Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a kuncinta..... Ihu ta dunga zundumawa take gurin ya cika da jama'a labari ya isa kunnen sarki yasa Jakada ya kira masa Omar din don ya tambayi ba'asi.






*Littafinan na kudi ne idan kina bukatar karantawa ki tura #300 ta wannan accont din 0542382124 Binta Umar Gt ban idan kuma katin waya zaki tura sai ki same ni ta wannan numbars 08089965176_07084653262 Sai in fada miki yanda zaki biya kudin karatu bana mallaka ba.*


*Kika futar min da book waje na barki da Allah ya bi min hakkina/Kika karanta baki biya ba kema na barki da Allah!*






12/3/2020



*BINTA UMAR ABBALE*



19



Ganin yanda jini yake zuba bakin aysha yasa sarki ransa ya baci ya kalli Omar dake gurfane a gabansa yace." Haba Omar ka rasa a ina zaka gwada jarumatar taka sai anan duba fa kaga yanda ka fasa mata baki ayshar guda nawa take gaskiya banji dadin wannan abu shin wai ma meye ya hadaku rigima nasan kai ba halinka bane." Shiru yayi ya kasa magana domin dai shi ba zaice ga abunda ya hadasu da ita ba. galadima ya kwatsa masa tsawa rai! a bace yace." Shin wai ba magana ake maka ba kayi shiru ka raina maganar mutane Har idan banda karfin hali da rashin hankali irin naka ina kai ina dukan yar masu gida har da zubar mata da jini ko me tayi maka ai tana da na gaba da ita sai kazo ka same mu kafada mana ba ka yanke hukunci da kanka ba." Sarki baiji dadin irin maganganun da galadiman nayi ba yace."Galadima wannan magana taka bata dace ba ni da Omar da aysha duk daya suke a gurina kuma na kira du ne domin in tambayi ba'asi sannan na yanke musu hkunci bai kamata kayi magana ba."


Galaadima ya sunkuyar da kansa ransa a mutukar bace wulakantaccen yaron kamar wannan nan shine da zubdawa yar sa jini babu shakka dole ya dauki mataki a kansa.


Sarki yace."Omar me aysha tayi maka kayi mata irin wannan dukan harda jini." A hankali yace."Allah ya baka nasara zuwa tayi har inda nake ta zage ni.'' Cike da mamaki! sarki yace." Zagi kamar yaya."!? aysha tayi zurf tace"Wallahi ni ban zage shi ba kawai daga kiransa da bawa shine ya doke ni a baki!

sarki ya bata rai yace." kinyi dai-dai kenan da kika kirashi da wannan kalmar aysha? sunkuyar da kanta tayi gabanta na faduwa tana jin tsoron kar ya dora mata laifi.


ya cigaba da cewa"Nasan dama haka kawai omar bazai doke ki ba dole sai da wani dalilin shin me ya kaiki sashen su ko kin manta da dokat gidanan ne."!? gabanta ne ya fadi sai ta hau inda inda sarki ya gane itace mara gaskiya aikuwa ya shiga yi mata fada da nuna mata muhimancin omar din a masaratuar sannan a take a sannan ya umarce ta da ta bashi hakuri.aysha na kuka ta bashi hakuri tana Allah ya isa cikin zuciyarta.

Sarki ya dawo kan Omar fada yayi masa kan ya daina saurin duka kada ya taso da wannan dabi'a ya nuna masa rauni da baud'ewa irin na mace dole sai ana tausaya musu. Sallamar su yayi bayan ya gargadi aysha kan karta kara yi masa rashin kunya ko ta zage shi to wannan shine musababbin gabarsu da kinn junansu da suke.......Hukumcin da Sarki ya yanke bai masa ba don haka saida ya samu Omar din yayi kasa fatata! tare da gargadi kan duk sanda ya sake dokar masa yarinya to sai ya daureshi." Duk irin cun mutumcin da galadima yayi maasa yasan zai iya domin dama tun bai ka hankalin haka ba ya fahimci cewar mutumin baya kaunarsa,.


Haka rayuwa ta cigaba da tafiya Kulu da mukarrabanta irinsu aysha da sauransu suka cigaba da kuntatawa Omar cikin gidan, Omar kuwa ko kallo basu isheshi ba rayuwarsa yake cijin kwanciyar hankali yana cigaba da kula da Fulani da kula da masarautar gaba gaba daya


*Wannan shine abunda ya faru a shekarun baya zamu cigaba da labari*



Sai da gari yayi haske sannan ya samu damar futowa daga dakin yana futowa yaga idanun jama'a ya koma kansa ya dunga ganin kungiya kungiya mata da maza suna zind'ensa wani irin gumi ya shiga zuba a jikinsa Yunusa ya karaso inda yake fuskarsa da yanayi na damuwa yace."Omar da gaske ne abunda ya faru."!! ? kafin Omar djn yayi magana Tafida ya karaso gurin fuskarsa shima cike damuwa yace."Sadauki! Omar Umarni daga gurin ke martaba yace." Yanzu yanzu ka same su dakin sulhu."!! Omar ya samu ya motsa bakinsa da kyar yace."Tafida kafi kowa sanin halina kafi kowa sanin abunda zan aikta da wanda bazan yi ina fatan dai cewar kuma ba ku gazgazata abunda ake zargina dashi ba." Tafida yace." Haba Omar wallahi bamu yarda ba mun san idan akwai abunda ka tsana a duniya bai wuce zina ba kuma nasan wallahi baza ka aikata wannan aiki da gan-gan ba face cikin 'kaddarar ubangji."!! Omar yace." tabbas shine zai wanke ni daga zargin da ake min."Yunusa yace." insha Allah gaskiya zata futo.


Yunuda ya kore mutanan da suke tsaitsaye suna kallon Omar din wasu na murna wasu na tausaya masa sai bayan wucewar su ne sannan ko wanne ya koma bakin aiki.



"Wallahi tallahi! Mommah babu abunda yayi min kinji na rantse miki zazzabi ne fa ya kamani kuma nasan lokacin da ya shigo dakin har ya bani magani nasha taimakona yayi bai cuce ni."! aysha ce take wannan maganar tana kallon kulu da ta kafe ta da ido wai lallai sai tace Omar yayi mata fyad'e!


Kulu tace" Aysha kina boye min ko ki fito ki fadamin idan yayi miki wani abun a dauki mataki akansa kin tsaya kina tsoro nasan kina jin tsoron ki fada ne don kar a mayar dake dakin dabbobi shine kike kareshi ni nasan wannan munafikin yaron me shegen ido a tsakiyar ka zai aikata abunda muke zarginsa dashi.


Cikin yanayi na bacin rai tace"Wai Mommah! karya zanyi ne nifa nace miki bai min kome ba wallahi taimako na ma yayi don Allah ku daina zarginsa." To me yasa ya cire miki riga."!? kulu tafada tana tsatstareta da ido." Mommah! riga ni na cire kayata saboda maganin da ya bani nasha shine ya saukar min da zazzabin zufa ta rufe ni bashi ne ya tube min kayana ba."

Kulu ta soma matsar hawaye tana fadin"Shikkenan aysha tunda kinki fada min gaskiya ni mai kaunar ki shiyasa bana kaunar shigar ki cikin mugun hali aysha saboda kaunar da nake miki ina so ko da sarki ya tambayeki kan abunda ya faru kice fyade ya shigo yayi miki bayan yw baki maganin bacc."! aysha ta kalleta da sauri kulu ta goge hawayenta ta cigaba da cewa''Nasan ke din me kishina ce bazaki so a na tozarta ba shin wai ko kin mance marin da yayimin d'azu." aysha ta tuno lokacin tace."Mommah! kiyi shuru don Allah na gane abunda kike nufi kuma nima zan iya yina domin in faranta miki Mommah! babu abunda bazan iya yi miki ba. Sabida haka na amince zanyi miki yanda kike so."kulu ta saki dariya cikin ranta take suka cigaba da shirya plan dinsu kafin kiran mai martaba ya riske su.


Cikin wata irin tafiya kamar ta 'yan koyo tana yi tana tale kafafu suka shiga gurin..... Duk suks zuba mata ido har suka karaso Kulu ta kamata a hankali tw zaunar aysha ta ya mutse fuska tana cije bakinta alamun tana jin zafi da kyar ta zaune tana ya mutse fuskarsa ga idonta yayi jazur alamun taci kuka ta koshi Omar bai kawo komai a ransa ba yafi tunanin ko zazzabin da take ne ya kashe mata jiki.



Dakin yayi shiru kowa na sa'ke-sake cikij ransa gyaran muryar maimartaba ne ya sanya kowa ya mai da hanks nsa kansa.


Yace." A tarihin masarautar nan ba'a taba aikata wani mummunan lamari wanda yayi mutukar girgixani irin wannan al'amarin da ya afku ba bani kadai ba ma duk wanda ya kwanabya yini cikin wannsn gida al'amarin ya girgizashi! hakika Omar ka bani kunya ban ta'bs tsammanin afkuwar wannan abu daga 'bangaran ka ba na farko dai kane mai kare min 'kimar masarautata baka yarda da aikata farijinci irin wannan ba duk wanda ke ciki wannan gida ya shaida hakan amma abun mamaki kaine na farko da ka fara aikata 'barna mafi muni da 'kazanta a cikin gidan tabbas dole za ka bar wannan masarauta har abadah sabods zama da irinku cikin al'umma akwai had'ari wannan zai zama izina ga duk wanda yake da irin halayyan ka."!Kulu taji wani irin sanyi dadi na ziyartar zuciyarta babu shakka yau burinta ya cika kan Omar.


Omar ya dago kanda dake kasa kana kallonsa zaka gane yana cikin bakin ciki da taikaci hade da nadama me tsanani yace." Ranka ya dade idan har wannan hukunci da ka yanke a kaina yayi maka dai-dai kuma zai sanya zuciyarka tayi sanyi naji na amince dashi amma ina so in sanar daku cewar Ban aikata abunda kuke zargina dash.......''Karya yake wallahi."!! muryar Aysha ta karade gurin duka hankalinsu ya koma kanta. tana wani irin kuka mara sauti hawaye sai an baliyya yake a fuskarts tace"Ranka ya dade zuwa yayi ya danne ni ya d'ura min wani magani ina kuka ina rokansa yaki ina jin jiri naji ya soma cire min kayan jikina ya hau kaina tunda ga sannan ban sake sanin in da nake ba."!!!! Ta karashe maganar tana rusa ihu!

Omar yayi 'kasa da kansa cike da tsananin mamakin ayshar daga taimako sai sharri ya biyo baya ashe tsananin kiyayar da take masa har ta kai haka lallai ya yarda da ake cewa sharrin wata macen yafi na shaidan!


Waziri yace."aysh daina kuka kinji ko dole ne mu tsaya tsayin daka gurin ganim mun karbar kiki hakkin ki don haka ki share hawayen ki." Duk wanda yake gurin ya tausaya mata saboda kukan da take bana wasu bane kanar gaske dama sun gama shirinsu da kulu babu wata alama da zata nuna ,tsari ne sai dai shi Omar din yasan sharri ne.


Sarki yayi gyaran murya a nutse yace." aysha kin tabbatar Omar ya sanki a matsayin 'ya mace."!? kai ta d'aga alamun ta tabbatar...Omar ya dago kansa ya tsura mata jajayen idonsa na 'yan sakwwani ya mayar da kansa 'kasa yana mamakin yarinyar.


Sarki yace." Aysha Omar na da laifi kema kina da laifi saboda haka akanki zan yanke hukumci wanda babu wanda ya isa ya tayar dashi na farko dai ke yarinya ce mara jin magana mara kunya bakya ganin kowa da mutumci cikin gidanan sau uku dani dake da Omar din muna zama a wannan guri don sasanci ina ganin da baki ruga kim zubar 'kima da mutumcin ki na 'ya mace ba babu wani namijin da zaiyi kokarin shiga gonar ki saboda haka wannan halayen naki sune suka jawo miki koma meye na yanke wannan shine. saboda haka na yanke hukuncin auraar dake ga Omar din domin haka shine yafi cancanta daku gaba daya kuje duk infa zakuje kuyi rayuwarku ku kadai zama ciki mu ya kare za'a daura muku aure rana mai kama da irin ta yau."!!! Wani irin ihu!! ta kurma!! tana sakko a guje taje ta rirrike kafafun sa tana kuka da fad'in"Ranka ya dade kar ayi mun haka kar a hadani da bawa wallahi bana sonsa zai cuce ni Baba galadima bsba Waziri ku shiga maganar nan Wayyo Allah! Mommah! wayyo Allah Nanne! ku taimake ni rayuwata na cikij hadari."!!! Kwanciya tayi a gurin tana birgima da tumami.


Kulu wani irin farin ciki ya sake ziyarta zuciyarta jin hukumcin da sarki ya ysnke kan aysa yayi mutukar faranta ranta burinta aysha ta shiga cikin kunci da jajala zata auri bawan da bai da komai bai da kowa uwa uba bawan da ya kasance makaskanci cikin bayi." Zuciyarta fari kwal amma a zahiri kai kace an aiko mata da mala'ikan mutawa ne yanda tayi kici kici da fuska tana fadin"Ranka shi dade a garfarce ina da magana a gaskiya wannan hukumci da aka yankwa aysha yayi tsauri da yawa ta yaya za'ayi aysha tayi rayuwa da talaka wanda bashi da komai shin ina zasu zauna wace irin rayuwa aysha zata da bawan da bashi da kowa aysa yar gata gaba da bayavke dangi da iyaye ta ko wane bangare wannan hukumci a duba adalaci a cikinsa."

Sarki yace." Kulu magana daya nake kuma bata tashi saboda haka na riga na gama magana." Ya mike tsaye da niyar futa Galadima ya rasa me yake mas dadi cikin ransa tabbaas da badon yana tuna wasiyyar mahaifinsa ba bsbu abunda zai hanashi hana zartuwar wannan hukumci kafij mahaifinsu ya rasu ya fada musu cewar ko wane irin hukumci Sarki Salisu ya yanke su bashi goyon baya hakan zai karawa masarautar kima da daraja." Waziri mikewa yayi yabi bayan sarki domin yasan magana ta kare hukumci ya zartu.


Faisal ne ya rirrike hannun Galadima yana kuka tare da fad'in"Baba galadima kar ayi min haka a duba lamarina ina son aysha tun tana 'yar karama nake da muradin auranta naji na gani zan aurta a haka nine yafi cancanta dans aureta ba wancen mahaukacin ba." Yafada yana nuna Omar.....Shi kuwa Omar kallonsa yake yana mamakin sokwancin sa namiji ya zauna yana kuka kan mace ji yayi kamar ya kangareshi saboda tsabar takaici mikewa yayi ya kama hanya futa yana jin wata irin zufa na keto masa! Galadima ya daka masa tsawa da fadin"Ka bar ganin hukumcin da sarji ya zartar ya tabbata wallahi tallahi na same ka da cutar min da yarinya sai ja dauki mummunan mataki a kanka wawan yaro mujirimi kawai."!!! Omar ya juyo yaja kallon Galadima fuskarsa a kirne!! gyda kansa yayu kawai ya fuce! kulu tace"Dan banza msi suffar askarawa!!! Nanne ta mike ba tare da tacewa kowa komai ba ta kama hanyar futa hukuncin da sarki ya yanke kan ayshar bai dame ta ba saboda ta yarda da yaron tana gani wannan lokacin aysha zata gane ya rayuwa take.

Fulani tana so tayi magana tana tunanij abun fad'a sai kawai ta mike tana fad'in"Allah ya sawakke! Faisal ta kalla ta bata fuskarta tace"Dube ka don Allah ka zauna kana kuka saboda shashanci wai kai yaushe zakayi hankali ne."! Kulu tace"Kinga mari ki kyaleshi ya koka an cuce shi ne duk namijin da ya samu aysha a matsayin matar aure ya dace saboda hakabki kyaleshi yayi kuka ko ya samu sassauci a zuciyarsa."

Fulani wucewa tayi ba tare da ta tanka mata ba wani irin haushin matar take gefe guda kuma tana zargin kanar akwai sanya hannunta a lamarin zata zauna da marmartaba kan maganar tasan sharrin shaidan bau wuce kan kowa ba tunda har annabawa bai bari ba amma kuma a yanda taga Omar din na rantsuwa bai aikata ba tabbas ta yarda dashi saboda tun yana karamin yaro tasan halayen sa da d'abi'unsa da kuma abunda zaiyi da wanda ba zaiyi ba tasan da yayi zai fadi gaskiya kuma ya nemi a fuwa.






An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


3 Comments On SADAUKI OMAR
avatar
auwal-mohammed

1 year ago

Reply

It nice book to read ????

avatar
hafsat-9-3

1 year ago

Reply

Very nice biik

avatar
hafsat-9-3

1 year ago

Reply

Very nice biik

Please Login or Register in order to submit comment