Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kuwa kullum kulu ta kai mata abincin da irin k'aryar da zata yi mata kulu tayi mata nacin taci abinci ko don cikin dake jikinta Fulani tace"Tayi hakuri zata ci ko da anjima ne...
Kulu ta tashi ta tafi tana jiran taji abunda zai faru sai taji shuru babu labari. Sai ya zamana kullum tana tasa Fulani a gaba sai taci abincin tun Fulani na lallab'ata haro ta soma fahimtar wani Abu haka kawai tazo ya turketa lallai sai taci abinci hakan yasa ta rage sakar mata fuska ko ta shigo gaisuwa ce tsakaninsu ita kulun itace mai magana Fulani Maman so take ta bata hakuri yanzu ta soma fahimta itama tabbas Tunda cikinta ya kai wata shiga a jikinta ta soma zargin da akwai sanya hannuta gurin zubewersa
[3/11, 7:41 AM] Bintu: Kulu ganin duk yanda taso cikin ya samu matsala kamar sauran na baya Allah ya karashi sai ta sauya shawara ta daina matsawa Fulani kan lallai sai taci abincinta cigaba da kula da ita tayi da nuna soyayyar ta akan cikin Fulani taji dadin hakan kuma yanzu ta gazgata maganar Jakadiyar ta mai Martaba Sarki Salisu yayi farin cikin ganin wannan cikin ya kai har watannin bakwai ba tare da wata matsala ta afku dashi ba don haka sai ya sanya aramma malam Isa ya fara rubuce mata al'kur'ani mai girma ya sanya a ka cigaba da saukar al'kur'ani kuma duk ranar juma'a bayan an idar da sallahr juma'a haka za'ayi ta sadakar abinci danye da dadaffafe.


Cikin ikon Allah ciki ya shiga watan haihuwar sa kulu ta kara sanya ido akai sai ya zamanto ma bata zama sosai a sasheshen ta kullum tana sashen Fulani a cewar ta yanzu ne lokacin da ya kamata a sanya ido sosai kada nakuda ta kamata bata gurin, ita dai Fulani sai dai ta kalleta kawai tana mamakin halin dan Adam.



*Kasuwar Abubakar Rimi*



Wata mahaukaciya ce kwance karkashin wata tsogowar fada data rufta masu siye da siyarwar gurin duk sun Tara shara kasan gadar amma Wannan mahaukaciya nan take kwana ita da tarkacen kayanta.... Hangota nayi tana murkususu da rike ciki sai da na karasa gurin sosai sannan na fahimci cike ne da ita kuma da alama haihuwa zatayi kasuwar a cike da mutane kowa na harkar gabansa Wannan Mara hankali kuwa sai rintse ido take tana rike cikinta tana sambatu babu Wanda yasan tanayi sai Allah.



****

Da sauri ta isa sashen ta zube gabanta tana fadin"Ranki shi Dade Fulani babu lafiya kuma da alama haihuwa ce."! Kulu ta mike zumbur! Tana fadin"Yanzu fa na Baro sashen banga wata alama ba." Jakadiya tace." Hakane ranki ya Dade kin San kowa da irin nakudarsa wani yana da dauriyar ciwo watak'ila tana jin ciwon daurewa kawai take ."

Kulu tace"To Allah ya raba lafiya amma kar a Sanar da mai Martaba domin kada hankalinsa ya tashi kije ganin shigowa insha Allah zan kira likita wacce take zuwa yi mata awo dama ita zata karbi haihuwar da izinin Allah zata haihu lafiya."


Jakadiya ta amsa da "ameeen" sannan ta mike ta futa, kulu kuwa jiki na rawa ta dauki waya ta fara kiran Habi dake Habi ma'aikaciyar asibiti ce kuma cikin dakin haihuwa take ita ke zuwa har gida tana suna cikin Fulani shine dalilin da yasa tayi ruwa tayi tsaki kan al'amarin tace ko haihuwar ce tazo ita zata karba hakan ya sanya mai Martaba ya aminta da ita bayan haka kuma yana ganin aminiyar kulu ce




"Habi Nakuda fa ta takama mutsiyaciyar matar nan kiyi maza kizo Yanzu -yanzu don Allah." Habi dake tukin mota tace." Ayya gani kan hanyar zuwa gurin aiki amma ki kwantar da hankalin ki yanzu zan zo." Kulu tace." Ina saura ranki bana so ta haihuwa lafiya don Allah kizo ki cika aikinki." Habi tace"Nace fa karki damu ganinan." Kashe wayar tayi ta nufi sashen Fulani hankali a tashe Habi kuwa tana juya kan motar ta ta hango cincirindon mutane bakin gada ta tsayar da motar tana tambayar abunda ke faruwa. Wani me siyar da kayan miya cikin baro yace." Wata mahaukaciya ce zata haihu gatacan karkashin gada anrasa Wanda zai taimaka mata sai dai aukin kallo." Ba tare da bata lokaci ba habi ta bude motar ta fito ganinta sanye da kayan likitoci yasa jama'ar da suka rufu a kan mahaukaciyar suka watse habi ta nufe ta zata kamata wata tsoho tace" Ke kuwa 'yar nan bakya jin tsoro ne mahaukaciya ce kuma ance tana dauke da cutar kanjamau shine kike kokarin kamata."

Habi ta fara share hawaye cikin damuwa tace." Kuji tsoron Allah kuna ganin matar nan cikin wani yanayi na bukatar taimako amma dukanin Ku an rasa Wanda zai taimaka mata ba kwa duba yanayin rayuwarta ne." Wannan matar tace"Ke da yake malamar asibitce sai ki taimake ta dama aikinku ne ana biyanku albashi da hakkinmu saboda haka mu Cikin mu babu me ta'ba domun idan muka dauki kanjamau! Gomnati ba siya mana magani zatayi ba." Habi ta tabbatar da maganar da tsohowar ta fada hakane gomnatin dake ci a wancan lokacin bata tausayin talaka shiyasa garin yake a hargitse kowa abunda ya ga dama shi yake. Habi ta samu wani gardi irin masu son kudin nan ta bashi dubu ashirin ya shigar mata da mahaukaciyar mota....... A maikokon ta wuce a asibiti da ita kai tsaye gidanta ta koma da ita ta bud'e k'afafunta sosai ta sanya mata tablet guda uku ta sanya mata ruwan nakuda harshenta ta daga ta manna mata tablet kafin kace kwabo matar ta fara buge-buge haihuwa tazo ta dunga kurma ihu ita kadai habi na tsaye na kallonta tana ganin kan d'a ya faso ta ta jawo shi da karfi wata irin kara matar ta kurma ta fadi a gurin...... Cikin towel ta nade yaron yana wani irin kuka daga ni bashi da koshin lafiya a sukwane ta shiga motar ta figeta sai gidan sarki to tun kafin ta isa gidan ma yaron ya daina kuka hakan bai dameta ba burinta kawai ta isa domin Kulu ta kirata a waya ya kai sau goma....

Fulani na durkushe kasan kujera yar tsuguno sai nishin wahala take Kulu ta hana kowa shiga dakin da take sai ita Nanne matar Galadima tayi tayi ta barta ta shiga taki Nanne tana ganin me Kulu ta sani ta b'angaran haihuwa da zata hanata shiga itace ya kamata ta shiga tunda dai ita ta haihu amma kulu ta hana Jakadiyar Fulani kamar ta sanya kuka don bakin ciki kofa sarki ya aiko da rubutu kulu tana karba ta shige dakin kai tsaye toilet ta nufa ta zuba rubutun cikin masai ta futo tana muzurai!!! Lokacin Fulani ta kai makura gurin galabaita ita kuwa kulu kaiwa take tana kawowa habi kawai take jira tazo.


To ko da Habi ta shiga sashen sai akayi sa'a Nanne da Jakadiya sun kebe suna tattauna magana kan cewar a Sanar da Sarki halin da ake ciki gwara kawai su je asibiti ko Allah yasa ta haihu a can.


Habi na shiga ta d'ago Fulani da idanunta yake rintse kwantar da ita tayi ta sanya safa tana duba ta haihuwa tazo domin ga kan da nan ya Faso kwaya ta sanya mata a baki lokaci guda ciwo ya karu Fulani ta kasa gane waye yake kanta salati taje tana nishi cikin hukuncin ubangiji d'a ya fad'o.... Idanunta a rufe ruf take hamdala ga ubangiji tana jin duk wani motsi da suke yi Amma ta kasa bude idonta sai ajiyar zuciya take sauke wa

Kulu kuwa fadi take "Alhmdullahi Allah ne abun godiya kai masha Allah Habi me muka samu ne." Habi tace." Ina dubawa ne yanzu na yanke cibiya ai ta haihu lafiya sai godiyar ubangiji. " Fulani ta bude idonta tana kallonsu ta kalli yaron dake hannun Habi tana daure masa cibiya habi tace"Namiji ne Amma kuma abun mamaki! Tunda ya fado baiyi kuka ba irin na jarirai." Kulu ta karbeshi Cikin towel ta futo bakinta har kunne Lokacin ne kuma me Martaba ya shigo nanne da Jakadiya suka mike cike da murna da farin ciki Kulu tace"Alhmdullahi ta haihu mun samu d'a namiji sarki ya karbi yaron bakinsa har kunne bakinsa ya kara kunnensa yana masa salatin Annabi Muhammad gami da Kalmar shahada kulu sai farin ciki take bakinta yaki rufuwa....... Habi CE ta futo tana fad'in ranka shi Dade ya kamata mu wuce asibiti yanzu domin dai yaron bashi da lafiya a gaskiyar magana Alhmdullahi Ita Fulani lafiyar ta lau. amma yaron yana da kyau a duba jikinsa. " Sarki jikinsa yayi sanyi ya dunga duba jikin yaron yana kallon fuskarsa sai ya rasa wace fuska yaron ya dauko cikin dangi yace." Likita aikin ki ne komai don haka na baki suka da nama na aminta dake da kulu don haka Ku shirya zuwa asibitin domun a duba yaron."

Nanne ta nufi sashen ta cikin sauri tana so ta shirya zuwa asibitin Kulu kuwa ta aiki Jakadiya Cikin kasuwa domin hado kayan garwa to To a wannan lokacin ne suka samu duk wata dama suka aiwatar da abunda suka niyyata kan ainihin jaririn da Fulani ta Haifa..... Fulani na futowa daga wanka taga babu kowa a sashen ta zauna gefen gado da kyar a hankali ta dauki yaron ta bude fuskarsa tana dubawa sosai take kallon yaron da yanayin sa kamar ma bashi da rai!! Ta daga rigar dake jikinsa tana kallon harbawar k'irjinsa gabanta ya buga ganin baya nuffashi tattaba jikinsa tayi taji sanyi k'alau!! Kuka ta sanya yanzu ta tabbatar da cewar yaron bashi da rai..... Cikin wannan haki Sarki ya shigo ya same ta hankalinsa a tashe ya karbi yaron yana dubawa Innalillahi wa'ina ilahi raji'un!! Shine abunda ya fada ya zauna kusa da ita hade da rungume gawar yaron a k'irjinsa tace"Ranka ya Dade ya mutu kenan." Yace." Eh Mariya sai hakuri haka Allah yaso." Fulani ta cigaba da share hawaye tana addu'a Cikin zuciyarta cikin Wannan halin kulu ta shigo ta same su ko da taji abunda yake faruwa sai ta kurma! Ihu! Ta fadi a gurin tana timami! Wanda ya sanya Nanne da Jakadiya shigowa dakin hankalinsu a tashe ko da suka ji abunda yake faruwa suma sai jikinsu yayi sanyi suka fara sharar hawaye ita kuwa Habi tana samun nasarar futa da jaririn daga cikin gidan kai tsaye gidanta ta nufa dashi inda ta tadda Wannan mahaukaciyar a sume ta samu ta bata taimako ta dawo nutsuwar. ta babu abunda ta fara nema sai d'anta *Nace Ashe mahaukata ma sun San d'ansu* Habi na ganin tana neme neme tace"Ki kwantar da hankalin ki ga danki kinji kin haihu lafiya, yanzu bari in hada miki ruwan wanka kiyi in baki abincin sai ki shayar da danki nono."


Mahaukaciyar ta karbi yaron tana wata irin Dari harda shashsheka bakinta ta Dora kan fuskarsa tana lasa." ina sonka. "!!! Abunda ya futo daga bakinta kenan." Habi ta mike ta nufi karamin toilet din dake cikin karamin dakin da mahaukaciyar ta haihu ruwa ta hada mata ta dawo tana lallab'ata taje tayi wankan da kyar ta bata yaron ta nufi band'aki tana rangaji, bayan shigarta bandakin Habi ta k'urawa fuskar yaron kallo tana murmushin nasara ta San karshen Wannan yaro bola tunda ya zama Dan mahaukaciya babban abunda ya sanya ta kawo shi gurin matar tana so ta wanke kanta gurin mutanan da su kaga lokacin da ta dauketa a motar ta tasan wasu sun Santa Kuma wasu zasu iya daukar numbar motar ta shiyasa take ganin zata maida matar cikin kasuwar domin jama'a su shaida da hakan



Da kyar ta rarrasheta ta ci abinci sai dariya take tana fadin"Bani d'ana in bashi nono ya sha. " ! Ki bani d'ana in shayar dashi nono."!! Habi tace"Ki gama Cikin abincin tukkuna." Dariya ta sanya ta bubbuga kanta sai ta hau loma Kamar zata had'a da kwanan abincin.
Ta cinye tasha ruwa habi ta bata yaron ta fara bashi nono ya kama yana sha sosai ita kuma sai dariya take taba dukan kansa hade da fadin"Ja'iri ya kama min nono zai shanye hahahahaha!!! Ina sonka."! Habi ta mike tana dariya daki ta shiga ta dauko mata sabbin kaya ta futo ta tadda ita tana cillah yaron sama tana masa rawa da wa'ka sai wata irin dariya take.... Habi ta dinga lallab'ata ta bari ta bata kayanta ta shirya har sabon wando da auduga irin mai kaurin nan. Ta Dora mata kan wandon ta saka ta saka kayan ta yafa mata mayafi sannan suka futo tare yaron na hannun uwarsa ta kanainaye shi



Kai tsaye *Kasuwar Abubakar Rimi* suka nufa Habi da Matar suka futo mutane sukayi caaaa! A Kansu kowa na fadin albarkacin bakinsa kan mahaukaciyar Dama Ashe karya ne bata da kanjamau! Gashi ta haihu lafiya kamar ba ita ba. Sai suka fara le'ken fuskar jaririn ita kuma ta dunga guduwa tana'buya karkashin gadar ta shige tana zazzare ido gami da zabura! Gani take Kamar za'a kwace mata d'anta.


Habi ta isa gurin Wannan matar wacce take hana ta ta'ba mahaukaciyar matar tana siyar da dangin abinci ne irin su kosai da kunu da safe sai shinkafa da wake da rana dasu awara
Habi tace"To gashinan Ku shaida na dawo da Ita inda na dauketa na taimake ta kamar yanda kika fada akinane gashinan ta haihu lafiya ga danta nan saboda haka ni zan tafi." Tafad'a tana Ciro kudi cikin Jakarta matar ta mik'awa tace"Gashi dubu ashirin ne don Allah Ku dunga siya mata abinci tana ci." Matar ta karba sai sanya mata albarka take Habi ta. shiga motar ta ta bar gurin zuciyarta wasai kai tsaye gidan sarki ta nufa.......



K'arfe uku na dare ta mike zumbur tana 'kunduma ashariya shiru garin ba kajin motsin komai sai kukan karnuka da suka yawaita a gurun saboda tsoron dukiyar jama'a


"Eyeeeee! Don durun uwarku! Ni zaku kwacewa jaririna!!!!!! " Ina son sa."!! Babu Wanda zan Bari don kutumar ubanku!!!!! Gilmawar mutum ta gani ta fito daga karkashin gadar tana zare ido!!!! "Kutumar ubanku !! Don bura ubanku."!!!!! Sai ta yanka a guje ta mike titi! Tana falfala Gudu ta dauki hanya ta kankame yaron tana fad'in" Ina sonka!!!! Ubanku yaci uwatar!!! Abunda take fada kenan. Tana gudu sai da tazo dai-dai wata k'atuwar kwata sannan ta fad'i gefenta jiri ya rufe mata ido jini ya tsinke ya dunga zuba kamar an kwance famfo yaron ta rike 'kam! Jikinta na makyarkyata "Ina sonka."!!!! Abunda ta iya fada kenan jikinta ya shika yaron ya su'buce daga hannunta a take ya fad'a 'k'atuwar kwalbatin







11/3/2020


*BINTA UMAR ABBALE*
[3/12, 10:31 PM] Bintu: [3/10, 9:58 AM] Bintu: *SADAUKI!!! OMARđź‘‘*





_*Ki biya ki karanta Cikin kwanciyar hankali ke kuma da kika futar min da book na barki da Allah!."*_


Accont numbar
*0542382124..... Binta Umar GT bank*

My numbars
*08089965176_07084653262*



16


Da karfi Kulu ta fasa wani irin ihu tayi kan Aysha a gigice! Tana fadin"Innalillahi wa'ina ilahi raji'un! Shikkenan ya lalata min yarinya Shikkenan yayi Mata fyad'e wayo! Allah na."! Take gurin ya amsa da sautin murya kasancewar gari yayi shiru saboda dare

Aysha dake mutukar galabaice ihun! Kulu yasa ta mike zaune a furgice tana rarraba ido ganin jikinta babu Riga yasa ta gigice can ta hango rigarta ta hannun Omar take abunda ya faru tsakaninsu ya fado mata taji gabanta yayi mummunan fad'uwa..... Mai Martaba kuwa Omar ya zubawa ido fuskarsa da yanayi na bacin rai yace." Babu shakka Omar kayi min bazata! Ban taba tsammanin haka kake ba sai yau Ashe gaskiya jama'a da duke fadin Dan hakkin da ka raina shike tsone maka ido yanzu na fahimci abunda Kulu take taso na fahimta tuntuni Ashe da can din ba ba laifin Ayshar bane nakane!! Tabbas nayi wauta Dana amunce maka na kuma sanya ka gadinta Ashe kana shigowa kana aikata alfasha Omar ka bani kunya.""!! Wata irin zufa! Ta shiga keto masa daga ko wace kusurwa ta jikinsa bakinsa na rawa ya zube kasan k'afafun sarkin yace"Allah ya gafarta maka wallahi ban aikata abunda kuke zargina dashi Ku yar da dani wallahi ban kusanci Aysha ba babu cuta atsakanina da ita saboda ina daukar ta tamkar kanwata ta jini." Faisal ya dallah masa mari a fusace yace." Raina mana hankali zakayi kome? Ga zahiri nan mun gani da idanmu dan durun uwarka ba rigarta ce a hannunka ba, kana so ka karya ta abunda ka aikata ne anyi walkiya mun ganka shege Dan akuya." Sarki ya d'agawa Faisal hannu a nutse ya kalli Kulu yace." Ki kamo hannunta Ki futo da ita." Juyawa yayi da niyar futa Galadima Waziri suka rufa masa baya sun San tunda ransa ya b'aci sosai dole zai yanke hukunci me tsauri kan Omar din...... Nanne futa tayi tana sharar hawaye har yanzu zuciyarta ta kasa gazgata lamarin itace ta Haifi Aysha a cikinta Duk da ba a hannunta ta girma ba amma tasan yarinyar tana da mugun rawar kai da tsiwa tabbas taura d'aya bata taunuwa dole akwai abunda yake faruwa.


Fulani kuwa Kasa cewa komai tayi ta kalli Omar dake durkushe a gurin kansa a kasa ya rasa me yake masa dadi tace"Jarumi ka kwantar da hankalin ka kaji ki na tabbatar da cewa baza ka aikata wannan aikin ba duk da cewar nasan baka fi karfin shaidan ba amma yanda kake rantsuwa da Allah jikina na bani kana da gaskiya insha Allah Allah zai wanke ka daga zargin da muke maka."


Kulu dake rike da Aysha tace"Ke munafuka ga abu a zahiri amma saboda 'kin gaskiya kice anyi masa sharri kar kiyi tunanin cewar ban San da cewar da hadin bakin ki haka ta kasance ba saboda haka kema ki saurari naki hukuncin gurin mai Martaba.

Fulani tace"Kulu kiji tsoron Allah kiji tsoron ranar da zaki had'u dashi ni bana nufin ki da sharri Amma ke kullum cikin bina da sharri kike wai shin me na tsare miki ne a duniya? Kin tsane ni kin tsani duk Wanda zai ra'be ni Insha Allah duk wani sharrin ki sai ya koma kanki." Tsaki taja tana watsa mata kallon banza tace"an dai ji kunya wallahi kin tsaya kina kare fasiki mazinaci saboda kina kwadayin kema ya kwanta dake ai duk abunda kikeyi a kansa nagane kema so kike ya kwan....... Kafin ta 'karasa Omar ya kifa mata Wani lafiyayyan mari! Wanda yasa taga glimawar taurari! Hannu tasa ta dafe kuncin ta bakinta sai rawa yake...... Yana wani irin tsuma yace." Ki sake cewa tak!! Kiga abunda zanyi miki idan babba bai rike girman sa ba sai yaro ya hau kan girman yayi tumurmusu ke ko kunyar fad'ar wannan maganar bakiji ba ? Ko Aysha da kuke zargina da ita bana fatan haka ta kasance a tsakaninmu da ita ballanta matar Dana dauke ta a matsayin mahaifiya saboda haka Nine Omar duk hukuncin da zakiyi kan na mare ki INA sauraron sa."


Kulu tayi kasa da kanta cikin tsananin kunya gami da tsoro wai yau bawa ne ya daga hannu ya mareta da girman ta da komai girgiza kanta kawai take kafin ta ja hannun Ayshar suka futa daga dakin tana fadin,"Zakaga abunda zai faru da kai."! Omar yace." Sai dai inga alkairi." Fulani ta kalleshi a nutse tace"Omar banji dadin abunda kayi ba da ka sani ka barta da halinta a rayuwa ka aikata alkairi ma ya ka cika ballanta sharri ina me tabbatar maka da cewar da sannu duniya zata koya mata hankali. " Yace. " Mama kiyi hakuri don Allah da abunda ta fada a kanki." Tace"Babu komai Omar in da sabo na saba da halin ta. Yanzu zan koma cikin gida da safe ka shigo zamuyi magana da kai." Yace."Insha Allah Mama." Tare suka fito ya taka mata har kofar sashen ta kafin ya juya can dakin dai ya koma yayi zaune kan buhun abincin dabbobi yana tunani rayuwa.



*TUSHEN LABARI*



Sarki Abdullahi shine Sarki na goma sha uku a cikin masarautar Masarautar kano masarauta ce da ta Dade tana kafa tsofaffin tarihi lokacin da Sarki Abdullahi yake kan kujerar mulki mutane na mutukar jin dadin mulkinsa saboda adalcinsa mutum ne mai mutukar hakuri da kauda kai kan komai yana da Yaya uku kacal a duniya kuma duk maza ne a tarihin masarautar Wanda yake kan kujerar mulki shi ke zabar Wanda zai gajeshi da rai ko babu rai duk cikin 'yayan sa hankalinsa yafi kwanciya da Salisu domin shine ya dauko irin halayen sa na hakuri da kawaici sannan uwa uba ilimin addini Dana shine dalilin da ya sanya yake jan sa jikinsa yana nuna masa dabarun iya jagorancin Al'umma duk da cewa shine Karami Cikin yayansa yana ganin shine zai iya tafiyar al'amuran mulki saboda hakurinsa kasabcewar shi jagorancin Al'umma dole sai an samu mai hakuri, Wannan shine dalilin da ya sanya bayan ran Sarki Abdullahi Salisu ya maye gurbin kujerar mahaifin NASA kafin faruwan hakan an dan yi hatsaniya daga b'angaran gomnan garin a wancan lokacin ya kawo mutumin da yake so ya zauna kan karagar mulki a cewar sa gomnati ce take da hakkin zabar Wanda take so ya zama Sarki da kyar dai da jibin Goshi a kasamu a ka shawo kan gomna mai ci a lokacin ya hak'ura Sarki Salisu ya cigaba da gudanar da mulki Tun ba'aje ko ina ba sai abun ya soma bawa kowa mamaki ciki kuwa harda shi gomna din ganin yanda Sarki Salisu yake gudanan da mulkinsa bisa tsari don har yaso ya zarta mahaifin nasa iya mulki da adalci gurin ganin ya bawa mai Gaskiya gaskiyar sa hakanan ya bawa Mara gaskiya rashinta...... Take Garin Kano ya soma samun nutsuwa kwamciyar hankali mutane masu aikata rashin gaskiya suka rage dalili suna jin tsoron ta kaisu ga tsayawa gaban adalin Sarki!

*Wannan kenan*


Sarki Salisu matayen sa biyu Kulu da Fulani Mariya wacce ta kasance 'Yar Sarkin Zazzau macece mai ilimin addini da hankali da nutsuwa gami da sanin ya kamata, Kulu 'Yar babban Hadimin Sarki Abdullahi ce Wato Sarki me rasuwa kenan mahaifinsu tun kafin ya rasu ya dam'ka amanata hannun Salisu tare da fad'in "Ita ya zaba masa a matsayin matar aure lokacin mahaifinta yayi shekara uku da rasuwa ita kuma tana da shekara goma sha biyar a duniya Sarki Abdullahi yaji dadin zama da mahaifinta ya hidimata masa mutum ne shi Mara son jikinsa kullum cikin kokarin kare kafiyarshi yake data Iyalansa su Kansu sun sannan mahaifin nasu yana kaunar Sarki Hidima wato mahaifin Kulu kenan ciwon ajali ya kamashi dare daya ya fadi ya mutu Sarki! Salisu ya girgiza da mutuwar sa mutuka sai ya cigaba da rike matarshi da yarsa Cikin kulawa...... Dab da zai rasu Allah ya bashi ikon daurewa yaransa aure duka su ukun Cikinsu Salisu ne kawai Ya auri baiwa Amma Waziri da Galadima duk yayan sarakai suka aura

Kwata-kwata Kulu bata kwanta masa a rai ba kawai dai yana zaune da ita ne saboda mahaifinsa ya gama fahimtar halayen ta macace muguwa mai mugun son kanta ga shegen son mulkin tsiya kullum cikin zagin bayin ta take don ma Allah yasa tana masifar tsoron sa shiyasa take rage wani abun shekarunsa uku da aure a lokacin duk matayen 'yan uwansa sun haihu suna shirin kara wata amma daga bangaransa babu labari kulu ko batan wata bata taba yi ba gashi shi mutum ne mai son yara sai ya fara Neman aure take Sarkin Zazzau da ya kasance abokin mahaifinsa ya bashi 'Yarsa Fulani Mari tunda Kulu taji labarin auran tayi mugun tayar da hankalinta a wautar ta tana ganin da ita kadai zai zauna tunda ita din amanar mahaifinsa ce bayan haka kuma taga duka 'yan uwansa basu kara aure ba, 'Kawayenta da ta sake sune suka fara d'ora kan muguwar hanya da bata mugwayen shawarwari sai ta tabbatar ya zauna a fada sannan take fucewa su baxama ita da kawayenta Neman asiri kan kar ayi auran..... Sai da suka je can Wani k'auye dake cikin Zaria wani malamin tsubbu ya tabbatar musu da yiwur auran kuma akwai tarin albarka a ciki akwai zuria da za'a samu kuma ya tabbatar musu da cewar idan ta takura zata iya mutuwa domin ya gango

3 Comments On SADAUKI OMAR
avatar
auwal-mohammed

1 year ago

Reply

It nice book to read ????

avatar
hafsat-9-3

1 year ago

Reply

Very nice biik

avatar
hafsat-9-3

1 year ago

Reply

Very nice biik

Please Login or Register in order to submit comment