Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

rabo da gaggawa aikuwa Kulu ta kwanta tana kuka a gurin tana rokansa kan ya taimaka kar ayi auran take,lallab'ata yayi yace taje za'a taimaka mata amma dole zata bada kudi sosai aikuwa batayi kasa a gwiwa ba ta zube masa kudi masu kauri suka tashi malamin yace ta zuba ido taga abunda zai faru suna futa ya zura kudinsa a aljuhu bayan ya kirgasu yaga ko nawa ne murna yake sosai Wanda tunda ya fara aikin tsubbu bai taba kama kudi irin wannan ba kudin sun isheshi ya siyi gida yaja jari


Haka Kulu ta dunga yawace yawacen bin bokaye tana 'barnar kudi duk kan auran Fulani Mari da ta dai-dai ci lokacin da yake tashi daga fada sai ta dawo gida to garin yawace yawacen da take ne tayi gamo da bakaken aljanu suka bude mata ido take magana dasu a cewar su sunga tana shan wahala ne sun shiga jikinta zasu taimaka mata kulu ta amunce a haukanta tana ganin hakane bata son sharrin Aljani ba kullum sai sun zukar mata jini suke samun lafiya dama kuma abunda ya kawo su kenan Sam babu taimakon da zasuyi mata cutar da ita suke shine ita kuma har da ke"be musu daki idan tana son ganawa dasu sai ta shiga ta kulle ta kirasu su kuma a wannan lokacin ne suke samu su sha jininta yanda ransu yake so kafin su tafi su fada mata karya da gaskiya ita kuma ta hau kai ta zauna...... Suna ganin idan suka ce zasu ra'bi jikin Sarki ko ita Dukanin zasu iya konewa ne saboda suna da tsari a jikinsu sosai Kuma dukaninsu suna da rik'on addini da ya waita karatun al'kur'ani mai girma.

Cikin ikon Allah aka d'aura aure kamar yanda addini ya tanadar Fulani mari ta tare a d'akinta ranar kulu kwana tayi kiran Aljanu gami da banka haya'ki ta kulle dakin da mukkuli kamar sabuwar mahaukaciya tayi zir babu tufafi a jikinsa su kuma wannan damar suka samu suka dinga tsotse mata jini sai da suka sha iya son ransu sannan suka kama gabansu suka barta kwance a dakin..... Da safe ta tashi cikin mutuwar jiki dama sallah bata dameta ba sai taga dama takeyi tayi wanka ta shirya cikin kayan alfarma ta zuba gwalgwalai Kai tsaye sashen Fulani Mafi ta nufa Babbar Baiwar ta Baiyo ta na take mata baya,,,Fulani na kishigide bayinta data zo dasu sun kewaye ta tufa ce a hannuta tana ci suna hira kad'an-kad'an kawai suka ga ta shigo babu sallama, cika da kaisatar Fulani yasa jikinta yayi sanyi mutuka bata dauka haka take ba dake makira ce sai ta sanja siga ta karasa tana fadin"Nazo na kwashi gaisuwa gurin amaryata tunda ita ta kasa zuwa inda nake. "Fulani Mari ta fahimci wacece ita take ta basu umarnin su basu guri suka fita gaba daya . tace ta zauna suka gaisa a nutse Kulu tace" Kece ya kamata kizo inda nake mu gaisa amma baki zo ba shine ni nazo mi gaisa kuma mu had'a kanmu guri guda domin samar da zaman lafiya ga mijinmu." Fulani tana da labarin halayyar mata shine dalilin da ya sanya ma tayi mamaki mutuka da ganin sauyi a tare da ita tace"Ayya! Kiyi hakuri wallahi yau din nan nake so na shiga gurin ki mu gaisa ai babu komai insha Allah zamu zauna lafiya da juna." Kulu tace"Allah yasa ni zan koma sai kin shigo ko."! Fulani ta mike domin taka mata. Sai bayan tafiyar ta ne ta dawo ta zauna tana mamakin matar tsaf tana da labarin dauki ba dad'in da ta dunga yi kan auranta don haka ko da mai Martaba ya shigo sai da ta Sanar masa nashi b'angaran yaji dadin abunda Kulu tayi yana ganin kamar ta soma hankali ne Don haka ko da ya shiga sashenta sai da ya nuna mata yaji dadin abunda tayi ita kuma ta nuna masa komai ya wuce da yardar Allah.







10/3/2029

*BINTA UMAR ABBALE*
[3/12, 10:32 PM] Bintu: 18

Misalin karfe shida na safe wani matashin saurayi ya futo da niyar fara aikinsa na sharar titi tun kafin ya karaso inda take kwance yake mamaki tabbas mahaukaciyar babu inda ba 'asanta saboda tsananin yawonta garin hakane ma aka samu wani mara imanin ya dirka mata jiki da sauri ya karaso yana duddubata kafin kice kwabo mutane d'ai-d'ai ku dake wucewa kafa da abun hawa sun fara tsaya kowa na mamakin wani dattijo wanda yana daya daga cikin masu shara cikin kasuwar yace"Ya kamata a dauketa akaita asibiti ko da sauran ranta..... haka kuwa akayi suna kokarin daukarta ne sukaji kukan jinjiri cikin kwalbatin take suka duba shi din ne yake kuka yana wurga kafafunsa inda allah ya taimaka ma lokacin da ya fada kwalbatin ya tsaya kan tarin kedoji da tsummokara da ya fada cikin ruwan da yake gudana da babu shakka sai ya tafi dashi.


Wannan matashin saurayin ne ya shiga ya dauko shi kowa sai mamakin tsahon ran yaron yake take wani mai d'ab sahu yazo wucewa yaga abunda ke faruwa sai kawai ya kwashe su suka nufi babban asibitin Murtala Muhammad.


Likita na dubata ya tabbatar da cewa ta dade da mutuwa kimanin awa biyu data wuce ya futo ya sanar dasu yana kuma tambayar yan uwanta.


Dattijon mutumin nan yace." Aikin Allah mukayi dukanin mu babu dan uwanta na jini sai dai a musulunce matar ta dade cikin kasuwa taba yawo kusfa-kusfa babu wanda ya san daga ina take."


Likita ya jijina kai yana mamakin lamarin wato jaririn ma ba d'an sinna bane kenan. Yana kokarin komawa dakin ne Matashin sarauyin yake tambayar sa jikin yaron, Yace." Yaron baida wata matsalar komai sai ta yunwa yanzu haka ya samu bacci." Ya shige ciki domin ya bada umarnin had'a gawar.


A tsakaninsu sukayi shawarar yanda za'ayi da gawar matar da kuma yaron sanin da sukayi cewar gomnatin dake ci a lokacin bazata iya komai ba koda sun kai mata kukan faruwar lamarin don haka sai mutum biyu daga cikinsu suka nufi gidan Ma'adalin Sarki domin sanar masa da halin da ake ciki......... Lokacin da suka isa gidan sarautar sarki na cikin gida bai futo fada ba gurin zama suka nema domun jiran futowar sarkin.



"Mariya kiyi ha'kuri ki daina wannan kukan nasan ba halin ki bane kiyi tawakalli ga Allah shine ya baki kuma shine ya karbi abinsa kiyi hakuri kinji ko ki roki allah ya baki wani me amfani."Sarki Salisu ne yake wannan maganar.


Fulani ta share hawayen ta a hankali tace" Nakasa daurewa ne ranka shi dade wallahi duk lokacin dana tuno fuskar yaron sai naji hawaye ina tausaya maka ranka shi dade ina ganin idan babu wata matsala ka kara wani auran ko Allah zai sa ka samu dan kanka."


Sarki ya 'bata fuskarsa yana Kallonta yace"Wato ke har kin fidda rai daga rahamar Allah kenan? ba kya tunanin Allah ya baki wani da har zakiyi min maganar karin aure to ba'ayi wa allah dubara duk sona dana haihu idan Allah bai nufa ba sai in kare rayuwata haka saboda haka ki barwa Allah lamarinsa kuma kada na karajin kinyi min magana makamanciyar wannan."


Fulani ganin ransa ya baci yasa ta soma bashi hakuri da fadin"In allah ya yarda baza ta sake masa maganar ba.


Karfe goma dai-dai sarki na fada bayan gama gaishe-gaishe yasa aka shigo masa dasu suka zube suna gaisuwa sarki ya amsa musu a nutse yake tambayar su abunda yake tafe dasu.


Cikin nutsuwa suka fada masa abunda yake faruwa sarki ya jinjina lamarin kuma ya tausaya jinjirin yaron yace." maza aje azo da jinjirin yaron hade da gawar mahaifiyar tashi domin a suturta ta." Fadar ta dauki kabbara ga yabo ga ma'adakin sarki.


Cikin gidan sarki aka sallaci gawar mahaukaciyar nan aka kaita gidanta na gaskiya Sarki ya dam'ka amanar Yaron hannun Fulani ta karba tana murna da farin ciki ta fara shayar dashi nonota.


Kulu kuwa yanzu sai tayi sati bata shiga sashen fulani ba tunda abunda take so ya samu shikkenan ta dauke kafa amma duk tana da labarin abunda yake faruwa a gidan...... to ban garan fulani ma abun rashin shigowar kulu gurinta ya dameta don haka sai ta shirya tsaf! ta sanya aka shirya Omar sunan da Sarki ya rad'a masa kenan Omar yayi wata irin kiba nonon Fulani ya karbeshi sosai Fulani kuwa kullum sonsa kara yawa yake cikin zuciyarta.


Kulu na zaune kan kujera fulani ta shiga da sallama kafadarta sa'be da Omar sai kamshi suke futarwa mai dadi." Kulu ta ya mutse fuska tana fadin"Abunda ya hanani shiga gurin ki fa kenan wannan 'Dan zinar d'an mahaukaciya bazan iya shiga in ganshi ba a gaskiya fulani kinyi ganganci karbar yaron nan nice ya kamata na karbeshi amma ban karbeshi ba saboda gudun zai faru anan gaba Haka kawai domin son gwaninita akawo mana dan shege cikin gida kin dauka kin rungume.".


Fulani tace"Haba uwargida ai kya bari mu gaisa kafin ki fara yi min wannan surutan gaskiya banji dadin wannan abunba." Kulu tace"Raina ne a abace wallahi na tsani wannan yaron dake hannunki."

Rai a bace fulani tace"Kin tsane shi Allah yana sonsa ni ina sonsa kuma insha Allah zan rikeshi kamar dan cikina zan cigaba da shayar dashi nono na nan gaba ko haihuwa nayi bazai taba ganin banbanci a tsakanin sa da dan dana haifa ba, a gaskiya wannan abunda kikeyi bai dace ba a yanda mijinmu yake da tausayi da adalci ya kamata mu hadu mu bashi kwarin gwiwa bisa ga nauyin da Allah ya dora masa ni banga laifi don ya suturta wannan yaron ba baki san ko wace irin baiwa Allah yayi masa ba sai kiga sanadin wannan abu dukaninmu mun shiga aljanna don haka don Allah ki daina kiransa da dan zina idan ya taso yaji kina kiransa da wannan sunan bazai taba ganin girmanki ba har abada."" Cike da bacin rai Ta karasa maganar

Cikin fusata Kulu ta daga mata hannu tana fadin"Dakata Mariya!."!! Fulani ta tsaya tana kallonta ganin tana huci sai kace wacce take jiran kiris!! "Daga maganar gaskiya kike kokarin zagina to na fada d'an zina da d'an menene idan ba dan zina ba dan mahaukaciya waye yasan ubanshi waye yasan iya mazan da suka kwanta da uwarshi kafin asame shi da har zaki zo kina yiwa mutane wa'azin banza da wofi kije kiyi ta rikeshi din sai me mai cikin haihuwa kina maganar Allah ya baki wani d'an zaki hada ki rike to bari kiji kamar yanda ban haihu a cikin gidanan ba to kema baza ki haihu ba idan kinga kin haihu kuwa ta allah ne ya nufa." Fulani ta mike tsaye itama rai a bace tace"Gwara da kikace Allah domin shine mai bayarwa idan ya bani sai ki kwace." Tana gama maganar ta ta kama hanyar futa tana mamakin bakin halin matar Kulu ta dunga surfa mata xagi gami da gorace-gorace tayi mata abubuwa amma dake ita butulu ce tazo har dakinta tana zaginta

.Fulani futa tayi ba tare da ta sake cewa da ita komai ba..... ita kulu hankali a tashe ta mike tana le'ken Fulani da dan da ta sa'ba a kafa Tana tsaye jikin tagarta har taga bacewar ta daga gurin ta dawo ta zauna tana tunanin me zatayi mata ta huce daki ta shiga ta dauki waya ta kira Habi nan ta gama xayyane mata abunda yake faruwa Habi tace"Karki damu zanje miki gurin Ubar arna me bishiyar kuka!!!! Da ita da yaron duk sai an hanasu jin dadi."! Kulu tace"Nifa na soma zargin wani abu a game da wannan yaron anya kuwa ba danta bane ya dawo shiyasa ba naso mu kashe shi kika hana." Habi tace"Ki kwantar da hankakin ki don Allah idan ma shine ya dawo babu wata alama da zasu gane cewa dansu ne har duniya ta dane zasuyi ta daukar cewa dan mahaukaciya ne mara uba kuma Tun yanzu zamu fara aiwatar da aikinmu a kansa." Kulu tace"Nifa idan zaki bi shawarata kawai tun tafiya batayi nisa ba aka sheshi kowa ya huta."


Habi tace"Ki dai barshi kawai Ni nasan yanda za'ayi." sallama sukayi kulu tayi zugum! tana tunani karfa yaron ya girma ya zama sarki wata zuciyar tace ta ina zai zama sarki alhalin bawa ne makaskanci daga cikin bayi. haka dai tayi ta tunanin ta ina zata bullowa alamarin.


fulani kuwa na can tana hidima da Omar duk kwanan duniya yaron sake girma yake gami da shiga ranta ...... Ranar wata asabar ta wayi gari da wani irin ciwon nono mara misali ya sankame mata sosai ya hanata motsa koda hannunta ga wani irin ciwon kai da zazzabi daya zuba mata.... likita tazo ta duba ta ta bata magani tare da sharadin cewar ta dakatar da shayarwar da take domin samun lafiyarta Wannan lamari ya daga mata hankali sosai take tausayin omar tana tunanin waye zai cigaba da shayar mata dashi.... likita tace"Ranki ya dade karki damu yaron yayi kwari tunda kince wataninshi bakwai saboda haka sai a dorashi kan abincin mai gina jiki insha Allah bazai samu Matsala ba." fulani bata so hakaba babu yanda ta iya ta shiga gwadawa Omar abinci aikuwa cikin ikon Allah ya karba, nauyin kula dashi ya koma gurin jakadiya Saboda halin lakura da fulani ke ciki nonota ya motse ya bushe saboda tsananin ciwon da yake mata ita kanta tayi wata irin rama mara kyau yau da lafiya gobe babu lafiya..... haka rayuwa ta cigaba da tafiya fulani da 'yan uwanta kullum cikin neman maganin ciwon nono suke har yanzu Allah bai kawo maganinsa ba..... Wani me magani ne da yake zuwa daga azare duk ranar juma'a yake zuwa garin kano bayan an iddar da sallahr juma'a sai ya fara bada magani haka jama'a ke zagaye shi suna bada sadaka suna karbar magani......Yana zaune har inda yake alharin mai martaba ya iske shi buhun shinkafa da gishiri aka kawo masa har inda yake zaune sako ga sarki yana yabawa da yanda yake taimakon mutane kuma sarki na son ganinsa.


Ba tare da bata lokaci ba ya isa fada bayan gaisuwa sarki ya fada masa abunda ke faruwa ga matarshi na lalurarta data ki ci taki cinyewa. Wani daurin magani ya dauko cikinn wata tsohowar jakarsa ta ajiye magunguna kai idan kaga maganin sai ka raina yace"Ajika mata tasha na kwana uku ne insha Allah ta rabu da lalurar har abada." Godiya Sarki yayi masa sannan ya karayi masa kyautaka na ban mamaki yana adduar Allah yasa karshen abun ne yazo.



Cikin ikon Allah fulani na shan maganin nan ta soma samun sa'ida kwana biyu taji alamun ruwan nononta na dawowa wanda da ya zama kamar takalmi saboda ya mutsewa Kwanaki uku nononta ya ciko ya dawo yanda yake kuma bata jin yanayi mata ciwo ko kadan ranar kwana tayi tana yiwa mutumin addua..

Kulu kuwa jin labarin samun lafiyar fulani yasa ta saki dariya da shewa tana fadin"Wahallaliya ko banza na sanya ki jinya yanzu wani irin zama suke mara dadi duk dai kan Omar yaron da kulu ta kafawa kahon zuka kullum burinta ya za'ayi taga bayansa.

*****

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya duk abunda mutum yake a rayuwa to da yar dar Allah yake yinsa Omar na da shakara biyar a duniya Fulani ta haihu Da namiji duk wani sharri da kulunboto kulu tayi Allah bai bata nasara kan cikin ba ranar da ta samu labarin haihuwar kwana tayi tana kukan bakin ciki da tunanin neman mafuta gashi wacce take taimakonta tayi tafiya haka tana ji tana gani akayi shagalin suna yaro yaci sunansa Abbas. Tana kuka ta shige dakin aljanunta tayi ta kirari da kiran sunayensu su taimaketa kan halin da take ciki kuma su fadi kome suke so zatayi musu..... Umarni suka bata kan taje ta samu rago mai bakin ido amma ya kasance duk jikinsa fari idonsa baki ta nemi gidan turorowa a yanka shi a gurin idan tayi musu haka sunyi mata alkawarin duk yayan da Fulani zata haifa to zasu zama lalatattu." Kulu tayi godiya ta mike ta futa jikinta babu kwari tarasa me yasa jikinta yake mutuwa idan ta shiga dakin.... Ni ko nace suna shan jininki ne baki sani ba.


kamar yanda suka umarce ta hakane ya kasance Daya daga cikin bayin gidan tasa aka kira mata ta duka ta fada masa bukataunta sannan tace idan yayi mata duk abunda ta bukata to babu shakka zata'yan tashi zai zama daya daga cikin yaranta... Yace." ya amince kudi masu kauri ta bashi ya nufi kasuwar dabbobi domin samo kalar ragon da aljanun suka bukata.

*****

Omar ya taso da tsananin farin jini saboda kyawawan halayen sa mutun ne me rikon addini ga tsabta gami da kawaici Sai da kuma mugun muskili ne wanda yake a jininsa Omar idan ba ganin dama yayi ba sai ya kwana ya yini baiyi magana ba baya sakewa da kowa sai mamansa ko a makaranta haka yakeyi Salim dan gidan Waziri wanda Suke karatu tare yayi tajin haushinsa ganin jin kai da isa da takamar da yake yana yawa shine ya kamata yayi irinn wannan isar tunda shine dan sarauta, Salim bai san abun a jininsa yake ba, akwai ranar da ya tara abokansu yake fada musu cewar Omar din ba jininsu bane asali ma tsintarshi akayi cikin kwatami tun yana yaro a ranar Omar yasan waye shi dama kuma duk sanda zasuyi arangama da kulu takan fada masa shi din ba kowa bane a gidan face bawa makaskanci bai taba gazgatawa ba sai da yaji a bakin Salim tabbas hakane salim ba zaiyi karya ba, to tunda ga sannan wasu daga jikin abokansu suka soma sauya masa har da masu yar masa da magana. Omar yana mutukar kaunar Fulani wacce yake kira da mama, Duk wanda zai ta'ba masa mutuncinta sai inda karfinsa ya kare shiyasa kwata-kwata basa shiri da Kulu ko kad'an.... Omar yana da wata irin siffa ta mazantaka wanda ko wace mace ta ganshi zataso ta samu kamarsa kullum fuskarsa a daureta take tun lokacin da ya tabbatar da cewar shi din bashi da ala'ka da masarautar ya killace kansa amma kuma duk da haka baya yarda da raini fulani kwana biyu taga rage walwala ta zaunar dashi tana tambayarsa abunda yasa ya daina sakewa da mutane kuma ya rage walwala sannan tana tuhumarsa dalilin da sanya ya tattara kayansa ya koma sashen bayi.

Omar bai iya munafurci ba kai tsaye yace." Mama ki gafarce ni dalilin da ya sanya na koma sashen bayi saboda na gane nima bawa ne mafi kaskanci daga cikin bayin dake cikin gidanan ki gafarce ni mama banyi wannan abu domin in bata miki rai ba.

.Fulani ta fara share hawaye tana kallonsa da damuwa a tattare da ita tace"Omar Waye ya fad'a maka wannan maganar cewar kai bawa ne makaskanci." Omar yayi kasa da kansa yace."Mama bana bakin cikin kasancewata a matsayin bawa a masarautar nan zan iya kare rayuwata gurin ganin na kare kima da lafiyarku ke da me martaba saboda kunyi min abunda nake ganin har na koma ga mahallicina bazan manta dashi ba.....Tun inada shekaru goma sha biyar na gane ni din ba kowa bane face dan tsintuwa Kulu ta tabbstar mun da haka hakanan Salim ya fad'a min asali na don haka bana bakin ciki da sanin waye ni nasan tunda ina daku a duniya bani da sauran damuwa sannan ina so in nunawa jama'ar da suke min kallon dan sarki su gane cewar ba haka bane shine dalilin da ya sanya na koma cikin bayi da zama duk domin na tabbatar musu da cewar nima ina daga cikinsu."

Fulani ta dinga share hawaye tana Ala wadai da halin kulu..... koda me martaba ya samu labarin abunda ya faru ba karamin batawa kulu rai yayi ba gaban idonsa tayi ta bashi hakuri tana fadin Ya gafarce ta ita bata sanar dashi asalinsa domin ta tozarta shi ba kawai tsauysayi yasa ta fada masa maimartaba ya tabbatar mata da cewar duk da ta sanar Omar waye shi hakan bazai sanya ya daina kaunar da yake masa ba kuma bai fasa daukar sa a matsayin dansa ba." Kulu dai bada hakuri take tana kuka kamar gaske martaba na barin gurin ta saki dariya harda shewa tana fadin"Kamar wani dan cikinsa yazo yana fuffuka watakila ma shine yayi wa mahaukaciyar ciki ta haifeshi. Baiyo dake gurfane a gabanta ta dago kanta cike da mamaki tana kallonta. kulu tace"Ki kalleni da kyau Namiji babu abunda bazai iyaba. baiyo dai kasa tayi da kanta tana mamakin halin matar ta lura ta san takan sharri

****


Komai Allah yaso yana faruwa ne da izininsa Abbas da Faisal suka taso cikin halin rashin ji gami da gagara addua da saukar al'kurani anayi babu adadi sauki sai a gurin Allah........Karatu ma da kyar suka samu damar had'ashi bangaran boko kenan bangaran addini kuwa ba'a magana in banda fatiha da sauran surorin da suke 'kasa babu abunda suka iya idan kace daya daga cikinsu ya kawo maka sabbi daga farko har karshe bai iya ba.
mai martaba yana jin ciwon wannan lamarin shiyasa yake mutukar alfahari da Omar saboda shi ya futa zakka a cikinsu Omar al'kurani ne a kansa gami da hadisai da sauran littafan addini shiyasa yake da tsantseni gurin bin dokokin Allah ance dan adam tara yake bai cika goma ba Omar yana da wata dab'ia da yake yi mutukar ransa ya baci baya iya control din kansa sai ya zu'ki shisha yake jin dadin zuciyarsa bayan wannan dabi'a tashi duk cikin halayen sa masu kyau ne.



Tun ta sowar Aysha suke rigima da ita saboda 'yar dakin kulu ce tun tana yar shekara biyar kulu taje ta sakawa galadima kuka kan tana so yq bar mata Aysha a cewar ta sunan mahaifiyar tane sannan Allah ya dora mata kaunarta cikin zuciyarta ganin irin kukan da take ne yasa Galadima amincewa bukatarta Nanne bata so lamarin ba saboda sanin halin kulu me bakar aniya ga kowa tabbas idan da Galadima yasan niyyar kulu akan 'yar sa bai amimce ba. Nanne ta barwa Allah rikon Aysha ya koma gurin kulu.... Abunka da mai tsiwa dama can haka take to tarbiyar da kulu ke bata sai al'amarin ya kara tsamari Aysha ta taso da sangarta da rashin jin magana dalili kenan da ya sanya shi kama kansa amma duk da haka bai tsira ba kullum sai tazo in da yake tayi masa rashin kunya wataran ma har da zagi da gorace-gorace!! Omar bai taba kulata ba sai wata rana da ta shigo har sashen su yana motsa jiki... Siffofinsa na mazantaka sun fito fili wanda tun a wannan lokacin Aysha ta kasa gane kanta dangane da lamarinsa.

Tsaye tayi tana kallonsa bai Shi kuma yayi bala'in shan murr!! yarinyar fa tana nema ta matsamin." yafadi hakw cikin ransa yana cigaba da motsa jikinsa. fuskarsa a mugun had'e!!


Cikin tsaww!! tace"Kai dabba makaskancin bawa baka ganina a gurin ne baza ka tsaya da abunda kake ba ka saurari abunda nazo dashi." Omar ya cigaba da abunda yake ba tare da ya kalli gefen da take ba ckin zuciyarsa yake fadin"Nasan ko dame kika zo dashi 'Yar sarkin rashin kunya

Haushin abunda yayi mata ya sanya ta kai masa duka a damtsen sa dake a murd'e!! Hannunta taji ya sage! don har sai da yatsunta suka bada sautin 'kas!!! ta kalleshi taga ko gezau! baiyi ba yanw cigaba da abunda yake gabansa.

Ido jazur ta taufa masa miyau!! tana huci! tace"Kai d'an tsintuwa d'an mahaukaciy..........Kafin ta 'karasa ya buge mata bakinta da bayan hannunsa yanda ya daki! bakin da karfi dole ne ya fashe take jini ya soma zuba ta fasa! muguwar 'kara tayi kansa da duka d'ane jikinsa tayi tana cizo da ya kushi dama ta dad'e tanayi masa wannan d'abi'ar Omar ya rasa ya zaiyi da ita ta d'ane sa sai naushi take kai masa ita a ganinta yana jin zafi! hakoronta ta datsa gefan wuyansa sai da ta huda gurin sannan ta dura 'kasa ta cigaba da zaginsa Omar ya fusata!! da karfi ya kwakkwad'a mata marika lafiyayyu Shatin hannunsa suka kwanta

3 Comments On SADAUKI OMAR
avatar
auwal-mohammed

1 year ago

Reply

It nice book to read ????

avatar
hafsat-9-3

1 year ago

Reply

Very nice biik

avatar
hafsat-9-3

1 year ago

Reply

Very nice biik

Please Login or Register in order to submit comment