Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

party'n cikin tsari da burgewa, bayan Dalibai sun gama gabatar da cultural dance na kabilu daban-daban, sannan aka fara kiran daliban da suka fi k'ok'ari ana basu gift cikin karramawa, class by class, har aka zo kan yan class din su Maleek.
Maleek dake zaune cikin dalibai a tsabtatacciyar Uniform din sa, ya riga ya sa a ransa cewa shine zai zo na ɗaya, sabanin haka sai ya ji wani suna, bai fidda rai ba yana jiran a kira shi a matsayin *second postion* still wani aka kira, suka kalli juna shi da Shakur, kiran sunan wata yarinya da aka yi a matsayin ta uku ya katse musu kallon da suke wa juna, nan kallo ya dawo kan Maleek musamman dalibai da malaman da suka san kokarin sa, suna tunanin what happened this time around? Amma class teacher din su ta san za a yi haka shiyasa Bata yi mamaki ba, Maleek yayi kasa da kansa, ya ji hawaye ya cika idanun sa, saboda hango wasu dalibai da suke nuna shi suna dariya, dama akwai masu jin haushin kokarin sa, ya saka hannu ya goge hawayen, jijiyoyin kansa suka fito radau suka kwanta a gefen kansa, alamun ransa a bace yake, bai kuma fahimtar komai ba har aka tashi taron, Sa'adah da itama ranta ba dad'i, domin ita ce duk shekara take amsar wa Maleek gift cikin alfahari, a yau ma ta riga ta san cewa zai ci, shiyasa ta dau wanka cikin rantsatsan lace, ta shirya ta zo, saboda a san uwar su Maleek bata wasa bace, amma sai taji sabanin abinda ta saka rai, domin yanda ake yabo da koda Maleek a duk lokacin da za a bashi gift ba karamin fasa mata kai yake ba, wani zubin ma idan ta kawo su makaranta haka malamai zasu ke yabon sa a wajen ta.
Jiki a sanyaye ta karaso wajen motar da driver ya kawo ta yana jira,
Su Shakur kuma suka tafi classes din su domin karbo report book din su.


Tana nan tsaye tana jira, class teacher din su Maleek ta zo tace "Good day ma, kamar yadda kika sani sunana miss blessing, class teacher din su Maleek, a gaskiya ban ji dadin yanda performance din ABDUL-MALEEK DAWOOD BULAMA ya yi kasa ba, nayi kokarin jin ko akwai wata damuwa ko wani abu da yake hana shi karatu amma yace min ba komai, shiyasa nace bari na Miki magana tunda ku iyayen sa ne, zai iya sanar da ku wani abu dake damunsa ko ke hana shi karatu"

Sa'adah tayi saurin cewa "TOH shikenan Nagode Anty, zamu tuntube shi, in Sha Allah za a samu improvment next term, thank you"
Da haka suka yi sallama, ko kadan son zuciyar ta bai sa tayi la'akarin cewa abinda take masa da maganin da take dirka masa bane ya janyo wanna sauyin daya wajen Maleek, har yake kokarin affecting brain din sa.

Tana nan tsaye, ta hango su sun taho hannun su rike dana juna, yanda Shakur ke magana da Maleek zai sa mutum ya gane cewa rarrashin dan'uwan sa yake, bayan sun karaso wajen ta , duk suka mika mata result din, ta bude ta ga Shakur ya zo na uku, amma ba overall ba, Maleek ta bakwai, lallai dole Maleek ya damu, ko ta biyu baya zuwa, domin karfafa masa guiwa tace " my boy ka yi kokari kaji, worry not, everything will be fine ok?"

Ya girgiza kai yace " I'm sorry mum, ban yi kokari ba, nima ban san abinda yake damuna ba"

Tausayin sa ta ji sosai, amma ta kasa yin la'akarin cewa ita ce sanadin matsalar sa.


Ta kamo shi jikinta, ta rungume shi tace "it's ok, daina kuka, mu je gida, komai zai yi daidai"

Ta saka yaran a gidan baya, itama ta hau, driver ya ja suka tafi.


****

Bayan sun dawo gida, Shakur yace "mum Dan Allah karki gayawa Daddy Maleek bai yi kokari ba, zai yi fushi" ya fada shima kamar zai yi kuka

Sa'adah tayi Murmushi, ta riga ta san kaunar da take tsakanin su, kai kace uwa daya ce ta haife su, kuma ko Shakur bai fada ba, me ya kai ta fadawa Alhaji ta shiga uku, domin sai ya bi diddigi ya gano meye damuwar Maleek din, ta san halin sa, when it comes to maganar yaran sa, baya wasa da ita.

Ta shafa kansa tace " bazan gaya masa ba Shakur, i promise."


**Before i proceed i will like to thank my fans, Ina godiya da yanda kuke karban duk wani Novel dana kawo muku, jazakallahu Khair*. Ana cewa wannan karon da salon da kika zo kenan Noor?😹 oh yes!... Afuwan Ina bayyana wasu abubuwan ne musamman abinda Sa'adah ke yi wa Maleek, ina hakan ne domin ma'anar labarin ya fito, amma ina dai kokarin Sakaya kalaman....*
*Sannan ina rokon Allah ya bawa iyaye ikon tarbiyyar ta da yaransu bisa tafarkin addinin Muslunci, ya kuma tsare ya'yan su da mutane irin Sa'adah*.


Bayan kwana biyu da faruwar al'amarin Maleek ya ware ya cigaba da harkokinsa, ya kuma dage da karatu, sai dai da yayi kadan zai gaji, kasancewar Sa'adah Bata daina bashi maganin baccin ba, sannan duk sanda tayi romancing din shi, washegari kuma sai ciwon mara, Sa'adah kuma ta dura masa pain reliever, sai ya ji sauki, daya fara ciwo kuma sai ta kara bashi, a haka rayuwar ta cigaba da tafiyar musu, ta bangaren Sa'adah kuma za a ce rayuwar na tafiyar mata yanda take so, musamman da Alhaji Dawood ya jima wanna karon bai dawo ba, domin the last time daya zo bai mata dadi ba, domin daya nemi karban hakkin sa, ki tayi, shi kuwa ya gwada mata karfin ba daya bane, domin ya kai gajin da hakurin sa ya kare, sai dai shi yayi rawansa, yayi kidan sa, sam ta ki bashi hadin kai, haka duk suka kwana rai ba dad'i, musamman ita Sa'adah, ranta sai suya yake, shi bai san cewa Maleek take tanadawa jikin ta ba, ita bata san yanda abubuwan zasu faru ba, and she didn't bloody care, Abu daya ta sani, take kuma muradi sai Maleek ya zama mallakin ta, sai ta ɗanɗana shi...


********

*BAYAN SHEKARU GOMA SHA TARA*

A cikin wadannan shekarun abubuwa da dama sun faru, wani mai daɗi wani akasin hakan, dangi wasu sun tafi gidan su na gaskiya, yayinda wasu ke kara hayayyafa.
Still a cikin shekarun nan Maleek ya gama karatun sa a kasar Spain, inda da kyar Sa'adah ta bari ya tafi, a cewar ta yayi kankanta da zuwa wata kasar karatu kar tarbiyyar sa ta lalace, amma a zahirin gaskiya ba haka bane a ranta, bata son ya yi nesa da ita saboda jin dadin kan ta, inda da kyar Alhaji Dawood ya lallaba ta, sai ta fara kuka wai yana nuna mata ba ita ce mahaifiyar Maleek ba, ya kan ji ba dadi idan ta fadi haka, domin wani zubin yana manta cewa ba Sa'adah bace mahaifiyar Maleek, saboda tsananin kulawa da son da take masa. Ya riko hannun ta yace "Sa'adah ban yi tunanin jin haka daga gareki ba, kin sani cewa ban taba nuna wa Maleek cewa ba kece mahaifiyar sa ba, ban ma taɓa bashi labarin uwar sa ba, banda yan'uwana da suka fada masa, da Maleek bazai san ba ke bace mahaifiyar sa ba, yaron nan yace a kasar waje yake son karatun sa, shi kuma dan'uwan sa Shakur yace a nan yake son, duk da Maleek ya girme shi da aji biyu, amma nayi masa tsallake saboda yace yana son suna tafiya tare da maleek din, sannan karki manta alkawari na musu cewa matukar suka ci SSCE exams din su kowa zai zabi makarantar da yake so yayi karatu. Kuma maganar tarbiyya da kika cewa, ba inda tarbiyya bata lalacewa, ko da a gida ne, dan Allah addu'a kaɗai zaki musu, wai ma tsaya sai maganar Maleek kadai kike, shi Shakur fa, just pray for them, addu'ar ki karbabbiya ce a gare su" maganar da yayi akan Shakur sai taji kamar magana ya gaya mata a fakaice, ta dan ji shakku a ranta, sai kuma ta yi shiru, duk da ba haka ta so ba, amma kar ta je ta matsa masa, shirin ta ya lalace, ita fa tsoron ta kar Maleek ya kyalla ido a kan wata baturiya yace yana so, tayi saurin kawar da tunanin a ranta, saboda bata fatan hakan ya kasance, not even in her dream.


*******

Bayan sun tafi hankalin ta ya gagara kwanciya, kullum cikin bin kwakwafin halin da yake ciki take, ko maganar mace ta ji a kusa dashi ta kan ce "wacece Maleek, ba dai ka fara kula yanmmata ba, TOH kar ma ka soma, karatu muka tura ka" azahiri zaka dauka cewa fada da uwa ta gari kan yi wa dan ta take, amma sam ba haka bane, kishin sa take sosai, shi ma yakan yi mata murmushi yace " mum trust me, kin San babu mace a gaba na, i promise har na dawo bazan yi budurwa ba, i will focus on my study's, Zaku yi alfahari da mu" a duk lokacin daya gaya mata haka ta kan ji sanyi a ranta, she trust Maleek, baya shiga harkan mata, domin akwai wasu yanmmata ya'yan makotan su da suke yawan zuwa kan Maleek ya musu lesson, sai ya shige dakin sa, ya ce ace baya nan, sai Shakur ya musu, yanmmatan tun basu gane ba, har suka gane Maleek baya son koya musu ne, Shakur kuwa ya dinga tsokanar sa da cewa mai tsoron mata, hakan kuma ba karamin dadi yake wa Sa'adah ba, gani take rainon data masa ne ya sanya baya kula mata.



Kullum sai ta kira Maleek, amma banda Shakur, shi ne mai kokarin kiran ta, wani zubin sai ya kira take tuna cewa tana da ƊA data haifa a cikin ta yana karatu a kasar saudiya, ba dan komai ba, sai dan zuciyar ta duka na ga Maleek ne, tayi matukar kwallafa rai a kan yaron.


Shima Shakur bai wani damu da rashin kiran na ta ba, tunda bata bari sun shaku ba, babu wannan shakuwa ta *UWA DA ƊA* a tsakanin su, tun yarinta ya fahimci tafi son Maleek bai damu ba, domin shi mutum ne da bai barin damuwa a ransa, he's always smiling, besides yana tare da soyayyar mahaifin sa, haka zalika brother dinsa na matukar kaunar sa, so he's okay with that.


******

Shakur ya riga Maleek gamawa da shekara daya, kasancewar courses da suka karanta daban-daban ne, then the following year shima Maleek ya dawo da sakamako mai kyau, kasancewar bai taba zuwa gida hụtu ba, hakan yasa kowa ke dokin dawowarsa, ciki har da Alhaji Dawood daya dawo takanas domin ganin Maleek din, Hajiya Sa'adah farin ciki kamar ta zuba ruwa a kasa ta sha, domin ta sha gaya masa zata zo ta gan shi a kasar Spain din ya kan ce mata "a'a mom, bana son ki zo ki wahala, banda isasshen lokaci kullum ina school, ki kwantar da hankalin ki, your son is fine" bai san a matse take da yin tozali da dashi musamman da take ganin hoton sa da yake sawa a dp da story din sa, fiye da yanda take hasashen Maleek zai dawo cikakken namiji ta ga ya dawo, kafadar sa ta bude sosai, ga muscles all over his body, idan ta kebe tana kallon hoton har wani zooming take tana kallon ko wani sashe na jikin sa, yanayin da take shiga a kallon iya hoton sa bazai fasaltu ba, ina ga ya cika mata burin ta data dauki shekaru masu yawa tana kwadayin hafkuwar sa?.

Sosai ake Shirye-shiryen dawowarsa, abinci different varieties aka shirya masa, har da ƙaramin cake ta haɗa masa, wanda ta rubuta *welcome back Home my boy* Hajiya Sa'adah tafi kowa rawar jiki, duk wani abu data san yana so sai data tanadar masa, Alhaji Dawood sai tsokanar ta yake da cewa "lallai Sa'adah dole mu dinga kama kafa da Maleek idan muna son abu Ni da Shakur, wanna lifayar da kike shirya wa Maleek ko ni idan zan dawo Nigeria baki taba min ba" ya fada a wasance, duk da gaskiya ce, dariya kawai tayi, bata ce komai ba.

*******

Bayan ya sauka a airport Alhaji Dawood da Shakur ne suka je taryar sa, duk da Hajiya Sa'adah ta so zuwa amma bata kamalla shirya wa ba, Alhaji Dawood kuma yace ta jira kawai su je su kawo shi, bata so ba, amma haka ta hakura.


***
Babu jimawa suka dawo gidan, Hajiya Sa'adah data kasa zama waje daya saboda doki, tayi saurin gyara zaman rigar ta da kyau sakamakon horn din data ji, babu jimawa suka shigo falon, Alhaji Dawood ne a gaba, yana kaucewa sai ta ga Maleek da Shakur tsaye suna kallon ta fuskar su dauke da murmushi.
Waro idanun ta waje tayi, Domin gani tayi hoto ya rage masa kyawun fuska dana jiki, a yanzu ne take ganin zallan kyau da cikar halitta a gaban ta, lallai sai yanzu ta kara tabbatar da cewa wahalar data sha na jiran sa ba a banza bane, he really worth it..."i miss You Mum" had'add'en Muryar sa da ta kara mata kaimi wurin ganin lallai ba abinda zai hanata mallakar sa ya daki dodon kunnen ta, amma bata ji dadin MUM daya kira ta da shi ba, dama "Anty ko sa'adah i miss You yace", saboda sai ta ga kamar ya mai da ta tsohuwa, ita gani take daidai take dashi, ai ba wasu shekaru ta bashi mai yawa ba, budurwar zuciyar ta ta raya mata hakan, amma ba komai, nan bada jimawa ba zai fahimce ta.


"Ashe kewar bata gaske bace tunda har kin tsaya kallon sa" Muryar Alhaji Dawood mai dauke da amon sautin dariya ya kaste mata tunanin ta. Ai kuwa ta kwasa a guje kamar yar yarinya ta je ta rungume shi, runguma bana wasa ba, har sai da Maleek ya dafa bango, ita kuwa wani duniya daban take jin ta a ciki, musamman kwanciya data yi a lafiyayyen kirjin sa da daddaden kamshin sa, su Shakur na mata dariya sun dauka duk rungumar ta kewa ce, amma ga Sa'adah ba haka bane, ita kadai ta san abinda take ji a jikin ta...

Alhaji Dawood yace "to ya isa haƙa, mu karasa mu zauna ko" sai a lokacin ta sake shi, ta kamo fuskar sa tace "my boy, Kai ne ka dawo haka? i really miss you"
Sai da Shakur ya ji wani abu ya taba zuciyar sa, ba wai kishi ba, amma yayi saurin kawar wa, da a ce bai sani ba, ko wanda bai sani ba, za a dauka cewa shine uwar sa ta mutu, Maleek kuma Sa'adah ce ta haife shi.

******

Bayan sun gama murnar dawowarsa, aka ci abinciccikan, sannan ya samu ya tafi dakin sa wanka, bayan ya fito, yana cikin shirya wa, shakur ya shigo yace "Bro shirya mu tafi masallaci an kusa shiga sallar la'asar"
"ok bro" ya amsawa Shakur. Shi yama manta bai yi azahar ba, komawa yayi toilet yayi alwala, kana ya fito ya yi azahar din cikin yan kananan surorin daya iya, sannan ya fito suka wuce masallacin dake bayan layin su har Alhaji Dawood.

****

Bayan an sallame sallah, bai jira an shafa addu'a da shi ba, ya fito wajen masallacin, ya samu kofar wani dakali dake kallon masallacin ya zauna yana jiran fitowar su Shakur.



_in sha Allah a next page nake son mu Karkare tuna bayan MunayaMaleek, mu koma cigaban labari, na san kun koso ko_?🙂



Mun kusan kammala free pages, ga wadanda suka shirya payment zasu biya ta
3200689860 Haruna Rukayya first bank, shaidar biya ta 07082281566.


Share please❤️


#MunayaMaleek
#Nooreemaan

07082281566
[14/12, 12:54 pm] 𝙽𝚘𝚘𝚛𝙸𝚖𝚊𝚗✨: 🍇 MunayaMaleek🍓



https://whatsapp.com/channel/0029Va5o0Gc4o7qU8MCJuN32



https://www.facebook.com/groups/1346404966270527/?ref=share_group_link



Xiv.....
(14)



Jingine take jikin bango, yayin da idanun ta ke kallon sama, tsayuwar Mota taji a kofar gida, da ba dan doctor Abbas bai jima da tafiya ba, da ta ce shine ya zo, waka ta ji yana tashi sosai, wanda take kyautata zaton Wanda ke motar ne ya sanya, Wani Irin emptiness da kewa ke kara shigar ta sakamakon wakar dake fita slowly, tausayin kanta ya ƙara kamata, a hankali bakin ta ya fara motsawa cikin bin wakar, hawaye na sintiri a fuskar ta, kwarai wakar ya ƙara fama mata ciwon da bata san Ranar warkewar sa ba.

_im so lonely broken an angel_🥺💔

_im so lonely listening to my heart_💜❤️💚


_One and only broken an Angel_💔

_Come and save me before i fall apart_ 😔🥹

_im so lonely broken an angel, I'm so lonely listening to my heart_💙💔🧏‍♀️

Haka ta cigaba ta rera wakar, daga baya karfin sauti na wakar na ƙara raguwa har ta daina ji da alama mai motar ya tafi ne, hawayen bai bar zuba ba, Kyakkyawar fuskar ta ya kara ramewa sakamakon damuwar da take ciki, duk wanda ya ganta cikin wanna halin dole ya tausaya Mata domin maraicin ta ya fito muraran a tare da ita, haka zalika rayuwa ita kadai a cikin gidan ke kara sanya mata damuwa, domin in dai ba doctor Abbas bane yazo, takanyi kwanaki ba tare da ta furta ko da "a" ba, a yau ta tashi da matukar kewar Amnah da Umma, bayan sallar asuba tayi kuka mai tarin yawa kana ta roki Allah ya yafe mata zunubin da ta aikata, tun asuba har kowa yanzu bata dawo daidai ba, Dama rabon ta da walwala tun ranar data rasa abubuwa biyu masu matukar muhimmanci a tare da ita, dan zabura tayi a lokacin data ji tamkar abu ya karci fatar marar ta daga ta ciki, ta mike tana kallon cikin ta a tsorace, domin tunda ta san ta samu ciki bai taba motsi ba sai yau dinan, can taji motsin ya karu tamkar kifi na wasa cikin ruwa ko tace kadangare, tsoron ta ya karu, har tasa hannu ta daki gefen cikin, abin mamaki kuma sai ya daina motsin, hannun ta dafe da cikin still taji inda ta dafe din yayi tauri, taji cikin na bada wani irin abu tamkar ana kyankyasan abu, ta kuma ji kamar ana hurawa, ta rasa yanda zata fasalta wanna abin da take ji, rikicewar data yi ba a maganar sa, ta sulale kasa cikin rashin sanin abin yi.

***


*Doctor Abbas*

Tsaye yake a bedroom din dakin sa, yana gyara kwalar long sleeve shirt din daya sanya, bayan ya gyara ya taje sumar sa da bai fiye yawa ba, ya kai hannu ya dauki turaren sa, har zai fesa wata murya daga can kasan zuciyar yace "Munaya bata so, remember?" and he dropped the perfume, ya saki wani irin murmushi da shi kadai ya san ma'anar sa, yana tuna yanda munaya ke kwarara amai a ranar nan, and that hurt's him so much ganin karamar yarinya na shan wuyar rayuwa haka, sai daya tabbatar baya kamshin komai, domin a matsayin sa na likita ya san ba kowace Mace mai ciki ke kaunar jin kamshin turare ba, and Munaya is one of them, car key ya dauka kana ya bar gidan.

Mintuna ashirin kacal ya kawo shi kofar gidan su Munaya, ya yi tsayen mintuna biyar kana wani yaro yazo gifta shi, cikin sauri yace "Ammmm abokina ji mana" Yaron ya dawo da baya yana kallon shi
"Dan Allah shiga gidan nan kace Munaya tazo"

"Toh" yaron yace ya nufi cikin gidan da gudu, sai dai a soro ya tsaya sakamakon duhun daya gani, ya daga murya sosai yace "an ce Munaya tazo inji wani mai mota a waje" daga haka yaron ya fito not minding an ji ko ba a ji ba, shi kam bazai iya shiga cikin duhun da ko tafin hannun sa baya iya gani ba.
Doctor Abbas ya zaro dubu ɗaya sabo fil daga aljihun sa ya bawa yaron bayan ya fito.

Munaya dake zaune a tsakar gida cikin duhu ta ji saukar Muryar yaron, ta san ba Kowa bane fa ce doctor, duk uban sauron dake cizon ta ba ta ji saboda nisan data yi cikin tunani, domin yawan motsin da take ji a cikin daga shekaranjiya ya kara daga hankalin ta, a hankali ta mike da hijab din dake jikin ta ta fita, as usually yana tsaye jikin motar sa idanun sa kafe kan bakin kofar gidan.

Tun kafin ta karaso inda yake yake kallon yadda ta ƙara zabgewa, hakan kuma yasa zuciyar sa sosuwa, ya sauke numfashi yana sakar mata murmushi a lokacin data karaso inda yake, sannan yaji sallamar ta cikin dashashiyar Murya wanda da bai saka kunne ba, bai zama Lallai ya ji ta ba, cikin sakin murya ya amsa mata, kana ya shiga tambayar ta ya take, ya kuma jikin ta?

Shar shar hawaye suka dinga rige-rigen sauka a idanun ta, a dame ya kara kusa da ita yana fadin "ya Salam! Munaya meya faru?"

Cikin sanyi murya mai cak'ude da tarin damuwa tace "Ni wani abu ne yake yawa a cikina tun jiya, ni kamar numfashi yake fitar wa, sai kartata yake a ciki, anya ba kadangare bane ya shiga cikina doctor?" Ta faɗa zuciyar ta daya, domin bata san mai juna biyu na jin wandannan alamomin ba.

Da a ce cikin nan na halak ne, daɗin dadawa ace na sa ne, da sai yayi dariya saboda maganar Munaya, amma ya ji dadi at Long last dai ta buɗe baki yau ta masa magana mai tsayi, dama zai dinga samun hakan daga gareta a duk lokacin ɗaya zo da yayi farin ciki, domin hakan ma zai taimaka wurin rage mata damuwa idan tana fito da wasu abubuwan daga zuciyar ta. "Munaya" ya kira sunan ta.

Ta kalle shi ba tare da ta amsa ba.

Ya sake gyara tsayuwar sa, yace "Munaya ba wani abu bane, wanna abin da kike ji sign ne na cewar abinda ke cikin ki yana cikin koshin lafiya, kin fahimta, the baby is so healthy, saboda haka kar ki wani damu "


Munaya taji wani tukikin bakinciki ya tsaya mata a rai, musamman kalmar baby daya ambata, sosai taji ta kara tsanar cikin jikin ta, kamar yadda ta tsani uban, ta saka hannu ta goge hawayen ta, still ya cigaba da zubowa, doctor dake kallon ta yace "Munaya har yanzu kin ki daina saka kanki a damuwa, ki sani cewa if you focus on the hurt, you will continue to suffer. But if you lesson, you will continue to grow, that's life, babu abinda zai Sanja, abinda ya faru ya riga ya faru bazaki iya gogewa ba, so the best thing to do is ki yawaita istigifari, da rokon Allah yafiya kin ji ko?, Sannan ki kwantar da hankalin ki, kina bukatar hakan sosai a wanna matakin"

Ta budi baki sau uku ta ƙasa magana saboda kuka, sai a karon na hudu tace "doc... doctor ban so wanna cikin ba, ban so wata alaƙa musamman irin wanna ya ƙara hada Ni da Maleek, ban so kara hada komai da shi ba, kamar yadda ya tarwatsa rayuwata na so bacewa a tasa rayuwar, doctor Maleek is a monster bashi da Imani bare tausa..."ta kasa karasa maganar saboda kukan daya ci karfin ta, ta saka bayan hannun ta tana goge hawayen.

Ya runtse idanun sa, tausayin ta daya mamaye zuciyar sa ya sa kasa magana, tsawon dakika goma kana yace "Munaya! Ni kai na banaso ko kallo ta kara hadaki da Maleek balle magana ta fatar baki, bai cancanci haka ba, Kula da cikin nan da kuma haifo shi duniya hawai yana nufin saboda Maleek zaki yi ba, domin Allah da kuma shi bawan Allah dake cikin ki da bai da laifin komai, amma kike son hukunta shi da abinda uban sa yayi? Ki saka a ranki cewa kin fi karfin Maleek, ki saka a ranki cewa abinda ya faru ƙaddara ne wanda shi ya haɗa ku, abu na karshe da zan fada miki shine ki rike Allah a ko wani hali shi zai miki maganin komai ba dai mutum, matukar kika rike hakan zaki ga haske da tarin sauyi a rayuwar ki"
jinjina kai Munaya ta shiga yi, tana dan ji nutsuwa na saukar mata, musamman kalaman da doctor yayi amfani da su

1 Comments On MUNAYA MALEEK
avatar
nusaibabello

12 months ago

Reply

Dghhjhujvghkjvg

Please Login or Register in order to submit comment