Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya sako kansa cikin ɗakin yana mai cewa.
“Iya innare yau me kika dafa mana ne, dan tun jiya da na dawo ƙasar nan banci komai ba, nace sai abincinki zanci ko na Ummina�?.
Sai kuma yayi shiru tare da matsowa kusa da ita...

Cikin Masarautar Gembilan kuwa.
Wata Kekkyawar matace yar duma-duma mai kyan shiga da haiba, ke zaune bisa kujera, yayinda System ke gabanta bisa ɗan madaidaicin stool yayinda fuskarta ke manne da wani ɗan farin glass siriri.
Da alamu typing takeyi.

Kai ta ɗan jinjina tare da juyowa ta kalli dinning area inda hayaniyar yaranta ke tashi.
Kai ta ɗan jinjina tare da kallon wata yar narkekkiyar matashiya da bazata wuce 14 year's ba.
Ido ta zuba mata ganin ta nufota da sauri.
Hannunta ɗaya.
Riƙe da school bag da takalmin sinika da kuma ɗan madaidacin hijabin Uniform ɗin ta.

Da sauri ta rusuna gaban Matar tare da juya mata baya tana cewa.
“Ayya Momy tubke min kaina, nayi-nayi yaƙi sai na ƙulleshi sai ya sule�?.
Kwaffa tayi tare da cewa.
“To wai ke kam Khausar yaushe ne zaki iya, tubke gashin kanki�?.
Ta ƙare mgnar tana tattaro suman Khausar din yana mai zamewa,
Sai kuma ta ɗago kanta ta kalli Ɗan matashin yaron da yanzu ya fito cikin Uniform ɗinsa. Wanda yake iri ɗaya dana jikin wacce aka kira da Khausar.
Da alamun ya gama shirinsa tsab.
Cikin tsuke fuska ya watsawa Khausar din harara tare da cewa.
“Gsky ni zan tafi Ramadan Raudat zomu tafi, kullum ita ke jaza mana yin letting muje aita zanemu kamar bayi.
Ni wlh da zan samu a rabamun hanya da ita inaso, muna shiga school kamar wasu shaidanu zakaji an fara cewa.
FATTANAH kuka biyewa ko, duk sai an gama shiga aji kafin ku iso.�?
Cikin yanayin tsiwa da son girma ta miƙe tsaye tana ɗaure ɗan kwalinta harara ta watsa mishi tare da cewa.
“Wallahi ka shiga hankalinka dani Haydar in baka dena cemin FATTANAH ba zan fasa maka baki�?.
Dogon tsaki yaja tare da juyawa ya nufi ƙofar falon, yana gyara zaman net ɗin sa. Tare da cewa.
“Sai ki gayawa wanda yasa miki sunan, ko kuma ki nitsu ki dena rashin kunya da rawan kai�?.
Cikin ɗan ɗaga murya Momyn nasu tace.
“Gsky Babana bana son wannan sunan da aka liƙawa Mamana sam bafana son sunan�?.
Da sauri yace.
“Toh Momy ai ita ta jawa kanta fitinenneyar ce ta gasken gaske, in dai kinji faɗa to da ita a ciki, in kuma babu ita to zakiji ance ai gulma akayi ta maidawa maishi, wai ita ba'a gulma da ita, itafa tana iya zuwa zuwa ta samu ana faɗa ta shiga tayi kane-kane sai an gama tace wai me dalilin faɗan�?.
Ya ƙare mgnar yana fita.
Ita kuwa Khausar zama tayi gefen Momynsu tana sa takalmanta da ɗan sassarfa domin yau din ranace ta musamman a wurinta tana cike da ɗokin zuwa makaranta kasancewar yau suka dawo hutu, kuma hutune na canjaza aji da JSS zata tafi SS 1 wanda takega matakin samun encinta ne kenan zata taka, tunda yanzu zata koma aji da matan aure, a islamiyar safe, sai kuma na bokone tacan anan ne babu enci sai randa ta gama sa takalmin ta saka, tana sakin yelwataccen murmushi.
Yayinda Ramadan da Raudat suke tsaye gefenta.
Hannu tasa ta kama hannun Raudat tare da cewa.
“Mu tafi�?.
Da sauri ta juyo ta kalli Momyn nasu tare da kwaɓe fuska jin tana cewa.
“Ku biya sashin Gimbiya Dadu ku gaidata, bata da lfy�?.
Cikin kwaɓe fuska tace.
“Momy zamuyi letti muje wannan mai sunan baban naki ya samu damar sawa a azabtar dani�?.
Ta ƙare mgnar cikin son zillewa zuwa sashin Gimbiya Duda, ita kuwa Momy tsuke fuska tayi tare da cewa.
“Ku biya ku gaisheta da jiki nace ko�?.
Cikin bin umarnin mahaifiyar tata badon tasowa tace.
“Toh Momy�?.
Daga nan ta kada kan ƙannen nata Duk suka fito.
Sai kuma tayi sauri ta juyo tare da cewa.
“Momy mun tafi�?.
Murmushi tayi sanin manufar ta yasa cikin lumshe idanu tace.
“Allah ya kaiku lfy ya baku Sa'a Allah yasa ki shiga SS 1 da ƙafar dama, Allah ya shirya min ku�?.
Cike da jin daɗi tace.
“Amin Ya Allah�?.
Kana suka fita.
Suna fitowa suka samu duk sauran yaran gidanma sun fito.

Kamar haɗin baki kab ɗin su sashin Gimbiya Dadu suka nufa.
Kai tsaye suka wuce har bedroom ɗin ta domin bata falon.

Su Asiya ce, a gaba ita da sauran ƙannenta, sai kuma su Khausar din.

Zaune suka sameta bisa tsakiyar gadon mulkinta, mai martaba Lamido Gembilan yana zaune ƙasa bisa carpet, yana haɗa mata tea,
Cikin tarin biyayya, da sauri suka rusuna baki ɗayansu, kusa haɗa baki sukayi wurin cewa.
(“Allah saine Abba, noi nɓanɗu Dadu?) Allah ya faranta maka Abba ya jikin Dadu?�?.
Cikin son ahlin nasa ya jinjina masu kai tare da cewa.
(“Yettore Allah nwodi dama) an godewa Allah da sauƙi�?.
“Allah ntokkin dama�?.
Suka faɗa a tare, cikin tankwashe sawunsa yace.
“Allah jabu�?.
Amin suka faɗi baki ɗayansu,
Yayinda Khausar kuma taketa jan hijabinta, tana mai sunkuyar da kanta ƙasa,
Allah ya sani bata ƙaunar abinda zai kawo ta gaban Gimbiya Dadu,
Domin jikinta da nitsuwarta duk rasasu takeyi, sabida wani irin mayataccen kallo mai bada tsoro da tsohuwar ke Binta dashi.
Kamar koda yaushe kuma hakane, duk da bata da lafiya, amman wani irin masifeffen kallo ta tsare Khausar ɗin dashi har bata jin gaisuwar da jikokin nata keyi mata,
Cikin taɓe baki Asiya tace.
“Dadu wannan wanne irin kallo ne? muna gaidaki kinyi shiru?�?.
Jin hakanne yasa Khausar ɗan ɗago kanta,
Ai kuwa ido cikin ido sukayi da Dadu.
Da sauri ta motsa lips ɗin ta a hankali tare da cewa.
“Innalillahi wa innailaihi raji'un�?.
Sabida wani irin tashi da tsikar jikinta ya farayi, yam-yam.
Ita kuwa Dadu har lau bata cire idanunta a kantaba,
Haydar ne ya ɗan miƙa tsaye tare da kamo hannun Ramadan da Raudat yace.
“Dadu Allah ya sauwaƙa, zamu tafi school kada muyi letti Raudat muje�?.
Abin mamaki har lau Dadu batama san anayi mata mgna ba, bare ta amsa musu, gaba ɗaya nitsuwarta da kallonta yana kan Khausar....!

Lamido kuwa ido ya zubawa maifiyar tasa, cike da mamakin lamarinta, ya zama ana kallon kalo, ita tana kallon Khausar data kasa koda ƙwaƙƙwaran motsi shi kuwa yana kallonta.
Asiya kuwa itama miƙeqa tayi tare da kaɗa kan ƙannenta tayi gaba Amina ce ƙanwar Asiya mai binta ta ɗan miƙa tare da cewa,
“Uhum�?. ta fice
Ya zama daga Dadu sai Lamido sai Khausar.

Cikin wani irin yanayi da Khausar din keji ta kuma kallon Dadu, wacce zuwa yanzu ta saki laɓen bakinta na ƙasa, wani irin yawu mai cike da mayataccen kwaɗayi ne ya tsinko mata, har yana ɗan sauƙowa kan lips ɗin ta.
Cikin sauri Khausar ta miƙe jin Lamido yana cewa.
“Mamana tashi ku tafi�?.
Ai kafin ma ya rufe bakinsa, tuni ta fita tana mai cewa.
“Toh Abba�?.
Ita kuwa Dadu wani nannauyan numfashin ta sauƙe tare da juyowa takalli ɗan nata, dake miƙa mata cup ɗin tea.
Cikin diriricewa tace.
“A'a bana buƙatar abin zaƙi, a kawo min abu mai yaji-yaji�?.
Cike da biyayya yace.
“Toh�?.
Kana ya miƙe ya fita.

Tuni su Khausar kuwa sun shiga school bos ɗinsu,
Amina ce ƙanwar Asiya mai binta ta kalli Ramadan dake cewa.
“Kalli fa 8:13 na tabbatar yauma zamu zanu�?.
Cikin sanyi tace.
“Mu dai Allah ya rufa mana asiri daga SS 2 akwai matan aure da yawa a ciki, so ba batun duka a side ɗin mu.
Kuma ma duk bama saɓa doka cikin nitsuwa da tarbiyyar mu muke, ko nayi litting nasan za'ayi min uzuri.
Cike da jin daɗi, Khausar tace.
“Nima dai Allah ya yaye min masifa da cin zalin su Moddibo tunda yau dai zan tafi Ss 1 ɗin, da ba duka ba zagi, wlh inci karena babu babbaka�?.
Taɓe baki Haydar yayi tare da cewa.
“Mu gefen maza, babu manya, duk yarane, manyan da dare suke zuwa, shiyasa babu roggomi�?.
Asiya ce ta kalli Khausar cikin yanayin son yarinyar tare da cewa.
“Ai wlh ke dai in baki nitsuwa ba ko jami'a kikaje in dai Moddibo na cikin malamanku, na tabbatar zai san matakin da zai ɗauka a kanki.
Sannan ma da kike batun kin tafi Ss1 akwai matan aure, kin mance cewa, na safene, na islami.
Akwai na rana zuwa biyar bokone, kuma kuna tare da moddibo.�?
Kwaffa tayi tare da cewa.
“Kai na shiga ukuna wlh�?..

Anan gefen su Modibbo ku, fir innayi taki aje asibitin. Su kuna su kasa fahimtar ta, gani suke zafin zazzaɓin maleria ne yake son sata surutai shiyasa suke hanata mgn sukayi ta mata addu'o'i hardai ta ɗan fara samun nitsuwa har bacci ya ɗan sureta.
Gani ta ɗan rumtsane yasa suka tafi wurin Ummin M Jameel suka ɗauko Ummin dan tazo ta ɗan kula da ita.

Suna isa bakin gate, ba tare da sun shigaba, Ummin ta kalli M Jamil da yayi saurin fitowa bayan yayi parking marfin motar ya buɗe, mata cikin tsananin son mahaifiyar tasa, yace.
“Bismillah Ummi fito ki shiga wurin Innayinki, domin mu dai yau mun gaza gane kanta, da alamun Ita dai dare ɗaya gigin tsufa ya sauƙo mata�?.
Ɗan buge ƙeyarsa tayi tare da ciwa.
“Tsufa kan zai cimma taka uwar mafa, kawai dai inaga zafin zazzaɓine kusan wasu lokutan yanasa yara surutai, to ita kuma girma yazo dole in ciwon yayi zafi zatayi kamar na yara�?.

Juyowa tayi ta kalli Moddibo daya jingina kansa jikin kujerar gaban motar gefen mai zaman banza,
Cikin sanyin murya yace.
“Uhmmmm Ummi waifa cewa tai taga taurari suna sauƙowa ƙasa har kamar zasu taɓa rufin side nan, anya kuwa Ummi wannan zazzaɓi ne?�?.
Sai kuma ya ɗan fesar da numfashi tare da lumshe idanunsa cikin alamun nazari yace.
“Ina tsoron kada fa matsalar ƙwaƙwalwa ce, nayi nayi muje asibiti kuma taƙi.�?
Ya dire mgn tare haɗa kan yatsun hannunsa.
Jamil ne yaci gaba da cewa.
“Saida fa Moddibo yayi ta mata tofi kafin muka samu tayi bacci har muka fito ɗin.�?
Cikin kulawa Ummi tace.
“In sha Allah babu komai, bari in shiga, ku kuje�?.
To Jamil yace kana ya shiga mota, ita kuma tayi cikin gidan.

A hankali ya miƙa dalleliyar motarsa ƙirar BMW kan shimfiɗeɗen titin,
Yana tafiyar hawainiya, murmushin yayi ganin kallon da Moddibo yake masa.
“Sanin yau za'a dawo makaranta ne, yasa nayi ƙoƙarin dawowa baro Marrocco, duk da akwai ayyukan da ban gama dasu a company'nba,�?.
Cewar M Jamil shi kuwa Moddibo kai ya jinjina alamun yana jinsa, shi kuwa M Jamil gudu ya ɗan ƙara tare da ci gaba da mgn dan yasan ba lallai ne Moddibo ya amsa mishi da bakiba, inda sabo ya saba, kuma shi yasan cewa body language al'adane ko ɗabi'a koma yace halittar Moddibo ne.
Juyowa yayi ya kalleshi tare da cewa.
“Na zaƙu muje makarantar nan, dan nasan zaiyi kyau sosai a tsarin gyarashi da akayi�?.
Cikin ɗan ƙwaɓe fuska yace.
“In an gama gyaran ba�?.
Da sauri M Jamil yace.
“Kamar yaya za'a gama mana�?.
Juyowa yayi ya ɗan kalli M Jamil ta gefen ido kana a takaice yace.
“Toh ba'a gaman ba�?.
Cikin sauri M Jamil yace.
“A.S da gaske ba'a gama ba?�?.
A.S shine sunan da yake kiran Moddibo dashi kuma su biyu kaɗai suka san ma'anar sai kuma abokan karatunsu.
Shi kuwa Modibbo littafin dake gaban motar ya ɗauka tare da buɗe wa kana yace.
“Dama tun lokacin da za'a bada hutun na faɗa bazai isa a gama gyaran school ɗin ba, musamman da ya zama an ƙara yawan class, kana ga gina hall din da akace za'ayi, kuma dole aikin bazaiyi guduba sabida Ramadan, tun lokacin nace a ƙara kwanakin hutun, sabida samun isasshen lokacin, wannan Ba fulatanin yaƙi�?.
Murmushin M Jamil yayi tare da cewa.
“Toh kai meyasa baka ƙara hutunba, ai da sai ka sanar�?.
Juyowa yayi ya kalleshi bayan hannunsa yasa ya shafa tattausan sajensa tare da cewa.
“Uhmmmm�?.
Ya san me wannan Uhmmm ɗin take nufi, kai ya jinjina tare da cewa, “Mu dai yan kallone,".
Da sauri yace.
“Nima haka, dan na gaji ko yaushe sai ya kwaɓa abu yazo yana cemin ina mafita�?.
Dai-dai lokacin aka buɗe musu gate din makarantar, Ya Salam.
Wani irin tsarine da zubi makarantar yake dashi, tsari mai burgewa, yayinda shima makarantar Moddibo ya ƙawatata da tsirrai na kyautata muhalli.
Tabbas gyara kam da saura ba'a gama shi ba.
Domin daga woje dai kam an kammala komai amman daga ciki, duk cikin ajujuwan a hargitse yake.
M Jamil nayin parking, wani kekkyawan dattijo bafulatani ya nufo matar tasu da sauri, bisa alamu dai shine shugaban makarantar domin duk malaman na miƙa gaisuwar garesa cikin mutuntawa.
“Moddibo! Moddibo!! Moddibo!!!.�?
Jamil ne ya fito yana murmushin tare da cewa.
“Allah rene,�?.
Da sauri yace.
“Ina Moddibo�?.
Cikin motar Jamil ya nuna masa, da sauri ya sunkuyo,
Yayinda shi kuwa Moddibo meda bayansa yayi ya jingina tare da lumshe idanunsa, murmushi Dattijon yayi tare da cewa.
“Ga ɗalibai duk sun dawo makaranta ta cika maƙil ga sabbin ɗauka, kuma aiki baifi rabi ba, ya zamuyi?�?.
Cikin taɓe baki yace.
“Allahu a'lamu!�?.
Jamil ne ya juyo ya kalli Malam Ahmad da Malam Habibullah da suma fitowar su kenan daga can cikin makarantar.
Shi kuwa Malam Arɗo Umaru mamallakin makarantar kuma .
Kai ya ɗan dafe tare da cewa.
“Dan Allah ka fito Moddibo kasan bayanin da zakayi musu, kana ka kara musu kwanakin hutun, tsawon lokacin da kakega za'a iya gama gyaran�?.
Yadda ya dire mgnar da karya wuyane yasa Moddibo fitowa.
Murmushin sauran malaman sukayi, domin sosai tsufa ya fara cimma Mala Arɗo, zuwa yanzu ya kamata ragamar makarantar ya zama a hannun yara, domin badon Allah yasa Moddibo ke tsara komai na jadawalin abubuwan ciki da wajen makarantar ba, da tuni ta durƙushe, to amman sabida shi da sauran haziƙan malamai da suke da tsananin kula da tarbiyyar yara da sukeyi yasa har yau makarantar bata da na biyu a faɗin birnin Gembila.
Kusan a tare suka rakaya cikin makarantar.

Yayinda hayanin ɗalibai manya da yara maza da mata, ke tashi.

Juyowa yayi ya kalli Jamil tare da cewa.
“J kaje masallaci kayi mgn duk mu su haɗu a tsohon halla ɗin mu na sama.�?.
To Jamil yace yana tunanin to me zaice musu,
Masallacin ya wuce tare da yin sanarwan.
Nan take kuwa, duk ɗaliban suka haura sama, suka shiga cikin babban hall ɗin nasu wanda yake ƙato sai dai duk da haka yanzu ya musu ƙaramin,.

A gafen mazama suma duk sun haɗu a halla nasu.

Shi kuwa Moddibo office nasa ya wuce.
Jim kaɗan ya fito, da Lapel Microphone a hannunsa yana saƙalasa a wuyan tattausan jallabiyar jikinsa Malam Ahmad ne ya matso kusa dashi tare da cewa.
“Zamu jirane ko an ƙara mana hutu�?.
Ɗan murmushin gefen baki yayi tare da cewa.
“Hutu kuwa sosai ma har na tsawon mako uku za'a ƙara�?.
Cike da murmushi yace.
“Mu tafi kenan�?.
Kai ya gyaɗa masa tare da cewa.
“Suma duk yanzu zan kaɗa kansu ko wacce tai gida sai dai muma muna da zama na musamman�?.
Ai kuwa jin haka yasa duk malam suka zauna jiran.

Shi kuwa ya haura saman yana mgn da M Jamil a waya.

“Su maza basu da hayaniya, kawai J ka ɗanyi musu nasiha, kana kace sai bayan mako uku zasu dawo kafin nan an gama gyara,
Sai dai masu zuwa hadda suci gaba da zuwa."
Cike da gamsuwa M Jamil yace to.
Kana sukayi sallama.

Dai-dai lokacin kuma su Khausar suka shiga cikin makarantar,
Da in ka gani kace a ƙasashen ƙetarene, domin makaranta ce mai zaman kanta, mai cike da haziƙan malamai, duk da sunyi makarar mintuna 20, an bar motarsu ta shiga ne, sabida magiyar da sukayi tayi da kuma girman gidan da suka fito, da bada uzurin motar ta ɗan lalacemusu a hanyane kana da kuma ganin ma yau ba karatun za'ayi ba, hutun za'a kuma ruɓanyawa.

Suna shiga kuwa, ga mamaki su aka barsu suka shige ba hukuncin komai.

Kana ko wa ya nufi sashin da ajinsa yake.

Da sauri duk suka tsaya jin Malam Habibullah na cewa.
“Fattanah uwar yan letti yau makarar har ta 20 minute duk da yau aka dawo, duk kuyi sama ana taro a hall�?.
Cikin ɗan tura baki tace.
“Toh Malam�?.
Yayinda tuni su Asiya kam sun haura har sun shiga hall ɗin.

Da ɗan sassarfa ta fara take steps ɗin da zai sasanta, da hall da yake a sama ganin ita kaɗai ta rage.

Daga corridor'n steps ɗin, ta ɗan lumshe idanu ta, tare da gyara saƙala school bag ɗinta a kafaɗar dama.
Sabida ƙamshin turarensa ya shaida mata, tabbas tuni ya shiga hall ɗin.

A hankali ta sauƙe numfashin ta tare, da nemo dukkan nitsuwarta.
Lokacin da ta gama haurowa, sama, da sauri ta tsaya, jikin window dake gab da bakin ƙofar shiga, ido ta lumshe tare da buɗewa a hankali kana ta kutsa kai cikin hall din da a kalla mutane ciki sun kai ɗari da hamsin, duk da tasan bai taɓa barinta, ta shiga ajiba, muddin ya rigata shiga, to amman kullum sai ta gwada sa'anta musamman yau da yake a hall ne.
Taku ɗaya tayi ana biyu, ta tsaya, sabida, ganin ya ɗaga mata, tafin hannunsa.
Cikin yin mui-mui da bakinta tace.
“Afwan ya mu'allim sayyara...�?.
Da sauri ta ɗan ja da baya ta koma jikin window ganin ya juya baya tare, da gyara ɗan masaƙalin Lapel Microphone dayake saƙale a wuyan jallabiyar jikinsa, sabida tsananin sanyin sautin muryarsa yasa dole sai dashi yake amfani a cikin class, domin ɗalibansa su samu damar jinsa sautinsa ras domin sam baya iya kware muryarsa yayi mgna da ƙarfi haka Allah ya haliccesa da nitsestsiyar sauti to bare a irin taron maƙil da hall ɗin yayi yau.
Cikin tattausar muryar sa mai cike da sanyi yace.
“Makfut?�?. Cike da jin daɗin nasihar da yakeyi musu suka amsa da “Na'am�?.
Kai ya jinjina tare da cewa.
“Ɗeyib!�?.
Sai kuma ya ɗan juyo ya fuskancesu, hakan ya zama, ya ɗan bawa Khausar baya, tattausan sumar ƙeyansa dake kwance lib-lib ta zubawa harara.
Numfashi mai sanyi taja tare da shaƙa daddaɗan ƙamshin turarensa mai sawa ɗan adam salama.
Sai kuma tayi ƙasa da kwayar idanunta dugadigin sawunsa, ta zubawa idanu tana ganin yadda sukeyin ja in ya taka sawun, in kuma ya ɗaga sai suyi fari, baki ta ɗan tura sama ta da liƙa ƙeyarshi wani sabon hararan.

Shi kuwa Moddibo a hankali yake taku a gaban ɗaliban nasa, masu biyayya da girmamawa a garesa, cikin tattausan lafazi yace.
“Falalar zikirai da karatun Alqur'ani , nakeso son in tunasar mana, sabida kididdigar manazarta, ta nuna mana Al'ummar wannan ƙarnin sun samu naƙasun zikiri da karatun Alqur'ani mai girma, sun maida hankali akan sashin yanar Gizo-gizo fiye da yadda ya kamata, mu maida hankali kan Al'ƙurani littafin Allah da hadisan Manzon Allah, mu samman a wannan taki da muke ciki, na shuɗewar Ramadan wanda zaka samu da yawa mutane sun fuskanci aikin al'khairai da bautar ubangiji a cikin watan, da zaran watan ta gabata sai a koma gidan jiya aita sharholiyar duniya.�?
Sai kuma yayi shiru, tare da fesar da numfashi a hankali, kana ya juyo a hankali yace.
“Mutane da yawa sun mance koma ince wasu basu san me Allah maɗaukakin sarki yace ba A cikin Suratul Baqara, ayata 152.
Allah maɗaukakin sarki yace.
فَاذْكُرُونِي أَذْكُرْكُمْ وَاشْكُرُوا لِي وَلَا تَكْفُرُونِ.
Ma'ana:
Ku ambaceni zan ambaceku, ku godemin kada ku butulcemin.�?.
Ya ƙare mgnar da rumtse tafin hannunsa alamun ƙarfafa mgnar, wanda kuma wannan ɗabi'arsace ko ace halittar sace.
Duk mgnar da yakeyi yana kamantata ko suffantata da tafukan hannunsa like dai yadda manyan sarakuna keyin mgn turawa kuma suka cewa hakan body language, Wanda mafi akasari ɗabi'ar yan jarida ne, in suna mgn.
Shiru hall ɗin yayi alamun suna fahimta sosai.
Shi kuwa Moddibo cikin girmama zancen Allah madaukakin sarki yaci gaba da cewa.
“A dai wannan ƙarni da muke ciki da yawa, suna butulcewa faɗin Allah madaukakin sarki, daga barin ambatonsa, gaba ɗaya shagala tayiwa al'ummar mu ƙawanya, shafukan sada zumunta na yanar Gizo-gizo ya maiye gurbin da yake muhallin Qura'ani ne a wurin wasu musul manmu, sai a wuni a kwana musulmi bai ɗauki Qura'an ya karanta ya duba kyan baƙin da yake haɗawaba, amman sai ka sameshi awa 14 na awannin 24 na rana yana rungume da wayarsa, ana charting, a Facebook a koma whatsApp, daga nan a tafi Instagram, sai kuma a murgina a koma twitter sai kuma a rarrafawa zuwa wannan lalataccen kuma kazamin dandalin Tiktok, ayi ta raye-raye da waƙe-waƙe, anaiwa juna cin zarafi, wasu su koma yiwa malamai isgilanci ana yaɗa fasadi da fajirci ana meda ashariya kamar ruwan sha.�?
Ya dire ayar mgnar tare da haɗe kan yatsun hannunsa gaba ɗayansu wuri ɗaya alamun ya dunƙule mgnar kenan bawai ya gamata bane zai tafi sashi mafi muhimmanci ne.

A jikin window a waje kuwa, cikin jujjuya ido Khausar ta raɓa jikin window tare da maida hankalinta baki daya cikin.
Shi kuwa Moddibo a hankali ya ɗan juyo gefen damansa, jin inda sautin surutu yake ɗan tashi kaɗan.
Ganin yana kallon sune kuwa yasa,
Samira Sani yin shiru.
Cikin nitsu ya kuma cewa.
“A wata ayar kuwa a cikin suratul Ahzab ayata 41, me Allah maɗaukakin sarki yace mana!???�?.
Ya ƙare mgnar da alamun ayar tambaya, hakan na nufin su ja mishi baƙi yake so, sanin mafiya akasarinsu yan haddansa ne,
Ji kakeyi, hall din sit kowacce tayi ƙasa da kai, gudun kada ya nuna ta kaɗan daga cikinsu kuma bawai basu sani bane diricewa ne da kwarjininsa ke sasu yin ƙasa da kai.
Cikin sanyi yace.
“Na'am Samira Sani�?. Da sauri tace.
“Malam ni?�?. Fuskarsa ya tsuke tare da juyowa ya kalli Asma'u Ahmad dayi mata alama da hannu, tsilli-tsilli tayi da idanu.
Samira Sani kuwa ganin ya cire ido a kanta ne yasa tayi saurin buɗe Qura'an ɗin ta.
Dan dubo ayar,
sai kuma duk suka ɗago kansu suka zuwa Khausar dake jikin window idanu,
jin ta uzi shaitan tare da yin basmalla kana taja numfashinta tare da lumshe idanu murya cike da tajwed ta fara jan ayar.
Surah Al-Ahzab aya ta 41:
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا اذْكُرُوا اللَّهَ ذِكْرًا كَثِيرًا
Murmushin mai cike da jin dadin Asma'u Ahmad tayi tare da sauƙe numfashin, FATTANAH ta ɗauki belinsu kamar yadda aka saba, domin in dai batun jane na ƙwaƙwalwa to kwanyar Khausar ta musamman ce.
Mata da yawa kuma cikin manyan mata kallonta sukeyi cike da sha'awa da jin daɗin zazzaƙar muryarta na kuma ratsa musu kunnuwa.

Shi kuwa Moddibo ba tare da ya juyo ya kalle taba.
Ya fara kawo musu fassarar ayar.
“Allah madaukakin sarki yana cewa:
Yaku waɗanda suka yi imani, ku ambaci Allah ambato mai yawa.
Ammato kuma na haƙiƙa bawai kawai kije kiyi karatun Qura'an kara zube ko gatsa-gatsa ba, kuyi karatu kwatankwacin yadda tayi inma kunce juyawa ih zuwa irin nawa da wuya.�?
Cikin sanyi Asma'u Ahmad tace.
“Malam ai karatun Khausar irin nakane, ba banbanci kawai dai, ita muryar mata kai muryar maza muna son mu koya irin ƙira'ar sosai.�?
Kai ya ɗan juya ya ɗan basu baya tare cewa.
“In sha Allah zaku iya�?.

Samira Sani kuwa, tattausar sajensa ta zubawa idanu cikin wani irin salo dake cikin jiki da zuciyarta.
Shi kuwa Moddibo a hankali ya kuma yin gyaran murya tare da cewa.
“A wata ayar kuwa cikin suratul A'araf aya ta 205. Allah maɗaukakin sarki na cewa...
Sai kuma yayi musu alamun suja ƙira'arar.
Cikin kauda kai Khausar ta lumshe idanu ganin wani irin masifeffen kallon daya watsa mata, wanda saida taji hantar cikinta ta kaɗa.
Cike da dagiya a fagen neman ilinta dan bata wasa kuma bata barin tsoronsa ya hanata fahimta, cikin nitsuwar da take samu in zatayi karatu tayi bismilla tare da fara jan ayar.
“Surah Al-Araf, aya ta 205:
وَاذْكُر رَّبَّكَ فِي نَفْسِكَ تَضَرُّعًا وَخِيفَةً وَدُونَ الْجَهْرِ مِنَ الْقَوْلِ بِالْغُدُوِّ وَالْآصَالِ وَلَا تَكُن مِّنَ الْغَافِلِينَ
Ta dire ayar da sauƙe nannauyan numfashi sabida tagib da taja, wanda dole ta ɗan riƙe numfashinta na kusan second 32.

Samira kuwa, wani irin malolon bakin cikine, ya tokare mata maƙoshi, sabida masifar kishi da takaicin yadda ko yaushe Khausar ke gaba dasu.
Asma'u kuwa sai murmushi takeyi,
Yayinda da yawa suke fatan Allah ya buɗa musu kwakwalensu kamar na Khausar.

Shi kuwa Moddibo a hankali ya fara fassara musu ayar.
“Abinda Allah madaukakin sarki yake cewa.
(Kuma ka ambaci Ubangijinka, a cikin zuciyarka, kana mai ƙanƙan da kai, da tsoro, ba da ɗaukaka murya a, tsaka-tsaki tsakanin asirtawa da bayyanawa da safe da kuma maraici, kuma kada ka zamo cikin falaki,.
A wata ayar kuwa, Allah madaukakin sarki na cewa.
(Da masu ambaton Allah, maza, da masu ambaton sa mata, Allah ya tanadar musu gafara da lada mai girma)�?.
Sai ya kuma ɗan tsagaita wa tare da kallonsu yana cewa.
“Makfut?�?.

“Na'am�?. Suka amsa baki ɗaya,
“Ɗayyit�?. Yace tare da kallon agogon hannunsa, ganin saura 9 minute lokacin da ya kamata ya sallamesu yacika ne, yasashi ci gaba da cewa
“Kuma Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace:
(Misalin wanda yake ambaton Allah da wanda baya ambaton Ubangijinsa kamar misalin rayayya ne da matacce.
A wani wurin kuma yace.
(Shin bana baku labarin mafi al'khairin ayyuka ba, kuma mafi tsarkinsu a wajen Sarkin da yake mallakarku, kuma mafi ɗaukakarsu, ga darajojinku, kuma

1 Comments On SAKAYYA
avatar
hajara-ahmad

1 year ago

Reply

Nice novel

Please Login or Register in order to submit comment