Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba har ya afka mata, ya mike tsaye hannun sa sanye cikin aljihu ya taka zuwa ga dogon window'n glass din office din, tarr yake ganin mutanen da suke wucewa kan ababen hawa da masu haɗa haɗar su cikin kwanciyar hankali, ya jima a tsaye idanun sa a wajen yana kallo, sai dai ba kallon yake ba, yayi nisa a tunani ne, sai daya bata lokaci tsaye a wajen kana ya dawo ya zauna kan kujerar sa, can kuma kamar an tsikare shi ya mike zuwa dakin hutun sa ya shiga, tun ranar da abin nan ya faru ya daina barin masu aiki shiga Wajen, daya tashi zai rufe kofar da kansa, yana shiga jinin daya bata farin sofan na nan bai goge ba, ya sauke idanun sa masu rikitarwa kan sofan yana kallo, ya dauke idanunsa daga kallon jinin ya sauke kan mataciyyar ribbon din ta daya tsufa sosai ya ga har da silin dogon gashin ta daya manne da ribbon din, ya dauke idanunsa daga nan ya zauna kan kujera, ya dawo da cctv Cameran baya zuwa ranar da abin nan ya faru, ya dinga kalla daya bayan daya, sai dai daya zo kan inda komai ya kankama sai ya yi saurin kashe wa, domin haushin kansa yake ji, he hate his self for what he did, Sam baya nadamar zinar daya aikata, sai haushin kansa da yake ji da aikata hakan da yarinyar da ya tsana, ya furzar ga iska mai dumi daga bakin sa ya shaki kamshin mouth spray ɗin a hancinsa.

***
_8:00pm_

Cikin farin ciki mummy take yau, zata samu cikar burinta, motsa coffeen dake cikin kyakkyawar wani mug take, bayan ta gama ta nufi hanyar dakin ta, ta san Maleek yana shigowa zai shanye coffeen, domin baya wasa da coffee, Shakur ba sha yake ba tunda shi ba masoyin sa bane, yafi ganewa shayi, ta shiga daki ta shirya cikin had'add'en nighty tana jiran sa, domin an tabbatar mata da kansa zai shigo ya neme ta bayan ya shanye.


Munaya!!!
Har ila yau komai baya yiwa Munaya dadi, taji duniyar ta tsaya mata cak, gata dai tana rayuwa cikin mutane sai dai kallo daya mutum zai mata ya fahimci tana fuskantar kalubalen rayuwa, ta zama shiru shiru, bata fita ko ina, bata zuwa ko ina, kayan kwalaman da likita ya bata har yanzu bata gama cinye su ba kasancewar ta rasa apetite din ta, sai ta ji y'a'yan hanjin ta sun motsa Sannan take neman abu ta saka a cikin ta, ta sake ramewa sosai tamkar zata ɓalle idan an mata kyakkyawan riko.
Tana kwance idanunta na kallon farin wata wanda hasken sa ne ya haskaka dan tsakar gidan, domin ta daina rayuwa da fitila ko wani abu da zai haskaka gidan idan dare yayi, daman ba'a zancen nepa, takun mutum taji zuwa cikin gidan kana ta ji Muryar wani yaro na fadin "Assalamu alaikum, wai ana kiran Munaya in ji wani a waje" yana gama fadin haka ya juya ya fita bai jira amsa ba, kamar ko ya san da cewa ba amsar zai samu ba.
Tsawon mintuna biyar kana Munaya ta yunkura ta mike tsaye, taji jiri zai kada ta tayi saurin dafa bango, ta saka takalmi hadi da zura hijab din ta, a hankali ta nufi hanyar fita, she thought as much doctor ne kuwa tsaye jikin motar sa.

***

Cikin nutsuwa Alhaji Dawood ya buɗe karamin gate din gidan ya shiga hannunsa rike da karamin trolley, sanye yake cikin wasu hadaddun suit ash color, kallo daya mutum zai masa ya hango cewa shi din business man ne, kana ga kwarjini, wayewa, hadi da kamala a tare da shi, mai gadi daya sallame sallah yayi saurin juyowa sakamakon motsin mutum da ya ji, fara'a ta wadatu kan fuskar mai gadi, cikin sauri ya tashi zuwa gaban Alhaji ya ɗan durkusa cikin girmamawa yace "Barka da zuwa Alhaji, ya hanya?"
"Cikin murmushi Alhaji Dawood yace "lafiya Lou alhamdulillah Audu, mun same ku lafiya?"
"Wallahi alhamdulillah Alhaji"
"Masha Allah!" Alhaji Dawood ya fada yana barin wajen bayan ya hana mai gadi karban masa trolley din sa, kansa tsaye ya shiga cikin had'add'en falon inda ba kowa sai motsin plasma dake bango yana aiki shi kadai, ya saki murmushi yana hango farin cikin da iyalansa zasu yi idan suka gan shi, hakan yasa yayi musu zuwan bazata, tunda waccan zuwan daya ce musu zai zo bai samu zuwa ba shi yasa this time ya shirya musu surprise, sai dai su gan shi, har ya gota dinning din ya dawo da baya saboda kamshin coffee daya daki hancin sa, ya dauki mug din mai dauke da coffee ya kurba kadan, ya ji ya masa dad'i sosai, sai ya shanye duka, bayan nan ya dire mug din, ya ajiye trolley din gefen kujera, ya nufi dakin mummy domin yayi kewar ta sosai.

Mummy kam data ji motsin bude kofa ta wani lumshe ido cikin jin dadi fuskar ta dauke da murmushin nasara, Finally dai yau zata kashe ƙishirwar da ta daɓe shekaru masu yawa tana jira, cikin wani salo ta buɗe idanun ta tarr ta sauke su cikin na Alhaji Dawood dake mata murmushi, ta zabura hadi da mikewa kirjinta na ludugan bugu, ta murza idanun ta da kyau ta ga dai still Alhajin take gani a tsaye, take fuskar ta ya Sanja har bata san sanda ta furta "haba Alhaji, ya zaka dawo yau?" ta karasa cikin dacin murya.

Kalaman sun dan bawa Alhaji Dawood mamaki, ya kalle ta da kyau yace "ban gane da ban dawo ba yau, akwai matsala ne Sa'adah?"

Sai a lokacin ta fahimci subutar data yi, cikin kissa ta karasa gareshi hadi da rungume shi tace "ina nufin daka sanar min ai, ya kamata a shirya maka tarba mai kyau tunda baka taba dadewa irin haka baka dawo ba" ta karasa tana share hawayen takaicin daya zubo mata cikin dabara, tana jin kamar ta shake Alhaji Dawood ta huta.
Murmushi bai gushe a fuskar Alhaji Dawood ba, ya rungume ta da kyau yace "karki damu matata, ko me kuke da shi zan ci, besides na Sha dadd'ad'an coffeen da kika yi, kamar kin san zan dawo, kodai kin ji hakan a jikin ki?" Ya karasa cikin wani salon soyyaaya irin na su na Manya.
Wani tukikin abu ya kara tsaya wa mummy a makoshi, ta danne ta hanyar sakin murmushin yake, yanzu haka tana ji tana gani duk tanadin data yi domin Maleek sai Alhaji ne zai more shi, bakin ciki kamar ta mutu amma haka ta daure gudun kada Alhaji Dawood din ya gane.

***
A hankali Munaya ta karasa wajen doctor da sallama ciki ciki, ya kuma ji ya amsa, kana cikin wasa yace "na zata sarautar ce ta motsa bazaki fito ba" bata ce komai ba, duk da ta lura yana daga cikin mutane masu yawan fara'a da wasa.
"Ina yini" tace ba tare da ta bashi amsar waccen maganar da yayi ba.

Bai hakura ba ya sake cewa "lafiya kalau, ai yau sai kin budi baki munyi hira sosai, tunda na ga rowar magana kike min, na gano wayon ki"
Still bata ƙara cewa komai ba, shi ma bai damu ba, domin har yanzu yana mata uzuri, shiru ya ratsa tsakanin su kana ya fara Mata fada mai haɗe da nasiha "ina kara baki hakuri kan abinda ya faru, Allah kuma ya jikan Amnah da Rahama, amma abinda kika aikata Munaya ba karamin laifi bane, kinyi wauta sosai, ki sani cewa shi Allah ke bada lafiya ba Mutum ba, haka zalika mutum bazai iya kara wa bawa lokaci ba, matukar lokacin sa yayi zai mutu ne , what you did was very bad, and i prayed Allah subhana wata ala ya yafe Miki, Bazan boye Miki ba naji haushi sosai kan abinda ya faru, shiyasa kika ga ban dawo ba sai yau, daga yanzu idan zaki yi abu ki nemi shawara ta kinji tunda na dauke ki matsayin kanwata, karki kara gaban kanki kin ji ko?" Ta jinjina kai hawaye na cika idanun ta.

"Good girl" ya fada yana mata murmushi sannan yace "kafin mu yi hirar da nake so ya kamata ki san sunana, tunda bazaki tambaya ba, ni zan fada Miki"
Ya kara motsawa kusa da ita yace "sunana Abbas Muhammad, Ni dan asalin garin Kano ne, nayi karatu a Kano, nayi bautar ƙasa a Katsina, sai dai aiki ya kawo Ni Abuja, ina da kanne biyu mata Amina da Zainab, suna tare da mahaifiyata a Kano, Allah yayi wa mahaifina rasuwa 4years back, wanna shine takaitaccen tarihina"
Munaya jinjina kai kawai take domin babu abinda ke Mata wahala yi kamar magana yanzu, likita bai damu ba, ya mata uzuri mai yawa amma so yake ya zama silar dawowar ta daidai, ko da bai yi nasara duka ba, amma at least ya rage wani abun.

Ya dan kara matsowa kusa da ita, ya rage murya yace "wacece Munaya, Tell me?".



*Ayi hakuri da Page din yau, nayi busy ne*

_Akwai sanarwar da zan yi saboda mutane na ta tambaya ta, na so bari sai na kammala free pages kafin na sanar amma yawan tambayar ya sa na sanar, tambayar da ake min shine "littafin kuɗi ne ko free?” TOH littafin MunayaMaleek paid novel ne, amma muna kan free pages ne har yanzu, thanks for your support, Allah ya ƙara muku budi ya biya bukata_
07082281566


#MunayaMaleek 2023
#NoorEemaan
#Heartouching
#selffishness
[14/12, 12:54 pm] 𝙽𝚘𝚘𝚛𝙸𝚖𝚊𝚗✨: 🍇MunayaMaleek🍓




_by NoorEemaan_📚✍️




All my books are available a waɗandanan platforms din, usernames are:
Wattpad @NoorEemaan
Arewa books:nooreemaan
Please follow me, and also vote my stories, thank you.❤️


ix....
(9)


*Su waye MunayaMaleek?*
*Menene Tarihin Rayuwar MunayaMaleek*?
_Let's find out.!_



_Abuja_
*Unguwar Masaka*

Unguwa ce ghetto, amma akwai manyan gine-gine a cikin ta, a takaice dai unguwar ta hada da talaka da masu hannu da shuni.


Alhaji Dawood Bulama na daya daga cikin masu hannu da shuni a unguwar, domin gidan sa shine gida mafi kyawu da girma a unguwar, yana da arziki domin harkar man fetur yake, wanda ya gaji sana'ar ne a wurin mahaifin sa, yana da gidajen mai guda hudu a yanzu haka mai suna *Dawood and son's Nig LTD* duk da wanna arzikin nasa, wanda zai iya yin, ko siyan gida a unguwar zallar masu kuɗi, amma hakan bai sa ya bar ghetto ba, domin shi Mutum ne mai son zama cikin jama'a sosai, ya kan ce jama'a rahama ne.


Asalin sa ɗan nan garin Abuja ne, wato yan *Gbagyi* wanda Hausawa ke ce masu *Gwari* asalin su a nan Abuja yake, kuma yan Gbagyi ko nace yan Gwari sun fi ko wanne kabila yawa a Abuja domin nan din nan asalin su, kuma tushen su, sai yan kabilar *koro* wanda su ma ba laifi suna da dan yawa, da kuma sauran wasu kabilu. Iyayen sa sun rasu, yana da yayye biyu Laraba da Isma'il inda shine ya kasance Auta.
Sai dai Alhaji Dawood har yanzu bai yi aure ba, dangi kuwa sun gaji da magana sun zuba masa ido, Shi kansa yana son yin aure, amma ya kasance irin namijin da bai san yanda zai tunkari mace da sunan yana so ba, gashi bashi da isasshen lokaci na kansa.


A yau juma'a yake kai ziyara wa yan'uwansa, domin mutum ne mai zumunci, duk da bashi da isasshen lokaci, amma da zarar da samu lokaci komai kankantar sa yana Amfani da ita domin samun lada, gidan yayar sa laraba ya fara zuwa inda take aure a unguwar Gwarinpa, bayan y'a'yan ta sun gama murnar ganin sa, yaya Laraba ta gabatar masa da abin motsa baki yayi godiya, sai ta fara masa zancen dake cin ta cikin Yarensu na Gbagyi "yanzu Dawooda haka zaka cigaba da zama, ba zaka yi aure ba, bar ganin kana da tarin dukiya, ba fata ba, ace a yau ka fadi ka mutum bayan an gama jimamin mutuwar ka Labarin ka zai gushe na har abada, sai dai mu yanuwanka na jiki ne bazamu manta ka ba, amma idan kana da ƴaƴa, a duk lokacin da wani da ya san ka ya ga yaran zai ce Allah Sarki Rayuwa, ga ƴayan Dawooda nan, Allah ya jikan sa, haka zalika y'ay'anka zasu na maka addu'a, amma idan babu y'a'yan fa, saurin mantawa za a yi da kai, shin Kanina bazaka so ƴay'anka su maka addu'ar samun rahamar Ubangiji ba?" Shiru yayi, jikin sa yayi sanyi sosai, tabbas it's about time daya kamata yayi aure, amma wa zai aura? Shi bai taba soyayya ba, ya budi baki zai yi magana, sallamar wata budurwa ya karade kunnuwan su, ba tare da ta jira ba ta dage labulan falon ta shigo, domin gidan ba bakon ta bane, cak ta tsaya, sakamakon kyakkyawan mutumin data gani zaune, saurin juyawa tayi da gudu ta bar falon, domin bata san maman Abdallah (yaya Laraba) ta yi bako ba.


Cikin mamakin abinda budurwar tayi, da kuma dariyar da yaya Laraba ke yi daya kara masa mamaki, hakan yasa ya gyara zaman sa yace
"wacece ita, kuma me yasa ta koma yaya?"


Yaya Laraba ta dakatar da dariyar da take yi, tace "sunan ta Bilikisu, gidan su ne yake kallon namu, marainya ce, mahaifiyar ta ta rasu, kishiyar maman ta ke cigaba da kula da ita da nata y'a'yan, yarinyar kirki ce, su Abdallah ma sun saba da ita sosai, kunyar ka ta ji, bata san kana nan ba da bazata shigo ba, shiyasa kaga ta gudu"


Numfashi ya sauke bayan ya gama sauraran yayar tasa, ya shiga shawara da zuciyar sa, can kuma ya ce " yaya Laraba na baki zabi, ki min Mata"

Yaya Laraba ta washe baki cikin jin dadin tace "Madallah Dawooda, kamar yadda ka bani zabi, bazan baka kunya ba, Zaka yi farin cikin da zabi na, Allah ya tabbatar mana da alkhairi"
" Ameen" ya amsa fuskar sa babu yabo babu fallasa.

***
Bayan sati biyu da maganar su, yaya Laraba ta kira shi ta sanar da shi ta masa mata, yayi godiya, ta sanar da shi yarinyar ma ta amince. "Yaushe zaka je ku gana?"
"Gaskiya yaya Laraba ban da lokaci yanzu, gobe ma zan yi tafiya, na bar muku komai ku neman mun auren ta, tunda ta amince alhamdulillah, duk abinda kuke bukata ki sanar min sai na bayar"

"TOH shikenan zan yi waya da Isma'il din, sai aje nema maka auren ta" da haka suka yi sallama.


Magana kamar wasa sai gashi an saka biki sati Uku, shi wanda za a yi wa bikin, baya dokin da yan'uwansa suke, sosai suke murna Finally Dawood zai yi aure.


*****

*Bayan Aure*

Bayan yan kawo amarya sun watse, Dawood ya zo gidan sa, direct ya shige dakin da yake na amaryar da ledogi a hannunsa. A kallon farko da yayi mata ta, ya tabbatar yarinyar nan ce daya gani a gidan yaya Laraba, bai san meyasa ba, amma sai yayi farin ciki da kasancewar ita ce matar sa.

Kamar yadda yaya Laraba tace tana da kunya, tabbas ya gani fiye da Hakan, bai takura mata ba, ya ajiye mata ledar hannun sa, ya mata sallama ya fice.


******

Tsakanin mata da miji sai Allah, wanna haka yake, a hankali shakuwa ya fara shiga tsakanin su, kana daga baya suka gane cewa ashe sun yi matukar kamuwa da son junan su, tun a ganin farko, a gidan yaya Laraba. Zama mai cike da soyayya da mutunta juna wadannan ma'aurata suke, har suka yi shekara daya cif da aure, a duk lokacin da suke hira ya kan ce " Allah ya bani ɗa ko ƴa mai launin Fatar ki Bilikisu" domin yana matukar son bakar mace, musamman ma na Bilkisu da fatar ta ke sheki, saboda sauyin rayuwa data samu, sai hakan ya taimkawa fatar ta wajen kara kyau, ita kuma tace "in Sha Allah ni fari zan haifa kamar ka, Ni na fi son farin baby" ya kan yi dariya a duk lokacin data ce haka.



*******

Kamar yau suna zaune a yalwattace kuma had'add'en falon su, Bilikisu dake dariya tace "dear ni dana ji sunan gidan man ka Dawood and son's, na zata fa kana da y'a'ya, sai bayan auren mu na gane cewa ashe kawai sawa ka yi"

Shi ma ya saki murmushi yace " haka mutane da dama suke tunani, ina dai fatan na samu yaya maza da zasu gaje ni, kuma bana kin mace ma, Ni duk wanda Allah ya bamu ina so, kuma zan gode masa"


Bilikisu ta ce "TOH idan Allah bai kaddara cewa zaka haifi yaya maza kuma ba fa, ya zaka yi da sunan daka sa a filing stations din ka?"

Yayi shiru na yan mintuna kana yace " TOH sai na mayar da sunan *Dawood and daughter's Nig LTD*"

Suka yi dariya a tare, kasancewar sunan bai yi dadi kamar Dawood and son's ba.


****

Sai da Bilikisu ta shekara uku kafin Allah ya nufe ta da samun ciki, bayan wata tara ta haifi kyakkyawan danta namiji fari tas, sai dai Allah bai bata ikon ganin abinda ta haifa ba, Allah ya dauki ranta a gadon asibitin data haihu.

Mutuwar ta ya taba mutane sosai, musamman Alhaji Dawood, riko hannun ta yayi yana cewa "Billy dan Allah ki tashi, ki tashi ki ga kyautar da Allah ya bamu, addu'ar ki ta karbu, farina ya yo, yama fini fari" sai dai ko motsi Bilikisu bata yi ba, sai ma fuskar ta dake fitar da wani haske sosai, kamar ka kira ta ta amsa.

Fahimtar cewa Dawood ya fita a hayyacin sa, ya sanya Isma'il yayan sa fitar dashi da kyar daga dakin, bayan wasu mintuna aka basu gawar, suka mata wanka a dakin mijin ta, sannan aka sada ta da gidan ta na gaskiya.



******

Sai da jaririn yayi kwana biyar kana Dawood ya samu nutsuwar rada masa suna *ABDUL-MALEEK* kuma ikon Allah yaron yana da matukar hakuri, madaran da ake bashi baya ki, sosae yake sha, hakan ya kara kwantar wa da Dawood hankali, domin har yanzu yana jin kewar Bilikisu, dole yaji kewar ta, domin macece mai kyawun hali, yaya Laraba ce mai kula da Maleek har yayi wata shida, a lokacin ne kuma Dawood ya zo mata da wata magana...


"Kana da hankali kuwa Dawooda? taya zaka ce na baka wanna dan yaron ka nemo masa masu kula shi, ka gane i understand, Na san cewa zaka so kana ganin sa kullum a gidan ka, amma ka bar maganar cewa zaka dauko nany's domin kula dashi, bayan kana da tarin yan'uwa, lallai idan kana son na baka wanna yaron sai dai ka kara wani auren, a hakan ma sai yayi shekara daya ko biyu kafin na baka shi, zuwa lokacin yayi kwari, sannan na Kuma tabbatar matar da zaka aura mai kyawun hali ce" ta karasa da hawaye, domin tana jin ciwon rasa yarinya Kamar bilkisu da suka yi, amma waya isa ya ja da ikon Allah?

Ya rasa mai zai ce mata, kawai yayi mata sallama, bayan ya mika mata Maleek dake hannun sa ya bar gidan, yana son jin dumin dan sa akoda yaushe, amma maganar auren da yaya Laraba tace yayi shine abu na ƙarshe da yake fatan yi, amma kuma rashin yin auren nasa daidai yake da nisanta kan shi da dan sa, ba kuma ya son hakan ta kasance, so yake ya nuna wa Maleek soyayya da kauna irin na uba da uwa, tunda ya rasa uwa.
Bayan tsayin kwanakin daya dauka yana shawara da zuciyar sa ya yanke hukuncin zai yi aure a duk lokacin daya ga yarinyar da ta masa.

******
Maleek na da shekara daya a duniya Allah ya haɗa Alhaji Dawood da Sa'adah, bazawara ce yar garin Katsina, ta kawo wa kawun ta ziyara nan Abuja, ba a dauki lokaci ba suka fahimci juna kasancewar su din duka ba sabbin shiga bane, abin da ya kara kwadaitawa Alhaji Dawood auren shine yanda take tsananin nuna son dan sa Maleek tun ma kafin ta gan shi.

Bayan wani lokaci aka daura auren Alhaji Dawood da Sa'adah, watan ta uku a gidan, aka dawo da Maleek gidan mahaifin sa, inda ita ke ta rokon sa da cewa ya dauko shi, kuma sosai Sa'adah ke kula da shi, hakan ya kara faranta ran Alhaji Dawood, yana mai godiya ga Allah daya bashi mace kamar Sa'adah, domin bayan ya rasa Bilikisu bai yi tunanin zai kara samu mace mai kyan hali haka ba.

Sa'adah na da wata biyar a gidan Alhaji Dawood, Allah ya nufe ta da samun ciki, sosai Alhaji Dawood yayi farin ciki, bayan wata goma cif kafin ta haifi dan ta namiji kyakkyawa, wanda yaron ya dauko launin Fatar ta baki, ranar suna yaro ya ji suna ABDUL-SHAKUR, Maleek kuwa sai murna yake ya yi Kani. Shakur na da shekara daya, hanyar business din Alhaji Dawood ya kara haɓaka, domin har wasu jahohi a nigeria ya bude branches, daga baya ma ya haɗa hannu jari da wani Company da ake yin carpets a kasar Indonesiya, da shekara ta zagayo aka turo masa Ribar da ya samu ba karamin mamaki ya yi ba, bayan wasu watannin ya kara saka hannu jari a wani Company dake America, a haka hanyar samun sa ya dinga habaka, domin cikin shekaru uku yana da hannun jari a kasashen Turai guda biyar, hakan ya sanya zaman sa a Nigeria ya ragu, ya fi mayar da hankalinsa a kasashen ketaren da yake zuwa, Sa'adah ko kadan bata damu ba, tunda yana mugun sakar mata kudi, ga kuma y'a'yan ta a kusa da ita hakan yasa ba ta tare da wani kewan sa.

And that's how it started, Daga nan mafarin komai ya soma, wanda hakan zai tarwatsa zuciyoyi da dama.


*Bayan wani lokaci*

Sa'adah ce kwance daga ita sai ficicin sleeping dress maroon color a jikin ta, tana da kiba wanda ya dace da tsarin jikin ta, baka ce amma ba wuluk ba, wasu yara maza biyu ne ke wasa a gefen ta, farin ya dan fi bakin wayo kasancewar ba shekarun su daya ba. idanun ta da suka kad'a ta zubawa farin yaron nan(Maleek) tana masa wani kallo, a hankali ta mike ta je kofa ta murza key, kana ta dawo ta kwanta Hadi da janyo farin yaron nan zuwa jikin ta, ta fito da maman ta ta sanya masa a baki, yaron kuwa ya kafa baki ya fara sha, tayi wata mika hadi da cije labb'an ta tana shafa kan yaron, bakin yaron nan (Shakur) kuwa cikin tafiyar sa da bata gama Kwari ba ya zo gefen matar ya fito da dayan maman zai sa a baki kasancewar bata yaye shi ba, without even minding ta ture yaron nan, ya koma gefe ya fara kuka, daga baya ma bacci ne ya ɗauke shi.

Sa'adah kuwa bata fasa mika hadi da cije labban'ta ba, sai wani k'ananun sauti take saki, da alama she's enjoying yanda ta saka yaron na mata, kimanin Mintuna talatin sannan farin yaron nan yayi bacci, bata so hakan ba, amma haka ta kwantar da shi a jikin ta, ta ɗauki hannun yaron tana yawo dashi a wasu sassa na jikin ta, idanunta da suka kada ta lumshe. Sai da ta gaji dan kanta sannan tayi bacci tana K'amk'ame da Maleek dan kimanin shekaru uku a duniya...


_4:48pm_

Fitowa Sa'adah tayi daga kitchen din ta, warmers biyu dauke a hannu ta, ta ci gayu cikin tsad'add'en shadda ɗinkin buba tsabanin tun safe da take sanye da sleeping dress, bayan ta gama jera dining table ɗin, ta dawo falo ta zauna, yaran nan kuwa na zaune kasan Centre carpet suna wasa, hannu ta sa ta dauki Maleek ta ɗora a cinyar ta, tana shafa kansa yayinda idanun ta ke kafe a kansa, Shakur kuwa ya cigaba da wasan sa, da alama ya saba da rashin kulawar da Baya samu daga wajen matar data kasance uwar sa.
Horn aka yi a bakin tamfatsetsen gate din, cikin sauri mai gadi ya bude gate din.... Magidancin Mutum ne, dogo mai dan jiki ya fito daga motar sanye da ɗinkin babban riga

1 Comments On MUNAYA MALEEK
avatar
nusaibabello

12 months ago

Reply

Dghhjhujvghkjvg

Please Login or Register in order to submit comment