Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

believe" Majeederh da fararen Idanunta wanda suka kuɗe kawai ake gani,ta juya su a taushashe ta ce "Ke macace, ita mace sirri ce, sirrinki tsaraicinki ne, ki riƙe shi kamar tazugenki" Latifa Omar ta saka dariya mgn ɗaya kawai Majeederh za ta yi mai cike da ma'ana da azanci ta ce "Ok zan riƙe da hannu bibbiyu, Majeederh sbd ke na ce zai kaimu, nasan Abbu bai baki kuɗin mota ba, kuma is like compulsory to you na zuwa karɓo form ɗin, ki yarda dani in sha Allah nothing will happen as you think" Kafin Majeed ta yi magana ta yi gaba abinta hakanne kawai zai saka ta taho. Ta cikin madubin motar yake ƙare mata kallo har ta buɗe ta shiga sai a lokacin nauyin da zuciyarsa ke masa tun daren jiya ya saki, ciwon kan ya yi nasa waje. A ransa yake mamakin yadda ko kwalli bata sakawa cikin Idanunta. Key ya yi tare da yin reverse kana ya ɗauki hanyar da zata kaisa B.u.k new side.... Sun yi nisa sosai babu abin da ke tashi sai maganar Latifa Omar, Aliyu ya ɗan ya tsuna fuska yana tunanin yadda abu kamar wasa yake neman zamar mishi gaske, ya ce yana son Latifa Omar amma baya jin aurenta a ran shi duk da furta a baki, ya rufe idanu ya buɗe saman kwalta his heart disappointed him. Ya kasa daurewa ya ce "Na zama drivern kurma" Latifa ta ce "Kurma? Yana driver idanunsa rabi da rabi akan madubi ya ce "Ur friend, Jiddatul-khairy" Latifa ta buɗe ido kana ta juya ta ce "Malamarmu, Malama Majeederh mijin da zan aura ba sai anja masa aji? Ba gaisuwa" Aliyu-haydar ya ce "Hakan kuma ba halin Malaman ƙwarai bane" Duk tana jin su sai da suka gama surutu da wajan minti biyu suka ji ta ce "I don't want interfere" Wata ɓoyayyiyar ajjiyar zuciya Aliyu ya sauke lokacin muryarta ta sauka cikin kunnenshi, ba zai iya cewa ko ranar daya fara ganinta ya ji muryarta ba, sbd baya cikin nutsuwarsa ji yake kamar new Aliyu akai a lokacin ba shi Aliyun ba, sai ya ji kamar bai taɓa jin murya irin haka ba in his whole life, sanyi, nutsuwa, haƙuri da kamalarta duk ta bayyana cikin maganar da tayi ta kalmomin da baza su gaza biyar ba. Suna zuwa cikin B.u.k ɗin Majeederh ta fita babu jimawa ta dawo lokaci Aliyu na zaune hannunsa riƙe da Swn water yana sha ganin yadda ta yi tsaye ta kasa knocking Glasses ɗin motar yasa gently ya saka hannu ya fito daga cikin motar yana zuba hannu a aljihu tare da juyawa ya dinga ganin Students different department suna ta zirga-zirga. Ya kalli Majeederh ya ce "Jiddatul-khairy, you are too..." Da sauri ta ɗaga kanta a tunaninta ko yau Allah zai sanya wani namijin ya ce tana da kyau, saɓanin Uncle Isma'il da yake cewa tana da kyau da kuma ƴan-uwanta mata sai ta ji ya yi shiru ya ce "Kin gama ne?" Ta girgiza kai tana addu'a a zuciyarta Aliyu yana son ya ƙara jin muryarta ya ce "Mene ya faru? Me bada form ɗin ne baya nan ko?" Har ranta ta gaji da magana ga yunwa sosai take ji ga kewar Little da rashin sanin inda yake ta marairaice kamar za ta yi kuka sosai ta ce "Uhm ba nan bane" Aliyu ya ware ido hadda riƙe ƙugu ya ce "Oh ni Haydar sai aka ce ina?" Batai magana ba har Latifa ta fito daga cikin motar ta ce "Meke faruwa nan?" Aliyu ya yi mata shiru Majeederh ta ɗauke kai can ta ce "Murtala way" Murmushi kawai Aliyu ya yi ya ce "Oh Kano state ministry of education, i think Government office?" Ya faɗa yana duban Majeederh "To yanzu can zamu kenan? Domin idan muka koma gida ba wannan form ɗin mun shiga uku wajan Abbu kwana zai yi yana faɗa" Aliyu ya ce "Waye?" Kai tsaye Latifa Omar ta ce "Her father" Sosai ran Majeederh ya ɓaci Latifa na son nunawa Aliyu Mahaifinta masifaffe ne ko yana takura musu ta ɓata fuska duk da ba'a ganin yanayin nata. Cikin Aljihu ya saka hannunsa ya ji ba kuɗi ya juya yaga babu wani pos a kusa da su, babu cash da sauri ya juya mota tuna cewa kamar ya bar kuɗi ciki jiya daya siyi Popcorn 2k ne ya miƙawa Latifa ya ce "For transport, ku yi amfani da shi wajan napep ina da shari'a 1:00" Latifa ta ce "Ok bye" Ya girgiza kai kawai jin ko godiya babu bawai kuma damuwa da hakan ya yi ba, Majeederh ya san ba za ta yi magana ba.....
Sun jima cikin haɗaɗɗen office ɗin na commissioner for education ɗin, kafin a hankali su ji an shigo duk suka miƙe tsaye ya nemi waje ya zauna, magidancin mutumi ya zauna saman kujera, babba ne mai shekaru amma kuɗi sun zauna rayuwar daula ga hutu da kwanciyar hankali plus jin daɗin rayuwa. Ya amsa gaisuwa ya ce "How can I help you?" Majeederh ta yi ƙasa da kanta a hankali ta ce "Sunana Majeederh Abdul'aziz Khan, ance na zo na amshi Form na scholarship ɗin da akai mana al'ƙawari ranar Candy da Musabaƙa" Ya jinjina kai ya ce "Ok" Kana ya shiga jawo file gefe ɗaya kuma yana danna waya ya ce "I, Alhji Aliyu S, Commission for education" Bayan sun amshi form ɗin ya haɗa su da wani ya yi musu bayani, Sai dare Majeederh ta ci abinci towon masara biyar kuɓewa bushasshiyya bacci ɓarawo shi ne ya ɗauketa. Washegari babu inda ta fita sbd ciwon kai da zazzaɓi tana ta kiran number Akeeth shiru a kashe. 5days left da yamma ranar laraba tana zaune a ɗaki tana tunanin hanyar da za ta yi cigiyar Little sai kawai ta yi ta sauke application ɗin facebook ta buɗe Acct da full name ɗinta Malama Majeederh Abdul'aziz Khan, ta saka photon Little cikin uniform da rubutu mai tsayi da ma'ana, tausayi da neman taimako. Comment ɗin data gani ya ɗaga hankalinta zuciyarta tayi nauyi, ta ji kanta na juyawa komai ya yi mata zafi, ta ƙara buɗe Idanunta akan comment ɗin da aka ce mata “Ke aure ya kamata dake, shekaru sun ja” Ta cillar da wayar tana miƙewa tsaye kena kowa ya san bata da aure? Me ya sa ake son goranta mata yin aure ne? Ita zata aurar da kanta ne ko ita za taga namiji ta ce tana son auren shi? Ta ƙarasa gaban madubi ta shiga kallon kanta Majeederh ba zata iya tantance da gaske tana da kyau ko bata da shi ba, tasan dai ita fara ce ba ruwanta da Powder, kwalli, lipstick kullum fuska a rufe cikin liƙab sai duguwar riga da take sawa ko ƙaton hijabi. Ko dai gwada fita za ta yi babu wannan abubuwan? Idan ta fita hakan zata samu wanda zai ce yana sonta? Ta yi shiru... Washegari Alhamis bikin Widad ya kama yau za a fara za su yi Arabian night. Gabaɗaya suna zaune a parlourn gidan Uncle Isma'il, ga Uncle Bello ga Abbu sai Yaya Bilkisu da Innati. Uncle Isma'il ya ce "Na fahimci matsalarka Abdul'aziz, sbd baka da ɗa namiji shi ya sa ka ɗauki Majeederh kamar namiji? Tunda ita ce babba, duk abinda yake faruwa na sani, kawai zan maka cewa ba ka yi kanka da ƴarka mai hankali adalci ba, Majeederh does not deserve this Abdul'aziz, idan karatu ne kaima kana iya faɗaɗa naka kaje ka ƙaro ilimi, idan ma hakan kake so ta yi why not ka fara yi mata aure first sai karatu ya biyo baya, kaga da mijinta da komai babu wata fargaba, amma Fisabilillahi ka ɗauki Majeederh wacce take kan shekarunta na balaga tun daga Nigeriya zuwa Misira? Kasan halin da zata kasance a tsayin shekaru takwas ɗin da za ta yi? Yanzu ko namiji ne ka sadaukarwa ilimi shi ba tare da tunanin lafiyarsa ba?" Abbu ya kalli yayan nasa Uncle Isma'il ya ce "Lafiya kuma? Ina tunanin ai akwai kulawa ta makaranta?" Uncle Isma'il ya ce "Ok bari na na fito maka a mutum, idan Majeederh ta buƙaci namiji makaranta zata bata? Ko maza zata fara bi? Ka haifi yarinya a cikinka amma You don't even know abinda ke damunta, da abinda take so ba, Majeederh Allah ne kawai yake kula da ita kuma shi ne ya bata yawon da take da shi, gata ƴar fari ga babu kulawar uwa data uba a wajanta" Sai a lokacin Yaya Bilkisu ta ce "Allah na tuba gata dai kyakkyawa amma ai babu mai ganin kyanta bata da kaya sai duguwar riga kamar haihuwar Larabawa, ai Allah ne ya san manufar Fulani da tace ka aurar da ita tun tana 15 amma kaƙi, ka ci mana wasiyya Allah ya sanya ta fito da kabari tai maka fatalwa sai ka fahimci tashin hankalin da take ciki" Innati ta zare idanu ta ce "A'a ba amin ba wannan kuma ai fatan tsiya ne meye kuma fatalwa ana zama lafiya abi dai komai a nutse tunda shi ya ce karatun take so ku zuba masa idanu idan yana laifi sai ya yi, duniyar gabaɗaya nawa take? Allah na tuna ya rubuta ya ajjiye komai ya faru ya shirya amsa" Uncle Bello ya ce "In sha Allah babu abin da zai faru, da dai ya barta tayi auren shi ne kawai" Abbu ya ce "Aure fa baya bari ayi karatu by the way waye ya ce yana son aurenta na hana?" Duk su ka yi masa shiru haka dai taron ya tashi ba fahimtar juna tsakanin Abbu da Uncle Isma'il da ƙaninsa Uncle Bello, familyn Khan maza ba su fiya yawa ba mata duk sun fi yawa. Majeederh na parlour ta yi shiru tana kallon yadda ƴan matan suke shiryawa cikin abayas baƙa Ruma jiya Imran ya bata, Raihana ma saurayinta ne ya siya mata, Aaliyyah kuma Majeederh ta siya mata da kuɗin albashi. "Anti Jeederh ba zaki ba?" Majeederh ta kalli Ruma ta ce "Eh" Aaliyyah ta ce "Amma me ya sa Anti Jeederh?" Ta yi musu shiru kawai Mami ta ce "Hawwa'u me ya sa baki son shiga cikin ƴan uwanki ne?" Ta ce "Ba komai" cewar Majeederh tana rufe ido Mami ta ce "To Allah yana kallo na yi nawa yin, Majeederh idan kana da kyau ka ƙara da wanka amma dai kuma ta wani ɓangaren kina da gsky tunda duk kin girme su sai dai ko Sahar" Aaliyyah ta ce "Kai Sahar ɗin ce sa'ar Anti Jeederh? Naga na girmeta da shekara ɗaya ma" Mami ta ce "Ji ƙuruciya to ai duk wanda ya yi aure ya zama sa'anta yanzu hirar da za ayi da Sahar waye zai yi da Majeederh?" Majeederh ta miƙe tare da shigewa bedroom ɗinta zuciyarta a cunkushe ji take gwarama kawai ta tafi karatun ta huta zuciyarta ta samu salama. Gidan Uncle Isma'il akaiwa decorations ya yi kyau sosai bride mate da friends ɗinta sun yi kyau aci make up, ga abokan ango sun kyau yawancin su classic ne masu aji ilimi ga wadata ta iyaye. A hankali Majeederh ta sako ƙafarta cikin harabar gidan kiɗa na tashi zuciyarta sai rawa take for the first time data zo event har haka, wanda kuma bayin kanta bane tabi ragamar zuciyarta akan abinda take jin kamar shi ne daidai, abaya ce mai ƙaton hannu a jikinta ga faɗi da take da shi ta yi mata yawa sbd ramewar da tayi, tayi rolling kanta a hankali ta saka hannu ta zame liƙab ɗin fuskarta a karo na farko in her whole life data cire liƙab a gaban maza tafiya ta fara yi zuwa wajan, gabaɗaya idanun jama'ar wajan suka dawo kanta duk wanda ya ganta sai ya taɓo na kusa da shi ya nuna masa Majeederh daga mazan har matan, ta ci-gaba ta shiga cikin wajan tana zuwa dab da wani matashin mutum tun kafin ta ƙarasu ya juya da sauri kamar yaga Aljana yabar wajan jiki na rawa......


MIJIN MALAMA
Via this number..... 0811923761623
Duk inda ta sanya ƙafarta sai taga ana matsawa tare da jan jiki baya, Majeederh was Shocked ta yi saurin saka hannunta ta shiga shafa fuskarta ko wani abu ne ya sameta, amma bata ji komai ba, bata iya shiga razani ba sai numfashinta ya fara sauka da ƙarfi ciwonta ya fara neman tashi, wani saurayi ya dinga kallonta daga nesa ganin attention ɗinsa yana kanta ya sa ta nufesa duguwar rigar jikinta na neman yarda ita sbd tayi mata yawa sosai. Tana zuwa wajan saurayin taga ya yi saurin rufe idanunsa a fili ya shiga faɗin "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un, Ya subuhanallahi!" Kalamansa da salatin da yake na neman taimako daga Ubangiji ya ƙara firgita Majeederh da jirkita duniyarta idanunta da sukai jajur ta buɗe akan saurayin ta ce "Don Allah mene ya samu fuskata? Me ya sa kowa ke kallo na?? Me ya sa maza suke guduna?" Sosai muryarta ta razana shi amma ya dake deep down na zuciyarsa addu'a yake na neman tsari ya dai daure ya ce
"But are you a Baha'i?" Majeederh ta dinga kallonsa ya ce "Ina nufin ke Bahaushiya ce?"
Ta jinjina masa alamar eh ya ce "Ki dai bincika amma duk wanda ya ganki zai ci Aljana ce, kyanki ya yi yawa ni ma dauriya kawai na yi" Yana faɗin haka ya bar wajan da sauri jikinsa na rawa. "Aljana??" Majeederh ta tambayi kanta tana nuna kanta da yatsa a fili ta ce "Is this really happens to her?" Ta zube saman kujera tare da dafe kanta "Wai meke faruwa? Ni ce Majeederh ko wata new Majeederh? Ko dai gaske Aljana ce, Innalillahi" da ƙyar ta iya jan jiki tare da ɗaukan liƙab ta mayar a fuskarta tana fita Aliyu ya shigo wajan shi kansa bai san mene ya kawo shi ba..... Gabaɗaya suna zaune a parlour Hajia ta gyara zama speaking calmly ba faɗa ta ce "Sannu fa, ai zata aikata duk me aka ce ta yi bana doubting" Hajiya Rahmerh ta ce "I don't think so, amma dai ta ce komai zai daidai In sha Allah" Hajia ta girgiza ƙafa kawai hankalinta yana ga Aliyu-haydar da har yanzu ba taga shigowar shi ba. Anti Biba mai bin Hajiya Rahmerh ta ce "Ni wai ina Autanki ne Hajia? Babu shi ba Almustapha?" Kafin ta yi magana Aliyu ya shigo muryarsa mai ɗauke da damuwa ta ɗan baiyana a parlour. Daga Mahaifiyarsa Hajia har ƙannenta Hajiya Rahmerh da Anti Biba suka dubi Aliyu. "Kai lafiya kake? Wannan idanun kamar mai azumin Kaffara?" Ya nemi waje kusa da Hajiya ya ce "Am Good, ya hanya Aunties?" Anti Biba ta ce "Lafiya, lawyer sarkin ƙarya" Bai ce komai ba ya shafa kansa feeling better ganinsa kusa da Hajiarsa "Aliyu" Aliyu ya kalli Hajiya Rahmerh har sai da gabansa ya faɗi ta ce "Aliyu, Aliyu, Aliyu how many times do I call your names?" Ya yi ƙasa da kansa ta ce "Ok na kira na ji daɗin bakina ne ko mene? Eh?" A hankali ya ce "Afuwa" Ta gyara zama ta ce "Kana da gata, kana da kuɗi, kana da ilimi ka fara aiki zaka gina kanka to me ka ke jira? What are you waiting for??" Shi dai bai magana ba ta ce "To ka fita daga cikin idanuna, ku biyu kawai Allah ya bawa Hajiya Laylerh ai yana da kyau yanzu zuri'a su fi haka yawa, bari na buɗe maka zancan a faifai maganar aure nake maka" Ya yi shiru daman ya san abin da zata ce kenan ya ce "To" ta ce "Ba wannan nake son ji ba, cewa zakai to Hajiya Rahmerh zan yi nan da wata kaza ka gane, ni a kawo maganar ba ga can ƴar uwarka ta ƙare karatunta a London Buhayyerh talk to her ina da tabbacin zata amince maka" Ya cira idanunsa ya kalleta ya ce "She is not strong enough to be my wife, I need someone stronger" Ta ce "Are you kidding me, right?" Ya yi shiru, Hajiya Rahmerh ta shiga faɗa ta inda take shiga bata nan take fita ba har tayi masa tas bai ce komai ba. Ya miƙe tare da shigewa part ɗinsa, yana shiga Anti Biba ta bi bayansa ta ce "baka kyauta ba Aliyu" ya riƙe kansa ya ce "Goodness, me na yi?" Ta ce "Ba haka ya dace ka bata amsa ba, ana iya yin ƙarya domin kare kai wannan ya halatta a mazahabar malam Bahaushe, ana iya lashe rai ɗaya domin kare rai dubu" ya yi shiru for some seconds ya ce "Kawai sai a haɗa aure? Kamar an daina wannan abun an shige ƙarnin tun tuni" Ta yi Murmushi kawai ya ce "Ina Antin Turkey?" Anti Biba ta ce "Sun sauya sheƙa an yi mijinta transfer na wajan aiki" Yana kwanciya tare da rufe idanu ya ce "Zuwa ina?" Ta ce "Ban san ƙasar da take ba, tana ta complain dai bata so sbd karatun yaranta baya yake dawowa" Ya mirgina ya ce "Tana da gaskiya" Hira su ka yi sama tana lura da yadda ƙirjinsa ke ɗagawa sosai da ramar da ya yi sai ba tayi masa magana ba.... Washegari da safe Innati ta dira gidan Abbu lokacin duk suna karyawa ta dubi Abbu ta ce "Audil azizu saɓon Ubangiji kake amma ba zaka gane ba" Da damuwa sosai ya ce "Saɓo Innati?"
"A'a, Allah na tuba ai duniyar gajere ce kaje ka yi bance komai ba, amma zaka sha mamaki da izinin Allah ka kuma shirya" Kalaman Innati suka daka Abbu cikin shakku na rashin sanin abinda ya aikata har haka da zai gani? Innati ta kalli Majeederh data raƙube gefe ɗaya kamar ba gidan Ubanta ba ta ce
"Babu komai, jarrabawa ce amma ni kaɗai na san abinda idanuna ke gani akan ki Kululu ki yi ta addu'a takanas na zo wajanki tunda na ji ance jirgi zaki hau ki bar duniyar"
"Ƙasar dai ba duniyar ba" Aaliyah ta faɗa tana kallon Majeederh wanda ko kunun ta kasa sha. Kamar daga sama kuma su ka ji ta ce "Inna da Aljanu nake kama?" Innati ta zare idanu tana dafe ƙirji ta ce "Yanzu to mene haka? Ina ruwanki da zancen Aljanu da sanyin safiyar nan don Allah? Allah ya yafe miki" A raunace kamar bata son yin magana ta ce "Na taɓa ji kince na tsorataki" Innati ta ce "To bance komai ba, ke kuma kwaɗayayyiya wacce ta sha nonon maita ki ke idan wancan yaron ne zaki gani, abin da naga komai ina kan gani" Ta faɗa tana nuna Ruma da hannu ita kuma ta tura baki gaba, ta juya kan Mami ta ce "Ban yi mamaki ba, haihuwar Legas ce ke sai abinda Ubangiji ya ƙaddara za mu gani, duk ƴan iska ne Legas ɗin ai" Abbu dai bai ce komai ba sbd yasan halin mahaifiyarsa kamar wacce take da matsala idan tana abu sai dai kawai su dinga jinta. Majeederh ta yi shiru a ɗakinta inda take kwance akan gado sai juyi take, bata san meke damun zuciyarta ba, wacce kullum ke ƙaryata ta akan zata iya samun wanda zai aureta ya rusa zuwanta Egypt.
Ta juya a hankali tana ƙanƙame pillow jin tsigar jikinta na tashi wani abu yana mata yawo a jiki, wanda ta kasa sabawa da jinsa a kullum, yanzu ko ta ɗauki azumi ma sai ya karye bata san meke kawo wannan abun ba, ta ƙara juyawa tana kiran sunan Allah ko zata daina jin abin amma ina, ruwan saman da akayi ya ƙara haddasa bayyanar abu a jikinta kamar cin wutar kara. Miƙewa tayi ta nufi toilet tana zuwa ta dinga sheƙawa kanta ruwan sanyi a hankali ta durƙoshe akan ƙafafuwanta duk yadda ta kai da haƙuri, juriya, da miƙa lamura ga Ubangiji sai da ta fashe da wani raunataccen kuka har da shassheƙa. Da ƙyar bacci ya ɗauke ta, ta farka da wani irin zazzaɓi ta juya tare da kallon Mami dake zaune bakin gado ta zabga uban tagumi ta ce "Kin farka?" Majeederh ta miƙe zaune tana mistake idanunta da suka kumbura "Mami"
"Kuka ki ka yi Majeederh?" Ta yi shiru domin bata ƙarya Mami ta sauke numfashi ta ce "Hawwa'u, kina ji cewa a ranki bana kyautawa ko?" Majeederh couldn't speak Mami ta ce "Majeederh bani da iko dake, haka kullum mahaifinki yake ce mini, shi ya sa na tattara komai na ja bakina nai shiru, to na ce me? Ina tofa tawa zai ƙullace ni, mun sha samun saɓani da shi akan ki amma ya ce ba ruwana ƴarsa ce ke ba wani ya haifa masa ke ba, hatta tafiyarki ba a son raina ba dana faɗa masa gasky cewa ya yi zan yi ta igiyar aurena, ni kam mene ya yi mini zafi? Ƙatuwa dani ina shirin kai ƴa ɗaki na samu jika da yawon zawarci?" Ta ja numfashi ta sauke ta ce "Allah yana gani na fara gajiya yana neman shafa mini baƙin fenti" Murmushi kawai Majeederh ta yi ta ce "Ba komai"
"Da gaske babu?" Ta jinjina kai ta ce "To Allah ya iya mana, ko can ɗin kika je kiyi ta addu'a, ki riƙe mutumcinki har zuwa shekaru takwas ɗin" Kanta a ƙasa ta ce "Na gode" Mami ta miƙe tsaye tana cewa "Maza ki tashi ki shirya wani sa'ilin ke kike mai da kanki baya ayi mace ba kwalliyya? Ba kwalli ba powder, fuska kullum a rufe da wata ƴar malafar uban duguwar riga, kamar matar mamaci ko wacce aka koro daga Saudiya? Fuska a maiƙaci sai farin bala'i kamar an kwara miki man ɗanyar gyaɗa haba Majeederh? To ai shikenan" ta saka kai ta fice abinta.
Majeederh ta sauke ajjiyar zuciya, wai ta yi kwalliyya? Ai bata da wata sauran dama ta riga ta sallama, ta yarda ta amince domin ta yi ilimi da bautar Ubangiji take raye, ta yarda ita ta rako mata duniya ko me za ta yi a rayuwa ba zai taɓa sauya abin da zuciyarta ya yarda da shi ba, ko fata za a sauya mata ba zata taɓa samun mijin aure ta yarda za ta yi karatu zata zama cikakkiyar Malamar addinin Musulunci zata fafata da duk wanda zai ja da wata ɗiyya mace zata zama jaruma mai yarda da suke abin da Ubangiji ya zo mata da shi, yarda da ƙaddara ta zama feminist. Ta buɗe wayarta tare da kunna network ta shiga facebook, abin ya bata mamaki ganin ta samu mabiya da yawa sosai kamar jira ake ta buɗe. Ta shiga wajan timeline ta yi rubutu ta ce “ITA MACE, BA BAIWA BA CE, KO A GIDAN MIJI" tana gama rubutawa hannunta na rawa ta yi posting ɗinsa, Just now amma over 100 comment ta duba sunan wani Bilal-Habib ya ce
“Uhm ke ba aure ba, kuma zai kashewa wasu? Shi aure ne ba bauta ba? To uwarki ne?" Tana gama karanta idanunta ya sauka akan wani da ya rubuta.
"Malama Majeederh ki bari ki fara auren ko? Ai wannan maganar bata yara ba ce" Da sauri ta yi wurgi da wayar bayan ta kashe datar zuciyata na harbawa. Ta daɗe kafin ta samu nutsuwa. Mami da maƙociyyarta na zaune suna hira Latifa Omar ta yi sallama ta shigo cikin wani lace mai kyau ta sha kwalliyya ta ce "Ina yini Mami?"
"Lafiya lou Latifa ya Maman taki?" Ta ce "Ta ce a gaisheki, Majeederh fa?" Da hannu ta nuna mata hanyar ɗakin Majeederh ta shiga da sallama ta sameta zaune ta ce "Ya naganki zaune ba kyan gani? Kamon ba?" Ta yi shiru idanunta akan waya tana da Research more than 2hrs tana abu ɗaya "Amma dai baki isa ki ce ba zaki ba ko? Bikin Widad ƴar uwarki ni ma zani balle ke?" Ta ce "Mene amfanin zuwa? Ana zuwa domin farin ciki ni raina ke ɓaci Latifa Omar ki bari kawai karatu zan yi" Latifa ta zauna ta ce "Mene ya faru?" In brief ta faɗa mata komai, Latifa ta yi jigum ta ce "Kamar wata mujiya, Majeederh anya lafiya?" Majeederh ta yi murmushi ta ce "Lafiya lou, i believed

Please Login or Register in order to submit comment