Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta gwada Maleek dake juya cokali cikin mug mai dauke da coffee tace "my boy meya faru tsakanin ka da dan'uwan ka?"

"Ba komai mum" ya amsa hadi da mike wa shima ya fita.
Mummy tace " i Said it, na san bazai faɗa ba, haka zalika dan'uwan sa" sai ta mike zuwa wajen window ta yaye labulen, daidai lokacin da Maleek ke kokarin bude motar sa, Shakur daya zo ta baya ya ɗan buge shi a baya, Maleek ya juyo, Shakur ya jefa masa hararan wasa, and then Maleek smile widely hadi da rungume dan'uwan sa, domin yasan tunda yayi hakan ya sauko daga fushin da yake dashi.
Shima Shakur ya rungume shi, domin yayi missing din sa kwana biyun nan, duk da ya ji matukar haushin abinda Maleek yayi, amma dan'uwan sa ne , is only brother, kuma hannun ka baya taba rubewa ka yanke ka yar, komai munin halin sa jinin sa ne" ya raba rungumar da cewa "muje ka fara ajiye ni a school sai muyi magana a mota" Shakur ya karasa maganar da zagayawa bangaren mai zaman banza.
Mummy ta koma da baya ta zauna kan kujera, ta na jin ina ma ina ma ta ji abinda suke cewa, ta shiga duniyar tunanin hanyar cimma burin ta.

A nutse yake tuki kan kwalta, Shakur ya kalle shi yace "ka min alkawarin ka daina shan giya"
Maleek ya rage gudun da yake, yace "zan yi kokarin dainawa Shakur, ka san I'm addicted to it, dainawa bazai yiwu a take ba, but zan yi iya kokari na wurin dainawa"
Shakur ya jinjina kai, ya san Maleek baya karya dan a so shi, kuma shi mutum ne irin open minded basa boye abinda ke ransu, duk da ba surutu ne da shi, a lokuta da dama ya kan kuma ce "Bazan taba yin abu domin wani ba"

"Amma kayi kokari saboda lafiyar ka da Allah, kasan haramune ko?" Maleek ya jinjina kai.
Shakur ya kara cewa "Sai alkawari na biyu amma sai Munaya ta dawo aiki zan faɗa maka, ina jin rashin lafiyar kanwar ta ne yasa bata yi resuming ba, amma hopefully zata iya dawowa this week"

Maleek ya dage kafadar sa, daidai lokacin da suka iso *Nile University* inda Shakur ke lecturing, Shakur ya sauka suka yi sallama.

****

A hankali Cikin rashin kuzarin da har yanzu bai dawo mata ba take tafiya, sanye take da dogon hijab dinta onion color, Saboda yanda tunani ya mata yawa ko nisan tafiyar bata gani, kafar ta yayi bututu. BAYAN ta iso Company'n Maleek Nura mai gadi ke tambayar ta ko lafiya kwana biyu bata zuwa, ta ce masa lafiya a takaice, bata ko biyewa surutun sa ba, ta nufi bangaren da office din Maleek yake, a yayin da take taka matatakalar benen komai daya faru a ranar ya shiga dawo mata, ta daure zuciyar ta domin bata son yin kuka, bayan ta isa ga kofar glass ɗin tana jiran kofar ta buɗe a lokacin ta hango Maleek zaune a had'add'en office din sa cikin sigar suit looking so smart and handsome as ever, taji mugun tsanar sa ya kara cika mata zuciya, har take jin tamkar ta rufe shi da duka, daidai lokacin da kofar ta bude kanta, a daidai lokacin ne Maleek ya dago rikitatun idanun sa ya zuba wa Munaya ko motsa su baya yi, fuskar sa dauke da wani yanayi da ba zai fasaltu ba, Munaya ta tako zuwa tsakiyar office din sa, ta fito da hannun ta dake cikin hijab mai dauke da ledar kuɗin nan ta jefa masa har ya daki fuskar sa, raunin ta ya fito fili Sosai, ta fashe da kuka, ta kasa daurewa tace "I hate you with passion! Azzulumi Ga kudin ka nan na dawo maka da shi, Amnah is dead, kanwata ta mutu, meya amfanin kudin ka a gareni, nayi nadamar baka budurcina, Allah ya saka min abinda ka min ban yafe maka ba Maleek!" Ta karasa maganar cikin dacin murya, kana cikin sauri ta juya ta bar office din.

Maleek!
A hankali bacin ran jefa masa kudin data yi a fuska da bakaken maganganun data masa ya rikide izuwa wani yanayi, yanayin da bazai fasaltu ba, saboda kai tsaye mutum baxai iya karantar fuskar sa ba, ya fi maka da wanda maganar Munaya ta tabashi har ya darsa masa wani abu a zuciya, musamman daya ji kalmar mutuwa a ciki, yet fuskar sa a dinke tsaf wanda kai tsaye mutum bazai iya karantar yanayin sa ba... Ya shiga murza hannun sa cikin na juna cikin sauri sauri ya mike zuwa kofa tamkar zai bita, sai kuma ya dawo ya nufi dakin da yake hutawa, inda a nan ne komai ya faru tsakanin sa da Munaya, kai tsaye ya nufi gaban cctv Camera ya zauna, ya yi tariya zuwa ranar daya kusanci Munaya, a yau ya nutsu ya kalli tun daga farko har karshe, idanunsa suka yi matukar kadawa zuwa jajawur tamkar an watsa masa jini cikin su...

_"Dan Allah dan Annabi kayi hakuri, wallahi Amnah kanwata ce bata da Lafiya, yanzu haka tana asibiti unconscious, tana da brain Cancer, likitoci sun ce kudin aikin da za mata 3.9millon, dan Allah dan Annabi ka taimaka min kada na rasa kanwata, wallahi na yarda ko a albashina ne na yarda kana cire har na gama biyan ka kaji?"_

_" i hate you with passion, Azzulumi ga kudin ka nan, Amnah ta mutu, kanwata is dead"_.... Kalaman Munaya ke dawo masa daki-daki, kansa ya ɗauki caji, ya ji zuciyar sa tayi nauyi, ya rasa tunanin daya dace yayi, ya mike zuwa box da yake ajiye kayan mayen sa, har zai bude ya ji Muryar Shakur tamkar yanzu yake gaya masa _"promise me bazaka kara shan giya ba"_ ya ji jikin sa yayi sanyi, ya ajiye box din, lallai neman mafita yake, so yake hankalin sa ya gushe ya manta kalaman Munaya masu matukar daci agareshi, but yana son rage shan giya, saboda yayi wa Shakur alkawari, ko da bazai daina ba, but at least he should try ya rage ko yaya ne" ya saka hannu ya rufe fuskar sa tsawon mintuna goma yana a haka ya ji zugewar kofar glass din sa alamun shigowa, ya kuma san Shakur ne domin babu mai shigo masa kai tsaye ba tare da izinin sa ba...

"Bro!" Shakur ya faɗa bayan ya buɗe Kofar da Maleek din kan huta a ciki, a hankali ya cire hannunsa daga saman fuskar sa Wanda hakan ya bayanna Halin da yake ciki.
"Subhnanallah!" Shakur ya fada yana zama a gefen sa, cikin kulawa yace "what happen Maleek?"

Tsawon mintuna uku kana Maleek ya kalli Shakur straight into his eyes yace "she came"

Cikin rashin fahimta Shakur yace "who came...?" Sai kuma ƙwaƙwalwar sa ta bashi yace "oooh You mean Munaya?" Maleek ya kafe sa da ido ya kasa cewa komai, cikin murna Shakur ya cigaba da dacewa "where is she, ban gan ta ba, ko ka aike ta ne?" Domin yana matukar bukatar ganin ta.

"Ta dawo da kuɗin nan, and she said kanwar tavta ta rasu"


"Innalillahi wa Inna ilahi raju'un!" Shakur ya faɗa yana dukan hannun sa cikin na juna yanda maza ke yi, yana mai jin matsanancin tausayin Munaya, ya mike hadi da kamo hannun Maleek yace "let's go find her bro, ya kamata muyi magana da ita" Maleek ya mike ba musu ya bishi, ko za a titsiyeshi da wuka ba zai iya fadin takamaiman abinda yake ji a zuciyar sa ba, sai dai ya san kalaman Munaya sun dake shi matuka.

A mota suka dinga zaga unguwanni da layuka ko zasu ganta, amma ko mai kama da ita basu gani ba, gashi babu address din ta, domin haushin ta da maleek ke yi bai saka ya bata form na employee bare a samu address din ta a ciki ba, haka suka dawo cikin sakin guiwa, musamman Shakur da shi bai iya boye damuwar sa ba, sosai hankalin sa ya tashi, kasancewar bashi da zurfin ciki.

★★★
Munaya!!!
Bayan barinta office din maleek ta koma gida a kafa kamar yanda ta zo a Kafa, ta yi kuka sosai mara amfani, nadama kuwa ta yi shi babu adadi, ta rungume kayan Amnah da suke yan siraru cikin matukar kewar ta, a karshe ta shiga linke kayan daya bayan ɗaya, bayan ta gama ta zuba su cikin leda har da takalman ta, sai guda ɗaya data bari wanda ta siya mata ranar da ta siyi hijabai, ita kanta bata san dalilin ajiye takalmin ba, ta dai samu kanta da ajiye shi, ta sake fita babban titi, ta samu almajirai mata ta basu kayan sadaka da niyyar Allah ya kai ladan kabarin ta, haka ta juyo hanyar gida cikin sanyin jiki, iska na kada hijab dinta a yayin da take takawa, hakan ya sake bayyana loneliness din ta, domin kallon daya mutum zai mata ya hango damuwa, kadaici, da kewa a tare da ita.

★★★

"Ni na ga jaraba ni maimoona, Sa'adah zaki kashe kanki ne kan wanna yaron, toh wai in tambaye ki dole ni, bazaki iya hakura da shi ba" maimoona kawar mummy ke wanna maganar cikin jin takaicin kawar tata.

Mummy da ta dan yi zuru-zuru ta cire tagumin da ta yi, ta saki murmushin yake wanda yafi kuka ciwo da labb'anta da suka bushe, tace " maimoon ke nan, bazan iya hakura ba, baki san waye Maleek ba, ni na san kalar namijin da nake farauta, toh bari ki ji abinda baki sani ba, wallahi na sha leken sa idan yana wanka bai sani ba, tashin hankalin da nake shiga idan na kalle shi yasa na daina leken sa, idan ana maganar namiji iya namiji ingarma mai kyakkyawar sura toh idan an samu my boy an wuce nan, ke dai bani mafita kawai, domin harkar malaman nan ba son shi nake ba, ke kika kwadaita min, gashi ya ja min matsala har kiwon da nake yi domin kaina kadai wata ce can taci moriyar sa"

Hajiya Maimoona ta ɗan harari mummy, domin haushin yanda ta kwallafa rai akan Maleek take ji, ta gyara zamanta, cikin salon duniyan ci tace "Toh kawai ki fito fili ki fada masa abinda yake ran ki, ayi a wuce nan, a toh shi yaro ne da zai ce bai gane karatun ba, idan ma bai gane ba ganar da shi, ki fito masa da abinda yake ranki, ki kuma kwadaita masa Sa'adah"

"Anya k'awata zan iya? Kina ganin ba za a samu matsala ba, kin san dai yanda suka shaku da Shakur sosai, ga shi da bin diddigi bana son a samu matsala" mummy ta fada.

"Wai ma wannan lusarin mijin naki meye amfanin sa, shine kullum yawon kasuwanci kasashen waje tamkar akan sa aka fara neman arziki" Hajiya Maimoona ta faɗa tana harare harare tamkar daddyn su Maleek ne a gaban ta.
Mummy maimakon ta kare mutuncin mijin ta sai tace "ke rabu dashi, ni mutumin nan haushi yake bani wallahi, gashi wai ya kusan dawowa, Ni Wallahi bana son ya rabe ni, domin baya tsanana min abin arziki, dashi da babu duk daya, ayi mutum bai iya komai ba, ga kudi dai a gida kamar zasu yi magana amma babu gams..." Mummy ta kasa karasa maganar cikin jin takaici har cizon yatsan ta take.
Hajiya Maimoona ta mike tsaye tana rataye tsad'add'iyar jakar ta hadi da sanya glass din ta, kallo ɗaya mutum zai mata ya hango budewar ido a tare da ita, ta kalli mummy tace "Sa'adah kiyi tunani sosai kan maganar nan, ki fito muraran ki nuna masa abinda yake ranki, shine kawai mafitar da nake hanga miki" ta karasa da barin falon mummy cikin takun kasaita irin na gogaggun mata yan duniya...




Wattpad@NoorEemaan
@Arewabooks @nooreemaan
Whatsapp:07082281566




Thank you for reading my story.

07082281566
[14/12, 12:54 pm] 𝙽𝚘𝚘𝚛𝙸𝚖𝚊𝚗✨: 🍇MunayaMaleek 🍓




_by NoorEemaan_📚✍️


https://www.facebook.com/groups/1346404966270527/?ref=share_group_link



V...
(5)



Cikin sauri doctor'n ya bi bayan ta, domin Ya lura tayi matukar fita a hayyacin ta.
*Munaya*
Cikin wani irin zafin nama da bata san tana da shi ba ta bude dakin da aka kwantar da Amnah, sai dai abinda tayi tozali da shi yayi sanadiyyar daskewar ta a bakin kofar, idanunta kuri kan Amnah dake kwance flat rufe da farin yadi irin na asibiti, ji take tamkar bata duniyar, komai ya tsaya mata cak, a hankali ta sulale kasa, hawaye na cigaba da fita a idanun ta, kallon gawar kanwar ta dake lullube a farin zani take, ta rasa wani kalar tunani ya kamata tayi, ji take tamkar ƙwaƙwalwar ta ya daina aiki...

Tana a wanna halin likita ya bude Kofar shi ma ya shigo, damuwa kwance ƙarara a fuskar sa, bai taba damuwa da ko wani mutum daya zo asibitin nan kamar yadda ya damu da su Munaya ba, tayi matukar bashi tausayi sosai, yar yarinya da ita amma tana shan gwagwarmayar rayuwa.

"Munaya!" Ya kira sunan ta cikin Muryar tausayi.

Sunanta da doctor ya kira ya ɗan taimaka wurin dawo da tunanin ta data fara rasawa, ta dago jajayen idanunta ta watsa masa su, tamkar mara hankali haka ta zuba masa manyan idanun ta tsawon mintuna uku, ya kara kiran sunan ta, ta dauke kanta daga kallon sa, ta rarrafa zuwa gadon da Amnah ke kwance, hannun ta na rawa ta shiga yaye farin zanin da aka rufawa Amnah, Kyakkyawar fuskar kanwar ta daya kara matukar haske ta kurawa ido, tana kara ƙaryata managar doctor, tana dan bubbuga fuskar Amnah cikin raunin murya tace "Amnah, bacci kike har yanzu? maza tashi ayi Miki aikin nan ki warke gashin ki ya fito, kin tuna nace zan Miki kitso?" Ta faɗa cikin kuka mai haɗe da Murmushi, ta kara kallon doctor tace "likita ka gani, nace maka bata mutu ba, kalli kalli kaga murmushi fa take min, kuma ka san me, Amnah bata taɓa kyau irin na yau ba, tana raye ku mata aikin nan dan Allah ta huta da ciwon nan" ta karasa maganar da kuka, so take ta bawa kanta hope na cewa Amnah tana raye, duk da ta san bata ko motsi, she's lifeless, babu rai a tare da ita, amma bata son ƙwaƙwalwar ta ya dauka balle har ta yarda da hakan a ranta.

Likita da jikinsa ya gama sanyi ya tako a nutse zuwa gaban gadon, ya ɗan rage tsayin sa yace "Munaya! Kiyi hakuri, Amnah ta rasu, babu abinda take bukata yanzu fiye da a sadata da mahallin cin ta, wanda ya fi son ta fiye da mu, ki sani ko wani rai sai ya dandani zafin mutuwa, and who life is given to, death is a promise, Dan Allah ki dauki hakuri da dangana, i know you are too small to bear this, but you can do it, cos you re very strong, more than you can imagine..."
Ihun da Munaya tayi wanda ya karade har wajen dakin da kuma shirun daya biyo baya shi ya kara dagawa doctor hankali, ya kara matsawa kusa da Munaya, a daidai lokacin nurse ta shigo, ya dago kan Munaya data kife kan gawar Amnah ya ga ta suma, ajiyar zuciya yayi, yayin da lugudan bugun da kirjin sa ke yi ya ragu, ya mayar da rufin Amnah wanda Munaya ta yaye, sannan ya dauki Munaya zuwa wani dakin domin bata taimakon gaggawa, bayan ya fada wa nurse din da a shirya gawar Amnah shi zai yi settling sauran bill's dinsu.

Zaune su mummy suke a Wasu alfarman kujeru dake dakin, sam mutum bazai taba zaton dakin mushiriki bane, yafi kama da normal falo irin na masu rufin asiri, bambancin dai shi wanna dakin akwai abubuwan duba a ciki da sauran kayan aiki da mushrikai kan yi amfani da su.
Cikin karan sauti, takalmin mutumin ke tunkora inda suke zaune kana ya bayyana a falon cikin shigar alfarmar tamkar malami har da dan carbin sa, a zahiri idan mutum ya ganshi zai yi tunanin mutumin kirki ne, sai dai a badini sam ba haka yake ba, son zuciya da son duniya ne fal cikin sa, fuskar sa babu yabo babu fallasa ya zauna a kujerar dake kallon su mummy, mummy cikin rawar jiki da baki tace "Barka da fitowa malam" har da dan rissinawar ta...

"Yawwa sannu ku" ya amsa .

Hajiya maimoon ta zunguri mummy alamun tayi magana, mummy ta sake gyara zaman ta tace "Malam na aiwatar da komai yanda ka umarce ni, sai dai har muka taho nan bai zo gareni ba kamar yadda ka fada...."

"Sa'adah kin yi kuskure!" Ya katse ta cikin Muryar sa mai kaushi.

"Kus.....kuskure kuma malam?" Mummy ta fada cikin damuwa daya bayyana a fuskar ta.


"Eh kwarai kin yi kuskuren barin sa fita, kinyi kuskuren barin wani ya ganki"


"Innalillahi wa Inna ilahi raju'un! Ban bari kowa ya ganni ba wallahi, ban san waya ganni ba, ni daka ce za a dinga k'awata masa sura ta na zata ko a ina ne yake zai dawo gareni malam, shiyasa na bari ya tafi, da yake kaninsa na nan da safe na rasa yanda zan yi kin hana sa fita gudun kada ya zargi wani abun" Mummy ta fada hankali a tashe har hawaye ya cika idanunta.

Mutumin ya sake gyara zaman babbar rigar sa yace "kuma mafi girman kuskuren da sakacin ki ya janyo shine Maleek ya sadu da wata mace, macen ma karamar yarinyar...."

"Na shiga uku" mummy ta katse mutumin hadi da mikewa tsaye ta fashewa da kuka, tamkar zararriya ta tayo kan Mutumin, sai kuma ta durkusa a gaban sa tace "dan Allah dan Annabi malam ka taimaka min, wallahi zuciya ta zata fashe, ina matukar kishin sa" ta karasa cikin dacin murya alamun abinda take faɗa daga can kasan zuciyar ta yake fitowa"

Hajiya maimoon ta mike zuwa inda mummy ke durkushe ta kamo ta cikin rarrashi take fadin "haba Sa'adah ki nutsu mana a samu mafita, ni wanna yaron ko shine autan maza sai haka, gaba-daya kin damu kanki domin shi, bayan akwai maza zarata cikakku bila adadin a duniya"

Mummy kam bata ma jin abinda kawarta ke cewa, sai rusar kuka take tamkar yar yarinya.

Cikin shakiyanci mutumin daya Kira kan sa malam yace "gwara kina faɗa mata gaskiya, ko ni nan zan jiyar da ita fiye da daɗin da take kwadayin samu daga wanna yaron, amma ba lallai, sai ta amince"

Hajiya maimoon ta masa wani kallo hadi da jefa masa hararan wasa wanda hakan ke nuni da cewa ba sanin yau suka yi wa juna.


Mutumin ya saki dariya, kana ya tsuke fuska tamkar ba shi ya gama magana ba.


Malam ya jefa carbin sa kan tiles din dakin, sai bin carbin yake da kallon tamkar mai neman wani abu a jiki, bayan wasu seconds ya dago hadi dacewa "bana iya ganin fuskar yarinyar har yanzu, haske Mai tsanani ya rufe fuskar ta, sai dai karamar yarinya ce sosai, haka zalika zanen ƙaddara su a haɗe take"

Mummy da tun fara maganar Malam tayi dif da kukan, sai dai tashin hankalin ta ya karu, cikin dacin murya tace "malam ina mafita? Maimoon kin yi shiru, ki ce wani abu"


A dame itama Hajiya maimoon tace "malam ko da wata mafita ne da za a taimaka mana da shi, kawata na cikin damuwa"

" Hajiya Maimoona kin fi kowa sanin ka'idar aikina, bana aiki wa mutum sau biyu, sau daya tak nake aiki akan abu daya, sai dai idan tana da wata damuwar zan yaye mata shi, amma kan yaron nan Maleek babu abinda zan iya yi akai kuma, ta riga tayi kuskure a farko"

Ran mummy a jagule ta mike fuuu ta bar dakin zuwa waje, ita gani take kamar malam baya son mata aikin ne, amma yanda maimoon ke bata labarin sa zai iya cika mata burin ta yasa ta amince masa, mota ta bude ta shiga, tana jiran fitowar Hajiyar maimoona su tafi, ta rufe idanun ta, tana watsafa yanda al'amarin ya kasance tsakanin Maleek da kuma yarinyar da malam yace ya kusanta, tsana mai yawa ta ɗora a kan Munaya duk da bata santa ba, ta bude idanun ta da suka yi matukar kadawa saboda kukan data sha tace "babu macen da zan sake kuskuren ta rabe ka, kai nawa ne ni daya, wallahi zan iya komai domin cikar burina a kan ka Maleek, idan nace komai, ina nufin komai"
*MALEEK!*
A hankali ya fara bude idanun sa da suka bata awani uku a rufe dalilin bacci mai nauyin daya dauke shi, tarr ya sauke idanun sa kan had'add'en pop'n saman dakin, ya yunkura zai mike ya kasa sakamakon nauyi da kansa yayi, har Wani ciwo yake ji, ya lumshe idanunsa hadi da komawa ya kwanta yana cije labb'ansa da suka kara yin ja, tsawon mintuna biyar ya ɗan ji dama-dama ya sake bude idanun sa, wannan karon kan farin sofan da yake kwance ya sauke ta, zaro idanun sa waje yayi sakamakon ganin jinin da ya ɗan bata sofan, sai kuma ya ga wani tsohon jan ribbon na gashi a can bakin sofan, ya runtse idanun sa yana kokarin haɗe tunanin sa waje daya, a hankali komai ya shiga dawo masa daki-daki tun shigowar Munaya office din sa da komai ɗaya faru, cikin sauri ya mike ya naushi bango hadi da dafe kansa, ya dawo bakin sofan ya zauna hannun sa dafe da kansa, "damn it!" Ya faɗa can kasan makoshi yana fatan abubuwan da suka faru su zama mafarki, sai kuma ya mike cikin sauri zuwa gaban cctv Cameran dake dakin yana karfafa wa zuciyar sa cewa mafarki ne, domin babu ta yanda idanun sa biyu zai taba kusantar kazamar yarinyar nan, forwarding zuwa baya yayi, ya ga lokacin daya shigo da Munaya rungume a kirjin sa, sannan yaga ya kwanta ya danne ta, saurin kashe cctv Cameran yayi, lallai baya bukatar ƙarin bayani, a gaske abin nan ya faru, gumi ya ji ya wanke masa fuska, ya dawo da baya ya zauna dabas kan sofa'n daidai lokacin da Shakur ya turo kofa ya shigo, sallamar Shakur ya katse a lokacin da idanun sa ya sauka kan jinin dake sofa, cikin tashin hankali ya yo kan Maleek daya ga ya dafe kansa.


Maleek! Are you okay, Jinin meye wanna?" Shakur daya Dafa shi ya tambaya cikin tashin hankali hadi da duba jikin sa domin ya zata ko wani abu ne ya same shi.

Tsawon mintuna uku kana Maleek ya dago jajaye idanun sa da suka yi matukar kadawa ya zuba su cikin na Shakur, kirjin sa har wani harbawa take, bawai na tsoro ba, illa na tsananin tashin hankali, bai iya karya ba, ba kuma zai fara yau saboda Munaya ba, besides Shakur is his only brother da yake shi a duniya, his other half, bai taba boye masa komai ba, cikin murya mai sanyi kamar ba tashi ba yace "i slept with her bro!"

Wani dum Shakur yaji a kunnen sa kana yace "What! Ban gane ba, wacece ka kwanta da ita?" ya karasa fada cikin tashin hankali mara mistaltuwa ya kuma shiga jero addu'o'i a ransa yana fatan ya kasance mafarki dan'uwan na sa yayi.

Shiru Maleek yayi na wasu sakwanin kana yace "yarinyar daka bawa aiki..."

Shakur's heart skip a bit, cikin wani irin zafin nama ya cakumi Maleek yace "kana cikin hankali ka kuwa? Don't tell me Munaya kake nufi? innalillahi wa Inna ilahirin raju'un!"

"Bana cikin hankalina Shakur, i wasn't my self, Ina cikin maye ne, ina cikin hankalina ka san Bazan aikata hakan ba, kai ma ya kamata ka san da hankalina bazan kusanci kazama kuma karamar yarinyar nan ba"

Shakur da tunda Maleek ya fara magana ya zuba masa ido, yana ganin kamar a Sanja masa dan'uwan sa ne yau, Wato duk da abinda ya aikata yana da kwarin guiwar kiran ta kazama, ya hadiyi yawun daya taru a bakin sa, kana cikin raunananiyar murya yace "daman kana shan giya Maleek?" Ya fada yana jijjiga shi sosai, ga bacin rai ƙarara a fuskar sa, domin da ba dan yana controlling kansa ba, zai iya rufe Maleek da duka saboda yanda ransa ya kai kololuwa a ɓaci.

Maleek sai yanzu ya gane subutar da yayi, amma bashi da zabin da ya wuce fadin gaskiya a yau, "Ina sha Shakur, ina sha tun muna kanana, basan ta yaya ba, na dai tsinci kaina cikin shan Kayan maye ne"

1 Comments On MUNAYA MALEEK
avatar
nusaibabello

12 months ago

Reply

Dghhjhujvghkjvg

Please Login or Register in order to submit comment