Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

lib-lib gwanin burgewa jajayen lips ɗinsa dake cikin zagayen sajensa da kota million ɗinsa sai sheƙi sukeyi, a hankali yake taka tattausan silifas dake sawunsa.
ya nufi can gefen yamma inda wasu kyawawan bukoki na zamani da yake wajen hutuwansa,
Wurine mai kyau da ban sha'awa a hankali ya zauna bisa ɗaya daga kujerin dake cikin bukkar da tafi sauran ƙawayuwa da flawers.
A hankali yake motsa lips ɗinsa alamun yana tasbihi yalwataccen sumar kansa kamar na larabawa na sheƙi da ɗaukar ido idanunsa na lumshe yana motsa bakinsa a hankali.


Cikin nutsuwa Asma'u da Khausar suka fito duk da rawan kai irin na Khausar komai nata anitse takeyi cikin nutsuwa suke tafiya yayinda hijabansu yarufe har takalmansu adedeta suka tara tare da sanar dasu inda ze kaisu.
Tafiyar Mintuna ashirin da biyar sukayi suka isa aƙofar gidan.
A gaban gate ɗin adedeta ya ajiyesu.

Asma'u ce agaba tasa hannunta da babu komai ta tura ƙofan gate ɗin yayin da ɗaya hannu ke riƙe da Kula wanda Ummi ta yiwa Innayi dambun naman kaza.
Cikin wani irin shauƙi Khausar ke bin ilahirin gidan da kallo ganin yanda flowes da shuke shuken kayan marmari suka zagaye gidan tamkar garden,
Da sauri ta juyo da kallonta kan Asma'u tare da cewa.
“Wooow masha Allah.
Kai Asma'u wannan gidan waye haka? gaskiya yayi kyau sosai�?.
ta ƙare mgnar tana lumshe idanunta tare da shaƙar sassayan iskar dake haɗe da ƙamshi flawers da kuma turare jikin Moddibo.
Kana ta riƙa bin fulawowin tana shafa duk wanda hannunta ya sauƙa akai saita tsinke takai hancinta kana taja dogon numfashi tare da lumshe ido.

Shi kuwa Moddibo tun ƙarar buɗe gate ɗin da yayi ya ɗago kansa yana kallon wajen.
Cikin mamaki yace
“Khausar Usman Lelelwal a gidan nan�?.
Hannunsa yasa ya tallabe habarsa tare tsuke fuskarsa.
Ita kuwa Khausar cike da shauki ta buɗe hannunta tare da jujjuyawa har hijabinta na buɗuwa cikin ɗan ɗaga sauti tace.

“Agaski Asma'u gidan nan ya min komai na ciki sun burgeni gawani irin ƙamshi da suke, ji yanda ilahirin gidan ke fitar da wani ni'imantaccen ƙamshi.
Gaskiya gidan nan shine aljannar duniya da alamu kuma mutanen ciki maƙurane wajen tsabta ina son komai na gidan nan�?.
Asma'u Kam dariyar dake cinta take ƙunshewa ta tabbata da Khausar tasan cewa gidansu Moddibo ne babu dalilin dazai kawota sannan ta tabbata yau juma'a ya irin wannan lokacin Moddibo na gida babu inda zeje.

Ita kuwa Khausar juyi ta cigaba da yi tare da sauri ta nufi side din Moddibo steps din ta fara tattaunawa tana shafa furannin dake jere a kan.
Saida ta hau har tsakiyar barandar kana ta juyo ta fuskanci yama.
“Wooww Masha Allah Asma'u zo ki hau ki gani wlh ina hango bakin Teku kinga yadda ruwa da tsuntsaye keyi!".

Ita dai Asma'u hannunta tasa ta rufe bakinta tana murmushi.
Yayinda tun shigowarsu Moddibo ya zuba musu idanu saidai sam su basu lura dashi ba,da gudu Khausar ta juya ta fara taka steps din tana sauƙa ta nufi sashen da Moddibo ke zaune tana faɗin.
“Wowww gaskiya wannan gidan yayi mugun yimin kyau da ace zan rayu a ciki da wanda raina zaiso zan meda mishi gidan tamkar dausayin farin cikin duniya�?.
Cikin danne dariya Asmau tace.
“Khausar zomu tafi mana�?.
kai Khausar ta girgiza tace.
“A'a ki tafi ni wlh saina cire inabin can da Appel kije kawai�?.
Ahankali Asma'u tace.
“Kizo muje mugaida Innayi sai mu gaya mata kafin ki cire�?.
dan tasan a irin wannan lokacin tabbas Moddibo na nan shiyasa take mgn a hankali wai dan kar ya jisu.
Kai Asma'u ta dafe tare da cewa.
“Idan masu gidan kuma suka zo suka sameki fa?�?.
Taɓe baki Khausar tayi tace.
“Gida kamar wannan masushi bazasuyi rowa ba, kuma ai nan kamar babu kowa babu wanda zaizo�?.
ta faɗa tana komawa inda inabi yake tasa hannu ta fara tsinka tana tsalle jin hijabinta zai takurata ne yasa ta zare hijabin tare da ajiyeshi kan kujerar dake ƙasan bishiyar.
Middibo kuwa dafe kunci yayi yana ganin ikon Allah Aransa yace.
“Yarinya kamar ba mace ba dubi yanda take tsalle kamar biri wannan ba budurciba abinda yafi budurcima zata watsar domin yasan illar hawa bishiya yakan buɗa mace duk da cewa ita ba hawan tayi ba.
Tunaninsa ne yakatse asanda ta nufi bishiyar Appel tsalle tayi da niyyar tsinkowa dan bishiyar Appel irin yan masaƙaitan nanne,
tsalle ta kuma yi amman ta kasa ga dai hannunta na taɓawa sede baza ta iya tsinka ba.
tattare gashinta tayi tare da dan mai dashi bayan wuyanta kana ta nannaɗe ƙafar wandonta,
tsalle tayi tare da kamo rashen da yafi kusa,
sai kuma ta hango wasu a can sama haka yasa ta fara taka jikin bishiyar har ta hau bisa rashen duk da ba wani tsowone da shiba,
Cal sai gata akan bishiyar.

Cikin tsananin takaici da sassarfa ya mike tare da nufar wajen, yasan koda yace zeyi mata tsawa muryarsa baze fita ba saboda bashida da amo mai karfi sannan yasan dai baya cikin tarbiyya mai.kyau ƴa mace tai ta hawe-haween bishi yana isa bakin bishiyar ya tsaya tare da harɗe hannayensa aƙirji kafin yayi magana ta juyo da niyyar kai hannu zata tsinki appel sukayi ido huɗu dashi ido cikin ido sukayi kamar yadda damisa kan iya tsare kenwa da ido haka yayi mata.

Cikin tsananin firgici da tsoro da kaduwa tace.
“Hasbunallahu wani'imal wakin,
Aizubillahi Minal shaiɗanirrajim, innahu min sulaimanu wa innahu Bismillahir rahmanir rahim�?.
Cikin tsananin tsoro take jera addu'o'in domin gani take shin fatalwane ko kuma aljan yazo mata asuffarsa cikin kiɗima da firgici ta rikito tayi ƙasa ta faɗo gababsa yayin da hannayenta suka sauƙa akan.....!




Kada dai ku shagala wannan duk garaɓasar FREE PAGE. Labarin sashi-sashi gareshi. Ko wacce kusufa da darasin dake ƙunshe a ciki. Al'amarin babbane fa babu abinda babu cikin lbrin

Inada lbri na musamman
Wanda nake son in rubuta in Allah yaso ya yarda ya bani aron rai da lfy da dama.
In na gama TUBALI.
Zafin labarin kan sani inji Tamkar in aje TUBALI na fara wancan ɗin
*SAKAYYAH*

lbri ne mai cike da abubuwa na musamman masu tarin rikitarwa al'ajami matsalar kasarmu kalubale masautu.
Taraddadin rayuwa, tsaka mai wuya, tsubucewar dama da samunta,
Nesanta da kusanta, tausayi, kuka, dariya, barkwamci, iko, isa, mallaka, kasaita, kekkyawan ilimin addini, da aiki dashi, fasadi, zalumci, shirka da sakamonta, kalubalen dalibai ga Malami, matsalar , yadda ya kamata gomnati da jami'an tsaro da masarautun gargajiya su juyo kam lamarin bindiga Dadi Zazzafar soyayya mai kekkyawan tubalin raino a ɓoye!!!.
Ya Salam Labarin ya rusa min tunanin da nake cewa bazan sake wani littafi Mai kamar GARKUWA ba sai gashi in second's Allah ya buda min tunanin na harhaɗo Labarin *SAKAYYAH. FATTANAH kenan.*

Amman sai dai kuwa kusan wani Abu!??!
In kuna son sani ku biya 1k ne kacal 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276. In kin biya kikuma bibiyeni zakusha al'ajab.

By
*GARKUWAR MARUBUTA*
9/13/23, 20:03 - Buhainat: 📝🍇✨💫⏰🤴🏻👹❤️❤️❤️🍇


*SAKAYYAH*
_Page 4_

*NA*
*AYSHA ALIYU GARKUWA*

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*Free page*

*KADA DAI KU MANTA WANNAN FREE PAGE NE, KI KI BIYA KI KARANTA CIKIB AMINCI BA HAƘƘIN WANI GABA GAREKI SAKAYYAH 1k ne kacal ƴar uwa. 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA. Sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276*


*Al'bishirunku Ma'aurata, GA GARKUWAR KU nan tafe muku da tsarabobi na musamman gareku ma'aurata daga cibiyar mgnin mata mai taken GARKUWAR MA'AURATA*

NI DAI AYSHA Ɗiyar ALIYU GARKUWA.
Ina matukar mamakin wani irin lokaci da ya riske mu mai wahalallan fassara. Kullum dai magana daya ce, akan ma’aurata, fada, rashin jituwa, mutuwar aure, akan kuskure kalilan, rashin kula, rashin yi wa juna uziri. Toh wai duk me ya janyo hakan? Na zurfafa a tsananin tunani hakan ya tilasta min bincike mai tarin yawa wanda ya kai ni ga gano inda matsalar take? Shin yar’uwa ke macece amma kin san wacece mace ku? Kin san me ake kira mace kuwa? Mace ita ce matar da take zama iyali a wajan namiji ta zame masa bango, sanyin idaniyarsa, ta zame masa gata da farin cikin rayuwarsa ta zame masa ruwa abar kore ƙishinsa ta zame masa mayafi mai karesa daga gigitar kadaici, ta kuma dorar da mijinta kan turbar gaskiya, ta kashe masa jiki da salonta ta rikita shi da baiwa da ni’imar da Allah ya bata idan har ta san hanyar mayar da kanta sabuwa dal awajanta, wato kullun takasance masa tamkar amarya har ya kasa tantance daren amarcinsu da sauran dararen rakun rayuwar su.

Wannan ita ce mace. Ina da wata saukakkar hanyar da zaki zama abar so da kulawa da soyayya a wajan mijinki ta hanya mafi sauki, 09097853276 hanyar ita ce ki gwada amfani da kayana na gyara ki gani, ina mai tabbatar miki da in sha Allahu sai kin dara da murna sai kuma kin gode min. Kayana kaya ne da aka yi shi da zallan itacanmu na gado marasa illa a cikin jikin dan adam musamman mace, kaya ne da suke taimakawa (sex hormones 😍) dinki.
Misali kina kallon India😘, hollywood, Asian film🥰 kina ganin yanda mazansu ke nunawa matansu tsananin soyayya kamar su ba su kyautar ransu!?
Saboda me hakan? Saboda suna sadaukar da lokacinsu wajan gyara jikinsu da kayan da ke tsattsafo da ni’ima cike da tsukewa, kayan nan kuma ana yinsu ne zallar magungunan gargajiya wanda ba su da illa domin haɗine na ingantattun itatuwa da yayansu.
Ina baiwar Allahn da miji ke daure mata fuska babu hirar arziki?
Zo ki ji yar’uwa zan baki gumbata da zallar gari wanda aka yi su da nagartattun itacen da ke da matukar amfani a jikin mace. Gubar ciko, gumbar tsalle dole, gubar da ba'a baiwa mai kishiya, garin maɗi, garin mallaka, tsumin goron tula, tsumin tsartai, tsumin maratsi, pala-pala butar sirri, kwanon k’asaitacciyar mace, furar mata madararta gareki Hajia takenta sha yanzu mgni yanzu,
Ina mata masu fama da sanyi? Sanyin mara ji zo na hadaki da magani na na sanyi wanda yake wanke mara ya fitar da duk wata cuta da ke samun mazauni a wajan set ɗin 10k ne kacal wlh koda sanyin mahaifane in sha Allah zakiji saukin.
Ina da ciccibi mai kyau. Ina da hadin amare mai kyau wanda zai gyara yarinya ya kankaro mata kimarta akwai hadin mai jego wanda muke yinsa na asali inada kekkyawan Hadi maida tsohuwa yarinya.

Akwai ɗaya bangaren wato *KAMSHI*
Kimarki gyaranki da kamshinki. Matan da suka gane suka san yanda za su kankaro da mutunci su ne masu amfani da kayan gyara da kuma sanyaya jikinsu da kamshi, ina da turaren wanka da na bandaki na daki na jiki da na kaya dana tsuguno kamshin turarena na dabam ne mai sanyaya zuciyar wanda ya shaka ina da kayan kamshi na amarya da na maijego da na uwargida da dukkan macen da take kokarin mayar da kanta mai daraja a idon kowa ta zamo sarauni a idon mijinta, akwai shu'umar humra, kana da kulaccar sirri sayan na gari maida kuɗi gida, banda harkar karanta yayin gyara Hajia.

Zaku iya samun kayyakina a duk garin da kike, zakiyi min mgn ta whatsApp number na 09097853276 domin yin zaɓinki, ko karin bayani, zaki tura kuɗin ta account na 0005388578 Jaiz bank AISHA GARKUWA ALIYU in mun gama mgna zan sa miki kaya a mota yazo duk garin da kike, in baki shirya saya yanzuba Please kada mu wahal da juna ki bari sai kin shirya kafin kiyi min mgn.

🤝🏻🥰😘 Daga taku AYSHA ALIYU GARKUWA
*(GARKUWAR MA'AURATA)*


Tana dirowa hannunta dake dungule da Appel suka sauƙa kan ƙafarsa.
Yayinda yatsun hannunta dake ɗauke da zoban azurfa na kusa da da ƙaramin yatsa da kuma ƙaramin suka sauƙa akan faratun yatsun sa,
atake yatsun hannunta suka bada sautin ƙash! yayin da shi ma Moddibo yatsun ƙafansa suka bada sautin ƙas-ƙas!, Idanshi ya rumtse da sauri, sabida wani irin masifaffen zogi da yaji ya ratsa sa cikin sauri ya tsugunna da niyyan matsasu tuni ɗanƙwalin ta ya zame yalwataccen sumar kanta baƙi daya sauƙa zuwa kafarɗarta ya zubo yana fitar da wani sihirtaccen ƙamshi...

Khausar kuwa jin zafin daya ratsa ƙafarta data malkoɗe ne yasa ta furta.
“Wayyyo Allah ƙafata!�?. ta faɗa da ƙarfi tare da ɗago kanta yayin da yalwataccen sumar kanta ya rufe mata fuska da sauri tasa hannu ta janye ta ɗago kanta.
Idanunta ne suka sauƙa akan Moddibo dake durƙushe, cikin ruɗewa da tsanananin tsoronsa ta ɗauki ɗan kwalinta kana ta miƙe da gudu tana cewa.

“Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n dan Allah kayi haƙuri wallahi Allah bansani ba�?.
Ta faɗa tana ƙoƙarin fita daga gate ɗin.

Asma'u kuwa fitowarta daga gate ɗin da zai sadaka da cikin farfajiyar Innayi kenan ta hango Khausar na shirin fita babu ɗan kwali akanta.
Cikin Sassarfa tabi bayanta tana faɗin.
“Khausar! Khausar!! Khausar!!!�?.
ta kira sunanta har sau uku Kafin ta sake cewa.
“Dan Allah kada ki fita ahaka Khausar ki tsaya�?.

Moddibo kuwa cikin yanayin nutsuwarsa da kuma sanyinsa ya kira sunanta da faɗin.
“Asma'u�?.
Saidai akwai alamun ɓacin rai acikin sautin Muryansa.

Atsorace Asma'u ta juya Idanunta cike da tsoro tace.
“Na'am Yah Moddibo�?.
Tsayuwarsa ya gyara tare da lumshe idanunsa masu ƙwarjini da haiba kana ya buɗe su ya dubi Asma'u da har yanzu take tsaye da tsoro a idanunta yace.
“Meyesa zaki ɗauko Biri ki kawo mana gida!?�?.
Ya ƙare mgnar da bin Khausar da ido wacce tuni ta kai bakin gate.

Asma'u kuwa saurin ɗagowa tayi ta dubesa jin ya kira Khausar da Biri saidai bata yarda sun haɗa ido ba.
Shi kuwa cike da takaici
ya cigaba da cewa.
“Koda wasa kada ki sake zuwa da wannan yarinyar gidan nan, tunda ita bata da hankali da kuma nutsuwa da kamun kai�?.
Ya ƙarashe mgnar yana mai lumshe idanunsa dake cike da ƙwarjini har zuwa sannan yatsun ƙafar na masa rawa tamkar alokacin ta buga masa yatsunsa.

Ajiyar zuciya Asma'u ta sauƙe ganin tuni Khausar ta fice kanta a ƙasa tace.
“Dan Allah kayi haƙuri Insha Allah hakan bazai sake faruwa ba�?.
Moddibo kuwa baice da ita Komai ba saima lumshe idanunsa da yayi yana motsa laɓɓansa alamar tasbihi yaci gaba da yi.

Ita kuwa Asma'u jin baice komai ba yasa ta juya cikin sassarfa ta nufi gate dan bin bayan Khausar...

M Jameel dake zaune cikin falon Moddibo kuwa wanda ya tsirawa window idanu yana ganin duk abinda ya faru ya saki lallausan murmushi tare da miƙewa yana gyara zaman Farin t-shirt da blue jeans dake jikinsa kana ya sanya hannu ya buɗe ƙofan falon ya fito fuskarsa ɗauke da ƙayataccen murmushi cikin yanayin sa na ƙaunar Amininsa yace.
“Ba sa ido ba?,ka fita sabgar yarinya ka ƙi yanzu inba sa'a ba kasa taji ciwo dan naga lokacin da take gudu tana ɗin gishi�?.
Moddibo kuwa buɗe idanunsa dake lumshe yayi tare da zab gawa M Jameel Harara cikin yanayin nutsuwarsa daya zame masa jiki yace.
“Dama karyewa tayi da shi yafi yarinya bataji bata da hankali ko kaɗan�?.

Da gudu Asma'u ke bin Khausar tana cewa.
“Khausar ki jira ni mana�?.
Ƙin tanka mata Khausar tayi tana cigaba da sassarfa yayin da ko wani gaɓa na jikinta ke rawa kana tana cigaba da ɗaure gashinta daya baje kasancewar unguwa ce da babu hayaniyar mutane yayin da take yarfe hannunta dake masifar zugi kana tana me ɗingisa ƙafarta.
Ganin da gaske Khausar ba zata tsaya ba yasa Asma'u ta ƙara gudunta har ta isa inda take tana sauƙe numfashi saboda gudun da tayi tace.
“Ayyah Khausar ki tsaya mana ga hijabinki saka�?.
Hannunta tasa ta amshi hijabin nata tare da zirashi a jikinta kana taci gaba da tafi.
“Ayyah Khausar ki tsaya mana�?.
Asma'u ta kuma faɗa tare da shan gabanta,
a raunane tace.

“Bazan tsaya ba Asma'u meyesa zaki min haka Asma'u? banyi tsammanin zaki yimin haka ba gidansu Moddibo kika kawoni mutumin da kin san baya ko son ganina.
Gashi yanzu kinsa na buga masa yatsuna masu zobe aƙafa naji masa ciwo,yanzu bansan wani irin hukunci zai ɗauka akaina ba�?.

Tsoron Khausar ɗaya kada Moddibo yace zai zaneta duk irin rashin ji da ƙiriniyarta tana matuƙar tsoron bulala kana tasan duk hukuncin da Moddibo zai ɗauka bazai wuce yasa Malam Bello ya zaneta idan taje Hadda.

Cikin sanyin murya Asma'u tace.
“Ayyah Khausar kiyi haƙuri, amman kuma ai da kinji mgnata da haka bai faruba. kece bakya ji sannan ba kyaso ataɓa lafiyar jikinki�?.
Kallonta Khausar tayi da Idanunta dake cike da tsoro da kuma fargaba tace.
“Meyesa zaki ce haka Asma'u kawai naga Appel da inabin ne ya ban sha'awa shiyasa na cira�?.

Kai Asma'u ta girgiza tace.
“Inabi Khausar? na tabbata duk wannan abubuwan da kika gani akwai su a gidanku ku fiye ma da hakan�?.

Sake Marerece fuska Khausar tayi tace.
“Na ganine ya bani sha'awa laifi ne dan na cire!?�?.
Murmushi Asma'u tayi ganin har zuwa lokacin Atsorace Khausar take sai kuma tace.
“Kema dai baki jira kanki ba daga zuwa gidan mutane sai ki fara cire musu abu batare da neman izini ba�?.

Ita kuwa khausar jin abinda Asma'u tace yasa ta watsa mata Harara cike da tsiwa tace
“Tun da kinsan gidan masu baƙin hali zaki je Meyesa zaki ɗaukeni ki kaini?, Kisa aranki daga yau babu inda zan sake rakaki tunda haka kikayi min�?.

Wara ido Asma'u tayi sai kuma ta langwaɓar da kai tace.
“Kiyi haƙuri Khausar bansan haka zai faru ba ni kawai da niyyar mu gaida Innayi nace ki raka ni amma kada kice baza ki sake raka niba na tuba�?.

Kallonta kawai Khausar tayi amma ba tace komai ba, sake langwaɓar da kai Asma'u tayi cike da tausayinta tace.
“Ki zauna awancan dakalin se inja miki ƙafar!�?

Kai Khausar ta girgiza tana rintse Idanunta tace.
“Basai kin ja minba kawai sama mana adedeta mu hau�?.
Kai Asma'u ta jinjina tare da riƙe hannunta suka ɗan tsaya bakin titi cikin sa'a tsayuwar su babu daɗewa suka samu adedeta hawa sukayi tare da yimasa kwatancen inda ze kaisu...

Aƙofar gida me Adedeta ya sauƙe su bayan sun isa Asma'u ce ta ciro kuɗi ta basa kana ta riƙe hannun Khausar suka nufi gate Khausar ce tasa hannu ta tura gate ɗin cikin rashin sani suka buge juna da Samira Sani wacce ke ƙoƙarin fita Amina na biye da ita.

Saurin ɗago kai Khausar tayi jin Samira Sani na cewa.
Ke 'yar uban waye da zaki haɗa kafaɗa dani shin dame kike taƙama!?�?.
Kamar Khausar za tace wani abu sai kuma ta fasa taja siririn tsaki tare da jan hannu Asma'u suka bar wajen tana me cigaba da ɗingisa ƙafarta.
Ƙwafa Samira Sani tayi cikin kumfar baki tare da tsanan Khausar aranta tace da Amina.
“Wallahi na tsani wannan shegiyar yarinyar me kama da sadaka yalla Idan ban sabautata ba bazan taɓa samun nutsuwa ba!�?.
Tsaki Amina taja tana kallon Samira tace.
“Allah ne kaɗai yasan irin abinda zan mata�?.

Kafin su ƙarasa shiga falon Khausar ta janye hannunta dake cikin na Asma'u kana ta gyara tsayuwar tare da dai-dai ta tafiyarta tana me rintse Idanunta sam bataso Momy ta fahimci abinda ya sameta.
Asma'u kuwa kallon ta tayi cike da tausayinta amma batace komai ba Ƙofan falon suka tura
suka shiga tare da haɗa baki wajen cewa.

“Assalamu Alaikum�?.
Momy dake zaune kan kujera ta ɗaura ɗaya kan ɗaya ce ta faɗaɗa Murmushin fuskarta tace.
“Wa'alaikum salam har kun dawo?�?.
Zama suka yi daga gefen ƙafarta aƙasan chanis capet Asma'u tace.
“Eh Momy�?.

“Masha Allah ya jikin Innayin?�?.
Cewar Mommy.
Khausar na ƙoƙarin miƙewa tace.
“Da sauƙi Momy�? Sannan ta nufi Bedroom ɗin ta da sauri Asma'u ta miƙe tabi bayanta.

Bakinta ɗauke da sallama tashiga ɗakin nata kana tayi saurin ɗin gisa ƙafarta se kuma ta kwanta agefen gadonta dake shimfiɗe da white bedsheet tana sakin ajiyar zuciya akai-akai alamar har yanzu akwai tsoro atare da ita.
Zama Asma'u tayi agefenta ganin yanda ƙafan Khausar ke rawa yasa tace.
“Bari na ɗebo ruwan ɗumi na matsa miki�?.
Kai Khausar ta girgiza da faɗin.
“A'a ga can man zafi agaban mirrow ki ɗauka min na shafa�?.

Kai Asma'u ta gyaɗa kana ta miƙe ta ɗauko man zafin ta ɓude kana ta kama ƙafar Khausar tana mulka mata.
Khausar kuwa rintse Idanunta tayi tanajin zafin man na ratsa jikinta yayin da aƙasan zuciyarta tsakanin tsoro da firgicin hukuncin da Moddibo ze ɗauka akan tane.
Asma'u kuwa hira ta riƙa yiwa Khausar na ɗebe kewa kana daga bisani ta miƙe ganin yamma tayi seda ta biya ta kichen ta sake yiwa Momy Sallama kana ta tafi.

Khausar kuwa yanayin zogin da ƙafarta da kuma hannunta ke mata yasa bayan tafiyar Asma'u ba jimawa bacci ya ɗauke ta...

Ita kuwa Momy ganin har maghariba tayi bata jiyo motsin Khausar kuma bata nemi Raudat suyi salla ba se abin ya bata mamaki bayan ta idar da Sallah ta fito daga Bedroom ɗinta Kai tsaye Bedroom ɗin Khausar ta nufa,
bakinta ɗauke da sallama ganin Khausar na bacci yasa ta ƙarasa bakin gadon tare da taɓa fuskarta da hannunta dake da damshin ruwa ruwa tana kiran sunanta da faɗin.

“Khausar! Khausar!! Khausar tashi kiyi Sallah maghariba tayi�?.
Momy ke faɗa tana me sake shafa fuskarta da hannunta dake da damshin ruwa.
jin muryan Momy da kuma damshin hannunta da take shafa fuskarta yasa ta buɗe Idanunta ahankali tace.
“Na tashi Momy�?.
Juyawa Momy tayi ta fita ita kuwa khausar miƙewa tayi tare da furta.
“Alhamdulillah�?,Jin babu ciwo da Zugin da ƙafar ke mata se kuma hannun data ji ya sake baki ɗaya tamkar ba ajikinta yake ba.

Ta lumshe lumsassun idanunta kana ta miƙe ta nufi toilet tana me furta.
“Allahumma Inni Auzubika Minal khubsi wal khaba'is�?.
Kana tashiga cikin toilet ɗin da komai ke akimtse yana fitar da wani irin ƙamshi Anutse tashiga yin alwalan har ta ida kana ta fito bayan ta furta.
“Gufra naka�?.
Bayan ta gabatar da Salla tayi adduo'i ta miƙe tare da naɗe darduman se kuma ta juya ta fice tana me buɗe hannunta da rufewa koda ze dawo dai-dai...

Zaune ta samu Momy kan kujera hannunta riƙe da hisnul Muslim tana Azkharul Masa,Yayin da Raudat ke gefenta daga ƙasa tana bin bakinta zama Khausar tayi daga gefen Raudat kanta aƙasa tace.
“Momy gobe zan tafi JAURO YAYAH�?.
Da mamaki Momy ta zuba mata ido jin mgnar a bakatatam cike da mmki tace.
“Zaki tafi Jauro yaya kuma Khausar?�?.
Ataƙaice Khausar tace.
“Eh�?.
tana mai cigaba da jan yatsun hannunta.

Momy ta sake duban ta da mamaki akaro na biyu tace.
“Anma babu yanda banyi dake ba jiya kan cewa kishirya yau kutafi tunda mutanen garinsu na zuwa sallan jumma'a sosai ku tafi tare, kika ce ba zaki tafi dasu ba kuna hadda, sannan kun kusa zuwa ƙarshen surar idan kika tafi karatun ki ze koma baya sannan na yarda na barki kan cewa se sati me zuwa yanzu kuma kice zaki tafi gobe�?.

Murmushi ta ƙaƙalo tare da faɗin.
“A'a Momy babu damuwa munyi magana da Asma'u tace koda awaya zan iya ƙarawa da kaina batare da anwuce Ni ba�?.
Dubanta Momy tayi tare da cewa.
“Kin tabbata Khausar har cikin ranki kikeson zuwa Jauro Yaya!?�?.

Kai ta gyaɗa tace.
“Eh�?.
Aranta kuwa cewa tayi ba gwara masifar wancan tsohuwar ba dan ko yaya bazan tsaya ta dake niba amma wannan mutumin ya riƙa tsareka da firgitattun idanunsa masu saka tsoro da fargaba, baya ga haka in banyi sa'a ba duka na zai sa ayi banyi masa lefi bama idan yasamu sarari sawa yake aci zalina bare kuma nayi masa laifi...

Muryan Momy dake cewa.
“Toh shikenan nima nafi so ki tafi Kinga idan hutun ku ya ƙare sannan anƙarasa muku gyaran makaranta seki dawo�?.
Ya dawo da ita daga duniyar data lula.

Kai ta gyaɗa tare da cewa.
“Shikenan Momy�?, Sannan ta miƙe ta shiga Bedroom ɗin ta.
Momy kuwa Hisnul Muslim ta ɗauka ta cigaba da Azkhar yayin da Raudat ta miƙe tabi bayan Khausar.

Ita kuwa khausar na shiga ɗaki ta hau kan stoll ta janyo trolley ɗin ta sannan tashiga haɗa kaya Raudat dake kallonta tace.
”Dani Zaki tafi Addah Khausi?�?.
Girgiza mata kai Khausar tayi alamar a'a.

Kuka

1 Comments On SAKAYYA
avatar
hajara-ahmad

1 year ago

Reply

Nice novel

Please Login or Register in order to submit comment