Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cikinta daga sharrin Mai sharri�?.
ta faɗa tare da shafawa Alkur'ani ta ɗauka ta fara Muraja'a tun daga Kahf sai data je Hajj kafin ta tsaya ta miƙe ta ida da Isha'i awajen ta kishingiɗa da haka bacci ya ɗauke ta.

Washe gari juma'a Khausar na zauna afalon Mommy akan Lallausan Capet yayin da Mommy ke saman kujera Khausar na matsa mata ƙafafunta ahankali Khausar ta ɗago kai tare da kallon Mommy da Idanunta ke lumshe tace.
“Mommy wallahi nayi missing Hajja Nana, Baffa Jauro Sadik, Dije duka mutanen Rugar ma nayi kewarsu gashi babu network bare nakira naji Muryansa�?.

Murmushi Mommy tayi tare da jan numfashi kana ta buɗe Idanunta dake lumshe tace.
“Lalle kam Khausar yau kece ke faɗin Kinyi kewar Hajja Nana da bakin ki?�?.

Murmushi Khausar tayi wanda ya lotsar da dimple ɗin ta kana tana cigaba da yiwa Mommy massaging ƙafafunta tace.
“Allah tana da daɗin zama kawai dai faɗanta da kuma mulkin mallaka da take nunawa yasa bamu jituwa amma tanason Babana da yawa sannan tana masa addu'a ni kuwa kinga duk mai yiwa Babana addu'a ina ƙaunarsa�?.
Ta ƙarashe tare da buɗe Idanunta dake lumshe wanda ruwan hawaye ya cika su.
Shafa kanta Mommy tayi tare tace.
“Ubangiji Allah yajiƙan sa da rahma Allah ya gafarta masa Ubangiji ya jiƙan dukkan musulman da suka rigamu gidan gaskiya�?.
Sanyayyar Ajiyar zuciya me haɗe da kyewa Khausar ta saki kana ahankali ta furta.
“Ameen�?.
Mommy tace.
“Sai ki shirya idan kunyi wani hutun kije ki gansu�?.
Wara ido Khausar tayi tare da gyara zamanta kana fuskarta ɗauke da murmushi tace.
“Ai lalle kam�?.
Sai kuma tayi saurin juyawa jin Muryan Asma'u na sallama.

Ƙarasawa Falon Asma'u tayi tare da zama daga gefen hagun Khausar ta ajiye Handbag dake hannunta ta shiga Matsawa Mommy ƙafanta na hagu da faɗin.
“Mommy ina kwana yasu Raudat?�?.
Hannu Mommy ta sanya ta shafa kanta da faɗin.
“Lafiya lau Asma'u ya gida yasu Umminki?�?.
Asma'u na cigaba da Matsawa Mommy ƙafanta tace.
“Tana lafiya tace na gaisheki�?.
Mommy tace.
“Ina amsawa�?.

Ita kuwa khausar kallon Asma'u tayi tace.
“Sannu da zuwa taso mu shiga ciki�?.
Kai Asma'u ta gyaɗa sannan ta miƙe ta ɗauki Handbag ɗin ta suka shiga.
Zama tayi agefen gadon Idanunta akan Khausar data buɗe ƙaramin fridge ta ɗebo mata kayan marmari tace.
“Anbani saƙon gaisuwa in kawo miki�?.

Ajiye ƙaramin Plate ɗin Khausar tayi tare da zama tace.
“Toh ina Amsawa wani bawan Allah ne?�?.
Da sauri Asma'u ta ƙumshe dariyar dake cikinta kana tace.
“Moddibo ne yace agaisheki da hannu�?.
Zare idanu Khausar tayi lokaci ɗaya ta ƙware da Inabi dake bakinta da dugu ta miƙe ta nufi fridge ta ɓude Goran Swan water ta ɓude ta kafa abakinta saida tasha fiye da rabi kafin ta janye roban daga bakinta tana maida numfashi.

Asma'u kuwa kasa riƙe dariyar ta tayi cikin dariya sosai tace.
“Me haka Khausar daga jin sunan Moddibo zaki wani ruɗe haka?,sai kace wani abin tsoro!?�?.
Zama Khausar tayi tana maida numfashi tace.
“Wallahi mutumin nan ya wuce inda kike tunani yanda kika san bashida zuciya aƙirjinsa baya jin bada haƙuri fa�?.
Ta ida maganar tare da jan siririn tsaki tana tuno fuskar Moddibo lokacin da take bashi haƙuri.

Asma'u ta katse shirun tare da buɗe Handbag ɗin ta ta ciro takardan Economics da Mi'atu Hadith da sauran darasin da sukayi ta miƙa mata tace.
“Gashi ki kwafa sannan kiyi karatu akai�?.
Amsa Khausar tayi tare da budewa tace.
“Toh shikenan ba matsala zan duba�?.
Bayan sun sake taɓa hira Asma'u tace.
“Zan tafi�?.
Khausar tace.
“Tun yanzu?�?.
Hararanta Asma'u tayi tayi tace.
“Eyyyyy lalle kam aigwara ni dakeke sai ki kusan shekara bakije gidanmu ba�?.
Tana gama Fadar haka ta Miƙe ta fita.
Dariya Khausar tayi tare da sanya Blue Black ɗin hijabinta ta fice afalon ta samu Asma'u nayiwa Mommy Sallama bayanta tabi suka fice.

Washe gari ta kama ranar.
Asabar Hajiya Bunayya da Hajiya Lami ce acikin mota, suka nufi unguwar shamaƙi, yayin da Hajiya Bunayya ke tuƙi suna sauraron wakar Nazeer Sarkin Waƙa mai taken Bamu babu ku,kuma baku babu mu.
Cike da nishaɗi Hajiya Lami tace.
“Hajiya Bunayya Matsalar mu tazo ƙarshe da zaran munje wajen wannan mutumin komai yazo ƙarshe dan ina da tabbacin aikinsa�?.
Dariya Hajiya Bunayya ta sheƙe dashi tare da buga stairing motar tace.
“Kedai bari nayi al'ƙawari saina tarwatsa wannan matar�?.
Da wannan hiran suka isa unguwar daga can bakin hanya sukayi parking motarsu.

Kana suka ɗanyi tafiyar ƙafa kaɗan suka tsallaka titin, suka nufi wani ƙaton kango mai zagaye da dogon katanga da duhuwar bishiyoyi,
da baya-baya suka fara shiga cikin wajen da manyan bishiyoyin Tsamiya dana kuka suka masa ƙawanya sai kuma wasu manyan bishiyoyi irin na Ceɗiya masu masifar tsawo da duhu kana sai wani ƙaramin bukka daya kasance Atsakiyar bishiyoyin,
jikin bukkar ke waye yake da jajayen ƙyalle da wasu irin ƙwarya masu masifar munin gani ajikin ƙwaryan akwai kuratandu sai kuma wasu baƙaƙen ƙaho masu siffar fuskan bil Adam.
Daga nesa suka ajiye takalmansu kana suka cigaba da tafiya da baya har suka shiga cikin gidan da ƙafar hagu yayinda wani masifaffen ɗoyi ya cika gidan baki daya ya mamaye ilahirin gidan.

Cikin ɗaga sautin murya suka haɗa baki wajen faɗin".
“An gaida Boka Kar'uzu uban bokaye angaida la'anannen Uban la'anannu mugu uban mugaye
Hatsabibi uban hatsabibai�?.
Daga ciki kuwa wata daskararriyar murya mai firgitarwa mara daɗin saurara yace.
“Kushigo da baya-baya kana ku tabbata ƙafar hagu zaku riƙa takawa har ku iso gareni�?.

Cikin tsinkewar zuciya da matsanancin tsoron kada su saɓa masa doka cike da biyayya suka gyaɗa masa kai tare da ƙara sawa kusa dashi suka zauna suna maida numfashi.
Cikin daskararriyar muryarsa mara daɗin sauraro yace.
“Ku tashi anan suna zaune zaku danne ɗan ƙundalo mai ido agoshi! Maza ku koma ta gefen hagu bana ƙaunar ganin ku.
A dama saboda ba aikin dama zamu yiba�?.

Tsaban tsoro saidai Hajiya Bunayya ta dungura tare da kurje hannunta kana jikinsu na rawa suka koma gefen hagunsa.
Kallon Hajiya Bunayya yayi ya kece da wata mahaukaciyar dariya me tsananin razanarwa, ya nunata da wani mummunan yatsansa da farce yayi tsawo kana yace.
“Kin makara cikinta har ya kusa wata uku amma zamu jijjigesa da ƙarfin ikon mu zamu fito dashi!�?.
Ita kuwa Hajiya Bunayya Atake taji tsoron ta ya tafi ta washe baki da faɗin.
“Laaa Malam kasan abinda ke tafe dani?�?.

Cikin fushi yace.
“Sunana ba Malam ba Kur'ani kika gani agabana ko hadisai da za ki kirani da Malam ki kirani da Boka Kar'uzu uban bokaye La'anannen uban la'anannu Mugu Uban Mugaye�?.

Ƙasa da kai tayi tana cewa.
“Tuba nake Boka Kar'uzu bazan sake ba�?.
Kai ya gyaɗa mata yace.
“Sai kuma batun Jameel da ’yarki Amina�?
Cikin rawan jiki tace.
“Eh boka Kar'uzu�?.

Ya kece da wata mahaukaciyar dariya yace.
“Ai ƙaddarar abai-bai take,Ai ƙaddarar abai-bai take, ƙaddarar abai-bai take!�?.
Ita kuwa Hajiya Lami cikin zaƙuwa take gyaɗa kai.
Hajiya Bunayya tace.
“Boka kamar ya ƙaddara abai-bai take ban fahimta ba�?.
Yace.
“Babu damuwa za'ayi Miki aiki�?.
Hajiya Lami ta gyara zama sosai tace.
“Toh Boka Kar'uzu ni ya batun ‘yata?�?.

Ya sake kecewa da wata mahaukaciyar dariya yace.
“Aike batun ki mai sauƙi ne shi wannan babu wata Aransa shi wannan dakike gani yana nan kamar Waliyi ne, koko ince katako, sai dai fa akwai ganye bishiya da yake tsirowa ajikinsa har ta fara jijiya ajikinsa tana gab da zuba rassuna�?.

Hajiya Lami tace.
“Boka koma wani irin ganye ne Indai bana Samira bace atun ɓukesa�?.
Kai ya gyaɗa kana yace.
“Angama angama�?.
Cikin jin dadi ta juya ta kalli Hajiya Bunayya tana sakar mata da murmushi alamar da akwai Nasara.
Sai kuma ta juya ta kalli Boka Kar'uzu tace.
“Ya batun abubuwan aiki?�?.

A tsawace boka Kar'uzu yace.
“Zaku kawo Fararen Bunsuraye guda uku, Da baƙaken karnuka guda biyu da baƙar kaza mai bungi-bungi guda ɗaya na batun aikin zubar da ciki.
Batun Jameel kuwa zaki kawo gurguwar jaka mace sannan ki samu makauniyar tinkiya me watanni bakwai sai kuma agwagwa fara mai ƙafa ɗaya�?.
Zare Idanu sukayi Atsorace jin abubuwan da ake buƙata.
Ya cigaba da cewa.
“Batun aikin Moddibo kuwa zaku kawo Gurguwar shanu ja mai Ido ɗaya da kuma namijin doki fari soll wanda aka haifesa acikin gida sai kuma ku samo Alade guda biyu mace dana miji�?.

Cikin tashin hankali da damuwa Hajiya Lami tace.
“Boka a ina zamu iya samo wa'annan abubuwan aise kai saidai mu bayar asamo�?.
Yace.
“Toh ku ajiye kuɗin masu tarin yawa�?.
Cikin rawan jiki Hajiya Bunayya tasa hannu a jakarta ta ciro kuɗi wanda batasan adadin suba ta ajiye masa�?.
Kallon kuɗin yayi yace.
“Kuje bayan sati biyu kuzo ku karɓi kayan aikinku sha yanzu magani yanzu�?.
Godiya suka masa kana suka tashi suka fita kamar yanda suka shigo.

Acan ɓangaren su Khausar kuwa karatu suke sosai babu kama ƙafar yaro sabbin Malamai da aka kawo musu sun zage damtse wajen koyar da ɗalibai ga kuma sabbin ɗalibai da ake shigowa dasu saboda yanda aka tsara Makarantar sosai makarantar ya sake samun ɗaukaka fiye da farko ga kuma shirye-shiryen musabaƙa da akeyi na Jahar Taraba baki ɗaya Khausar da Asma'u sun sake dagewa.

Bayan sati biyu Hajiya Bunayya da Hajiya Lami ce zaune agaban Boka Kar'uzu.
Wani ƙullin magani ya ɗauka tare da kallon Hajiya Bunayya ya miƙa mata kana yace.
“Wannan ki dafa shi da farfesun kayan ciki ki bawa Hajiya Aysha tana ciki, sunan cikinta anyi angama saide wani cikin bashi ba!.
Sannan idan kin shirya kizo za'a zazzage mata mahaifa asa mata ajiya yanda baza ta sake ɗaukar wani cikin ba, sannan kuma mijinta zai tsaneta ba zai sake sha'awar kusantar taba!�?.
Murmushin samun nasara Hajiya Bunayya tayi tace.
“Boka Indai cikin nan ya zube zan dawo akan aikin amma yanzu burina cikin ya zube sannan ajawo hankalin Jameel kan Amina�?.

Wata mahaukaciyar dariya Boka Kar'uzu ya sheƙe dashi yace.
“Ga wannan�?.
Hannu bibbiyu Hajiya Bunayya tasa amshi ƙullin maganin tana jujjuyawa yace.
“Ki bawa ‘Yarki Amina tayi wanka dashi sannan tayi hayaƙi idan zatayi hayaƙin ta ɗago kaskon ta kawo bakinta ta riƙa kiran Jameel!, Jameel!!, Jameel!!! na tsawon kwanaki uku sannan ta tsallake kwana uku ta sake na kwana uku na sannan ta sake kwana uku ta tsallake kwana uku sannan ta sake kwana uku kuma ko wanne idan tazo hayaƙin sai takai kaskon bakinta ta kira sunansa kada ku yarda asamu kuskure dan in an fa samu kuskure abun bazaiyi kyau ba�?.

Kallon Hajiya Lami Hajiya Bunayya tayi tare da jinjina mata hannu tana murmushi cikin ƙasa da murya tace.
“Alhamdulillah nakusa ganin ƙarshen wannan matsiyatan�?.
Martanin Murmushin Hajiya Lami ta mata itama ranta fess burinsu ya kusa cika.
Tunda Boka Kar'uzu yace.
“Muddin tayi na tsawon wannan kwanakin shida kansa zai kawo kansa gareta idan kuma wannan baiyi ba akwai wanda zamu sakeyi saidai shi wannan kankat ne amma shi sai farkon damuna tukunna zamu samu ayishi�?.
Cike da farin ciki Hajiya Bunayya tace.
“Boka Kar'uzu Uban bokaye Insha Allahu ma nasan wannan aikin zaici�?.
Cikin wata razananniyar tsawa yace.
“Oho Ni dai nace kada ki sake kiramin sunan Allah anan domin da kina jin tsoronsa ba zaki zo nanba bare har kinemi aikata mugun abu akan wani idan kuma kina son aikin ki ya ɓaci ki sake kiran Allah anan�?.

Cikin rawan baki da tsoron kada aikinta yaƙi ci tace.
“Tuba nake Boka Kar'uzu Uban bokaye La'anannen Uban La'anannu Mugu Uban mugaye da ikon ka wannan aiki zaici�?.

Ya sheƙe da wata mahaukaciyar dariya mai kama da sautin ƙaran lalataccen Injin Markaɗe yace.
“Yanzu ne aikin ki zaiyi yanzu ne kika yi magana mai ma'ana�?.
Ta saki ajiyar zuciya cike da farin ciki.

Hajiya Lami ta matso kusa tare da gyara zama sosai tana fuskantar Boka tace.
“Ni kuma ya maganar ’yata?�?.
Wani irin kallo ya mata kana yace.
“Na ‘yarki sai anyi babban shiri domin wannan da kike gani shida saƙago basu da banbanci baya kallon mace ako wani irin mataki daya wuce ɗaliba ya karantar da ita ya kuma bata ilimi da tarbiyya shi koda mace zata wuce tsirara agabansa babu abinda zai damesa da ita tamkar zuciyar dutse ne aƙirjinsa!�?.

Ta gumi Hajiya Lami tayi tare da faɗin.
“Ikon Allah aƙasan ranta�?.
Boka Kar'uzu ya cigaba da cewa.
“Sai munyi mata shiri sosai yanda lokaci ɗaya zata jawo hankalin sa gareta sai bayan wata biyu zaki zo ki karɓi haɗin da muke tsuma shi sannan tayi kokari ta bashi yaci daya ci aiki ya gama�?.
Ajiyar zuciya Hajiya Lami ta saki tace.
“Da ƙarfin ikon ka zamuyi hakan boka�?.
Ya kece da wata mahaukaciyar dare yace.
“Na gama daku zaku iya tafiya�?.
Miƙewa sukayi suka ce. “Godiya muke Boka Kar'uzu Uban bokaye La'anannen Uban La'anannu Mugu Uban mugaye�?.
Shikuwa Dariya ya kece dashi yana jin daɗin kirarin da ake masa kamar yanda suka saba shiga haka suka fita da baya.

Cikin tsananin farin ciki Amina ke kallon Hajiya Bunayya dake mata bayani karɓan maganin tayi tare da rungume Hajiya Bunayya tace.
“Nagode Umma�?.
Ƙullin maganin ta karɓa sannan ta shiga ban ɗaki tayi wanka dashi tana fitowa Hajiya Bunayya ta kawo mata wuta akasko ta bata zama Amina tayi tare da kai saitin kaskon bakinta tace.
“Jameel!, Jameel!!, Jameel!!!�?.
Ta faɗa da ƙarfi yayin da hayaƙin ke bin ilahirin jikinta kallon Hajiya Bunayya tayi cikin jin daɗi tace.
“Umma M Jameel ya Kusa zama mallakina?�?.
Dariya Hajiya Bunayya tayi tace.
“Ƙwarai kuwa?�?.
Asiya ce tashigo falon da Sallama da sauri ta toshe hancinta jin wani masifaffen wari da ƙauri tayi saurin kallon ƙofar Bedroom ɗin Hajiya Bunayya inda nan take jin wari da ƙaurin ke fita.
Tana ƙoƙarin shiga Hajiya Bunayya ta fito Kallonta Asiya tayi tace.
“Ummah warin meke fita daga ɗakinki?�?.

Harara Hajiya Bunayya ta watsa mata tace.
“Warin lafiya ko kuma ke ki kafi kowa hanci?�?.
Girgiza kai Asiya tayi tace.
“Wallahi Ummah da gaske akwai..�?.
Tsawa Hajiya Bunayya ta buga mata da faɗin.
“Ki wuce kibani waje sakaryar banza mara tunani�?.
Ahankali Asiya tace.
“Allah yabaki haƙuri Ummah�?.
Kana ta juya cikin mutuwar jiki ta nufi ɗakinta.

Bayan wata ɗaya:
Amina ta gama amfani da duk maganin da Hajiya Bunayya ta karɓo mata awajen Boka Kar'uzu cike da farin ciki ta dubi Hajiya Bunayya asanda take sanya uniform ɗinta tace.
“Ummah na matsu na isa Makaranta inga irin tarban da Jameel zai min!�?.
Murmushi Hajiya Bunayya tayi da faɗin.
“Kede ki kama kanki karki bari ya gane kina sonshi ya rainaki dan yanzu sai yanda mukayi dashi�?.
Asiya data fito daga kichen hannunta riƙe da Cup ɗin tea dake tururi ta zauna akan ɗaya daga cikin kujerun falon Idanunta akan Amina tace.
“Amina ki maida hankali akan karatunki kada kice zakiyi wasa da damarki komai da kika gani arayuwa muƙaddari ne daga Ubangiji�?.
Cikin tsawa Hajiya Bunayya tace.
“Asiya zanci Ubanki fa idan baki fita sabgar Amina ba shegiyar yarinya me baƙin halin tsiya.
Niko anya ma ba canza min ke akayi ba, dan wallahi badan kamannin dake tsakanin mu ba sai ince sauya min ke akayi�?.

Miƙewa Asiya tayi tace.
“Allah ya baki haƙuri Umma amma ita gaskiya ɗaya ce�?.
Harara Amina ta watsa mata tace.
“Ke har wani gaskiya ce dake to ki riƙe gaskiyar ki bama bukata�?.
tana gama fadar haka ta fice.

Atare suka fito da Khausar dake riƙe da hannun Raudat kallo ɗaya Khausar ta mata ta kawar da kanta gefe,
Ita kuwa Amina murmushi mai cike da ma'anoni ta sakarwa Khausar sannan tashiga motar yayin da Khausar tabi bayan ta suka shiga sannan driver yaja motar suka tafi.

Motar na tsayawa kowa ya nufi ajinsu kamar kullum saida Khausar takai Raudat ajinsu kafin ta wuce ajinsu.
Aɓangaren Amina kuwa kai tsaye ajinsu ta nufa tare da zama tana sakin murmushi duk da Amina da Khausar

Shigansu baa daɗewa M Jameel ya shigo ajin cikin wata farar gezner me kyau yayin da kansa ke sanye da baƙin hula gashinsa ya fito ta ƙeya ƙafarsa sanye da sau ciki baƙi jikinsa na fitar da sanyayyan ƙamshi Amina kuwa ta gumi tayi tare da zu bawa sajensa zuwa gemunsa idanu tana mai furta.
“Wowww�?.
Shi kuwa M Jameel hankalinsa ya mayar kan Black Board.
Cikin karya murya tare da lanƙwasa harshe Amina tace.
“Malam Barka da safiya�?.
Anutse M Jameel ya juya ya kalleta cikin sauri ya runtse Idanunsa da ƙarfin gaske.
Sai kuma ya sake buɗewa akan fuskarta still da sauri ya sake runtse Idanunsa yana mai furta.
“Hasbunallahu wani'imal wakil.
Astagfirullah wa'atubu ilaik�?.
Ita kuwa Amina cike da ƙissa ta sake karya harshe tana juya Idanunta tace.
“Malam ina kwana�?.

Shi kuwa M Jameel Batare daya juya ya kalleta ba ya ɗaga mata hannu, domin tun sanda ya kalli fuskarta sau ɗaya yaga kamar an ƙona fuskar Biri, sosai ta masa muni tunda yake kallon fuskar yarinyar bai taɓa ganin tayi masa muni irin na yau ba, baki ɗaya fuskarta babu haske bare annuri Kawar da kansa yayi ya cigaba da koyar wansa batare daya yarda ya sake kollon inda take ba har yagama ya fita.
Ita kuwa Amina bata kawo komai aranta ba domin atunaninta maganin ne ya fara aiki.

Acan ajinsu Khausar kuwa Moddibo ne tsaye jikin Black Board Ya rubuta Geography ajiki,
Da alama shine subject ɗin da zai riƙa ɗaukansu.
Jikinsa sanye da Jallabiya Coffee color yayin da kansa ke naɗe da hirami siririn sajensa zuwa gemunsa yasha gyara sai sheƙi yake jikinsa na fitar da sanyayyan ƙamshi tularen Oud.
Cikin nutsuwa da kuma sanyin Muryansa ya gyara tsayuwar sa tare da harɗe hannayensa aƙirji kana ya ɗan lumshe idanunsa kafin yace.
“Class What is Geogry?�?.
ya ƙare tambayar cikin tsananin tsuke fuska da tsare hirar samata ƙasa, sabida yanayin dariasin in yayi garaje yara zasu rainasa, Allah ya sani ba ƙaunar darasin yakeba sabida yanayin abubuwan dake ƙunshe a ciki masu cin karo da addini.
Shiru class din yayi ba wanda yayi magana sabida yadda baya kallon idonsu haka suna kan suke shayin koda motsi bare Kallonsa.
Khausar da Idanunta ke lumshe ta buɗe tare da zaro harshe ta ɗan lashi lips ɗin ta sai kuma ahankali ta ɗaga siririn hannunta dake maƙale da zoben azurfa da kuma Gold.
Shi kuwa Moddibo ahankali ya maida da idanunsa zuwa ta inda take.
Kana tsare sashin da taken yayi da ido amman ba fuskantar yake kalloba, ƙara tsuke fuska yayi tare da sa hannunsa ya shafa yalwataccen sajen dake fuskarsa kana ya mata alamun ta tashi.
Cikin nutsuwa tare da taka tsan-tsan akan gudun lefin da zatayi ta motsa lips ɗin ta da yayi pich saboda man baki data shafa kana ta lumshe Idanunta tace.
“Geography can be defined as the discription of the Earth�?.
Jinjina kai Moddibo yayi tare da faɗin.
“Dayyit, sit-down�?.
Kai ta gyaɗa tare da zama.

Ahankali ya motsa lips ɗinsa da faɗin.
"Yah Salam". Yayi mgnar yadda ba mai jinshi.
gajeren tsaki, Samira Sani taja dan ji tayi kamar ta haɗiyi zuciya ta mutu saboda baƙin ciki taso ace itace zatayi wannan karatun
Shikuwa Moddibo kallon Khausar yayi tare da yimata alamar tazo cikin sauri ta miƙe ta isa gabansa, ba tare da yace mata komai baya miƙa mata hannunsa.

Kallon tattausan farin tafin hannunsa dake ɗauke da zara-zaran yatsu da ga wasu zoben azurfa fari da baki daya ƙawata yatsun.
Cikin rawan murya tace.
“Malam mai zanyi?�?.
Ya mutsa fuska yayi tare da watsa mata harara daya sa ‘ya‘yan hanjinta kaɗawa da ido ya nuna mata zobunan hannunta.
Cikin rawan jiki ta cire ta basa lokaci ɗaya Idanunta suka sauya launi sosai take masifar son zoben ɗaya Mommy tace ta bata ɗaya kuma Hajja Nana ce ta bata ta kuma shaida mata tun na babantane na azurfan.
Saida ta koma ta zauna yace.
“Nasha faɗa muku cewa nan ba wajen ado bane idan kowa yace zaiyi ado yazo ai wasu ma baza agansu ba�?.
Ya ida maganar tare da juyawa ya cigaba da koyar musu cike da ƙwarewa tare da kare ƙa'idar musulunci gudun dulmuyar tunanin ɗalibai.

Bayan kwana uku baki daya Amina tashiga damuwa da tashin hankali koda ta gaida M Jameel baya Amsawa sai dai ya ɗaga mata hannu, gwara ma da yana kallonta Sannan wataran yakan mata murmushi amma yanzu koda kallonta baya ƙaunar yi.
Bayan antashi tana komawa gida.

Kai tsaye Bedroom din Hajiya Bunayya ta nufa.
Zaune ta samu Hajiya Bunayya riƙe da kofin tea mai ɗumi ahannunta.
Zama tayi agefen Hajiya Bunayya cikin raunin murya tace.
“Ummah tunda fa nagama aiki da maganin M Jameel Koda kallona ne baya ƙaunaryi, ko gaishesa nayi saidai ya ɗaga min hannun!�?.
Da Mamaki Hajiya Bunayya tace.
“Ikon Allah to ya zama dole inshirya na koma gidan Boka Kar'uzu inji me yesa�?.
Gyaɗa kai Amina tayi tace.
“Gaskiya ya kamata dai Ummah".

Hajiya Bunayya tace.
“Gashi nima yau nakeso in fara na wannan matsiyaciyar matar dan nafi so dama sai kin gama naki sai in dafa in bata�?.
Amina tace.
“Ya kamata dai kam yazo tana ta cika mana gida da yara�?.
Ita kuwa Hajiya Bunayya miƙewa tayi da kanta ta shiga kichen ta buɗe fridge ta ɗauko kayan ciki ta haɗa masa kayan ƙamshi da kayan hadi Sosai sai tashin ƙamshi yake.
Warmers ta ɗauka ta juye kana ta dauko ƙullin maganin da boka Kar'uzu ya bata ta barbaɗa akai sannan ta ɗauka ta nufi sashen Hajiya Aysha dashi.
Mommy na zaune afalo ta miƙe ƙafafunta ta jiyo Sallamar Hajiya Bunayya murmushi tayi tare da tace.
“Yaya kece da kanki sannu da zuwa�?.

Murmushi Hajiya Bunayya tayi tace.
“Wallahi kuwa kinga Perpesoup nayi na kayan ciki, nasan kuma kina so, shiyasa nace nari na kawo miki, idan kinsha da dan ruwan Tea mai ɗumi zakaji daɗi asanyin da ake�?.
Murmushi Mommy tayi tace.
“Aikuwa Nagode yanzu nake tunanin tashi in dafa ko indomie ne naci dan na gagara cin tuwon".
Murmushi Hajiya Bunayya tayi tace.
“Ayyah ƙanwata to ga wannan sai kisha ai zakiji daɗinsa�?.

Acan ɗaki kuwa Khausar ce tsaye jikin wodurobe tana gyara kayansu da Raudat ta burkitasu.

Siririn tsaki ta saki tare da kallon tulin kayansu dake burkice kamar basu taɓa ganin ninkiba bare guga stool taja ta zauna tana ninke kayan.

Acan falo kuwa yunƙurawa Mommy tayi da faɗin.
“Bari na ɗauko Plate".
Da sauri Hajiya Bunayya ta mike tare da cewa.
“A'a bari na ɗauko Miki�?.
Ta Faɗa tare da shiga kichen ɗin.
Ita kuwa Mommy murmushi tayi aranta tana jinjinawa ƙaunar da Hajiya Bunayya ke nuna mata tabbas samun irinta acikin kishiyoyi sai antona.
Hajiya Bunayya kuwa nashiga kichen ta fashe da dariya mai ɗan sauti tace.
“Shegiyar mata zaki ci Ubanki atunaninki har ƙasan raina nake sonki�?.
Sai kuma ta sake tun tsirewa da wata dariya mai sauti can ƙasa, kana ta ɗauki cup ta zuba mata Tea kana ta ɗauki Plate da spoon ta fita.
Miƙa wa Mommy plate ɗin tayi tare sa faɗin.
“Naga kamar kwana biyu bakyajin daɗi�?.
Ya mutse fuska Mommy tayi kana tace.
“Wallahi kuwa gaba ɗaya bana jin daɗin jikina wannan karon kuma da laulayi sosai yazo min�?.
Cike da tausayawa Hajiya Bunayya tace.
“Ayyah sannu Ubangiji Allah ya inganta�?.
Aranta kuwa cewa tayi Allah ya tarwatsa matsiyaciya.
Ita ko Mommy tace.
“Ameen ya Allah�?.

Miƙewa Hajiya Bunayya tayi tare da ɗaukan Plate din ta ɓude perpesoup ɗin dake tururi yana tashin ƙamshi ta zubawa Mommy tare da miƙa mata da kofin shayin.
Lumshe idanu tayi sosai ƙamshin ya bugeta, a take yawunta ya tsinke abinka da mai cike lokaci ɗaya taji ranta yabiya da Perpesoup ɗin hannu tasa ta amsa tare da ajiye plate ɗin bisa cinyarta kana tasa spoon ɗin da sauri ta ɗebo sokar hanta da rokon ta perpesoup ɗin takai bakinta.....!


*GARKUWAR* taku ce dai MA'AURATA, da masu shirin aure, da masu jego, da yan gayu masu son k’amshi kece raini, da gyaran da zaike maimaita muku dararen forkon kuruciya*

Ko kunsan Jikinmu na da sinadaran hormones da suke taimakawa dan’adam akan komai musamman lokacin da mace take mu’amalar aure da mijinta. Mafi akasari wannan hormones din ne ke samun matsala ko su yi sanyi koma su daina aiki kwata-kwata shi ne dalilin da zai sa mace tace bata jin sha’awa ko bata san dadin aure ba. Albishirinku ina da kayan da ke taimakawa wannan sinadaran du dawo aiki tukuru don karkato miki da kimarki wajan mai gida sannan su taimakawa wannan sinadaran hormones dinki su dinka secreting din ni’ima wadatacciya da zata taimaka miki ki gamsu mijinki ya gamsu fiye da tunaninki. Note: Kayana ba sa tsinka ruwan ni’ima suna dai taimakawa hormones dinki ne su tsattsafo da ni’imar musamman wacca cutar sanyi ko dattin mahaifa ya dankarar da su ya hana su yin aikinsu yanda ya kamata. Haka zalika idan kina da kyau ki kara da wanka. Zaki iya amfani da magani na na gargajiya wanda zai gyara miki sex hormones din kullum ki kasance cikin humidify wato cikin damshi mai albarka kamar yanda ake son mace. Yana gyara miki mara.

Sai kamshi. Hajiyata daure ki fara amfani da turarena ki ji irin salon kamshin sa salo ne da zai daidaita ki da mijinki ya kankaro miki da kimarki a wajansa. Siyan na gari mayar da kudi gida.

Ga masu buƙata ga number' wayata wanda nake whatsApp dashi 09097853276 kimin mgn ta whatsApp in har kin tabbatar kin shirya saya mu dai-dai ta, kayana ba ƙanana bane, shiyasa bana harkan karanta, muddin kinsan baki shirya sayaba Please kada kiyi min mgn ki bari sai kin shirya kuɗinki a hannu, ba ina nufin kayana bana talaka bane, no akwai

1 Comments On SAKAYYA
avatar
hajara-ahmad

1 year ago

Reply

Nice novel

Please Login or Register in order to submit comment