Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zaiyi karatu.
Jinjina kai Mommy tayi kana tace.
“Eh haka ne da wannan dan wannan amma dai ki dage kema�?.
Kai ta gyaɗa kana tace.
“Toh shikenan Mommy zan dage insha Allah amma Mommy ke izu nawa kikayi�?.
Murmushi Mommy tayi kana tace.
“Insha Allah nima zan samu uku kaman na Haiydar�?.
Ware Ido Khausar tayi tare da tura madedecin bakinta kana tace.
“Insha Allah nima zan dage duk azumi goma sai nayi sauƙa�?.
Jinjina kai Mommy tayi tare da faɗin.
“Aikam da kin kyauta amma sai kin rage baccin safe�?.
Jinjina kai Khausar tayi kana tace.
“Insha Allah zan rage�?.
Jin kiran assalatu yasa suka miƙe Haiydar ya tafi masallaci Mommy da Khausar suka shiga ɗaki suka ɗaura alwala kana suka gabatar da sallah bayan sun idar Khausar ta zauna tayi Azkharul sabah tana gamawa ta mike ta dawo falo ta gyara tare da sharewa kana ta fita zuwa kofar sashen nasu ta gama share ko ina sannan ta wuce Bedroom ta kwanta kasancewar akwai mai yi musu wanke-wanke tun kafin su shiga Sallah ta zo ta kwashe kayan ta wanke.

Ahankali azumi ya cigaba da tafiya kwanaki suna tafiya lokaci yana ja cikin ikon Allah har angama goman farko goma na marmari inji hausawa ko?. Har an shiga goma na biyu, goma na wuya ko? Yau an kai azumi na goma sha biyu.

Yayin da Aɓangaren Moddibo da M Jameel sunyi nisa acikin tafsirin Suratul Nisa sun fassara har zuwa ayoyi na tamanin da tara zasu tashi akan aya na Casa'in

Da daddare Misalin ƙarfe tara M Jameel da Moddibo ne zaune acikin masallaci gaban ko wannensu ɗauke da system da kuma roban Swan water mai sanyi Moddibo na cikin shigarsa as Usual kamar ko yaushe Jallabiya Neavy blue kansa ɗaure da Hirami M Jameel kuwa sanye yake cikin gezner blue da babbar riga.
Cike da nutsuwa M Jameel Yayi gyaran murya tare da hura Microphone ɗin kana yace.
Ya buɗe da addu'a kamar ko yaushe.

Lokaci guda masallacin ya kaure da kabbara tamkar zasu tsaga masallacin saboda yanayin zafin jinjinsa da kwarjininsa cike da sakin fuska.
Ya cigaba da cewa.
“Anma ba'ad faya Ikhwatul musulmi Assalamu alaikum warahmatullah wabarkatuhu�?.
Atare suka hada baki wajen cewa.
“Wa'alaikum Salam warahmatullah wabarkatuhu�?.

A hankali ya numfasa tare da sauƙe nan-nauyan ajiyar zuciya kana ya dubi ɗumbin jama'ar dake zaune acikin masallacin cikin tsantsar nutsuwa ya juyo da system ɗin gabansa kana yace.
“Acigaba da tafsirin Alkur'ani mai girma Amasallacin. Juma'a dake ƙofar gidan Mai martaba Sarki Gembulan Lamido Bashiru zamu cigaba da tafsirin Alkur'ani mai girma acikin Suratul Nisa'i zamu tashi a aya ta cassa'in�?.
Sai kuma ya juya ya Kalli Moddibo kana yace.
“Aramma Bismillah�?.

Jinjina kai Moddibo yayi tare da gyara zamansa kana ya ɗan jingina bayansa da jikin kujeran cikin Sanyayyar muryarsa mai cike da nutsuwa da zaƙi yayi basmala kaya ya fara karanta ayoyin kamar haka;
_�?(90)Illallazina Yasiluna Ilaƙaumim Bayna Kum wa Bayna hum misaƙun Auja,Ukum hasirat suduruhu an yuƙatalalukum.Walau sha Allahu lasallaɗhum Alaikum falaƙatalukum.Fa'in'itazalukum falam yuƙatilukum Wa'alƙau Ilaikumussalama fama ja'alallahu lakum Alaihim Sabila�?._

Moddibo ya ida kai Ayar yana mai lumshe idanunsa akuma take tsikar jikinsa suka tashi yayi saurin buɗe idanunsa tare da ƙoƙarin dai-dai-ta nutsuwarsa kana ya cigaba da furta Aya ta gaba kamar haka.
_�?(91)Satajidunah Akharina Yuriduna Anyamanukum Wayamanu Ƙaumahum kullamaraduu Ilalfitnatin Urkisu fiha.Fa'in lam ya'atazilukum Wayulƙau Ilaikumussalama Wayakfuru Aydiyahum Fahuzuhum Waƙtuluhum haysu saƙiftumuhum.Wa Ula'ikum ja'alnalakum Alaihim sulɗanammubina�?._

Wani irin numfashi M Jameel ya saki tare da rintse idanunsa kana jikinsa ya ɗauki tsuma yana mai jin fassarar Ayar na yawo Atsakiyar kansa Atake kuma zuciyarsa ta cigaba da bugawa da kaso tamanin cikin ɗari.
Yayinda gaba ɗaya al'ummar dake cikin masallacin dama wajensa sit kakeji kamar ba mai numfashi sabida tsananin yadda sautin karatun ke ratsa musu zuƙata da ƙoƙwale.

Shi kuwa Moddibo ya kai minti ɗaya kafin ya saki gauron numfashi gaba ɗaya jikinsa yayi sanyi sabida sanin ma'anar ayoyin da zai kawo a gaba, cikin wani irin raunin tare da tsoron Allahu wahidun ƙahhar, gaba ɗaya muryarsa ta sake rauni cikin dakiya ya cigaba da Karanta Ayar Kamar haka.
_�?(92)Wama kana limu'uminun An yaƙtula Mu'uminan Illakhaɗa'a.Waman ƙatala Mu'uminan khaɗa'a fatahriru Raƙbatatin Mu'uminatin wadiyyatun Musallamatu Ila'ahlihee Illah An yassaddaƙun.Fa'in kana min ƙaumin Aduwwillakum Wahuwa Mu'uminun Fatahriru Raƙbatin Mu'uminatan.Wa'in kana min ƙaumim baynakum wa baynahum miysaƙun Fadiyyatun Musallamatun Ila Ahlihi watahriru raƙbatin mu'uminatin.Famallam yajidu fasiyamu shahraini mutatabi'ayni taubatan Minallah.Wakanallahu Aliman hakima�?._

Wani irin nutsuwa cikin masallacin yayi musamman ma wa'anda suka san fassarar ayoyin wa'anda basu san fassarar ba kuwa mu'ujiza ta Kur'ani ta dinga ratsasu tare da Sanyayyar sautin Muryar mai karatun.
Moddibo kuwa idanunsa ya lumshe sakamakon wasu zafafan hawaye masu ɗumi da suka cika cikin ƙarfi ya furzar da iska mai zafin gaske Tabbas kashe ran mumini baƙaramin tashin hankali bane amma baki ɗaya awannan zamanin an maida rai ba abakin komai ba.
Ya gyara zamansa tare da cigaba da karantar Ayar kamar haka.
_�?(93)Waman yaƙtul mu'uminan Muta'ammidan Fajaza's'uhu Jahannama! halidan fiha wagadiballahu Alaihi wala'anahu! wa'aaddalahu Azaban! Azeeymah!!!!!”_.

Awannan lokacin hawaye ne suka ciko idanun Moddibo jin irin tsananin azaban da Ubangiji ya tana darwa duk wanda ya kashe ran mumini batare da wani hakkiba.
Walahabahu la'anar Ubangiji kana fajaza'ahun jahannamu khaleedan fiha, fa ubangiji yace kana aka ɗaura da Azaban Azeeymah!!!, Duk wannan tanadinefa da Ubangiji yayiwa mai kashen ran mumini da gangan.

Wani irin rawa jikin Moddibo keyi tamkar wanda aka konawa wuta a jikinsa cikin tsananin sheshsheƙan kukan da yake son dannewa ne ya bu ɗe baki a hankali dan kawo aya ta 94 sai kuma ya juyo cikin tsananin rauni ya kalli M Jameel da gaba ɗaya j....



*WOHOHO IN KAJI ANA ƘI GUDU TABBAS SA GUDU NE BEZO BA*

_Ina kuke Ma'aurata masu sha'awar ganin sun zama taurari kuma fitilu a idanun mazajensu Uwar gida,Amarya,Tsakar gida,hadda tan kaɗen gida Shararriya kuma ƙasaitacciya data saba kawo muku nau'ikan sirrin sahihan magungunan ma'aurata wato *AYSHA ALIYU GARKUWA* Garkuwar Marubuta ayau ma ta dawo muku da Ingantattun magungunan mata masu kyau da inganci domin gyara kanki ki zamto tauraruwa a idanun mijinki...Muna da Ingantattun Abubuwa kamar haka_ :_Munada Garin mallaka, garin maɗi, garin Hakkin mayi, garin ɓelɗamhi Garin ilanwaddihi, Gumbar da ba'a baiwa mai kishiya, Gumbar kolli mai kellin al'khairi, Gumbar Riɗi wato 3 in 1, Gumbar makwaranyi, Masin Maliƙi mai masifar ƙarfi da matse mace, ka masin Daɗi har Maɗigan Akwai, kwanon ƙasaitacciyar mace mai masifar kyau da ratsa jiki da samar da inƙantacciyar ni'ima yanada abubuwa masu kyau haɗinsa, Zumar goron tula mai masifar kyau, tsumin dabino, mai ratsa jiki, tsumin Riɗi mai ƙarfi, Furar Mata mai tsastsafo da ni'imantaccen damshi, Cida kaza, Ciccibi Abodi, Tsumin Ɓaure, tuwon ɓauren, kana akwai maganin sanyi sadidan, da dai sauransu...Se kuma fannin ƙamshi kasance da Shu'umin ƙamshi wanda ze gigita ƙwaƙwalwar Oga tare da jin ko wacce mace bata kaiba...._ _Shin ko kina da labarin Miskilinci da ƙasaitar Rayyan Naaan amma lokaci ɗaya ya zamto zautacce sakali akan soyayyar Jannart bakomai Jannart ta riƙe ba face sirrinkan gyara da kuma shu'uman humran da kulaccar sirri na Aysha Aliyu Garkuwa(Tubali) tabbas taga tasirin haka domin Naanunta ya zame mata tamkar bawa_
_Shin ko kinsan sihirtaccen haɗin da Aysha ke sha kenan ta zamto tauraruwa a idanun Hamma Yusuf(Miwasmiti)...Tabbas Mahmud ya zamto zautacce kuma makaho akan sauyayyar Bazawara wato khadijarsa duk da kuwa gashi da budurwa(Namiji Baya Kaɗan) ko kinsan hakan nada alaƙa da amfani da sahihan maganin da kuma shu'uman humran Aysha Aliyu Garkuwa??.Nasan ba zaka ku manta da irin kima da kuma darajar da Aysha ke dashi acikin Idanun Sheik Jabeer ɗin ta duk da kuwa shekaru sunja anma jinta yake tamkar budurwa 'yar sha bakwai(Garkuwa) sirrin hakan na tare da Ingantattun kuma sahihan magungunan Aysha Aliyu Garkuwa Wato Garkuwar Marubuta da kuma Ma'aurata na tabbata kunsan da cewa basirarta ba'a iya rubutun littafi ya tsaya ba hadda inganta rayuwar ma'aurata ta hanyar kawo musu Nagartattun abubuwa Ga duk wacce ta shirya saya seta tuntuɓi number ta 09097853276 muna iya tura kayan mu aduk inda kuke afaɗin Nigeria harma da ƙetare Dan Allah 'yar uwa idan baki shirya siyaba kada kiyi min magana muɓatawa kanmu lokaci...._



🤝🏻🤝🏻🤝🏻🤝🏻🥰😘sai.kunzo. sayan na gari maida kuɗi gida,



*By*
*GARKUWAN MARUBUTA*
9/13/23, 20:03 - Buhainat: 📝✨💫⏰🤴🏻👹❤️❤️❤️🍇
*SAKAYYAH*
_page 16_

_NA_
*AYSHA ALIYU GARKUWA*

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*In sha Allah daga gobe zan gama free page, ƴar uwa baki makara ba ki biya ki karanta cikin Aminci littafin SAKAYYAH 1k ne kacal 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276 daga wannan page ɗin sai na gobe mun gama free page, ki biya yafi sauƙi tsira ba haƙƙin kowa kanki.*



*GARKUWAR* taku ce dai MA'AURATA, da masu shirin aure, da masu jego, da yan gayu masu son k’amshi kece raini, da gyaran da zaike maimaita muku dararen forkon kuruciya*

Ko kunsan Jikinmu na da sinadaran hormones da suke taimakawa dan’adam akan komai musamman lokacin da mace take mu’amalar aure da mijinta. Mafi akasari wannan hormones din ne ke samun matsala ko su yi sanyi koma su daina aiki kwata-kwata shi ne dalilin da zai sa mace tace bata jin sha’awa ko bata san dadin aure ba. Albishirinku ina da kayan da ke taimakawa wannan sinadaran du dawo aiki tukuru don karkato miki da kimarki wajan mai gida sannan su taimakawa wannan sinadaran hormones dinki su dinka secreting din ni’ima wadatacciya da zata taimaka miki ki gamsu mijinki ya gamsu fiye da tunaninki. Note: Kayana ba sa tsinka ruwan ni’ima suna dai taimakawa hormones dinki ne su tsattsafo da ni’imar musamman wacca cutar sanyi ko dattin mahaifa ya dankarar da su ya hana su yin aikinsu yanda ya kamata. Haka zalika idan kina da kyau ki kara da wanka. Zaki iya amfani da magani na na gargajiya wanda zai gyara miki sex hormones din kullum ki kasance cikin humidify wato cikin damshi mai albarka kamar yanda ake son mace. Yana gyara miki mara.

Sai kamshi. Hajiyata daure ki fara amfani da turarena ki ji irin salon kamshin sa salo ne da zai daidaita ki da mijinki ya kankaro miki da kimarki a wajansa. Siyan na gari mayar da kudi gida.

Ga masu buƙata ga number' wayata wanda nake whatsApp dashi 09097853276 kimin mgn ta whatsApp in har kin tabbatar kin shirya saya mu dai-dai ta, kayana ba ƙanana bane, shiyasa bana harkan karanta, muddin kinsan baki shirya sayaba Please kada kiyi min mgn ki bari sai kin shirya kuɗinki a hannu, ba ina nufin kayana bana talaka bane, no akwai ƙananan set na masu karamin karfi, banson aimin mgn a ɓatamin lokacin aiyukana a shirme baki shiryaba. Shine karantan da bana so.
0005388578 Jaiz bank AISHA GARKUWA ALIYU. In kin shirya ga number ta ga kuma account number ta wanda in mun gama mgn zaki turo kudin ki, kana insa miki kaya a mota, duk ƙasar da kike kayana zaije gareki, amman fa in kinada dalilin zuwan nasune🤝🏻sayan na gari meda kudi gida.


GARKUWAR MA'AURATA

Shiko M Jameel Wani irin tsuma ilahirin jikinsa keyi sakamakon tuni da ayoyin sukayi mishi na jin azabar da Ubangiji ya tanadar wa da duk wanda ya kashe ran mumini da gangan ba tare da wani haƙiba.
Cikin raunin murya me cike da tsananin tsoron Ubangiji M jameel ɗin ya kawo fassarar aya na 90 da kuma 91, tsit gaba ɗaya masallacin yayi babu abinda ke tashi sai sautin kukan M Jameel daya kasa ci gaba, yayinda kukansa yasa da dama cikin mutanen yin kuka.
Middibo kuwa kife tafukan hannunsa yayi kan fuskarsa yana maiyin wani irin sassayan kuka mai masifar sa rawan jiki, gaba ɗaya fuskarsa tayi jazir.
Cikin ƙarfin hali M Jameel ya fara mgn cikin rawan murya yace.
“A cikin suratul Nisa, Aya ta 92 Allah ma ɗaukakin sarki na cewa, 92:
-:Baya halasta ga mutum da ya kashe ran mumini, sai dai idan ya kasance kuskure ne.�?.
Sai kuma ya tsagaita tare da sayan tafin hannunsa ya share hawyen daketa kwaranyowa da idanunsa, cikin rawan murya yaci gaba da cewa.
“Duk wanda kuma ya kashe! Mumini da kuskure toh, zai ƴanta wuyan Muminin, sannan ya bada Diyya ga iyalan wanda ya kashe�?.
Sai kuma ya dire ayar mgnar tare da rushewa da zazzafan kuka mai cike da tashin hankalin da raunata zukata aya ta 93.
Cikin rauni yasa hannu ya karɓi hankicif ɗin da ɗan agajin dake bayansa ya miƙa masa, sharce hawayensa yayi tare da juyowa ya kalli Moddibo da gaba ɗaya jikinsa rawa yake sai sheshsheƙan kuka mai fuzge numfashin da yakeyi, bazai iya hana kansa kuka ba, bare ya samu iko da damar hana aminin nasa.
Cikin sheshsheƙan kuka M Jameel ya gyara zamanshi tare da cewa.
“Huymmmm, a kuma cikin suratul Nisa ɗin ayata 93, Allah madaukakin sarki nacewa-:
(Duk wanda ya kashe Mumini bisa ganganci, ko Mugunta da zalumci. Toh Sakamakonsa shine wutar Jahannama�?.
Sai kuma ya sake sakin wani irin raunataccen kuka mai cike da tsoro kana yaci gaba da cewa.
“Allah madaukakin sarki cewa yayi-:
Duk wanda ya kashe ran mumini zai dawwamane cikin jahannama, kuma Allah yayi fushi dashi, sannan kuma ya tsine masa�?.
Kawai sai ya kife kansa bisa Table ɗin dake gabansa, shar-shar haka hawayensa ke kwaranyar babu ƙaƙƙautawa.
Modibbo kuwa cire tafukan hannunsa yayi bisa fuskarsa tare da dafa kafaɗar M Jameel ɗin kawai saka sufashe da kuka a tare, cikin kukan murya na rawa M Jameel ya buɗe baki da nufin zaiyi mgn amman ina ya kasa.
Haka yasa Moddibo rumtse idanunsa kana murya na rawa yace.
“Bayan fushi da tsinuwar ubangiji Allah Mabuwayi da komai baya ɓuyar masa yace.
-:Wa ahdalahun Azaban Azeeymah).
Ma'ana ya tandarwa duk wanda ya kashe ran mumini da ganganci Azaba mai girma!!!!.�?
Zuwa lokacin wasu daga mutanen cikin masallacin kuka sukeyi da sheshsheƙan mafi akasari kuma duk jikinsu yayi sanyi.
Shi kuwa Moddibo cikin rauni da sanyi yace.
“Duk waɗannan ugubobin sun ta'allaƙane ga wanda ya kashe ran mumini da ganganci, sakamakonshi Jahannama, kuma a cikinta zai tabbata, sannan Allah yayi fushi dashi, kana ya tsine masa, kuma ya ƙara masa da azaba mai girma.
Wannan masifa har ina ɗan adam zai kaishi koda iyayenka ne sukayi fushi da kai taɓewa kakeyi bare Ubangijin talikai, koda iyayenka ne suka tsine maka lalacewa kakeyi bare tsinuwar Allah, sannan azaba koda ta tururin tea ne tsoronsa muke bare kuma tabbata ta jahannama sannan da tanadin azaba mai girma�?.
Kawai sai lips inshi suka fara rawa kar-kar shima ɗin ya kasa ci gaba.
Ganin hakane yasa M Jameel sharce hawayensa tare da cewa.
“Aramma kawo mana dukkan wata Ayar Al,qura'ani da Ubangiji yayi magana akan duk wanda ya kashe ran mumini�?.
Cikin tsumar jiki tare da wata raunatacciyar murya mai cike da tsananin tsoron Ubangiji da kuma sanin hukuncin wanda ya saɓa masa Moddibo yayi gyaran murya dai-dai zai fara karanta Ayar manyan Malaman dake wajen suka nuna musu agogon dake liƙe a can bayansu a jikin gini.
Wanda hakan ke musu nuni da alamar lokaci yayi.

Nan-nauyan ajiyar zuciya M Jameel ya sauƙe tare da share ƙwallan da suka zuba masa kana cikin raunin murya yace.
“Lokaci yayi sai dai idan Allah ya kaimu gobe zamu ɗaura daga inda muka tsaya�?.
Ya sauƙe nannuyar Ajiyar zuciya tare da cewa.
“Ya Allah Ubangiji yabamu zaman lafiya ya Allah karabamu da sharrin ƴan bindiga daɗi Ubangiji ya tsare mu da sharrin kidnappers Ubangiji ya bamu zaman lafiya Allah yajiƙan iyayen mu da duk kan musulman da suka rigamu gidan gaskiya.
Wa subhanakallahumma wabi hamdika ash shahadula'ilahu. nastagfirka wanatuubu Ilaik�?.
Tunda ya fara addu'ar suke Amsawa da Ameeen har aka shafa.
Mata ne suka fara fita kafin maza.

Acan ɓangaren Khausar kuwa, bayan ta koma gida kai tsaye Bedroom ɗinta ta wuce batare data shiga wajen Mommy ba, tana shiga ta kwanta lamo akan gado hawaye na tsiyaya daga kyawawan Idanunta sosai.
Tafseer ɗin da M Jameel Yayi ya riƙa ratsa jikinta har ƙwaƙwalwar kanta Muryar Modibbo kuwa har yanzu yana ratsa kunnuwanta, da haka bacci ya ɗauketa batare data shirya ba.
Washe gari Da safe still haka Khausar ta tashi cikin mutuwar jiki Anutse ta fito daga Bedroom ɗin ta zauna agefen Mommy dake falo.
Lumshe Idanunta tayi kana cikin sanyin murya tace.
“Mommy ina kwana�?.
Anutse Mommy ta maida kallonta gareta tare da na zartan yanayin ta batare data amsa gaisuwar data mata ba ta jefo mata tambya tare da cewa.
“Meke damunki Khausar na lura tun jiya jikin ki Asanyaye�?.
Ɗago Kai Khausar tayi Idanunta cike da ruwan hawaye kana cikin sanyi murya tace.
“Wallahi Mommy tun jiya da muka je wajen tafsir ɗin da Malam M Jameel yayi jikina ya mutu hankalina ya tashi gaba ɗaya na rasa mai yasa tsoro ya kamani�?.
Miƙewa Mommy tayi tare da matsowa kusa da Khausar ta shafa kanta kana tace.
“Babu komai wannan masiface-masiface ne da Allah ya jarabci Al'umma wannan ƙarnin saidai mu dage da addu'a Allah ya yaye mana ya kuma tsaremu da faɗa wa mummunar ƙaddara Allah ya rufa mana asiri ya karemu da zamewa sanadin mutuwar koda kadagare ne�?.
Jinjina kai Khausar tayi tare da cewa.
“Ameen�?.

Acan gidansu Moddibo kuwa Innayi ce zaune atsakar gida ta zabga tagumin tunda taji tafsirin da M Jameel sukayi jikinta yayi masifar sanyi wani irin tsoron Allah mara misaltuwa tashiga hakan fargaba ya rufeta.
Washe gari.
Da hantsi A hankali Moddibo da M Jameel suka fito, Moddibo na sanye cikin Shigarsa as Usual Jallabiya Sky blue mai yauƙi da santsi kansa ɗaure da farin Hirami kana takalmamsa farare jikinsa na fitar da sanyayyan ƙamshi turaren Oud Khareem na tashi.
Shima M Jameel sanye yake cikin irin shigar Modibbo jikinsa na fitar da sanyayyan ƙamshi kai tsaye sashen Innayi suka nufa,Innayi dake zaune gaban barandar akan kujera ƴar tsugunno ta ɗago kai ta kalli Moddibo da M Jameel kawai sai taji Idanunta na tsats-tsafowa da ruwan hawaye.
Tsayuwa Moddibo ya gyara kana yace.
“Ya dai Innayi�?.
Idanu ta zuba masa batare data iya furta komaiba kawai sai hawaye suka shiga kwaranya daga idanunta.

Cikin yanayin tashin hankali Moddibo ya tsugunna agefenta na dama yayin da M Jameel ya durƙusa agefenta na hagu kana suka haɗa baki tare da cewa.
“Innayi ya dai me yasame ki?�?.
Kallonsu tayi hawaye na cigaba da kwaranya daga idanunta ta sauƙe numfashi kana tace.
“Wa'azinku na jiya ya ratsa jikin mutane wa'azin yasa mutane acikin ɗimuwa wa'azinku na jiya ya tunatar sannan yasa tashin hankali kuma wannan zamanin muna fama da Masifa Allah dai ya yaye mana jiya hankalina atashe yake domin ire-iren abubuwan akeyi!�?.
Jinjina kai M Jameel yayi tare da sauƙe numfashi kana yace.
“Hakane sosai ma Innayi amma mu cigaba da addu'a babu abinda ya gagari Ubangiji ga dama yazo watan Ramadan muyita addu'a Allah ya yaye ya taƙaita ya sauƙaƙa mana�?.
Atare Modibbo da Innayi suka amsa da.
“Ameeen�?.
Miƙewa M Jameel da Moddibo suka atare kana M Jameel ya Kalli Innayi tare da cewa.
“Toh Innayi zamu tafi Tafseer A masallacin makarantar mu�?.
Jinjina kai Innayi tayi kana tace.
“Ubangiji Allah ya tsare ku ya kuma sake ɗaukaku�?.
Ameeen suka amsa tare da juyawa zasu fita har sun kai ƙofa Innayi ta ɗan ɗaga sautin Muryanta tare da cewa.
“Yauwa wai niko ya batun tafiyar mu ne?�?.
M Jameel ya juya tare da cewa.
“Komai ya kammala na tafiyar mu Insha Allah ranan sha biyar ga wata zamu tashi misalin sha biyu da rabi na dare jirginmu zai tashi jibi kenan ba in sha Allah, kuma sai munyi tafsir ɗin ranan ma zamu tafi Taraba�?.

Kai ta gyaɗa kana tace.
“Allah ya nuna mana Ubangiji Allah ya kaimu lokacin lafiya amman kuma kace sai kunyi tafsirin ranar?�?.
Kai ya jinjina tare da cewa.
“Eh kinga Tara na dare zamu fara, goma zamu tashi, dama kuma kafin mu tafi zamu gama shirin mu duka, tsananin mu Gembulan da taraba kuma tafiyar awa ɗaya da rabine, kinga kenan sha ɗaya da rabi zamu isa, zamu samu awa ɗaya ma acan kafin mu tafi, Abba na kuma su gobe nema zasu tashi�?.
Cike da gamsuwa Innayi ta jinjina kai tare da amsawa.
“Allah ya kaimu lfy�?.
Ameeen suka amsa a tare kana suka fice mota suka shiga M Jameel ke Driving cikin nutsuwa har suka isa masallacin.

Suna shiga suka fars gabatar da tafsirin kamar yanda suka saba ƙarfe ɗaya da rabi dai-dai suka gabatar da sallah Moddibo yayi limanci bayan sun idar suka cigaba kiran sallar La'asar yasa suka dakata da karatun tare da miƙewa suka gabatar da sallah bayan sun idar suka fito suka shiga mota awannan lokacin ma M Jameel ke Driving har suka iso gida.
Hong M Jameel Yayi Modibbo ne ya fita ya buɗe musu.
Anutse suka fito tare da furta Bismillahi,
Ahankali Moddibo ya gyara tsayuwarsa tare da fesar da sassayan numfashi.
Ido ya tsirawa bishiyar Ayaba da iska ke kaɗawa har na tsawon sakonni goma, sai kuma ya maida kallonsa kan Bishiyar mangoro Idanunsa ya lumshe domin Allah ya sani ganin sirrai ya fiye mishi ganin komai daɗi. sannu ahankali ya riƙa tuna lokacin da yarinyar tashigo gidan har tayi nasaran hawa reshen bishiyar mangoro mai girma da tsawo, da kuma sanda ta faɗo akan yatsun ƙafarsa.
Da sauri ya buɗe idanunsa
Tare da jan dogon tsaki mai cike da tsanar lamuran yarinyar. Idanunsa ya juya jin M Jameel na cewa.
“A.J tunanin mai kakeyi haka ka tsiwara Bishiya ido?�?.
Sanyayyar Ajiyar zuciya Moddibo ya sauƙe tare da furzar da iska mai sanyi daga bakinsa kana yasa hannu ya shafa kwantaccen Sajen fuskarsa ya maida kallonsa kan M Jameel da har zuwa lokacin shiyake kallo,Ya mutse fuska yayi kana yace.
“Babu komai�?.
Daga haka ya wuce gaba Kai M Jameel ya Girgiza tare da bin bayansa suka shiga Babban falon Moddibo da komai ke kimtse sai tashin ƙamshi yake.

Zama M Jameel Yayi akan 3sitter tare da faɗin.
“Wash' Allah!�?.
Kallonsa Moddibo yayi amma bai ce komai ba Bedroom ya nufa tare da janye Hiramin kansa kana ya cire jallabiyar dake jikinsa ya buɗe ƙofar toilet da addu'a
Kana yashiga shawer ya sakarwa kansa yashiga cuɗe jikinsa ya ɗauki kusan minti ashirin kafin ya fito zama yayi agaban Dressing mirrow ya shafa Mai sama-sama kana ya miƙe ya sanya Jallabiya Maroon colour da farin hirami. Feshe jikin sa da turarukansa masu daɗin ƙamshi yayi. shima M Jameel wanka yayi tare da sauya kan jikinsa zuwa Jallabiya fari kana ya ɗaure kansa da Maroon Hirami Sosai sukayi kyau atare suka fito zuwa farfajiyar gidan anan suka samu Innayi da Asma'u na aikin abin buɗa baki kallon Innayi dake soya ƙosai yayi sai kuma ya maida kallonsa kan Asma'u dake dama kunun sadaka na masallaci har ta gama ta rufe sai kuma suka bita da ido.
Kallon Asma'u dake kwaɓa fulawa, kuka, da kanwa M Jameel Yayi yace.
“Yau kuma ɗan wake ake mana ne Asmeey?�?.
Kai ta jinjina kana tace.
“Eh dan naji jiya Yaya Moddibo nacewa ɗan wake mukayi ne shiyasa yau nace bari ayi�?.
Murmushi Moddibo yayi ya mai binta da wani irin amintaccen yace.
“Kai kin kyauta mun kuwa, kwana biyu bamuci ba inaga tunda azumi ya kama kamar baku yimana shiba�?.

Kallonsa Asma'u tare da ce wa.
“A'a munyi amma ranan baka ciba agidan Ummi kuka sha ruwa ranan�?.
Jinjina kai yayi yace.
“Toh yau kam Insha Allah zamu dawo muci ɗanwaken nan�?.
Murmushi tayi ta na jefa ɗan waken da cokali tace.
“Allah ya dawo daku lafiya�?.
Ameeen suka amsa kana suka mayar da Kallonsu kan Innayi dake musu gashin Zabbi sai tashin ƙamshi yake.
Idanu M Jameel ya lumshe yace.
“Innayi zamu wuce�?.
Da murmushi afuskarta ta kallesu tace.
“Ubangiji Allah ya tsare�?.
“Ameen�?,Suka amsa sannan suka fice atare kai tsaye masallacin Juma'ar da suke limancin suka nufa cike da nutsuwa da kuma kamala suka gabatar da tafsirin Alkur'ani acikin Suratul Zariyat yayin da Moddibo ke jan baƙi M Jameel na tafsiri ƙarfe shida dai-dai suka tashi.

Anutse suka fito daga cikin masallacin suka shiga mota akuma dai-dai lokacin wayar M Jameel ya hau ruri cike da nutsuwa ya gyara zamansa tare

1 Comments On SAKAYYA
avatar
hajara-ahmad

1 year ago

Reply

Nice novel

Please Login or Register in order to submit comment