Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Wani Abu ba ta fada kan bed pillow ta jawo ta kankame shi tana cizar lips dinta daga zarar ta tuno suffarshi sai gabanta ya fadi yanayin da take ji a jikinta sai ka ruwa yake tana marmatse pillow da lumshe ido hade da harharde k'afafunta Nanne ta shigo dakin ba tare da ta sani ba. Nanne ta jima a tsaye a kanta tana kallon yanayin da take ciki, ba yarinya bace tsaf ta fahimci halin da yarinyar ta ta take ciki...... Murya a sama ta kira sunanta"Aysha. "!! Tayi saurin mik'ewa zaune tana zare ido ido suka hada da Nannen taji gabanta ya fadi towel din jikinta ta matse tana rufe k'irjinta Wanda yake duk rabin su a bude saboda tsabar yanda take mutsika pillow a jikinta, kallon zargin da take mata ne yasa jikinta yin sanyi ta sunkuyar da kanta kasa tana addu'ar Allah yasa bata fahimci halin da take ciki ba."


Cike da damuwa ta zauna kusa da ita tana kallonta a nutse tace"Ki d'ago kanki ki fada min abunda ke damunki nafi karfin minti goma da shigowa dakin nan kina kwance kina lailaya pillow a k'irji baki San na shigo ba me yake damunki? Duk da na fahimci halin da kike ciki amma wa'ka a bakin me ita tafi dadi."!!

Aysha tayi tsili-tsili sai zare ido take dalilin da yasa basa shiri da nanne kenan saboda bin kwakkwafin ta yasa bata shigowa sashen tafi sakewa sashen ta ko na Mammah! Wato me dakin kusurwa!!! Cikin tsawa tace"Ba magana nake miki ba kinyi min shiru dama ni tunda naga shigowar ki gurina nasan akwai matsala shin zaki fada min ko sai na bata miki rai.""!!! Hawaye ne ke kokarin zobo mata ta fara inda inda!!"Nanne ba fa wani Abu ban.... Dama kwana biyu ne nake ta fama da ciwon Ummm!!."" Shiru tayi tana kara yin kasa da kanta.


Tace"Kike fama da ciwon me."!!? Ciwon Mara ne ya takura min Nanne mybe zanyi al'adane." Rufe min baki anan gurin."!? Nanne ta fada tana kallonta ta cigaba da cewa"Na haife ki a cikina kice zaki min wayo don ubanki! Ciwon Mara ne zai sanya ki rungume pillow kina lumshe ido? Yanzu na fahinci aure kike so don haka yau din nan zamu zauna da mahaifin ki akan batun ki don haka tun daga yau ki fara tunanin wane namiji zaki tsayar a cikin jerin samarin ki ya zama abokin rayuwar ki."

Yanda taga Nanne tana fada ne yasa tayi shiru kanta a kasa har Nannen ta Karachi fadace- ta futa.... Minti biyar da futar ta sake dawowa lokacin INA sanya a kaya a jikina Alhmdullahi na Dan samu saukin dan gane da halin da nake ciki kaya nake sanyawa tace"Kiyi maza ki futo Yanzu sakon mai Martaba ya iso yana son magana dake Wannan karon barni jikina na bani wannan kiran ba na dadi bane."
Aysha bata kawo wani Abu Cikin ranta ba ta sanya kayanta ta futo ta tadda Nanne na jiranta Tare suka futa nanne na cikin wata lafiyayyar lifaya mai kalar sararin samaniya tayi mata kyau sosai ita kuma Aysha tana sanye da doguwar Riga bak'ar yar Saudia kana kallonsu kasan 'ya da uwa ne saboda tsananin kamar da sukeyi wa juna.

Ko da suka isa kebatanccan gurin tatattaunwar sai jikinsu yayi sanyi ganin Mommah! Na kuka tana fadin"Wannan al'amari kazafi ne da sharri Ayshata bazata aikata haka sharri akayi mata ranka ya Dade a dad'a duba lamarin." Kuka take harda fyatar majina..... Aysha ta soma bin gurin da kallo Sadauki ta gani dogare a gefe kansa a kasa taji gabanta ya fadi shi me ya kawo shi Wannan zaman tunda tasan duk ranar da zasuyi irin wannan zama iyakacin su sukeyi babu wani bare.... Ta cigaba sa bin gurin da kallo duk suna zazzaune suna mata wani irin kallo na tuhuma Maimartaba Baba Waziri baba Galadima Wanda take ganin fuskarsa kamar ta zaki saboda tsabar bacin ran da yake ciki.... Fulani Mariya na gefen Sarki kanta a kasa Yarima Faisal Yarima Abbas harda Karima dake gidan auranta ita tana zaune a gurin..... Jiki a sanyaye taje ta zube gabansu tana gaishe su. Duk rashin kunyar ta tana jin shakkun iyayenta tana kuma gudun b'acin ransu shin wai me ya hada wannan taro ne? Bata da Wanda zai bata amsa sai ta mike tana tana hard'ewa taje ta zauna kusa da Mammah nata wacce ke ta faman sharar hawaye..... Hoton dake hannunta ne ya dauki hankalinta ta leka kanta, Da sauri ta cire kanta gabanta ya yanke ya ya fad'i inda SADAUKI yake tsaye ta kalla suka hada ido da sauri ya sunkuyar da kansa kasa, kafin kice kwabo sai hawaye sharrrrr!!!! Murya na rawa tace"Mommah! Menene wannan ? Waye yayi min wannan sharrin wallahi ban........."Rufe mana baki ja'irar yarinya Mara jin magana. "!! Da Sauri ta gumtse bakinta da hannunta tana kallonsa da idanunta dake zubar da hawaye.


Sarki! Ya gyara zamansa yana kallonta kana ganinsa kasan yana cikin b'acin rai mutum ne shi me mutukar hakuri zaka Dade kana yi masa Abu bazai nuna maka bacin ransa ba har sai ya kaishi k'arshe tukkuna yana da hakuri sosai amma bai iya fushi ba.

" Aysha Wannan zaman da kika ga anyi shi saboda ke ayi shi shin yaushe kika lalace kike bin namiji haka? Ko kina so ki zubar mana da kima da daraja mu ne? Kina so ki sanya masarautar da ta Dade tana kafa tarihi mutumcin ta da kimarta ya zube Yau raina ya b'aci abunda kikayi kuka dole sai an dauki mataki a kanki ba ke ke dai ba har da Omar din duk yanda nake dashi dole hukunci ya sauka a kansa tunda shima ya yarda ya biye miki koke Neman zubar mana da daraja da mutumci shin Aysha wannan Abu da kukayi yayi dai-dai kenan."!!! Shiru gurin yayi Sarki ya kalli Omar dake tsaye dogare a bakin kofa yace." Omar ina magana nace shin wannan abun kunyar da kuke so Ku jawo mun Cikin masarauta ta shine dai-dai Ashe haka ake? Duk daukar da nake maka me hankali da nutsuwa Ashe ba haka kake ba Omar ka bani kunya mutuka kuma dole ne ka karbi hukunci kamar yanda sauran mutane ke karba wannan Karin har Ayshar bazan bari."

Omar ya sunkuyar da kansa cike da tsantsar ladali yace." Allah ya baka yawan nasara kan wannan lamarin bani da abincewa na yarda ko wane irin hukunci za'a dauka akaina na amunce zan karba Allah ya huci zuciyarka....."Yi mana shiru! Munafikin Allah ta'alah."!! Yarina Faisal ne ya fadi wannan maganar yana wani irin huci! Yace." Mu zaka kawowa iskanci cikin gida kake kokarin ka lalata mana kanwa!! Ranka ya Dade ka bani dama kan wannan makaskancin bawa in bashi Horo ta yanda gaba in akace masa ga Aysha a guri sai ya sauya hanya."


Nanne tunda ta zauna ba tayi magana ba kanta na kasa tana so ta fahimci inda maganar take to sai Yanzu da Faisal ya fito da maganar fili ta gane inda al'amarin yake, wata irin fargaba ce ta kamata babu shakka lamarin ya afku tunda Yarinyar ta shigo mata gida cikin wani irin yanayi Mara dadi.... Take taji ruwan hawaye na nema ya zobo mata wannan wace irin masifa ce waye kuma mai laifi tsakanin Omar din da Ayshar.? Bata da me bata wannan amsar.


Fulani Mariya ta kalli Faisal dake ta faman zazzagawa Omar rashin mutumci yau ya samu damar da ya Dade yana Neman irinta cin mutumcin sa kawai yake Sarki bai ce komai ba gabaki daya ma al'amarin yana bashi mamaki ne kamar Omar da ya dauke shi a matsayin mutum me hankali da kamun kai shine zai aikata wannan d'anyan aiki."


"Kai kayi mana shiru ko kuma Yanzu ranka ya b'aci." Fulani Mariya ta fada da yanayin na 'bacin rai!! Shiru yayi saboda yasan halinta macace wacce bata son wargi bata wasa cikin lamarinta duka suna shakkarta.....Wata irin harara Mai dakin kusurwa take watsa mata tana daukar alwashi a kanta, shiru gurin yayi Fulani ta kalli Mai Martaba a nutse tace"Allah ya ja da ranka ya baka yawancin kwana INA ganin wannan lamarin yana da kyau a tsaurara bunkice a cikin........"Yo wane irin binkice kuma Abu ga zahiri an ganshi wato kina so ki goyi da bayan wancan lalataccen Bawan ko.""! Mai dakin kusurwa ta katse mata magana a fusace! Sarki ya d'aga mata sannu ransa a yace." Bana son hayaniya ki bari ta gama maganarta na saurara nasan Mariya akwai kaifin tunani kar in kara jin kin saka baki cikin maganar ta." Mai dakin kusurwa taji kamar ta kurma ihu! Dan bakin ciki ta sunkuyar da kanta 'kasa tana Neman afuwa. Sarki yace." Ina sauraron ki Mariya." Tace"Ina ganin ya kamata a kara bunkice kan lamarin nan jikina na bani kamar akwai lauje cikin nadi Omar da ita Ayshar INA ganin baza su aikata wannan aiki ba tunda dukaninsu suna da ilimin addini dai-dai gwargwado kuma sun San illahar yin haka ina ganin a bunkici daga ina aka samu hotonan suka futo."" Mai dakin kusurwa tace." Kyace a bunkice daga INA hotona suka futo daga sashen ki suka futo don haka sai yanzu a kira wannan yarinya da kike rik'o ta fad'i waye ya bata hotonan don Wallahi INA ji ina gani bazan lamunci ayi ma Aysha kaxafi ba a kuma 'bata mata rayuwa dole ne a dauki tsautsaran mataki kan ha....... "Hauwa bakiji abunda nace ba kenan." Sarki yayi maganar yana kallonta da yanayi na bacin rai! Shiru tayi tana sunkuyar ra kanta kasa sai huci take.

Shiru gurin yayi na minti goma Sarki ya kalleta a nutse yace." Wace yarinya ce ta kawo miki hotonan." ? Da sauri taje"Wannan yarinya Safara'u itace ta kawo min har cikin dakin nan tsabar tashin hankalin da nake ciki bai sa na tsaya tambayar ta waye ya aikota dasu ba."


Sarki ya tashi Jakada yace maza yaje yazo masa da Safara'u minti goma suka shigo tare Safara'u ta dinta rarraba ido tana kallon su tsawa! Faisal ya daka mata Omar yaji wani iri a jikinsa k'wafa kawai yayi yana masifar jin haushin Faisal amma Idan kere na yawo zabo na yawo watarana dole a had'u zai banbamce masa tsakanin aya da tsakuwa.

Safara'u ta dunga binsu d'aya bayan d'aya tana gaishe su Sarki ya dafa kanta a nutse yace." Safara'u kwantar da hankalin ki kiyi min bayanin kan wannan hotonan." Ya fada yana mik'a mata hotonan. Hannu tasa ta karba tana dubawa ta kalli gefen da Omar yake tsaye ya kansa a kasa, ta kalli gefan da Aysha ke zaune tana kukan bakin ciki.

Safara'u mai kaudin baki tace"Ranka shi Dade Gimbiya ce da SADAUKI na ai."!! Sarki yace." K'warai sune shine nake tambayar ki waye ya baki hotonan ki kawo wa Mai Wannan dakin." Safara'u taji gabanta ya fad'i Mai dakin kusurwa ta kalla cike da tsoro da fargaba tace." Ranka ya Dade bani na kawo wannan hotonan ba na kawo wani abune cikin farar takarda." Sarki yace." Waye ya baki ki kawo mata..... Shiru tayi tana tunanin shin ta fadi gaskiya ko kuma kar ta fad'a gabanta ne ya fad'i da ta tuno irin hukuncin da Matar tace zatayi mata mutukar ta kama sunan wani a cikinsu tace"Ranka shi Dade ban San shi ba kwata-kwata ma ban ta'ba ganinshi a masarautar nan ba yana bani ya juya ya tafi." Shiru gurin yayi kowa na nazari maganarta Shin wanene wannan? Meye dalilin sa na aikata min haka me nayi masa a duniya." Abunda Aysha ke ta fad'a cikin ranta tana zubar da hawaye.


Babu zato suka ji Muryar Safara'u na fadin"Ranka shi Dade muna zaune ni da SADAUKINA yana koya min karatu ta shigo gurin ta dunga dukansa tana rungume shi wai dole sai ya zama bawanta shine yake bata hakuri ranka ya Dade SADAUKI na bashi da laifi a wannan lamarin itace tazo inda yake."







7/3/2020


*BINTA UMAR ABBALE*
[3/12, 10:31 PM] Bintu: *SADAUKI!!🏹*
_OMAR💫👑_




_*Ga masu bukatar karanta littafin zasu tura #300 ta wannan accont din.....0542382124 Binta Umar GT bank.... Idan kuma katin waya zaka tura sai ka tuntu'be ni ta wannan numbars .....08089967176.....07084653262 Insha Allah zan fada maka yanda zaka biya kudin... Mutanan Nijar Idan kuna bukata zaku tura dala Dari ta wannan numbars....90899076 _88137740 Katin Airtal ko Orange Daka Dari itace a madadin Dari uku kudin Najeria.*_


Free pege
12


Hankalin kowa ya koma kan Aysha dake tsiyayar da hawaye shikkenan asirin ta ya Tono ita kuwa me zatayi wa 'yar iskar yarinyar nan ta huce takaicin ta.... Mai marba ya kalli Omar dake sunkuye da kansa a 'kasa yace." Maganar da Safara'u ta fada shin haka take ko ba haka bane menene ya Kai Aysha har inda kake bayan nayi sulhu a tsakanin ku." Omar ya rasa abunda zai ce ganin Ayshar na kuka sai ta bashi tausayi amma saboda yana so aka ja mata kunne yasa yace." Ranka ya dade babu wani Abu da ya sake shiga tsakanin mu tun bayan sulhun da kayi mana a fada yau din ma akasi aka samu ranka ya dad'e ni na amunce na zama bawan nata kamar yanda take bukata mutukar hakan zai sanya ta zauna lafiya dani." Sarki yace." Maganar runguma fa shin da gaske ta rungume ka ko A'a." Omar yayi kasa da kansa kwata-kwata a rayuwarsa shi bai iya karya ba shiyasa yayi kasa da kansa Mai Martaba yace." Tunda naga ka sunkuyar da kanka kasa nasan da gaske hakan ta faru domin nasan kai din mutum ne mai fadin gaskiya Cikin lamuranka.


Nanne ta fara share hawaye tace"Ranka ya dade ina da magana. "! Sarki yace." Bislimillah ." Tace''Duka wannan maganar da ake gaskiya ne Aysha ta aikata abunda ake tuhumarta dashi lokacin data shiga gurina naga alama Allah ya taimake ka gatanan a gabanku Ku tambaye ta idan aure take so to ta futo da miji ayi mata tun kafin ta jawo mana abun kunya.


Baba Waziri ya kalli Aysha ransa a bace yace. " Aysha kin bani kunya wallahi kuma kin zubar da darajarki da kimarki ta d'iya mace kaf! A tarihin masarautar nan babu Wanda ya ta'ba aikata irin wannan aikin saboda haka yanzu ba sai anja wani lokaci ba Sarki zai yanke miki hukuncin da duk ya dace dake..... "Wai yaya zaku Dora mata laifi ita kadai ne na tabbatar da cewar wannan abun Aysha ta bata aikata ba duka sharrin wannan munafukar yar ne da Uwar rokon ta dashi kanshi munafikin Yaron Ina rokon alfarma kafin a yanke mata hukunci a tsaya a tsaurara bunkice kan lamarin." Mai dakin kusurwa ce take wannan maganar sai share hawaye take..... Babu Wanda yace mata komai duka suna sauraron hukuncin da mai Martaba zai yanke.......Gyaran murya yayi yace." Aysha daga nan zuwa kwana goma ki tsayar da mijin aure cikin mane man ki.. Shiru yayi na minti biyu ya cigaba da cewa "Zaki zauna cikin Dakin dake kusa da rumfar dokona tsawon kwanaki bakwai ba tare da kin le'ko waje ba sai dai komai za'a mik'a miki." Duka suka kalli Mai Martaba jin irin hukuncin da ya yanke...... Wani wawakeken daki ne me wata gajeriyar kofa duk wani nau'in abincin dabbobin dake cikin gidan a cikin dakin yake duk kwa'kwar mutum bazai gano karshen sa ba saboda yanda yake da mugun zurfi da fadi kofofi sun kai goma a cikinsa daga ko wane sashen ana iya shiga dakin. Wannan dakin Sarki yake so ta zauna tsawon sati daya..... Da rarrafe ta karasa kusa dashi ta rike k'afarsa tana kuka tana Neman afuwarsa.""" Babu Wanda ya tausaya mata a cikinsu shi kanshi Galadiman yaji dadin hukuncin da Dan uwansa ya yanke kan yarshi idan ya daga kansa ya kalli Omar sai yaji Kamar ya shake shi ya huta saboda yanda yake jin haushin sa...... Kukan da take yana ta'ba masa rai don haka sai ya 'kagu a sallame shi ya bar gurin.... Mai dakin kusurwa ta hakikance sai kuka take Kamar gaske take "Fadin" A gaskiya wannan hukuncin yayi tsauri ranka ya Dade na tabbata ko bawa ne yayi laifi cikin gidanan baza'a tura shi irin wannan dakin ba dakin da ake aje abincin dabbobi Wannan ya nuni da cewar kun mayar min da yarinya Kamar dabba." Waziri yace." Hauwa duk Wannan bata taso ba hukuncin dai an zartar dashi kin San kuma Sarki baya magana biyu, saboda haka magana ta wuce." Hanci ta fyace tace"Shikkenan shi wane irin hukunci za'a dauka a kansa? " da sauri Nanne tace"Meye laifin Omar anan gurin? Hukunci dai mai laifi ta kar'ba Allah yasa ya zama izina a gare ta.....Mai Martaba ya mike da niyar futa Waziri da Galadima suka rufa masa baya..... Aysha ta rarrafa tana kuka ta rirrike k'afafun Nanne tana kuka da fadin"Wallahi Nanne ba da wata manufa na rungume shi ba asalima ban San lokacin da haka ta faru ba."

Don Allah Ku yarda dani wallahi bana jin komai a dangane dashi Asali ma shine Babban Wanda na tsana a duniya makiyi na ne shi na tabbatar dashi aka hada min wannan sharrin.....! Tana wani irin kuka ta k'arashe maganar.

Nanne ta mike ba tare da ta komai ba ta kama hanyar futa ranta duk babu dadi........ Wani irin murmushi ta saki tabi bayanta da harara tana tab'e baki! Ta kalli Ayshar da ta kwanta kasan kafet tana gurshen kuka Cikin zuciyarta tace"Shegiya kadan kika gani naso an yake miki hukuncin da yafi haka na tsane ki Aysha na tsani duk wani d'a dake cikin gidanan sannu a hankali duk sai na lalata muku rayuwa...... Duk a zuciyarta take wannan maganar a zahiri kuwa sakkowa kasa tayi tana kuka ta rungume ta tana fad'in "Ki daina kuka kinji ko nasan Wannan sharrin ba daga gurun kowa ya fito ba sai daga gurin Fulani kina dai gani 'yar dakinta CE ta bada shaida a kanki tana so ki lalace kamar yanda 'yayanta suka lalace saboda haka ki kula da ita ki San irin zaman da zakiyi da ita. Bata kaunar ki ko kadan.".

Aysha na kuka take fadin"Mommah! Nima nasan daga gurinta sharrin ya futo dama tuntuni nasan bata kaunta ko meye ya faru na San da saka hannunta shiyasa na tsane ta gabaki daya bana kaunar ta cikin raina." Kulu tace"Aysha ni zan fada miki sharrin Fulani Mari kiri-kiri ta hanani haihuwa tabi boka tabi malam an daure min mahaifa ko batan wata bantaba yi ba, an d'aura mana aure rana daya ankawo mu rana daya amma saboda tsabar iya asiri ranar da aka kawo ta ta samu ciki shiyasa na dauki alk'awarin salwantar da abunda yake Cikin kuma Allah ya bani iko na 'batar dashi a doron duniya. " !! Mammah ban fahimci maganar ki ba me kika batar."!? Jin tambayar da Ayshar ke mata yasa ta dawo nutsuwarta ta gane tana so ta tona abunda ya faru sama da shekara talatin a masarautar....... Baiyo ce ta shigo da sallama ta durkusa gurin tana gaishe su, Tace"Ranki ya dade Fulani Mari ta aiko ni na kira mata gimbiya Aysha tana son magan....."Kije kice nace inji ni banzan zo ba." Baiyo tace*Allah ya huci zuciyar ki gimbiya Kulu tace"Maza kije ki fadi sa'kon ki." Baiyo ta mike da sauri ta futa.

Kulu tace"Ko uban me zatayi miki da zata aiko kiran ki munafukar mata mai siffar mutanan kirki a zuciyarta kuwa sharrin ta yafi na shaidan." Tace"Mommah! Ki k'yaleni da ita sai na kirta mata rashin mutumci duk sanda ta sake ta shiga gona ta." Kulu tace"Kinyi min dai-dai irinsu dama haka ake musu."

Omar ne yayi sallama ya shigo Kulu ta watsa masa mugun kallo cikin tsawa tace"Me kuma ya dawo da kai munafiki an hada baki da kai za'a tozarta yarinya."!! Yace." Umarni daga Mai Martaba Aysha ta fito ina jiranta waje domin kaita dakin hatsi." Kulu tace"Au! Kaine ma zaka kaita dakin saboda ka samu d'aurin gindi kayi laifi a dorawa baiwar Allah sannan a had'u da kai gurin hukuncin ta." Omar yana kokarin futa yace." Wannan umarnin mai Martaba ne bana wa." Futa yayi yana tsaki ya tsani matar nan wallahi.

Aysha kam ta rasa ma abunda zatace saboda tsabar bakin ciki da takaici kulu tace"Tashi kije Aysha zan biyo ki da duk abun bukata kar ki damu kullum zan shigo ina debe miki kewaya."

Hawaye ta share tace"Mommah dare fa ni tsoron dakin nake ji wallahi har da kadangaru da kwadina kunami babu abunda babu." Kulu tayi dariya cikin ranta tace"Shegiya da zanga kunamar ma zan sa miki ita cikin Riga ki ne ai haka nake so ki shiga cikin kunci." A zahiri kam cewa tayi"Ki kwantar da hankali nasan sarki ba zai sanya ki a dakin ba sai an duba lafiyar sa babu abunda zai same ki insha Allah. " Aysha ta mike jikinta duk a sanyaye tace"Mommah ina jiran ki don Allah. "! Kulu tace " Kar ki damu yanzu zan shigo inga lafiyar dakin. "


Yana tsaye waje yana dakon fitowarta ta futo sau daya kawai suka hada ido da juna ko wanne ya dauke kansa Omar yayi gaba ba tare da yace mata komai ba, bayansa tabi tana sak'e-sak'e cikin ranta yanzu take da ta sanin shiga hurumin sa da tasan al'amarin zai juye kanta da batayi ba yanzu kowa yana mata kallon yar iska, wasu zafafan hawaye suka shiga zubo mata..... Daf da zasu shiga kofar ne ta kara sauri har ta taddashi ya sanya mukkuli ya bude dakin da hannu ya nuna mata yana fadin"Bisimilah." Wai ta shiga, taji irin takaici! Had'e fuska tayi sosai tace"Naga kamar kai ma kana yi wani irin kallo kar kayi tunanin da wata manufa na ta'ba jikinka baka kai wannan matsayin ba baka da abunda zaka burge ni dashi abunda ya faru tsakanina da Kai tsautsayi ne da kuma bacin rai! Amma ni ban taba jikin ka da wata manufa ni ba yar iska bace." Murya na rawa take maganar... Shi tausayi ma ta bashi yace." Naji bani da abunda Zan burge ki dama bana so na burge kowa nafi so nayi ta burge kaina ni bawa ne makaskanci dame zan burge ki."!! Tsaki taja ta fara kokarin shiga dakin. Gurin shiga ta buge kanta da sauri ta dawo baya ta manta kofar shiga gajeriya ce sosai sai ta sunkuya sosai...... Yace." Sannu baki ji ciwo ko."!! Ina ruwan ka."! Ta fada tana watsa masa mugun kallo. Hannu ya daga sama yace." Babu ruwana ni dai Shiga in kulle da akwai abunda zanyi. Tace"Wallahi baka isa ka kulle ni cikin dakin nan ba so kuke Ku kasheni ko."?







8/3/2020


*BINTA UMAR ABBALE*
[3/12, 10:31 PM] Bintu: *SADAUKI!!🏹*
_OMAR💫👑_




_*Ga masu bukatar karanta littafin zasu tura #300 ta wannan accont din.....0542382124 Binta Umar GT bank.... Idan kuma katin waya zaka tura sai ka tuntu'be ni ta wannan numbars .....08089967176.....07084653262 Insha Allah zan fada maka yanda zaka biya kudin... Mutanan Nijar Idan kuna bukata zaku tura dala Dari ta wannan numbars....90899076 _88137740 Katin Airtal ko Orange Daka Dari itace a madadin Dari uku kudin Najeria.*_


Free pege

13


Kallonta yayi a tsana ke yace." Umarnin ki zan bi ko kuma umarnin me Martaba? Shiru tayi masa tana zabga masa banzar harara, ya gyada kansa ransa ya soma b'aci da irin kallon banzan da take masa yace." Zaki shiga ko kuwa ko kuma kina so anan ma a biyo mu a dauke mu a hoto idan hakan ta kasance kece a ciki bani ba kina ganin dai yanda al'amari ya juya ." Tace"Shiga kamar na shiga na gama amma ina so kasan da cewar Wallahi sai na dauki mataki kan wannan yarinyar 'yar Makaho Itace duk ta sake dagula lamarin sai na sanya an Horo ta ta inda gaba in ta ganni sai ta sauya hanya." Yace"Duk hukuncin da zaki mata kiyi min shi ai ba sharri tayi miki ba kin aikata ne in banda Neman fitina ina Ruwan ki dani kin takura min duk inda nake kina bibiyata duk abunda ya faru dake kece kika jawo kanki kuma wallahi kika kuskura ki ka ta'ba min amanata sai kin raina kanki." Yanda taga yana magana cikin bacin rai yasa ta buga tsaki ta ran'kwafa kasa sosai ta shige dakin kafin ta Ankara yasa kwad'o ya rufe......

3 Comments On SADAUKI OMAR
avatar
auwal-mohammed

1 year ago

Reply

It nice book to read ????

avatar
hafsat-9-3

1 year ago

Reply

Very nice biik

avatar
hafsat-9-3

1 year ago

Reply

Very nice biik

Please Login or Register in order to submit comment