Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tare da ta amsa ba tace"Baiyo jiya kin tabbatar min da cewar Aysha taci Wannan miyar naman ko."!? Baiyo tace"Na tabbata ranki shi dad'e." Kulu ta girgiza kanta tana sakin murmushi tace"Haka nake so amma Kuma har yanzu banji wata magana ta bullo ba saboda haka ki had'a min tea ki zuba cikin Fula's bari in futo." Baiyo tace"Angama ranki ya Dade." Tana futa Baiyo ta dafa tea ta juye a Fula's kamar yanda aka umarce ta ta Sanar da ita ta kammala...... Kamar jiya a tare suka nufi dakin hatsin sai zubewa kulu ake ana kwasar gaisuwa wani ta amsa wani tayi musu banza haka suka isa dakin.

Tun daga nesa suka hango shi dogare bakin kofar dakin shima da ya hangi zuwan su sai yayi mutukar daure fuska, Suka karaso gurinsa dauke kansa yayi..... Kulu tace"Kai isasshe kana ganina ka dauke kai wato ban isa ka gaishe ni ba kenan." Omar yayi mata wani kallo yana ya mutsa fuskarsa ba tare da yace komai ba ya kauda kansa daga kanta. Girgiza kanta tayi cikin zuciyarta tace"Zan dawo kanka ne a fili kuwa cewa tayi"bude min kofa in shiga in duba Aysha." Ya sanya dan mukkuli ya bude suka shi yabi bayan su dogarewa yayi bakin kofa yana kallonta ta fara tashin Aysha dake bacci kasa duk tayi fururu! Aysha ta mike a furgice tana ganin kulu ta saka kuka rungume ta tayi tana fad'in"Mommah kinga halin Dana ke ciki ko jiya kince zakije gurin me Martaba naji shiru baki dawowa ba Mommah! Tun jiya da safe rabon da in sanya wani Abu a cikina."! Kulu taji gabanta ya fad'i! Tace"Ina Abincin Dana kawo miki kaddai kice min baki ci ba." Aysha tace"Bacci nayi na tashi naga banga abincin ba mybe wancan bawan ne ya dauke." Ta fada tana nuna Omar dake tsaye kulu ta kalleshi tana mamakin Ashe a yana gurin to meye amfanin tsayuwarsa a Kansu tace"Kai tantirin yaro Dan tsintuwa kaje duk inda ka kai wannan miyar naman da taliya kaje ka kawo min yanzu yanzu ko kuma ka fuskanci hukunci." Kai tsaye yace." Na haka rami na zuba a ciki kwanukan kuma suna bayan gida na watsar."""" Cikin masifa kulu tace'Kan wane dalili? Zaka aikata haka saboda kawai kana bakin Cikin taci abinci wato kunfi bukatar ta kwana da yunwa ko daganan sai ta mutu burinku ya cika."


Yace." Wannan abincin da kike magana a kansa ba abinci bane guba ce nasan komai don haka ki iya bakin ki idan ba haka ba sai na tona miki asiri a gidanan Kuma INA so in tabbatar miki da cewar duk wani binne-binnen da kikayi na ha'ka na tone su sai ki sanja wani ni kuma nayi alk'awarin mutukar zan gani sai na tone.''!

Kulu taji gabanta ya fadi jin abunda yake cewa babu shakka sai ta tashi tsaye akansa tunda komai take idonsa na kai! Cikin tsawa tace"Sharri da kaxafi zakayi min saboda an baka kwangila akai na kace kana ganina ina binne-binne Ubanka na binne!!!? Aysha tace." Mommah ki kyaleshi don Allah na lura kamar bashi da hankali..Omar yayi saurin kallonta wato shine ma Mara hankali lallai zai nuna mata rashin hankalinsa 'karara! Aysha ta cigaba da cewa"Tun jiya yake min wasu banzayen maganganu akan ki wai bakya kaunata ke din kina so ki kashe ni ne."!! Kulu ta fashe da kuka tana fadin"Amma Wannan yaro Allah ya isa tsakanina da kai ni zakayi wa wannan sharri. "! Tafad'a tana kallonsa kallonta yake ido cikin ido yana mamakin kaidin ta.

Kulu ta dauke kanta da sauri yanzu ba taso su hada ido dashi ta lura ya gano ta ya Kuma San wacece ita zata bullo masa ta bayan gida. Tace" Aysha yanzu kin yarda zan cutar dake kin yarda zan iya kashe ki.''! Aysha tace"Mommah har abada babu wannan tsakanina dake kauna da so ne na Allah don son da kike min ko iyayena basa yi min iransa saboda haka Mommah na yarda dake Dari bisa Dari baza ki cuce ni ba." Kamar gaske kulu ta goge hawayenta tana fad'in''Nasan dama babu abunda za'a fada miki aikana ki amunce duk kuma wani me yunk'urin shiga tsakanimu sai da yaji kunya, Ga tea na hado miki ki karya sai kiyi wanka ko."Omar naji maganar tea ya karaso gurin rumfa yayi a kansu suka dago kai suna kallonsa Aysha saurin dauke kanta tayi ganin yanda k'wayar idonsa ta sake girma gashi tayi wani ja wani sa'in haka idonsa take riked'ewa Kwayar tayi fari wani lokacin kuma ta rine kamar Jan gauta amma ba tayin hakan sai ranar da ya sanya kwalli.

Ita kanta Kulu sai da ta furgita ganinsa tsaye Kansu tace"Meye haka kai kafa tsaya a matsayin ka ko kuma wallahi tallahi ka bar gidanan ." Omar bai ce mata komai ba ya dai zuba musu ido..... Kulu tace"Baiyo bani kayan tea din in hada mata ta karya." Baiyo dake tsaye can gefe hannunta rike da tire Jere da kayan tea ta karaso gurun tana kokarin direwa 'kasa ya daga hannunsa ya daki tiren duk abunda yake kai ya watse can gefe take Fula's din ya fashe ruwan tea din ya fara gangarowa in da suke." Kulu ta mike a fusace! zata kifa masa mari! kaucewa yayi ta mari iska! Ta nuna shi da hannu tana fadin"Ni zakayi wannan rashin mutumcin ka San dai a haife na haife ka wato saboda kana samun d'aurin gindi gurin Sarki shiyasa kake kokarin taka duk Wanda kasi ciki kuwa har dani babu shakka zaka San ka ta'bowa kan ka bala'i!!! Fuuuuuu! Ta nufi kofar fita Baiyo tabi ta baya tana farin cikin abunda Omar din yayi ya burgeta......Aysha ta fashe da kuka tabi bayanta tana kiran ta..... Hannunta guda ya rike yayiwa rik'on tsauri ya jawo ta ta dawo ta zauna." Kofar futa ya nufa tabi shi da gudu tana kuka tana dukansa da fadin munanan kalamai a kansa Omar yayi banza da ita yan daf da futa ta jefa masa cup na glass Wanda ya rabe biyu sauka yayi dai dai wuyan sa aikuwa a take ya yanke shi jini ya soma zuba! Ya juyo yana kallonta da jajayen idonsa tsaye! Tayi rike da 'kugu sai numfarfashi take tana huci hancin ta duk ya tara zufa! Kana kallonta zaka fuskanci a cikin bacin rai take ko meye zata iya aikata wa.

Ya jima yana kallonta fuskarsa da yanayi na bacin rai! Ya juya ya kawai ya bude dakin ya futa mukkuli yasa ya kulleta yayi alk'awarin daga nan har zuwa dare baza budewa ta kamar yanda ta kwana da yunwa jiya yau ma haka zata yini da yunwa tunda dai bata da hankali ya rasa wace irin macace Aysha mai Wani irin tunani.... Haka ya futa jikinsa na digar da jini mutane sai kallonsa suke haka har ya isa sashen su ya samu ya daure gurin sannan ya shiga wanka ya futo ya sauya kaya...... Yunusa ya shigo yana tambayarsa yace." Kawai mu bar maganar Yunusa muje ka rakani asibiti. " Tare suka futo da Yunusa Tafida dake zaune cikin wata rumfa ya hangi futowar su dauke kansa yayi kamar bai gansu ba babu yanda baiyi da Yunusa a kan su hadewa Omar din kai su dunga shirya masa tuggu amma Yunusa yaki yarda shiyasa ya futa harkashi kuma yana bakin cikin ya gansu a tare.


Asibitin dake kusa suka je akayi dressing din gurin, suka nufo gida Tsakanin Omar da Yunusa kauna CE ta fisabillahi.


"Ranki shi dade " Jarumi yana Neman iso."! Muryar Jakadiya kenan wacce ke gefen Fulani Ta d'ago kanta a nutse tace"Jakadiya kice ya shigo mana Omar ba bako bane in da sabo yaci ace ya saba kuma kun saba duk ranar da zai shigo ba sai ya nemi Iso ba."

Jakadiya tace" A gafarce mu ranki ya Dade." Mikewa tayi ta futa minti uku suka shigo tare dashi..... Omar ya zube gabanta yana gaishe ta Fulani ta mike zaune tana kallonsa da murmushi a fuskarta tace"Jarumin Namiji! Omar Sarkin Ya'ki!!! SADAUKI na gaban Sarki!! Wannan haka yake duk wani Omar ba ka samun sa da matacciyar zuciya Omar akwai jarumta da rik'on gaskiya bazan gaji da fad'a maka cewar d'ab'iun ka na bani sha'awa ina ji ina ma Nina haifeka." Tafad'a k'walla na taruwa a idonta. Omar yace." Ranki shi Dade ki daina fad'ar Wannan magana bana jin dadinta wallahi bani da uwa sama dake a duniya kunyi min komai kin dauke ni Kamar dan cikin ki baki yarda na tozarta ba kin kula dani kin tsaya a kaina kamar yanda kika tsaya kan 'yayan Cikin ki, ke da mai Martaba baku nuna min bambanci komai ba a kan 'yayan Ku Faisal da Abbas kun bani ilimi irin Wanda kuka bawa 'yayan Ku kun ciyar dani daga irin abincin da kuke ci komai na rayuwa kunyi min abunda na samu daga gurun Ku bana tunanin wani wanda yake da iyaye a Raye zai fi ni gata saboda haka ni danki ne Kamar Su Faisal da Abbas." Hawaye ta share tana tuno wani Abu da ya shud'e shekara da shekaru tace"Omar idan ka dauki kanka Kamar su Faisal a gurina to duk sanda zaka shigo gurina kai daina Neman iso ka shigo kan ka tsaye kaji ko." Yace." Insha Allah Mama dama na shigo ne mu gaisa kuma in duba Amanata. "


Murmushi tayi tana kallonsa tace"Kamanta da cewar amanar taka na makaranta sai k'arfe daya na rana zata dawo." Yace." Yar dariya yayi wacce ta sanya na tsaya ina kallonsa Ashe haka dariya ke masa kyau gefen fuskarshi ya lo'ba sai 'kasan bakin sa hakoran sa Ashe haka suke da haske gasu a jere reras lallai dole dariyar sa tayi tsada saboda yasan yan yanda yake kyau in yanayi Yace." Na manta tana fara zuwa makaranta to bari in koma aiki zuwa k'arfe biyu na shigo mu gaisa." Fulani tace"Kwana biyu ta rage walwala na kasa gane abunda yake damunta...... Yace." Insha Allah kome yake damunta in mun zauna zata fad'amin." Fulani tace"To Allah yasa." Mik'ewa yayi yayi mata sallama ya futa.



****

Aysha tayi mutukar galabaita tsananin yunwa da take barazanar cinye mata 'yayan hanji yasa ta dinga dirkawa cikin ruwa aikuwa cikin ya kulle ta dunga kwara amai ta galabaita matuka kasan gurin ta kwanta tana wani irin nishi mai wahala.

Omar kamar yanda ya fada hakane ta kasance k'arfe goma na dare ya shiga sashen Fulani yasa aka had'a abinci dai-dai cikin ta da kansa ya dauka ya nufi dakin. Mukkuli yasa ya bude ya kunna fitila tsakiyar dakin ya hango ta.a kwance ya 'karasa ciki tsayuwa yayi kanta yana kallo tsuguna wa yayi bayan ya aje kayan abincin a gefe. Ya haska fuskarta da fitila, hasken Fitilar yasa ta idonta Wanda ya koma Kamar na mashaya. Hada ido sukayi dashi ta mayar da idon ta rufe....."Tashi kici abinci. "! Ya fada Cikin dakakkiyar murya." Shiru tayi masa ya sake maimata maganar sa, nan babu amsa. Hannu ya sanya ya d'agota zaune ta zame ta kwanta Dan yanda take jin yanayin jikinta da rashin kwari baza ta iya zama ba hannunta ya rike yana fadun''Kar ki kwanta mana." Ta fuzge hannun da karfi ta kwanta..... Shiru yayi yana nazari tabbas zazzab'i ne a jikinta don yaji zafin sa, zama yayi ya jawo ta jikinsa sosai ya rungume kafadarta rashin k'warin jiki ya hanata k'watar kanta lamo tayi q jikinsa tana lumshe ido..... Abincin ya zuba Cikin plate ya fara bata da hannunsa babu gaddama ta fara kar'ba Tana ci hannu baka hannu kwarya sai da ya tabbatar taji ta koshi sannan ya k'yaleta ruwa ya bude ya kara mata a baki aikuwa ta buge hannunsa jin wani irin a mai na taso mata kafin tayi wani yun'kuri har ya zubo haka ta dunga kelayashi duk ta bata musu jiki gab daya rike ta yayo sosai hat sai da ta gama tana wani irin nishi ya kwantar da ita gurin mik'ewa yayi ya futa da sauri ya nufi sashen su maganin zazzab'i ya dauko cikin magungunansa na dazu ya sauya kaya da sauri ya koma har yanzu tana kwance inda take janye ta yayi ya gyara gurin tsaf ya sake futo lallausan bargonsa ya dauko da pillow ya tsaya yana wani tunani dare yayi yanzu babu halin ya shiga sashen ta da ya daya daga cikin bayinta ta dauko mata kaya sanyawa saboda gudun abunda ka iya zuwa ya dawo ya sanya ya koma dakin nasa jallabiyar biyarsa mai karamin hannu ya dauko mata ya futo..... Duk wannan Abun dake faruwa a idon Tafida..... Omar ya shiga dakin ya mai Da kofar ya rufe..... A hankali ya zauna ys dagota Aysha sai langwabewa take dama haka take ita bata iya ciwo ba,


Da kyar ya rarrasheta tasha magananin gurin sauya kayan ne ya rasa yanda zaiyi gashi duk alkyabar ta jike da kyar yace." Ki Dan tube wannan kayan na jikin ki ga wani na kawo miki." Idonta a lumshe ta girgiza kai! Yanayin yanda take yana mutukar saukar masa da kasala bakinta ya tsurawa ido ya Dan lumshe idanunwan sa da suka soma sauyawa...... Yace." Aysha yana da kyau ki cire Wannan rigar ta jike Kuma akwai datti a jikinta zaki fi jin dadin kwanciya. " Bazan iya cirewa ba ka cire min."!? Omar yaji abunda yake ji a jikinsa ya sa'ke nunkuwa..... Shiru yayi yana Nazari kawai ya kai hannunsa madaurin igiyar alkyabar ya soma kwance wa a hankali ya zare ta k'irjinta ya tsirawa ido yana kallo a take yaji wani irin han'koro da jijiyarsa keyi ta mike zandar sosai ya soma shiga wani irin hali Mara miskatuwa addu'a ya soma yi yana so ya dauke idonsa daga kan k'irjinta abun ya fassakara ba tare da wani tunani ba ya soma cire mata k'aramar rigar dake jikinta take lafiyyayun Brest dinta suka bayyana Cikin beriziyya.... Yayi saurin kauda kansa ya mike tsaye hannunsa ri'ke da rigar still yana jin yanda jijiyar sa take harbawa Kofar futa ya nufa yana Neman tsari da shaid'an kawai haske ya gauraye dakin.

*Sarki*
*Galadima*
*Waziri*
*Faisal*
*Abbas*
*Kulu*
*Fulani*
*Tafida*
*Nanne*

Su ya gani tsaye a cikin dakin suna kallonsa cike da tsananin mamaki da zargi!

*INNALILLAHI WA'INA ILAHI RAJI'UN!*

shine abunda ya fad'a a cikin zuciyarsa Shikkenan babu mai futar dashi sai Allah.





*Nan na kawo karshen free pege duk me son karanta littafin nan sai ya tura kudin karatu #300 ta wannan accont din 0542382124 Binta Umar GT bank.... Idan kuma katin waya zaka tura sai ka tuntubeni da wannan numbars 08089965176_07084653262 insha Allah zan fada maka yanda zaka biya kudin karatu ba na mallaka ba duk Wanda yasan zai zo ya biya domin ya ci min amana don girman Allah yayi hakuri bana bukatar sa wannan littafin mallakina ne ban yarda ka tura min shi ko ina ba kai da ka biya kai na yarda ka karanta ban yarda asiyar min da littafina ba Wanda yayi daya daga cikin abunda na fada Allah ya isa hakkina Allah ya bi min HAKKINA da gaggawa.*



_*Masu siyar min da novels ban yafe muku ba insha Allah tun kafin mu tsaya gaban ubamgji Allah sai ya bi min hakkina a duniya duk mai bukatar wad'annan novels din sai ya tuntube ni da numbars dina gasu can a sama ina Mara da masoyana duk inda suke INA sonsu kuma ina alfahari dasu*



*BINTA UMAR ABBALE*

MARUBUCIYAR


*NANA KHADIJA*
*YARO DA KUDI*
*GIMBIYA BALARABA*
*BABBAN YARO*
*TSANTSAR BUTULCI*
*MASHAHURI*
*LADIDI KWADAGA*
*RUWAN DARE*
*SADAUKI! OMAR*

*Mai bukatar karanta daya daga cikinsu sai ya nemi ni ina k'ara fada muku kada kuje Ku biya gardi ko gardiya kudin littafina suna ci da gumin wasu ne kuzo Ku biya mai hakki hakkinta Ku karanta Cikin kwamciyar hankali*



9/3/2020
[3/12, 10:31 PM] Bintu: [3/11, 12:30 AM] Bint *SADAUKI!!! OMARđź‘‘*





_*Ki biya ki karanta Cikin kwanciyar hankali ke kuma da kika futar min da book na barki da Allah!."*_


Accont numbar
*0542382124..... Binta Umar GT bank*

My numbars
*08089965176_07084653262*

17


Kulu da Fulani mari suka cigaba da zama cikin fahimtar juna don a yarda kulu take nunawa komai ya wuce kuma duk an zama d'aya ko da Fulani ta samu ciki Kulu bata nuna wata damuwa ba murna tayi sosai tayi ruwa tayi tsaki kan kula da lamarin Fulani da yaron cikinta da kanta take shiga kicin ta yi girki lafiyayye ta kai harsashen Fulanin sai ta tabbatar taci sannan take dawowa gurin ta mai Martaba yayi ta murna da farin ciki.

Ranar wata asabar Fulani gama cin abincin ta kenan Wanda Kulu ta hado mata towon alkama miyar kubewa busasshiya taji nama da man shanu dake towo kawai take iya ci Lokacin Kulu ta bar sashen wani irin ciwon ciki da Mara ya murda mata ta rike cikin cikin tsananin jin azabah ta mike tsaye lokaci gudu wani irin jini ya tsinke mata kamar an kwance famfo dai-dai lokacin ne Jakadiyar ta ta shigo Palo ganin halin da Uwar dakinta ke ciki yasa ta sanya salati da gudu ta nufi sashen Kulu lokacin ita kuma tana zaune hannunta rike da waya landline tana waya da 'kawarta sai kyalkyala dariya take...... Ganin Jakadiyar da shigo a gigice yasa ta dago kanta cikin tsawa tace"Ke baki da hankali ne zaki shigo min guri a guje." Jakadiya tace"Ranki ya Dade ki gafarce ni Uwar d'akina Fulani babu lafiya gatacan tana zubda jini." Kamar gaske kulu ta saki telephone din hannunta ta saka ihu!!! Fadi take "Jiki ganinan zuwa kai! Innalillahi wa'ina ilahi raji'un! Maza kuje Ku Sanar da mai Martaba halin da ake ciki." Jakadiya ta futa a guje Kulu ta koma ta zauna kan kujera tana sakin wani irin murmushi telephone din ta dauka ta gyara ta sake kiran kawarta Habi..... Wata irin dariya suka kwashe a tare Kafin Kulu tace"Ke komai ya faru fa don yanzu na samu labari cewar gatacan tana zubda jini." Habi tace"Ke dai bari nasan dama Wannan maganin k'arshe ne ko yan goma ne a cikinta sai sun zube shegiya maga cikin da zata haihu dashi." Kulu tasa dariya tana fadin"Bari in barki haka sai anjima yanzu zan nufi gurin algungumar ne." Habi tace"Allah yasa kafin kije ta margaya." Dariya suka kwashe da ita kulu ta kashe wayar ta aza mayafi a ka ta nufi sashen Fulani tana hawaye

Ganin jinin dake zuba jikin Fulani ya dan so ya bata tsoro wata zuciyar tace "Kada kiji tausayin ta idan ma mutuwa zatayi gwara ta mutu kan a haifi wannan cikin..... Ta karasa cikin damuwa da tashin hankalin take kokarin kama Fulani wacce ta galabaita don har ta fara jiri saboda yanda jinin yake zuba..... Ta kamata ta mike tana kallon Jakadiya tace" INA fatan kun Sanar da mai mart..... Kafin ta karasa ma dai gashi ya shigo hankalinsa duk a tashe suka rirrike Fulani suna kokarin tafiya ita dai-dai Lokacin ta cije ta kasa takawa take ta zube a gurin tayi wani yun'kuri wani Abu ya fado to tun daga fad'owar abun bata sake sanin inda kanta yake ba jini ya kece mata.

Hankali a tashe Sarki da kansa ya dauketa cikin gaggawa suka nufi asibiti mai zaman kasa, ganin halin da take ciki ya sanya likitoci rufuwa a kanta domin ceto lafiyar ta Hankalin duk Wanda ya kwana ya tashi a gidan yana a tashe banda kulu da take jin zuciyata kamar takarda tunda ta tabbatar cikin ya futa ta kwantar da hankalinta taba da umarin a gyara palon sannan ta futa ta sanya aka samu kwali aka dauke Dan tayin Wanda yake kamar kadangare wai dole sai ta nunawa sarkin don taga halin da zai shiga.
Asibitin ta bisu tana addu'ar Allah yasa kafin taje Fulanin ta mutu tabbas da tayi farin cikin haka.


Cikin ikon Allah aka samu nasarar tsayar da zubar jinin bayan sunyi binkicen su sun tabbatar da cewa cikin ya futa babu wani saura.


Tunda ya samu labarin zubewar cikin yake kukan zuci yayi mutukar Dora ransa kan cikin yana murna Allah yayi masa kyauta Wanda ba kowa yakewa irinta ba.... Addu'a yayi a fili da zuciya kan Allah yasa haka shine yafi alkairi Allah kuma ya bashi wani mai amfani.


To ko da Fulani ta dawo nutsuwar ta da taji labarin futar cikin ta shiga halin damuwa mutuka daga k'arshe sai ta barwar Allah tana ganin shine ya bata kuma shine ya karbi abunsa..... Lokacin idan kaga kulu zaka dauka duk tafi kowa shiga damuwa domin bini Bini sai ta share hawaye tana fad'in"Allah dai ya bamu wani cikin gaggawa amma mun sanya rai gaskiya." Mai Martaba da ya lura tana nema tayi sa'bo take ya tsawartar mata kan cewar abunda take ba dai-dai bane duka su barwa Allah lamarin sa


Satin Fulani daya a asibiti ta samu lafiya garau suka dawo gida cike da kulawar ma adalinin sarki. Kauna ko da so Fulani ta gani ta ko wane b'angare haka aka dunga turereniyar zuwa dubata asibiti.


To bayan dawowar ta gida zama suka cigaba dayi kamar da duk Wanda zai gansu bazai CE sun hada miji ba saboda yanda suke zaman mutumci da juna...... To ance rabon wani shi ke korar na wani Fulani ta sake samun ciki Wannan karon ma Kulu ta dunga murna da farin ciki komai Fulani take so kulu ke hidimar girka mata bata bari wata baiwa ta sanya mata hannu a ciki sarki ma yayi farin cikin samun karuwa yana addu'ar Allah ya bar masa wannan. Abun mamaki tun ba'aje ko ina ba ciki na da wata uku ya 'bare kamar na farko wannan karon Fulani tayi kuka Sosa don ta kwallafa ranta akansa, Sarki ne yayi ta rarrashinta duk da shima yana cikin halin rashin dadi daurewa kawai yake a matsayin sa na namiji.

Haka rayuwa ta cigaba da gudana gidan sarautar yau da dai gobe babu dadi Ga Fulani yawan 'barin da take ya soma damunta don a 'kalla yanzu tayi 'bari sau uku don haka sai ta fara Neman magani gami da addu'ar tsare jikinta tana tunanin ko harda shaidanu cikin lamarin.

Ranar wata laraba jakadiyarta tazo ta sameta zaune ita kadai ta zurfafa a cikin tunani tace"Ranki shi Dade ina da wata yar shawara da zan baki Allah yasa banyi laifi ba kuma ina fatan zaki dauketa da muhimanci. "

.Fulani ta gyara zama tana kallon Jakadiyar tace"Ina sararonki jakadiya ki fadi ko wace irin shawara ce."


Jakadiya tace"Ranki shi Dade nifa na soma zargin Kulu mai dakin kusurwa da wannan abun dake faruwa dake na yawan zubewar ciki a gaskiya jikina na bani da sanya hannunta a cikin lamarin.



Fulani tace"Jakadiya zargi babu kyau haramun ne har ga Allah ni bana zargin kowa nafi tunanin al'amarin daga Allah ne.'"

Jakadiya tace''Ranki ya Dade ban tari numfashin ki ba ki gafarce ni don Allah ki tsaya ki saurari shawarar da zan baki."

Fulani tayi shiru tana tunani cikin zuciyarta tace"Ba'a kin ta mutum wani sai ka raina shi baka san baiwar da Allah yayi masa ba. Don haka sai tace"Ina sauraron shawarar ki."


Jakadiya tace"Idan kika sake samun ciki ki daina ci da shan duk wani Abu da zai futo daga hannun kulu ina ganin tanan zamu gane ko daga ina matsalar take."!! Fulani tace"Ni kam Jakadiya bana so kike zargin kulu da cutar dani."


Jakadiya tayi murmushi tace"Ranki ya Dade kenan na lura har yanzu baki San mutane ba wallahi na rantse miki da Allah kulu ba da zuciya daya take zaune dake ba, kawai Don kina zaune da ita tsakanin ki da Allah yasa ubangiji yake kare ki daga sharrin ta amma idan akwai wacce ta tsana a duniya to kece."



Fulani tace"Ya isa Jakadiya na dauki shawarar ki insha Allah kuma zan gwada na gani." Jakadiya tace"Nagode K'warai Ranki ya Dade in yaso duk abunda kike son ci ko sha sai ki sanar dani in hada miki."

"Insha Allah haka za'ayi." Tafad'a tana tunanin maganar tasu babu shakka mutum mugun ice ne ka amince masa ya ha'ince ka."



****
Wannan karon cikin da ta samu ba mai laulayi bane don haka sai da yayi kwari wata hudu sannan Kulu ta lura dashi aikuwa ta shiga tsanani. Damuwa take suka bazama ita da Habi suka sake karbo magani tazo tana shirya abinci babu dare babu rana tana kaiwa fulani.


Fulani

3 Comments On SADAUKI OMAR
avatar
auwal-mohammed

1 year ago

Reply

It nice book to read ????

avatar
hafsat-9-3

1 year ago

Reply

Very nice biik

avatar
hafsat-9-3

1 year ago

Reply

Very nice biik

Please Login or Register in order to submit comment