Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Raudat ta fashe dashi tana cewa.
“Ni zan biki�?.
Zama Khausar tayi ta riƙe hannunta tare da langwaɓar da kai tace.
“Raudat garin bashi da daɗi fa, ga tsohuwar garin ta fiye masifa, kana yi mata kuskure kaɗan zata zane Mutum�?.
Jin haka yasa Raudat ta girgiza kai tace.
“Nide ba zanje ba idan haka ne�?.

Aɓangaren Momy kuwa bayan tashiga turakar Lamiɗo sunyi shirin kwanciya ta dubesa fuskarta ɗauke da murmushi me sanyi tace.
“Uhum wai ɗazu Khausar ke cemin idan Allah yakaimu gobe tana son zuwa Rugar Jauro Yaya�?.
Zamanshi ya gyara tare da faɗaɗa Murmushin dake fuskarsa kana yace.
“Allah ya kaimu hakan nada kyau idan yaso tunda gobe weekend ne zamuje dukan mu kema sai ku gaisa tunda kinyi shekaru baki jeba�?.
Kai ta jinjina kafin tace.
“Kai naji dadi Allah ya kaimu�?.
Amin yace kana sukaci gaba da hirarsu.

Washe gari Ya kama asabar da wuri Khausar ta tashi ta gyara ɗakinta sannan ta nufi ɗakin Momy ta gyara kana ta share har zuwa falo da kuma duk sashen saida ta gyara ko wani lungu da saƙo.
Bayan ta gama ta dawo ta shiga kichen ta zuba musu Breakfast soyayyan cheaps da tea ita da Raudat ke ciki.
Bayan sun kammala ta miƙe tana ƙoƙarin tattare wajen Momy tashigo Idanunta akan Khausar.

fuska ta ɗan tsuke tare da faɗin.
“Maza kije yanzu Aunty Jamila tayi Miki kitso�?.
Aunty Jamila matar ƙani Lamiɗo ne sannan Momy tasan inba tayiwa Khausar dagaske to baza taje ba domin bata ƙaunar kitso.

Ganin fuskar Momy babu walwala yasa Khausar gyaɗa kai tare da shiga Bedroom ta ɗauko dogon hijabinta fari Nevy blue daya sha ninkin guga ta ɗaura akan riga da wandon dake jikinta kana ta fice ta nufi gidan Aunty Jamila tana zumɓura baki da kuma kifiya da kum a hannunta.

Bakinta ɗauke da sallama tashiga gidan, Aunty Jamila dake zaune ta amsa Sallamar tana faɗaɗa fara'ar dake fuskarta tace.
“A'a Khausar kece?, sannu da zuwa�?.
Sake fuska Khausar ta ɗanyi tace.
“Eh nice Aunty wai kitso nazo kiyi min zanje Jauro Yaya�?.
Murmushi Aunty Jamila tayi tare da cewa
“Masha Allah kice zakije ziyara?�?.
Kai Khausar ta gyaɗa tana murmushi.
Cikin sakin fuska Aunty Jamila tace.
“Allah Ya kaiku lafiya".

“Amin ya rabbil izzati�?.
Cewar Khausar.
“Kinga kuwa kinyi sa'a duk na gama aiyuka na�?.
Da sauri tace.
“Aunty Jamila manya fa zakiyi shida ko takwas�?.
Murmushi Aunty Jamila tayi.
Kana ta miƙe ta shiga ɗaƙi tare da kwantar da yaronta kana ta fito,
Akan kujeran roba Khausar ta zauna ita kuma ta tsaya ta fara yi mata kitson suna cikin kitson ne suka jiyo Sallamar Gimbiya Dadu.
Anutse Aunty Jamila ta ɗago kanta fuskarta ɗauke da murmushi tace.
“Sannu da zuwa Mama�?.
Asaman laɓɓa Gimbiya Dadu ta Amsawa Aunty Jamila baki ɗaya nutsuwarta da hankalinta suna kan Khausar.
Miƙewa Aunty Jamila tayi tashiga ɗaki dan ɗaukowa Gimbiya Dadu Darduman zama.

Ita kuwa khausar ahankali ta ɗago kanta caraf Idanunta suka sauƙa akan Gimbiya Dadu data tsareta da ido ita kuwa khausar cikin hanzari tayi ƙasa da idanunta tana mai karanto duk wata addu'ar da tazo bakinta kamar minti ɗaya Khausar ta sake ɗago kanta akaro na uku still Idanun Gimbiya Dadu na kanta.

Ita kuwa khausar kasa jurewa tayi ta tsayar da Idanunta akan Gimbiya Dadu cikin dakiya tace.
“Wai dan Allah Gimbiya Dadu Meyesa kike kallona haka?�?.
Wani murmushi mai cike da ma'anoni Gimbiya Dadu tayi tare da cewa.
“Uhum yaro man kaza,
ai tunda kika bar cikin Awaki 'yan uwanki kika dawo cikin Kuraye ai dole akalleki! In kalleki in kuma�?.
jin abinda Gimbiya Dadu tace yasa ta miƙe cikin rawan jiki da alamar tsoro aƙwayar Idanunta ta sanya hijabinta ta fita batare data jira Aunty Jamila ta fito ta ƙarasa yi mata kitson ba...

Sauri-sauri gudu-gudu take tafiya har ta isa bakin gate dinsu da sassarfa ta shigo coumpund ɗin su har yanzu jikinta be daina ɓari ba tana gyara zaman hijabin kanta Momy ta fito,Kallonta Momy tayi tare da cewa.
“Har angama kitson ne".
Ka ta gyaɗa mata ba tare da tace komai ba.
“Dama yanzu zan aika Haiydar ya kira ki kizo mu tafi�?.
Murmushin karfin hali ts ƙirƙira kana tace.
“Eh mun gama�?.

Wuce ta Momy tayi taje tashiga gaban mota Ita kuwa khausar kallon Raudat, Ramadan, da kuma Haiydar dake tsaye tayi tare da ɗaga musu hannu suma hannu suka ɗaga mata ahankali ta juya ta nufi wajen motar tana isa tasa hannu ta buɗe tashiga gidan baya Haiydar da Ramadan na cigaba da ɗaga mata hannun.
Babban gate mai gadin ya buɗe musu kana Lamiɗo ya cilla hancin motarsa.
Khausar kuwa jingina bayanta ajikin motar tayi tare da lumshe Idanunta zuciyarta na bugawa da mugun sauri abu biyu ne suka yiwa zuciyarta ƙawanya na farko hukuncin da Moddibo zai ɗauka akanta na biyu kalaman Gimbiya Dadu wanda suke ƙara tabbatar mata da zantuka dake yawo a gari cewa matar nan mayyace...

Anutse Momy ta dubi Moddibo dake sharara gudu akan Lafiyayyan titin nasu tace.
“Abban Haiydar gudun nan baiyi yawa ba�?.
Kanshi ya ɗan jujjuya mata,
Ita kuwa cikin sanyi tace.
“Gsky dai ka rage gudun kamar yayi yawa�?.
Juyowa yayi ya kalleta da murmushi a fuskarsa yace.
“Lokaci na tafiya kinga yanzu goma tayi gwara mu isa da wuri kada rana tayi mana mu samu mu juyo da wuri�?.
Kai ta gyaɗa kafin tace.
“Amma duk da haka arage gudun".

Tattausan murmushin ya sakar mata tare da gyaɗa kai...

Sunyi tafiya mai tsawo kafin suka fara hango garin Atake suka fara tabbatar da sanyin da ake acikin Gembila wasa ne.
Domin tun kafin su shiga garin suka hango tamkar hayaƙi ke tashi saboda masifaffen sanyin da ake tsugawa acikin Jauro yaya suna shiga cikin garin suka fara ratsa bishiyoyi masu korayen ganye suna rangaji tare da fitar da sanyayyan Iska kasancewar hantsi ne duk makiyaya sun tafi se kuma,
'yan dalo da aka ɗaɗɗaure masu kyan launi ga kuma kukan tsuntsaye dana zabbi da ke tashi suna ajiye ƙwai.

Suna shiga tsakiyar Rugar Jauro,
kai tsaye ƙofar gidan dake kusa da babbar fadan Rugar suka nufa anan sukayi parking motar tare da fitowa.

Wasu dattawa dake zaune aƙofan masallacin dake kusa da babbar fadan suka taso baki ɗaya idanun su akan Khausar data fito daga mota tana gyara zaman hijabinta suna faɗin.
“Audiii Barka da zuwa kece?�?.
ɗaya daga cikin dattijon ne ya taso wanda ya kasance shine Jauron garin ya riƙe hannun Khausar.
Fuskarsa ɗauke da murmushi yake faɗin.
”Addah, Addah, Addah, kizo ga Khausar�?.
sauran ma bin bayansu sukayi zuwa cikin gidan suna masuyiwa Momy da Lamido Barka da zuwa.

Biyu daga cikine suka ce da Momy da kuma Lamiɗo.
“Sannunku da zuwa ya kuka tsaya ku shigo daga ciki�?.
Kai Momy ta gyaɗa kana suka yi musu godiya bisa jagoranci suka nufi cikin gidan.
Jauro kuwa yana riƙe da hannun Khausar yana mata wasa da faɗin.
“Iyeee girman falo ji jiki kamar auduga,
bakisan riƙe sandar kiwo ba sannan baki san ta tsar nono ba girman burodi wayon shayi kawai�?.

Ita kuwa khausar hannu ta wara da faɗin.
“Ban iya ba kam�?.
Murmushi yayi kana yace.
“Zamu koya muki ai�?.
maƙale kafaɗa tayi tace.
“Bana so ba kace min girman bread wayon tea ba�?.
Murmushi yay i tare da cewa.
“To girman fura da nono�?.
Akuma dai-dai lokacin suka shiga ɗakin tsohuwar wanda yake ginin gargajiya shatin kobo.

Suna shiga Jauro yace. “Addah ga 'yar Usman tazo�?.
Ya mutse fuska Hajja Nana tayi tare da kallon Khausar tace.
“Shegiyar kaya me wuyar ɗauka se yau kika ga damar zuwa??�?.
Murmushi Jauro yayi still hannunsa na cikin na Khausar yace.
“Tazo da mahaifiyarta da kuma Mahaifinta�?.
Wani kallo Hajja Nana ta masa tare da cewa.
“Kai Jauro ka gyara kalamanka,
badai mahaifinta ba mahaifin riƙo dai ko? ka manta mahaifinta da kai aka binnesa shekaru goma sha biyar da suka wuce?�?.
Kai ya jinjina alamar hakane amma bece komai ba ita kuwa miƙewa tayi ta ɗauko taburma ta shimfida tare da ɗauko darduman kilisa ta shimfiɗa.

A kuma lokacin Momy da Lamiɗo suka shigo cikin sakin fuska tashiga yi musu lale marhaba.
zama Momy da Lamiɗo sukayi akan shimfiɗar data musu kana ita kuma ta zauna awajen zamanta na farko yayin da duka ƙannenta maza suka zauna daga bayanta se ta zamto tamkar sarauniya acikinsu ko wannensu fuskarsa ɗauke da murmushi yake faɗin.
“Addah yau kam ga Khausar tazo�?.
Haka yasa ta juyu.
Ta dubi Khausar da alamun farin cikin ganinta afuskarta saidai yanayin zafinta bazai sa ka fahimta ba.
Ta dubi Khausar da tayi kicin-kicin da fuska tace.
“Menene kike wani kumbura fuska? gwara ma ki saki ranki fa�?.

Zumɓura baki Khausar tayi saidai ba tace komaiba.
Hajja Nana kuwa sake kallon Khausar tayi akaro na barkatai tace.
“Ki tashi ki kawo ma baƙi abin taɓawa�?.

Lumshe idanu tayi kafin tace.
“Nice zan kawo abin taɓa wa?,Nima ai baƙuwa ce akawo mana dai�?.

“Ina magana kina magana!?�?.
Hajja Nana ta fadi a faɗace.
Cikin tura baki tace.
“Ai gaskiyane�?.
Danƙolo Momy ta yiwa Khausar hakan yasa ta tsuke bakinta.
Ɗaya daga cikin ƙannen Hajja Nana wanda ya kasance shine ƙaramin su (Autah)ya miƙe da faɗin.
“To bari na kawo musu�?.
Sannan ya shige uwar ɗakan Hajja Nana ba daɗewa ya fito hannunsa riƙe da Akwashi ya ajiye agabansu sannan ya koma ya ɗauko goran zuma kana ya koma ya sake ɗauko wani Akwashin.

Hajja Nana ta dubi Momy tare da cewa.
“Ayyah wallahi ban san da zuwanku ba�?.
Kai Momy ta gyaɗa tare da cewa.
“Ai inata gwada kiran layin ki baya shiga�?.
Murmushi Hajja Nana tayi kana tace.
“Kinsan Rugar tamu bamu da network se kaje bishiyar ƙare zancenka in kaje bishiyar ma seka hau sama ni kuma ban cika son zuwa ba da girmana Inje in hau bishiya na faɗo�?.

Khausar kuwa taɓe baki tayi tace.
“Hmmm ba network kuma har sai anje wani bishiya?�?.
Harara Hajja Nana ta watsa mata ta cigaba da cewa.
“Wallahi bansan da zuwan kuba dana shirya muku abin taɓa wa�?.
Murmushi Momy tayi batace Komai ba.
Akwashin da aka shigo dashi ne Autansu Hajja Nana ta buɗe Nono ne me zafi yana tururi ga kuma goran zuma dake gefe ɗayan kuma daya buɗe ɗumamen danɗerun zabbi ne suna tururi.
Sauran mazan dake kewaye da Hajja Nana ce suka shiga Gaisawa dasu Lamiɗo.

Muskutawa Hajja Nana tayi tare da gyara zamanta ta kalli Lamiɗo dake zaune ya tanƙwashe ƙafafunsa tace.
Wa'annan daka ke kallo duka ƙannena ne mu goma ne acikin mahaifiyarmu gaba ɗayansu Mazane ni Kaɗai ce mace kuma nice 'yar Fari.

Jinjina kai Lamiɗo yayi yana sauraronta da duka nutsuwarsa duk da yasa abinda take faɗa kishin. tunda ba yaune zuwansa na firkoba.
Ita ko Hajja Nana nuna wanda ke gefenta tayi tare da cewa.
“Ga mai bina Jauro, Sannan kuma sai Sadu, Sannan se Abubakar, Sai kuma Garga, sannan sai Aliyu liman, Sannan kuma sai Dumau ,Sai Salmanu, Sannan kuma Isa sai kuma Umaru�?.
Lamiɗo kuwa kallon su yake yana sake tabbatar da abinda ta faɗa saboda kamannin dake tsakanin su.

Hajja Nana tayi murmushi tace.
“Duk ƙanne nane sannan kuma duk da matansu�?.
Ta nuna Jauro tace.
“Matan sa biyu,Garga ma Matansa biyu, Sannan Sadu ma matansa biyu, sai kuma Liman shima Matansa biyu�?.
Ta sake nuna Jauro, Sadu, Garga, da kuma Liman tace.
Jauro da Sadu 'ya'yansu maza biyu sunyi aure kuma 'ya'yan Liman da Garga suka Aura ma'ana Auran dangi sukayi�?.
Lamiɗo kuwa murmushi yayi alamar yana fahimtar abinda take faɗa masa.

Ita kuwa Hajja Nana cigaba tayi da cewa.
“Duk garinmu babu bare mu ya mune, sannan kuma babu maye mu garinmu atsarkake yake kushigo hankalin ku kwance ku fita lafiya,
Salamun Ƙaulan Min rabbil Raheem�?.

Momy kuwa sunkuyar da kai ƙasa tayi Saboda tasan ana zargin Mahaifiyar Lamiɗo da Maita.
Shima Lamiɗo sun kuyar da kansa ƙasa yayi dan yasan zargin da ake yiwa Mahaifiyar sa kenan kasancewar sa mutum me haƙuri da kuma dattako saiya ɗago kansa fuskarsa ɗauke da murmushi yace.
“Masha Allah yayi kyau zuri'a tayi albarka Allah yaƙara rufa asiri�?.
Murmushi Hajja Nana tayi tace.
“Ameen ya Allah�?.

Domin Hajja Nana 'yar takife ce bata tsoro inma tsoron wani abu ake itace ke isar dashi.
Miƙewa Sauran sukayi suna kallon Lamiɗo suka ce bari mu barku kuci abinci sannan suka fice.

Itama Hajja Nana miƙewa tayi tace.
“Khausar zo mu shiga ciki kici naki�?.
Girgizi kai Khausar tayi tace.
“A'a zanci anan�?.
Ta juyi ta dubi Khausar da kyau tace.
“Kizo mu tafi nace�?.

Shi kuwa Lamiɗo cike da ladabi yace.
“Da kin barta munci anan ɗin babu matsala�?.
Juyawa Hajja Nana tayi kafin tace.
“Toh shikenan�?.

Miƙewa Khausar tayi tabi bayanta ta karɓo ƙananan akwashi aka zuba mata sannan suma suka zuba,Yanayin sanyin da ake tsugawa agarin yasa mazauna garin ke bukatar abu me ɗumi,Suna cin zabbin suna ɗaurawa da Nono me ɗumi bayan sun gama Khausar ta miƙe ta tattara akushin ta mayar.
Ganin ta mayar ne yasa Hajja Nana fitowa suka zauna.
Atake sega yara suna ta shigowa a jere a jere angama abincin rana suna kawowa duk gida Jen garin Hajja Nana tana da kwanonta acan suna kawo mata abinci domin ita bata girki abinci safe ne kawai bata Yarda akawo mata ita take dafa wanda zata ci,Duk ƙannenta taran nan sai ankawo kwanuka tara an ajiye mata ga kuma na 'ya'yansu da sukayi Aure tana da ƙore goma sha uku.
Ga yaran garin ƙanana kyawawa dasu farare soll kamar irin yaran ƙauyen larabawa.
Lamiɗo da kansa da yaga yaran na shigowa sun basa sha'awa,Ko wacce idan tashigo zata ce.
“Goggo Hajja! Goggo Hajja!! Aɗonna�?.
Ƙannenta da Addah Nana suke kiranta 'Ya'yan ƙannenta kuma Goggo Goggo Hajja idan kuma jikoki zasuce mata Hajja Nana.
Duk Wacce ta kawo mata abinci zata ce nice,daga gidan Sadu,Nice daga gidan Garga,saboda yawansu kowa ke gabatar da kansa.
Duk wanda yazo ya ajiye zata ce.
“Angode masu nomawa Allah ya basu ƙarfi da lafiyar nomawa masu girkawa ma Allah yabasu ƙarfin girkawa�?.

Sannan ga yanayin tsarin yaran garin babu alamar ƙazanta ajikinsu ko wanne tsaf dashi ga kuma tarbiyya duk wanda suka zo sai sun tsugunna sun gaida Lamiɗo da Momy da fulatanci kasancewar basu iya Hausa Sosai ba.

Ɗaya daga ciki data zone ta ajiye kwanon Idanunta akan Khausar tace.
“Goggo Hajja Khausar naa�? .
Murmushi Hajja Nana tayi tace.
“Eh�?.
Murmushi yarinyar tayi ta matso kusa da Khausar tace.
“Sunana Dija�?.
Murmushi Khausar tayi tace.
“Yayi kyau Dija�?.
Dija ta kuma murmushi tace.
“Kullum Goggo Hajja na bamu labarin ki rabonki da nan tun kina ƙarama yanzu ya kai shekara shidafa ake cewa�?.
Kai Khausar ta jinjina da faɗin.
“Eh�?.
Hannunta Dija ta riƙe tace.
“Kizo muje gidanmu ku gaisa da Mamana�?.
Ta ƙare mgnar tare da jan hannu Khausar suka fice...

Kiran sallan Azahar yasa Lamiɗo ya miƙe ya tafi masallaci tare da Ƙannen Hajja Nana ita kuma Momy tayi alwala tare da gabatar da sallah bayan sun idar da Sallah Hajiya Aysha ta ɓude jakan da tazo dashi ta fito da turaman zannuwa da Sabulai ta miƙawa Hajja Nana.
Murmushi Hajja Nana tayi tace.
“Hadda ɗawainiya haka?,To angode Allah yayi albarka�?.

“Ameen�?, Momy ta amsa kafin tace.
“Hajja ga Khausar nan na kawo tayi hutu amma mako uku ne hutun nasu�?.
Murmushi Hajja Nana tayi tace.
“Toh Nagode�?.
Ita ko Momy tana gyara mayafinta tace.
“Sati uku ne hutun nasu�?.

Faska Hajja Nana ta tsuke tare da cewa.
“Sai kin sake Jaddada min ne?�?.
Da sauri Momy ta girgiza mata kai.
Cikin isa tace.
“Toh sai sanda naga dama zata dawo kinyi naki saura nawa�?.
Ƙasa da kai Momy tayi tare da faɗin.
“Shikenan Hajja duk yanda kikace yayi mukan zamu tafi�?.

Miƙewa Hajja Nana tayi tace.
“Bari akira muku Khausar kuyi sallama�?.
Cike da ladabi Momy tace.
“A'a Hajja base ankira taba�?.
Dan tasan muddin aka kirata sai tayi kuka kafin su rabu.
Sallama suka sake yi musu kafin suka fice suka tafi...

Acan Gembila kuwa Washe gari.
Asabar Moddibo ya shirya kamar ko yaushe cikin Jallabiya Sky blue Kansa sanye da hula da kuma hirami cikin nutsuwarsa kamar ko yaushe ya shiga cikin makarantar yana motsa laɓɓansa alamar tasbihi da hannu kawai yake amsa gaisuwar da ɗaliban haddar ke masa kai tsaye Ajin haddarsu Khausar ya nufa yayin da Aransa yayi ƙudurin sawa Malam Bello ya casa masa ita saboda gaba ta kiyaye domin ya lura ganganci da sakalci ke damunta.
Cikin rashin sa'a yana shiga ajin ya samu bata nan.
Asma'u ya kira.
Cike da ladabi ta fito tare da tsugunnawa agabansa tace.
“Gani Yah Moddibo�?.

Tsayuwar sa ya gyara cikin yanayin sanyin Muryansa yace.
“Ina wannan Birin?�?.
Asma'u kuwa kanta aƙasa tace.
“Nima yau da nazo ban ganta ba sai nake tambayar Amina ina take shine tace wai taje garin Kakanninta�?.
Ƙwafa yayi yace.
“Shikenan yayi kyau�?.
Kana ya juya ya bar waje....

Acan mota kuwa Momy ta dubi mijinta tace.
“Kayi hakuri da Hajja Nana yanayin tsufa ne�?.
Murmushi yayi still Idanunsa ahanya yace.
“Ai bakomai ba gamu da Gimbiya Dadu ba ai haka take�?.

Acan Rugar Jauro yaya kuwa bayan Khausar ta dawo gida ta tar da Momy ta sun tafi ta tsare Hajja Nana da ido tace.
“Meyesa ba ki kirani ba kafin su tafi?�?.

Salati Hajja Nana ta sanya tace.
“Tuhuma ta kikeyi? Ko kuma me?�?.
baki ta cinna sama tare da cewa.
“Ai gaskiyane abinda ya dace na faɗa�?.
Salati Hajja Nana ta sanya tare da faɗin.
“Ohhh ni Shatu Allah ya nuna min 'yar Usmanu yarinya kamar ruwan aski sai rashin ta ido�?.
Ta ƙare mgnar tana kallon Khausar dake tsaye fuska akumbure cikin tsawa tace.
“Bari kiji in faɗa miki ni agarin nan idan nayi magana kamar yankan wuƙa yake babu me bani Amsa ko musu ko jayayya dani!�?.
Ita kuwa Khausar wani irin juya Ido sama tayi tare kana tace.
“Uhummm to gwara ma ki sani.
Idan maganarki yankan wuƙa ne to kin samu me yankan rez�?......!



Littafin SAKAYYAH na kuɗine biya ki karanta 1k ne kacal 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA


By
*GARKUWAR MARUBUTA*
9/13/23, 20:03 - Buhainat: 📝🍇✨💫⏰🤴🏻👹❤️❤️❤️🍇

*SAKAYYAH*
_Page 5_

*NA*
*AYSHA ALIYU GARKUWA*

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*FREE PAGE*

*LITTAFIN SAKAYYAH NA KUDINE, 1K NE KACAL ki biya ki karanta cikin Aminci ba haƙƙin wani a kanki. 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA, sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276.*


Zare Ido Hajja Nana tayi cikin faɗa da fushi tace.
“Ke! Ke!! Ke!!!.Faɗimatu ki kiyayi kanki dani fa zan tsige Miki fuka-fukinki!�?.

Ita kuwa khausar fuska ta haɗe Idanunta tsaye akan Hajja Nana tace.
“Nifa ba tsuntsuwa bace da zaki tsige min fuka-fuki, ai gaskiyane tsakani da Allah da Annabi mahaifiyata zata tafi kinsa ankawo ni aise ki kirani muyi sallama na musu Allah ya tsare�?.
Ta ƙare mgnar tare da juyawa ta kalli Dija tace.
“Fisabillilhi ba haka ya kamata ba Dija?�?.

Dija kuwa tuni ta sunkuyar da kanta yayin da jikinta ya shiga ɓari tsananin tsoro ya bayyana afuskarta sanin halin Hajja Nana babu wanda ya isa tana magana yana mayar mata da martani!.

Cikin rawan jiki da tsoro daya bayyana amuryanta tace.
“Khausar kidena kar ki sake bata amsa ki bata haƙuri�?.
Tana ida maganar ta tsugunna gaban Hajja Nana tace.
“Goggo Hajja Waɗɗu munyal�?.

Hajja Nana kuwa kwaffa tayi kana tace.
“Aaaa Dija matsa kusa da ita inzo na same ta ai ke ba ruwanki�?.
Ita kuwa khausar batare da tsoro ba tace.
“Toh kizo mana kawai dan mutum ya faɗi gaskiya don dai ba'a son gaskiya da zaman lafiya ai yakata dai akirani muyi sallama da Momyna tunda dai ansa an kawoni wataƙila ma sai nayi sati biyu ko uku bangan taba aida se akirani muyi sallama ince agaida mutanen gida sannan nayi musu fatan isa gida lafiya�?.

Ita kuwa Hajja Nana afusace tace.
“To idan kece zaki kaisu gida lafiya kada Allah yasa ki kaisu shegiyar yarinya mara ji Ɓee Usmanu La'ilaha illallahu ohoho gabtarel�?.

Tuni Baffa Jauro da Baffa Sadu suka shigo idanun su akan yayar tasu suka ce.
“Lafiya Addah Hajja?�?.
Kai ta girgiza tare da nuna Khausar dake cika tana ba tsarewa tace.
“Ɓeee Usmanu,Nikam ban taɓa ganin fitsararriyar yarinya kamar 'yar Usmanu ba�?.
Itade Khausar na jingine jikin bango tana tura ƙaramin bakinta dake ƙarawa fuskarta kyau.

Kallon ta Hajja Nana tayi cikin harara tace.
“Nikam Usamanu na Kam ba haka yake ba, haka zalika Mahaifiyarki ko surukata ce bazan mata ƙazafi ba macece mao mutunci amma ke kam waya fitsare miki Ido? Kodan zama tsakiyan Mayun gidan kune yasa kika zama haka!?�?.

Khausar dake jingine da bango ta ɗago kanta kana ta wara manyan Idanunta masu kyau da tsari tace.
“Nikam de kar kice min Mayya idan su Mayu ne toni ba Mayya bace idan kince ni Mayyace sede idan awajenki na gada!�?.

Baffa Jauro da Baffa Sadu suka dubi juna alokaci ɗaya cikin ƙasa da murya yanda Hajja Nana ba zata jiba Baffa Jauro yace.
“Lalle akwai rigima anan? Addah Hajja ba abata amsa idan tayi magana amma ga 'yar Usmanu daga zuwa tana bata amsa gatse-gatse jika kenan mafi akasari duk zafin mutum jikoki bazasuji tsoronka sosai ba�?.
Murmushi Sadu yayi yana jinjina kai.

Baffa Jauro kuwa kan Khausar ya ɗan buga yace.
“Kay Hausajo kidena mu ba'a rashin kunya agarin nan!�?.
Ita kuwa khausar inda ya ɗan bugeta tasa hannu ta riƙe tana sosawa duk da cewa bawai zafi ya mata ba ta tura ƙaramin bakinta tace.
“To ai muma ba rashin kunya bane wannan kam�?.
Dan ƙolo ya mata yace.
“Dije jata ku tafi�?.
Kai Dije ta gyaɗa wacce se alokacin ta samu kuzarin miƙewa tace.
“Khausar kizo mu tafi�?, Sannan taja hannunta suka fita.
Suna fita Khausar kuwa hannunta dake cikin na Dije ta janye tace.
“Yanzu ina zamuje?�?.

Murmushi Dije ta sakar mata tace.
Rafi zamuje�?.
Murmushi mai sanyi Khausar ta sakar mata wanda ke ƙarawa fuskarta kyau tace.
“Toh mu tafi�?.
Dan sosai weather garin yake abin burgewa da sha'awa.

Cikin nutsuwa suka nufi Rafin suna hira.
Da sauri Dije ta riƙon hannun Khausar tare da nunawa mata gefen damansu, masu wasa da birine ke tafiya kana yaran rugagen dake gefe dasu na biye dashi, bisa alamun yanzu kuma rugarsu zasu shiga.
wani ƙaton Biri yake ta kolongoiso yara nata ja da baya.
Cike da nishaɗi Khausar tace.
“Muje muma mu gani�?.
Kai Dije ta gyaɗa mata , kana suka nufi wajen me wasa da Biri suna ganin yanda Birin ke duk abinda aka sashi.

Cike da farin ciki Khausar ta kalli mai wasa da Birin tana ƙara kusawa cikin yara matan tace.
“Mai Biri yanzu duk abinda na sashi zai min?�?.
Kai mai wasa da Birin ya jinjina yace.
“Idan kuma baki yarda ba ki gwada ki gani�?.
Kusa da Birin Khausar ta matsa tana murmushi tace.
“Yauwa yaya salon mugun Malami yake idan zai daki ɗalibansa?�?.
Da sauri ta ware idanunta ganin.
Birin ya wani ja baya tare da harɗe hannunsa aƙirji kana ya ɓata fuska tare da harɗe sawunsa sai kuma ya ɗauki wani sanda ya riƙe yana nuna Khausar da Dije.

Hannu Khausar tasa ta dafa kafaɗar Dije tare da tintsirewa da dariya mai cike da sautin shauƙi yayin da ɗaya hannun kuma ta ɗaura saman shafefen cikinta tana mai cigaba da dariyar.
Domin kuwa babu wanda ya faɗo mata arai lokacin da Birin ke gwadawa face Moddibo duk da kasancewarsa ba mutum ne mai Fara'a ba amma duk sanda zaisa a zaneta a makarantar Islamiyya seya sake tamke fuskarsa..
Dariya sosai takeyi wanda da yawa cikin yaran tayata sukeyi.

Ganin bata da niyyar daina dariyar ne yasa Dije jan hannunta cikin dariya tace.
“Khausar Mu tafi,Dariyar me kuma kike haka!?�?.

Tsagaita Dariyar Khausar tayi sai kuma lokaci ɗaya jikinta yayi sanyi tuna wa da tayi Moddibo zai iya jira duk lokacin da tawo ya yanke mata hukunci ahankali tace.
“Kawai na tuna da wani Malamin mune�?.
Murmushi Dije tayi tace.
“Allah sarki shike zaneki kena�?.
Kai ta jujjuya tare da cewa.
“Wancan da shegen madarar ƙasaita sawa yake a zaneni dai yana nan jiki kamar auduga ai shi dukan ma aikine a wurinsa�?.
Murmushi Dija tayi tare da cewa.
“Da Goggo Hajja zataji haka sai ta sa mishi al'barka�?.
Baki ta tura ba tare da tace komai ba sukaci gaba da tafiya.

Suna shiga Rafin idanun Khausar ya sauƙa akan Bishiyoyin Piya, Caɓɓulle, Mangoro, Ayaba, Gwanda, Gwaba, Lemo, da sauran kayan itatuwa duk sun yiwa wajen ƙawanya.
Sake wara Ido Khausar tayi ganin bishiyoyin Inabi guda uku a jere,
Cikin farin ciki ta dubi Dije tace.
“Harda Inabi Laha'Ila Ha'illalhu Masha Allah zan kuwa ci�?.
Ta ida maganar tare da nufar jikin Bishiyar zata hau.

Saurin riƙe hannunta Dije tayi tace.
“Kada ki hau Khausar Baffa Liman ya hanamu yace ba shida amfani 'ya'ya mata su riƙa hawa bishiya ba tarbiyya bace mai kyau�?.
Ita kuwa khausar janye hannunta

1 Comments On SAKAYYA
avatar
hajara-ahmad

1 year ago

Reply

Nice novel

Please Login or Register in order to submit comment