Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta dinga tafiya har ta iso bakin titi, ta ga babu wasu ababen hawa, kasancewar garin bai ida wayewa ba gashi lokacin sanyi ne, ta tsaya har na mintuna biyar bata samu ba abin hawa ba , sai ta fara tafiya cikin sauri, tana yi tana kallon fuskar Amnah da yayi fayau, idanunta sun shige ciki sosai, ramar ta ya fito muraran, kiris ya rage basu zube a kasa ba, sakamakon kallon da take wa Amnah, ta yi saurin jan tunga ta tsaya, ta cigaba da tafiya tana waigen bayan ta ko zata ga abin hawa, ta ɗan jima tana tafiya sannan ta ji dan sahu na mata horn daga baya tayi saurin juyowa, ta shige dan sahun, cikin rikicewa, fuskar ta a kacame da hawaye tace "muje asibiti ɗan Allah"
mai dan tsahu yace "wani asibiti?" ta kira sunan asibitin da Umma ke kai Amnah ya ja suka tafi, mintuna daya biyu ta kira sunan Amnah, amma shiru ba amsa, Munaya na tsoro, tsoron rasa tilon kanwar ta, bata son rasa Amnah, kaf duniya ita kadai ta rage mata, ita ce sanyin idaniyar ta, Amnah bata ko iya magana, sai numfashin ta dake fita da sauri tamkar zai fasa dan kirjin ta ya fito, sai juyi take a jikin Munaya alamun tana cikin zafin ciwo, wanda hakan ke saka kirjin Munaya lugudan bugu.


"Mun iso asibitin" mai dan sahu ya fada yana waiwayo ta, cikin sauri Munaya ta sauka, ta bashi dubu daya cikin kudin dake hannun ta, ya girgiza kai da cewa "ki barshi, Allah ya bata lafiya" ta kasa ko da magana balle godiya, ta yi cikin asibitin da gudu, mai dan sahu ya girgiza kan sa, tayi matukar bashi tausayi, domin ya hango damuwa mai tarin yawa a tare da ita, a bayyane yace "ko ina iyayenta suka bar karamar yarinya da wanna wahalar, domin ko shakka babu wanna yarinyar bazata iya haifar mara lafiyan ba" ya sake Girgiza kai, yana tada Babur din sa, ya Kuma gode wa Allah daya wadata shi da lafiya, Domin idan kana tunanin kana cikin halin kunci ko kana fuskantar wani kalubalen rayuwa, toh idan ka ga wanda kafi sai kayi godiya ga Allah da yayi maka wanna ni'imar, ba dan kafi wasu ba,sai dai ko wani bawa da tashi kalar ƙaddarar.
Cikin asibitin kuwa a gagauce suka karbi Amnah, aka mata fixing drip, domin babu karfi ko daya a jikin ta, Munaya na gefe tana kuka sosai, bayan likita ya gama duk wani abu daya dace yayi wa Amnah ya juyo ga Munaya yace "ina maman ku?"

"Ta mutuuu" tace cikin kuka.

"Baban ku fa, ko wani daga dangin iyayen ku?"

"Doctor bamu da Kowa, bamu da Kowa sai kan mu"


"Ya Salam!" Likita ya fada cikin rashin sanin abin yi, domin bai san yadda zai mata wanna bayanin ba, gani yake tayi kankanta da yawa, ya kara kallon munaya yace "muje office dina" ya karasa yana barin dakin cikin sauri, Munaya ta kara kallon Amnah dake kwance kamar mara rai, sannan ta bi bayan likitan a sanyaye.


"Zauna" likita ya fada yana nuna wa Munaya kujera.

Kamar mai zama kan wuta haka ta zauna, a tsorace take matuka, likita yayi gyaran murya yace "am...i believe kin San cutar da kanwar ki ke dauke dashi ko?"


Cikin sauri ta daga kai alamun "eh".

"Good! A yanzu dai ta kai stage na karshe wanda take daf da rasa rayuwar ta matukar ba a mata aiki cikin gaggawa ba, domin shi Cancer yana undergrowing kullum ne, because is a disease in which the cells of a tissue undergo, uncontrolled (and often rapid) proliferation, it's Something damaging that spreads throughout something else, So the best shine a mata aikin, sannan sai ta cigaba da shan magunguna, domin shi karin ruwan nan da aka mata babu abinda zai kara mata a fanin cutar, sai dai ya kara mata karfi data rasa sakamakon aman da tayi, amma cutar na cin ta ta ciki, shiyasa dazu nake tambayar ki ko ina dangin ku, saboda kudin aikin ba kananu bane, I know you can't afford it alone, million uku da dubu dari tara ba wasa bane baby girl"


A firgice Munaya tace "do..doct....doctor! million uku da dubu dari bakwai aka ce wa Umma na last time"

Likita yace " gaskiya a da kenan, domin maganar da kike shekara daya data wuce kenan, yanzu kudin ya karu" daga nan bai kara cewa komai ba ya cigaba da aikin sa.


Munaya ta rufe idanun ta da tafukan hannayen ta ta fara rera kuka, ta mike zuwa gaban likitan ta tsugunna tace "dan Allah likita ku taimaka ku mata aikin nan, wallahi Allah zan nemo kudin duk inda yake na biya, Ni dai fatana ta rayu, wallahi zan biya, idan ma baku yarda ba muyi yarjejeniya, ku rike ta a wajen ku har sai na gama biyan ku sai ku bani kanwata, Ni dai ina so ta warke, dan Allah likita ka taimaka, ita kaɗai gareni..." Ta karasa cikin Muryar kuka mai narka zuciya.

Likita ya girgiza kai, yana kara tabbatar da yarintar Munaya, saboda abubuwan data faɗa bazai taba yuwa ba, tsari da dokar asibitin bazai taba yarda da hakan ba.


"Hakan bazai yu ba, ki Sani cewa ko iya kudin gado da karin ruwan nan dana yi wa kanwar ki aka barki dashi bazaki iya biya ba, You re even lucky kin samu ina duty ma da kika zo, da baza su karbe ta ba har sai kin ajiye dubu saba'in, which i know baki da irin wanna kudin, amma na dauki nauyin Hakan tunda baki da su, kuma kanwar ki na Cikin mayuwanci hali, abu daya dai zan iya taimaka muku dashi yanzu, magani za'a siya mata, wanda zai dan taimaka mata kafin a samu kuɗin aikin, but note kada a dauki lokaci Kafin a mata aikin nan, domin komai zai iya faruwa da ita" ya karasa maganar da rubuta mata maganin a farar takarda hadi da cewa "gashi bashi da tsada sosai i think bazai wuce dubu goma sha biyu da dari biyar ba, so ki siyo mata a pharmacy'n cikin asibitin nan a bata, but i repeat, aikin nan shine abinda sister'n ki ke bukata, magani bazai mata abinda ake so ba, so ki sa wanna a ranki"



Jinjina kai Munaya tayi, ta lashi busassun labb'anta kana ta fita daga office din likitan, cikin sauri taje pharmacy din, luckily kamar yadda likita ya fada 12,500 aka siyar mata, ta duba hannun ta ta ga saura 1,500 ta fita wajen asibitin ta ga wani provision store ta siyi yoghhurt mara sanyi sannan ta dawo cikin asibitin, direct dakin da aka kwantar da Amnah ta nufa, ta buɗe Kofar a hankali, idanun ta suka sarke dana Amnah dake kwance, tadan ji sanyi a ranta ta lumshe idanun ta cikin sakin ajiyar zuciya, ta kara buɗe idon, and then she saw Amnah smiling at her, ta karasa wajen gadon da sauri ta dago ta zuwa jikin ta tace "sannu Amnah, ya jikin ki, kin ji sauki ko?" Amnah ta gyada kai, Munaya ta sumbaci goshin ta da kumatun ta, sannan ta bude yoghurt din ta bata, Amnah ta kau da kai gefe, Munaya ta marairaice tamkar zata saki kuka tace "ki sha ko kadan ne ki sha magani kin ji" ta karasa cikin rarrashi.


Amnah ta buɗe bakin ta ta sha kadan, sannan Munaya ta ballo yan kananan maganin ta, ta dinga zuba mata a baki da daddaya ta sha, har ta ɗan sha yoghurt din kadan, Amnah ta kwantar da kanta a jikin Munaya, tace "mu...na....za..ki..mun...kitso ko?"

"Zan Miki mai kyau ma, da zarar kin warke"

"Yau..she...zan...War...ke mu...naaa?" Amnah ta tambaya tana kallon Munaya.

"Nan kusa da yardar Allah, nan kusa Amnah" dakin ya kara daukan shiru na wasu mintuna, suna rungume da juna abin tausayi, Amnah ta kara breaking shirun da cewa "ina... son...ki munaaa..., Ku...ma ina... son Umma, Am...ma na..fi son ki a...kan kowa, sa...bo...da baki ta..fi kin barni ba, ku...llum ki..na ta..re da ni, amma ita Um...ma ta ta..fi ba...ta da..wo ba"

Zafaffan hawaye mai tafe da murmushi ya wanzu a fuskar Munaya, ta ji mutuwar Umma ya dawo mata sabo, yayin da tsanar mahaifin su ya cika zuciyar ta, domin bata taɓa ganin mutum mara tausayi irin sa ba, ya tafi ya bar su, a kan dalilin sa mara tushe.


Cikin Muryar ta ɗaya dan shake sakamakon kukan da ta sha tace "Amnah ina son ki sosai nima, ina matukar kaunar ki kanwata, Umma ma na son ki sosai, amma bata da zabi ɗaya wuce ta tafi ta barmu"

Dakin ya sake daukan shiru, can Munaya tace "kwanta Amnah, bari nayi fitsari"
bayan ta kwantar da ita ta mike zuwa toilet, tana cikin gyara skirt din, ta ji karar faduwar abu kamar karfe kan tiles, tayi saurin buɗe Kofar toilet din ta fito, ta ga karfen da ake rataye karin ruwa ne ya fadi, ta kalli gadon taga Amnah ta fisge karin ruwan da aka Mata, hannun ta tallafe da kanta tana jijjiga hadi da mika sosai, cikin sauri ta nufi gadon tana kiran sunan ta cikin tashin hankali, amma ba amsa, ta fara kiran sunan doctor da karfi, tun daga office din sa ya jiyo Muryar ta, haka zalika nurses ɗin, cikin sauri suka shigo dakin, likitan baya bukatar ta mai karin bayani, he knows something is wrong.

Tsawon mintuna goma kafin likita yayi nasaran laffar da jijjigan da take, sai dai bata fasa rike kan ta ba, hakan yasa likitan yayi mata alluran bacci domin ta samu sauƙin radaddin ciwon kan, ya mayar mata da karin ruwan, cikin k'ak'arwan murya Munaya tace "likita, ya take yanzu?"

"Likita ya saka hannu a aljihu, ya sauke numfashi sannan yace "as you can see, she's unconscious, kamar yadda na fada Miki a baya mafita daya ce a mata aikin nan cikin gaggawa, domin za ki iya rasa ta a ko wani lokaci, I'm sorry to say, Amma cutar ya dai gejin da komai zai iya faruwa" yana gama fadin hakan ya fice daga dakin, nurses ɗin ma suka rufa masa baya.

Munaya ta bi likitan da kallo, tamkar ta ga sabon Hallita, gaba-daya ta rude ta firgice, ta dawo bakin gadon ta rike hannun Amnah, ta fara rera sabon kuka ƙasa-kasa, can kuma kukan ya dauke dif sakamakon tuno da *AA DAWOOD MOTORS* ma'ana wajen aikin ta, shaf ta manta da cewa tana aiki a wani waje banda yanzu, ta tuno kirkin Shakur, zata je wajen shi domin ya taimaka mata da kuɗin asibitin Amnah, ta yarda ko a albashin ta ne a dinga Zara, zata cigaba da musu aiki har ta gama biyan kudin da suka ara mata, koda shekaru goma sha biyar hakan zai dauke ta, wanna tunanin da ta yi ne yasa wani ƙarfi yazo mata, ta sumbaci hannun Amnah, tamkar wacce Amnah ke jin ta tace "in Sha Allah za a dace, Bara na je yanzu nan zan dawo kin ji" ta saki hannun ta a hankali ta nufi Hanyar barin dakin, har ta ɗora hannun ta a kan handle na kofar ta waiwayo tana kallon fuskar Amnah data yi fayau ta kuma kara fari, ta ji wani abu da bata san menene ba ya daki zuciyar ta, tayi saurin dauke idanun ta daga kanta ta bude dakin ta fice da gudu.

****

*MALEEK*

Tun zuwan sa office ya kasa gane kansa, wani irin mixed feelings da bai taba jin makamantansa ba yake ji a yau, ya mike zuwa dakin da yake hutawa, Bayan dan madaidaicin fridge dake dakin ya dauko irin box din da yake ajiye barar sa a gida ya dora kan doguwar sofa ya danna password ya ciro Barasa guda biyu ya zauna ya shanye tas, kana ya mayar ya rufe, yana ganin tunda ya sha barasan nan zai dawo normal, da wannan tunanin ya mike ya mayar da box din ya fita zuwa cikin office din sa, ya zauna, yana son taba aiki a system amma har wani biyu-biyu yake ganin rubutun screen din, ya kifa kansa da yayi masa nauyi a kan table glass.

Cikin sauri-sauri, gudu gudu take taka matatakalar benen domin isa office din Maleek, sai haki take saki domin ko da hawo saman kaɗai aka bar mutum zai gaji, bare ita dake zirga-zirga tun safe, bayan ta zo kofar shiga office din maleek sai ta tsaya tana sakin numfashi, sai data yi seconds biyar a haka kana ta tsaya bakin kofar ya buɗe ta shiga, ta fara neman Shakur, sai dai baya office din, hakan ya tabbatar mata da cewa bai zo ba yau, sai Maleek data gani ya kifa kansa a table, ta ma kasa magana sai ido data zuba masa.


*Maleek*

Shigowar mutum da ya ji ne ya sanya shi dago kansa, ya zuba wa Munaya rikitatun idanun sa, Wanna karon ba kallon tsana yake mata ba, kallon sosai yake bin ta da shi, tun daga kasa zuwa sama, a hankali ya motsa labb'ansa yace "You! Duk lokacin da kika ga dama kike zuwa aiki huh?"

Duk da bada fada yayi mata magana ba, amma sai da sautin Muryar sa ya bawa Munaya tsoro, domin amon ya fita da wani irin kalar tune da baki bazai iya furtawa ba, sai dai a bar wa zuciya, cikin rashin sanin abin yi ta durkusa tace "dan Allah dan Annabi kayi hakuri, wallahi Amnah kanwata ce ba lafiya, yanzu haka tana asibiti unconscious, tana da brain Cancer, likitoci sun ce kudin aikin da za a mata 3.9 million ne, Dan Allah dan Annabi ka taimaka min, kada na rasa kanwata, wallahi na yarda ko a albashina ne kana cire wa har na gama biyan ka, dan Allah kaji" ta karasa tana fashe masa da kuka mai ban tausayi.



Maleek ya cigaba da kallon Munaya, sai k'awata masa surar ta ake, yana ganin sabanin abinda yake a zahiri, gani yake bai taba ganin kyakkyawa kuma cikakkiyar mace kamar ta ba, ya saki wani shu'umin murmushi yana ganin zai yi amfani da damar sa, zai yi amfani da abinda ta roke shi ya kawar da abinda yake ji, domin shi kadai ya san balai'n da yake ji a marar sa, daurewa kawai yake, cikin takama da isa yace "ina da kudi fiye da abinda kike bukata, akwai wasu ma a drawer nan, zan baki million hudu ma, amma on one condition, zaki bani kanki" ya faɗa cikin gushewar tunani.

Murnan da Munaya take ya koma ciki, tashin hankali ya maye gurbin murmushin data fara yi, sam bata taɓa sammanin irin wanna maganar Daga bakin Maleek ba, duk da karancin shekarun ta amma ta fahimci abinda yake nufi, ta fara girgiza kai tana komawa da baya, har ta jingina da bango, tasa hannun ta ta share hawayen dake zuba a idanunta tamkar an balle famfo tace "dan Allah ka taimaka min, kaji tausayi na, , I'm only 15 year's, and I'm a virgin, karka lalata min rayuwa ta please"


"Hey shut up! ban yarda baki san namiji ba, a zamanin nan bana jin akwai mace da zata ce min tana tare da budurcin ta na yarda, don't pretend to me, ba dole na miki ba, zaɓi na baki, if you truly love your sister Zaki iya komai domin ceto rayuwar ta, so the choice is yours" ya karasa cikin Murya da zuwa yanzu mutum zai fahimci cewa ba a hayyacin sa yake ba, Munaya ta dinga ji tamkar mafarki take, daman haka boss din ta yake bata sani ba? Sam bai yi kama da wanda zai iya furta kazaman kalaman nan ba, bare Kuma ya aikata su , ga koshi ga kwanan yunwa, tana tuno nasihar Umma kan rike mutuncin ta, ta kuma tuno halin data bar Amnah a asibiti, tamkar zararriya haka ta fita daga office din tana fadin a'a Bazan iya ba!" Har ta sauka kasan bene, taji Muryar likita tamkar yanzu yake mata magana _"as you can see, she's unconscious, kamar yadda na fada Miki a baya, mafita daya ce a mata aikin nan cikin gaggawa, domin za ki iya rasa ta a ko wani lokaci, I'm sorry to say, Amma cutar ya dai gejin da komai zai iya faruwa_"


And then taji Muryar Umma tamkar yanzu take gaya mata _"Munaya ga amanar kanwarki nan na baki, ki kula da ita, karki bari tayi kukan maraice, ke ma ki kila sosai, ki kula da mutumcin ki na diya mace domin shine darajar ki, kar ki bari wani rudi na duniya yasa ki rasa wanna tsadadden darajan naki"_ kalaman Umma na karshe a gareta kenan.


Sai ta zama so confused ta rasa ya zata yi, ta zube nan karkashin stairs din tana fashewa da kuka gwanin tausayi, ta toshe kunnen ta saboda ta daina jin maganar Umma dana likita, domin sai amsa kuwwa maganar su take a hannun ta, ta tuna duk minti daya data bata daidai yake da rasa Amnah, ba kuma zata so ta rasa tilon kanwar ta ba, ta mike cikin sauri kamar an tsikare ta ta koma saman cikin gudu, wanna karon bata ji wahalar hawa benen ba saboda tashin hankalin da take ciki, har gaban sa taje tana jin mugun tsoron sa da take ji na barin zuciyar ta, a raunane tace "na amince, na yarda ka kwanta da Ni, na amince zan baka kaina, na amince ka karbi budurcina, matukar zaka bani kudin asibitin kanwata, i don't want to lose her please" ta karasa cikin wani sanyin murya tana runtse idanun ta, amma hawaye bai zuba ba, sai jaa da fuskar ta yayi tamkar tumatir.


Maleek ya mike, yana haɗa hanya har ya zo gabanta, ya watsa mata idanun sa da suka yi mugun ja, domin abu biyu ne ya hade masa, sha'awa da gushewar hankalin (maye), ya saki wani shu'umin murmushi, Cak ya dauki Munaya kamar yar tsana zuwa dakin da yake hutawa, Munaya da jikin ta ke k'ak'arwa ta fashe da kuka, duk yanda ta so dakewa kasa wa tayi.




#Share
#MunayaMaleek2023
#NoorEemaan


07082281566
[14/12, 12:54 pm] 𝙽𝚘𝚘𝚛𝙸𝚖𝚊𝚗✨: 🍇MunayaMaleek 🍓




_by NoorEemaan_📚✍️


Vi...
(6)


Numfashi ta sauke a lokacin data ga likita ne ke tsaye a kofar gidan su, ta taka a nutse zuwa gaban likitan wanda ya ke tsaye kusa da motar sa ya kafe kofar fitowa da ido, da alama sumayin fitowar ta yake.

A sanyaye tace "ina yini" bayan ta isa gareshi.
Cikin sigar wasa yace "Bazan amsa ba, bayan ko sunana ba ki sani ba"
Munaya ta dago fararren idanun ta da Yawan kukan da take yasa ya rine ta zuba wa doctor, Da ace a lokacin baya ne, da a ce Amnah'n ta na raye da tayi dariya daya ce hakan, sai dai a yanzu farin cikin ta yayi kaura ba kuma ta san yaushe zai dawo ba, tayi kasa da kanta tana murza sirarran yatsun ta.
Doctor kuwa ya fahimci yanayin ta, ya kuma mata Uzuri yasan is not easy manta abu irin wannan musamman ita da akwai shakuwa tsakanin ta da kanwar ta, ya mata Uzuri, amma yana son ya zama silar rage mata damuwa, domin a kallo daya ya mata ya hango tarin ramar da ta yi, ya kuma san har da zaman kadaici ke kara mata damuwa, ya saki ajiyar zuciya a bayyane yace "ya karin hakurin mu?"
Munaya taji kuka na son kufce mata, ta daure tace "alhamdulillah!"
Doctor ya kara cewa "Allah ya jikan ta da Rahama, Allah yasa mutuwa ta zamo hutu a gare ta"
Munaya ta kasa amsa wa, kukan da take kokarin rike wa ya kufce mata, ta saka hijab dinta ta rufe fuskar ta dashi...

Likita ya rufe idanun sa yana yana jin yanda sheshekar kukan ta ke fita na taba zuciyar sa, ya bude idanun sa yace "ooh Munaya kuka kuma? Ki hakuri, Amnah bata bukatar kuka a yanzu, addu'a kadai take bukata daga garemu, kiyi hakuri Please"

Munaya ta shiga jinjina kanta yayin da ta saka hannun ta innocently tana goge fuskar ta.

Tsawon mintuna uku suna a haka kana doctor yace "daman na zo ne domin mu yi magana sosai Ni dake, sai dai har Yanzu na ga You re not your self, so zan bari next idan na zo sai muyi maganar"

Munaya ta jinjina masa kai alamun "toh" ya bude seat din bayan motar sa ya fito da ledoji guda biyu ya mika mata na farkon mai dauke da tambarin *amrish delicious snacks* yace " ga wannan kayan kwalama ne na taho Miki da shi" Munaya ta girgiza kai hadi da cewa "Nagode"
Ya bata rai sosai yace "ai ba roko na kika yi ba, kuma in dai Kin dauke ni yayan ki kamar yanda na dauke ki kanwata toh ki karba" ya karasa hadi da mika mata ledar... Bata da kuzarin jayayya da mutum a halin da take ciki hakan yasa bata ƙara cewa komai ba.
Ya mika mata dayan leda da fadin "wannan kuma kudin ki ne wanda kika bari a office dina"
Kirjin Munaya ya buga sosai a lokacin data yi tozali da ledar data zuba kudin asibitin Amnah a ciki, taji tamkar an fama mata ciwon da ke ranta, ta daure ta karbi ledar tana jin wani tukuki a ranta, ta juya a sanyaye ta nufi cikin gidan, tana daf da shiga gidan ta ji Muryar likita yace "amma Munaya ina kika samu kudi mai yawa haka cikin kankanin lokaci?"
Wani murmushi daya fi kuka ciwo ta saki, hawayen da take ƙoƙarin rikewa suka balle mata, ba tare da ta juyo ba tace "i sold my virginity doctor, budurcina na siyar domin samawa Amnah lafiya, soyayyar kanwata ya rufe min ido har na manta cewa Allah shi ke rayawa ya kuma kashe, tsananin son da nake wa Amnah da kuma burin ganin ta rayu dani yasa na manta cewa babu wanda ya isa ya samawa bawa lafiya fa ce Ubangijin daya hallice shi, i so much hate my self, na tsani kaina doctor, ina kuma rokon Allah ya yafe min laifin dana aikata" Munaya ta karasa cikin kukan mai karfin sauti daya taho mata kana ta nufi cikin gidan da gudu. Bata da kowa, babu Wanda zata fadawa damuwar ta domin taji sauki a ranta, amma a Yau data samu ta fadi wani abu, she felt a bit relieved. Sannan bazata iya masa karya ba, toh karyar me zata yi da zata gamsar da shi dalilin samun kudi har 3.9m a cikin abinda bai fi awa biyu ba?.


Doctor ya fi mintuna goma a tsaye cikin matukar mamaki, lallai bai taba jin abinda ya daga masa hankali irin abinda Munaya ta fada masa ba, yaji ransa ya kai kololuwa a ɓaci, yana jin tamkar kanwar sa ta jini ce abin nan ya faru da ita, a fusace ya shiga motar sa ya tayar ya bar layin.

MALEEK!!!
Tun bayan faruwar al'amarin nan ya rasa nutsuwar zuciya, domin har sai ya sha barasa, tunanin sa ya gushe yake samun saukin zuciyar sa, ga Shakur da har yanzu baya kula shi abin ya ƙara damun sa.
Kamar yau zaune suke a dinning table su ukun, har da mummy, sai dai zaratan samarin babu annushuwa a tare da su, mummy dake serving din su breakfast sai a yanzu ta lura basa hira cikin kaunar junan su kamar yanda suka saba, Domin tun bayan dawowarta daga gidan malam ta shiga damuwa mai yawa, domin har karyan rashin lafiya tayi ta dinga zaman daki, domin idan tace zata bari su hadu da Maleek a ranar da abin ya faru komai zai iya faruwa har ta kai ta tona rufaffen sirrin dake zuciyar ta, wanda hakan zai sa komai ya lalace mata har ta kasa cimma burin ta.
Ganin shirun yayi yawa yasa tace "daddyn ku yace next week zai dawo" ta fada hoping zasu yi murnar da suka saba a duk lokacin da daddyn nasu zai dawo kasar, amma sai ta ga sabanin hakan, Shakur ne ya yi Karfin halin cewa "Allah ya dawo da shi lafiya" kana ya dire mug din hannunsa, ya mike hadi da cewa "na tafi mummy" bai jira amsar ta ba ya fita, nan mummy ta kara tabbatar da cewa something is fishy, Amma ta san bazasu fada mata abinda ke faruwa ba, domin ba a shiga tsakanin su, tun suna yara masu rike sirrin junansu ne,

1 Comments On MUNAYA MALEEK
avatar
nusaibabello

12 months ago

Reply

Dghhjhujvghkjvg

Please Login or Register in order to submit comment