juya tare da kollon Dije tace.
“Muje gidan Hajja Nana�?.
Dije tace.
“A'a kije Ni zan dafa mana abinda zamu ci kinga Goggo Nanne bata jin daɗi�?.
Kai Khausar ta gyaɗa sannan ta miƙe ta fita atsakar gida ta samu Hajja Nana ta jiƙa wankekkdn wakenta ya jiƙa,
Zama Khausar tayi tace.
“Ina kwana Hajja Nana�?.
Ba yabo ba falassa Hajja Nana tace.
“Lafiya".
Sannan ta ɗaura da cewa.
“Ga can wake ki ɗauka ki markaɗamin acan�?.
Ta ida maganar tana nunawa Khausar inda ta kafa dutse irin na mutan da saboda basu da inji agarin".

Ita kuwa khausar inda Hajja Nana ta nuna mata da faɗin zatayi markaɗe ta riƙa bi da kallo kafin ta mayar da kallonta kan Hajja Nana tace.
“Wai in markaɗa Miki me?�?.

Hajja Nana tace.
“Waken ƙosai kinga kwana biyu banyi ba tunda kika zo Mai nane ya ƙare sai jiya na samu da Sadik ya shiga Gembila ya sayo min�?.

Ita kuwa khausar da Mamaki tace.
“Kamar ya in miki markaɗe?�?.
Kallonta Hajja Nana tayi tace.
“Kiyi min markaɗe nace�?.
Ita kuwa Khausar ƙugu ta riƙe tace.
“Ni wallahi ban taɓa ganin yanda akeyi ba ban sani ba kuma ban iya ba�?.

Hajja Nana kuwa sheƙeƙe ta dubi Khausar tace.
“Insaki aiki kice baki iya ba?�?.
Baki Khausar ta tura tare da riƙe ƙugu tace.
“To ban iya ba ya za'ayi na iya ni Wallahi ba zanyi ba taya ma nasan zan iya riƙe dutsen nan nace zanyi markaɗe kije ki kirɓasa aturmi mana kawai�?.

Haɓa Hajja Nana ta riƙe cike da mamaki tace.
“Ni kike cewa Inje in kirɓa aturmi Meye amfaninki Kai Allah wadaran naka ya lalace ke kam ba irin Addarki ba sam�?.

Ita kuwa khausar hannunta ta harɗe aƙirji Idanunta tsaye akan Hajja Nana tace.
“Toh yanzu tunda kinsan Ni ba irin Addah bace sai kiyi min hakuri Addah na agabanki ta girma duk wani horonki ta iya Ni Kuma ba agaban ki na girma ba, kuma ban iya ba ya za'ayi kice min haka wata ƙil ma bakya tuna ta kiyi mata addu'a sai in magana irin haka aya tashi kike tunata�?.

Dafe ƙirji Hajja Nana tayi da faɗin.
“La'ilah ha ilallahu Muhammadu Rasulullah (S.A.W) Khausar ni zaki nunawa son Nanne?�?.
Ita dai Khausar na riƙe da ƙugu sannan tace baza tayi markaɗe akan dutse ba.

Suna nan atsaye haka Baffa Umaru ya shigo ganinsu tsaye ahaka yasa yace da Khausar.
“Lafiya kuwa�?.
Fuskarta babu walwala tace.
“Wai Hajja Nana ce saina yi mata markaɗe akan dutse Ni kuma ban iya ba�?.
Baffa Umaru kuwa juyawa yayi ya sake kallon Hajja Nana yaga sai wurgawa Khausar Harara take Kallonsa ya mayar kan Khausar yace.
“Ayyah Khausar ki gwada mana ba aikin mata bane�?.
Da sauri tace.
“Toh ban iya ba Baffa Umaru taya zan gwada�?.

Hannunta ya riƙe tare da faɗin.
“Zo in koya miki�?.
Ba musu ta matsa kusa dashi ɗan dutsen ya ɗauka ya kafa sannan ya matso da roban waken ya ɗibi wake cikin hannunsa yace.
“Ki markaɗa�?.
Ta gyaɗa masa kai sannan ta fara Markaɗawa ga mamakinta sai taga yana markakaɗuwa har tayi niyyan zagewa ta markaɗa sai ta fasa ta fara jefar da ɗaɗɗaya tasan muddin tayi mai kyau Hajja Nana zata mayar dashi aikinta baya ga haka kuma daga riƙe dutsen yatsun hannunta sun sage tun lokacin data faɗo daga bishiya agidansu Moddibo hannunta bai dawo dai-dai ba.

Ganin tana jefer da waken da guda-guda yasa Hajja Nana cewa.
“Hegiya gantalelliya kibar min abuna�?.
Ta ƙarashe maganar tare da amsar dutsen tashiga markaɗawa.
Miƙewa Khausar tayi tare da kaɗe hannunta tace.
“Yafi Nono fari�?.
Shi dai Baffa Umaru murmushi yayi tare da yiwa Hajja Nana sallama ya tafi,
Ita kuwa Khausar saurin bin bayansa tayi suka tafi adai-dai ƙofar gidan Malam Liman suka tsaya tagaishesa cike da ladabi.
Sannan suka cigaba da tafiya suna taɓa hira har suka isa gidansa.
Adda Adama na ganinta ta sakar mata murmushi tare da faɗin.
“Khausar sannu da zuwa ya gida ya gajiyarku na jiya?�?.

Murmushi tayi da faɗin.
“Ba gajiya Adda Adama ya Aiki�?.
Ta amsa da.
“Alhamdulillah.
Kana tace.
“Ke kam tunda kika zo baki taɓa zuwa kin kwana mana ba�?.

Khausar na gyara zama tace.
“Insha Allah yau zan zo mukwana�?.
Murmushi Adda Adam tayi da faɗin.
“Aikam Nagode�?.
Khausar ta juya tare da kallon Baffa Umaru dake sakin murmushi tace.
“Amma fa ki faɗawa jarumin mijinki ya kawo min abu mai daɗi�?.
Murmushi kana tace.
“Inde wannan ne baki da matsala�?.
Bayan sun gama hira tayi musu sallama ta tafi.

Da daddare bayan sun idar da Sallah Isha'i Khausar tace da Dije.
“Muje gidan Garkuwan Rugarku mu kwana�?.
Dije tace.
“Toh muje�?.
Sannan ta miƙe suka shiga ɗaki sukayi wa Goggo Nanne sallama.
Adda Amada dake ɗaki tana jin Sallamar su ta fito fuskarta ɗauke da murmushi tana cewa.
“Ai yanzu nake cewa zanbi sawunku�?.

Khausar tayi murmushi tace.
“To aigamu ina Jarumin mijin naki?�?.

“Yana nan mai zaki bashi?�?.

“Babu abinda zan bashi abin daɗi da yace zai ajiye min zai bani idan kuma babu in tattara in tafi�?.
Ta Ida maganar tana murmushi.

Miƙewa Adda Adama tayi tace.
“Toh ki kwantar da hankali ga abin daɗi�?.
Tayi maganar tana ajiye musu karamin kwandon kaba dake ɗauke da Inabi, Tuffa, Mangoro, Ruman, da sauran kayan itatuwa sai kuma kwanon farfesun kifi yana tururi.

Murmushi mai sauti Khausar tayi tace.
“Lallai yana yina ashe wannan gara haka�?.
Ita dai Dije murmushi kawai take musu.
Duka suka haɗu suka ci sannan suka kwanta ɗaki ɗaya da Adama.

Shiko Baffa Umaru yana can aɗakinsa ya kwana.

Misalin ƙarfe biyu na dare Khausar ta farka aɗan firgice sakamakon hayaniya da take jiyowa.

Dije ta gani itama zaune tana zazzare idanu ganin sukayi Adda Adama ta fice aɗakin da mugun sauri suma cikin sauri suka bi bayanta.
Da gudu Adam ta nufi ɗakin mijinta dai-dai lokacin daya fito.

Hannunsa ta riƙe cikin raunin murya tace.
“Dan Allah kada ka fita da alama suna da yawa kaji hayaniyar su�?.

Da sauri ya juya ya kalleta tare da faɗin.
“Idan ban fita ba wa zai dakatar da su wannan daga ji mutanen Ƙauyen Garinga ne bamusan mai suka zo dashi ba dare dare zasu zo mana haka babu yanda za'ayi dole in fita�?.

Ta girgiza kai tare da riƙe sa kana tace.
“Dan Allah kada ka fita".
Tureta yayi daga jikinsa ya fita yana fita ya hango Arnan mutanen Garinga ne wanda yawansu zai kai kimanin mutum ɗari da sauri ya nufi hanyar jejin yayin da bayansa ke rataye da kwari da baka hannunsa na riƙe da touch light mai masifar haske.
Cikin fushi da tsawa ya haskasu da touch light ɗin hannunsa mai masifar kashe ido yace.
“Menene wai ma tukun ina kuka nufa!?�?.

Ɗaya daga cikinsu wanda ya kasance babban su yace.
“Ƴar mu muke nema ta ɓata�?.
Duk da acikin duhu ne hakan bai hana shi watsa musu kallon banza ba yace.
“Ƴarku ta ɓata shine dare-dare haka zaku zo wajenmu nemanta?�?.
Biyu Daga cikin su suka ce.
“Ai kidnapping ɗinta akayi�?.

Afusace yace.
“Kuma in kidnapping ɗinta akayi sai akace muku tana nan Rugarnu?�?.
Babban cikinsu yace.
“Tana nan Rugarku dama Fulanin ku ai sune suka sace ta suka kawota dan haka an saceta tana nan mu nan muke zargi�?.

Cikin tsananin fushi da zuciya Baffa Umaru yace.
“Baku isa ba babu yanda za'ayi haka ya faru!�?.
Babban cikinsu yace.
“Dole sai mun shiga garinku gida-gida ɗaki-ɗaki mun bincika�?.

Cikin tsananin fusata Baffa Umaru yace.
“Wallahi in dai ina raye baku isa ba babu wanda ya isa yashiga garinmu yace yayi bin cike indai haka kuke so kuje kuzo da rana muyi magana�?.

Babban su yace.
“Mu adaren nan muke so muyi magana�?.
Baffa Umaru yace.
“Toh baku isa ba�?.
Dumfaro sa sukayi da niyyar shiga Rugar gadan-gadan.
Shi kuwa baya yaja tare da jan kwari da baka yace.
“Duk wanda yake jin shi Jarumi ne kuma ya kai to ya kuskura ya shiga mana cikin Ruga yaga abinda zai faru�?.
Tsayawa su kayi akuma dai-dai lokacin ne sauran mazan cikin Rugar suka fiffito mafi yawa ma sautin Baffa Umaru ne ya tashe su dan shi mutum ne mai zafin gaske musamman ma idan ransa ya ɓaci.
Acan bakin ƙofar gida kuwa sosai Khausar ta shiga mamaki sai asannan ta tabbatar da maganar Adama da tace mijinta Jarumi ne kuma Garkuwan Rugar.

Malam Liman ne yayi gyaran murya bayan isan su wajen yace.
“Tun da kunce haka yanzu ku koma da safe sai kuzo aje wajen Mai gari sai ayi magana�?.

“Toh�?, Babban su yace sannan suka juya suka tafi badan ransu ya soba.

Washe gari da safe bayan sunyi ta tsansu sun daddawo da hantsi Arnan garin Garinga suka zo suka haɗu aƙofar gidan Jauro.
Bayan sun gama gaisawa Jauro ya dubesu Anutse cike da kamala irin na shugaba yace.
“Mai yafaru muna sauraron ku".
Babban su yayi gyaran murya yace.
“Ƴar muce buke ce akayi kidnapping sannan muna zargin tana cikin wannan Rugar�?.
Cikin danne takaicin ƙazafin da arnan ke son yi musu Jauro ya jinjina kai kana yace.
“Kun tabbatar tana cikin wannan Rugar?�?.
Kai Babban su ya jinjina yace.
“Ƙwarai mun tabbatar sannan mun zo zamu shiga Umaru ya hana mu sannan Umaru shi yake sa mana Ido komai akayi bamu isa muyi magana ba sam Bama ƙaunar abinda Umaru yake mana yayi rayuwarsa muyi rayuwar mu!�?.

Wani banzan kallo Baffa Umaru ya watsa musu cikin yanayin zafinsa yace.
“Ba zanyi rayuwata kuyi rayuwarku ba muddin kuna so nayi rayuwata kuyi naku to ku fita sabgarmu banga wanda ya isa ya shigo cikin Rugar mu yace zai taka mu inbar saba�?.
Da sauri Jauro ya ɗaga masa hannu hakan yasa Baffa Umaru yayi shiru.

Baffa Jauro kuwa maida kallonsa garesu yayi kan yace.
“Munji mun yarda an sace muku yarinya anyi Kidnapping ɗinta�?.
Sai kuma ya maida kallonsa kan Malam Liman yace.
“Ɗauko mana Bible agidanka�?.

Kallon Yaya Abba Malam Liman yayi yace.
“Jeka ɗauko min asalin Bible na da acikin littatafai na�?.
Miƙewa Yaya Abba yayi babu daɗewa ya dawo hannunsa riƙe da Bible ɗin ya mikawa Jauro.
Karɓa Jauro yayi tare da miƙawa Babban su yace.
“Gashi ku rantse da littafin ku tunda kuce ƴarku ta ɓata kuma tana garin nan�?.
Ƙin amsa Babban su yayi.
Cikin sanyi Jauro yace.
“Inde ka tabbata ƴarku ta nan to ka karba ka rantse Inde ka rantse.
To mukuma zamu baku damar shiga sannan muma zamu rantse da Alkur'anin mu mai girma cewa ‘yarku bata nan amma duk da haka idan kun rantse zamu baku damar shiga cikin gida-gida ɗaki-ɗaki kuyi bin cike�?.

Shi dai babban nasu kin rantse wa yayi sai wuƙi-wuƙi yakeyi da ido.
Ganin haka yasa Jauro ya kalli sauran na bayansa yace.
“To ɗaya daga cikin ku ya karɓa ya rantse�?.
Still suma ƙin karɓa sukayi.
Afusace Baffa Umaru yace.
“Ba gashi ba basu da gaskiya

1 Comments On SAKAYYA
avatar
hajara-ahmad

1 year ago

Reply

Nice novel

Please Login or Register in order to submit comment