Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gado hadi da yin duk wani taimako dana san zai taimaka wa Amnah, bayan na saka mata drip, aka kawo min tests Dana sa aka yi running mata na gane cewa yarinyar na dauke da cutar daji ta ƙwaƙwalwa wanda har ya kai stage wanda bazai ji magani ba fa ce surgery, Munaya cried to my office, na mata bayanin cewa ga halin da kanwar ta ke ciki, ta durkusa gabana tace dan Allah na taimaka na yi wa Amnah aikin zata nemo kudin a duk inda yake, she even told me that a fara yi wa kanwar ta aikin ko da bazamu sallame su ba, ta yarda mu cigaba da rike Amnah har sai da biya kuɗin ita dai burin ta kanwar ta ta warke, na Girgiza kaina nace Mata hakan bazai yu ba saboda dokar asibitin ce haka ba a fara aiki sai an ajiye kudi kuma kudaden kimanin miliyan uku da dubu dari tara ne, so nace mata ayi gaggawar samun kudin asibitin domin yarinyar na cikin ciwo sosai, nace mata taje ta sanar da dangin su domin a samu mafita, dana sani ban bari ta fita ba, saboda dalilin fitar ta yayi sanadiyar halin da take ciki yanzu"

Doctor Abbas ya kara shiru, na wasu seconds yana jin dama hannun agogo ya dawo baya da tabbas bazai bari Munaya ta rasa budurcin ta ba.

"Fitar Munaya daga asibitin da mintuna talatin kanwar ta ta rasu bakin ta na kiran sunan yayar ta Munaya, hakika a ranar na ji mutuwar yarinyar duk da ban san su ba, amma nayi matukar tausaya musu, after some hours like two Munaya ta dawo asibitin da leda mai dauke da kudaden nan kimanin miliyan uku da dubu dari tara, i was so shock ta Ina ta samu kudi cikin ƙalilan din lokaci haka? Amma ban tambaye ta ba, duk da tarin damuwa dake kwance a fuskar ta amma kanwar ta ce first on her mind, tace min likita ɗan Allah ka tashi ka yiwa Amnah aikin ta warke, ga kudin nan, jikina yayi sanyi sosai na shiga tunanin ta yanda zai sanar mata, daya baya sanar mata cewa kanwar ta ta rasu, fadin tashin hankali da damuwar data shiga bata lokaci, domin a lokacin data yi tozali da gawar Amnah din suma tayi, hakika ranar har kwalla na zubar saboda tsananin tausayin Munaya, saboda tayi kankanta sosai da fuskantar kalubalen rayuwa iri wanna, a takaice bayan an binne yarinyar, da kwana biyu, na je mata ta'aziyya, na ga ta fara fita a hayyacin ta, na mata nasiha kan ta kwantar da hankalin ta, sai da zan tafi nace mata ga kudin ki nan, kasancewar i office dina ta barshi ranar rasuwa, hawaye ya zubo Mata ta karɓe ledar mai dauke da tambarin wannan Company din, wanda shi ya taimaka zuwa wajen nan, har ta juya zata tafi nace Munaya a ina kika samu kudade masu yawa irin wanna, her answer melt my heart, tace i sold My virginity doctor, na siyar da budurcina domin samawa Amnah lafiya, alhalin na manta cewa babu wanda ya Isa ya bawa wani Lafiya ko kara masa tsawon rai face Allah daya hallaci wanna bawan, a ranar na kasa bacci domin ban taba jin mutum dake shan gwagwarmayar rayuwa haka kamar ta ba, na ji haushin ta data amince ta bayar da budurcin ta, sai daga baya na mata uzuri, domin akwai karancin shekaru a tare da ita, bayan kwana biyu nace gidan su na sanar mata cewa ya kamata ta fada min ina ne address din inda Maleek din yake, na ga ta shiga sabon tashin hankali tana kuka tace ita bata son haduwa da Maleek har abada bata son ganin sa, ta tsani Maleek ta cigaba da cewa ranar da abin nan ya faru wajen Shakur ta taho da niyyar ta roke shi ana cirewa cikin albashin ta, sai dai bata samu Shakur din ba, Wanda from all indication na tabbatar kai ne, Maleek ta samu yace mata yana da kudade masu yawa ga su nan ta dauka amma ita ma sai ta bashi jikin ta in return, tace ta roke shi ya yi hakuri ya dinga cirewa a kudin aikin ta ita bata taɓa yin komai ba, bata san komai ba, yace karya take babu Mace virgin a yanzu" idanun doctor Abbas ya kada, ya kalli Maleek yace "i hope yanzu ka tantance cewa ba duka aka taru aka zama ɗaya ba, duk lalacewar Duniya ba'a rasa na gari ɓalle ita ƙaramar yarinya" ya karasa maganar yana jefan Maleek da harara wanda ke tsaye kekam har yanzu cikin yanayi mai wuyar fassaruwa...

"Tun daga wanna lokacin na yi alkawarin kula da Munaya, musamman dana ji labarin ta rasa iyayen ta duka, gashi su ba yan kasar nan bane ya Chadi ne, har raina ina jin ta kamar kanwata ta jini, na kuma yi alkawarin shigar Mata kan abinda danuwan ka ya mata, sai dai duk lokacin dana mata maganar Maleek din kan ta bani address din sai ta fara kuka, akwai lokacin dana je wajen ta ta shiga amai, na Kaita asibiti Mafi kusa domin na ga ta galabaita aka tabbatar min da cewa tana dauke da ciki ga hawan jini, abin ya daga min hankali sosai Domin karamar yarinyar da ciki ga kuma hawan jini, lokacin data san tana dauke da ciki hankalin ta yayi matukar tashi tace dan Allah na taimaka na zubar mata dashi, Ni kaina nayi takaicin samun cikin nan na ta, sai dai zubar da shi din wani karin zunubi ne domin kashe rai ne, na fahimtar da ita cewa kar ta zubar da cikin domin Allah zai yi fushi da ita, lokacin zuwa lokaci ina so ta sanar dani address din Maleek din, amma taki, abinda bata gane ba Ni kaina bana son ta da Maleek din, amma ina so ya sani cewa akwai cikin sa tare da Munaya ina yin haka ne saboda darajar babyn da bai san komai ba, amma ban samu hadin kai ta faɗa min ba, ganin kuma duk lokacin dana fadi sunan Maleek din hankalin ta na tashi ya saka na bar yi mata maganar, amma a raina ina neman mafita. dazu bayan naje duba wani mutum wanda nine family doctor din su danger ta tsayar dani a tsallaken nan, a nan naga sunan company *A.A Dawood MOTORS* sai na shiga tunanin ina na san wanna sunan, and then I remember cewa cikin ledar da Munaya ta kawo kudin asibitin Amnah na gani, jikina ya bani cewa nan ne wajen, hakan yasa na juyo, da haka na gano nan wajen, saboda haka Maleek wait for it, ni zan samawa Munaya Justice, i don't care da tarin dukiyar ka Allah yana tare da mai gaskiya, domin idan Munaya yarinya ce bata da wayo kai fa? meyasa zaka yaudare ta da kudi ka keta mata haddi, idan bazaka iya taimakawa mata fisabilillahi ba meyasa baka bar ta ta tafi ba, You could have allow her go, Amma saboda son zuciya ka garara yin Hakan, saboda takamar ka kudi? Toh ka saurari tsammaci daga kotu ".... doctor Abbas ya karasa maganar da mikewa domin tafiya, Shakur yayi saurin goge kwallan tausayin Munaya domin Baya son a gani, Sai dai fuskar sa ta nuna yayi kuka domin ja da dan kumburi da suka yi, ganin da gaske doctor zai bar office din yayi saurin rike hannun sa yace.





_wandan da suka yi payment duk ina sane da ku, nayi saving number's din ku, zan kuma yi adding din ku a grp da xaran na gama free pages in Sha Allah._
_Sannan Promo da nayi ya kare, kudin littafin ya dawo dari biyar din sa, duk wanda ya kara turo 300 TOH ya sani cewa kuɗin shan lemo ya bani a kyauta😂🙌👏_


MunayaMaleek is 500 via 3200689860 Haruna Rukayya first bank, shaidar biya ta 07082281566
Thanks for your support, Allah ya ƙara muku budi a hanyoyin samun ku🥰



#MunayaMaleek
#Heartouching
#MMSquare
#disflowering
#arrogance
#selfishness
#virginity lost
#painfuldeath
#NoorEemaan
#Paid book


07082281566
[14/12, 12:54 pm] 𝙽𝚘𝚘𝚛𝙸𝚖𝚊𝚗✨: 🍇MunayaMaleek🍓


𝓫𝔂 𝓝𝓸𝓸𝓻𝓔𝓮𝓶𝓪𝓪𝓷📚✍️



Wattpad@NoorEemaan
Arewabooks: nooreemaan




Xvi...
(16)


"Dan Allah ka saurare ni, na san an cuci Munaya, cuta mafi muni, ka fada min inda take, wallahi muna neman ta, tun ranar data dawo da kuɗin nan muke neman ta, but she's no where to be found, karka duba zafin abinda dan'uwana yayi, saboda Allah ka nuna min inda take, na dade ina neman ta domin in bata hakuri, but trust me brother dina baya cikin hankalin sa ya aikata abinda yayi da ita wallahi, You may not believe" doctor abbas ya kara jinjina sauki kai da sanyin hali irin na Shakur, domin sam daukaka ko arzikin su bai rufe masa ido ba , yayinda haushin Maleek ya cika shi, ganin ko kala mai bai ce ba bare bada hakuri, shi da yayi laifi amma ya kasa bada hakuri sai wanda ba ruwan sa ne ya damu, ya lura Shakur na matukar son dan'uwan sa sosai, ba kuma zai yarda cewa Maleek baya hayyacin sa ya keta wa Munaya haddi ba, mahaukaci ne da shi da bai san abinda yake ba ko mene, kawai ya yarda da abinda Hausawa suka ce so so ne amma son kai yafi yawa.

"I don't think zaka samu Ganin ta yanzu, domin bata ma san nazo nan ba, tace bata bukatar ganin dan'uwan ka, ni kaina bana son ciwon ta ya tashi...." Doctor Abbas ya kara maimaitawa domin yana son ran Maleek ya ƙara ɓaci.
Cikin sauri Shakur ya katse shi da cewa "ni zaka kai, nice nake son ganin ta Please"

Numfashi Abbas ya sauke, mutuncin Shakur ya saka yake kasa yi masa musu, ya ce "zaka ganta but not today, lemme have your contact, zan mata bayani first, idan na ga babu tashin hankali sosai a tare da ita zan kira ka muje gidan na su" cikin sauri Shakur ya shiga karanta masa lambar wayar sa, sannan suka yi musabaha, Shakur ya jaddada masa cewa ya kira shi ɗan Allah, kallon daya doctor Abbas ya kara watsawa Maleek mai cike da jin haushi hadi da kishi kana ya fita.

Bayan fitar doctor Abbas Shakur ya kalli Maleek dake tsaye har yanzu fuskar nan tayi ja jijiyoyin kansa sun fito rudu-rudu, kai tsaye mutum bazai iya fassara yanayin na sa, a zahiri Shakur ya fishi shiga damuwa sai dai from the inside, Maleek kadai ya san abinda yake ji, tsabar jarumta ce irin ta sa.

" You kept quiet, You didn't say anything Maleek, meke damun ka ne, ka san irin tawayar da ka yi wa yarinyar nan kuwa,, and yet ka yi shiru baka ce komai ba, duk abubuwan nan sun faru amma ka zabi boye min wasu daga ciki sai yanxu nake ji, na kasa yarda dan'uwana ya aikata wanna munana ayyukan, Maleek what came over you?"


"Is that why kake bashi hakuri? meyasa zaka bashi hakuri, who is he da zai zo ya fadi abinda ya ga dama wa mutane, yaje ya kai maganar duk inda zai kai, i don't bloody care!"

Tsabar haushi Shakur ya dauki ƙwallin serviette dake kan table ya jefi Maleek da shi ya daki kirjin sa, a fusace ya isa gareshi yace "You still have mouth to talk huh? Kana da bakin magana bayan tarin rauni da tawaya da ka yi wa diyar mutane, dan ka ga bata da kowa ko me, toh ka sani in dai maganar nan yaje kotu i will back Munaya, ko kana tunanin dan kana jinina zan goyi bayan karya, no i won't, da kuma dukiyar ka zan diba in bi mata hakkin ta"

Idanun Maleek suka sake kadawa, yace "You know I'm not afraid of anything in this world right, ko ina zaku kai ni ka san bana jin tsoron komai, ba kuma zan fara kan wannan maganar ba"

"Eh na san cewa zuciyar dutse ce dakai baka shakkar komai, amma ka shirya yi wa mummy da Daddy bayani? Ni ne na yarda da cewa baka cikin hayyacin ka kayi wa Munaya haka, kana tunanin kowa zai yarda da hakan? Huh tell me" Shakur ya faɗa kamar zai kai mishi duka.

"Tun ranar farko da yarinyar nan ta shigo rayuwar mu na san ba alkhairi a tare da ita, gashi ta haɗa mu fada, abinda Bama yi, raina ya sosu da har za ka bar ni jininka ka goya wa wata can baya, taya bazan tsani yarinyar nan ba? kamar yadda ta tsane ni, haka nima i hate her, more than she does" yana gama fadin haka ya fice daga office din domin har an fara kiran magrib, basu taba kaiwa wanna lokacin a office ba, Shakur ya ɗan ji ba dad'i, musamman kalaman Maleek din ya ɗan saka jikin sa yin sanyi, shi ma ya san fadi yake kawai, tabbas bazai bari Munaya ta Cutu ba, ba kuma zai bar gefen dan'uwan sa ba, tun yarinta suna tare, ba kuma zasu rabu ba sai mutuwa in sha Allah"
A sanyaye ya fita shima yana fatan Allah ya warware musuz matsalolin su.

Yana zuwa haraban Company'n ya hango Maleek zaune cikin mota ya haɗe girar sama da ta kasa, duk da damuwar da yake ciki ya ɗan ji sanyi a ransa, dama ya san Maleek bazai taba tafiya ya barshi ba, ya shige motar, Maleek ya ja suka fice Nura mai gadi ya musu fatan sauka lafiya amma babu wanda ya kula shi, a yanda yake sharara gudu zai tabbatar maka da cewa ransa ba dad'i, Shakur ya dinga mamakin karfin hali irin na yayan na sa, kai ne da laifi amma kai ne da yin fushi.

*Mummy*

A dame ta dinga kallon agogo ganin shiru basu dawo ba, Domin basu taba dadewa irin haka ba, hankalin ta yayi matukar tashi, domin a wanna karon kam hakurin ta ya kusan karewa saboda yanda ta Kai kololuwa a bukatar Maleek, asirin ta zai iya tonuwa if care is not taken, ta rasa dalilin daya sa bai dawo ba, a yau ta zauna tayi wa kanta wanna tambayar, meyasa sai ranar data shirya cimma burinta a kansa ake yawan samun matsala in one way or the other?
Kasa da awa ɗaya mummy na zaune jugum har makeup din da ta yi domin Maleek ya fara lalacewa saboda gumi, duk ac din dakin amma zafi take ji, tana zaune haƙa taji horn din mota da karfi, bata kawo komai a ranta ba ta saki kayataccen murmushi, yayin da tashin hankali da damuwar data shiga na gushewa a hankali, tana cikin tunanin yadda al'amarin zai kasance tsakanin ta da maleek, har wani lumshe idanun ta take murmushi bai gushe daga fuskar ta ba... Budewar kofar falon data ji ne ya dawo da ita tunanin ta, Maleek ne a gaba, yayinda Shakur ke bayan sa, dukkanin su babu walwala ko digo a fuskar su, fuskar Maleek ma yafi bata tsoro, wani yawu mai kauri ta hadiye, ta dake hadi da mikewa tsaye tana faɗin "welcome home my son's" ta fada da irin sigar da takan musu wasa ko Maleek zai saki ransa domin shine damuwar ta, shi kadai take gani, ta kama hannun Maleek zata zaunar da shi a kujera ya zame hadi hannun sa ya raba ta gefen ta ya nufi hanyar dakin sa cikin sauri tamkar zai tashi sama...

Shakur ne mai karfin halin sakar mata murmushi yace "thanks mummy, ya gida?"

Shima zai bi gefen ta ya wuce ta tare shi da cewa "lafiya meke damun my boy, kunyi fada ne?"
Mummy ta fada not minding halin da shi Shakur yake ciki, wanda shima akwai damuwa mabayyane a fuskar sa...

"Babu komai mummy" shima ya bata amsa da barin gaban ta cikin sauri, domin bai san sauran abinda zai ce mata ba kuma.

Mummy ta koma da baya kwaraf ta zauna kan kujera, ga koshi ga kwanan yunwa, dama ta san Shakur bazai fada mata ba, tun suna ƙanana basu fadin sirrin junan su bare yanzu da hankalin su, tunanin mafita kawai take yanzu, can ta mike zumbur kamar wacce aka mintsila ta nufi hanyar dakin Maleek da abincin data shirya masa, ta san yana jin maganar ta, da wanna damar da zata yi amfani, bugu da kari kuma bazata so tayi asarar wahalar ta da kuɗin ta ba, dole ne yau ta kasance da Maleek, ta kuma kashe ƙishirwar ta, ta san na yau ne da wahala, amma daga baya shi zai dinga neman ta da magiya, ba kuma zata yi masa yanga ba ko ja masa rai wurin bashi kanta ba, saboda tsananin so da kaunar da take masa, har hango hakan take a idanun ta, she can't wait for that day, tayi wani irin juyi tamkar yar budurwa bayan ta ajiye tray din a gaban dakin sa, sannan ta shiga kwankwasa masa kofar a hankali.

*MunayaMaleek is not for free, Its 500 via 3200689860 First bank, shaidar biya ta WhatsApp number na 07082281566, thank you for your patronage, Noor tace madallah da masoyanta na gaske*😘

( na san da yawa kun zata free pages ya kare ne a nan ko? TOH ku duba kasa akwai sauran👇😂❤️)

Sai dai shiru, ganin bashi da alamar buɗe mata yasa ta shiga kiran sunan sa cikin kwantar da murya, yanda babu wanda zai jiyo ta sai shi Maleek ɗin, amma ko motsin sa bata ji ba, duk wata dabara ta gwada, hatta kuka ta saki, domin ta san baya jurar kukan ta, baya kaunar damuwar ta, ta san dole zai zo ya buɗe mata, sai dai bata ci nasara ba, mamaki ya kamata, yaushe Maleek din ta ya fara share damuwar ta? hankalin Mummy ya kara tashi, tana jin cewar bata cikin masu Sa'a a Duniya, hakika bata ci sunan ta ba Sa'adah ba, ta bar kofar dakin sa jiki a sanyaye musamman da ta ji motsin buɗewar Kofar dakin Shakur alamun zai fito, ba kuma ta son ya ga halin da take ciki.


*MALEEK*
A haukace yake hargitsa sumar kansa, gaba-daya ya rasa meke masa dadi har yanzu, shi ba tsoro ba, shi ba farin ciki ba, yanayi ne mai matukar wahala ya riske shi, gaba-daya ji yake Baya son ganin kowa, ya tsani kowa, he just want to be alone without anyone by his side, not even Shakur, shiyasa duk kira da kukan da mummy tayi masa bai bude ba, duk da kukan na ta ya daki kirjin sa, amma baya bukatar kowa a tare da shi, ya mike a zafafe, yana naushin iska, tamkar kuma mai yin fada ya shiga kiciniyar cire rigar sa, yayi saura daga shi sai dogon wando, ya nufi had'add'en babban toilet din sa, ya sakar wa kansa ruwa yayinda dogon wandon ke jikin sa still, hannun sa dafe da bango yana sauke numfashi a jejere tamkar wanda yayi tseren gudu, yayinda ruwan shower din ya cigaba da dukan jikin sa, ko kusa bai ji sanyi a ransa ba, duk da sanyin da Ruwan ke da shi, idanunsa sun yi matukar kadawa, idanunsa kuri a waje ɗaya baya ko kifta su, lallai ba karamin abu bane ke damun zuciyar Maleek din.

*MUNAYA*

Kamar kullum tana zaune tayi zurfi cikin tunanin data saba yi, ta ji sallamar yaro, ko ba a faɗa ba ta san doctor Abbas ne yazo, ta cire tagumin data zabga, ta mike tsaye, ta kalli yanda cikin ta ya fito ta cikin hijabin ɗin ta, ta saka hannu ta cikin hijab din, domin kare cikin, a sanyaye ta taka zuwa waje domin isa wajen shi, ta kuwa tarar da shi tsaye jikin motar sa sanye da kananan kaya da suka yi matukar kar bar sa, ya kura Mata ido cikin tausaya wa, tabbas Munaya bata dauki shawarar da ya bata na cewa ta cire damuwa ba, domin kullum kara ramewa take, halin kuma da ya ganta a ciki ya kara masa kaimi wurin aiwatar da abinda da yake ganin shine zai rage mata damuwa da kadaicin da take ciki.

"Ina wuni" ta ce cikin Siririyar Muryar ta mai cak'ude ta tarin damuwa, hakan ya kara masa tausayin sa, ya yi taku uku zuwa gare ta kana ya ja ya tsaya, ya rungume hannunsa a kirji yace "munayaaaaa! Bakya jin magana ta ko? Don't take life too seriously. You Will never get out of it alive, challenges are what make life interesting, and overcoming them is what makes life meaningful, ki sani cewa Allah didn't promise days with pain, laughter without sorrow, sun without rain. But he did promise strength for the day, comfort for the tears, and light for our way, Dan haka na roke ki, ki bar damuwa, everything is goona be alright ok?"

"Ok" ta amsa tana share siririn hawayen da ya zubo mata.

"Baki ji abinda naci Miki ba kenan, meyasa kike kuka again?"

"Ba...bani nake basu umarnin zubowa ba, su kan zubo ne a duk lokacin da suka ga dama
ya Abbas!" Ta karasa tana fashewa da kukan da take kokarin hadiye wa ta durkusa kasa ta rufe fuskar ta da hijab.

Sosai yanda ta kira shi da ya Abbas ya yi matukar sanyaya masa rai, domin yau yaji ta taɓa kiran sunan sa na ainihi, and that means a lot to him, wani yanayi na musamman yaƙe ji a kanta, ya sauke ajiyar zuciya, ya shiga kwantar mata da hankali har sai da ya tabbatar tayi shiru, sannan yace "mu karasa kan dakalin can mu zauna, akwai magana mai yawa da zamu tattauna karki gaji" ya fadi hakan ne, domin yasan ko yace ta shiga motar sa bazata shiga ba, bugu da kari kuma yana lura da Wani kallo da yan unguwar ke bin sa dashi, kallon wanda ya lalata wa Munaya rayuwa, hakan kuma bai dame shi ba, tunda Allah ya ga niyyar sa, ba musu Munaya ta yi gaba, ta zauna, shima ya zauna, Tsawon dakika biyar kana ya numfasa yace
"I meet Maleek and Shakur yau a ma'aikatar sa ta siyar da motoci" ya fada da zuba mata idanun sa domin ganin reactions din ta.
A zabure ta dago kanta, ta zuba wa doctor Abbas idanun ta, hawayen data samu ya fara kafewa ya sake tara ruwa cikin kwarmin idanun ta, a rayuwa bata son jin wani abu ɗaya danganci Maleek, domin babu abinda hakan ke kara haifar mata face karin damuwa, cikin rawar Murya take son fadin wani abu doctor Abbas ya dakatar da ita, cikin tattausa murya yace "Munaya i understand, Amma yanda kike so bazai yiwu ba, dole ya san da cikin nan, because he's responsible, in gaya miki wani abu? Ina jin nafi ki tsanar wata halaka ta shiga tsakanin ku, because i hate him, duk abinda kike ga ina yi, ina wa babyn dake kwance a mahaifar ki gata ne, dole ya tashi ko ta tashi ta san uban ta, zaki so ya amsa sunan Bara Uba a duniya, for how long Zaki cigaba da yin shiru, gwara ya Sani tun yanxu, domin a gaba bai zama lallai ya amince ba, kina tunanin idan abinda kika haifa ya girma ba zai nemi Sanin waye baban sa ba? Komin dare gaskiya zata bayyana, Domin jini ba wasa ba, blood is thicker than water Munaya, zan iya kula da ke da babyn nan, har ya girma ya zata nine mahaifin sa, amma hakan ba mafita bace, ba mu yi wa babyn adalci ba, saboda innocent soul ne bai san komai ba,so meyasa zaki yi punishing din babyn da laifin baban sa? Kuskure da zunubi an riga an tafka ta, sai neman tafiyar Allah, saboda haka ki bani hadin kai domin yin abinda ya kamata, kin sani na dauke ki tamkar yar kanwata, bazan taba cutar dake ba kin ji?" Cikin gamsuwa ta jinjina masa kai, kima da darajar sa na sake samun mazugunni a zuciyar ta.

Ganin ta ɗan nutsu ya sa ka ya bata labarin yanda ta kaya tsakanin sa da su Shakur, bata yi mamakin halin ko in Kula da Maleek din ya nuna ba, she's knows zai iya yin fin haka, ta kuma ji dadin yanda Shakur ya nuna damuwarsa ga halin da take ciki, ta sauke numfashi daidai sanda taji doctor Abbas ƴace "that

1 Comments On MUNAYA MALEEK
avatar
nusaibabello

12 months ago

Reply

Dghhjhujvghkjvg

Please Login or Register in order to submit comment