Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tare da cewa.
“Yaya Jameel Ina wuni ya ibada?�?.
M Jameel ya Amsa da.
“Alhamdulillah�?.
Miƙewa Bashir yayi ya koma ya cigaba da aikin da yake.

Moddibo kuwa bayan yayi tasbihi sai ya koma Azkharul masa ƙarfe shida da minti Ashirin da biyu aka kira Sallar maghariba Plate din Dabino da Ummi ta ajiye musu agabansu Anutse Moddibo ya miƙe tare da ɗaukan ruwa ya kuskure bakinsa kana ya dawo ya zauna.
Shima M Jameel miƙewa yayi ya wanke bakinsa dabino Moddibo ya ɗauka ya buɗe sanan ya sanya abakinsa bayan ya furta.
“Zahabazzaba'u Wabitallatil,Uruƙu wasu batul Ajri Insha Allah�?.
Anutse ya ke cin dabinon inda yaci sai ya sanya ƙwallon atafin hannunsa na hagu.
Guda bakwai yaci kana ya dakata.
M Jameel kuwa dabino Uku yaci kana ya janyo faranti kayan friut ɗin ya fara da Abarba.

Lumshe idanu Moddibo yayi tare da ɗaukar Inabi ya kai bakinsa sai kuma ya buɗe Idanunsa akan Ummin data ƙara so wajen zama tayi tare da tsirawa M Jameel idanu baki ɗaya hankalinta da nutsuwar ta yana kansa.

Iska Moddibo ya furzar daga bakinsa tare da jingina bayansa da jikin bangon ya lura da tun zuwansu wani irin kallon da Ummi ke bin M Jameel dashi kallone mai nuni da tsantsar so, da kuma ƙauna da shaƙuwa irin wanda uwa ke nunawa ƴaƴan ta.
Ƙasa da kansa yayi yayin da yaji ruwan hawaye masu ɗumi na tsata-tsafo masa saboda ganin shi ya rasa wannan damar bazai samu irin wannan ba arayuwarsa ba still Kansa na ƙasa ba tare daya ɗago ba ya dai-dai-ta muryarsa tare da faɗin.
“Ummi kiyi buɗa baki mana�?.

Sai asannan Ummi ta lura da kallon da take bin M Jameel dashi, Malam Ahmad ma murmushi yayi domin ya lura da kallon da Ummi kebin M Jameel dashi Shikuwa M Jameel sai alokacin ya ɗago kansa ya lura da irin kallon da Umminsa ke binsa dashi.
Murmushi yayi mai cike da so da ƙauna.
Kana yace.
“Ya dai Ummina nayi kyaune ko muni kike ta kallona?�?.

Ajiyar zuciya ta sauƙe kana ta ɗan lumshe Idanunta tare da girgiza kai kana tace.
“A'a kawai dai naga azumi ɗaya akayi ana biyu har ka rame�?.
Murmushi yayi tare da gyara zamansa kana yace.
“Hmmm Ummi kenan ai kinga mu ba azumin ne kaɗai ba. akwai yawon zirga-zirga sannan abincinma bama nutsuwa mu cisa yanda ya kamata musamman ma idan na biyewa Babanki�?.

Jinjina kai Ummi tayi kana tace.
“To yau kam anan sai kunci kuncika cikin ku sannan in dafa muku na Sahur ma ku tafi dashi�?.
Girgiza kai Moddibo yayi kana cikin sauri yace.
“A'a Ummi ki zauna Innayi na mana sannan ga can Asma'u na taya ta yanzu idan mun koma sai mun rasa inda zamu sanya abincin a cikinmu�?.
Jinjina kai tayi kana tace.
“Toh shikenan Babana�?.
Murmushi Moddibo yayi kana yace.
“Ummi kici abinci mana�?.

Kai ta gyaɗa sannan ta janyo Plate ɗin dabinon ta ci guda uku Bayan tayi addu'ar buɗa baki.
Malam Ahmad ma danino uku yaci sannan Ummi ta ɗauki Flaks da niyyar haɗa musu tea Moddibo dake cin friut yayi saurin cewa.
“A'a Ummi bari sai munyi Sallah�?.
Kai ta gyaɗa kana tace.
“Toh shikenan sai kun dawo�?.

Miƙewa sukayi M Jameel da Moddibo suka ɗauki buta kana suka ɗaura alwala suka fice Malam Ahmad kuwa ya riga su fita.
Kai tsaye masallacin ƙofar gidan su Ummi da Baban Asma'u ke limancin suka shiga. Suna idar da Sallar Maghariba bayan sun idar suka dawo cikin gida shigowarsu yayi dai-dai da rurin da wayar M Jameel keyi.

Kallon Moddibo M Jameel yayi kana yace.
“Innayi ce ke kira�?.
Jinjina kai Moddibo yayi tare da cewa.
“Uhm�?.
picking call din yayi ya kai kunnensa.

Daga ɗaya ɓangaren Innayi tayi gyaran murya kana tace.
“Jamilu lafiya baku dawo kunyi buɗa baki ba mai kuke yi har yanzu awaje?�?.
Sajensa ya shafa kana yace.
“Innayi wallahi Ummi ce ta riƙe mu wai saidai muyi buɗa baki agidan ta�?.
Murmushi Innayi tayi kana tace.
“Toh mu kuma na gidan mu ya zamu yi dashi�?.

Kallon Moddibo yayi sai kuma yayi Murmushi kana yace.
“Innayi abawa Almajirai dai sai kibar mana na Sahur dan nasan kinyi miyarki mai daɗin nan miyar me kika mana ma tukunna?�?.

Dariya Innayi tayi kana tace.
“Miyar roman da kake so na daddawa da ƙarago shi zanyi muku na Sahur�?.
murmushi ya saki tare da faɗin.
“Yauwa ina son wannan miyar�?.
Kai ta gyaɗa kana tace.
“Toh shikenan sai kun dawo ka gaishe da Ummin�?.
Ta faɗa tare da katse kiran.

Suna ida shiga gidan suka samu wajen suka zauna Ummi ta miƙe tare da ɗaukar Flaks da kofina ta haɗa musu tea mai kauri yana tururi kana ta zuba musu soyeyyen dankali da ƙwai.
Anutse suka fara ci kaɗan Moddibo yaci ya janye hannunsa daga ciki.
Kallonsa Ummi tayi kana tace.
“Ya dai Babana kaci mana�?.
Murmushi Moddibo yayi tare da ɗaura hannunsa na dama akan shafefen cikinsa ya shafa kana yace.
“Ummi na ƙoshi�?.
Girgiza kai Ummi tayi tare da cewa.
“Kai Babana me ma kuka ci?�?.
Ɗan kwaɓe fuska yayi kana cikin sanyin murya mai kama da shagwaɓa ya lumshe idanunsa tare da cewa.
“Ummi kar muje muna sallah abinci yan fitowa ta hancin mu�?.
Kallonsa Ummi tayi tare da murmushi kana tace.
“A'a Babana me ma kuka ci da zai zazzago ta hancinku?�?.
Murmushi yayi tare da shafa sajensa zuwa gemunsa kana yace.
“Allah Ummi mun ƙoshi ko ba haka ba J?�?.
Kai M Jameel ya gyaɗa tare da Hararan Moddibo ya cire hannunsa a Plate din dan kalin.
Hira suka sake taɓawa kana Moddibo ya miƙe tare da kallon Ummi kana yace.
“Ummi zamu tafi�?.

Jinjina kai Ummi tayi tare da cewa.
“Idan kunyi sallah Isha'i zaku dawo ta nan?�?.
Girgiza kai Moddibo yayi kana yace.
“A'a Ummi sai wani lokaci�?.
Gyaɗa kai tayi tare da cewa.
“Toh ku tafi da kunun nan�?.

Ajiyar zuciya Moddibo ya sauƙe tare da gyara tsayuwar sa kana yace.
“Toh Ummi ina son kunun abamu zan tafi dashi�?.
M Jameel ya juya ya kalli Ummi tare da langwaɓar da kai kana yace.
“Ummi Ni dai ba abani abinda nake so ba�?.
Cike da kulawa da kuma so ta juya ta kallesa kana tace.
“Me kake so?�?.
Murmushi yayi kana yace.
“Inabin za'a bani in tafi dashi�?.
Saurin Kallonsa Moddibo yayi sai kuma ya juya ya kalli Ummi tare da cewa.
“Ummi kar ki basa yasha muna dashi agida�?.
Tura baki M Jameel Yayi kana yace.
“Iyeee to na haƙura tunda ba aso ayimin kyautar�?.
Ummi Kam murmushi take Cike da ƙaunar su, ji takeyi tamkar su duka biyu a cikinta ta rainesu ta haifesu.
Sallama suka mata kana suka fice suka shiga mota Moddibo ke mazaunin Driver yayin da M Jameel ke gefen mai zaman banza kai tsaye Masallacin da suke limancin na ƙofar gidan Sarki suka nufa sunyi tafiya mai ɗan tsayi kafin suka isa lokacin da suka isa ankira sallar Isha'i suka shiga Moddibo ne yayi limanci suka idar da Isha'i kana sukayi Asham bayan an watse kana suka fito suka shiga mota wannan karon M Jameel ke driving Kai tsaye gidan Innayi suka wuce.

Ƙarfe takwas da rabi suka isa gidan bayan sunyi parking sun fito kai tsaye sashen Innayi suka shiga bakinsu ɗauke da sallama a farfajiyar gidan suka tarar da Innayi da Asma'u zaune Innayi dake gashin nama akan mangal da tarin gawayi agefenta ta daga kanta tare da Kallonsu kana ta amsa Sallamar su.

Ƙara sawa kusa da ita sukayi M Jameel yaja kujera ya Zauna kana ya Kalli Innayi tare da cewa.
“Innayi ya dai mai ake gasa wasa ne?�?.
Murmushi Innayi tayi kana tace.
“Nama nake dan gasawa nasanku da cin nama kamar kuraye!�?.
Dariya M Jameel Yayi kana yace.
“Aikam Innayi kin kyauta gashi asalin gashi na gargajiya kike yi�?.
Kai ta gyaɗa tana ɗaukar Plate tace.
“Eh ai nasanku�?.
Ta ida maganar tare da miƙa musu naman data yayyanka ta zuba a Plate tare dasa musu yaji agefe sannan ta yaryara ɗa musu man shanu.
Kallon Asma'u dake yi musu sannu da zuwa tayi kana tace.
“Asms'u ɗauko musu capet su zauna�?.
Cikin murza kai gefen dama da hagu Modibbo yace.
“Uhmm Innayi kin dai sanshi shi J ɗinki da son nama kamar kura�?.
Murmushi M Jameel yayi dan yasan tabbas Modibbo bai cika damuwa da namaba, asalima in dai gasheshene ko soyayya in dai yaci yanka huɗu zuwa biyar zaice muƙa-muƙinsa sun gaji da taunawa, in kuma dafaffene wani lokaci da haƙorin gaba zai ɗan tattauna in yaji ya gaji sai ya tura masa naman gabansa.
Shi kuwa M Jameel Allah ya sani yana masifar son nama, shi kuwa Moddibo yafi bawa ƴaƴan itatuwa mahimmanci.
Cikin murmushin yace.
“Yoh in ban so namaba me zanso A.J Namafa shine maƙurar daɗi�?.
“A wurinka ba, gashi kuma kana son koyamin�?.
Cewar Moddibon,
Asma'u kuwa ganin Innayi na kallonta cikin mamakin tace.
“A'a Asma'u ɗauko musu abin zama mana�?.
Kai Asma'u ta gyaɗa kana ta miƙe ta shiga falon ta ɗauko capet ɗin ta shimfiɗa musu awajen da yake agyare tass babu alamar ƙazanta.
Zama sukayi akai, Innayi ta sake kallon Asma'u tare da cewa.
“Haɗa musu Tea sannan kisa musu zuma yaji�?.
Kai Asma'u ta gyaɗa kana ta miƙe ta zuba musu shayi tare da zuba wadataccen zuma aciki ta kawo musu.

M Jameel kuwa Anutse ya kai yankan naman bakinsa lokaci ɗaya ya lumshe idanunsa tare da buɗe su akan Innayi kana yace.
“Kai gaskiya gashin nan yayi daɗi sosai�?.
Murmushi Innayi tayi tare da kallon Moddibo dake cin naman kamar ko yaushe kamar dai dole, yana ɗan taunawa kaɗan-kaɗan cikin kula tace.
“Kai kuma fa Moddibo?�?.
Ɗago kansa yayi ya kalleta kana yace.
“Uhm yayi�?.
Girgiza kai tayi kana tace.
“Wato kai dai baza ka iya Yabawa ba kenan?�?.
Kansa ya sake ɗagowa tare da kallonta kana yace.
“Ai gashinan J ya yaba kuma danɗanon harshen mu ɗaya ne ai�?.
Murmushi M Jameel da Asma'u sukayi.

Innayi kuwa baki ta taɓe M Jameel da Moddibo suka cigaba daci Ahankali Moddibo ya ɗago hannunsa tare da kallon tsadedden agogonsa kana ya mayar da Kallonsa kan M Jameel tare da cewa.
“Sai munyi sauri lokaci ya kusa J�?.

Kai M Jameel ya gyaɗa tare da cire hannunsa a Plate din kana yace.
“Toh shikenan mu tafi�?.
Miƙewa Moddibo yayi tare da kallon Innayi kana yace.
“Bari naje na canza kaya�?.
Daga haka ya juya ya nufi sashen sa, shima M Jameel bayansa yabi.

Moddibo nashiga Bedroom ya sauya kayansa zuwa Jallabiya Coffee color tare da ɗaura farin hirami irin na samarin larabawa kana ya feshe jikinsa da turarukansa masu daɗin ƙamshi.
Anutse ya fito falo ya samu M Jameel da shima ya canza kayansa buɗe fridge M Jameel Yayi ya ɗauki goran faro mai sanyi sannan suka jera tare da Moddibo suka sauƙa.

Kai tsaye sashen su Innayi suka koma batare da sun shiga farfajiyar gidan ba .

“Toh Innayi mun tafi�?.
Cewar M Jameel
Tana rufe roban yajin da suka ci nama dashi ta ajiye kana tace.
“Toh Allah ya tsare muma yanzu muna bayanku�?.
M Jameel na gyara ɗaurin agogon dake tsintsiyar hannunsa ya kalleta kana yace.
“Toh idan za kuje kuzo mu tafi mana sai mu sauƙe ku�?.

Girgiza kai tayi tare da cewa.
“Ai akwai Napep zamu hau�?.
M Jameel kuwa kai ya Girgiza kana yace.
“A'a ai abin baiyi ba bayan tanan muke tafiya kuma kuce zaki shiga Napep kawai kuzo mutafi�?.
Jinjina kai Innayi ta gyaɗa kana tace.
“To bari mu tattara da sauri sai mu tafi�?.
“Toh�?,M Jameel yace Shi kuwa Moddibo bai ce komai ba sai harɗe hannunsa da yayi aƙirji.

Cikin sauri Innayi da Asma'u suka tattare wajen sannan suka sanya hijabansu kana suka rufe kichen da gidan suka fice abayan Mota suka zauna ita da Asma'u yayin da M Jameel da Moddibo ke gaba.
Suna isa babban masallacin M Jameel yayi Parking Innayi da Asma'u suka fita suka nufi sashen mata su kuma suka shiga cikin masallacin daya cika sosai da al'umma.

Bayan sun zauna Kamar ko yaushe M jameel ya buɗe musu da addu'o'in kana Moddibo ya gyara system ɗin sa tare da ƙara rage girms Idanunsa kana yasa lallausan tafin hannunsa ya gyara zaman microphone din dake gabansa tare dayin gyaran murya cikin sanyayyar sautin muryansa ya fara kamar haka:
_“Auzubillahi Minal Shaiɗanir Rajim, Bismillahir Rahmanir Rahim.
(10) Innalazina ya'akuluna, Amwalal yatama zhulman innama ya'akuluna fiy buɗunihim naraa,wasayaslauna sa'irah�?._
Jama'ar dake wajen masallacin cikin sassarfa suka ƙaraso cikin masallacin dan basa so koda harafi ɗaya ne su rasa daga cikin karatun Moddibo saboda baiwar muryarsa.

Moddibo kuwa sanyayyar numfashi ya fesar tare da jingina bayansa da kujeran kana ya cigaba kamar haka:
_�?(11)Yusikumullahu fii auladikum,Lilzikri mislu hazzil unsaynan.Fa'in kunna Nisa'a fauƙasnatayni falahunna sulusa ma tarak,Wa'in kanat wahidatan falahannisf,Wali abwayhi likulli wahidin Minhumassudusu,Mimma taraka inkana lahuu waladun,Fa'in lam yakun lahu waladu wawarisahuuu abwahu fali ummihi sulus.Fa'in kana lahu Ikhwatun fali ummihi sudus min ba'adi wasiyyatin yusi biha audayn,abaukum wa'abna ukum latadruna ayyuhum aƙrabuna lakum naf',a,Faridatan Minallah,Innalaha kana aliman hakima�?._
Ya dire ayar tare da jan numfashin sa da ya riƙe.
Jinjina kai M Jameel Yayi yayinda ayoyin ke ratsa sa cikin yanayin sakewa ya lumshe idanu kana yace.
“Aya ta gaba�?.

Jinjina kai Moddibo yayi kana cikin zazzaƙan muryansa mai sanyi da ratsa jiki kana da nutsuwa ya cigaba da jan ayoyin saida ya kai aya ta Ashirin kana ya tsaya.
Shi kuwa M Jameel Cike da tsantsar ƙwarewa da nutsuwa kana da sanin makaman tafsir ya fara fassara ayoyin tare da cikekken kaddima da kowa amintattun haɗisai da suka da munasaba da ayoyin harma da sababul nuzur na ayoyi, lokacin ɗaya cikin masallacin ya sake samun nutsuwa tafsirin na ratsa su.

Ƙarfe goma dai-dai suka tashi tafsir ɗin mata suka fara fita ta ɓangarensu kafin maza suka fita acikin mota Asma'u da Innayi suka jira M Jameel da Moddibo goma da kwata dai-dai suka fito suka tafi.
Acan ɓangaren Khausar kuwa yauma kamar kullum taje tafsiri ita kaɗai ta dawo duk da masallacin a ƙofar gidansu yake bakinta ɗauke da Sallama tashiga cikin falonsu Anutse ta cire hijabinta tare da nufar kichen inda take jiyo motsin Mommyta kasancewar yau itace da girki yasa ko tafsir bata jeba.

Juyiwa Mommy tayi jin motsi abayan ta ganin Khausar yasa ta maida hankalinta kan aikinta kana tace.
“Kin dawo?�?.
Kai Khausar ta gyaɗa tana kallon tuƙeƙken tuwon shinkafa da Mommy ke kwashe maran ƙarshe.
Ahankali Khausar ta matsa kusa da Mommy kana tace.
“Mommy ki bari zanyi miyar�?.
Kai Mommy ta gyaɗa kana tace.
“Ok to Miyar zogala za kiyi�?.
Kai Khausar ta gyaɗa tare da ɗaukar.
Da fara aikin haɗa miyar zogalen.
Cikin abinda bai gaza awa ɗaya da rabi ba, duk ta haɗa ta sanya komai na buƙata kana.
Ta rufe nan danan kichen ɗin ya kaure da ƙamshin miyar sauran kayan da Mommy tayi amfani dasu ta haɗa ta wanke tare da sauƙe Miyar ganin tayi tik gwanin kyau.

Bayan ta gama ta buɗe miyar da yayi mugun kyau a ido ta ɗauki kular wani sashe ta zuba miya kasancewar babban gidana yasa kowa kaina nasa akeyi, na buɗa baki kuwa ki wacce a side ɗinta takeyi, mai girki zata sawa Lamiɗo, da Dadu, haka tsarin nasu yake.
Shigo wa Mommy tayi fuskarta ɗauke da murmushi ta kalli yanda kichen ɗin yayi fess ga ƙamshin miyar zogalan da yaki kifi da naman dariko, kallonta ta mayar kan Khausar kana tace.
“Sannu da ƙoƙari ki ɗauki na sashen Hajiya Bunayya ki kai mata�?.
Kai Khausar ta gyaɗa sannan ta ɗauka kular Hajiya Bunayya ta wuce Haidar Mommy ta ƙwalawa kira bayan yazo tace ya ɗauki kular sashen Gimbiya Dadu ya kaimata dan Mommy tunda ta lura da Khausar batason zuwa yasa ta rage aikanta sashen shi kuwa Haiydar daga sashen Gimbiya Dadu ya wuce sashen Hajiya Bunayya.

Hajiya Bunayya dake zaune akan kujera ta faɗaɗa fara'ar fuskarta ganin Haiydar ta tsira masa idanu kana tace.
“Babana kaine dama yanzu nake niyyan zuwa in yi maka albishir�?.
Murmushi Haidar yayi tare da zama kana yace.
“Daga sashen Gimbiya Dadu nake nace bari nazo na gaishe ki�?.
Murmushi tayi masu cike da Ma'anoni tayi kana tace.
“Insha Allah bayan sallah mashin ɗinka zai zo kaga dama tun shekara biyu baya naso saya maka Abbanka yace saika ƙara girma kuma kaga yanzu aika girma�?.
Jinjina kai Haidar yayi cike da tsananin farin ciki mara mistuwa ya gyara zamansa kana yace.
“Nagode Ummah Allah yarabaki da sharrin maƙiya�?.
Murmushin gefen baki tayi kana tace.
“Bana son godiyar nan Babana�?.

Cike da farin ciki ya miƙe ya nufi sashen su fuskarsa ɗauke da murmushi ya shiga falon zaune ya samu Mommy da Khausar.
Kallonsa Mommy tayi kana tace.
“Ina ka tsaya?�?.
Zama yayi daga gefen Khausar still.
Fuskarsa da murmushi da yakasa ɓoyewa ya numfasa tare da cewa.
“Mommy Machine ɗina ya Kusa isowa fa, kinga tun shekara biyu baya Umma taso siya min shine Abba ya hanata yace saina ƙara girma ai yanzu kam dai na sake girma bazai hana ba ta saya min Machine sabo mai kyau bayan sallah zai iso�?.

Khausar kuwa tunda ya fara magana ta tsira masa idanu saida ya kai aya ta sauƙe ajiyar zuciya mai zafi tare da furzar da iska daga bakinta kana babu walwala afuskarta ta kawar da kanta gefe tare da cewa.
“Kai kuma farin ciki kake ko?�?.
Juyawa Haiydar yayi tare da kallon ta kana yace.
“Sosai ma kuwa kema kamata yayi kije kiyi mata godiya�?.
Harara Khausar ta ɓalla masa.
Murmushi Mommy tayi kana tace.
“Rabu da ita ai ni zanje.
A yanzu kam aika girma yanda kake da tsawon ƙafan nan�?.

Murmushi yayi tare da kallon Khausar kana yace.
“Sosai ma Mommy ai yanzu na girma yanzu fa shekara kusan sha shida nake nema gashi mai shekara sha takwas ɗinma na fita koda yake sha bakwai ne da yan watanni ne ko gareta�?.

Jinjina kai Mommy tayi kana tace.
“Ai lallai dai kam kama cika sha shida kam Allah yasa kafara hawa asa'a.
Ubangiji ya tsareka da sharrin ƙarfe.
Allah yatsare gabanka da bayanka!.
Ubangiji ya makantar da idanun makiyan ka akanka!.
Allah ya tsare ku ga duk kan abinda zai cutar da rayuwar ku! Allah ya muku katangan ƙarfe da dukkan abin da zai zama sharri acikin rayuwarku!�?.
Cike da jin daɗin Addu'ar ta Haiydar yayi Murmushi tare da cewa.
“Ameen ya hayyu ya ƙayyum Mommy na�?.
Ajiyar zuciya Khausar ta sauƙe tare da kallon Mommy kana tace.
“Ameen ya Allah Mommy tunda kinyi addu'a magana ta ƙare baza'a ji tsoron komai ba babu bakin uwa akansu duk kan mai sharri zaiyi ya gama babu abinda zai sameshi da izinin Ubangiji�?.

Murmushi Haiydar yayi tare da kallon Khausar kana yace.
“Aikam Addah Khausy babu bakin uwa akaina duk kan wani mai mugun nufi zai ƙare akansa�?.
Murmushi Mommy tayi cike da ƙaunar ƴaƴan nata,
kallon ta ta mayar kansu tare da cewa.
“Ku tashi kuje kuyi bacci dan mu samu mu farka da wuri mu kaiwa Ubangiji bukatun mu�?.
Miƙewa sukayi tare da yiwa juyawa sai da safe kana kowa ya wuce ɗakinsa ya kwantar.

Misalin ƙarfe ɗaya na dare Mommy ta farka kallon Lamiɗo daya miƙe yashiga toilet tayi sai kuma ta miƙe ahankali ta tafi side ɗinta.
ɗakin Khausar tashiga tare da kunna haske.
Idanunta suka sauƙa akan Khausar dake sharan bacci ƙara sawa tayi tare da bubbuga ƙafarta kana tace.
“Khausar ki tashi kiyi nafilla�?.
Ahankali Khausar ta buɗe Idanunta cikin Muryan bacci ta kalli Mommy kana ta yunƙura ta zaune bakinta ɗauke da addu'a tace.
“Toh Mommy�?,Sannan ta Sauƙa ta shiga toilet.

Juyawa Mommy tayi ta koma ɗakin Lamiɗo lokacin data shiga har ya fara Sallah kai tsaye toilet ta shiga ta ɗaura Al'wala bayan tayi ta fito tare da shimfiɗa Sallaya ta tada Sallah cikin nutsuwa ta keyi bayan tayi sujja tayi Subhana Rabbiyal a'ala³ kana ɗaura da du'inta.
“Ya Allah kayuwa ƴata zaɓin alkhairi,Ya Allah kashirya Khausar kasata ahanya madaidaiciya Ya hayyu ya ƙayyum ka tsare mata imaninta, Ya Allah ka kare min Haiydar ɗina ya Allah katsaresa daga sharrin mai sharri ya Allah ka kare min ita ya Allah kabawa Ramadan da Raudat ilimi mai albarka da yayunsu dama dukkan ƴaƴan musulmai. Ya Allah katsare min ƴaƴana daga sharrin,Mutum, aljan da kuma ƙarfe, ya Allah katse min imanina Allah ka tsaremin zuciyoyinsu, ka tsaresu da sharrin hassada, ƙeta, munafurci, da ƙyashi ya Allah ka kare min mijina kabiya masa buƙatunsa na Alkhairi dama ɗauka cin al'ummar musulmai.
Bayan ta idar da nafillah ta ɗauki Alkur'ani ta shiga Muraja'a.

Khausar kuwa ƙarfe biyu da rabi bacci ya riƙa fisgarta akan Sallaya ta kwanta nan da nan bacci mai nauyi yayi nasarar ɗauke ta.
Can cikin baccinta ta fara wani mafarki mai cike da al'ajabi ganinta tayi.
Gata nan tsaye a wani ƙaton fili.
Baki ɗaya ilahirin filin ashare yake kuma , yashine malale a wurin iya ganinka sai wani irin haske mai masifar ƙyalli da ɗauke idon da ya cika wajen baki ɗaya, ahankali ta ɗaga kanta ta fuskanci gabas, da sauri ta rumtse idanunta gani wata ya fito ta gabar juyawa tayi taga yamma da sauri Still nan ya fito ta yamman sake juyawa kudu tayi still ta nan ma ya fito ahankali ta sake juyawa arewa, wani irin masifeffen karkarwa jikinta ya farayi, ganin tanan ma watan yafito duk kusurwa huɗu wata ya fito sai asannan ta lura da haskensa ne yake ɗauke mata ido.
Ahankali taga wani kyakkyawan.
Yaro fari ƙal agabanta yayinda gashin kansa ke kwance lib-lib, daga bayansa ta hango wani kyakkyawan mutum sai dai fuskarsa na kallon gefe hannunsa na kan yaron yana shafawa cikin wata.
Sanyayyar murya yake kallon yaron kana yace da ita.
“Wannan shine jininmu mahaɗinmu, wannan shine sanadin haɗayyarmu bugun zuƙatanmuuuhh�?.
Ya ƙarasa jan kalmar cikin wata iriyar ƙasalalliyar murya mai cike da shauƙi.
Ita kuwa ƙoƙari take taga fuskar mutumin sai dai ta kasa sai iya fuskan kyankyawan yaron take iya kallo.
Dai-dai lokacin kuma ta buɗe Idanunta jin Muryan Mommy nacewa.
“Khausar, Khausar ki tashi zaki makara fa ƙarfe huɗu tayi bakiyi Sahur ba anjima kaɗan zaki fara ce mana kin fara jin wahalar azumi�?, Ta faɗa tana buga ƙafarta da saurin Khausar ta tashi zaune tare da sakin ajiyar zuciya kana tace.
“Innslillahi wa'inna ilahi rajiu'n Hasbunallahu wani'imal wakin Astagfirullah wa'atubu ilaik�?.
Sai kuma tayi addu'a ta shafa.
Mommy dake tsaye har yanzu kuwa sake taɓata tayu tare da cewa.
“Khausar kada ki koma bacci fa kitaso�?.
Kai ta gyaɗa kana tace.
“Mommy na tashi bazan koma ba�?.
Juyawa Mommy tayi ta fice ita kuma Khausar toilet ta shiga.
Brush tayi kana ta fito kai tsaye falon ta nufa.

Samu tayi Mommy ta haɗa mata ɗumamen tuwon jiya da Tea mai kauri ahankali ta zauna tare da kai tuwon bakinta da ƙyar ta haɗiye baki ɗaya jikinta yayi mugun sanyi da mafarkin da tayi.
Mommy dake zaune a kujeran falon ta juya ta kalleta ganin bata cin tuwon yasa ta girgiza kai tare da cewa.
“Kici abinci fa Khausar kin sanki sarai da cin abinci anjima kaɗan zaki fara cewa yunwa kike ji�?.
Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da fesar da iskar bakinta kallon Mommy tayi kana cikin sanyin murya ta lumshe Idanunta tare da cewa.
“Mommy wallahi tuwon ne nakeji kamar ba zai shiga ba babu wani abu ne?�?.
Kai Mommy data tsira mata Idanu ta gyaɗa kana tace.
“Kije kichen akwai indomie dana ɗaura wa Haiydar shima yace ba zai ci tuwo ba to amma ke kam nasan indomie ba wani riƙe Miki ciki yake yi ba�?.

Lumshe Idanunta tayi kana ta buɗe su akan Mommy ahankali ta motsa laɓɓanta tare da cewa.
“Bari in cisa yau ɗin kam amma Mommy da kifi ne koda nama�?.
Tayi tambayar ne domin bata fiye son kifi ba.

Kawar da kai gefe Mommy tayi kana tace.
“Da kifi ne idan zaki ci kici idan kuma baza kici ba ki bari�?.
Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da jan siririn tsaki kana tace.
“Bari dai inci, tuwon ne naji kamar bazai ciwu ba shi ɗin ma miyar aida kifi�?.
Mommy dai Bata sake cewa komai ba ahankali Khausar ta miƙe tashiga kichen ta ɗauki Plate ta ɗibi yanda zai isheta kana ta fito ta zauna tare da Bismillah ta fara ci bayan ta gama ta ɗauki tea da Mommy ta haɗa mata da bread taci.
Haiydar ne ya shigo da Sallama idanunsa akan Plate da Khausar ta gama cin indomie.
Kallonsa Mommy tayi kana tace.
“Jeka ɗebo indomie yayi sannan ka taho min da tuwo�?.
“Toh",Ya amsa kana ya wuce kichen ɗin ya juye indomie sannan ya zubawa Mommy tuwon ya fito.
Khausar dai na zaune tana lumshe Idanunta tare da tuna irin mafarkin da tayi wanda ya tuno mata wanda tayi shekaru biyu baya a Jauro Yayah.

Ahankali ta saki ajiyar zuciya tare da juyawa ta kalli Haiydar da yagama Sahur ɗin ta gyara zamanta tare da cewa.
“Haiydar nikam yanzu wani surah kake?�?.
Murmushi yayi kana yace.
“Ke ɗin wace surah kike?�?.

Zama ta gyara tare da cewa.
“Hmmm aini nayi nisa ina Maryam kaga insha Allah zan samu sauƙa biyu�?.
Kai ya gyaɗa mata tare da cewa.
“Toh ni ina Yasin Insha Allah zan samu sauƙa uku insha Allah duk azumi goma zanyi sauƙa ɗaya�?.
Murmushi Mommy dake duba wani littafin addini tayi kana tace.
“Masha Allah yayi kyau Khausar ya akayi kika tsaya wasa ya wuce ki�?.
Langwaɓar da kai tayi kana tace.
“Mommy kinga ai shi baya taya ki yin aiki nice ke tayaki aiki kinga shi duk lokacin daya keso

1 Comments On SAKAYYA
avatar
hajara-ahmad

1 year ago

Reply

Nice novel

Please Login or Register in order to submit comment