Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Bata gama tantance ya yanayin dakin yake ba duhu ya mamaye shi da sauri ta juyo tana dukan kofar dakin tana kukan bakin ciki wai Yau itace cikin dakin Hatsi kan laifin da ta aikata shi ba tare da wata manufa... Shi kanshi bai so wannan hukuncin ba saboda ya San dakin yana da hadari sosai idan bashi ba ba kowa ne yake iya shiga dakin ba domin akwai manya manya-manyan kwarika ciki macizai yasha kashe su ya futo dasu kuma duk duban da za'ayi wa dakin akan rasa daga wane rami suke futowa shi kansa yasan akwai tsofaffun gadangaru a cikin dakin Yasan kuma babu abunda Ta tsana irin kadangare, Har ya bar gurun yana tunanin yanda zata iya zama a dakin ita daya har tsawon kwana bakwai.


*****
Daf da zai shiga sashen nasu Tafida ya futo kana ganinsa kasan yana cikin farin ciki da annushuwa amma yana hango Omar sai ya sauya yanayin sa daga farin ciki zuwa bakin ciki Omar na karaso wa ya fara yi masa kirarin da ya saba yi masa Omar har da durkushewa saboda tsabar makirci!

Omar yace." Tafida kasan abunda yake faruwa kuwa."! Cikin alhini yace." Naji labari gurin Yunusa take kuma na 'karya ta faruwan hakan nasan sharri ne aka shirya maka don ganin an hadaka da Sarki!! Murmushi me ciwo Omar yayi yace." To waye ya shirya sharrin sai ya koma kansa da yardar Allah kuma naga amfanin gaskiya da dogwaro da Allah an so a hadani da me Martaba Allah bai nufa ba inanan kamar yanda nake a gurinsa sai ma wani kusanci ya kara shiga a tsakanin mu ta dalilin wannan Abu." Tafida yaji kamar ya shake shi don bakin ciki yaso Sarki ya Kore shi daga masarautar gaba daya yace." Nasan dama duk inda akaje aka dawo gaskiya sai tayi halinta shiyasa kake mutukar burgeni Jarumi Kuma ina so inyi koyi da halayen ka Wanda ya shirya maka wannan sharrin Allah ya tona masa asiri ." Omar yace." Wannan al'amarin da ya faru akwai sanya hannun makusanta na a ciki kuma Insha Allah INA nan ina addu'ar Allah ya bayyana min su sai sun gane shayi ruwa ne. " Tafida yaji gabansa ya fadi a zahiri kam cewa yayi "Gaskiya ne mu kan mu idan asiri ya tuno sai inda karfin mu ya kare gurin ganin mun kare maka mutumcin ka." Omar ya girgiza kansa kawai ya wuce...... Tafida ya bishi da kallo yana gyda kai wuce wa yayi ya nufi sashen Kulu wacce take zaman jiran sa.... Yana zama yace." Yanzu muka had'u da wancan Babban bawan sai wani cin alwashi yake yana fadin sai ya dauki mataki kan wadanda suka hada masa sharri." Dariya suka shek'e lokaci guda Kulu tace"Rabu da shashasha don Allah kasan ma abunda ya sanya ana kira ka." ? Tafida ya girgiza kansa yana fadin"Sai kin fada ranki ya Dade. Tace"Zakaje cikin gari ga samo min kashin bakin kare yanzu yanzu na kira Aljani Najadu ya bani wani aiki Wanda indai nayi shi kan dai-dai to babu shakka duk wata bukatata zata biya a cikin gidannan ." Tafida yace." Don dai kashin bakin kare Kar ki damu Uwar d'akina zan futa yanzu in samo miki." Tace"Bayan Wannan kuma zaka samo min kashin ba'kin jaki Dana bak'ar akuya wacce bata ta'ba haihuwa ba." Yace." In Allah ya yarda za'a samo tace"Amma fa shi kashin akuyar guda Dari ba daya zaka kawo min." Mik'ewa yayi yana mata sallama da fadin"Kamar ya kawo mata ya gama ne tw saurare shi daga nan zuwa awa guda

Kamar yanda ya fada din hakane ta kasance ko awa guda baiyi ba ya kawo mata dukanin abunda ta umarce Shi jin dadin haka yasa tayi masa kyauta ta bajinta Tafida yayi ta murna da farin ciki

Take ta shiga wani daki Wanda takebance shi domin ganawa da bakaken aljanunta marasa imani Aljani Najadu ta kira kamar yanda ta saba hira dashi yazo ya fada mata yanda zatayi aiki da komai.Sallama tayi masa ta futo daga dakin bayan tasa mukkuli ta kulle Baiyo ta kira tace ta Dora nama zallah babu gashi take Baiyo ta shiga kicin ta fara akin da aka sanya ta

Kicin din ta shiga Baiyo tace"Ranki ya Dade kece a kicin tace"Akwai akin da zanyi ne Baiyo taja gefe guda tana kallon ta ta kwance wata bak'ar ledar kashin bakin kare Dana bak'ar akuya ta hada su guri guda ta dake ta zuba kan tafashen Maman ta mai da murfin ta rufe ta kalli Baiyo tace"Idan kun lura abunda na zuba yabi jikin Maman sai ki zuba tattasai a kai ki hada miyar." Baiyo tace." Angama ranki shi Dade." Har taje kofar futa ta juyo tace." Kiyi fa sauri ki gama ina jiranki a Palo."


Bayan futar ta Baiyo ta shiga tunanin kan abunda tayi tabbas wani ta shirya wa Wannan muguntar ita kam bata so tazo cikin jerin bayinta ba ta lura matar bata tsoron Allah ko kadan kullum cikin cutar abokanan zamanta take babu shakka zata sanya ido kan lamarin.... Tsaf ta gama miyar taje ta Sanar da ita ta gama nan ta sanya ta dafa farar taliya cikin mintu goma tafiya ta dawo cikin wasu kwanuka aka hada komai suka nufi dakin Hatsi tare Baiyo ta dunda tunanin ya za'ayi ta hana Aysha cikin Wannan abincin tunda taga sun nufi dakin Hatsi tasan don Aysha aka hada miyar sai take tunanin wane irin Abu Ayshar tayi mata take so taga bayanta a zahiri tana nuna mata kauna a badi ni kuma ba haka yake ba tasan dai duk Wanda aka baiwa Wannan gubar yaci karshen sa mutuwa....Kofa daya ce a bude wacce ta zama kamar taga don babu yanda za'ayi mutum ya iya shiga ta cikinta ta wannan kofar take le'ko da kanta tana ganin Zuwan su ta fashe da kuka Mara sautin


Kulu tace"Me zan gani ni Hauwa wato duka kofofin aka kulle Wannan wane irin Horo ne kiyi shiru ki kwantar da hankalin ki daga nan bazan zame ko ina ba sai fada gaban kowa za'ayi Shari'a don Gaskiya Wannan hukuncin da aka yanke miki yayi tsauri an kulle Ku kamar wata wacce tayi kisan kai haba wannan Abu banji dadinsa ba." Aysha na kuka tace"Mommah tsonran dakin nake ji wallahi tun dazu nake jin motsi a cikinsa don Allah ki rokar min Sarki ya janye min wannan takunkumin na yarda da laifi na."


Tace"Kiyi shuru ki daina kuka ga abinci na dafa miki da kaina na shiga kicin nayi miki miyar zallahr naman sanyi nasan kina son takiya da miya ki kwantar da hankalin ki kici abinci insha Allah baxaki kwana cikin dakin nan ba." Kwandon abincin ta karba hannun baiyo ta mik'a mata Aysha ta karba tana godiya Tace." Ki zauna kici ki koshi kinji."! Daga kanta tayi tana kallonsu suka juya da niyar tafiya Baiyo tana jin kamar ta dawo ta hana Aysha cikin abincin.


A maimakon su nufi fada Kamar yanda ta fada sai kawai ta wuce sashen ta cikin zuciyarta tana fad'in'Yar iskar yarinya yau zaki mutu da yardar Allah. na daina wahalar da kaina a kanki..... Suna isa sashen ta sanya Baiyo hada mata wuta sai da tayi gawarshi sannan ta kawo mata Cikin Wani kasko Tace Baiyon ta futa ta bata guri Baiyo na futa tayi tumbur zigidir ta dauko wani garin magani da ta hadashi da kashin bakin jaki ta kwaba da Wani mai me wari ta fara sanya wa cikin wutar kafin kice kwabo kauri ya gauraye sashen gaba daya haka kulu ta gurfana gaban wutar tana sambatun kiran sunayen mutanan dake gidan... Kome take nufi da haka oho.

Dai-dai lakacin da take Wannan Abu Aysha ta dinga jun kanta na wata irin juyawa jiri na dibar ta ta zube gurin ruwan gora ta dauko Wanda ke cikin kwamdon abincin ta tuttula a cikinta taji kamar wuta take sanya wa cikinta don wani irin zafi yake mata kwanciya tayi lamo a gurin tana rarraba ido hawaye na zubo mata kokari take taci abinci ta kasa motsi jikinta duk ya saki dai-dai wannan lokacin ne kuma Baiyo ta futo daga sashen su Omar hankalinta a tashe tazo futa ta hango shi cikin rumfar dokuna kai tsaye can ta nufa Omar na ganinta ya bata fuska don ya San Baiwar Kulu CE ya tsani duk Wanda ya dangance ta yace." Menene ya kawo ki sashen nan." ? Jiki na rawa Baiyo ta shiga zayyane masa abunda yake faruwa ya kalleta a nutse yace." Duk ba dake ake shirya komai ba shine yanzu zaki zo min da wata maganar banza ki sati biyu ba'ayi ba cikin dare naga Uwar dakin naki na haka rami kun binne Abu to na Ciro ko menene na kona sai me."!! Tace"Kayi hakuri yanzu babu lokacin mai da magana kazo ka ceci Aysha bana so taci gubar da aka sanya mata idan Aysha ta mutu ina da hakki saboda nice na dafa abincin." Gaba yayi Baiyo ta bishi a baya jikinta sai rawa yake.


Yana bude dakin ya ganta kwance magashiyan tana wani irin bacci Wanda kana ganinsa kasan ba me dadi bane kayan abincin ta hau budewa. Ya dauki Fula's din miyar yana dubawa hancisa ya kai ya sansana wani irin karni da wari ya daki hancin sa da sauri ya rufe ya dudduba ya tabbatar bata ci komai ba tun bayan ruwan da tasha kwandon abincin ya dauka ya futa dashi Baiyo ta tare shi tana tambayar sa yace. " bacci take kuma bata ci komai ba." Hamdala ga Allah Baiyo tayi da sauri ta koma sashen don kar ta neme ta.


Omar kuwa bayan gida ya nufa da kwandon abincin ya aje ya fara haka sai da yayi zurfi sosai sannan ya juye miyar gabaki daya mayar da k'asar daya hako ya rufe gurin taliyar ya wa tsawa kadangaru ita..... Ya futo daga gurin yana mamakin bakin halin matar shi kansa da ya shanshana miyar har yanzu kansa juyawa yake ina ga anci yasan Duk Wanda yaci miyar karshen sa mutuwa... Sashen su ya nufa ya bude d'akinsa kai tsaye toilet ya nufa yayi wanka har yanzu yana jin rashin dadi a jikinsa ya dauro alwala ya futo Riga da wando yasa na Koran yadi duk kayansa ya dika ne da saukaken dinki turaran sa ya shafa a jikinsa ya futo da niyar shiga massalaci sallahr magariba.

Aysha tunda ta kwanta wannan baccin bata farka ba sai kusan sha d'aya da rabi na dare a furgice ta mike tsaye dakin duhu dumdum sai ta wannan tagar take gano haske kadan.... Wani Abu taji yabi kafarta ta kwala kara mai karfi Omar dake shawagi a harabar gidan ya jiyo ihunta da sauri ya nufi dakin dama shigar sa kusan biyar duk lokacin da ya shiga sai ya tadda bata tashi ba.... Ihu! Take so ta d'ane jikin kofar tana zuro kanta.... Yayi saurin kunna torchlight ya bude dakin da sauri ya shiga... Tana ganin haske ta dura kasa a guje ta nufe shi yayi saurin kaucewa yana tsoron abunda zatayi ya lura muguwar zabuwa ce...... Dam'ka ta Kai masa ya kauce a karo na biyu yana fadin"Wai menene. " ? Tana wani irin haki tace"Duba can gurin wani Abu Kamar kadan gare naji ya hau kafana." Gurin ya karasa yana haskawa da fita aikuwa k'aton dangare ne yayi kwance a lokon gurun da alama nan ne gurin kwanansa..... Aysha ta fasa ihu! Bayansa ta rike tamau! Don saura kadan ma su fadi saboda irin rik'on da tayi masa na bazata ya bata fuska sosai yana kokarin xame jikinsa yace." Ke baza ki fasa halin ki ba ko."!! Tana zubar da hawaye tace"Duba fa ka gani kadangare ne. A dakin amma saboda ba'a sona an tsane ni ace a cikin dakin zan kwana." Yana jin yanda gabanta ke bugawa tunda duk maganar da take bata sake shi ba.

Yace." Kece kika kwanta matsa a makwancin sa saboda haka sai sauya gurin kwanciya ni sake ni na futa."

Rike shi tayi tamau!! Tana fadin"Na ranshe da girman Allah baka isa ka futa ka barni a dakin nan ni kai dai ba."






8/3/2020


*BINTA UMAR ABBALE*
[3/12, 10:31 PM] Bintu: *SADAUKI!!🏹*
_OMAR💫👑_




_*Ga masu bukatar karanta littafin zasu tura #300 ta wannan accont din.....0542382124 Binta Umar GT bank.... Idan kuma katin waya zaka tura sai ka tuntu'be ni ta wannan numbars .....08089967176.....07084653262 Insha Allah zan fada maka yanda zaka biya kudin... Mutanan Nijar Idan kuna bukata zaku tura dala Dari ta wannan numbars....90899076 _88137740 Katin Airtal ko Orange Dala Dari itace a madadin Dari uku kudin Najeria.*_



Free pege

14


'Kara shigewa jikinsa take yana kara janyewa domin gudun abunda ka iya kaiwa ya kawo duk sanda zata kusanta jikinta da nashi ya Kanji duk wani karsashi gami da jarumtar sa na Neman guduwa kasala da sha'awa subi su dabaibaiye shi, jikinsa a Dan sanyaye yake kokarin jawo ta amma taki sakin shi rike shi taki sakeyi tana goga masa k'irjinta dake mutukar kashe masa jiki.

Ya jawo ta da karfin gaske ta tsaya gabansa tana zazzare ido hade da waiwayaewa bayan ta....... Hanya fita ya kama, a guje tabi shi ta rirrike shi tana wani irin kuka gwanin tausayi k'irjinta sai bugawa yake. Tausayi ta bashi yasa yaja hannunta suka zauna kan wani buhu dake cike da abincin dabbobi ko da suka zauna din sai shiga jikinsa take tana rirrike hannunsa tana waige-waige kana ganinta kasan a furgice take...... A hankali nutsuwa ta soma zuwa jikinta ta saki hannunsa a hankali tana sauke ajiyar zuciya tace"Don girman Allah kar ka barni anan gurin ka taimaka min kaji."!! Cikin wata irin siga ta fadi maganar yaji wani irin bakon yanayi na shiga jikinsa idonsa ya tsura mata tayi saurin kauda kanta kunyar abunda tayi masa a baya take ji yau gashi tana Neman taimakon sa..... Cikin dakakkiyar murya yace." Kin san dai bazan saki aikina nazo nayi ta gadinki ba ko."!? Aysha tayi shuru tana jin fad'uwar gaba addu'a take Allah yasa kar ya botsare mata. Ya cigaba da cewa "Kiyi hakuri ki zauna nan in da na zaunar dake Insha Allah babu wani kwaro da zai zo kusa dake zan baki fitila ta kiga haske, Idan bacci ya kamaki ki kwanta kan buhun ina tsaye a waje har wayewar gari Idan jin ji motsin wani Abu ki hasko min fitila zan zo."


"Uhumm! Ni dai ba inda zakaje kawai ka zauna tunda dama ai bani kadai nayi laifin ba." Yanda take magana k'asa-k'asa Cikin shagwaba yaja hankalin sa sosai ya tsirawa bakinta ido yana kallo

Aysha tayi saurin dauke kanta tana marairaice fuska kanta ta d'ora kafadarsa tana lumshe idonta. Omar ya rasa yanda zaiyi yarinyar na so ta saka shi tsaka mai wuya zaman sa tare da ita daki daya zai janyo masa matsala babba a kankin kansa yana fargabar kusancinsu domin dumin jikinta na rikita shi mutuka gefe guda kuma yana fargabar wani ya gansu a tare ga aikin tsaron gida da yasa kansa...... Wata jarumta ce ta zo masa lokaci guda ya ingije ta saura kadan ta fadi, ta bude idonta da yake da alamun bacci Tana kallonsa tana marairaice wa ganin ya mike tsaye ne yasa ta mike da sauri zata rik'o hannunsa ya daka mata wata razananniyar tsawa! Hannu ya daga mata cikin fushi yace." Kika kuskura kika kara sanya hannun ki a jikina sai nayi mugun bata miki rai."!! Aysha ta tsira masa ido ya cigaba da cewa"Ke ko kunyar da'kumar mutane baka ji kina so ki jefani wani hali ki jefa kanki idan zaki dangana ki dangana ki kwanta kan buhunan na fada miki babu abunda zai same ki kin tsaya taurin ka. Kina so in zauna tare dake wani sharrin ya sake biyo wa baya kome." ? Aysha taji zuciyarta nayi mata zafi ganin sai wani buga mata tsawa yake yana hantarar ta tana ganin kome tayi masa tunda ta bashi hakuri sai ya hakura ba sai ya fada mata magana ba."
Hanyar futa ya nufa tace"Kaje din Idan ka tafi sai me? Aikin banza kawai an hada ka da Allah da Annabi kamar ba musulmi ba komai zai faru dani na hak'ura idan ma mutuwa nayi sai Ku zuba ruwa a 'kasa kusha."! Juyo wa yayi Dan kalleta ya juya yana girgiza kansa mamakin rashin kunyar yarinyar yake tabbas Aysha baza ta taba sanjawa ba ya rasa me yasa ta raina shi kofar ya bude ya futa ya mai da ita ya rufe. Aysha ta fashe da kuka cike da tausayin kanta ta kwanta kan buhun harawa 'kayoyi sai soke ta suke ga wani irin saura dake bin jikinta yana wani irin kuka Mara dadin ji.


Omar kuwa futa yayi ya cigaba da shawagi a harabar gidan kamar yanda ya saba raba dare yanayi wajejen k'arfe uku ya koma dakin yana bude kofar ya ganta kwance kasan kofar tana bacci.... Cike da tausayi yayi nufin daukar ta sai kuma ya fasa ya juya ya rufe kofar amma bai sanya mukuli ba tsaye yayi bakin kofar yana sak'e-sak'e minti goma ya sake komawa dakin yanzu ta tashi zaune sai buge-buge take tana kashe sauro Fitilar ya dauka yana haskata.... Ta mike tana jin wani irin jiri na dibarta yunwa da fargaba yasa ta tafi luuuuu! Zata fadi da sauri ya taro ta ta fado jikinsa...... Kokarin kwace jikinta take don har yanzu da sauran haushin sa a tare da ita ya rike hannunta yana Dan murzawa kadan baya so yayi magana saboda dare yaja hannunta suka zauna kan buhun ta dinga dauke kai tana kokarin kwace hannunta tace"Sakar min hannuna yanzu kuma meye ya dawo da kai wallahi ban taba tsammanin baka da imani ba sai yau na tsane ka."!! Ba tare da ya saki hannun ba yace." Yanzu ma ba wani Abu bane na shigo dubaki ne kuma in fada miki wata magana kafin in futa." A hankali yake magana saboda yanayi na dare

Shiru tayi tana sauraron sa yace." Ina so ki kula da duk wani nau'in kayan ci ruwa ko abinci ko kayan marmari da Mai dakin kusurwa zata baki ko ta aiko a baki komenen Kar kici matar bata kaunar ki kullum kokarin ta taga bayan........."Dakata Omar."!! Ta katse shi cikin bacin rai! Shi kam kasake yayi yana sauraron ta tunda yake da ita bata taba kiransa da anihin sunan sa ba sai yau *Omar!* kamar a bakinta aka rada sunanan.


"Mommah! Na kake kokarin yiwa 'kazafi da sharri Kamar ni ka kalli 'k'wayar idona kace wai Mommah! Bata kauna ta zata kasheni."!! Kai ta dafe tana fadin" Innalillahi! Alamun maganar da yayi mata ta bata mamaki! Fuska a murtuke take kallonsa cike da bada umarni tace"Karka kara zuwa gurina da magana makamanciyar wannan!Mommah! Na bazata cuce ni ba har abada matar da ko kuda bata so ya sauka a kaina shine zaka zo kace zata kashe ni Mtssssw..........!

Bakin ya buge da bayan hannunsa yana kallonta da yanayi na bacin rai yace." Ba tun yau ba kike min wannan halayyar taki ta tsaki wai me kika mayar dani ne? Sa'an ki ne ni."!!? Ya fada ransa a bace!

Hannu tasa ta dafe bakinta tana kallonsa cike da mamaki! Yau bawa makaskanci ne yake kai hannunsa jikinta da nufin duka lallai in da ranka kasha kallo."

Yace." Idan muna magana dake karki sake nuna ni da hannu duk sanda kika sake sai na karya shi I Dan bai karye ba sai na targad'a shi."!!!Aysha tayi fiki-fiki da ido tana kallonsa tsoron sa take ji Yanzu Dan ja da baya tayi..... Ya cigaba da cewa"Na fada din Kulu bata sonki bata kaunar ki sai me?." Aysha tayi shuru tana sauraron sa, rai a daure yace." Shashasha kawai ana nuna miki gabas kina kallon kudu to ki kiyaye wallahi Wannan matar fuska biyu gareta gaban idonta kike mutum bayan idonki sai Allah tsakanina dake gaskiya ce ba wani abun ba da har kike kokarin tsokane min ido saboda an fada miki gaskiya idan kinji maganar Dana fada miki ki ceci kanki idan kuma bakiji ba kije kiyi tayi...... "Idan na kijin maganar ka me zai biyo baya."!? Tafad'a tana mik'ewa daga Kusa dashi (saboda tsaro) ta cigaba da cewa" Na farko dai baka haife ni ba da har zaka fada min magana naji sannan cikin ku babu Wanda ya shiga halin damuwar da Mommah ta shiga lokacin da sarki ya yanke min wannan hukuncin, hatta da mahaifiya ta bata nuna damuwar ta kan lamarin ba kai ma baka damu ba Duk da Kaine silar faruwan komai Kaine me kulleni a daki ina hadaka da Allah da Annabi kana ji baka saurare ni ba shine Yanzu zakace naji maganar ka? To bari kaji yau ko Guba Mommah ta bani hannu da hannu tace inci zanci saboda na yarda da kaunar da take min, Kufa!"? Daga kai har wad'an da suka kawo ni duniya ba su nuna damuwar su akai na ba saboda haka bani da ma'kiya sama daku."!!!! Tsaf! Yake kallonta yana mamakin kuruciyar ta a fili girgiza kansa yayi ya kama hanya zai futa, tsaki taja sai tayi saurin rufe bakinta da hannunta tana addu'ar Allah yasa baiji tana tsoron mari don na dazu ya shige ta sosai karfin hali kurrum take.

Bude kofar ya futa ya mayar da mukkulin ya kulle yana joyowa sukayi arangama da Yarima Faisal ya shigo cikin gidan cikin mota Omar ya bashi hanya domun sa samu damar shigewa da motar Yarima Faisal ya bude motar ya futo yana tangadi kana ganinsa kasan a buge yake." Da hannu yake nuna Omar din yana sambatu "Kyai! Kai! Ina fada maka ka kiyayi had'uwata da kai wallahi sai na koya maka hankali!!! Shin me kayeyi dakin ka futo kana zare ido shin ka shiga ka cigaba da 'kwakule ta ne ko me!? Kai!! Wallahi sai na kashe ka in dai akan Aysha ne! Matata ce faaaa."!!! Omar ya dinga kallonsa yana mamakin tangadin yake Sam yaki ya tsaya guri guda sai zagaye gurin yake yana nunnuna Shi.....Hanya ya kama zai bar gurin yana masifar jin takaicin yanda Suka Mai da kansu shida Dan uwansa Abbas yana jin tausayin mai Martaba matuka saboda rashin nagartattun 'Yaya macecen ce kawai mai hankali Karima tayi aure harda yaranta uku...... Faisal yayi yunkurin rik'o rigarsa bakinsa a jirkice yake fadin"Kai! Wato ka raina ni ko ina magana kana tafiya."! Omar ya janye rigar sa take Ya fadi a gurin Amma duk da haka bai daina yunk'urin kamo Omar din ba. Sambatu kawai yake zangawa har bacci ya dauke shi a gurin.








9/3/2020


*BINTA UMAR ABBALE*
[3/12, 10:31 PM] Bintu: *SADAUKI!!🏹*
_OMAR💫👑_




_*Ga masu bukatar karanta littafin zasu tura #300 ta wannan accont din.....0542382124 Binta Umar GT bank.... Idan kuma katin waya zaka tura sai ka tuntu'be ni ta wannan numbars .....08089967176.....07084653262 Insha Allah zan fada maka yanda zaka biya kudin... Mutanan Nijar Idan kuna bukata zaku tura dala Dari ta wannan numbars....90899076 _88137740 Katin Airtal ko Orange Daka Dari itace a madadin Dari uku kudin Najeria.*_




Free pege

15

Kiran Farko Mai Martaba ya futo da niyyar shiga massalaci kusan tare suke futowa da 'Yan uwanshi Waziri da Galadima Yatima Faisal suka gani kwance a gurin nan Mai Martaba ya fahimci yaje yawon daran sa ne ya dawo a buge..... Wani irin ciwo zuciyarsa take masa addu'a kawai yayi masa ta shiriya ya sanya wasu bayi suka dauke shi suka nufi sashen sa dashi.



Aysha jin kiran sallah asubahi yasa ta nufi karamin bandakin dake cikin dakin cikin duhu ta dinga lalube har ta samu ta kunna famfo ta d'aura alwala ta futo lokacin haske ya Dan fara shigowa ta wannan kofar sallah ta tayar a kasan gurin tanayi tana kuka bayan ta idar addu'a tayi ta kwanta tana gurin tana jiyo sawun tafiyar mutane suna shiga massalaci hawaye sai ziraro mata yake iyayenta da suka haife ta sun yarda da wannan hukuncin gani take Kamar ma basu suka haife ta ba yanda suke nuna halin ko in kula a kanta...... Tananan kwance tana tunani bacci mai nauyi ya dauketa........."Baiyo na kicin tana had'a abun kari ta shigo kicin din baiyo ta zube kasa tana gaishe ta ba

3 Comments On SADAUKI OMAR
avatar
auwal-mohammed

1 year ago

Reply

It nice book to read ????

avatar
hafsat-9-3

1 year ago

Reply

Very nice biik

avatar
hafsat-9-3

1 year ago

Reply

Very nice biik

Please Login or Register in order to submit comment