Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register



Jikin Shakur ne ya mutu Saboda tsabar shock, ya samu ya koma da baya ya jingina da bango idanunsa kan fuskar Maleek, da wani ne ya fada masa wadandanan maganganun da sai inda karfin sa ya kare, amma abin takaicin dan'uwan sa mafi soyuwa a ransa ne ke faɗa masa ya aikata zunubi mafi girma cikin manyan Manyan zunubai, Maleek ya mike ya isa ga Shakur, a ƙoƙarin sa na son yi wa shakur din bayani, domin sam baya son dan'uwan na sa ya ga laifin sa, ko fara maganar Shakur bai Bari ya yi ba ya daga masa hannu cikin tsananin fushi, kana a fusace ya bar dakin...
Maleek ya naushi bango cikin bacin rai hadi da hargitsa sumar kanshi, ya dawo bakin sofan ya zauna hannun sa rufe kan fuskar sa, jikin sa har wani rawa-rawa yake.

★★★
*Munaya*
A hankali ta fara bude idanun ta, ta sauke su kan farin celling dake saman dakin, tunanin ta ya tsaya cak yayin da ƙwaƙwalwar ta ya daina aiki, Tamkar statue haka ta dawo, tsawon mintuna biyar tana a haka sai ga likita ya shiga, ganin idanun ta a bude yasa ya karaso cikin sauri hadi da mata sannu, ta bishi da kallo, tana ƙoƙarin tuna abubuwan da suka faru amma brain dinta yaki bata hadin kai, bayan wasu mintuna komai ya shiga dawo mata daki-daki har izuwa sanda tayi tozali da gawar Amnah, ta rufe idanun ta yayinda wasu zafaffan hawaye suka zubo mata, ta dafe kanta dake matukar sara mata, sannan ta mike, ta kalli doctor da jajayen idanunta, cikin raunananiyar muryar ta tace "ina Amnah doctor?"

Likita ya sauke ajiyar zuciya, domin ya dauka zaka birkice masa idan ta farka, amma to his greatest surprise ta nutsu, duk da kallo daya mutum zai mata tayi matukar bashi tausayi, ya yi kasa da murya yace "tana gidan ku, na duba address din ne ta file din ta dake asibitin nan, an Mata wanka an suturtata, har za'a sallace ta nace musu kina asibiti, Bara naje na dauko ki domin ki mata sallamar ƙarshe magriba na gabatowa, ko zaki iya tashi muje?"
"Sallamar ƙarshe" Munaya ta maimaita abinda doctor yace, kalaman biyun nan sun narke zuciyar ta, kamar yadda suka mata nauyi a kunnuwan ta, da gaske kenan zata rabu da Amnah a yau? Rabuwa ta har abada! Ta share hawayen daya zubo mata kana ta mike cikin dauriya tayi gaba likitan ya bi ta a baya, yana ƙara mamakin danganan da Allah ya sa mata, domin bai yi expecting nutsuwa da hakurin nan daga gare ta bayan ta farka ba.

Mutanen unguwar su ta gani makil a dan kofar gidan na su, hannun ta dake matukar rawa ta sa ta bude murfin motar, kana ta fito kanta a kasa, nan mutanan unguwar su har waɗanda basu taba mata Magana ba suka shiga yi mata gaisuwa hakan ya balai'n ƙarya raunananiyar zuciyar ta mai cike da damuwowi.

Tsakar gidan su ma ta ga tarin jama'a, domin Amnah yarinya ce mai farin jinin jama'a sosai, kowa nata ne, ta sa kafar ta cikin dakin, nan ta ga Amnah kwance cikin farin kal din likkafani, ta zube gaban gawar hadi da rungume ta ta saki wani marayan kuka, tana jin muryoyin jama'a na bata baki hadi da fada mata cewa ta daina ba a son ana yi wa mamaci kuka, sai da tayi mai isar ta sannan ta bude fuskar Amnah data ga ta kara haske fin yanda tayi dazu a asibiti, hannun ta kan fuskar Amnah da idanunta ke rufe tamkar mai bacci tace "Amnah rabin raina...." Ta kasa karasa maganar saboda wani mugun kuka daya taho mata, tayi kokarin hadiye kukan tace "Amnah Ummu ta tafi, ke ma tafiya Zaki yi ki bar ni? Kece komai nawa, ya kike tunanin zan jure rashin ki? Zan yi kewar ki sosai, ki yafe min, ina ji a jikina Kamar na gaza, kamar ban yi kokari wurin ganin kin samu lafiya ba, ina ji a jikina cewa ban cika wa Umman mu alkawarin dana Dauka na kulawa dake ba, but i tried all i could Amnah, Allah ya jikan ki da Rahama, Allahu Ya sadaki da annabin rahama, Allah yasa ki kasance cikin makarantar Annabi Ibrahim, ki yafe min Amnah, ina kaunar ki sosai, har abada zaki kasance a zuciya ta, Allah ya haɗa fuskokin mu a aljannatul firdausi, till we meet again my blood" ta karasa hadi da dora fuskar ta saman ta Amnah tana cigaba da rera kuka, kusan kowa a wajen sai daya zubar da hawayen tausayin Munaya, har masu shesheka da sautin ya bayyana, a daidai nan mazan suka shigo zasu tafi da gawar domin yi mata sallar, nan Munaya taki sakin gawar ta fara kuka mai sauti sosai, da kyar aka raba su aka fita da gawar, anyi sallar jana'izar ciki har da doctor, sannan aka tafi domin kai ta gidan ta na gaskiya. Hakika Amnah tayi jama'a sosai har wasu mutane na mamakin yawan jama'ar ta.

Zuwa bayan isha kowa ya watse a gidan ya rage saura Munaya ita daya, bata taɓa jin ciwon rashin yan'uwa irin yanda taji ba yau, musamman daya rage ita daya yanzu, tsabar kuka kuwa idanunta har yaji suke mata, suka yi luhu-luhu har bata iya bude su da kyau, amma hakan bai sa ta daina kukan ba, domin data tuno abubuwan da suka faru da ita a yau bata iya rike kukan ta, wanna ranar bazai taba goguwa a ran ta ba, haka zalika shine rana mafi muni a rayuwar ta, wanna rana ta zance bakar rana a gareta wanda bazata manta ba.
Tsoron Allah da nadamar abinda ta aikata ya cika zuciyar ta, tayi matukar nadamar zinar ɗata aikata a yau, gashi kwalliya bata biya kudin sabulu ba, domin samun kudin aikin asibitin Amnah daya sa ta aikata zina bai amfana Mata komai ba, gashi ko aikin ba a kai ga mata ba Allah ya dauki abar sa.
Ta shiga buga kanta a bango tana fadin "kaico na, kaicona, ya Allah ka yafe min, Amnah Allah ya jikan ki, wayyo Allah na" haka Munaya ta dinga kuka tana maganganu masu matuƙar ratsa zuciya har maganar ta ya daina fitowa saboda tsabar kuka, sai a yanzu ta tuna cewa bata yi sallar azahar har zuwa isha ba, ta mike a sanyaye, tana jin kasanta na mata radaddi har yanzu domin tsami wajen ya kara yi sakamakon bai samu kulawa ba, ta taka a sannu zuwa tsakar gidan ko damuwa da duhun gidan bata yi ba, domin gwara duhun nan da take gani a idanun ta akan mugun duhun da zuciyar ta yayi, ta dinga ji kamar zata ga Amnah ta biyo ta hadi da kama hannun ta tace "muna zan biki banɗaki" sai dai ta san har abada bazata kara jin Muryar kanwar ta ba, Domin ita mutuwa gaskiya ce, ba kuma a dawowa, ruwan sanyi ta diba ta shiga banɗakin su, duk da sanyin ruwan da kuma sanyin gari bata ji shi ba, haka tayi wankan tsarkin ta fito, ta daura alwala, kana ta shiga daki ta Sanja wasu kayan, ta shiga jero salollin da ake abin ta a zaune saboda ko jimawa bata iyawa a tsaye, bayan ta iddar ta daga hannun ta sama ta shiga jero addu'o'i ga Amnah sannan ta nemi yafiyar Ubangiji kan abubuwan data aikata musamman na yau, tana yi tana kuka, bayan ta gama ta sulale ta kwanta hannun ta dafe da kanta dake mugun ciwo, sosai ta kudundune kanta kamar kayan wanki, kewar Amnah na nurkukusan zuciyar ta, she's so lonely, basai an fada wa mutum ba, kallo daya mutum zai mata ya fahimci hakan, ta kuma baka tausayi mai yawa.

_Bayan sadakar bakwai_
*4:34pm*

Tana zaune a dan taskar gidan su ta zuba tagumi, ta ƙara ramewa sosai daman ba kiba ce da ita ba, tunda Amnah ta rasu ba ta sa komai a cikin ta ba sai ruwa. Wani almajiri ne yayi sallama cikin gidan, har sau biyu kana Munaya tayi firgigit saboda nisa a tunani ta zubawa yaron ido, yaron yace "wai ana sallama da Munaya a waje"
Her heart skip a little bit, ta shiga tunanin waye ke neman ta, ta jinjina wa yaron kai alamun "toh" dama da hijab a jikin ta tun wanda tayi sallar Asr, ta mike hadi da zura takalmin ta ta nufi waje tana jin bugun zuciyar ta na karuwa.
[14/12, 12:54 pm] 𝙽𝚘𝚘𝚛𝙸𝚖𝚊𝚗✨: 🍇MunayaMaleek🍓




_By NoorEemaan_📚✍️



Wattpad: NoorEemaan
Arewabooks: nooreemaan


xiii
(8)

Munaya da tunda ya matso kusa da ita taji kamshin turaren sa na hawan mata kai, ta dinga jin tashin zuciya, sai dai ta cigaba da daurewa, a gefe daya kuma tana mamaki, domin ita din ma'abociyar son kamshi ce, duk da bata taba samun kuɗin mallakar turare na kan ta ba, amma tana son jin kamshi ko da wani ne ya saka, ta cigaba da daurewa yayinda take jin jiri jiri tamkar zata fadi, sai dai yana kai karshen maganar sa ta ji amai ya taho mata, ta yi saurin durkusawa bakin kwatan dake wajen tana kwarara amai sosai... Gabanta yayi mummunar bugawa a lokacin da take ƙoƙarin tuno wani abu, sai dai jirin da take gani yasa ta kasa haɗa tunanin ta waje daya. Bugun zuciyar ta ya cigaba da karuwa, murya a mugun raunane ta samu hada kalmar "Inna lillahi wa inna ilaihi raju'un" ta karasa wasu hawaye masu zafi na biyo kuncin ta...
Doctor Abbas da hankalinsa ke tashe yana mata sannu ya yi saurin buɗe motar sa ya dauko mata ruwa hadi da mika mata, Munaya ta kasa karba, gaba-daya komai ya tsaya mata cak, ta rasa abinda ke mata dadi, kana ta rasa wani irin tunanin ya kamata tayi, ta mike a hankali ta juya zuwa cikin gida, taku uku tayi ta ji wani duhu ya gilma ta idanun ta, wani mugun jiri ya sake dibar ta, ta tafi luuu ta zube, cikin sauri doctor Abbas ya karaso inda take, ya shiga kiran sunan ta "Munaya! Munaya!!" Amma ta gagara amsa wa, hankali a tashe ya dauke ta zuwa wajen motar sa, da hannu daya ya bude murfin motar ya sanya ta a ciki, ya zagayo ya shiga gaban motar ya tayar da ita da saurin gaske ya bar layin, duk bayan seconds biyu sai ya juyo ya kalle ta, maimakon ya nufi asibitin su sai ya nufi wani asibitin dake kusa sosai, musamman daya fahimci cewa tana bukatar taimakon gaggawa...
Mintuna biyar kacal ya kawo su asibitin, ya dauke ta cikin sauri ya nufi cikin asibitin, nurses dake kan duty suka yi saurin karban ta, sannan ya nuna musu ID card din sa, hakan yasa suka bar shi ya shiga, sosai likitan asibitin ya shiga duba Munaya, tsawon mintuna sittin ana abu daya, domin har test ya yi mata running domin ya fahimci matsalar ta kana a ƙarshe ya daura mata drip domin babu karfi ko digo a jikin ta, yana mikawa nurses kayan da yayi amfani da su ya kalli doctor Abbas yace "see me in my office doctor" ya karasa hadi da ficewa, doctor Abbas ya bi Munaya da kallo, sosai zuciyar sa ta karye, ba sai an fada wa mutum ba kallo daya za a mata a fahimci tana cikin halin rayuwa, numfashi ya sauke, yana fatan Allah ya sa ba wata Matsala ce babban ke damun ta ba...

"Ban san ya kuke da yarinyar daka kawo ba, may be your sister, neither your wife, ba hurumina bane lallai sai na sani, i won't say anything much tunda kai likita ne, You re already
into the system ka san komai, that girl is in a critical condition, nayi mamaki sosai da har karamar yarinya kamar ta jininta ya hau har haka, sannan the worst part is she's 6weeks pregnant, banason shiga hurumin da ba nawa ba, amma yarinyar nan tayi kankanta da haihuwa gaskiya...." Ya dan yin shiru kamar mai tunanin Wani abu sai kuma ya kara da cewa "any way ga drug's da za a siya mata" ya kai karshen maganar da rubuta masa magunguna.

Doctor Abbas was so speechless at first, ko kusa bai taba kawo hakan a ransa ba, Banda innalillahi babu abinda yake maimaita cikin ransa, sosai maganganun likitan suka dake sa, tausayin Munaya mai yawa ya sake rufe shi, yasan Munaya tayi wauta, ta kuma yi kuskure da laifi mai yawa, amma ya mata uzuri, musamman idan aka yi duba da karancin shekaru ta, ya mike a sanyaye ya fice zuwa siyo mata maganin.

_WASHEGARI_
A hankali ta fara bude idanunta da suka bata awanin a rufe, a kallo daya da ta yi wa inda take kwance ta fahimci asibiti ne, komai daya faru da ita a jiyan ya shiga dawo mata, bugun kirjin ta ya fara bada sautin dim! dim! dim! Har tana jiyo sautin sa tamkar zai fasa kirjin ta ya fito, hawaye suka zubo mata, can kasan makoshi ta furta "ya Allah kasa ba abinda nake tunani bane, ya Allah ka yafe min na tubaaa!" Ta karasa wanna karon cikin dan karfin sauti yayinda ta fashe da kuka....

Ta jima tana kukan, har sai da taji kanta kamar zai cire dan ciwo sannan tayi shiru tana sauke ajiyar zuciya a jejere.

****
A hankali doctor Abbas ya turo kofar ya shigo, Ganin idanun Munaya biyu ya saka ya karasa gareta cikin sauri, cikin murya mai cike da kulawa yace "Munaya sannu kin tashi, I'm sorry na samu kiran emergency ne shiyasa na fita, ya kike ji yanzu?"

Munaya ta zuba masa innocent idanun ta masu tarin rauni, tana mai yaba kirkin sa a ran ta, ya taimaka mata sosai duk da basu hada komai ba, amma har yau ko godiya ta kasa masa, still bai tsare ba ya cigaba da taimaka mata, ta sauke idanun ta kasa, a hankali tace "da sauki"
"Alhamdulillah!" Yace cikin tausayin ta, bai ma san ta ina zai fara bata wanna bakin labarin ba, numfashi ya sauke kana yace "i brought you breakfast na san kina jin yunwa koo"

Ta kalli ledar hannun sa ba tare da tace komai ba, ya fito da takeaway mai dauke da chips da egg ya mita mata, ta girgiza kai alamun bata ci, ya ja kujera ya zauna yace "kin san baki da lafiya ko? Kina bukatar Energy, babu karfi ko digo a jikin ki, kici Please"

"Banason kamshin wanna abincin" Tace tana jin sabon tashin zuciya. Cikin sauri doctor Abbas ya matsar da ledar mai ɗauke da abincin a kusa da ita kana ya dawo ya zauna.

"Menene yake damuna doctor?"
Ba tare da ya shirya wa hakan ba ya ji saukar Muryar ta mai cike da rauni a kunnen sa .
Shiru doctor Abbas yayi ya kasa bata amsa, domin bai san yanda zata dauki maganar ba, a rayuwar sa bai taba ganin yarinya mai shekaru irin na Munaya dake fuskantar ƙaddarar rayuwa kamar haka ba.

"Please" ta kara rokon sa.

Jin shirun yasa jikin ta ƙara sanyi, jikin ta na fada mata cewa ciki ne da ita, amma tana bukatar a ƙaryata hakan, tanaso taji wani yasa mata hope din cewa zazzaɓi take, ta runtse idanun ta kana ta bude su, tsawon mintuna biyar sannan tace "Ciki ne dani ko doctor?" tace cikin Muryar kuka yayinda hawaye suka cika idanun ta.

Cikin mamaki mabayyane doctor Abbas zaro idanun sa, ta faru da kare, shi da yake tunanin hanyar boye mata, ya sauke karamar ajiyar zuciya yace "ciki! How did you know that Munaya?"


Lumshe idanun ta tayi, sai Yanzu ta tuna rabon ta da period kusan wata biyu kenan, tunda tana 13yrs ta fara gani, bata taba fashi a ko wanne wata ba sai wanna karon,
sai a lokacin hawayen suka zubo kuncin ta, ta saka bayan hannun ta na hagu ta share hawayen tace "baya ga Amnah Umma ce mutum ta farko da muka Shaku, Umma nah ta fadamin symptoms na masu ciki idan muna hira domin na kasance ni yarinya ce mai son sanin abubuwa musamman ɓangaren mata, ina da yawan tambaya kan wanna fannin, Umma na ce ta sa min sha'awar karatun likita, domin har alkawari ta min na cewa matukar ina son karatun likitan da gaske, ita kuma zata tsaya min da duk abinda take da shi domin cika burina, na kan ce mata Ummah idan na girma na zama likita zan yi wa Amnah aiki a asibitin da za gina har ta warke, a lokaci sai dai ta min murmushi, ashe bazasu rayu tare da Ni ba. Tayi shiru tana ƙoƙarin danne kukanta kana ta ɗora da cewa, Umma ta bani labarin irin laulayin data yi a cikina, irin shi nake ji a jikina doctor, da gaske ina da ciki doctor? hasashena gaske ne? Please say no doctor, ya Allah na tuba"

Jinjina kai likita yake cikin mamakin wayo irin na Munaya, lallai ta wuce inda yake tunani, tana da kaifin tunani daya girmamawa shekarun ta, lallai bawa baya iya tsallaken ƙaddarar sa, idan ba haka ba, Munaya na da wayo da bazata Bari wani namiji ya tara da ita ba, ya shafa fuskar sa cikin rashin sanin abin yi, can ya numfasa hadi da cewa "Munaya kiyi hakuri, ki sani cewa bawa baya wuce ƙaddarar sa, Allah gafurur Raheem ne, ki cigaba da istigifari, ni ma zan taya ki"

"Dan Allah doctor ka cire min cikin nan, wallahi Bazan iya ba, na tsani shi dan Allah doctor" ta karasa cikin rokon sa.

"Subhnanallah Munaya karki kara fadin haka, ya za'a cire cikin, bayan wancan zunubin kina son yin kisa, kina so Allah yayi fushi dake?"

Kuka sosai Munaya ke yi, har majina na zuba daga dogon hanjin ta, tsana mai yawa na Maleek ya kara cika zuciyar ta, hatta abun da ke cikin ta ta tsane shi, da ba dan karta zama mai tarin laifi ba data kashe kanta, domin komai ya daina mata dadi ko burge ta a wanna duniyar mai cike da kalubale, doctor Abbas kam ya ma rasa wani kalma zai yi amfani da ita wurin kwantar mata da hankali, ya cigaba da zuba mata idanun sa yayinda take kuka, can ya jif kukan ya dauke, ya kalleta da kyau sai ya ga jikin ta ya saki, hankalin sa yayi mummunan tashi, tsoron sa kada ta hadiyi zuciya ta mutu, ya ma manta cewa shi din fa likita ne, hankalin sa a tashe ya fice domin kiran
Likita, Babu bata lokaci likitan ya biyo bayan sa, cikin ikon Allah ta farfaɗo daga suman data yi bayan likitan ya bata taimakon gaggawa, sai dai jinin ta ya sake hawa, abinda ake son ya sauka musamman ga ita mai ciki.

***
Kwanan ta uku kafin aka sallame ta, doctor Abbas ya Kai ta gida, Bayan ya sake kwantar mata da hankali ya kuma roke ta tana dan cin abinci ko yaya ne, ya kuma yi mata alƙawarin cewa zai dawo jibi ya duba yanayin jikin ta, jinjina masa kai tayi kana ta fice daga cikin motar tamkar wacce kwai ya fashewa a jiki, doctor Abbas ya bi ta da kallo har ta bacewa ganin sa, ya sauke ajiyar zuciya ya tada motar sa ya bar layin .

A daren Munaya ta yi mafarkin da Umman a dan baccin daya dauke ta kasance allurar baccin bai gama sakin ta ba, abin data gani yayi matukar daga hankalin ta, ta tashi zaune ta jingina da bango, tana jin yanda jikin ta ya jike da gumi, abinda yafi daga mata hankali shine ko yaya ta kifta idanun ta ko ta lumshe su sai ta hangi umma tsaye fuskar ta babu annuri yayinda hawaye ke zuba daga idanun ta tamkar an balle famfo, ta kasa gane kan wanna mafarkin, domin tun bayan rasuwar Umma da kwana biyu bata kara yin mafarki da ita ba.



***
Kamar yadda doctor Abbas yayi alƙawari ya dawo, bayan sun gaisa, ya ɗan ja ta da hira wanda yawanci shi kadai ke maganar sa, domin ba wata amsar kirki yake samu daga gare ta ba, a karshe yace. "Munaya ina ganin ya kamata a sanar da who's responsible for pregnancy abinda ke faruwa, dole ya san abinda ya aikata, a ina yake, ki bani address dịn sa Ni zan je na sanar masa, idan ma yaki amincewa zan hada shi da hukuma" Girgiza kai Munaya ta shiga yi, hawaye cike a idanun ta.

Ya kara tausasa murya yace " na fahimci yanda kike ji, kiyi hakuri Munaya, Ni kai na bana son wata mu'amala ta ƙara hadu ku, amma jaririn da bai san komai ba, bai kamata laifin baban sa ya shafe shi ba, duk abinda nake yi ina yi for your own good, tamkar kanwata haka nake jin ki, bazan cutar da ke ba, kin ji koo?"

Ta runtse idanun ta, cikin jin ciwon kalmar jariri da uban da likita ya ambata, bata bukatar su, ko jin sunan, yaya za ta yi da rayuwar ta? Yanda ta tsani Maleek, haƙa ta tsani jininsa dake kwance a mahaifar ta, ta ja wata doguwar ajiyar zuciya daya sanya doctor Abbas kara tausaya Mata domin ya fahimci tunani ta fada.





Su waye MunayaMaleek???
We will find out as from next page, ku biyo ni dan ji tarihin MunayaMaleek...
Wanna tafiyar mai tsawo ce Fiye da sauran books dina, kuzo muyi tafiyar nan da ku fam, come one, come all❤️



I know today's chappy is short, shhhhhhh🤫😂❤️



MunayaMaleek is 500 via 3200689890 Haruna Rukayya first bank, zaku iya fara payment Kafin mu gama free pages ngd.




NoorEemaan
07082281566
[14/12, 12:54 pm] 𝙽𝚘𝚘𝚛𝙸𝚖𝚊𝚗✨: 🍇MunayaMaleek🍓



_by NoorEemaan_📚✍️


Wattpad@NoorEemaan
Arewabooks@nooreemaan

https://www.facebook.com/groups/1346404966270527/?ref=share_group_link
(Kuyi following sabon account dina please)

https://whatsapp.com/channel/0029Va5o0Gc4o7qU8MCJuN32
(Follow my WhatsApp channel domin samun update )


*Gaisuwa ta musamman zuwa ga makarantar NoorEemaan, bazan iya rubuta yawan ku ba, amma ina muku son so*❤️



Vii
(7)

A ranar da Munaya ta sanar da likita cewa budurcin ta ta siyar Kafin ta samu makud'an kuɗaɗen nan bai runtsa ba, sosai zuciyar sa ke kuna tamkar ciki daya suka fito da ita, a ransa kuma yana ji tamkar har da laifin sa yasa hakan ta faru, a matsayin sa na likita ya kamata yayi la'akari da cewa Munaya karamar yarinya ce, bai kamata kai tsaye ya sanar Mata cewa komai zai iya faruwa da Amnah idan ba'a yi saurin yi mata aikin ba, yana ji a ransa cewa har da kalaman sa gareta yasa ta tsorata har tayi saurin bada budurcin ta, Amma yanzu ya ɗauki darasi a rayuwa, zai kiyaye yanda zai yiwa duk wanda ya Kawo patient magana da ma patient ɗin, zai kwantar musu da hankali ko da yasan cewa shi Mara lafiyar na dab da rasa ransa, ko dan gudun abinda ya faru da munaya ya sake faruwa ga wata, kila daya kwantar wa Munaya hankali duk da halin da kanwar ta ke ciki na halin rai ko mutuwa da kila bata rasa abubuwa biyu masu matukar muhimmanci a rayuwar ta ba, da kila ta tsira da daya, amma abin ciwo da takaicin, babu Amnah, Babu budurcin Munaya! Ya sake juyi kan gadon sa cikin damuwa, yana ji kamar yaga mara imanin daya aikatawa Munaya haka da tabbas sai inda karfin sa ya kare, qwarai abin ya tsaya masa a zuciya.

***
Bangaren Maleek kuwa tun bayan da suka dawo daga neman Munaya ya rasa meke damun sa, mintina daya zuwa biyu tunanin ta ya fado masa rai, sai dai ya alakanta hakan da managar da Munaya ta faɗa masa bayan ta watsa masa 3.9 million din sa, yayi tunanin zata dawo aikin bayan wasu kwanakin zuwa goma haka amma sai ya ga lokaci na dada ja ba tare da ko mai kamaninta ya gani ba, shi dai yasan bai bata muhimmanci ba saboda ita din ba komai bace a gareshi, kawai yana takaicin abinda ya aikata da karamar yarinyar da take basa kyama, sai kuma maganar mutuwar yarinyar (Amnah) da ya dake sa sosai, sai yake jin wani *quilty conscience*, bai taba nadamar shan giya ba sai ranar daya kusanci Munaya cikin maye, ko da yana cikin maye shi din tsayayyen namiji ba, sai dai bai san abinda yasa a ranar ya kasa controlling kansa

1 Comments On MUNAYA MALEEK
avatar
nusaibabello

12 months ago

Reply

Dghhjhujvghkjvg

Please Login or Register in order to submit comment