Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sai ya bata mamaki duk sanda ta kuskura ta sake aikata masa Abu makamancin wannan sai ya nuna mata cewar mulki ko sarauta shi basu isa yasa ji tsoron ta ba, babu Kalmar da take mugun daga masa hankali idan ya tuno yake jin kamar zuciyarsa zata buga *Wawa!* wannan Kalmar tana mutukar kona masa rai yayi alkwarin duk sanda ta sake kiransa da wannan suna babu shakka ranar zai nuna mata shi din wawa ne na gaske.


Yana daf da futa daga sashen shi kuma ya sawo kai Yarima Faisal kenan kallon kallo suke wa junansu Omar ya dauke kansa ba tare da yace masa komai ba ya wuce! Rigar sa ya jawo yana fadin"Kai din jakin ina ne! Dabbah kamar ni ka had'a kafad'a da kafad'a dani ka ganni kana kokarin wuce wa ba tare da ka gaishe ni ba."!!! Omar ya fuzge rigar sa yana masa kallon Raini kafin yace." Idan zan gaisar da kowa cikin masarautar nan to kai baka isa na gaishe ka ba domin baka kai Wannan matsayin ba.'''

A zuciya! Ya d'aga hannu zai kwada masa mari! Hannun ya rike yana sakin miskilin murmushi yace." Da ka kuskura ka mareni sai na jigata ka a gurin nan sai na baka 'kasar gurin kaci! Idan kayi gangancin Dora hannunka a jikina sai na baka mamaki sai nuna maka cewar Bawa makaskanci baya daukar raini! " Yana gama maganar sa ya saki hannunsa ya wuce cikin kakkarfan taku. Jiki a sabule Faisal ya bishi da kallo yana jin mugun takaicin da bakin cikin d'aurin gindin da ya samu dole ne ya samu mai Martaba ya shaida masa abunda ke faruwa ga dukan alamu yana so ya wuce gona da iri da mamakin abun ya bar gurin......"Mammah! Wani irin dadi nake ji wallahi yau na wulakanta wannan Dan iskan." Dariya kulu tayi tace"Duk abunda kikayi yayi dai-dai nasan kuma gaba zaiji shakkar tunkarar ki da wani abun duk sanda ya sake miki wani Abu to ki fada mun zan sa a kirashi ki kasanta shi." Alkyabatar ta dauka tana kokarin sanyawa tace"Wallahi Mommah! Na tsane shi."!! Sallamar Faisal ce ta katse maganar da za tayi ta saki fuska da fara'a take fadin"Sarki Mai jiran gadon mulki Yarima Faisal da daya tamkar da dubu yau an shigo gaishe ni kenan. "!?

Kusa da ita ya zauna ransa a bace yace." Maman! Me ya shigo da wancan bawan nan daf da zan shigo naga Yana kokarin futa. " Tace." Aysha ya 'batawa rai dalilin kenan da yasa na Tara bayi na nuna musu shi din ba kowa bane cikinmu kamar yanda wasu daga cikinsu s ganin kamar ba bawa bane shi.

Yarima Faisal ya kalli inda Aysha ke zaune lashe lebensa yayi ya tsira nata ido tana kici-kicin mai da alkyabar sa ba tun yau ba yake mutukar kaunar tsarin jikin yarinyar dirin jikinta na mutukar gigita shi. Shagala yayi da kallonta ta dago kanta suka hada ido dashi tsaki taja tana fadin"Nifa bana son kallo kai kuma kamar maye in kana kallon mutum." Ya sake lasar lebensa a karo na biyu wata lafiyayyar sha'awarta ce ke taso masa yace." Don na kalleki aibi ne? Kar ki manta daf kike da kizama mallakina ki aje a ranki baki da miji saini."

Harara ta banka masa yace." Koma ki zauna muyi magana." Ta zauna tana zumb'ura baki. Yace." Me ya faru tsakaninki dashi." ? Cikin shan kamshi ta fada masa duk abunda ya faru ya dunga jin wani irin jarabbaben kishi na cinsa jin cewar Omar din ya rike wa Aishar sa sannu har yana matsawa shi gani yake kamar ma da wata munufar yayi ba don mugunta ba yace." Amma kin dauki mataki me tsauri a kansa ko." Daga kanta tayi yace." Nima yanzu da zan shigo nan kasa kauce min yayi kafada-kafada muka hada dashi yayi kamar zai bangaje ni sai da na jawo shi na bashi lafiyayyun maruka sannan ya dawo nutsuwar sa."


Aysha da Kulu suka kalleshi cike da mamakin jin Abunda yace wai ya mari SADAUKI anya kuwa!?? Kulu tace' kayi min dai-dai maganin sarki haka nake son ka zama jarumin namiji domin rago baya iya mulki." Aysha kam dariya take boyewa tace"Anya Ya Faisal Wannan mutumin fa karfi ne dashi ina ganin bugu daya zai maka ka fadi gurin... Ka tuna dai ko shine dai ya mareka."!! Bata fuska yayi yace. " Kin ranani ko."!! Mik'ewa tayi tana yar dariya ya mike yana fadin muje muyi hira yau ina son ni dake mu tsayar da magana. " Futa sukayi tare...... Ta bisu da wani shu'umin kallo kafa daya kan d'aya ta d'ora tana girgiza kai tace"Duk zaku fi ubanku shegu 'yan iska nayi alk'awarin sai na hana Ku zaman lafiya sai na lalata Ku ina bakin cikin inga kuna walwala da farin ciki gidanan ina bakin cikin wayo gari inga bani da ko kowa a gidanan nice Uwar gida ni ya kamata na haihu na haifi magajin sarki ban haihu ba to saboda haka kuwa nayi alkwarin lalata farin cikin duk wani d'a dake gidanan idan ta kama ma nayi kisan rai zan iya mutukar bukata ta zata biya a kanku da iyayen Ku."!
Ita kadai take wannan zantukan a fili sai kace wata tababbiya.

Tofa!!





4/3/2020

*BINTA UMAR ABBALE*
[3/12, 10:29 PM] Bintu: *SADAUKI!!🏹*
_OMAR💫👑_




*_Ga masu bukatar karanta littafin zasu tura #300 ta Wannan accont din......0542382124... Binta Umar GT bank.... Idan kuma katin waya zaka tura sai ka same ni ta wannan numbars, 08089965176 _07084653262 Zan Sanar da kai yanda zaka biya kudin..... Mutanan Nijar idan suna bukata zasu tura dala dari ta wannan numbars 90899076_88137749 Katin airtal ko orange dala Dari itace a madadin Dari uku kudin Najeria._*



Free pege

3





Jiki a sa'bule Ikilima tayi sallama ta zube gabanta cikin sanyi murya tace"Allah yaja zamanin ki yace." Yana Dan wani uziri yanzu kiyi hakuri......"Saurara min."! Ta katse ta tun kafin ta 'karasa maganar tata mik'ewa tayi zaune tana wani irin huci! Tace"Kamar ni na kirashi yace." Yana da uzuri ko wane uziri yake dashi nasan nawa uzirun yafi nashi tunda yana a matsayin mai bauta ne bashi da uzirin kansa sai uzirin iyayen d'akinsa yau zai gaya mun Wanda yake d'aure masa gindi a cikin masarautar nan." Mik'ewa tayi Ikilima tayi saurin gyara mata rufaffafun takalmanta masu wani irin gashi a jiki tare suka futa ikilima na take mata baya gabanta sai fad'uwa yake! Ganin ta nufi sashen su Omar din......... Omar na gama bawa dokuna abincin su ya futo daga tsakanin su can wata rumfa ya nufa kafin ya karasa yaji alamun taku an shigo gurin da sauri ya juya suka had'a ido kallon kallo suke wa junansu Ikilima taja gefe ta tsaya kanta a kasa.


Tsayuwarsa ya gyara yana watsa mata wani irin kallo kai da ganinsa kasan na kaskanci ne. Wani irin b'acin rai ya sake kamata ita yake wa kallon raini irin haka. A fusace! Ta nufe shi ta d'aga hannu da niyar kwad'a masa mari! Hannun ya rike yana murd'ewa! Ba tayi tsammanin zai dauki matakin haka ba. Cikin dauriya gami da tsananin azabar da take ji ta buga masa tsawa tare da fadin"Sakar min hannuna ma kaskancin bawa Wanda takalmin kafana ma yafi ka daraja a gurina."!! Omar ya murd'e! Hannuna da karfi har sai da ya bada sautin 'kas-'kas! Ta cije baki cikin dauriya don saura kadan hawayen azaba ta kufce mata abunda saboda kar yaga gazawar ta yasa take kokarin dannewa duk da haka dai kana ganin kwayar idonta zaka gane tana kar'bar gashi.!

Hannun ya yarfar yana kallonta a ya mutse yace." Ne man me kike min.!? Aysha ta rasa me zata ce saboda takaici Kuka tasa tana nuna shi da hannunta da yake karkarwa tace"Wallahi sai kayi nadamar murd'e min hannuna da kayi bakin mugu azzalimi sai na kaskantar da kai cikin gidan nan wallahi!

Zagin da take masa bai dame shi ba don haka gyara tsayuwarsa yayi fuska a kirne! Ya sake maimata mata tambayar sa ta farko "Nai man me kike min.''!?

Hannu ta sake d'agawa cikin shammata zata sake kai masa mari a karo na biyu taji ya damk'i hannun da iya karfin sa! 'Kara ta saki! Tana kokarin zubewa a gurin! Saura kadan futsari ya kufce mata. Saurin sakin hannun yayi yana kara daure fuska hade da kafe ta da jajayen idanunsa masu girma."!!!

" Allah ya isa na."!! Abunda take iya fad'a kenan tana matse hannunta hawaye na silalowa a kumatun ta. Ko alamar tausayin ta babu a tare dashi ya sake gyara tsayuwarsa a karo na uku ya sake maimata mata tambayar sa ta farko " Ne man me kike min. "!?? Aysha yanzu ta fara dawo wa hayyacin ta kwata-kwata sai ta manta Neman ma me take masa ta diriri ce..... Nashi b'angaran so yake kawai yaji Neman me take masa da zata dunga aiko masa 'yan aike..... Ganin tayi shiru yasa ja tsaki ya juya da niyyar barin gurin....." Wawa Bakin azalimi Makaskanci Mara Iyaye kawai sai kayi nadamar zaman ka cikin masarautar mu Dan iska sai ka San ni kayi wa haka ni zaka ta'bawa jiki ko? Sai kayi nadamar abunda ka aikata a gare ni."!!! Kalamanta sunyi masifar bata masa rai har ya tsaya sai kuma wata zuciyar tace"K'yaleta kawai kar ka kulata." Ci gaba da tafiya yayi ya jiyo ta tana fad'in"Shashasha mai siffar Askarawa kawai."! Murmushi kawai yayi ya bude d'akinsa ya shige


Ta juyo a fusace! Ikilima tayi saurin sunkuyar da kanta Don duk abunda ya faru a kan idonta ya faru..."Allah ya taimake ki."! Ta fada tana sake dankwafar da kanta kasa, Cikin mutuwar jiki tayi gaba ba tare da ta cewa Ikilimar komai ba, da saurin ta rufa mata baya tana mamakin karfin halin Omar da jarumatar sa tunda take bata ta'ba ganin kukan gimbiya Aysha ba sai yau lallai Omar ya cika namijin da za'a jinjina masa.



Jikinta ta zube tana kuka harda shassheka Hajiya Kulu mai dakin kusurwa ta d'ago kanta tana cike da mamakin Wanda ya sanya 'yar gaban goshin ta kuka irin haka tabbas abunda ya faru Babban lamari ne..... Sai da taci kukan ta ta koshi kafin ta fad'a mata abunda ya faru.


'Kwafa kawai Kulu take tace"Wannan ta'kadirin yaro wannan annamimin yaro! Wannan Dan iskan yaro! Ya addabe mu na tsane shi na tsani na bude ido in ganshi cikin masarautar nan har kullum Idan ka zauna da mai martaba bashi da aiki sai na kwarzanta bajintar yaron gami da kwarzanta jarumatar sa wato d'aurin gidin da ya samu gurin mai martaba yasa yake ganin kamar yana ra wata fawa a cikin masarautar nan lallai yau tunda ya sanya ki kuka sai ya raina kansa tabbas zai gane shi din ba kowan kowa bane. Face makaskancin bawa."


Aysha ta sauke ajiyar zuciya tana fadin"Mammah duba ki gani fa yanda ya mummurd'e min hannuna duba ki ga saura kadan ya kwashe min fata."


Tace"Rabu da d'an banza Idan ma maye ne shi to sai dai yaci kansa domin dai ke Kin fi karfin sa shin wai ma me ya kaiki har inda yake."? Aysha ta soma inda inda "Nifa ba zuwa nayi ba aike nayi yazo yaki zuwa shine na futo domin zuwa nan kawai naganshi nake masa magana shine kawai ya kamani ya mummurde min hannu.''


" Yanzu na fahimce ki, Wane irin mataki kike so a dauka a kansa."? Kawai ki aika a kirashi ni nasan matakin da zan dauka a kansa."


"Baiyo."!!!!! Wacce aka kira da wannan suna futo daga wani karamin daki dake cikin palon gabanta ta zube tana fadin" A gafarce ni Uwar d'akina ina kimtsa miki gado ne."!


Tace." Maza je ki kira min Tafida."! Ta mike da sauri ta futa... Mintuna uku sai gasu sun shigo tare Tafida ya zube yana kwasar gaisuwa. Tace"Na amsa maka Tafida maza je ka kira min Makaskancin bawan nan."! Tafida ya gane ko wa take nufi da sauri ya mike ya futa.

"Baiyo kije ki cigaba da aikin ki."!
Da sauri ta mike tana godiya.


Suna tare da Yunusa Sakon Mai dakin kusurwa wato Kulu ya same shi kwata-kwata ya manta abunda ya faru tsakaninsa da Aysha don shi mutum ne Wanda baya barin Abu jikin ransa jin Kuli ce take Neman sa da kanta yasa ya amsa suka jera tare da Tafida har suka isa shashen nasu Tafida yaja ya tsaya kofar shiga daya daga cikin masu tsaron kofar ne yayi masa ido har katafaran palon Uwargin sarki Wato kulu mai dakin kusurwa!! Bai ji wani d'ar! Ba don ganin Ayshar hakimce cikin kujera ba ya dai yi saurin kauda kansa saboda ganin yanayin suturar dake jikinta dama haka take k'ananun kaya matsatstsu take sanyawa a jikinta kafin ta d'ora alkyaba gata ita tubarkallah macece mai zati a cike take ko ina mussaman a kirinta tana da manya manyan nonowa masu fadi da tsine. Ga uban ships dake bata da tsayi sosai yasa suka futo sosai ko cikin alkyabbata take motsi suke Idan babu alkyabba a jikinta ko ke mace kika kalleta sau daya sai kinyi marmarin sake kallonta saboda yanda take da tsarin jiki mai kyau.


Omar ya rankwafa tare da fadin"Barka da yamma Ranki shi Dade sakon ki ya isa gare ni wai kina nema na."


Tace." Wato wai ne ma ko? Omar yayi shiru tace"Kai wawa Wanda bai San hallaci ba ina mai tabbatar maka da cewar karshen ka yazo wato baka sanni ba har yanzu ko!? Omar yayi shiru yana sauraron hayaniyar da take masa ta cigaba da cewa"Nice nan Kulu Mai dakin kusurwa Kulu mai magana da aljanu idan baka San labarina ba to kaje ka tambaya kaji wacece Kulu Uwar gidan mai martaba nasan kafin ka futa wajen gari cikin gidanan za'a fada maka wacece ni."


Omar dai shiru yayi yana sauraran ta tace"Takad'iri kana ganin kana da girma da kwanji na daukar dutse da k'arfe to duk wannan karfin naka da jarumatar taka basa bani tsoro kawai naso zaman ka cikin masarautar nan Idan da ban so ba da tuni na fatattake ka domin ni nan da ka ganni sharrina yafi dubu naci dubu sai ceto."!!!!! Takaici da b'acin rai ya kamashi! Ya lura matar kamar bugaggiya take a nutse yace." Ne man me kike min ko da wani taimako da za'ayi miki." A fusace! Ta mike tsaye tana nuna shi da hannu "Kai baka isa ka taimake ni ba don ubanka! Waye kai me kake takama dashi!? Duk sanda wannan Kalmar ta sake futowa daga bakina sai ka kwana bakwai a daure."! Omar yayi shiru yana jinta a fusace! Tace''Me Aysha tayi maka kake kokarin karya mata hannu."? Gefen da take zaune ya Dan kalla yayi saurin dauke kansa.

Cikin tsawa tace" Ba magana nake da kai ba ka sunkuyar da kai kamar munafiki."

"Mammah! Kyaleshi."! Tafad'a lokacin da take mik'ewa inda yake tsaye ta nufa kansa dake sunkuye ta dago da hannunta ta ware karfinta ta kwashe shi da mari!!! Ko gezau baiyi ba...... " Baiyo."!!!! Ta kwala mata kira ta futo da sauri tana amsawa tace"Je ki taro min bayin dake sashen nan su kuzo tare." Baiyo ta futa da sauri domin cika Umarnin da aka bata.




3/3/2020

*BINTA UMAR ABBALE*
[3/12, 10:30 PM] Bintu: *SADAUKI!!🏹*
_OMAR💫👑_




*_Ga masu bukatar karanta littafin zasu tura #300 ta Wannan accont din......0542382124... Binta Umar GT bank.... Idan kuma katin waya zaka tura sai ka same ni ta wannan numbars, 08089965176 _07084653262 Zan Sanar da kai yanda zaka biya kudin..... Mutanan Nijar idan suna bukata zasu tura dala dari ta wannan numbars 90899076_88137740 Katin airtal ko orange dala Dari itace a madadin Dari uku kudin Najeria._*




Free pege
5



Can cikin wani lambu na hango shi zaune saman wani dutse hannunsa rike da wani Abu sai Dana na karasa gurin sosai na gane kome nene *Shisha* ce yake sha'kawa a bakinsa idonsa ya kad'a yayi jawur dashi! *Wawa* Kalmar da take ta yi masa yawo a kwakwalwar shi kenan....."Duk San da na sake aikewa a kira ka kaki zuwa sai na dauki mataki a kanka."!! Wannan maganar ma tayi mugun tsaya masa a ransa, Kansa yake girgid'awa yana zukar *Shishar shi* yana kuma tunanin wane irin mataki zai dauka kan yarinyar.
****

K'arfe biyu na dare masarautar tayi shiru ko ina haske tarwai!! Sautin kukan tsintsaye sai tashi yake, dai-dai Wannan lokacin ya futo daga d'akinsa yana sanye da dogon wando na bakin yadi sai bak'ar vest wacce ta matse masa jikinsa kamar zata yage wani farin Abu ya nannad'a a kansa babu tsoro a tattare dashi ya fara bin sa'ko da luku na sashen da yake..... Futa yayi yq nufi sashen Sarki yayi dube-duben sa kamar yanda ya saba duk daren duniya haka yake bin ko wane sashe na masarautar Yana dubawa saboda tsaro da kawo zaman lafiya ko Sarki bai San yana wannan aikin ba daga shi sai Allahn da ya hallice shi. Motsi yaji yayi saurin yin lamfo makalewa yayu jikin bango har suka wuce yabi bayansu a hankali har suka futa harabar masarautar...... Baiyo ta tsunga ta fara ha'ka sai da yayi zurfi sannan tace"Allah ya taimako Uwar dalina duba ki gani zurfin sa ya isa haka."""" Kulu ta durkusa gurin taba le'kawa tace"Zurfin ya isa haka. Wani Abu ta kwabto a jikinta ta tusa Cikin ramin tana fad'in" Aysha ki tafi uwa duniya ki zama gagararriya ki zama fandararriya ki dauko abun magana ki shiga uwa duniya! Tana gama sambatun surutan tafara mai da k'asar gurin..... Dake gurin tsit!! Yake yasa duk yaji abunda take fada mamaki yake sosai wannan wace Aysha ce ake jefan ta da wannan sharrin! Mik'ewa suka tare tace"Baiyo gobe Idan Allah ya kaimu tun kafin sanin mutane ya bayyana kiyi kokon rufe gurin nan saboda tsaro."! Tace"Zan yi insha Allah da wuri zan futo in rufe gurin."


Da sauri ya Dan matsa daga inda yake sai da ya tabbatar da wucewarsu ne ya karasa gurin tsugunawa ya sanya hannu wasa duk biyun ya kwakule k'asar gurin Abunda ke bunne yw dauko ba tare da tsoro ko fargaba ya mai da k'asar gurin ya bar gurin hannunsa rikayan abun.



Ya jima yana mamakin lamarin Yanzu dama duk kauna da so da take nunawa yarinyar Ashe duk na karya ne lallai dole ne ya kara saka ido sosai kan lamarin gidan don ya lura matar bata da imani ko kadan.


Washe gari da safe ya nufi wani kebantaccen guri ya fara bude abun wani irin wari yaji ya bugi hancinsa yayi saurin rufewa ashana ya kunna ya cinna kan abun ya mike daga gurin gefe ya ja ya tsaya yana kallon yanda wuta take ci sosai abun har maiko maiko yake kome ye dalili oho sai da ya tabbatar ya k'one kurmus sannan ya bar gurin.

Daf da zai futa ne ita kuma ta dawo Kai domin shiga gurin dake k'aramar kofa ce sai aka rasa wane zai ratsewa Dan uwansa gabanta ne yake fad'uwa ganinsa taja tsaki tare da fad'in"Kauce min daga hanya Wawa bakauy.....
Kafin ta karasa ya matse ta jikin bango ya danne kirjin ta da nasa da kyar take nishi idanunta sunyi jawur! NASA idanun yw zuba mata yace." Don ubanki! Waye Wawa."!? Bude baki tayi zatayi magana yasa hannunusa ya bude bakinta cizo ta kai masa ya take mata k'afafu sunkuyawa yayi ya debo k'asar gurin ya cusa mata a baki ya maida bakin ya rufe GAM da tafin hannunsa Aysha ta dunga sakin wani irin nishi nw azabar da yake gana mata yabi ya danne mata k'irjinta da nasa kirjin nonowanta sai zafi suke hawaye ne ya tsinke mata tana ji kamar ta saki fitsari


Ya tsira mata jajayen idonsa a murtuke yace." Dan ubanki waye Wawa."! ? Shiru tayi tana kifkita ido

Yace." Idan kina yiwa wasu iskanci da rashin mutumci ki kwana lafiya ni baki isa kiyi min in kyaleki ba ke baki da takidi sai na cin zarafin mutane! Shin kin San yanda Ubangiji yake karrama bawan sa kuwa ? Dame kike takama da har kike wannan abun? Na tabbatar da cewar da ubanki ne kan kujerar mulkin nan Abunda zakiyi sai ya wuce haka! To ki kiyaye ni wallahi ni nan da kika ganni nafi wuta zafi domin bana ta'buwa idan kika ce jurin ki ki shiga gona ta to babu shakka kina cikin hadari don sai na illata miki rayuwa shashasha Mara kamun kai mace mai futar da tsaraicin ta."!!! Janyewa yayi daga jikinta ya matsa gefe yana watsa mata makskancin kallo! Hawaye na zubo mata tace"Allah ya isa bakin mugu an kira ka da azzalimi an kira da *Wawa* kome zakayi Kay...... Kafin ta karasa ya dauke ta a kafad'a ya sa'bata ya nufi cikin gurin da ita ihu! Take tana dukan bayansa tana ciza tana harbe-harbe kamar da dutse take bai ko saurareta ba ya nufi ma tattara ta kadangaru manya manya-manyan tsofaffi yana zuwa ya jefa ta a gurin dake rami ne kuma yana da Dan zurfi sai ciyayi a gurin ta kwala wata razananniyar 'kara "Wayo na shiga uku."!!! Ko juyowa baiyi ba ys bar gurin..... Aysha nuffashinta ya fara sama jangwala yen kadangaru suka fara bin jikinta suna shiga riga idan da akwai abunda Aysha ta tsana bai wuce kadangaru ba ko karamaye ne bata kaunarsu ballanta iyayen su...... Daf da zai futa daga gurin ya sake jin ta saki ihu! Wanda yafi na dazu amo! Zuciyarsa tace koma ka gani ko Yanzu ka bata horo.... Yana isa ya ganta a sume har wani lafcecen kadangare yayi nasarar shigewa Cikin alkyabarta da sauri ya shiga gurin ya dauko ta ya futo shimfid'e ta yayi gefen gurin ya dauki wata buta dake gefe can gurin famfuna ya nufa ya taro ruwa ya dawo daga tsaye ya dinga sheka mata ruwa ta bude ido a furgice tana buge buge hade da sakin ihu!! Kamar sabuwar mahaukaciya gefe ya tsaya yana kallonta yana sakin miskilin murmushi, a dumauce ta mike tsaye dalilin wani irin gazar-gazar da take ji jikinta tafiyar kadangare ce alkyabbar take kokarin cirewa tana kuka Mara sauti sannunta ya danko mata jelar kadangaran ihu!! Ta kurma tayi kansa a guje d'afe jikinsa tayi tana ihu! Hade da zillo ya watsar da ita kasa gefe yaja yana hararata a gigice ta fara watsi da kayan jikinta yayi inda kadangaran ya samu nasarar fad'uwa kasa taja baya da sauri jikin ta sai kyarma! Yake duk da taga fad'uwar gadan garan bata yarda ba cigaba tayi da cire kayan har vest ta tsaya daga ita sai biriziya tana waige-waige zufa sai keto mata take, ganin tana kokarin yin tsirara a gabansa yasa ya bar gurin da sauri sai ya mutse fuska ....... A guje! Ta bishi ta d'ane bayansa tana kuka. Yana jin yanda zuciyarta take bugawa fat! Fat! Fat!!







4/2/2020

*BINTA UMAR ABBALE*
[3/12, 10:31 PM] Bintu: *SADAUKI!!🏹*
_OMAR💫👑_




*_Ga masu bukatar karanta littafin zasu tura #300 ta Wannan accont din......0542382124... Binta Umar GT bank.... Idan kuma katin waya zaka tura sai ka same ni ta wannan numbars, 08089965176 _07084653262 Zan Sanar da kai yanda zaka biya kudin..... Mutanan Nijar idan suna bukata zasu tura dala dari ta wannan numbars 90899076_88137740 Katin airtal ko orange dala Dari itace a madadin Dari uku kudin Najeria._*




Free pege
6



Cak! Ya tsaya tsigar jikinsa na mik'ewa wani irin yarrrrr!!! Yaji a jikinsa sakamakon jin taushin lafiyayyun Brest dinta suna sukan shi a baya tunda yake a duniya bai ta'ba hada jiki da 'ya mace ba sai yau! Da sauri ya sanya hannunsa ya fuzgo ta ta fadi a gurun jajayen idonsa ya kura mata! k'irjinta yayi matukar daukar hankalinsa amma saboda tsabar jarumta idan ka kalleshi a lokacin zakayi tunanin kashi yake kallo saboda yanda yake ya mutsa fuskarsa kamar baya so yace." Kika kuskura ki ka 'kara rungume ni sai na karya ki ko an fad'a miki kowa ma irin ki ne? Tsaki! Yaja ya gyada kansa hanya ya kama ya wuce yana fadin"Shashashar mace Mara kamun kai."!!


Aysha fad'uwa tayi a gurin tana wani irin kuka na bakin ciki ji take kamar ta hadiyi zuciya ta mutu *Shashashar mace Mara kamun kai."!!* Wannan Kalmar tayi mugun d'aga mata hankali wata irin 'kara ta kurma!

3 Comments On SADAUKI OMAR
avatar
auwal-mohammed

1 year ago

Reply

It nice book to read ????

avatar
hafsat-9-3

1 year ago

Reply

Very nice biik

avatar
hafsat-9-3

1 year ago

Reply

Very nice biik

Please Login or Register in order to submit comment