Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

masarautar."

Jiki a sanyaye Baiyo tace"Wallahi ina jiye maka ranar tonan asiri zata iya zame kanta ta barka a ciki." Yace." Baiyo wai ko bakin ciki kike min ne."!!! ? Baki ta rike ciki da mamaki tace"Wane irin bakin ciki daga magana zaka fassara ni." Yace." To kinga babu ruwan ki Malama ki tafiyar ki aikin ki." Baiyo ta kama hanya zata wuce ta tsaya tace"Amma dai Tafida ka ci amanar SADAUKI Wallahi."" Tsawa ya buga mata wacce tayi saurin barin gurun. Ya gyara hular kansa yana gyara zama yake fadin"Amanar banza amanar wofi!!! Eh amanar taci uwarta mu ba amanar mu yaci ba wa ya sani ma ko asirce sarkin yayi shiyasa baya ganin laifinsa to na tabbata wannan karon kashinsa ya bushe domin wannan tuggun da muka shirya ba me sauki bane....... Mai dakin kusurwa ta futo hannunta rike da wata bak'ar Leda Tafida yayi kasa da kansa harda dunkule hannu alamun girmama wa yace." Barka da futowa Uwar gida sarautar mata." Ledar hannunta ta mik'a masa tace"Karbi wannan shine tukucinka kuma daga yau na 'yan taka daga bauta zaka dawo sashena gaba daya zan sanya a dinka maka manya riguna zaka zama mai kula da shige da fucen b'angare na." Tafida yaji kamar ya zuba ruwa a kasa ya sha don dadi godiya kawai yake yau ya 'yantu ya daina bauta sai ta guri daya lallai yau babbar rana ce a gareshi

Ledar ya buda ya zaro ido ganin kudi dauri uku yace." Ranki shi Dade wannan duka ni kadai." ? Tace" Tafida kafi karfin haka a gurina kai dai kawai kaje." Tafida ya mike sai faman zabga godiya yake Kamar zai ari baki

Murmushi take tana jijjiga kafa tabbas yau hakarta zata cimma a ruwa a gidan ko wace 'yar iska zata daina hura mata hanci kan rashin haihuwa yau zata maida martanin abunda ya Dade yana damunta cikin zuciyarta burinta ya cika kan Abbas da Faisal Karima dama Aysha din ta kafawa arwa yau itama alkadarinta ya karye zaman jiran shigowar Sarki take tasan yana Dab da shigowa domin d'aura alwalar sallahr La'asar.....


Aysha kam Can b'angaran Galadima ta nufa Wanda ta dauki kusan wata guda rabonta da sashen ko gaisu bata zuwa sai taga Dama duk da sun kasance sune ginshikin Samar da ita cikin duniyar......... Nanne na zaune kasan kafet gabanta da wani faranti na silver mai dai-dai ci kayan marmari ne a ciki Jakadiyar ta na zaune kusa da ita tana 'bare mata lemon zaki tana karba tana sha suna hira a nutse kallo guda kayiwa matar zakaji ta shiga cikin ranka saboda kyawunta da kyawun halinta kana ganinta kaga shuwa fara tas da ita me dogon hanci da manya idanu masu kyau sumar kanta kuwa har baya take bata da tsayi sosai kamar su daya da Aysha mutuka..... Ta shigo cikin sallama ciki-ciki Jakadiya ce kawai ta amsa Mata tana mik'a gaisuwar ta, Aysha ta cire ta kalminta gefe ta karaso Wanda tun kan ta zauna Nannen ta fahimci tana cikin halin damuwa saboda yanda taga yanayin fuskarta babu walwala.... Nanne mun wuni lafiya."!? "Aysha sai yau kika tuna damu.? Ko da yake dai tunda kika shigo na fahimci kina tartare da damuwa dama bakya tashi zuwa gurina sai ta ciyo ki shin ina kika bar Mommah din taki." ?.

Murya na Dan rawa tace" Nanne ki gafarce ni kinji kullum kina raina wallahi wani lokacin kawai sai inji na manta ma dake a cikin gidan." Cike da mamaki take kallonta idan da sabo ta saba da halin Ayshar ta cigaba da shan lemon ta ba tare da ta tanka mata ba, Aysha ta fuskanci maganarta ta bata mata rai! Tace"Nanne Afuwa kinji ki gafarce ni don Allah. "

"A'a!!! Ni me kikayi min Aysha Allah ya gafarta mana gaba daya." Aysha tasan halin saukin kan Nanne sai ta rungumeta tana dariya duk da b'acin ran da take ciki taji dadi yau da ganin Nannen ta ta mi'ke ta shiga wani bedroom Wanda ya kasance mallakinta...... Kai tsaye toilet tana nufa ta fara tube kayan jikinta ruwa ta hada na wanka ta tsaya gaban mirror kirar jikinta take kallon take taji tsigar jikinta ta wani irin mik'ewa ta fara jin sha'awa na taso mata lumshe idonta tayi da ta tono rungumar da yayi Mata dazu"Wayo Allah."!!! Ta bude idonta da sauri tana bin toilet din da kallo gani take Kamar zata ganshi a jiyar zuciya take saukewa ta tsuguna tana takure jikinta tsigar jikinta ta fara mik'ewa tana jin wani irin sanyi na ratsa fatar jikinta Wanda yayi dai-dai da jin yanda kan nonowanta suke kauri suna mata kyaikyayi ta lumshe idonta tana cije bakinta ruwa tasa ta fara dauraye gabanta taji wani yauki ya'uki da sauri tw dauke hannunta daga gurin abunda take ji yau a jikinta bata taba jin irinsa ba tunda uwarta ta kawo ta duniya.







7/3/2020



*BINTA UMAR ABBALE*
[3/12, 10:31 PM] Bintu: *SADAUKI!!🏹*
_OMAR💫👑_




*_Ga masu bukatar karanta littafin zasu tura #300 ta Wannan accont din......0542382124... Binta Umar GT bank.... Idan kuma katin waya zaka tura sai ka same ni ta wannan numbars, 08089965176 _07084653262 Zan Sanar da kai yanda zaka biya kudin..... Mutanan Nijar idan suna bukata zasu tura dala dari ta wannan numbars 90899076_88137740 Katin airtal ko orange dala Dari itace a madadin Dari uku kudin Najeria._*



Free pege
8



Tana kuka take kutsa kanta cikin mutane sai rarraba ido take wani dattijo yazo ya rike hannunta jikinsa a sanyaye tabbas ya ga lokacin da suka shigo massalacin tare ya gane shi take nema tace"Baba na nake nema Makaho ne nice yar jagoran shi." Mutumin yaji tausayin ta ya kamashi ya rasa abunda zaice mata fad'ar mutuwa ko ga babba tashin hankali ce ballanta ga yaro Mara manta Abu yasan har duniya ta nade yarinyar baza ta taba mancewa dashi ba.

Tsira masa ido tayi jikinta ya soma yin sanyi tace"Baba naji wasu mutane na fadin Abdu Makaho ya mutu kafad'a min gaskiya baba."!!! Da kuka ta karasa maganar aikuwa kafin kice kwabo jama'a sun kewaye su Malam Ayuba Wanda ya kasance makocin su ya kutso gurin yana kokarin rike hannunta ta kalleshi ta fashe da kuka tana fad'in. " Malam Wai da gaske babana ya mutu."!? Kafin malam Ayuban yace wani Abu jama'ar gurin sun kaure da surutu kowa na fadin albarka cin bakinsa "Allah sarki! Yarsa ce wannan? Eh itace take masa jagora! Ayya! Ai gaban idona suka shigo massalacin kai Allah ya jikan wannan bawan Allah."!! Wannan zan tukan da suke ne yasa ta tabbatar da mutuwar yanke jiki tayi ta fadi a gurin........ Tashin hankali labarin faruwan hakan har ta isa kunnen mai Martaba ya umarci Omar yaje ya dauko ta Omar na zuwa gurin jama'a suka dare masa ya sunkuya ya dauke ta irin daukar da akewa jarirai ya nufi ciki da ita.

Jama'a sukayi dafifi a harabar massalacin suna jiran a futo da gawar domun su sallace ta.

Mai Martaba ya bashi umarnin kaita sashen Fulani Mariya matar shi ta biyu kenan wacce ta kasance Uwar 'yayan shi Yana tafiya yana kallon fuskar yarinyar wani irin tausayin ta na shigar sa tabbas dole yarinyar taji mutuwar a jikinta irin wannan mutuwar ta fuji'an ta kan Dade a zuciyar mutum ba tare da ya manta ba.

Fulani Mariya na zaune tare da bayinta suna jajanta al'amarin domin suma tuni labari ya iske su. Omar ya nemi iso mai tsaron kofar ya shiga dashi ganin shi dauke da yarinya yayi mutukar daga mata hankali tace." Lafiya dai Jarumi! Me ya faru."? Dake haka take kiransa da Jarumi. Ya nemi doguwar kujera ya kwantar da ita kamar matacciya ya dawo kansa a kasa ya gaishe ta yana mata bayanin abunda ya faru.... Fulani Mariya ta mike da sauri ta karasa inda Safara'u ke kwance tana tattaba jikinta Jakadiya dauko ruwa me sanyi a friji yarinyar nan ta suma." Jakadiya ta mike da sauri! Omar kasa futa yayi sai da yaga Farfadowar ta sannan ya juya ya futa cike da tausayin ta Omar mutum ne shi mai mutukar tausayin marayu da marasa galihu guragu da makafi yakan SADAUKAR da komai nasa a Kansu.


Omar shine kan gaba gurin shirya gawar Malam Makaho aka nufi gidansa na gaskiya dashi bayan dawowar su ne sarki ya Tara jama'a yana tambayar Wanda ya San asalin mamacin aka rasa Wanda ya sani sai mutum daya ne yace" Yasan garinsu Malam Ayuba ya cigaba da cewa"Shekaran Malam Abudu ashirin da biyu a garinan asalinsa Dan Garin kumurya ne duk dañginsa na can tare suka zo da matarsa a wancan lokacin dake ita mai gani ce itake masa jagora Da suna kwana ne cikin tashar tsohuwar kasuwar rimi cikin wata rumfar kwano daga baya Marigayi Alhaji Inuwa mai sabulu ya basu gurin zama cikin unguwar alfindiki muje shaida a wancan lokacin na mallaka masa gida mai daki biyu da shago a waje Malam Abdu ya cigaba da futa bara tare da matarsa Abu wacce take masa jagora shekaransu Tara da aure suka haifi wannan yarinya Safara'u tunda da kanta basu sake haihuwa ba, Abu itace karfin daukar nauyin gidan surfe wankau dakau! Duk itace Safara'u na da shekara goma cutar ajali ta kamata dare daya ta mutu sakamakon zazzab'i mai zafi to tunda ga sannan duk wani nauyin kula da Malam Makaho ya dawo hannun Safara'u dake yarinyar taba da fahimta da wayo duk ta dauke lalurar mahaifinta mu da muke makota muna taimaka wa da Dan abunda Allah ya yassare mana amma tunda muke dasu bamu taba ganin wani nasu yazo in da suke ba hakanan bamu taba ganin ranar da suka shirya cewar zasu je ziyara garinsu ba haka suke rayuwa su kadai har kawowa wannan lokacin... Ranka shi Dade wannan shine abunda na sani dangane da marigayi Malam Abdu

Duk Wanda yake gurin sai da labarin ya ta'ba zuciyarsa mai Martaba yaji wani irin tausayin yarinyar ya sake kamashi dama inda sabo ya saba rike yara irinta har ya aurar dasu ga mijin da ya dace yace." Insha Allah Wannan yarinya baza tayi maraici ba ga dukanin alamu na lura yarinyar ta shaku da mahaifinta Dole sai an kula da ita da taimako domin ta samu dangana.

Allarama Nuhu ya kalla yace."Allarama daga yau za'a fara mata taimako da addu'a idan da hali a hada mata da rubutu ko zuciyarta ta samu dangana." Arrama yace." Insha Allah ranka shi Dade za'a taimaka. " ya Kalli Omar da kansa yake 'kasa yace."Duk da dai nasan kai din ba mutum ne me fara'a ba amma ina so in sanya ka wani aiki."! Omar yace." Ranka ya Dade komai ka umarce ni a shirye nake da na aikata mutukar bai sa'bawa shari'a ba." Sarki yayi murmushi yana fadin"To masha Allah Omar ina so ka ja yarinyar nan a jikin ka sosai ka kula da ita kar ka bari tayi kuka ka na lura kana da tausayi da imani ina so ka sanya ido K'warai a kanta ka gane damuwar ta da walwalar ta wannan amanace na baka."

Omar yace." Insha Allah na dauki wannan alk'awarin ranka ya Dade." Fada ta amsa da fadin"Sarki yana godiya Jarumin Namiji."!!!!!!!


To b'angaran Fulani Mariya Al'amarin dai babu dadi don Safara'u ta haukace musu sai ihu! Take tana buge-buge ita lallai sai an kaita gurin babanta duk ta futa daga hayyacin ta tausayin ta yasa Fulani Zubar da hawaye tayi alk'awarin rike yarinyar har abadah saboda yanda take jin wani irin tausayin ta.....Da kyar ta rarrasheta tayi shiru Fulani Mariya ta cigaba da kawo mata misalai na mutuwa da cewar komai daran dadewa inda Mahainta nata ya tafi kowa zai tafi babu Wanda zai zauna jiran duniya dake tana zuwa isilamiyya sai ta dunga tunano wa'azin da malaminsu ke musu kan mutuwa dadin da taji ma da Fulanin tace mata mahaifinta Dan aljanna ne ya mutu ranar juma'a kuma cikin massalaci shine dalilin da ya sanya ta kwantar da hankalin ta.


Yau kwana bakwai da mutuwar Makaho Safara'u ta warware sosai ta sake kullum tana gefen Fulani suna hira har wata kiba tayi kadan farar fatar ta ta sake murjewa Omar kuwa kusan kullum sai ya shigo sashen duk domin ya duba amanar shi Fulani tayi ta mamaki har wataran ta tambaye shi dalilin shigowar sa nan yake fada mata dalili murmushi kawai tayi tana mamakin hallayar yaron yana da rike alk'awari tun yana yaro haka yake bashi da munafurci da cin amana komai idan zaiyi gaskiya da gaskiya yake.




6/3/2020


*BINTA UMAR ABBALE*
[3/12, 10:31 PM] Bintu: *SADAUKI!!🏹*
_OMAR💫👑_




*_Ga masu bukatar karanta littafin zasu tura #300 ta Wannan accont din......0542382124... Binta Umar GT bank.... Idan kuma katin waya zaka tura sai ka same ni ta wannan numbars, 08089965176 _07084653262 Zan Sanar da kai yanda zaka biya kudin..... Mutanan Nijar idan suna bukata zasu tura dala dari ta wannan numbars 90899076_88137740 Katin airtal ko orange dala Dari itace a madadin Dari uku kudin Najeria._*




Free pege

9

Duk abunda yake faruwa tana da labarinsa kuma tana da labarin yanda yake karakaina sashen Fulani Mariya Duk kan *Yar Makaho* sunan da take kiran yarinyar dashi kenan tana jin wani bala'in kishin abunda yake kanta..... Yau dai ta shirya zuwa ganin yarinyar domin taga wace irin kala ce duk da tana da labarin cewar Sarki ne ya damka amanarta a hannunsa hankalinta bai kwanta ba da yanda taji labarin na shiga kula da yarinyar... Ita kanta tunani take menene dalilin da zai sa ta tayar da hankalinta kan mutumin da ta tsana kaf a rayuwarta duk wata dubara da basirar ta kare gurin ganin ta dauki fansa kan a abunda yayi mata, yau kwana goma sha biyu kenan rabon suyi gaba da gaba dashi tayi alk'awarin duk sanda suka sake had'uwa dashi sai ta nuna masa cewar takalminta ma yafi shi daraja. *Aysha kenan sarkin jiji da kai da isa!*


Riga da wando ne a jikinta Wanda suka bala'in matseta! Ta Dora alkyabba mai hula gaban alkyabar igiyoyi biyu ne kacal sune suka Dan ruke jikinta amma duk sanda tayi kwakkwaran motsi sai ka hango matsatstsun kayan jikinta. Takalmi plate ta sanya k'afafunta suka futa tare da bayin ta wata irin tafiya take a hankali Kamar ba taso take taka kasa Ikilima na bayanta tana Dan tartare mata alkyabar saboda Jan k'asar da take...... Suna daf da shiga sashen ne suka futo shine a gana Safara'u a bayan shi tana sanye da wata bak'ar abaya mai jajayen stones da mayafin ta, abunka da dunguwa ga farar fata sai ta zama kamar balarabiya dariya take tana kokarin rike hannunsa....... Yayi saurin kaucewa ganin Ayshar fuska ya 'bata duk wannan annurin dake fuskarsa ya dauke dif!!!! Hannun Safara'un ya rike da gayya suka ratse ta suka wuce..... Aysha taji kamar ta d'ora a hannu aka tayi ta kurma ihu saboda tsabar bakin ciki da takaici kwallah ta taru a kwarmin idonta cikin ranta take fad'in "Wai me wannan mutumin ke nufi dani ne? Yana so ya zubar min da kimata a idon mutane wato har ya bawa yarinyar dama akan kowa kamar ita! Tana a matsayin yar Galadiman Sarki wata kucaka yar Makaho ta ratseta ta wuce babu shakka sai ta dauki kwakkwaran mataki akan yarinyar..... Juyawa tayi har tana take alkyabar daga baya Ikilima tayi saurin gyara mata suka fara tafiya..... Sai da suka danyi nisa da tafiya ne ta bude baki da kyar tace" Ikilima Ina suka nufa banzan mutumin nan Mara galihu!! Atika tace kamar Lamun bayan gida naga sun nufa.". Girgiza kai tayi kurrum suka cigaba da tafiya tana sak'e-sak'e abunda zatayi ma Safara'u ta huce Ashe kishin da jin haushin ba ita kadai take ba Atika har tafi ta shiga damuwa ganin wai yau SADAUKI ne ke murmushi k'aramar yarinya har tana ganin hakoransa kana kuma har. Yana rike mata hannu. Tabbas al'amarin akwai daure kai SADAUKI da kallon mace ma bai dame shi ba ballanta har ya taba mace Itama ta soma zargin ko son yarinyar yake.

Tana zaune saman wani dutse shi kuma yana tsaye a kanta ya Dora k'afarsa daya saman dutsen fuskarsa dauke da wani murmushi Wanda yayi masa bala'in kyau yana magana yana kallon fuskar yarinyar ita kuma sai kyalkyala masa dariya take fararan hakoranta sai shek'i suke abunda yake mutukar daukar hankalinsa da yarinyar kenan yana so yaga tana dariya..... Aysha tunda daga nesa take hango abunda yake faruwa 'Kafarshi ta tsurawa ido daga can nesa har suka karaso gurin wani irin kwantaccen bakin gashi ne kwance saman fatar shi tsigar jikinta ta fara mik'ewa tana jin shigar wani yanayi a tare da ita tunda take dashi bata ta'ba ganin kafafunsa ba sai yau kullum cikin bakaken kaya yake da takalma masu igiyoyo yau ya nan nade k'afafun wandon shi kuma ya cire takalmin shi wannan dalilin ne yasa kafafunsa bayyana a zahira ba karamin burgeta sukayi ba tamakar baya taka kasa dasu tas-tas gwanin ban sha'awa babban abunda ya ja hankalinta wannan gargasar ta jikinsa har suka karasa gurin tsigar jikinta na mik'ewa jikinta na rawa ta jawo Safara'un wacce suka shagala da kallon juna har shi kanshi ta dauke masa hankali bai ga zuwan su gurin ba.


Wani lafiyayyar mari ta kwad'a mata! Tana hura hanci Wanda wani irin gumi yake tsatstsafowa daga saman su. Kafafunsa ya sauke 'kasa yayi mugun shan kunu!!! Yana kallonta yace."Sake ta ko kuma yanzu ranki ya b'aci."!!!

''Anki sakin ta din."!! Ta fada idanunta tsaye a kansa kallonta yake yana ya mutse fuska yace." Kin San karon mu dake babu kyau ko."!!!! ? Tana numfarfashi tace"Kayi min abunda zakayi wallahi bazan sake ta ba sai ka fad'a mata matsayina a cikin gidanan."! Yace." Wane irin matsayi ne dake? Ke baki da bakin da zaki fada mata sai ni."!! Hannu ta sake dagawa zata mare ta ya rike hannun yana murdewa! Ta cije bakinta cikin jin azabah tace"Sakar min hannu kar ka karya ni."! Hannun ya yarfar yana hararata! Safara'u na kuka taje ta. Rike shi ya rungumeta gefen jikinsa. Ji tayi kamar ta rusa kuka tace"Aikin banza kawai mu kar azo ayi mana abun kunya a gida."! Shiru yayi mata kawai..... Ta kalli Safara'u da jan ido tace"Ke ki shiga hankalin ki dani wallahi tallahi duk sanda kika sake nazo wuce wa kika ratse min baki bari na wuce ba wallahi ranar sai na yi miki izayar da sai kin gwammace zuwan ki duniya Banza yar gidan Makaho kawai."!!

Zumb'ura baki tayi tana kunkuni "Ba dai Ubana ba kuma ba don Allah baya sonsa yayo shi a Makaho ba duk Wanda ya zagin iyayen wani nasa ya zaga."!!!! Ba karamin burgishi yarinyar tayi ba. A iya zaman da yayi da ita ya lura itama akwai tsayayya da kishin iyaye Yana mutukar son jarumar mace. Yasan ta ko wanne fanni zatayi jarumta.

Aysha tace" Ni kike zagi ko? Saboda kin samu daurin gindi a gurin bawa makaskanci to wannan da kika laru dashi ba kowa bane a cikin gidanan face bawa Mara galihu. "!! Cikin fushi take maganar k'irjinta sai wani irin zafi yake tana ganin kamar ma da hadin bakinsa yarinyar take kokarin zaginta..... Safara'u ta bude baki zatayi magana yace."Kiyi shiru ki rabu da ita tunda dai ke kin San darajar iyayen ki har kika rabu dasu lafiya sai ki k'yaleta taje tayi tai tayi ita."!!! Wannan lamarin yayi mugun bata haushi tace" yanzu ta tabbata kenan kai ke nuna mata cewar ni din ba kowa bace kana nuna mata dauke ni Kamar kai bawa da sauran bayin dake masarautar to ka rubuta ka aje wallahi sai nayi mata illah cikin rayuwarta mutukar baza tayi biyayya kamar yanda sauran bayin ke yi ba."!!!

"Aysha."!!! Ya fada cikin wani irin voice sai da taji Wani iri a jikinta ta kalleshi da idanunta da suka rine da b'acin rai.

Cigaba da magana yayi a nutse " Wai meye damuwar ki dani ne? Shiru tayi yace." Inace ko sati biyu ba'ayi ba Sarki ya raba ni dake anyi haka ko ba'ayi ba."!? Shiru tayi yace." Ko kuma tun ta sowarki kinga ina shiga sabgar ki! Babu dalilin da zai sanya ki matsa min tunda dai a gabanki Sarki ya tabbarwa da kowa ni din ya 'yan ta ni ba wai ina jin ciwon kira na da sunan bawa da kike yi ba idan zaki shekara kirana kirana da bawa bai dame ni ba tun dai nasan ke din ma itace, Yanzu kuma kawai daga ganin yarinya kin Dora mata kadan tsana saboda wani bazan dalilin ki, ni ban taba ganin mai son mulki da sarauta ba irinki kuma bari ki ji in fada miki wani Abu duk wannan abun da kike basa miki kyau gwara ma ki daina kije ki dauki Nasihar da maimartaba yayi miki hakika mai irin sunan ki bata da wannan mugun halin naki..""! Gurin yayi shiru dama su Ikilima na can bakin kofar shigowa a tsaye Sam ma basa jin abunda yake faruwa saboda akwai tazara me tsayi a tsakaninsu Ya cigaba da cewa"Daga k'arshe kuma nake so in kara tunasar dake cewar wannan yarinyar dake gabanki marainiya ce gaba da bayanta ya kamata ki tausaya mata ba ki cizgunawa rayuwarta ba, Zaki iya yi mun komai na hak'ura amma bazan iya hak'ura in zuba miki ido kina zalintar amanata ba."!!!
Ya k'arashe maganar cikin dakiya da jajurcewa!


Idonta har wani yaji-yaji yake saboda b'acin rai! Ta dago taba kallonsa na yan sakwanni kafin Tace." Wannan Umarni ne ko kuma gargadi da Jan kunne kake yi min."?


Shiru yayi mata kawai ta kalleshi sosai har yanzu yana rike da yarinyar jikinsa tace"Idan Umarni kake bani to ina so in Sanar da kai cewar baka isa ba baka kai Wannan matsayin ba, idan kuma shawara kake bani nan ma ina so ka sani cewar Kayi a banza da kai da ita bakwa gabana da har kake ikararin da cewar sarki ya rabu ina so ka fada min tun ranar na sake kula ka ko na sake shiga hurumin ka, Karewar runguma da kake mata ka hawo kanta a gurin nan shine zai nuna min da cewar kai din namiji ne jarumi kamar yanda wasu suk.......... Wani bahagon mari ya k'wada mata yana huci! Yace." Wai ke jahilar ina ce ne."!? Tuni Safara'u ta soma kuka tana Jan hannunsa su bar gurin....... A haukace! Tayi kansa ta kamashi da kokawa tana wani irin kuka da fadin"Sai kayi nadamar marina da Kayi Allah ya isana." Dukansa take ta koina tana fadin"Gakanan babban jahili ki dahumi! Mara iyaye!!!!!!! Omar gabansa ya dinga fad'uwa yana jin yanda take dakumar sa kamar ma da gayya take gogo masa k'irjinta a jikinsa tunda tun da farkon rungumat alkyabar ta fadi kasa kamar mahaukaciya ta zama tabi ta d'afe masa jiki tana duka had'e da ya kushi yar da cizo sai zaginsa take......"Wannan wace irin masifa CE!??Abunda yake fada kenan cikin zuciyarsa yarinyar tana nema ta zame masa jaraba kokarin funcike ta yake daga jikinsa abun yaci tura, haukata take masa sai kace me iskoki Safara'u tazo tana Jan hannunsa Nan Ayshar ta samu damar bata kyakykyawan Mari a kuncin ta! A gigice ta bar gurin hannunta dafe da kuncinta..... Ganin masifar tayi yawa ne yasa ya rungumeta kam-kam a jikinsa yana jin yanda zuciyarta ke bugawa fat-fat-fat!!! Kan dutsen ya nufa da ita a jikinsa ya zauna a hankali yake shafa sumar kanta yana mata magana k'asa-k'asa cikin kunnen ta..









6/3/2020


*BINTA UMAR ABBALE*
[3/12, 10:31 PM] Bintu: *SADAUKI!!🏹*
_OMAR💫👑_




_*Ga masu bukatar karanta littafin zasu tura #300 ta wannan accont din.....0542382124 Binta Umar GT bank.... Idan kuma katin waya zaka tura sai ka tuntu'be ni ta wannan numbars .....08089967176.....07084653262 Insha Allah zan fada maka yanda zaka biya kudin... Mutanan Nijar Idan kuna bukata zaku tura dala Dari ta wannan numbars....90899076 _88137740 Katin Airtal ko Orange Dala Dari itace a madadin Dari uku kudin Najeria.*_



Free pege
11



A takure ta dauraye gurin tanayi Kamar bata son ta'bawa ta mike jikinta duk babu kwari ta fara wanka har yanzu tana jin yanda nipples dinta ke mata kyaikyayi daurewa kawai take tayo wankan ta futo jikinta daure da towel ba tare da

3 Comments On SADAUKI OMAR
avatar
auwal-mohammed

1 year ago

Reply

It nice book to read ????

avatar
hafsat-9-3

1 year ago

Reply

Very nice biik

avatar
hafsat-9-3

1 year ago

Reply

Very nice biik

Please Login or Register in order to submit comment