Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shigo babu ko sallama hannunsa riƙe da kansa, Hajia ta miƙe da sauri ta ce "Zakina Lafiya? Baka da Lafiya ne? Meke damunka?" Aliyu ya kasa cewa komai sbd parlourn dake juya masa a hankali ya ce "Hajia lulluɓeni san yi nake ji" Hajia da bata jure rashin lafiyar yaran nata gabaɗaya ta rikice ta ce "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Aliyuna mene ya sameka yanzu ka fita lafiya lafiya fa?" Papa ya kalli Almustapha ya ce "Kira Dr" Almustapha ya juya da sauri zuwa ɗakko waya, Papa ya kama Aliyu ya kwantar saman duguwar kujera sai rawar sanyi yake idanunsa rufe jijiyoyin kansa duk sun fito, Hajia ta fashe da kuka ta ce "Na shiga uku mayu sun kama mini yaro, yarana kwaya biyu kacal a duniya shi ne za a ga bayan ɗayan?" Papa ya dinga kallon Aliyu shi kansa ciwon ya bashi mamaki, Aliyu dake cikin ciwo ya kama hannun Hajia ya riƙe ya ce "Ki danna mini ƙirjina Hajia, zuciyata zata fito waje" Hajia ta ƙara saka kuka, daidai nan Almustapha ya dawo babu jimawa Dr ya zo allura ya yi masa tambayar duniya ya faɗi meke damunsa amma yaƙi. Suna zaune har bacci ya ɗauke shi a cinyarsa Hajia yana sauke numfashi a wahale..
Har gari ya waye bacci baiga idanun Majeederh ba, ana kiran sallah ta tashi tayi wanka tare da yin Sallah ta jima tana addu'a sosai kafin ta shirya cikin wata duguwar riga Maroon tayi rolling kanta. Tana tsaye Latifa Omar ta shigo idanunta ya yi jaa taci kuka son ranta ta ce "Wai ki fito ba lokaci" Murmushi Majeederh ta yi ta ce "Haka aka damu dani? Irin wannan kuka" Latifa ta sake fashewa da kuka, bata hanata ba don dai itama taiwa kanta al'ƙawarin daina kuka ne, da babu shakka sai tayi nata kafin ta tafi, safiya ce amma ƴan-uwa sun cika gidan Abbu kowa yana son ganin tafiyar Majeederh, tafiya ce wacce ba lallai a sake ganin juna ba, inma ita ta mutu inma su, kanta a ƙasa ta fito daga nan suka rankaya airport, anan sukai ta ganin ɗalibai masa da mata, kasancewar a makare suka ƙarasu wajan yasa ta shiga sallama da mutane ta ƙarasa wajan Abbu ta ce "Abbu na tafi ka yafe mini don Allah" Ya ce "Babu komai, Allah ya bada sa a" haka ta dinga bin mutanen wajan tana zuwa wajan Aaliyah ta rungumeta, a can gefe ta hango Alpha yana tsaye rungume da hannunsa, uniform ɗin sojoji ne a cikinsa amy colour ta nufi inda yake ya kalleta bai ce komai a hankali ta ce "Na tafi" Ya gyara tsaiwa ya ce "All The best, ki kula" Za ta yi magana ya yi saurin shigewa mota, sai a lokacin hawaye ya taro a Idanunta ta nufi cikin wajan har tayi nesa da su kai tsaye jirgin ta shiga sai da ta zo matattakalar ƙarshe ta ɗago kanta ta kalli ƴan-uwanta kamar ance ta kalli gefe idanunta ya sauka akan Aliyu hannunsa maƙale da carnoner...


MIJIN MALAMA
08119237616
Uhm get ready...... Yanzu zamu fara🥹26
Majeederh ta sake kallon Aliyu, she saw that he had changed from the way she knew him, duk da ba wani mugun sani ta yi masa ba, ta ɗauke kai ganin yadda ya kafeta da idanunsa da suka janye, a hankali ta juya idanunta cike da hawaye ganin Khan's family maza da mata yara da manya suna ɗaga mata hannu. Jikinta na ƙyarma da ɓari na rashin sabon tafiya ita ɗaya ta ƙarasa kujera ta zauna tare da kifa kanta a tsakanin cinyoyinta, wani rauni ya mamaye dukkan zuciyarta fargaba da tsoran abin da zata tarar a ƙasar daba tata ba ya wanzu a zuciyar Majeederh Abdul'aziz Khan. Ya za ta yi a garin da babu uwa ba uba? Garin da ba wa ba ƙani? Garin da babu idon sanin? Garin da babu mai kwaɓarta? Ya za ta yi idan abu ya faru da ita wa kuma zata tunkara? Rashin sanin wanda zai bata amsar tambayoyinta ya sanya ta ƙara tura kanta wani mahaukacin kuka na kwace mata ta yi saurin rufe bakinta. "Assalamu alaiki" Wata murya ta sauka cikin kunnenta a hankali ta goge hawayen idanunta tas ta ɗago kanta bayan ta gyara zaman liƙab ɗin fuskarta. A hankali ya daidaita tsaiwar shi ya ƙara cewa "Assalamu alaiki" Su take ta amsa amma harshenta ya yi mata nauyi ta ɗaga kanta suka haɗa idanu, yana tsaye ya rungume hannu ɗaya a ƙirjin fuskarsa maƙale da face mars, ya ƙara zuba mata idanu ganin yadda take ta sauke ajjiyar zuciya ya ce "Ki duba number seat ɗin ki" Sai a lokacin ta duba taga a number 35 take zaune number ta kuma 34 ne, ta langwaɓar da kai alamar ban haƙuri kana ta tashi a hankali ta zaune a number dake window. Ya nemi waje ya zauna yana danna airplane mode a wayarsa tare da ware jarida ya shiga dubawa, yadda Majeederh ke sauke numfashi a wahale ya sanya ya juya ya kalleta tare da cewa "Are you okay?" Ta jinjina kanta.
"Are you sure?" Ta ƙara jinjina kanta ya bita da kallo kafin ya ce "Okey"
Sanarwar aka fara kowa ya shirya jirgi zai ta shi, a hankali ta jawo ballet ta ɗaura a jikinta.
Jirgi ya fara juyawa a ƙasa tsayin wasu daƙiƙo zuwa mintuna, Majeederh ta rufe Idanunta tare da ƙanƙame jikinta waje guda, lokacin da jirgin ya yi katantanwa zai tashi ji tayi kanta yana sarawa amai na shirin zubo mata. A taushashe ya ce
"Sorry" tana cikin wannan yanayin jirgin Emirates Airplane ya ɗaga da ɗarorun ɗalibai. Ta sauke ajjiyar zuciya ya ɗauki ruwa ya miƙa mata ta girgiza kai, har lokacin bai ji maganarta ba.
"Please bear with the interruptions, is this your first time on a plane?"
"Uhm" ta furta a yanayin da ba zai iya haddace muryarta ba.
"I see, sorry" Ya mai da hankali zuwa ga jaridar dake hannunsa deep down na zuciyarsa he was thinking ko dai bata jin magana, kurma ko bebiyya? Only God knows... Majeederh ta rufe Idanu yayinda da dukkan wani farin cikinta ta barshi a jihar Kano, ƙasar Nijeriya.
Aliyu ya zame idanunsa daga kan jirgin su Majeed wanda ya gama shigewa cikin gajimare, ji ya yi kamar da zuciyarsa ta tafi tare da nutsuwarsa ya sauke numfashi yana ƙoƙarin buɗe murfin motar shi ya ji an ce. "Hi"
Ya tsaya ta buɗe motar ya juya idanunsa ya sauka akan Alpha wanda baya jin zai iya mance yanayin daya gansu shi da Majeederh. Bai ce masa komai, Alpha ya gyara zama ce ya ce
"Alpha Bello khan my name, Captain, It is the highest rang in Tactical troops organization"

"Good" Aliyu haydar ya ce murya kuma can ƙasa, Alpha ya gyara tsaiwa ya ce "Sunanka Aliyu Sufyan Alhassan, ɗan Jarida a matakin farko na fara aiki, Kayi karatu a Al'ƙalam University, daga nan ka shige Cairo ka ɗora da karatu, a gida anso ka karanci ɓangaren politics Democracy, kai kuma ka ce Law ka ke so, mahaifinka Alhaji Sufyan Alhassan shi ne Commissioner for education, ku biyu iyayenku suka haifa, yayanka Almustapha shi ne Manager a Bua campaign, mahaifiyarku tana ji daku sosai shi ya sa bata jure dukkan ɓacin ranku, wannan dalilin ya sa bata takura ku akan maganar aure duk da akwai ƴan mata a familynku amma kuna jin kun girmi ajin su" Alpha ya yi murmushin gefen baki ya zuba hannu a aljihu ya ce.
"Idan har a kwana ɗaya zan iya sanin waye kai, to karantar zuciyarka ba zaiwa Alpha wahala ba, bayan kasanceweta soja ina aiki a hukamar fikira ta jiha ka kiyaye, kada ka fara abin da ba zaka iya ba, kada ka sanya zuciyarki cikin ramin da zata kasa fitowa, kada ka yi ƙullin da zaka saka cikin kejin kaza, kasan kaza uwar tune-tune ce, stay away from her, Ina nufin Majeederh Abdul'aziz Khan she's my sister"
Bar Aliyu Sufyan Alhassan dake jingine da jikin lafiyayyiyar motarshi ya ɗan miƙe hannunsa mai ɗauke carnoner ya ɗaga ya shafa kansa ya ce "Anzo wajan"
Ya dubi idanun Alpha dake kwance cikin nasa idanun kai tsaye ya gane me launin idanun yake nufi domin a yawan karatun English Novels da yake da literature daya karanta yasa fahimtar hakan bai masa wahala ba "Uhm"
Sai kuma ya ce "Me ya sa zaka nuna maitarka a fili? Kada ka manta nan fa ba filin yaƙi bane ko dajin sambisa Captain Alpha Bello khan, a tsare rayukan jama'a kafi ƙarfi, amma ba zaka nunawa Babba lauya fahimtar waye mutum ba, by the way, who are you talking about? Stay away name? Please open your heart ƙilan na fahimta sosai"

"Ka janye jiki daga gare ta, baku dace ba?" Cewar Alpha. Cike da rainin hankali irin na Lauyoyi Aliyu ya ce "Wai wa kake magana? stop bitting around the bush, just go to the point" Ya faɗa da muryar marasa lafiya.
"Na hango soyayyar Majeederh a cikin ƙwayar idanunka, shi ne nake maka gargaɗi kada ka sanya son abin da ba naka ba, ku dan muhimmancin rayuwarka ga wanda suka damu da kai" Alpha Said, ya na buɗe ido.
Aliyu ya ware idanunsa ya ce "Soyayya? Ni ɗin? Kuma wai da sister naka? Goodness, to an faɗa maka halin Lauyoyi da Sojoji ɗaya ne? A cikin gari muke fa ba wai barrack ba, balle ka ce zakai kishi akan kilaki, and ka yi kuskuren fahimta zatonka ya saɓa lissafinka"
Aliyu ya taka a hankali har gaban Captain Alpha ya ce "Yes Am in love, amma da ƙawar Hawwy ba ita kanta ba, bani da tabbaci da zuciyata, ban yi kuma al'ƙawari ba, domin shi kayana ne, zuciyata ba sansanin sojoji bane wanda a koda yaushe za a cillaku duk garin da aka so, zuciyata ba rigar sawa ba ce, balle a cire sanda aka so a kuma saka sanda aka so, Shi kuma so a makaho ne, baya ji baya gani baya kuma fahimta balle a gargaɗe shi, shi ne kamar dukiya ne wanda maganar mai shi kawai take ji, Ni bana soyayya domin So tsuntsune yana iya tashi daga kan wata ya koma kan wata, abun da zuciyar Barrister Aliyu Sufyan Alhassan ta sani shi ne _“KAUNA”_ irin ta har abada, ƙauna wacce zan iya mutuwa akan ta, ban san sacrifice a cikin Ƙauna ba, Cikakken namiji shi ne mai faɗa domin cimma nasara, nasara bata tabbata sai da tarin ƙalubale, ƙalubale a rayuwa shi ke nuna yarda da ƙaddara, yadda da ƙaddara ke nuna yarda da Allah Ubangiji maɗaukakin sarki" Ya yi shiru yana sauke numfashi kafin ya daki kafaɗar Captain Alpha ya ce "My friend, fight for your love"

"And you too Barrister Aliyu Sufyan Alhassan, kada ka manta ko a kasancewata Cousin zan iya yi maka illa"
Alpha ya sake faɗa a siga ta ya zama dole ka bar abinda zuciyarka ke so. Murmushi kawai Aliyu ya yi domin ƙoƙarin magana kawai yake yana faɗin hakan ya shiga mota, daidai nan Latifa ta ƙarasu ta ce

"Meke faruwa, kai da.....,"
Sauran maganar ta maƙale ganin Captain Alpha tsaye jikinsa sai ɓari yake shi kaɗai ta yi saurin nufar Aliyu ta ce "Yaushe ka zo?" “.... Not too long”
"Tafiya za ka yi?" Latifa ta sake tambaya ba tare daya kalleta ba ya ce
"In sha Allah" Ta ce "Ok then, Bye zan ki raka na ji jikin" Ya ware idanu akan Lafita ya ce "Ok love"
Ya yiwa motar key tare da yin reverse ya bar wajan da gudu.
Da sauri Alpha ya shiga ta sa motar har lokacin jikinsa ɓari yake yana jin Anti na kira amma ya yi banza. Gabaɗaya Khan's family suna can kan Aaliyyah dake ta faman kukan tafiyar Majeederh da ƙyar suka lallaɓata tare da shiga napep su kai gida.

New life
Airplane ɗin Emirates ya sauka a filin sauka da tashin jirgi na Cairo International Airport, kasancewar tsakanin Nigeria da Egypt tafiyar 5 hours 25 minutes ce. Ya sanya su ka yi saukar dare, weather garin ta bambanta data ƙasa Nigeria, Ruwan sama: 1 Laimar iska: 30 Iska 18km/h tun a step ɗin farko na jirgin ƙofofin fatar jikinta suka buɗe suka shiga amsar saƙon sauyin yanayin da suka samu. A hankali Majeederh ta ɗaga kanta sama tana ganin sararin samaniya sama ɗaya ce kaf duniya, amma ta bambanta da saman data gani a taushashe ta ce “Majeederh a Misira”

Misira/ Egypt
Kasar Misra,ko Masar tana kudu maso gabashin Afrika, kuma tana kudu maso yammacin Asiya, ɗaya daga cikin muhimman siffofin da take taƙama da su shi ne na kasancewarta a kan mararraba ta kusa da nahiyar Turai. Sannan kuma tana matsayin ƙasar da ta kasance mashiga tsakanin Afirka da nahiyar Asiya. Har ila yau kuma, ita ce ta haɗa hanyar safara ta cikin ruwa, tsakanin tekun Mediterrenean da tekun Indiya ta hanyar Bahar maliya. Harshen ƙasar Larabci ne, Shugaban ƙasar Abdul-Fatah El-sisi ya wadata ƙasar shi da komai, kuɗin ƙasar kuma Fam ne, ita ce ƙasar da tafi ko wacce yawan Al'umma a cikin ƙasashen Larabawa, ga babban birninta Al'ƙahira har ila yau gata a ƙarshen kogin Nilu, wanda shi ne kogi mafi girma a duniya.

Majeederh ta buɗe ido jin ana tambayarta da larabci "Shin ko lafiya kike?" Majeederh ta kalli kyakkyawar farar budurar dake tsaye kusa da ita kafin ta ce.
"Lafiya lou" Budurwar ta ce "Ma sha Allah, Sunana Ƙhulud Arzaan daga Saudiyya na zo nan karatu tare da mijina Ajlaal" Ta yi mata bayanin cikin larabci. Majeederh ta sake murmushi ta cikin liƙab ɗin kafin ta ce "Ma sha Allah, Allahumma Barik"

"May i knw You?"
Cewar Ƙhulud Arzaan Majeederh ta ce "Me zai hana?" Ta gabatar mata da kanta ganin yarinyar nada nutsuwa, Ƙhulud Arzaan ta juya idanu ta ce "Ina mijinki?"
"Bani da aure" Majeederh ta faɗa a taƙaice, Ƙhulud Arzaan da bakinta baya shiru ta ce "Oh sorry, kuma Abbanki ya barki barin ƙasarku zuwa wata babu muhrrami? Ba kyau hakan, shi namiji Garkuwa ne"
"Nawa Uban da kansa ya tursasani zuwa, ko da zan mutu a nan" Majeederh ta faɗa a zuciyarta tana ƙara karaya da lamarin mahaifinta. Daga nan gabaɗaya babbar mota ce ta sake kwasar su zuwa inda aka tana ta domin su, zuwa wayewar gari kuma za su fara shiga Al-Azhar University.
Tana kwance idanunta a sama tunanin rayuwarta da makomarta kawai take na yadda zata iya gabatar da rayuwa a ƙasar Misira babu kowa nata, har dare ya tsala bacci ya kasa ɗaukan idanunta a lokacin kuma ta mance da batun wanda suka haɗu a jirgi. Ta mirgina kaɗan tana riƙe mararta dake mata wani irin murɗawa tsigar jikinta sai tashi take tana zubewa kofofin gashin jikinta duk suka buɗe alamar a shirye suke da karɓar abin da suke buƙata. Ta ƙanƙame jikinta tare da jurewa waje guda tana jin gabaɗaya duniyar na yi mata zafi, al'amarin da take ji ya tsananta ta miƙe tare da tsugunawa tana girgiza kanta a raunace ta ce
"Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Ubangiji ka kawo mini ɗauki, Allah ka dubeni ka kare mini martaba da kimata har zuwa ɗakin mijina idan ina da rabon yin aure idan bani da rabo Ubangiji ka tsare mini imanina ka kare mini budurcina har zuwa sanda raina da ruhina zai dawo gareka" Jikinta duk ƙyarma da ɓari yake ji take kamar ana kwara mata wuta a fatarta mararta ta kumbura, ƙirjinta ya ƙara girma fiye da ƙima tabbacin tana kan buƙatar namiji. Tana nan har ta ji kiran farko na sallar Subhi da sauri ta miƙe tsaye tare da shiga toilet ta sakarwa kanta shower tana sauke wani wahalallan numfashi, ta fito ɗaure da towel duk a tsorace take na rashin sabo. Duguwar riga ta saka ta buɗe fridge ta ɗauki fruits da ruwa da dabino kaɗan ta ci ta sha ruwa sosai kana ta ɗauki niyyar azumi kamar yadda ta saba. Raka'atul fjr ta yi tana zaune Ƙhulud Arzaan ta shigo cikin kyakkyawar shiga ta ce "Zo mu je masallaci"
"A masallaci ake sallah?"
Ƙhulud Arzaan ta ce "Eh"
Ta faɗa ne kawai amma hankalinta duk yana kan fuskar Majeederh bata taɓa ganin zubi da tsarin halitta kamar na Majeederh Abdul'aziz Khan ba, har ta shirya cikin wata abaya ruwan huda idanun Ƙhulud Arzaan akanta ta sanya hijabi mai kyau kana ta saka Liƙab sabo. A hanya Ƙhulud ta ce
"Kuma are you sure a Nigeria kike?" "In sha Allah" cewar Majeederh "You look familiar"
"Me??" Majeederh ta tambaya domin bata ji ba, Ƙhulud ta watsa hannun ta ce "Mafi mushkila"..... Suna shiga Al-Azhar University Majeederh ta cike komai da komai akai sa a department ɗaya suke da Ƙhulud Arzaan, course ɗin farko Majeederh ta ɗauke komai da komai a kanta domin da gaske karatun ta zo ba wasa ba, burin mahaifinta zata cika har ƙarfe biyar suna cikin makaranta.
Abbu ne tsaye a gaban wani mutum ya ce "Maganar gaskiya nake maka, gidana da nake ciki nake so a rushe komai a sauya sabo kafin bikin ƴata Ruma" Alhaji Bashir ya ce "Taya zaka biya?" Abbu ya ce "Ni nake da hanyar biya, mai ƴa kamar Majeederh har a faɗa masa wani abu?" Alhaji Bashir ya yi dariya ya ce "Ƴarka jarinka, to yanzu dai gasky ko zan maka wannan kwangilar sai na ƙara maka kuɗi a ƙalla dubu ɗari biyar akai shi ne ribata, idan kuma ni zaka bani auren yarinyar ma shikenan zai na yi maka haɗaɗɗen gida 200by 200 matsayin sadakinta kaga data dawo sai ayi maganar biki, ko kuma a ɗaura auren idan ya so sai na bita can" Abbu ya yi shiru Alhaji Bashir ya ce "Think about that Malam Abdul'aziz, bayan gida har kyauta zan maka muddin zaka aura mini Majeederh" Abbu ya ce "To a nawa zaka iya bani?" Alhaji Bashir ya zaro takarda ya ce "Faɗi adadin miliyan nawa ka ke so, ni kuma take zan baka zaka tashi daga matsayin Malam ka koma Alhaji" Jikin Abbu na rawa ya ce "Na amince, na amince wallahi zan baka auren Majeederh.....27
Alhaji Bashir ya gyara tsaiwa yana shu'umin murmushi ya ce "Bana ɗaukan asara ba kuma zan fara akan ka ba, ka yarda zaka bani auren yarinyarka Majeederh? Ni kuma na baka dukkan abin da ka ke so?" Abbu bai dugun tunanina ba ya ce "Na baka aurenta ƴata Majeederh halak makal, ko bayan bana raye" Alhji Bashir ya ce "Baka raye to waye zai tashi matsayin shaida?" Ya yi jim kafin ya ce "Allah da Manzonsa su ne shaidar hakan?" Alhaji Bashir ya haɗe fuska ya ce "Na san da haka, amma mutane huɗu shaidu nake so" Abbu ya shiga nazari idan ya ce a'a ya san tabbas zai dauma cikin wannan gidan nasa da baya samun ci-gaba, mafarkinsa na zama wani a duniya ba zai tabbata ba, hanya ɗaya ce wacce ta kasance madafar shi shi ne “Majeederh” Abbu ya ce "Zuwa dare sai ka dawo ni kuma zan haɗa maka shaidun" Alhji Bashir ya ce "Never mind, Allah ya kaimu" Su kai sallama Alhji Bashir ya shiga mota ya tafi, Abbu kuma ya koma gida. Yana shiga ya samu Mami zaune ya nemi waje ya zauna tare da yin shiru yana mamakin abin da ya hana Majeederh kiransa gashi har anyi kwana biyu.
"Lafiya?" Ya sauke numfashi ya ce "Ina yaran? Aaliyyah, Raihana, Ruma?" Mami ta ce "Ruma ta tafi raka Imran, Aaliyyah da Raihana sun je gidan Widad" Abbu ya numfasa ya ce "Rumana ta dinga janye jikinta daga yaron nan"
"Wanne yaron?" Abbu ya tsareta da idanu babu alamar wasa ta yi saurin cewa "Naga aurenta zai yi shiyasa bana damuwa" Abbu ya ce "Kina da tabbacin haka? Baki san meke ɓoye ba" Mami ta yi saurin cewa "Me ka ke nufi? Bayan shi ya ce yana son ta zai aureta?" Bai ce mata komai ya miƙe ya shiga duba gidansa lungu da saƙo deep down na zuciyarsa yana tunanin wa zai kira matsayin shaidu?...
Da daddare misalin ƙarfe tara Latifa Omar na kwance idanunta a sama kewar rashin Aminiyyarta na damunta, ga rashin kiran Aliyu wayarsa ma gabaɗaya a kashe take, she so much loves you ya yi tasiri a zuciyarta sosai. Ta ƙara juyawa idanunta rufe a hankali ta sake jawo wayarta tare da danna kira a number da tayi saving da “Heart choice” Cikin sa a kiran farko ta ji an ɗaga a marairaice cikin damuwa ta ce "Sweetheart" Almustapha ya yi shiru yana gyara zaman wayar a kunnenshi tare da juyawa ya kalli Aliyu dake kwance saman gadon asibiti ya yi mahaukacin ramewa "Hello"
Muryar Latifa ta sake dawo da shi hayyacinsa ya ce "Majeederh Abdul'aziz Khan, right?" Latifa ta zaro idanunta waje zuciyarta na bugawa, mene haɗin Aliyu da Majeederh? Ta yi shiru tuna muryar da ta ji kamar bata Aliyu ba, a hankali ta ce "No, Latifa Omar ke magana, Aliyu fa?" Ta yi saurin tambayar hakan cike da bin umarnin zuciya. Almustapha ya ce "Ok, mai wayar yana kwance asibiti" A ruɗe cikin tashin hankali idanunta har ya ciko da hawaye ta ce "Subuhanallahi! Wanne asibiti" Musty ya ce "Aminu Kano"
"Am on my way" kafin ta ajjiye wayar ya ce "Amma kamar dare ya yi, da kin bari zuwa safiya" Ta girgiza kai kamar yana ganinta ta ce "I can't, ba zan iya bacci bangan shi please" Musty ya ce "Ok, daman daya farka ke ya kira, so na kira ki wayar a kashe shi ne ya ce a nemi Malama Majeederh kuna tare" Ya faɗi hakan yana gyara ɓarnar da ya yi a baya. Daga haka ya yi hanging off.
Papa dake jin duka maganganun Musty da Latifa ya ce "Me ya sa kayi mata ƙarya Almustapha Sufyan Alhassan?" Almustapha ya shafa kansa ya ce "Shi ne mafita Papa, zan so a ɗaura auren shi da Latifa in prioud time. "He doesn't like her" cewar Papa. Almustapha ya ce "Yanzu mene amfanin haka Papa? Duk jiya yake kira mana suna ɗaya Majeederh, Hawwy, Hawwa'u, na tambaye shi me ya sa yake son Latifa bayan Majeederh ce a bakinsa?"
"Me ya ce?" In ji Papa.
"He refused to answers my question" Hajia ta juya kan Aliyu dake jin duk abin da suke faɗa amma idan ka ganshi zaka ɗauka bacci yake, hannunsu dake danne da ƙirjinsa kawai ke motsawa dalili bugawar da zuciyarsa ke yi.
"Me ya sa Zaki?" Ya buɗe gajiyayyun idanunsa da sukai jajur kamar ba zai magana ba har Hajia ta ƙara cewa "Meke faruwa ne?" Ya yi saurin riƙe hannun Hajia ya ce "Ban sani ba, Amma ina sonta a gefena" "Aurenta za ka yi?" Hajia ta tambaya tana riƙe nasa hannun.
"A duk sanda na ji ina son aurenta sai na ji na tsaneta, amma idan na cire batun auren sai na ji babu wacce nake son gani sai Majeederh, i want to see by my side, ko sunanta na ji zuciyata bugawa take don Allah ki taimaka mini Hajia please" Papa ya yi zuru yana ganin ikon Allah, wani abu mai kama da almara. Bai taɓa ganin hakan ba, ko a film na hausa, Indian movie ko series balle novels, ace wacce mutum ke son aura daban wacce kuma take zuciyarsa daban "Ikon Allah" Cewar Papa Hajia ta ce "Ikon gaske, Yanzu me ka keso" Cikin sauri Aliyu ya ce "Majeederh na keson gani Hajia please" Hajia ta zabga tagumi Idanunta jajur alama ta jima tana kuka domin tun jiya Aliyu bai san inda kansa yake ba sai yanzu, Papa ya sauke numfashi cike da jimamin al'amarin da kuma tausayin ɗan nasa ya ce "Zan nema maka auren ita Majeederh a wajan Mahaifinta idan ka amince, kada ka sanwaltar da rayuwarka akan ta" Aliyu ya girgiza kai ya ce "Ba aurenta zan ba" Almustapha dake tsaye harɗe da hannu ya ce "Ok ita Teddy ce da za a ajjiye maka ita kai ta Kallonta? Me ya sa ka ke son kan ka har haka? Kana ganinta, But you don't want to marry her? what kind of nonsense and stupidity is that??" Aliyu ya marairaice ya ce "Ka tausaya mini Yaya, ni kaɗai na san halin da nake ciki idan kai baka rarrashi su Hajia ba waye zai taimaka mini?" Jikin Almustapha ya yi sanyi ya ce "Papa Hajiya help him don Allah kada wani abu

Please Login or Register in order to submit comment