Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya taka muhimmiyar rawa wajen samun saukin nauyin da zuciyar ta ke mata.

Haka doctor Abbas ya cigaba da kwantar mata da hankali hadi da bata shawarwari masu amfani a matsayin sa na wanda ya girme mata ya Kuma fi ta hangen nesa, ya sauke numfashi da ya lura ta ɗan saki jikinta, yana son yi mata maganar Maleek kan ya kamata ya san da cikin amma yana tsoron kada hankalin ta ya tashi, domin ya fahimci bata kaunar ko jin sunan sa, bazai yi gaggawa ba, zai bari zuwa wani lokaci ya kara mata magana, she kansa bazai so Munaya ta kara ganin shi ba kamar yadda ya faɗa, he really mean it, amma zai yi hakan ne saboda darajar jaririn innocent soul din da bai san komai ba, bai kamata yaron ya tashi da maraici ba, bayan yana da uba, da haka yayi mata sallama, ya kuma bata ledar da yayi mata siyayyar kayan kwalama, domin ya san ba a rasa mai ciki da cima irin wanna, karon farko da Munaya ta masa godiya.
"Thank you, Ubangiji Allah ya saka maka da gidan aljanna, You re truly a kind man" ta karasa hawaye da suka zame mata aboki ya gangaro mata...

Ya saki murmushin jin dadi, ya kuma ji dadin improvement daya gani yau tare da Munaya, ko ba bakomai ta danyi magana yau, ya san har da kewa rashin mutum ke kara wa Munaya damuwa, da da yanda zai yi da ya dinga kasancewa da ita daga safe har dare, da sauran murmushin da bai gushe daga fuskar sa ba yace "Ameen Ameen, wa'iyyakum"
Munaya bata ƙara cewa komai ba ta juya zuwa cikin gidan.


Washegari da safe Munaya taji cikin ta ya Murda, kana ya bada sautin mai ƙara alamun yunwa, ba shiri ta janyo ledar da doctor Abbas ya kawo mata jiya, jikin ta da hannun ta na rawa ta bude ledar ta ga snacks ne da yoghurts a ciki, sai dai yoghurt ɗin yayi tsami ya dauko hanyar lalacewa saboda zafi, hannu ta saka ta dauki meat pie daya ji filling din naman Sa, amma shi bai lalace ba, hannu baka hannu kwarya ta shiga ci sosai, tun da take bata jin yunwa irin na yau ba, gaba-daya ta kasa controlling yunwar, sai da ta ci meatpie din guda uku gasu manya kana ta ji daidai, ta sha yoghurt din duk da ba dad'i a baki, ta shiga sauke ajiyar zuciya, domin dazu ji tayi kamar zata mutu....

Mintuna uku da gama cin meatpie din nan amai ya taho mata, kafin tayi yunkurin mikewa amai ya zubo, ta shiga kwararawa a nan dakin, cikin seconds kalilan ta jigata sosai, da kyar ta iya jan kafa ta dauki summa ta goge aman kana ta wanke bakin ta, ta dawo dakin ta kwanta tana jan numfashi tamkar wacce zata mutu, ramar data yi ya kara fitowa ƙarara, idanun ta ya shige can cikin loko, gwanin tausayi, ta na a cikin wanna yanayin har bacci mara dadi ya dauke ta.


*Mummy *
*(Sa'adah)*

Zaune take a dakin ta, tsadaddiyar wayar ta a kunnen ta tana waya da Hajiya maimoona, cikin damuwa tace "maimoon bazaki gane ba, wallahi na gaji fa, mutumin nan yaki komawa inda ya fito bare na samu in aiwatar da abin da yake raina, bai taba zuwa ya jima irin haka ba, ko jikin shi ne yake bashi I'm after something? domin kin san jiya a lokacin da muke tarayya da shi, saboda yanda na kai kololuwa a bukatar dan sa, bashi ba, sunan sa na dinga kira, gaba-daya ban sani ba, ke na so tona asirin kaina, da asuba yake tambaya ta wai ya ina kiran sunan Maleek, wani Maleek din? Na ji tashin hankali amma na maze nace Ni Alhajina, a'a Ni ban kira sunan kowa ba, sai dai idan kunne ka ne bai juyo maka ba daidai ba, ai Ni jiya kaso zautar dani Alhajina, ina gaya miki da haka na samu ya bar maganar"...


Daga can bangaren Hajiya maimoon tayi dariya sosai tace "wato Sa'adah kin cika shu'uma, Wato dai kin nace sai kin dandani yaron nan, anya Sa'adah baki hada dangi da Mayu ba wanna naci yayi yawa, bayan akwai yara irin sa da suka fishi komai".....


Cikin sauri mummy ta katse ta da cewa" bazaki gane ba maimoon, kin san Ni na raini yaron nan, na san mena gani, ke da ba dan ina kishin sa ba da wallahi bayan na cika burina a kan shi zan baki aron sa ki dandana ko sau daya ne, amma ina bazan yi ba, yanzu ma dana yi maganar baki ji ba zuciya ta suya take, ke ina kishin yaron nan sosai fiye da tsamanin ki, Kin san Allah wanna yarinyar daya tare da ita da zan ganta kuma na san inda zan same ta babu abinda zai hanani yi mata ko me yazo raina, kai! I can kill person because of that boy ooo" ta karasa maganar cikin yanayin su na kangararrun mata da suka manta cewa jindadin duniya ƙadan ne.


Daga can bangaren Hajiya maimoon ta tabe baki tace "a'a rike Kayan ki Sa'adah bana so, ina da masu gamsar dani yanda nake so, kice zaki iya wanna wahala amma banda ni wallahi, yanzu dai ki samu ki lallaba Alhajin naki ki ji yaushe zai tafi"

Da haka da suka yi sallama da Hajiya Maimoona ta ajiye wayar, kana ta mike domin zuwa wajen Alhaji Dawood, ta tarar da shi a general falo yana karanta jaridar Daily trust mummy ta zauna a hannun kujerar da yake zaune tace "Barka da hutawa Alhajina"

Ya dago kansa daga jaridar yace "Yawwa Sa'adah kin fito?"......


"Eh" ta amsa tana sakin murmushin da bai kai zuci ba


Shiru ya ɗan ratsa na wasu mintuna kana mummy tace "Ni kam Alhaji wanna karon ka dade sosai, hakan bazai shafi kasuwanci ka ba tunda baka nan? Kasan mutanen yanzu babu tsoron Allah, mutum yana nan ma ya aka kare bare an ga babu idanun sa"

Alh.Dawood ya saki murmushin jin dadi na samun mace mai damuwa da duk wani abu ɗaya shafe shi, ya kalle ta yace "wato Sa'adah tunda na dawo wanna karon sai na ji ban son komawa can, baki ga yaya Laraba data zo rannan har da kukan ta ba kan kar na koma, Ni ma kuma na yi kewar kasa ta sosai"

Dum dum!! Kirjin Sa'adah ya shiga bugawa, hankalin ta ya kai kololuwa a ɓaci, saboda Alhajin ta yana son jiga mata aiki.
Alhaji Dawood ya ɗora da cewa "amma in sha Allah na kusan dawowa gaba-daya, tunda Allah ya bani zaratan samari har biyu zasu na zuwar min lokaci zuwa lokaci Domin kula da harkokina na can, kin ga nima na huta ko?"

Sa'adah ta sauke boyayyen ajiyar zuciya, ta sa a ranta cewa kafin ma ya dawo ta gama cika Burinta a kan Maleek, a lokacin ta riga ta lalata shi da soyayyar ta da bazai iya guje mata ba, wanda ko da Alhajin ya dawo Maleek zai dinga nema musu hanyar gamsar da junansu, tunda ya shigo hannu, da wanna tunanin ta samu ta kwantar da hankalin ta...



***

Kamar kullum idan Shakur bai da lectures da zai koyar yana tare da Maleek, cikin kaunar juna suke hira, a cikin hirar ne Shakur yace "Maleek da bana nan Munaya bata zo ba har yanzu? wallahi kullum ina tunanin yarinyar nan, jikina na bani like she's not okay"

Maleek ya hade fuska yana girgiza kansa alamun bata zo ba, ya Shakur zai tambaye shi yarinyar nan, yana kokarin cire maganar ta a ransa shine Shakur zai tambaye shi, Shakur bai lura da canjin yanayin da dan'uwan na sa ke ciki ba ya riko hannun sa yace "Maleek ka tuna alkawarina? Ka tuna nace idan Munaya ta bayyana a garemu, zan fada maka wata magana, za kuma ka cika min Ita"

"Yeah I remember, Amma ka fadamin me kake so na maka Shakur, dole sai ta dawo, What if ba'a sake ganin ta" a ransa yana fatan kar a ganta har abada, domin a kullum yana ganin shigowar ta Cikin rayuwar sa ba alkhairi bane, abinda ya fi kona masa rai shine ta saka ya aikata abinda bai taba aikatawa ba koda a Spain ne da yayi karatu, shi da yake ganin mata kusan rabin su tsirara, amma abin takaici a jikin kwaila Munaya ya fara sanin ya Mace, ya hadiyi wani yawu mai daci a bakin sa.

"In Sha Allah zamu ganta" Shakur ya katse masa tunani Cikin tabbaci, Maleek ya sauke numfashi a boye, ya zare hannun sa daga na Shakur ya cigaba da aikin da yake a system, so yake ya dawo daidai, domin yana kokarin rasa nutsuwar sa, duk sanda aka yi maganar ta sai yaji kirjin sa ya Sanja bugu, ya rasa meke masa dadi, he hate Munaya with passion, ya tsane ta, daga lokacin data shigo rayuwar sa komai ya dagule masa, ya saki siririn tsaki mara sauti yana rufe system din Domin ko aikin baya ganewa....


****

Tsaye yake a kofar gidan su Munaya kamar yadda ya saba, yana jiran ta fito, bayan shudewar mintuna biyar ta fito, amma maimakon ta fito inda yake, Sai ta sulale a soron gidan ta zauna, tana jin bazata iya fito ba, domin sam bata jin ƙarfi a jikin ta, cikin sauri ya shigo soron bakin sa dauke da sallama, ya durkusa gaban ta yana kiran ta "Munaya, Munaya Are You ok?"

"Bana jin ƙarfi a jikina" tace wasu hawaye na zuba a idanun ta, ya dauke kansa gefe, yana jin tausayin ta mai yawa a zuciyar sa, ta kara ramewa da lalacewa, hakan kuma na tabashi sosai idan ya ganta, cikin kulawa yace "Munaya bakya cin abinci, ba ke kadai bace kin tuna? Ko da bazaki ci ba dan kan ki, just be eating for the sake of the innocent baby you re carrying please, Ina jin ba daɗin ganin ki cikin wannan halin"

Ta tsuke fuska har girar ta na tattarewa "dan Allah ka daina min maganar cikin nan wallahi banasooo"

Doctor Abbas ya yi saurin cewa "toh shikenan kiyi hakuri" lallai akwai tarin kuruciya a tare da Munaya, ya kara tabbatar da hakan yau. Cikin lallabawa yace "TOH naji babu ruwan ki da shi amma kina ci dan lafiyar ki kin ji ko, yau ma na kowa Miki kayan dadi, na san zaki so shi"...

Suka yi shiru na wasu dakika, sannan yace "yawwa ina ta son in yi Miki magana, babu yan'uwan ki a nan kusa ki fada min, Ni zan je na musu bayani da kaina, karki ji tsoro, nan gaba bazaki dinga zama ke kadai ba babu idon babba ba, so tell me idan akwai yan uwa ko dangin ku Ni zan je na faɗa musu, kuma za su fahimta in Sha Allah "

Idanun Munaya suka soma kafewa suka ƙara ciko da kwalla tace "bamu da Kowa a nan kasar, asalin mu yan Chadi ne, daya baya iyayena suka bar Chadi zuwa nan Nigeria, dama can dangin mu dana sani yan sirarru ne, kuma iyayena basu kara zuwa Chadi ba, haka ya saka ban san Kowa na mu ba, a ranar da Umma ta haifi Amnah, Abba mu ya tafi ya bar ta, wai bazai iya cigaba da zama da ita ba saboda tana haifen ya'ya mata, har yau bai dawo ba, ban san Kowa nawa ba wallahi" ta karasa maganar da fashewa da kuka" doctor Abbas yaji ransa ya ɓaci, kana tausayin Munaya mai yawa ya kara cika zuciyar sa, dama akwai maza masu irin wannan jahilcin har yanzu, menene bambancin ya'ya maza da mata? Idan wani abu na daukakar rayuwa ne akwai matan da suka fi maza, ta yaya wasu mazan zasu ce lallai sai namiji suke so, abinda basu isa su siya da kudin su ba Amma suna zaba? kyautar Allah ce, ga wanda yaso yake bawa, Allah da kansa ya karrama ya'ya mata cikin littafin sa mai tsarki, wane mutum, wane dan adam da zai ce bai son ya mace, ya sauke numfashi, ya shiga kwantar wa Munaya da hankali, da alƙawarin zai cigaba da kula da ita da dukkanin iyawar sa, da kyar ya samu tayi shiru, ya koma mota ya dauko kayan daya siya mata ya tilasta mata Lallai sai data ci wani abu a ciki a gabansa, ya ɗan jima yana ɗebe mata kewa kana yayi matsy sallama ya tafi.





*Na kusan kamalla free pages, a Yau kuma zuwa gobe nayi promo, duk wanda ya biya dari uku zai samu karanta* *MunayaMaleek har karshen sa, amma ranar Litinin ainihin farashin sa na 500 zai cigaba da aiki ngd*.





MunayaMaleek is not for free, it's 500 via 3200689860
first bank, shaidar biya ta 07082281566, thank you for your patronage! Allah ya kara muku budi.
[14/12, 12:54 pm] 𝙽𝚘𝚘𝚛𝙸𝚖𝚊𝚗✨: 🍇MunayaMaleek🍓



_By NoorEemaan_📚✍️


Xv....

(15)


Duk wanda ya ga Munaya a Yanzu a kallo daya zai fahimci Akwai juna biyu a tare da ita,
gaba-daya ta kara lalacewa saboda cikin mai laulayi ne, ga karancin shekaru uwa uba babu mai zama ya kula da ita, baka hango komai sai cikin, Bawai saboda girman ba, sai dan mugun ramar data yi yasa cikin nuna kansa, a kullum idan ta kalli yanda cikin ke girma sai ta fashe da kuka, gaba-daya ta dawo wata kala babu kyawun gani.

Kamar yanzu zaune take ƙishirwa take ji sosae, makogwaron ta a bushe take jin sa, domin har wani kaikayi yake mata, gashi babu ruwa a gidan, domin na rijiyar ma ya kafe, ta tuna doctor ya bata kuɗi zuwan sa na ƙarshe, ta zari hijab ta saka, ta ɗauki dari biyu Cikin kudin ta fita zuwa kantin, hannun ta boye cikin hijabi saboda mutanen unguwa, da son samu ne da babu inda zata fita domin fitan ta babu abinda zai ƙara mata sai damuwa, musamman yanxu daya kasance rana ne. mintuna shida ya Kaita katin ta siyo pure water hadi da dawowa, har ta sha leda daya a wajen mai kantin domin ta kasa hakurin zuwa gida, ji take Kamar zata mutu, sai dai tana daf da zuwa kofar gida ta ga wasu yara ƙanana na wasa suna kallon ta, suna dariya, bata kawo komai a ranta ba ta cigaba da tafiya. Ta tsaya cak dalilin jin abinda yaran suke cewa, bugun zuciyar ta ya karu, tamkar zata faso kirjin ta ta fito "Munaya! Tayi cikin shege, Munaya! Tayi cikin shege" abinda suke maimaitawa kenan suna tafa hannu cikin sigar waka, har mutane sun dan fara taruwa, hawaye masu zafi suka zubo mata, bata juyo ba ta ruga cikin gidan da gudu tana kuka, yaran suka biyo ta har soro suna cigaba da fadin "Munaya! Tayi cikin shege" abin mamaki yara ƙanana sun san mace mai ciki, babu haufi iyayen su ke gulmar suka ji, sun jima suna yi, kana Muryar wani babban mutum ya daka musu tsawa hadi da kore su, ya kuma jawa kofar langa_langan su, hakan ya saka ta huta da jin abinda yaran ke faɗa, sai dai babban fami maganar su ta yi mata a ciwon dake zuciyar ta, ta cigaba kuka Kamar ranta zai fita, tsanar cikin da shi kan shi Maleek da a kullum yake daduwa a ranta, amma tafi jin tsanar su a yanzu fiye da ko koyaushe, ta shiga buga cikin da motsin sa ya yawaita tun data shiga 15weeks, take kanta ya fara ciwo tamkar zai rabe, kuzarin kukan ma ba da ta shi, hakan yasa ta yi shiru ba dan kukan ya daina zuwa bane, ta shiga sauke ajiyar zuciya, har bacci ya dauke ta a zaune tana sakin shesheka a cikin baccin.

***
Mita yake cikin zuciyar sa domin tun dazu masu bada hannu a titi suka tsayar dasu, gaba-daya a gajiye yake, yayinda a gefe daya na zuciyar sa tunanin yanda zai lallaba Munaya ta amince ta fada masa in da wanda ya Mata lalata mata rayuwa yake, domin ya kamata ya sani, ko dan jaririn ko jaririyar da za a haifa ya san da baban sa, amma ya ga kwata kwata bata son ayi maganar sa, ba kuma ya son hankalin ta ya dinga tashi, ya saki ajiyar zuciya yana tunanin mafita, kamar ance ya kalli sama ta gefen hagun su ya hango wani katon gini mai kyau da tsari, a saman an rubuta *A.A DAWOOD MOTORS* ya ɗan kankance ido yana son tuna a ina ya taba ganin irin wanna sunan amma ya kasa tunowa har aka bada hannu, ya daga kafadu yana tabe baki, sai dai sunan dake saman building ɗin ya ki bacewa a zuciyar sa, ya shiga tuki a hankali, har yayi nisa, can yace "yes Munaya!" Tabbas a jikin ledan da Munaya ta saka kudin asibitin Amnah ya gani, tabbas hakan ya gan wanna sunan, ya juya yana son sake kallon rubutun amma ya ƙasa saboda nesan, yayi gaba kadan ya ga wani U. Turn hakan ya saka ya juyo da saurin sa.
Bayan ya iso kofar gate din ya danna horn, Nura mai gadi ya fito zuwa wajen doctor Abbas ya gaida shi, Ya amsa cikin sauri, wata zuciyar na tunasar masa da cewa ya aka yi ka tabbatar da cewa shine, what if ba shi bane, amma zan tabbatar yanzu domin Munaya na yawan faɗin na tsani Maleek, bana kaunar ganin sa. Ya saki. numfashi kana ya leko da kansa ya kalli Nura yace "Maleek na nan kuwa?" Ya faɗa freely tamkar dama ya san shi.

"Eh boss na nan" Nura ya karasa fada hadi da nufar wajen gate domin buɗe masa, ajiyar zuciya Abbas ya saki, yana hamdala da Allah ya kawo masa komai cikin sauki, duk da ba zai so wata alaƙa ta haɗa MunayaMaleek ba, amma zai so ya san cewa Munaya na dauke da cikin sa, yana hakan ne saboda yaron ya samu gatan da duk wani da yake samu, duk da yaron bai zo ta hanyar da ake so ba, amma pure soul ne, bai ma zo duniyar ba ɓalle ya girma ya aikata zunubi, dan me za'a hukunta shi da laifin uban sa? da wanna tunanin ya hau benen kamar yadda aka kwantata masa, kwatancen ne ya kai shi floor din da office din Maleek yake ya ga an rubuta *CEO OFFICE* da kyakkyawan rubutu, kansa tsaye ya tsaya a kofar glass din har ya buɗe kansa sannan ya shiga, ya hango zaratan samari biyu masu kyau, aji da haiba a zaune, aka shiga kallon kallo a tsakanin su, shi doctor yana tunanin waye Maleek a cikin su, su kuma na tunanin waye wanna da zai shigo kan sa tsaye???...

*Mummy*
Tsaye take a kitchen, tana girkawa Maleek one of his favorite food Bolognese spaghetti jollof daya ji minced meat, farinciki bayyane a fuskar ta domin sabon malamin tsubbun ta ya tabbatar mata wannan karon matuƙar Maleek ya ci girkin nan babu abinda zai hana bai nime ta da kansa ba,
Hakan yasa jiki na rawa ta shiga tsara girkin na sa, domin already ta saka masu aiki yin girkin da sauran mutanen gidan zasu ci, saboda yanda ta kagu ya dawo a yi komai a gama, sai da girkin ya rage kadan ya yi ta fito da wani ƙaramin kwalba daga cikin bra din ta, wani abu ne cikin kwalbar wani abu mai dan kauri da maiko kalar maroon mai turuwa, ta saki murmushi tana tuno yanda aka ce maganin zai yi aiki, lallai ta yarda ta kuma tabbatar domin tana wajen karbar maganin wasu mata na zuwa suna fada masa yanda aikin da yayi musu ya ci kamar yankan wuka, hakan ya saka mummy kara yarda da aikin sa, ta buɗe kwalbar ta juye cikin spaghetti Bolognese din ta saka spatula ta jujjuya da kyau, seconds goma kacal ya kara ta sauke abincin hadi da juyawa cikin warmer mai daukar ido, ta kai dakin ta, domin so take ya zamana itace zata bashi da kanta yaci, domin bata yarda ta bar abincin a dinning ba, tafi son ya zama ita ce zata gabatar masa da shi da kanta domin aikin yafi ci tamkar yanda mutumin daya bata maganin ya fada, domin bayan wahalar zuwa wajen da ta yi domin a wajen gari yake, ga makudan kudaden data kashe kafin ta mallaki karamin kwalbar nan, amma bata damu da kuɗin ba, domin cikar burin ranta Worth kuɗin da ta kashe...


****
A nutse shakur ya ce "lafiya gentleman, who are you please, wa ka ke nema?"

"Maleek! waye Maleek among you two?" Doctor Abbas ya fada fuska a turbune.

"You didn't answer me, i said waye kai?" Shakur ya fada yana kallon sa.

Cikin dan fada-fada doctor Abbas yace "ban zo nan dan in gabatar maka da kaina ba, important issue ne ya kawo ni nan, who's Maleek here" ya faɗa yana rarraba idanun sa kan su.


Maleek dake cike da jin haushin Abbas musamman irin amsar da ya ji yana bawa kanin sa ya kara haɗe girar sama da ta kasa, har tsakiyar girar ta tattare yace "ba za a gaya maka waye Maleek ba, har sai ka fadi waye kai, You even have the guts ka shigo min office kan ka tsaye babu neman izini? now live my office" ya fada hankali kwance, irin na cikakken namiji daya iya boye bacin ran sa, sai dai fuskar sa kadai zaka kalla ka tsorata.


Doctor Abbas ya tako zuwa dab da Maleek yace "oh i see....you most be Maleek, because you are so arrogant and proud" shima doctor Abbas ya mayar masa cikin jin ciwon halin da ya jefa Munaya a ciki.

Maleek ya mike a zafafe zai isa gareshi, sai dai jin abin da doctor Abbas ɗin ya fara faɗa ne ya saka shi tsayawa cak.

"barin fito maka a mutum, domin kimar ka bata kai ayi magana ta fahimta da kai ba, Innocent girl da ta sanadiyyar ka take cikin kuncin rayuwa ne dalilin zuwa nan wajen nan da kake ikirarin office ne, i swear ko ta wacce hanya sai na bi wa Munaya hakkin ta, wadannan sune takardun asibitin ta, she's carrying your baby, tana dauke da cikin ka dan wata hudu" Dum! Dum!! Daram!!! Kirjin Maleek, Shakur da shi kan shi doctor Abbas din dake maganar ya yi lugudan bugu, sai dai shi nashi na ɓacin rai ne, shiru ya ratsa office din, tashin hankalin Shakur kuwa bazai misaltu ba, domin muraran ya nuna a fuskar sa kasancewar bai iya boye abu ba, ya mike cikin sauri ya kamo hannun Abbas ya zaunar da shi, domin ya dauka y'a'yan ta ne, cikin rawar Murya da damuwa yace "kayi hakuri, na san kana cikin ɓacin rai, ka kwantar da hankali ka, ka cire ɓacin rai a Muryar ka ka mana bayanin da zamu gane"

"Shi wanda yayi aika aikar ya san komai ai"

Shakur ya yi imanin Maleek bai san da zancen cikin nan ba, Toh ina ma ya ga Munayan balle ya sani?"

Kamar doctor ya san tunanin da Shakur yake yace "ya san ciki na shiga ai, kafin ya aikata son zuciyar sa" ya faɗa yana wurgawa Maleek wani mugun kallo.

Shakur ya dafa kansa kana yace "kayi hakuri dan Allah, ka sanar da Ni, You have no idea of yanda nake neman ta kullum tunda d abin nan ya faru"

Doctor Abbas ya kasa musawa Shakur domin yafi Maleek saukin kai nesa ba kusa ba, ya kuma lura kamar Maleek din bai gaya masa komai a yanda ya faru ba, sai daya kara watsa wa Maleek wani kallo mai kama da kishi kana ya kalli Shakur ya fara cewa "a watan march ranar 25 ga wata ita ce ranar da Munaya ta kawo kanwar ta Amnah asibitin da nake aiki...."

Maleek ya runtse idanun sa, har abada bazai taba manta wanna date din ba.

Doctor Abbas ya ɗora da cewa "ban taba ganin yarinya karama cikin rayuwa irin ta Munaya ba, so a ranar i was wondering Ina iyayen ta da zasu bar karamar yarinya da wahalar zuwa asibiti, so ganin halin da yarinyar da take ciki yasa na karbe ta na bata

1 Comments On MUNAYA MALEEK
avatar
nusaibabello

12 months ago

Reply

Dghhjhujvghkjvg

Please Login or Register in order to submit comment