Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Wanda ya tsaya gwiwarta wani irin kyau tayi na ban mamaki sosai Uniform din ya amshets tamkar dan ita akayi.
A gaban Dressing mirrow ta tsaya ta ɗauki kwalban turare sun kai kala biyar ta feshe ilahirin jikinta dashi sannan ta ɗauki combos Fari ta Sanya tare da ɗaukar school bag ɗinta ta rataya kana ta fito falo.

Murmushi Mommy tayi tace.
“Manana kinyi kyau�?.
Ta juya manyan Idanunta tace.
“Nogode Mommy na�?.
Haiydar kam murmushi yayi yace.
“Yau za'ayi ruwa da ƙanƙara shugaban ’yan letti ta riga kowa shiryawa�?.

Harara ta maka masa batare da tace komai ba ta shirya Raudat sannan sukayi Breakfast suka shiga mota Amina sai Harara take watsa mata ita kuwa khausar bata ma san tana yiba domin aƙasan ranta tunanin haɗuwarta da Moddibo take da kuma irin hukuncin da zai yanke mata.

Suna isa Makarantar lokacin har anfara shiga class cikin sauri sauri Khausar ta riƙe hannun Raudat suka nufi side dinsu Raudat ta ajiyeta a class kana da sauri ta juya, zata fita class ɗin kenan.
Taji Raudat ta saki ƙara tare da kiranta.
Da sauri ta juya tare da kamo Raudat ɗin da taga tana jujjuyawa, tsugunawa tayi tare da cewa.
“Raudat menene ya faru�?.
Cikin kuka da yarfa hannu Raudat tace.
“Wayyo idona Adda Khausy ido, borkono".
Da sauri ta jawota tare da fara hura mata idon.
Sai kuma ta amshi goron ruwar da Antin su ke miƙa mata.
Wonke mata fuskar ta ta farayi tare da murza mata idon.
Cikin Sa'a kuwa ɗan abin da ta shiga idon ya fita.
A hankali ta buɗe idann nata, da tuni yayi jazir.
Cikin sanyi tace.
“Ayyah Raudy na sannu ko, yanzu dai ya fita ko?�?.
Kai ta gyaɗa mata tare da kama hannun Antin nasu.
Ganin hakane yasa Khausar juyawa da sauri ta fito ta nufi harabar makarantar.

Shiru ba kowa a tsakiyar harabar alamun an gama shiga class kenan.

Cikin sassarfa ta fito daga side din ’yan nursery.
Kana ta nufi sude ɗinsu.

Da sassarfa ta nufi kan step ɗin.
Dai-dai lokacin kuma Moddibo ya fito daga class dinsu ya nufi ƙasa, a hankali yake take steps din yayinda hankalinsa baki ɗaya yana kan....!




Ki biya ki karanta, kiji ainin manufar labarin kiyi dariya kiyi shauƙi kibi haushi kiki tausayi kiyi kuka. Kiyi murmushi




By
*GARKUWAR MARUBUTA*
9/13/23, 20:03 - Buhainat: 📝🍇✨💫⏰🤴🏻👹❤️❤️❤️🍇

*SAKAYYAH*
_Page 9_

NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*FREE PAGE NE ƴar uwa ki biya ki karanta abinki cikin Salamah, littafin SAKAYYAH 1k ne kacal 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276. Kana in saki a Groups da na buɗe ba SAKAYYAH in da zaki karanta abinki salamun ƙaulum min rabbil rahim. Nama lfy fata lfy. Ba ruwan ki da jiran na sata na Allah ya isa*


Cikin nitsuwa yake tafiya, tare da taka steps ɗin a hankali, yana sauƙa ƙasa, yayinda hankalishi baki ɗaya ke bisa system nashi dayake kan hannunsa na dama yana daddanashi da hannun hagunsa, bisa dukkan alamu.
Abu mai mahimmanci ne yakeyi.

A dai-dai lokacin kuma Khausar ta iso bakin steps ɗin, cikin sauri take tafiya, da alamun tsoron kada malami ya rigata shiga aji ne.
Da sauri take tattaka steps ɗin tanayi sama.
Steps biyu ta taka ana uku, taji juyo da kanta da sauri dan jiyo muryar M Jameel na ce mata.
“Khausar sai yanzu?�?.
Ba tare da ta tsaya ba, kana bata kuma juyo kanta ba taci gaba da tafiya a haka, hannunta na kan da ƙarfe dake gefen steps ɗin cikin yanayin sakewarta da M Jameel ɗin tace.
“Wallahi tun ɗazu muka iso fa Malam�?.
Yana mai binta da ido yace.
“To kuma meya hanaki shiga class?�?.
Still bata janye kanta daga kallonsa ba, kana bata tsaya daga haurawa saman da takeyi ba tace.
“Raudat ce ta tsaidani a side ɗin su�?.
Da sauri yace.
“Da me ta tsaida ki?�?.
Ɗan guntun murmushi tayi tare da cewa.
“Wai ƙwarone ya shiga idonta, shinefa tai ta ihu taƙi sakina dole saida aka cire matashi Allah sai kaga yadda idonta yayi jazir�?.
Kanshi ya sunkuyar yana ɗan murza zaɓen azurfan dake yatsar yace.
“Ayya kwaro bai kyauta ba ya shiga idon Gimbiya Raudat�?.
“Ai dai kam fa�?.
Ta faɗina tana mai ƙoƙarin juyo kanta.
Cikin tsokana yace.
“Gashi kuwa har Malam Moddibo ya shiga ajinku�?.
Cikin sauri ta kuma juyo kanta da dama bata gama juyashi ba cike da kaɗuwa tace.
“Da gaske?�?.
Kai ya gyaɗa mata tare da cewa.
“Tun ɗazuma kuwa�?
Cikin yanayin tsoro ta ɗan zaro manyan udanunta tare da cewa.
“Na shiga ukuna�?.
Murmushi M Jameel yayi tare da cewa.
“Ato kiyi sauri ki hau, in kinyi sa'a ya barki ki shiga�?.
Jin haka yasa ta juyo da sauri tare da taka step ɗin gaba kana tayi kwanan haurawa kam steps ɗin da zai sadata da sama.
Wanda kuma dai-dai lokacin Moddibo ma ya taka step na ƙarshen kwanan.
Unexpected taji tayi karo da mutu.
Shi ma Moddibo ba zato ba tsammani yaji kanta ya bugi ƙirjinsa yayinda hannunta ya bugi System ɗin dake hannunsa ya subce ya tafi ƙasa da sauri ya sunkuyo ya cafe system ɗin da kana ya miƙe tsaye,

Ita kuwa Khausar cikin sauri ta ɗago kanta dai dai lokacin kuwa ya ɗago kansa shima ido cikon ido suka kalli juna kamar a fuzge ya furta.
“Again?�?. a lokacin guda kuma, cikin tsananin takaici da zafin rai ya ɗaga tafin hannunsa na hagu ya yarfa mata wani irin gigitaccen mari mai masifar zafi gami da raɗaɗi.

M Jameel kuwa jin sautin sauƙan marin ne yashi ɗago kansa da sauri.

Ita kuwa Khausar wani irin gigitaccen ihu mai cike da rauni tare raɗaɗi ta saki, tare da dafe kuncinta kana ta rumtse idonta wanda duhu mai tarin yawa ya mamaye mata gani, kana tayi taga-taga ta koma baya zata faɗi, jin ta tafi suuuuu ƙafarta ta sule yasa takuma sakin wani ƙaran tare da buɗe idanunta, sai kuma tayi sauri ta medasu ta rufe sabida ganin wasu irin taurarin masu wutsiya da tartsatsi suna gilmawa ganinta sabida zafin marin da yasa suka mamayewa ganinta.

Gaba ɗaya ta sadakar domin tasan muddin ta faɗo nan to ita da karaya sun zama aminan juna.

M Jameel kuwa kanshi ya riƙe da hannu bibbiyu tare da faɗin.
“Innalillahi!!�?.
Wanda faɗin hakane ya jawo hankalin Malam isa da yazo wucewa ta gefensa.
Shima ma Malam isa idonsa ya rumtse da ƙarfi tare da cewa.
“Yah Salam�?.

Shi kuwa Moddibo cikin takaici yayi sauri miƙa hannunsa da nufin kamo hannunta amman ina tuni tayi nisa.
Sai yatsunta biyu ya samu ya riƙe da masifan ƙarfi.
Wanda saida suka bada sautin ƙas-ƙas.
Cikin zafin nama ya fincikota da ƙarfi wanda hakan yasa ta afka jikinsa.

Ita kuwa Khausar jinta a jikin mutum ne yasa tayi masa wani irin sahihin rugguma mai cike da razani dan gani take kamar dai har yanzu bata tsira ba.
Kanta ta cusa cikin ƙirjinsa tana mai shaƙan turarensa mai masifar ƙamshi.
Wanda a take nitsuwarta ta fara dawowa.

Shi kuwa Moddibo cikin tsoro da wani irin masifeffen abu da yaji ya soƙi tsakiyar kansa har zuwa cikin ƙahon zuciyarsa kana ya harba masa wasu irin masifaffun baƙin al'amuran a cikin jijiyoyin jikinsa da suka sa jikinsa sakin wani irin masifeffen karkarwa da sabauta aniyarsa, ya ware hannunsa tare da rumtse idanunsa da masifan ƙarfi.

M Jameel kuwa ajiyan zuciya mai ƙarfi ya sake tare da jingina bayansa da jikin ƙarfen.
a hankali ya kuma sakin numfashi tare da kallon yadda Moddibo ya buɗa hannayensa duka biyu kana ita kuma Khausar tana kwance bisa ƙirjinsa tayi lip tana ruggume dashi da masifan ƙarfi.

Wani irin shu'umin dariya mai sauti M Jameel ya sake.
Wanda hakan yasa Moddibo buɗe idanunsa kana dai-dai lokacin yaji gaba ɗaya tsikar jikinsa na tashi.

Malam isa kuwa sunkuyar da kansa yayi yana murmushi.

M Jameel kuwa dariya yake tare da nuna Modibbo da Khausar ɗin wacce tuni fuskarta tayi jazir shatin yatsun hannunsa sunyi ruɗu-ruɗu a farar fatarta.
Cikin sauri Moddibo ya ɓalle hannunta daga jikinsa tare da matsawa gefe da sauri.
Wani irin tsuke fuskarsa yayi tare da watsa mata kallon da yasa hantar cikinta kaɗawa.
Wanda cikin rawan jiki da rawan murya cike da rauni tace.
“Ana Aspet ya Mu'allim Allah mi larai ma on! Please! Kayi haƙuri�?.
Ta ƙare mgnar cikin tsoro tare da gwamusa yaruka hudu duk a wuri ɗaya dan neman afuwa.
Shi kuwa Moddibo juyawa yayi tare da ratsa gefenta ya wuce kana cikin wata fusatacciyar murya mai matuƙar firgitarwa yace.
“Biyoni!�?.
Cikin ɓarin jiki tace.
“Toh�?.
Sannan ta miƙe tabi bayansa.

M Jameel dake riƙe da System ɗin yana juyawa yayi saurin bin bayansa da faɗin.
“Alhamdulillah kamar babu abinda ya samu System ɗin�?.
Shi dai Moddibo ko juyawa baiyi ba bare kuma ya tankawa M Jameel.

Malam Isa kuwa dake ƙasa ido ya zirawa Khausar dake sauƙwa dafe kuncinta da kunne ya da tun da tasha marin ya bada sautin kauwww har yanzu ƙaran takeji, kana ga idanunta da suka kaɗa sukayi jawur asanda ta saƙƙo yace.
Fattanah sam bakya yin abinda ya dace a rayuwarki�?.

Cikin zafin raɗaɗin marin da fuskarta keyi ta ɗago Idanunta da suke sake girma da ja ta kalli Malam Isa sai kuma tace.
“Wallahi bansa niba ne na juya ina kallon Malam Jameel ne dake yimin magana ne mukayi karo�?.
Bata jira jin abinda zai ce ba tabi bayan M Jameel dake biye da Moddibo.

Cak Khausar ta tsaya daga bakin Office ɗin, karo na farko kenan arayuwarta da zata fara shiga Office ɗinsa, duk da cewa da basu da office da yawa, amma yanzu gyaran da akayi an haɗa Malamai biyu akan Office ɗaya Office din ba wasu masu girma bane, haka zalika ba ƙanana bane, sannan duk kusan ajere suke.
Ahankali Khausar ta maida Idanunta bakin office ɗin da akasa wasu irin flowes masu launi mai kyau da ɗaukar hankali aka jera suna fitar da wani irin sanyayyan ƙamshi.
Cikin Office ɗin kuwa Madaidaitan deks ne da kujeru ɗaya na fuskantar gabar ɗaya na fuskantar yamma daga gaban ko wanne kuma akwai kujeru guda biyu daga kan deks ɗin daga gefen damar sa akwai wani Cubet kamar kanta dake ɗauke da tarin littattafai na addini da kuma na boko cikin wajen kamar dai Library haka wurin yake.
Daga gefen hagunsa kuma flowes ne masu kyau da tsari daga jikin bangon kuma Room hitane ne maƙale abango yana fitar da ɗumi mai daɗi a jiki,
Sai kuma labulayen window da suka kasance farare sol Sanyayyan iska na kaɗawa daga bangon kudu dake kallon yamma TV ne maƙale abango daga tsakiya kuwa wani irin dakekken turkey carpet mai yawan gashi fari sai ratsin maroon kaɗan. sosai Office ɗin yayi kyau.

Shi kuwa Moddibo cikin nutsuwa da kuma zafin da zuciyarsa keyi masa ya zauna akan kujeran dake gabar yana fuskantar yamma yayin da M Jameel ya zauna akan kujeran dake yamma yana fuskantar gabar kana da sunan ko wannensu ajiki kujerarsa.

Ita kuwa khausar cikin tsananin tsoro ta ƙarasa shiga office ɗin tare da tsugunnawa agaban table ɗin da Moddibo ke zaune.
Ta riƙe kunnenta Muryanta Araunane wanda ke nuni da tsantsar tsoro da tashin hankali tace.
“Malam kayi haƙuri bansan kana tahowa ba�?.
Shi kuwa Moddibo ko kallonta baiyi ba saboda yanda zuciyarsa ke tsananin ta farfasa ya tabbata idan yace zai daketa to zai iya karyata ko kuma ya sumar da ita hakan yasa ya janyo kujeran dake kusa dashi ya ɗaura ƙafafunsa akai kana ya lumshe idanunsa tare dasa hannu ya janyo Hiramin dake kansa ya rufe saman Idanunsa.

Cikin tsantsar nutsuwa da kuma sanyayyan sautin muryarsa mai zaƙi ya fara rara Ƙira'a acikin suratul Rahman yasan hakan shine kaɗai zai sanyaya masa ransa da zuciyarsa yasan muddin yace zai daketa ayanzu zai iya sumar da ita ko kuma karyata.
Saboda abubuwan da yarinyar ke masa yayi yawa.
Sabida tsabar raini da rashin kunya fa har gidansu ta bisa tayi masa rashin kunya sannan ta jima sa ciwo ayatsun ƙafansa wanda ya ɗauki tsawon kwanaki yana fama da ciwo.
Kana yaje ƙauyen su nan ma bata barshi ba saida ta bisa tayi masa rashin kunya ta nemi jefa shi acikin ruwa da wannan masifeffen sanyin garin nasu,
kana amakaranta ma bata barsa ba shin tsaranta ta mayar dashi kome?.

Ita kuwa khausar cikin Sanyayyar Muryanta me cike da tsoro tace.
“Ayyah malam na tuba kayi haƙuri wallahi bansani bane�?.
Ƙin tanka mata Moddibo yayi ya cigaba da rera karatunsa cikin zazzaƙan muryansa.
Shi kuwa M Jameel Gyaran murya yayi hakan yasa Khausar tayi saurin Kallonsa da manyan Idanunta da suka kaɗa sukayi jawur.
Da ido yanuna mata Moddibo alamar ta cigaba da basa haƙuri.
Kai ta gyaɗa sannan ta cigaba da cewa.
“Ayyah Malam na roƙeka kayi haƙuri bazan sake ba�?.

Acan sama ajinsu Khausar kuwa wani irin tsarin gini ne mai matuƙar kyau da ɗaukar hankali wasu irin windon Glass ne tsala-tsala masu tsayi da kyan tsari sannan ga flowes masu fitar da sanyayyan ƙamshi kana ga Room hita guda biyu gaba da baya daga farkon shiga class ɗin kuwa wani irin Black Board ne mai tsari irin wanda ake amfani dasu a manyan makarantu, kana ga wasu irin kujeru na zaman ɗalibai masu taushi da kyau, agaban ko wani kujeran ɗalibi akwai sunan sa ajiki, hakan yasa duk ɗalibar data shiga baza tasha wahala neman wajen zamanta ba wanda kuma manna sunan ake bisa alamu in an tashi kawai ɓarewa za'ayi a saka sunayen sabbin waɗanda zasu shigo ajin, kujeran Khausar shine na farko acikin jerin kujerun dake gaba da sunanta manne kamar haka _Khausar Usman Abubukar Lelewal._
Samira Sani ce ta ɗan juya Idanunta kan kujerar dake gefenta.
Wanda sunan Khausar dake manne kujerar afarkon.

Wani irin ya mutsa fuska tayi tamkar wacce taga wani abin ƙi cikin taɓe baki da tsanar mamallakiyar sunan tace.
“Ikon Allah wannan shine suna mai buƙatar hadda sunaye huɗu duk masu tsawo!�?.
Ta Ida maganar tare da bankawa kujeran harara tamkar Khausar ɗin na kai, kana ta zauna daga baya inda sunan ta ke kai.

Asma'u dake gefe azaune tace.
“Ha'a sunane de ai ba wani abu ba kuma duk sunayene masu inganci da Kekkyawar nasaba naga dai sunanta sunane na ɗiya ga Annabi Muhammad (S.A.W) sannan sunan mahaifinta sune na sahabin Manzon Allah (S.A.W) haka zalika sunan kakanta sune na sahabin Manzon Allah (S.A.W).
Lelewal kuwa naga suna ne da kowa ke fatansa�?.

Abeeda Sule ne ta watsa wa Asma'u harara tare da faɗin.
“Ke kuma wayasa bakin ki?�?.
Taɓe baki Asma'u tayi kana tace.
“Ai gaskiyane daga kallon sunan baiwar Allah zata fara ƙanan magana�?.
Ɗaya daga cikinsu manyan matan ajin nasu ne wacce bata fiye magana Hajia Khadija tace.
“Da wannan hatsaniyar da kukeyi tunda Moddibo ya fita tun ɗazu akan zaije ya dawo bai dawo ba aigwara kuje ku duba ko lafiya mai ya tsaida shi aji ba kowa kuma shine muke da First period?�?.

Cikin zumuɗi Samira Sani tace.
“Gaskiya ne kam bari naje na kirasa�?.
ta ida maganar tare da ficewa ta sauƙa ƙasa.
Cikin yauƙi ta nufi Office

Tana isa idanunta suka sauƙa akan Khausar dake riƙe da kunnenta, ga kuma Idanunta da suka sauya,
yayin da shi kuwa Moddibo idanunsa ke lumshe yana rera karatun Alkur'ani cikin Sanyayyar sautin muryansa daya haɗu da ɗumin room hita ga ƙamshin daddaɗan tularensa.
Numfashi mai nauyi ta fesar tare da tsirawa yalwataccen sajensa daya ƙawata kyawun fuskarsa idanu sai kuma ta maida kallonta kan zara-zaran yatsun hannunsa dake kan table yana ɗan bubbugasu ahankali cike da shauƙi tace.
“Wowww�?.Faɗar hakan da tayi shi ya janyo hankalin M Jameel yayi saurin juyawa ganinta tsaye acikin Office din yasa shi faɗin.
“Lafiya?�?.

Sai asannan ta dawo cikin nutsuwarta still Idanunta na kan Moddibo tace.
“Malam Barka da safiya�?.

“Barka dai�?.

Still idanunta na akan Moddibo tace.
“Malam dama munzo kiran Malam Moddibo ne, shine muke dashi tun ɗazu ya sauƙa, akan cewa zai zo ya ɗauki wani abu sannan kuma bai koma ba�?.

Da ido M Jameel ya nuna mata Moddibo da har zuwa lokacin idanunsa ke lumshe yana karatu sai dai ya rage sautin muryansa ya koma fita asaman laɓɓansa.

Shi kuwa Moddibo jin Muryanta yasa ya janye Hiramin dake fuskarsa kana ya buɗe idanunsa da har zuwa yanzu akwai alamun ɓacin rai acikinsu, kallo ɗaya ya mata ya kawar da kansa gefe.
Ita kuwa Samira gefe ta koma ta tsaya.
Khausar kuwa lumshe Idanunta da suka kaɗa sukayi jawur tayi sai kuma ta buɗe su still Hannunta nakan kunnenta tace.
“Ayyah Malam kayi haƙuri�?.
Shi kuwa Moddibo juyawa yayi tare da kallon M Jameel yace.
“J ka da keta�?.
Da sauri M Jameel ya juya tare da nuna kansa da babban yatsa kana yace.
“Ni!?�?.

Cike da tsuke fuska Moddibo ya gyaɗa masa kai kana yace.
“Eh ka daketa!�?.
Zare Ido M Jameel yayi tare da cewa
“Meyesa?�?.
A kufule Moddibo yace.
“J kadaketa nace!�?.
Kallon mamaki M Jameel yake masa tare da cewa.
“Akan me zan daketa?�?.
Cike da ɓacin rai Moddibo yace.
“Idan fa ka bari nace ni zan daketa zan sumar da ita fa!, zan karyata fa!!�?.
Cikin tsananin fusata ya ida maganar.

Ita kuwa Khausar tuni jikinta ya hau rawa Allah ya sani bata son duka, sannan mari ɗaya daya mata ya mugun gigita mata ƙwaƙwalwa wanda har zuwa yanzu take jin raɗaɗin sa asaman fuskarta.

Fuskarsa babu walwala yace.
“Idan har nace zan daketa zan sumar da ita�?.
Ita kuwa Khausar jin azaban mari ɗaya daya mata, aranta tace Ashe Allah ya rufa min asiri da yasa duk lokacin da nayiwa Moddibo laifi baya duka na yake sa Malam Adam display master ke dukana na tabbata dashi yake dukana kullum da tuni ya kasheni!.

Cikin hanzari ta juya tare da kallon M Jameel ta miƙa masa hannu Muryanta na rawa tace.
“Malam ka dakeni!�?.
Girgiza kai M Jameel yayi cikin sanyin murya yace.
“Ni dai kam bazan iya ba bazan iya dukanta ba Moddibo, ka dubi fuskarta fa mari ɗaya da ka mata kalli fuskarta fa ai ya wadatar wani hukunci ya rage bayan wannan?�?.
Ya kare mgnar a hankali
Moddibo kuwa cikin fushi yace.
“Kada keta in kuma baza ka daketa ba zan daketa da kaina fa�?.
Cikin sauri M Jameel ya fara girgiza kai yayi cikin wata Sanyayyar murya me cike da zallar jin ƙai tare da tarin tausayi gami da rauni yace.
“La! La!! La!!! A.J bazan iya ba! Wlh Bazan iyaba ba wannan ba hurumina bane hurumin taɓa ta awajenka yake bani da karsashi ko ƙwarin gwiwar da zan iya taɓa ta!�?.
Ya ida maganar cikin wani irin salo na daban, kana dai-dai lokacin Amina tazo Office ɗin domin kiran M Jameel ya shiga ajinsu wani irin sarawa kanta yayi jin yanda yake cewa bazai iya ba.
Da sauri ta dafe ƙofar office ɗin jin jiri na ɗibarta kadde ace dokon soyayyarsa za tayi abanza, kadde Khausar yake so yanda ya ƙarashe maganar na nuni tamkar itace rayuwar sa.

Da sauri Moddibo ya juya ya kalli M Jameel jin yanda yayi magana da kuma yanda ya lanƙwasa harshensa abun ya bashi mamaki.
Azuciye Moddibo yace.
“In daketa kenan?�?.

Langwaɓar da kai M Jameel yayi cikin sanyin murya yace.
“Kayi haƙuri ina mai bada haƙuri amada dinta ka nemi wani punishment ɗin ka bata amadadin wannan, amma nikam bazan iya dukan taba sannan kaima banaso ka daketa!�?.
Baki ɗayan su kallon Mamaki suka bi M Jameel dashi ganin yanda yake lanƙwasar da murya tare da nemawa Khausar ya fiya, ita kuwa Amina wasu hawaye ne masu zafin gaske ne na tsananin kishi da baƙin ciki, suka zubo mata saurin ta sanya hannu ta share.
Kwantar da Murya M Jameel ya kuma sakeyi ya cigaba da cewa.
“Kallifa A.J mari ɗayan nan da kamata kalli fuskarta fa ka daketa awaje mafi daraja�?.

Moddibo kuwa lumshe idanunsa yayi kana ya buɗesu akan M Jameel tare da cewa.
“J kadaketa ni idan nace zan daketa bazai mata daɗi bafa�?.
Sake Langwaɓar da kai M Jameel yayi kana yace.
“Kayi haƙuri Moddibo ni bazan iya dukanta ba!�?.

Ita kuwa Samari Sani na tsaye agefe ta harɗe hannayenta aƙirji yayin da ta zubawa Moddibo ƙananun Idanunta ko ƙyaftawa ba tayi.
Ita kuwa Amina Idanun ta nakan M Jameel da idanunsa ke kan Khausar zuciyarta nayi mata zafi.

Khausar kuwa kallon M Jameel ta sakeyi akaro na barkatai tace.
“Malam Jameel ni dai ka dakeni�?.
Kai ya girgiza mata tare da faɗin.
“Bazan iya dukan ki ba Khausar!�?.

Shi kuwa Moddibo cikin tsananin ɓacin rai ya juya ya kalleta a kufule yace.
“Toh inda keta da kaina!?�?.
Girgiza kai M Jameel yayi sai kuma yace.
“A'a asassauta mana dan Allah�?.
Ƙwafa Moddibo yayi da faɗin.
“Shikenan kije ki kaɗe ɗan kwali sau ashirin�?.

Cike da tsoro ta zaro ido domin kaɗe ɗan kwallon da yace yana nufin ta cire ɗan kwalinta tasa abokitin ruwa ta matse kana ta kaɗe har sai ya bushe,
sannan ta sake sakawa cikin ruwa ta matse kana tayi ta kadewa har sai ya bushe.
Tofa jin haka ne yasa a tsorace ta zare Ido Jin hukuncin daya yanke mata ba zata manta lokacin daya sata kaɗewa sau goma ba awannan lokacin ma saida tayi sati biyu gaɓɓanta na ciwo ko abu zata ɗauka da ƙyar take iyawa.

Cikin yanayin neman alfarma M Jameel ya sake langwaɓar da kai kana yace.
“Dan Allah ka sassauta mata karage mata�?.
Jin Muryan M Jameel yasa ita ma ta kalli Moddibo cikin wata raunatacciyar murya tace.
“Dan girman Allah Malam kayi haƙuri karage min�?.

Shi kuwa Moddibo wani kallo ya watsa mata cikin haɗe girar sama dana ƙasa yace.
“Kada ki sake haɗa ni da girman Allah da kinsan darajar girman Allah da zaki mutunta Malama ki,
kije kiyi shabiyar kinci darajar girman Allah.
idan kika sake cemin dan Allah in rage miki kuwa nida ke bibbiyu!�?.
Gyaɗa kai tayi kana tace.
“Toh shikenan�?.
Shi kuwa M Jameel kallon Moddibo yayi cikin jujjuya ido yace.
“Ina neman alfarma abarta tashiga aji tayi karatu idan antashi Break sai tayi�?.

Shi kuwa Moddibo Ɓata fuska yayi yace.
“Bana son ganinta a aji Idan naganta a aji zan kakkaryata in wurgar ta window�?.
Ita kuwa Samira Sani cikin lanƙawasa harshe tace.
“Malam Moddibo mu tafi�?.
Sake tamke fuska yayi tare da juyawa ya watsa mata wani bayyane harara sai kuma ya nuna mata ƙofa alamar ta ɓace masa da gani.

Sum sum ta juya da sauri ta fice.
Da harara yabi bayanta Aransa yace.
Shegiyar yarinya mai kama da Mayya,
sai shegen kallon jaraba tasani gaba zakiyi dan rashin kunya.

Samira Sani kuwa tana shiga ajinsu ta lumshe Idanunta tare da kallon gefen ko wannen kujera dake ɗauke da flowes ta saki murmushi mai cike da jin daɗi,
tasan wannan aikin Moddibo ne domin kaf cikin Malaman shike son flowers.
Hajia Ruƙayya ce ta dubi Samira data shigo kana tace.
“Ni kam ya banga Khausar ta shigo ba har yanzu kuma ɗazu na hangota kafin na haura�?.
Juye Ido Samira tayi tare da faɗin.
“Tana can tayiwa Moddibo rashin kunya yana cin Ubanta, shegiyar yarinya fitsararriya ‘yar marasa tarbiyya!".

Asma'u ce ta juya ta kalleta rai a haɗe tace.
“Haba Samira meyesa zaki zagi iyayenta ai bai kamata ki zagi iyayenta komai yaya iyaye nada daraja�?.
Harara Samira ta wurga was Asma'u kana ta buɗe baki da niyyar magana ta fasa sakamakon shigowar Moddibo.

Ganin shigowar Moddibo yasa ta tsuke bakinta tare da neman waje ta zauna cike.
Cike da ladabi suka gaishesa cikin harshen larabci tare da faɗin.
”صبح�? خير ىاعثتذ�?
Ya Amsa da.
“صبح�? نور كىفل قراء�?.
Suka amsa da.
”الحم�? الله�?
Kasancewar Tafseer zasuyi dake yanzu lokacin Islamiyya ne yasa yace.
“Kuyi muraja�?.
Cikin bawa ko wanne harafi hukuncinsa suka shiga karanta suratul Muhammad har zuwa karshe.
Bayan sun gama kawo haddan ya jinjina kai tare da faɗin.
“Sai gobe Insha Allah zamu fara tafsirin sa�?.

Aɓangaren M Jameel kuwa tare suka jera da Amina suka nufi ajinsu yayin da azuciyar Amina yayi baƙiƙƙirin data tuna yanda M Jameel ke karyar da murya akan Khausar har suka isa ajin tunanin da take aranta kenan yanayin yanda tsarin ajinsu Khausar yake haka ko wanne aji yake cike da ƙwarewa M Jameel ya shiga yi musu ƙarin Mi'atu Hadith daga na Arba'in bayan sun karanta masa.
Ko wanne aji da Malami aciki suna darasi.

Ita kuwa Khausar ita kaɗai ce tsaye aharabar Makarantar cikin gajiyawa ta ɗaga boket ɗin ruwan ta koma rana wai ko zata samu yafi bushewa da wuri, tsoma ɗan kwalin tayi aciki kana ta matse sannan ta fara kaɗewa.
Nannauyan ajiyar zuciya ta saki tun akaɗewa na uku taji hannunta ya sage aranta tace.
“Insha Allah Ina komawa gida zan nemi ɗankwali mai shara-shara mara nauyi wanda kodan irin rana ta yau ta faru zaimin sauƙi.
Cike

1 Comments On SAKAYYA
avatar
hajara-ahmad

1 year ago

Reply

Nice novel

Please Login or Register in order to submit comment