Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Ta doki kasan gurin da hannunta Cikin jin rad'ad'in zafi ta dago hannayen nata tana dubawa.... Hawayen bakin ciki na zubo mata take fadin"Ni wannan bawan yayi wa wannan yankar kaunar? Wallahi bazan yarda ba."!! Tafad'a tana durkushe wa a gurun tana wata irin shashshekar kuka.


Ikilima dake tsaye bakin kofar gurin taga futowar sa da sauri ta zube kasan gurin tana gaishe shi sama-sama ya amsa ya sa kai ya wuce zuciyarsa Sam babu dadi.


Da sauri ta mike gabanta na fad'uwa ta shiga cikin gurin can ta hango Ayshe durkushe ta hada kai da gwiwa jikinta babu kaya.... Jiki na rawa ta karasa gurin tana fad'in"Ranki shi Dade lafiya."?

Lokacin da ta d'ago kanta sai da ta tsorata ganin yanda idanunta sukayi jawur saboda kuka da tsananin baciin rai."

Baki na rawa Ikilima tace"Ranki shi Dade ina fatan dai baiyi miki komai ba ko."? Hannu ta daga mata muryarta na rawa tace." Mik'o min kayana gasu can zube."

Da sauri taje ta dauko ta kawo mata, a galabaice ta mike jikinta sai kyarma yake kayan take kokarin sawa amma ta kasa hannunta sai rawa yake Ikilima tazo ta taya ta sanya kayan Hannunta ta rike suka futa daga gurin suna isa shashen ta ta shige bedroom dinta kwanciya tayi kan gado ta bude shafin bakin ciki. Ikilima kuwa jikinta ne yayi sanyi tana jin tsoron Allah yasa ba wani abun ne ya faru tsakaninta da Omar din ba.

Firgigit! Ta mike zaune!!! *"Idan kika kuskura ki ka sake rungumeni sai na karya ki, shashashar mace Mara kamun kai."* Kalmar da take tayi mata yawo a kanta kenan.... Kamar mahaukaciya ta sauka 'kasa gaban mudubi taje ta tsaya tana kallon jikinta tasan ita din macace mai kyau da kyawun sura irin kallon kyamar da ya dunga yi mata yayi mutukar tashin hankalin ta meye aibu a tartare da ita wane irin rashin kamun kai tayi wato yana so ya 'bata mata suna da wannan Kalmar tasa, babu sata babu maita babu zina babu rashin Asali ta ko wanne fanni ta cika mace amma shi yana kiranta da shashasha Mara kamun kai."!!! Wani irin watsi tayi da kayan shafar dake Jere reras! Kan k'aton mudubin ta suka tarwatse a gurin na fashewa ya shafe na zubewa ya zube.... Kafarta ta sanya ta taka wata k'aramar kwalbar turare wacce ta fashe take jini ya soma d'iga b'acin ran da take ciki bai sai ta damu ba, kofar futa ta nufa tana dingisawa."!! Hawaye duk ya bushe mata a fuska.... Hadimanta dake zaune suka mike da sauri ganin ta futo cikin futar hayyaci! Ikilima itace mafi kusa da ita don haka itace ta karasa inda take tana rirrike ta, tace." Ikilima muje Fada."!! Tace"Allah ya baki nasara haka zamu je fada fuskar ki ta b'aci ga kafarki na digar da jin...... Wata razananniyar tsawa ta kwatsa mata "Zaki wuce muje ko sai na sa'ba miki." !! Kasa tayi da kanta cike da ladabi tace." Allah ya huci zuciyar ki. "! Gaba tayi ba tare da ta saurare ta ba Da sauri ta bi bayanta suka futa daga parlon.


****

Da Jan 'Kafa suka isa Fadar... Sai da suka zo shiga ne ta Ankara dashi yana dogare bakin kofar da sauri ta dauke kanta gabanta ya bada sautin rugu-rugu!!! Yanzu ta fara tunanin abunda zata fadawa Sarki game da Omar din. Shaf ta manta da cewar na hannun damar sa ne..... Galidima ya hangota zata shigo gashi kamar ma a jigace take. Mik'ewa yayi ya isa bakin kofar wani irin kallo ya wa tsawa Omar din yace." Kai gwani na iya! Kana ganin za'a wuce ka tsare kofa ko ba ganin halin da take ciki ne."!? Omar ya matsa daga gurin yana me sake yin kasa da kansa cikin girmama wa ga Galadiman..... Hannunta ya rike yana fadin"Ke lafiya ciwo kika ji me kika zo yi a fada."!! Shan majina tayi tana kokarin hana hawayen ta zubo wa saboda Omar din tace." Na kawo 'kara ne gurun Mai martaba." Yace." Sai ki wuce cikin gida bai futo ba tukkuna. "! Tace." Baba Galadima kaima zaka share min hawaye na ko."!? Yace." K'warai kuwa." Tana kuka tace." Wannan babban bawan ne ya fasa min glasss a kofar sashena ina futowa na taka kawai saboda ya tsane ni Ikilima ko ba agaban Ku jiya yace Sai ya lahanta ni ba Gabanku ya kirani da Shashashar mace Mara kamun kai."!! Baba Galadima ka duba lamarin da kyau! Bawa ne shi ni kuma 'yar gida ce duk da nasan yana da d'aurin gindi gurin sarki! Yana da kyau! A karbi k'orafi na.""!!

Ikilima tayi tsilli-tsilli jin irin 'karyar da Uwar dakin nata ke shigar wa duk dai bata San abunda ya faru tsakanin su amma tasan abunda Gimbiyar ta fad'a tsari ne kawai.


Nashi 'b'angaran ma hakane sosai yake mamakin sharrin da ta shirya masa 'kasa yayi da kansa don ganin irin kallon banzan da Galadima ke watsa masa.

Yace." Shin da gaske take abunda ta fad'a ka saka glasss kofar dakinta kuma ka fad'a mata Wannan mummunan kalamomin."!? Omar yayi shiru bai ce komai ba a Dan fusace! Galadima ya sake magana "Ba magana ake da kai ba."!!? " Gyara kintsi dai."!! Saurin Muryar Wani bafa de kenan.... Take suka shiga hankalinsu. Galadima ya koma cikin fada ya zauna ransa duk a bace yake idan Abunda Aysha ta fada a zama na gaskiya ne to babu shakka shi da kansa sai ya dauki mataki kan Omar din Idan har mai Martaba ya kasa daukar mataki a kansa.... Kansu a kasa sarki yazo ya wuce suna mik'a gaisuwa. Bayan shigewar sarki da kamar minti biyar magana takarda ya futo domin Sanar dasu sarki yace su shiga yana son ganinsu.


Kusan tare suka shifa Aysha gabanta sai fad'uwa yake tasan halin sarki baya daukar raini ki kadan a hankali ta d'ago kanta ta saci kallon Omar din sai taga yana rarrafawa gaban sarki ya zube hannunsa a sama a lamun jinjina yake haka suka gaisa sarki ya Dora hannunsa saman kansa yana murmushi

Cikin zuciyarta tace"Babban munafiki me ladabin karya. A hankali ta karasa gaban sarkin ta mik'a gaisuwarta ta dawo ta zauna inda take..... Omar kam yana kusa da k'afafun sarkin saboda tsabar samun gurin zama ji tayi jikinta yayi sanyi ta fara da ta sanin zuwa fadar tasan da kyar in zata samu nasara.






5/3/2020

*BINTA UMAR ABBALE*
[3/12, 10:31 PM] Bintu: *SADAUKI!!🏹*
_OMAR💫👑_




*_Ga masu bukatar karanta littafin zasu tura #300 ta Wannan accont din......0542382124... Binta Umar GT bank.... Idan kuma katin waya zaka tura sai ka same ni ta wannan numbars, 08089965176 _07084653262 Zan Sanar da kai yanda zaka biya kudin..... Mutanan Nijar idan suna bukata zasu tura dala dari ta wannan numbars 90899076_88137740 Katin airtal ko orange dala Dari itace a madadin Dari uku kudin Najeria.*



Free pege
7



''Fada tayi shiru kafin Mai Martaba yayi gyaran murya a nutse ya kalleta yace. " Nana Aysha mai babban suna Aysha matar manzon Allah (saw)ta hidimtawa ma'aiki tayi bautar aure taso manzon Allah so me tsarki Aysha ina fatan kiyi koyi da halayen Uwar muminai Nana Aysha." Tayi 'kasa da kanta cikin sanyi jiki kusan da ko wane lokacin idan zama ya had'a su da Sarkin sai yayi mata wannan nasihar.

Sarki ya cigaba da cewa"Yanzu ina zama Dan uwana ya Sanar dani abunda yake faruwa gaki ga Omar din sai ki fada min korafin ki a kansa yau fada zata fara sulhu akan Ku."


Muryar ta na rawa tace"Allah ya baka yawan nasara da tsawon rai me amfani."!! Fadar ta amsa da "Ameeeen!."" Ta cigaba da cewa"Dama ina so Abi min hakkina kan wannan baw....... Zata karasa Sarki ya katse ta ta hanyar fadin" Ashsha! Aysha wannan kalma ta daina futowa daga bakin ki Omar ba bawa ne a cikin masarautar nan tuntuni na 'yan tashi ya zama mutum mai 'yanci da iko saboda haka kada in kara jin kin kirashi da wannan suna."

Taji zuciyarta ta tsinke tana ji ma kamar ta tashi ta tafi tun ba'aje ko ina ba ta soma fuskantar matsala."

Yace."Ki cigaba da jawabin ki."! Cikin INA!INA! Tace." Dama na kawa kararsa ne don min yana jifana da mugwayen kalmomin yana kirana da lalatacciya Mara tarbiya dazu kuma ya zo kofar d'akina ya fasa glass na fito na taka Yanzu haka akwai glass cikin kafata guda."!


Sarki yace." Abunda kika fad'a daban da Wanda Dan uwana ya fada min Omar kai fad'a min gaskiyar abunda ya faru tsakaninka da ita." Aysha da galadima ransu yayi mugun b'aci wato ta tabbata kenan bai yarda da maganar su ba ta Omar din ce gaskiya saboda shine Wanda baya karya lallai al'amarin babban ne.


Omar ya gyara zama a nutse yace." Allah ya baka nasara da tsawon rai me amfani." Fada ta amsa da "ameeen."! Ya cigaba da cewa" Abunda ya faru tsakanina da ita shine......... Tiryan tiryan ya fada masa abunda ya faru dashi da ita can bayan gidan...... Rai a 'bace yake kallonta kafin yace." Aysha Ashe baki da d'a'a Ashe baki da kunya?? Kuka ta farayi tana shakar hanci da ta sani kawai take na zuwa fadar Sarki yace." Banga laifin sa ba don ya kira ki da Mara nutsuwa shin wai ma me ya shigar dake wannan gurin da yake da hadari! Tayi shiru rai a bace ya cigaba da cewa"To daga yau sai yau kar ki 'kara zaginsa karki 'kara kiransa da Wawa! Bawa makasanci ki bar ganin kina cikin gidan sarauta to watak'ila shi din da kike kira da wad'annan sunaye ya fiki daraja don haka ki kiyaye da magana ta."Tana kuka take fadin"Allah ya huci zuciyarka."! Yace." Bashi hakuri kafin in sallame ki."! Galadima ya kalleshi ransa duk a bace girgiza kansa kawai yayi hukuncin da ya dauka Sam baiyi masa ba. Sanin da tayi da cewar Sarkin baya maimata magana yasa ta kalli Omar din hawaye na zubo mata tace"Yi hakuri."! Mai Martaba yace." Sunansa zaki kira ki bashi hakuri.... Tace"Omar! Yi hakuri." Wani irin yanayi yaji a jikinsa lokacin da yaji ta ambaci sunansa *Omar!* kamar a bakinta a ka rad'a sunan. Yaji wani irin motsi da 'kasan keyi sha'awa na ta so masa abun ya bashi mamaki K'warai da gaske ya kasance saboda tsananin jarumtar shi da tsantsenin sa yasa kwata kwata baya tsayawa yayiwa mace cikkaken kallo saboda kar ya d'arsa wani Abu Cikin ransa yana ganin mata duka kayan damuwa ne gani yake zai iya rayuwarsa shi kadai a haka amma ganin da yayiwa Aysha a dazu ya sauya masa tunaninsa jin muryar ta a yanzu ya sanya yana jin wata gawurtacciyar sha'awa na yunkuro masa.


Mai Martaba yace." Yanzu kina iya tafiya amma kafinan ina fatan kin dauki nasihar da nayi miki ina so kiyi min alkwarin baza ki kara ba daga yau."

Tace." Insha Allah zan kiyaye." Yace." Allah yayi miki albarka." Maga takarda yace." Zaki iya tafiya Gimbiyar mata Sarki! Ya sallame ki." Ta mike jikinta babu kwari ko na kwabo.

Omar ya nemi izinin tafiya sarki! Ya hana shi yace." Ya zauna yayi zaman fada shima Omar yaji dadin hakan don haka sai ya zauna aka cigaba da tafiyar da al'amuran fada dashi.

*******

Washe gari ta kama Juma'a ce tun safe ma'aikatan gidan ke aikace-aikace Omar dama akinsa kula da dokona ne yana gama kula Dana sashen su ya futo ya nufi wani keban taccen fili Wanda dokona ke daure a gurin sun kai su Dari ko sama da haka d'aya bayan daya ya shiga ya dudduba su ya basu abinci da ruwa ya futo daga gurin wanka yake so yayi domin ya futa bakin masallaci yaga abunda yake wakana a gurin duk da cewa akwai jam'an tsaro sosai hakan baya hanashi kaikawo tsakanin masallacin da Cikin gidan duk domin a samu a sallaci sallah juma'a ba tare da wata tarzoma ta tashi. Yana daf da shiga sashen su Ikilima da Atika ne tsaye duk suna cikin kaya irin daya da alama uniporm ne hannunsa rike da tsintsiya sai kus-kus suke suka hangi tawowar sa da sauri ko wacce ta kama aikin gabanta yana zuwa gurin ya bata fuska kamar zaiyi magana sai kuma ya FASA ya wuce sai da suka ga shigewarsa sannan suka saki ajiyar zuciya Atika tace"Zo mu bar gurin nan. " hannunta taja suka bar gurin suna tafiya suna kara maganar Ikilima tace"Allah da gaske nake lokacin Dana shiga gurin babu kaya a jikinta shi kuma naga ya futo daga gurin."

"Ikilima ki daina wannan zancen ina ji zuciyata kamar zatayi binduga kishi nake wallahi ina sonsa da gaske." Ikilima tace"Atika ki kama kanki fa bana son wani Abu ya faru dake."

A Dan fusace! Tace"Kamar yaya? Shin ban kai matsayin da zai aure ni ba? Kar ki manta fa da cewar matsayinmu daya dashi a cikin masarautar nan bawa ne nima baiwa ce gwara ni akwai iyayena cikin gidan shi kuwa fa? Ikilima tace"Duk da haka dai ki kama kanki kin San yafi mu 'yanci a gidan." Atika tace"Aikuwa ina son sa bazan cuci kaina ba idan ta kama ma na fada masa zai fada masa ne." Girgiza kai Ikilima tayi tace"Shikkenan ai." Can cikin gidan suka nufa suna cigaba da maganar.


****
Tsaf ya shirya cikin wani farin yadi mai sauki kudi dinki Riga da wando rigar tazarce har kasa da botira hannun matse da links yanda yadin yayi masa kyau sai ka dauka da cewar me tsada ne saboda yana ya amshi jikinsa takalmi rufaffe ya sanya kafafunsa ya dadura kwallinsa a ido k'wayar idon ta kara girma da shek'i saukakken turaran shi ya fesa ya sanya takalmi baki mai gidan ya tsa a nutse ya futo hannunsa rike da carbi mai maddanai babbar kofa ya nufa domin futa daga gidan.


Tana tsaye jikin window ta hangi futowar sa tun da al'amarin ya faru ta kasa samun nutsuwa haka ta kwana batayi baccin kirki ba tsabar bakin ciki da damuwa kasa dauke idonta tayi da kansa ta dinga kallonsa yana tafiya a nutse bayin dake aikace-aikace a gurin suna ta gaishe shi sai kace wani basarake! Tsayawa yayi suna magana da Yunusa jikinsa ya bashi ana kallonsa yana d'aga kansa ya hangeta jikin tagar dakinta cikin wata irin rikar bacci cotton ta futo mata da shatin jikinta gashin ta duk a hargitse da sauri ya dauke kansa yana Jan tsaki. Ita bata kunyar futo da jikinta waje. Itama tana ganin sun hada ido ta saki labulen komawa tayi tq zauna kan gado ta rufe fuskarta da tafikan hannaye ta wani irin ciwo kanta yake mata babu irin tunanin da batayi ba akansa na yanda za'ayi ta dauki mataki idan ta tuni nasihar mai Martaba sai taji ta sare amma fa ta dauki alwashin komai daran dadewa sai ta rama wulakacin da yayi mata.

****

"Safara'u kina ina ne."? Ke Safara'u!!! Yarinyar da aka kira da wannan sunan ta futo daga wani daki wanda ko labulen arziki babu tana zumb'ura baki tazo ta tsaya gabansa " Gani."!! Ta fad'a kamar bata so." Hannu yasa yana laluben sandar sa yace." Kina sane da cewar yau juma'a ko? Jikina na bani lokacin sallah ya gabato."! Hannu ta sa ta dauko masa sandar tasa ta mik'a masa tana fad'in" Baba kai ba ido ba kace dole sai kaje massalaci ni wallahi yau bazan maka jagora ba ka tafi kai kad'ai."!!! " Buhun Ubanki! Safara'u."! Ya fada yana kokarin kai mata duka da sandar duk da baya ganinta yace." Sallahar juma'ar kike min bakin ciki na samu." Tace"Ni baba ba haka nake nufi ba kawai nafi son ka daina yawo ka zauna a gida Yanzu idan muje massalacin nan haka mutane zasuyi ta baka sadaka kana 'kar'ba kamar almajiri." Yace." Safara'u!! Zanci kaniyar ki fa! Mik'o min buta in d'aura alwala zuwa massalaci babu fashi." Ta wuce tana kunkuni "Ni nagaji kawai mutane sai su dinga baka sadaka kana karba ni kuma jama'a nayi min kallon yar jagora ni dai Umhum! Umhum!!! Kunkuni take tana so tayi kuka." Yace." Karkiyi kuka Safara'u nayi miki alk'awarin yau bazan tsaya karb'ar sadaka ba ana idar da sallah sai mu tawo gida.".

Ruwa a buta ta mik'a masa ya fara alwala tace"To naji dadin haka baba bari inyi sauri inyi wanka." Yace." Maza kije kiyi gashi nan ana kiran farko." Ruwa ta jawo a rijiya ta shiga band'aki minti biyar har tayi jika-jikanta ta futo." Dakin da ta futo dazu ta shiga tana shirya wa Safara'u yarinya 'yar shekara goma sha uku kenan yar Fulani me tsamurmurin jiki abun mamaki tana da Wannan k'ananun shekarun har ta fara kirgan dangi gashinan sunyi car-car dasu Riga da siket ta dauko na wata kodaddiyar atampa yaluwa ta dauko siririn mayafi da tattare ta yafa tana futowa ta taddashi a tsaye yana lalabar bango bulallan takalmin ta tasa ta kama sandar ta tsaya ya sanya takalmisa sannan suka futa daga gidan a bude suka barshi sanin da sukayi babu wani kayan arziki a cikin gidan. Sai tsummo karansu.



Duk Wanda zai shigo massalacin kan idonsa yana dogare bakin kofar shiga hannunsa rike da wata k'atuwar gora idan ka kalli fuskarsa zakayi tunanin bai taba dariya ba tunda Allah ya hallice shi. Kan idonsa suka shigo massalacin tana Jan Sandar tana surutai da kunkuni hangoshi tayi tsaye bakin kofar shiga tace"Baba ga Wannan katon mutumin nan a tsaye a bakin kofar shiga cikin massalacin wallahi zan juya ni kam ka shiga da kanka tsoransa nake." Yace." A'a Safara'u daure ki shigar dani." Sakin sandar tayi ta ruga da gudu.... Sai ya fara lalube lalube yana kiran sunanta Omar da duk abunda yake faruwa kan idonsa sai ya tawo da sauri ya kama Sandar ganin yana Neman fad'uwa. Yace." Yawwa yar albarka duk da bana ganin wannan k'aton da yake furgita ki naji dadin samunsa a wannan gurin nasan zai kawo tsaro da samun nutsuwa a gurin Allah ya biyashi da alkairin abunda yake." Omar dai shiru yayi masa ya shigar dashi Cikin massalacin kebantaccen guri ya aje shi sannan ya koma bakin aiki. Yana mamakin wannan wace irin 'yar jagora ce Mara hankali


Sarki ya futo yayi hud'uba kamar yanda ya saba lokacin tada sallah nayi ya tada ikama guri yayi tsit!!! Cikin nutsuwa da kwamciyar hankali aka idar da sallah sarki yayi masiha da addu'oi kafin kowa ya fara kokarin futa daga cikin massalacin Omar kwata-kwata ya manta da Wannan makahon hankalinsa na kan jama'ar dake futowa ta kofofi gaba da baya.... Hayaniya ya jiyo daga cikin massalacin ya shiga da sauri yana kutsawa Cikin mutane kafin ya isa gurin yaji wani yana fad'in"Innalillahi wa'ina ilahi raji'un! Ai ya mutu ." Da sauri ya isa gurin kawai sai yaga Wannan makahon kwance a 'kasan gurin gabansa ya fadi da sauri ya d'ago shi ya Dora a jikinsa yana dubushi tabbas babu rai a jikinsa, nan ya soma tambayar ba'asi wadanda suke kusa dashi a zaune suka ce yazo tashi ne kawai ya yanke jiki ya fadi a gurin Shikkenan rai yayi halinsa...... Kafin kice kwabo labari ya isa kunnen Sarki Wani makaho ya mutu. Sarki da kansa yazo ya ga abunda yake faruwa take ya sanya Omar din daukar shi ya shiga dashi cikin gidan domin a suturtashi jama'a suka futo suna jajanta al'amarin.

Tana tsaye jikin wata k'atuwar bishiyar darbejiya tana jiran futowar sa tunda yake sallah cikin massalacin bai taba samun nasarar shiga ciki ba a waje yake samun guri shiyasa Daga an idar take zuwa ta kamo hannunsa Yanzu kuma tunani take ta wace kofa zata shiga asalima bata San ta wace kofa ya shiga ba da ta sani take tayi masa shimfid'a a waje kamar yanda ta saba.

Duk Wanda zai wuce ta gabanta sai taji yana fadin "Allah sarki Allah ya jikansa. Bata kawo komai ba ta dinga waige-waige ko zataga irin abokanan sa da suke zama guri daya a massalacin bata ga kowa ba, wasu dattijai ne suka zo wucewa taji suna fadin" Allah Sarki Malam Abdu Makaho lokaci yayi Allah ya jikansa ai yayi shahada." Taji gabanta ya fadi *Malam Abdu Makaho* shine sunan mahaifinta da kowa yake kiransa dashi iya saninta tasan babu wani Makaho mai irin sunan sa Wanda jama'a ke kiransa shi. Duk da take da k'ananun shekaru sai daji wata fargaba da tashin hankali ta nufi kofar massalacin tana sharar hawaye Allah yasa ba Babana ne ya mutu ba abunda take fada cikin ranta kenan.








5/3/2020

*BINTA UMAR ABBALE*
[3/12, 10:31 PM] Bintu: *SADAUKI!!🏹*
_OMAR💫👑_




_*Ga masu bukatar karanta littafin zasu tura #300 ta wannan accont din.....0542382124 Binta Umar GT bank.... Idan kuma katin waya zaka tura sai ka tuntu'be ni ta wannan numbars .....08089967176.....07084653262 Insha Allah zan fada maka yanda zaka biya kudin... Mutanan Nijar Idan kuna bukata zaku tura dala Dari ta wannan numbars....90899076 _88137740 Katin Airtal ko Orange Daka Dari itace a madadin Dari uku kudin Najeria.*_


Free pege

10


"Aysha!! Ki nutsu ki daina wannan shirmen gaban bayin ki Na yarda daga yau nima bawan ki ne komai kika umarce ni zanyi mutukar zaki bar wannan yarinyar ta sake a cikin gidanan a shirye nake da na kwanta ki taka ni in dai kan Safara'u ne ni me yin komai ne na yarda ni din bawa ne makaskanci a gurin ki yanzu ki fadi me kike bukata nayi miki."!!! Cikin wata sanyayyiyar murya yake mata magana..... Duk da tana cikin wani yanayi me wahalar fasaruwa hakan bai hana ranta b'aci ba jin cewar da yayi kan yarinyar babu abunda bazai iya ba wato ta tabbata kenan ba a karan kansa zai yi mata bauta ba sai kan banzar yarinya Yar Makaho, ture shi tayi ta sauka daga jikinsa ya bita da wani sihirtaccan kallo cikin k'irjinta na mutukar bashi sha'awa wannan rungumar da yayi mata ita ta tabbatar masa da cewar shi din lafiyayyan namiji ne."

Tattare da b'acin rai a tare da ita ta dauki alkyabar ta ta sanya bata son kallon idonsa saboda halin da take ciki ta goge fuskarta kadan tace" Idan don wannan kucakar yarinyar zaka yi min bauta bana so idan kana so in barta tasha ruwa a cikin gidanan to kayi min bauta don karan kanka ba don wata banza ba." Ya mike tsaye hannayen sa cikin aljuhu yace." Naji Zan zama bawan ki amma nima kiyi min alk'awari daya." Ya mutsa fuska tayi yace." Ki tayani kula da amanata." Ya fada yana rik'o hannun Safara'u dake tsaye a gefe tana kallonsu idonta da busassan hawaye...... Aysha ganin yanda yake murz hannun Yarinyar ya sanya kishi ya karci zuciyarta hanyar fita ta nufa tana jin zafi cikin zuciyarta tunani take ma kan wane dalili take jin haushi idan ya kusanci yarinyar.... Sai da tayi nisa da tafiya yace." Baki bani amsa ta ba." Ko Wai wayo shi batayi ba ta fice Ikilima dake dakon futowar ta ta rufa mata baya.


****

"Hahahahaha!!." Sautin wata mahaukaciyar dariya na jiyo da sauri na kutsa kaina Cikin palon Mai dakin kusurwa na gani hakimce kan kujera ta Dora kafa daya kan daya hannunta rike da hotona tana dubawa, sai saki murmushi take kana ganinta kasan tana cikin farin ciki da annushuwa......"Gaskiya tafida baka taba faranta min rai irin yau ba, nayi mutukar jin dadin ganin wannan hotonan na tabbata zasu rusa farin cikin kowa a cikin gidanan Tafida dole ne inyi maka kyakyawar sallama." Tafida yayi kasa da kansa yana murmushi yace." Allah ya baki nasara ai ban tsaya sanya ba ina sanya ido kan komai nake fada miki ina ganin shigarta gurin na bi bayanta cikin ikon Allah na samu wata kafa na la'be nan na aiwatar da aikina." Mai dakin kusurwa ta mike tana fadin"Jira ni na dawo. " yace. " a futo lafiya ranki ya Dade." Baiyo najin shigarta daki ta fito tana kallon Tafida a tsorace tace"Tafida baka jin tsoron asirinka ya tuno kasan idan Sarki ya gane gaskiyar lamarin zaka fuskanci hukunci." Yace." Kema dai Baiyo ta yaya kike ganin wannan ibilishiyar matar zata bari asirin ta ya tono ni bana wani tsoro wallahi dama ina cike da jin haushin sa Dan iska duk ya kankane komai ya fi mu fada gurin sarki Allah yasa ma sanadiyar wannan abun a Kore Shi daga

3 Comments On SADAUKI OMAR
avatar
auwal-mohammed

1 year ago

Reply

It nice book to read ????

avatar
hafsat-9-3

1 year ago

Reply

Very nice biik

avatar
hafsat-9-3

1 year ago

Reply

Very nice biik

Please Login or Register in order to submit comment