Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Arnan nan neman fitina suke damu sam babu gaskiya alamarin su bayan sace-sacen dabbobi da kuke mana sai kun nemi fitina damu�?.

Babban su ya juya ya kalli Baffa Umaru yace.
“Wani irin sace-sace kuma?".
Harara Baffa Umaru ya watsa masa yace.
“kana tunanin bamusan kune kuke sace mana dabbobin muba to yanzu ga Bible ka karɓa ka rantse da littafin ku cewa ƴarku ta ɓata duk alamun rashin gaskiya ya bayyana atare da ku kawai ku taru dare-dare kuzo mana da mugun nufi�?.

Anutse Jauro yace.
“Umaru kayi haƙuri kaki�?.
Yasan idan ransa ya ɓaci babu wanda zai iya shawo kansa.
Malam Liman ya dubesu yace.
“Tunda har baku rantse da littafin kuba kenan ƴarku bata ɓata ba in kuma ta ɓata to baku da tabbacin tana garinmu�?.
Babban su yace.
“Shikenan babu matsala tunda zaku iya rantse wa da littafin ku munsan bata Rugarku yanzu magana ya ƙare.
Amma Jauro da malam Liman ku jawo Umaru kunne ya fita sabgarmu�?.

Miƙewa Baffa Umaru yayi tare da nuna kansa da hannu yace.
“Ni ɗin nan ka ganni nan Babu wanda nake tsoro sai Allah daya hallicceni".
Ƙwafa Babban su yayi yace.
“Tun da haka kace shikenan amma zaka ga abinda kake tsoro�?.
Da sauri Jauro ya juya ya kalli Babbansu yace.
“Mu ba mason fitina me kake nufi da zaiga abinda yake tsoro?�?.
Babban su yace.
“Indai zai shiga sabgarmu to zaiga abu da yawa�?.
Jauro yace.
“Toh bama son fitina tunda kuda kanku kun tabbatar da ‘Yarku bata cikin Garinmu sannan kuda kanku kunsan baku da gaskiya kun ƙi ku rantse, karku sake shigo mana Rugar mu haka ba maso idan kuma kuka sake to zamu haɗa ku da Sarkin cikin Gembila�?.
Jin Jauro yace zai haɗa su da Sarkin Gembila yasa suka ce.
“To ayi hakuri ba zasu sake ba�?.
Sannan suka juya suka tafi cike da baƙi ciki badan Umar daya hana su shiga ba adaren da sun samu damar kwasan dabbobi damar saboda haka suka ce ansace musu ‘yarsu.

Bayan kwana biyu Komai ya lafa ba fitina da hantsi Khausar da Dije da Ma'u sun ɗebo kayan marmari arafi suna fitowa daga cikin rafin suka hango wata mota fake agefen Rugar tasu sai kuma hango wasu mutane biyu ɗaya ya fito daga gefen dama ɗaya kuma daga gefen hagu da gudu suka shiga motar kafin su Dije su ƙara so sun figi motar.
Khausar kuwa sosai tsura fuskokin su ido kafin su shiga motar, sosai ta riƙe kamanninsu. sannan tabi motar da kallo lokaci ɗaya ta riƙe Number motar Dije da sauran 'yan matan kuwa mamaki suka shiga yi shin mai ya kawo masu motar garin sannan mai yasa da suka gansu suka gudu bayan sun san a irin wannan lokacin, duk mazan garin basa nan makiyaya sun tafi kiwo saura kuma su tafi jeji wa'anda ke rafi kuma sun tafi lambu jiki Asanyaye suka tafi.

Bayan kwana biyu da daddare Khausar na bacci, yayi da take ta takurewa wuri ɗaya sabida wani irin masifeffen sayin da ake tsula musu.
A hankali taja dogon numfashi kana ta fesar a hankali tayi lib.
Can cikin baccinta kuwa cikin wani ƙaton fili mai yalce da yashi fari ƙal-ƙal tana zaune bisa wani dutse tana fuskantar yamma kana daga bayanta kuma wani garden ne mai masifar kyau da girma babu kalan bishiya da sirran da baya ciki, wani irin ni'imtaccen iskane mai cike da ƙamshi furanni ke buso masu wata irin iska mai ɗan karen sanyi.
Gefen damanta ta juya ga mamakinta M Jameel ne zaune bisa wani dutse yana murmushi, da sauri ta juya gefen hagunta kuma, Adda Adama ce ta gani zaune bisa dutse tanata murmushi.
A can gabanta kuwa Mod....! *NO EDITING*

*Kuyi haƙuri sai yanzu na samu caji gashi ba editing. KUNSHA TYPING ERRORS*




By
*GARKUWAR MARUBUTA*
9/13/23, 20:03 - Buhainat: 📝🍇✨💫⏰🤴🏻👹❤️❤️❤️🍇

*SAKAYYAH*
_Page 7_

_NA_
*AYSHA ALIYU GARKUWA*

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*FREE PAGE NE YAN UWA, BA WAI FREE BOOK BANE! INA GAMA SAKIN FREE PAGE, KO KINGA an fiddashi waje na satane. Na kuma Yaseen ne doguwa. Dan haka ki biya ki karanta cikin Aminci ba haƙƙin wani a kanki 1k ne kacal 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA, sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276. Littafin SAKAYYAH na kuɗine ƴar uwa biya ki karanta*


*WOHOHO IN KAJI ANA ƘI GUDU TABBAS SA GUDU NE BEZO BA*

_Ina kuke Ma'aurata masu sha'awar ganin sun zama taurari kuma fitilu a idanun mazajensu Uwar gida,Amarya,Tsakar gida,hadda tan kaɗen gida Shararriya kuma ƙasaitacciya data saba kawo muku nau'ikan sirrin sahihan magungunan ma'aurata wato *AYSHA ALIYU GARKUWA* Garkuwar Marubuta ayau ma ta dawo muku da Ingantattun magungunan mata masu kyau da inganci domin gyara kanki ki zamto tauraruwa a idanun mijinki...Muna da Ingantattun Abubuwa kamar haka_ :_Munada Garin mallaka, garin maɗi, garin Hakkin mayi, garin ɓelɗamhi Garin ilanwaddihi, Gumbar da ba'a baiwa mai kishiya, Gumbar kolli mai kellin al'khairi, Gumbar Riɗi wato 3 in 1, Gumbar makwaranyi, Masin Maliƙi mai masifar ƙarfi da matse mace wanda bani da haufi kansa 7k ne kacal sai dai yar musilar robace., Kana masin Daɗi har Maɗigan yana da masigar kyau da tsatstsafo da ni'ima, wlh wasu in sunyi amfani dashi pan biyu sabida yadda zakiyi ta tsiyaya. 5k ne Akwai, kwanon ƙasaitacciyar mace mai masifar kyau da ratsa jiki da samar da inƙantacciyar ni'ima yanada abubuwa masu kyau haɗinsa 8k ne, Zumar goron tula mai masifar kyau, tsumin dabino, mai ratsa jiki, tsumin Riɗi mai ƙarfi, Furar Mata mai tsastsafo da ni'imantaccen damshi, Cida kaza, Ciccibi Abodi, Tsumin Ɓaure, tuwon ɓauren, kana akwai maganin sanyi sadidan wanda wlh koda sanyin cikin mahaifane fes yake wanke shi kuma ko mai ciki zata shashi baida illa, kama budurwa ko bazawara duk zasu iya sha harma da yara. Set ɗin da 10k ne innkuma za'a sa miki komai rabi-rabi ne 5k ne, da dai sauransu...Se kuma fannin ƙamshi kasance da Shu'umin ƙamshi wanda ze gigita ƙwaƙwalwar Oga tare da jin ko wacce mace bata kaiba...._ _Shin ko kina da labarin Miskilinci da ƙasaitar Rayyan Naaan amma lokaci ɗaya ya zamto zautacce sakali akan soyayyar Jannart bakomai Jannart ta riƙe ba face sirrinkan gyara da kuma shu'uman humran da kulaccar sirri na Aysha Aliyu Garkuwa(Tubali) tabbas taga tasirin haka domin Naanunta ya zame mata tamkar bawa_
_Shin ko kinsan sihirtaccen haɗin da Aysha ke sha kenan ta zamto tauraruwa a idanun Hamma Yusuf(Miwasmiti)...Tabbas Mahmud ya zamto zautacce kuma makaho akan sauyayyar Bazawara wato khadijarsa duk da kuwa gashi da budurwa(Namiji Baya Kaɗan) ko kinsan hakan nada alaƙa da amfani da sahihan maganin da kuma shu'uman humran Aysha Aliyu Garkuwa??.Nasan ba zaka ku manta da irin kima da kuma darajar da Aysha ke dashi acikin Idanun Sheik Jabeer ɗin ta duk da kuwa shekaru sunja anma jinta yake tamkar budurwa 'yar sha bakwai(Garkuwa) sirrin hakan na tare da Ingantattun kuma sahihan magungunan Aysha Aliyu Garkuwa Wato Garkuwar Marubuta da kuma Ma'aurata na tabbata kunsan da cewa basirarta ba'a iya rubutun littafi ya tsaya ba hadda inganta rayuwar ma'aurata ta hanyar kawo musu Nagartattun abubuwa Ga duk wacce ta shirya saya seta tuntuɓi number ta 09097853276 muna iya tura kayan mu aduk inda kuke afaɗin Nigeria harma da ƙetare Dan Allah 'yar uwa idan baki shirya siyaba kada kiyi min magana muɓatawa kanmu lokaci...._

🤝🏻🤝🏻🤝🏻🤝🏻🥰😘sai.kunzo. sayan na gari maida kuɗi gida,


Moddibo ta hango zaune a gefen gabas yana fuskantar tata, bima'ana yana kallon yamma, zaune yake akan wani dutse mai masifar sheƙi kana wasu mutane biyu na tsaye gefen hagu da damansa,
Sannan da buta gabansa bisa alama Al'wala yayi domin farin yashin daya mamaye wajen daga gabansa a jiƙe yake, kana yana mai fidda wani irin ni'imtaccen ƙamshi maisa ɗan Adam lumshe ido. Baki ɗaya haske ya mamaye ilahirin filin wajen hakan yasa itada Moddibo suna fuskantar juna yayin da M Jameel da Adda Adama matar Baffan Umaru suma ke fuskantar juna.
Kana lambu dake can bayanta kuwa yake feso musu iskar yammaci dana lambun suka haɗu waje ɗaya daga sama kuma rana ne yayi Ja yana shirin faɗuwa.
A hankali ta sauƙe numfashi mai nauyi tare da lumshe idanunta.
Da sauri ta buɗe idanun nata, jin wani irin sassayan sautin dariya mai cike da shauƙi da Moddibo yakeyi.
Cike da mamaki duk suka zuba mishi idanu.
Yayinda Adda Adama ma tuni ta fara dariya mai sauti.
Ita kuwa Khausar haka nan taji jikinta yana tsuma tare da sakewa, da sauri ta juya ta kalli M Jameel ga mamakinta shima ita yake kallo, da idonshi ya nuna mata Moddibo yana mai yin lallausan Murmushi, da sauri ta maida kallonta kan Kekkyawar fuskar Moddibo, wacce tunda take a rayuwarta dashi bata taɓa ganin yayi dariyar da har haƙoransa na gaba zasu baiyana ba.
“Fatabarakallahu fih hasanil khaliƙeen�?.
Ta furga a saman lips ɗinta, lokacin da ta sauƙe ƙwayar idanunta kan fuskar Moddibo, da sauri ta kuma lumshe manyan Idanunta sabida wani irin masifeffen sheƙi da ta hango sajenshi dake kwance lip-lip yanayi,
Sautin dariyarsa da har yanzu yake ne yasata saurin buɗe idanun.
“Subahanallah, tsarki ya tabbata ga Ubangiji da ya halicci wannan bawa ya kuma bashi waɗan nan haƙoran�?.
Ta faɗa a fili lokacin da taga ƙyellin da haƙoransa keyi har yana ɗauke mata idanunta,
Lobgoɓar da kanta tayi bisa kafaɗarta.
Wani irin sassayan numfashi ta fesar tare da tsaida idanunta a kanshi.

Shi kuwa Moddibo dariya yakeyi mai sayyan sauti wanda yake da daɗin ji, har maƙolloton wuyanshi yana ɗan haurawa yayi sama kana ya dawo ƙasa.
Yayinda ya ɗaura tafin hannunsa kan ƙirjinsa.
Cikin tsananin dariyar ya samu ya ɗan tsagaita tare da furta.
“Astagfurillah watubu ilaik�?.
Sai kuma ya ɗago ya kalli M Jameel lokaci ɗaya kuma ya sake sakin dariya mai sauti yana cewa.
“Astagafitillah Wayyo cikina�?.

Cikin rage girman idanunta take kallon gashin girarsa dake kwance lip.

Jameel kuwa sai Murmushi yakeyi tare da girgiza kansa.
Yayinda Adda Adama ma dariyar takeyi harda riƙe ciki.
Ita kuwa Khausar gaba ɗaya ta kasa ɗauke idonta daga kansa.
A haka har rana tayi mudun kuyanƙi alamun yana gab da faɗuwa.

amma kafin ya faɗi saiya rabu kashi biyu.
Yayinda Khausar kuwa ke zaune tana fuskantar yamma hakan yasata ganin abin.
Atake hankalin ta ya tashi ganin yanda ranan ya rabu kashi biyu.

Ita kuwa Adda Adama hannu tasa ta dafe ƙirjinta tare da faɗin.
“Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n yau mun shiga ukun mu ku dubi yanda ranar tayi fa!�?.
Tana faɗin haka duk dariya da murmushin da sukeyi ya tsaya.

Moddibo kuwa daga inda yake zaune ya ɗaga kansa sama tare da juyawa bayanshi kana a hankali yace.
“Ya Salam ya ilahi ya mujabat da'awati meke Shirin faruwa�?.
Cikin tsananin gigita da tashin hankali da firgici Khausar ɗin ta saki kuka mai cike da rauni tare da cewa.
“Innalillahi wa innailaihi raji'un, hasbunallahiwani'imanwakil, mun shiga uku�?.
Sai kuma ta juyo ta kalli Moddibo da ya gyara zamanshi kana a hankali yace.
“Babu abinda zai faru wanda Allah bai sani ba, Insha Allah Ubangiji zai mana maganin duk kan abinda yayi tsanani�?.

M Jameel kuwa kasa furta komai yayi sai hawaye dake kwaranya daga idanunsa.
ita kuwa Khausar ganin M Jameel na Hawaye kawai sai itama tashiga yin kuka amma ba mai sauti ba.
Cikin wani irin yanayin da bazai misaltuba Moddibo ya dubesa kafin yace.
“Haba J. Kamar ba namiji ba addu'a ya kamata muyi duk kan tsanani yana tare da sauƙi�?.
Still dai M Jameel baice komai ba.
Shi kuwa Moddibo cikin sanyin jiki ya fuskanci Khausar cikin wata iriyar murya yace.
“Khausar tausayi na kike ji ne?�?.
Cikin kwaranyar hawaye ta gyaɗa mishi kai tare da sakin raunataccen kuka mai cushe numfashi, lokaci ɗaya numfashin ta ya fara cushewa yana ɗauke wa, cikin yanayi wahalar neman numfashi taga Moddibo ya...!
Dai-dai lokacin kuwa ta farka daga baccin da takeyi ciki razana tare da kaɗuwa ta dafe kanta da takeji yana jujjuyawa.
Kana duk da sanyi da ake tsulawa a garin wani irin zufane ke tsastsafo mata ta ko ina.
Cikin sauƙe ajiyar zuciya, ta juya gefen hagunta ta karanta A'uziyya ƙafa uku kana ta canza hannun kwanciyar ta zuwa dama.
Sai dai sam baccin yaƙi zuwa mata, sai ta kama karatun Alqur'ani cikin sassayan sauti,
Cikin ikon Allah ta samu bacci ya kuma yin awon gaba da ita.

Baki ɗaya Wunin wannan ranan akasalance tayi koda abinci ta kasa ci haka zalika koda yawan surutu sai ta rage sosai mafarkin ya tsaya mata arai da zaran ta tuna irin mafarkin da tayi sai taji zuciyarta ta buga da ƙarfin gaske.

Da daddare cikin ikon Allah data karanta Alkur'ani mai girma tare da bin haddarta da Malam Liman ya bata sai taji sauƙin abin aranta duk da kuwa bawai ta daina jin tsinkewar zuciyar bane amma ya ragu sosai.
Da misalin ƙarfe takwas da rabi na dare Khausar suna zaune a farfajiya gidan Hajja Nana su uku ita Yaya Abba da kuma Dije suna hira jefi-jefi take sanya musu baki aciki daga ƙarshe ma ta miƙe tace zata je ta kwanta sai Dije ma ta miƙe ganin haka yasa Yaya Abba ya musu rakiya har gida.

Washe gari:Da safe still haka Khausar ta tashi bata da wani ku zari koda abinci ne ta kasa ci iyakacinta tasha Tea ko ruwan kunu sannan ta kasa faɗawa kowa irin mafarkin da tayi domin jikinta ya mutu sosai da mafarkin.
Da daddare ba kinta ɗauke da Sallama tashiga gidan Hajja Nana.
Asaman laɓɓa Hajja Nana ta amsa mata Sallamar tana binta da harara dan tunda taƙi markaɗa mata wake take jin haushi ta.
Ita kuwa khausar bata masan Hajja Nana nayi ba ta nemi waje ta zauna tare da kallon Hajja Nana tace.
“Yunwa nakeji ki bani abinci zanci�?.
ta faɗa tana kallon ƙorenta dake jere guda goma sha Uku.

Harara Hajja Nana ta wurga mata tace.
“Gashi ki ɗauka ki ci�?.
Kai Khausar ta gyaɗa tare da Matsawa jikin ƙoren tashiga buɗewa ɗaya bayan ɗaya tana dubawa saboda taga gidan Malam Liman anyanka kaji cikin Sa'a kuwa tana buɗe ɗayan taga Jan miyar dage-dage da kuma tuƙeƙƙen tuwon shinkafa.
Ta gyara zamanta tare da wanke hannunta ta fara cin tuwon cikin Mintuna kaɗan ta cinye tass sannan ta kuma janyo wani Ƙoren dan sosai take jin yunwa sannan bata wasa da cikinta dan ita dai ko ciwo bai cika hanata cin abinciba karo na forko kenan a rayuwarta da abu ya tsaya mata a rai har ya hanata cin abinci na kwana biyu son ta Tara yunwar shiyasa.
ta cinye ƙore biyun tas dan dama tuwon ba wani mai yawa ake samata ba tunda akwai yawan kanukan.

Hajja Nana kuwa juyawa tayi da mamaki ta kalleta kafin tace.
“Yanzu har kin cinye tuwon nan�?.
Kai Khausar ta gyaɗa mata tace.
“Na cinye mana kuma yanzu ma ƙarawa zanyi dan yunwa nakeji rabo na da abinci tun shekaran jiya da daddare fa sai dai in ta Shan abu mai ruwa-ruwa�?.

Taɓe baki Hajja Nana ta kuma yi tace.
“Toh bubbuga rumbu ga shican ki ƙara ki cinye duka ma in Kinga dama�?.
Ta Faɗa tare da tura mata wani akoshin.

Ɗauka Khausar tayi kamar wasa ta cinye dake abincin ba wani da yawa ake sawa aƙoron ba dake sun san cewa ƙorenta da yawa mafi yawan lokuta ma loma ɗaɗɗaya takeyi ako wani ƙoren idan tayi loma sha uku ya wadatar mata a dai cikin tsohuwa ta kuma tsinci nama ta cinye to shiyasa ba'asa mai yawa.

Ita kuwa Hajja Nana ganin yanda Khausar ke cin abinci yasa tayi zaton gatse take mata ta harareta da faɗin.
“Mutum kamar jaki wannan ci haka ki cinye wannan ƙoren ki cinye wancan�?.
Ta ida maganar tare da sake tura mata wani ƙoren.

Ita kuwa khausar ta ƙoshi amma saboda ta ƙular da ita yasa ta janyo ta buɗe naman kan abincin ta cinye sannan ta gutsiri kamar loma biyar ta zuba akwanan dake empty.
Wani kwanon Hajja Nana ta kuma tura mata still ta cinye naman ta kuma gutsura ta zuba a sauran kwanon.

Hajja Nana ta dube ta cikin tsareta da ido tace.
“Wai har yanzu baki ƙoshi ba?�?.

Khausar cikin yamutsa fuska ta gyaɗa kai kana tace.
“Eyyy ban ƙoshi ba�?.
Wani akoshin Hajja Nana ta sake tura mata, Khausar kuwa laluma ta cigaba dayi idan taji da nama ta cinye ta gutsits-tsira tuwon ta bari.

Ita kuwa Hajja Nana kamar wacce akace ta leƙa taga aika-aikan da Khausar keyi da tuwon ta miƙe cikin fushi tace.
“Shegiyar yarinya gantalelliya ni kike nunawa barikanci, 'yar banza kinje kin zauna gidan Mayu kema kin koma kamar Mayya, sai cin nama kamar kura, wato ma duk naman kike lalubewa dan mayta ai dai na sani in dai ba cikin zanine da keba ai yaci ki ƙoshi�?.
Ya mutsa fuska Khausar tayi tare da riƙe ƙugunta tace.
“Naci ɗin idan ni Mayya ce kinsan inda na samu maita, tunda nazo saboda shegen maƙo ko zabuwa ɗaya kin kasa yanka min gaki da Zabbi kamar zasu kashe ki ga shanu kuma aina Babana ne�?.

Salati Hajja Nana tayi tare da fashewa da kuka.
Kasancewar duk dare aƙofar gidan ta suke zama yasa Baffa Umaru daya ji sautin kukan ta ya miƙe kasancewar Allah ya bashi kunne komai ƙanƙantar sautin abu ya kan iya ji.

Ganin Hajja Nana na kuka yasa Baffa Umaru nufarta tare da cewa.
“Addah Nana Meya faru?�?.
Nuna Khausar tayi da hannu kana tace.
“Wannan ‘yar Usmanu har zata min gori wai gadon Ubanta na riƙe kaji shegiyar gantalalla yarinya dan ma Allah yayi dan ke macece!�?

Ƙasa da murya Baffa Umaru yayi yace.
“Dan Allah Addah Nana kiyi haƙuri kinsan yarinta ke damunta idan ta girma ba zatayi ba�?.
Ya ida maganar tare da jan hannun Khausar suka fice waje.

Bayan sun fita ya juya ya kalleta yace.
“Haba Khausar kidena ki koyi yanda zaki zauna da manya kinga Addah Nana tsufa ya kamata tana buƙatar rarrashi da lallami, kinga duniyar nan ba matabbata bace idan yau kaine gobe ba kai bane ita rayuwar nan bata da tabbas, ki koyi magana mai daɗi ke idan Mahaifinki ina ita fa ɗan ta ne data haifa acikinta kuma ɗan ta mafi soyuwa agareta kada ki sake haka kinji Khausar am�?.

Ta gyaɗa masa kai da faɗin.
“Toh shikenan Insha Allah bazan sake ba�?.
Ya shafa kanta yana murmushi yace.
“Allah ya miki albarka kizo muje gidana mu kwana zansa ayanka miki Zabbi kici tun da mun gama cin abinci".

Kai ta gyaɗa tare da yin murmushi tace.
“Toh�?.
Ya riƙe Hannunta suka tafi suna tafiya suna hira har suka isa gidan bakinsu ɗauke da Sallama suka shiga gidan Adda Adama ta fito daga ɗaki tare da amsa musu sallamar.

Kallon Adama Baffa Umaru yayi yace.
“Akwai nama ne?�?
Adama tace.
“Eh akwai Zabbin da aka yanka da yamma yanzu nake ƙarasa dahuwarsu�?.

Yace.
“Toh shikenan ki ƙara sa gyarasu ki kawo ma wannan Kuran Birnin taci�?.
Dariya Khausar tayi tana zama akan taburman da Adama ta shimfiɗa musu, shi kuma Baffa Umaru ya zauna daga gefenta yayin da Adama taje taci gaba da aikinta kasancewar farin wata ya haska ilahirin garin.

Anutse Baffa Umaru ya kira sunanta da faɗin.
“Khausar�?.
Ta ɗago kanta tana kallon fuskarsa acikin farin watan kafin tace.
“Na'am�?.
Idanunsa kanta yace.
“Kinsan kamannin Babanki?�?.
Kai ta girgiza masa tare da faɗin.
“A'a bansan kamanninsa ba�?.
A sanyaye yace.
“Amma kin san akwai Baffanki ai yayan Babanki Hammadu Ɓadamaya ko?�?.

Tace.
“Eh amma Ɓadamaya yake ko?�?.
Yace da ita.
“Eh yana can Ɓadamaya dashi da Iyalansa da kuma ahalinsa gaba ɗaya.
Insha Allah wataran Zakije shida Babanki Uwa ɗaya Uba ɗaya".
Kai ta jinjina da faɗin.
“Eh Mommy na tafaɗa min cewa inada Baffa yana can Ɓadamaya dashi da matarsa da kuma ‘Ya‘yansa�?.

Murmushi yayi yace.
“Toh idan kinje zaki ga mai kamannin Mahaifinki sak da sakin sunan sa Aliyu shine yake kama da Mahaifinki ya gaji Babanki komai da komai kuma shine aka aurawa yayarki Nenne�?.
Kai ta gyaɗa tace.
“Toh yaushe zanje in gansa?�?
Yace.
“Kinga kamannin Mahaifinki kamar balarabe kinga ba yabon kai ba mutanen Rugar mu duka kyawawa ne amma kyawun mahaifin ki ya fita da ban farin Mutum ne kyakkyawa ga kuma gashin kansa mai tsawo da sheƙi wannan gashin naki ma shi kika ɗauka�?.

Idanunta ta lumshe cike da kewar mahaifinta sai kuma ta buɗe su tace.
“Aikam nasan gashin sa na ɗauka ba Mamansa ba da kai agwagwiye".
Murmushinsa ya faɗaɗa da faɗin.
“Ina Addar tawa kike yiwa ba'a itama tsufa ce yasa gashinta kaɗewa�?.
Murmushi tayi tace.
“Ai lalle kam�?.

Sai kuma ta dai-dai-ta nutsuwarta tace.
“Ku kuma dama nan ne asalin Rugarku?�?.
Kai ya gyaɗa mata yace.
“Eh asali nan ne Rugar mu iyaye da kakanni�?.
Tace.
“Toh Meyesa ita Hajja Nana ta dawo nan kuma ina ne asalin garinsu Babanmu?�?
Murmushi yayi yace.
“Asalin garinsu Babanki yana da nisa lokacin da Addarmu tayi aure ta daɗe kafin tazo ta samu haihuwa to data haifi na farko sai Allah ya sake kawo wasu akan lokaci ta haifi yara uku sai Allah yayiwa kakanki daya haifi Babanki rasuwa,sai ta nemi zata dawo to data nemi zata dawo sai sukace tabarmu su yaran ita kuma tana son yaran sosai sai tace Inde akan dukiya ne tabar musu duka subarta ta taho da ‘Ya‘yanta�?.
Zama Khausar ta gyara tana sauransa da kyau.
Shi ko a hankali ya cigaba da cewa.
“Dake dangin Mahaifinki mutane ne masu karamci sai sukace su ba dukiyar su suke buƙatar ba kawai dai suna so suriƙa ganin ɗan uwansu ne sannan ita macece kada subar mata nauyi amma tunda tana son Zama da ‘ya’yanta baza su hanata ba sai suka bata duka gadon Mahaifinki da kuma na Baffanki da ƙannensa mata biyu hadda mai sunanki.

A ranar da tashigo Rugar nan tashigo da aƙalla shanu sun kai ɗari biyu sannan harda raƙuma da tumakai duk gadon sune aka ɗauka aka basu suka dawo�?.
Sassayan ajiyar zuciya ta saki tana jinjinawa lamarin.
Baffa Umaru ya cigaba da cewa.
“Toh tun daga lokacin ne zamanta ya dawo nan daga baya Allah yayiwa mahaifan mu rasuwa da gida huɗu ne kacal anan mahaifinmu su suka fara kafata da duk nan dajine mahaifinmu ne ya sare bayan rasuwar mahaifinmu da kuma mahaifiyarmu,
itace ta zame mana Uwa da uba tun muna yara itace ta renemu nida Mahaifinki mun taso tare atare mukayi wasan ƙasa ta raine mu tare ta zame mana kamar uwa Shiyasa mu awajen mu Adda Nana ba ya bace kaɗai uwa ace a garemu�?.

Ita kuwa khausar Ajiyar zuciya ta kuma saki tare da faɗin.
“Ikon Allah Allah mai iko Mabuwayi Gagara misali�?.
Murmushi Baffa Umaru yayi yace.
“Kin gane ko mu Addah Nana Uwace agaremu ba Ya ba sannan maganarta Umarni ne awajenmu muda ‘Ya’yanmu babu mai saɓa mata har jikokin mu kinga keda kika zo kina wannan abin sai akaga lallai ta samu karan tsaye�?.
Murmushi Khausar tayi tace.
“Lallai dai kam,to amma ina ne asalin su Babanmu?�?.
Murmushi yayi yace.
Gobe zan faɗa Miki Idan Allah yakaimu rai da Lafiya zan ƙara sa baki labarin insha Allahu�?.

“Toh Allah ya kaimu goben lafiya�?. Cewar Khausar

Cikin sauƙe numfashi yace.
“Naji ma Addah Nana na cewa kafin ki koma Abbah zai kaiki Ɓadamaya kije kiga Baffanki da ‘Ya‘yansa�?.

“Toh ina kuma ance da nisa?�?.
Khausar ta tambaya

“Eh danisa amma ai tafiyar wuni ɗaya ce zaku isa�?.
Ya bata amsa.

Miƙe sawunta tayi bisa taburmar tare da cewa.
“Toh shikenan ba matsala, Insha Allahu zamuje, nima ingansa sannan kodan inga mai kama da Babana�?.
Murmushi yayi tare da cewa.
“Sannan kuma kafin ku tafi zakuje kiga Addarki ‘yar Baffanki da yake Ɓadamaya tana nan Rugar Fulani dake ma ƙobtanmu Adda Ikki aikin santa?�?.
Murmushi tayi tare da gyaɗa masa kai tace.
“Eh na santa ai itakam tana zuwa har gidanmu ta dubani duk dangin Babana ma ita nafi sani�?.
Yace.
“Toh shikenan Zakije wajenta kiyi kwana biyu�?.
Tace.
“Tun kwanaki nake cewa Hajja Nana zanje in dubata, tace min ba yanzu ba, wai in bari ingama sanin mutanen garin nan�?.
Adama dake sauraron hiransu ta miƙe hannunta riƙe da kwanan da ta gama gashin Zabbin dake ta tashin ƙamshi sannan ta haɗo musu da madara mai ɗumi.
Akan tabarmu ta ajiye musu su duka ukun atare sukaci.

Gyatsa mai sanyi Khausar kana tace.
“Kai gaskiya naci naji daɗi Nagode�?.

Bayan sun kammala ne Khausar tashiga ɗakin Adama ta kwanta Adama kuwa ta nufi ɗakin mijinta suka kwanta tare.

Can cikin dare kamar misalin ƙarfe biyu Baffa Umaru

1 Comments On SAKAYYA
avatar
hajara-ahmad

1 year ago

Reply

Nice novel

Please Login or Register in order to submit comment