Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Mama ta ƙara sauke masa wani, ganin haka yasa Widad fashewa da kuka sosai ganin yadda ake marin yayan nata Uncle Bello ya nuna Alpha da hannu ya ce “General Ajzan-Alpha Bello Khan wallahi yau ko da gawarka ne sai an ɗaura aurenka da Hawwa'u" Alpha ya juya ya kalli Majeederh ya dawo ya dawo ya kalli Uncle Bello muryarsa bata fita ya ce "Sai a ɗaura da gawar tawa"
Yana faɗin haka ya fice daga cikin parlourn, Majeederh ta miƙe zata bi bayansa sai a lokacin Anti ta ce "Kada ki kuskura ki bi bayan wanda bashi da imani" Uncle Isma'il ya miƙe da hanzari ya ce "Kada Alpha ya cutar da kansa fa?" A takaice Uncle Bello ya ce "Rabo dashi daidai nake da zamaninsa, he really disappointed me ya nuna bashi da biyya ban isa da shi ba" Kafin kowa ya yi magana aka ji faɗuwar abu gabaɗaya suka juya Majeederh ta faɗi babu numfashi a ƙirjinta.....

Duk da kiran asubar da ake bai sanya ɗaya daga cikinsu ya motsa ba, ko wanne ka kalli fuskarsa za kaga tashin hankali musamman Dattijan mazan. Uncle Isma'il ya saka hannu ya sharce zufar data gangaro masa yana cire hular kansa ya ce "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un!" Ya juya ya dubi Uncle Bello daya kasa cewa komai idanunsa ya yi jajur ya kalli Mama dake rusa kuka sosai ya ce "Wai mene ya faru mai zafi har haka da yaron nan zai mana wannan cin mutunci?" Mama ta share hawayenta ta ce "Idan ni na haifi Alpha da cikina to wallahi.....," "A'a please" Anti ta tare ta da sauri wanda ya hana Mama ƙarasa faɗin abinda tayi niyya. Uncle Bello ya ɗago kansa ya ce "Ɗan cikina? Ɗan dana haifa Isma'ila?" Uncle Isma'il ya sauke numfashi ya ce "Dole akwai wani abu, yadda Alpha ya birkice kamar Mahaukaci sabon kamo zaka san something is fishy?" Jinjina kai kawai Mama take kafin suyi magana motar Abbu ta shigo cikin compound ɗin gidan Uncle Bello wanda aka baza rumfuna na ɗaurin aure, Abbu ya jima cikin motarsa kafin ya buɗe ya fito da sauri Mami ta fito tana mara masa baya, tun a balcony kafin su ƙarasa ƙofar parlour suka fara jiyo kukan Mama, Mami kamar zata kifa haka ta bangaje Abbu ta shige "Ba dai an fasa auren ba?" Abinda Mami ta faɗa kenan tana binsu da idanu, Abbu ya shigo tare da jingina da jikin bango can ya ce "Isma'ila, Bello na ji kira cikin gaggawa gashi ina ƙoƙarin rasa sallar asuba?" Uncle Isma'il ya miƙawa Abbu white paper ya ce "Read, karanta" Har Abbu yaƙi amsa sai kuma ya saka hannu ya karɓa tare da buɗewa hannunsa na rawa idanunsa ya sauka akan handwritten ɗin Alpha da yake cewa....

DEAR PARENTS.
_Bani da baki ko kalmar da zan muku bayani wajan fahimtar daku abinda nake nufi, amma na zaɓa mana hanya mai sauƙi da warware ƙullin da yake ƙoƙarin raba zumunci, ban kashe kaina ba, ban kuma zauna a cikinku na ɓata muku sunan family ba, more especially mahaifina, kayi mini komai a rayuwata ta duniya har kawo lokacin da nayi wayo na girma na mallaki hankalin kai na, Ina son Majeederh a matsayinta na ƴar uwata wacce jinina da nata suke yawo a jijiyoyin ko wannenmu, amma bana sonta ta aure bana ƙaunar zama da ita, akwai yarinyar da nake so a duk sanda kuka amince mini zan gabatar muku da ita a matsayin matar da zan aura kuma sirikar ku._
_Naso karɓarta matsayin mata kuma nayi muku biyayya, amma wallahi zuciyata ta kasa yarda da wannan ƙudirin idan na auri Majeederh ba zan iya sauke hakƙin aurenta akai na, zanta cutar da ita, zata zama bora a cikin gidana, zan wulaƙanta ta, wulaƙanci da human rights za su iya hukantani, zan muzantata, muzancin da babu macen da aka taɓa yiwa irinsa, zata zama baiwa a cikin gida, irin bayin da ba a samun su a yanzu sai ƙarnin baya irin bayin gidan sarauta ɗin nan, zata zama almajira a cikin gidan mijinta, To idan zan iya aikata mata duk wannan gwara ban aureta ba, nima ina mata fatan samun rayuwa mai ƴan-ci, ina gudun na tashi da ɓari ɗaya a shanye rana gobe ƙiyama_
_Babban Dalilia na rashin aurenta shi ne, Ni mashayi ne, ni mazinaci ne Majeederh bata dace da mutum mara tsafta kamar ni ba, ku yafe mini don girman Allah, kuji tausayina kada ku aibata ni, zan dawo duk sanda kuka yarje mini idan kuma mutuwata ta riskeni ina roƙan kuyi mini addu'a da samun dacewar Ubangiji!_

~G.A.B Alpha~

Abbu ya ɗauke numfashi lokacin da idanunsa ya sauka akan kalma ta karshe, date da time. A sanyaye ya ce "Yaushe ya tafi?" Mama ta ce
"Ya tafi ko ya gudu? Wallahi ƙarya Alpha yake baya Shaye-shaye, duk mutum bai hali irin wannan baya zama inda yake, ya tsani zin kamar yadda ya tsani fitar hawayena" Anti ta ce
"Me ya sa zaiwa kansa irin wannan tabon to?" Uncle Isma'il ya ce "That's what i was thinking too" Wayar Abbu ce tayi ƙara ya ce "Ina zuwa" fita ya yi yana ɗaga kiran ya ɗan yi shiru sai kuma ya ce "Thank you, na gode sosai" Ya kashe wayar kana ya dawo. "Yanzu mene abin yi?" Uncle Bello ya miƙe ya ce "Ku san hanyar daza ku bi ku kwantar da hankalin Majeederh, ita nake tausayawa wallahi da ina da wani yaron bayan shi da a yanzu ba sai anjima ba zan ɗaura masa aure da ita, Allah ne shaidata, Alpha kuma sam ba zan masa baki ba, amma zan ga illar bijrewa iyaye nasa kalar godiyar kyautatawar da mukai masa kenan" Yana faɗin haka ya fita gabaɗaya mazan fita sukai domin gabatar da sallar Asuba zuciyoyinsu babu daɗi. Mami ta kasa cewa komai domin ta girgiza da al'amarin, wani irin baƙon al'amari ne wannan? Only God knows! Bayan Anti tayi sallar Asuba bata jira mijinta ba ta nemi napep zuwa gida...
Wajejen huɗu na rana ta fara buɗe Idanunta da ƙyar, wanda sukai mata nauyi har lokacin drip ne manne a hannunta, ta juya kaɗan sbd ciwon da ɓarin kanta yake mata ga wani dishi dishi da take gani kamar mai hawan jini, da sauri kuma ta buɗe idanun tare da yin shiru tana ƙoƙarin tina mene ya kwantar da ita ciwo haka? Duk ƙoƙarinta na son ganin bata kwanta ba? "Sannu Anti Jeederh" Aka faɗa daga can gefe, ta juya suka haɗa idanu da Aaliyah da kuma Sona ɗiyar Anti ta ce "Ƙarfe nawa?" A sanyaye Aaliyyah ta ce "Huɗu da kusan minti goma" Majeederh tai shiru sai kuma ta ce "Huɗu?"
“....Ai an kwana har yamma tayi, don baki da lafiya ne" Majeederh ta ce "Kina nufin kwana na ɗaya kwance?" Ta bata amsa da "Eh" Daidai nan Anti ta buɗe ƙofa ta shigo tana kallonsu ta ce "Yaushe ta tashi?" Sona ta ce "Yanzu Anti" Anti ta ce "Sannu Hawwa'u" Ta ɗan yi murmushi tare da yin shiru a hankali kuma ta ce "Shikenan na zama matar Yaya? Ni ma nayi aure an ɗaura mini aure da Yayana General Alpha ko Anti? Allah na gode maka za a daina yi mini gorin aure ni ma nayi aure ƙaddarata ta zo ƙarshe....


*Mijin Malama it's a paid book..... Subscribe before you Read🤓*

6850917335
Na'ima Shu'aibu Sulaiman fidelity bank..... Kindly send your evidence via 08119237616 Book 1 and 2 1k.

Naso yin typing ɗin ya fi haka yau Sadakar Bakwan rasuwar da akai mini🙏🏿 Mu haɗu weekend a arewabooks.*_Huhuu! To bance komai ba, amma ya kuke yaƙin neman MIJIN MALAMA Don't you know cewa na kuɗi ne? Mata masu fama da Jinkirin aure wannan littafin sadaukarwa ne a gareku🤓😥..... A daina shelar neman Mijin Malama tunda akwai Mazan da yawa Allah kaɗai yasan waye mijin Madam come and Subscribe before you read, meye wata ƴar 1k da zata muku wahala?........ Chat me via WhatsApp 08119237616_*


Kasa bata amsa tayi saboda tashin hankali, ganin kowa ya yi shiru ya sa ta ce "Finally, ni ma na zama matar aure Allah na gode maka bisa wannan tarin Ni'imar da kayi mini, na ƙara yadda wani jinkirin alheri ni Anti, gashi yanzu Ubangiji ya bani nagartaccen miji" Majeederh ta yi murmushi tana goge hawayen farin ciki, duk wani zafi da ƙunci ya kau a ranta, tabon dake cinta a zuciya ya hanata sukuni gabaɗaya ta neme shi ta rasa. Aurenta da Yayanta Alpha ya zama abu na farko wanda ba zata taɓa iya mantawa fashi ba.
Anti ta juya ta kalli Aaliyyah da Sona ta ce "We need privacy, ku je waje yanzu zan fito" Aaliyyah ta yi waje, Sona ma ta bi bayanta. Anti ta kalli Majeederh tana murmushi wanda bai kai zuciya ba ta ce "To Amarya" Kunyar Anti ta kamata, ta ɗan yi ƙasa da kanta a hankali Anti kamar kazar da ƙwai ya fashewa ta ce "Ki je ki yi sallah, wanka,cin abinci we need to talk ok" Majeederh ta miƙe tsaye da sauri ta dafe gefen kanta "Sorry kan ne dai?" Anti ta tambaya tana riƙe kan nata, jijiyoyin kan duk sun fito sai har bawa suke idanunta jajir, ta ƙara yin murmushin ƙarfin hali ta ce
"Abbu ma zai farin ciki ko Anti? Zai yi farin ciki yaga aurena, ni kuma zan aurar da Aaliyyerh" Gabaɗaya Anti tunanin dake sarrafa ƙwaƙwalwarta ne ya tsaya da aiki ta tsaya ta dinga kallon Majeederh da ƙyar ta iya cewa "Ki je ina jiranki Majeederh" Ta nufi bathroom da ƙyar ta yi wanka tare da sallolin dake kanta, Anti ta kawo mata wata atamfa Valisco milk da yafin blue a jiki, ɗinkin duguwar riga Ashap. Majeederh ta dinga kallon kayan domin bata saba saka irin su ba, tina cewa ko wacce amarya irin kayan da take sakawa kenan sai bata ce komai ba, ta shirya tsaf tayi wani irin masifaffen kyau, kamar irin Fulanin Usul ɗin nan ko na Daji ko kuma irin Half-caste ɗin nan jinsan larabawa da yankin Niger na Agadas ko Sudawa. Idanunta zuru-zuru tayi muguwar rama kamar kuɗin guzuri, fuskarta kamar tafin hannu. "Anti na kira number Yaya a kashe fa? Zan yi masa godiya da aurena da ya yi" Anti ta kasa bata amsa ta juya da sauri tare da ficewa daga bathroom ɗin ta nufi part ɗin Uncle Isma'il lokacin yana zaune saman kujera yana waya, tana zuwa ta rushewa Uncle Isma'il da kuka tsabar firgici ya saki wayar hannun sa tare da miƙewa jikinsa na rawa ya ce "Subuhanallah! Ƴar Aljanna ke dawa?" Anti ta dinga kuka jikinta har rawa yake kai kace Uncle Isma'il ne ya rasu, ko kuma an aiko mata da mutuwar mahaifinta daga Gombe.
Cikin kuka ta ce "Mun shiga Uku Yallaɓai, mun shiga uku Abban Jawaad" Uncle Isma'il ya ce "Ba mu shiga uku ba da izinin Allah, Ubangiji na tare damu" Ya saka hannu ya ɗagota yana riƙe fuskarta ya ce "Majeederh ko?" Ta kasa magana sai kuka Uncle Isma'il ya rasa yadda zai rarrashi matar tasa ya kamo ya rungume ya ce "Haba bansan fulani da raguwar zuciya ba, haba jinin Gwambawa haba ƴar Bafullatanar matata uwar ƴaƴana kukanki azaba ne a zuciyata" Ya yi murmushi cikin dauriya ya ce "Akanki bulala nawa na shanye? Gwambawa sun gana mini azaba a haka na shanye shaɗin na aureki, mene ya kawo haka? Kinga juriya ce da yadda da Allah da ƙarfin addu'a, ki zama jaruma kamar yadda na zama jarumi a soyayyarki ki yi haƙuri don Allah uwar Jawaad da Sona, garkuwar Du'a haba matar Isma'il amarya kuma uwar gida, idan baki jure ba ina zaki samu ƙarfin qiwwar rarrashin Majeederh" Ya goge hawayen da suke bin idanunta tana shassheƙa ta ce "Na rasa yadda zan yi babu kalaman ban haƙuri ga Majeederh, wannan yaron ya cucemu he disappointed us" Uncle Isma'il ya ce "Da wannan salon yaudarar taki da kika sace zuciyar Isma'ila da shi zaki rarrasheta, komai na rayuwa yin Allah ne ba namu ba, bama da ikon hana komai ko faruwar shi take heart please" Miƙewa tayi tana gyara ɗaurin zaninta ta nufi part ɗin da Majeederh take ciki. A zaune ta sameta idanunta rufe ƙirjinta na ɗagawa kamar wacce asthma ɗin ta take shirin tashi, kafin ta ƙarasa ta nufi wajan freezer ruwa ta ɗauka mai sanyi ta tsiyaya a kofi ta ce "Drink"
"Azumi nake" Majeederh ta bata amsa, Anti ta ce "Ai kowa zaki karya azumin me?" Ta yi ƙasa da kai ta ce "Nuna godiya ga Ubangiji" cewarta.
Anti ta nemi waje ta zauna tana bin bedroom ɗin da kallo a hankali ta ce "Hawwa'u!"
"Na'am Anti" Ta amsa gabanta na faɗuwa haka kurum. Anti ta ce "Mece ƙaddara?" Da mamaki Majeederh ta kalli Anti sai kuma ta ce "Jarrabawa ce da Ubangiji yake jarabtar bawansa domin gwada imaninsa, shi ya sa aka ce yarda da ƙaddara shi ne cikin imanin ko wanne musulmi" Anti ta sauke ajjiyar zuciya ta ce
"Allahamdulillah" Wajan ya yi shiru can dai Anti ta ƙara kiran sunan Majeederh a wannan karam kasa amsawa tayi ta ce "Hawwa'u mace da ciki da ciki ta mutu, miji ya rasu ya bar matarsa da yaransa, uwa ta rasu tabar miji da yaranta, iyaye sun rasu sun bar yara, Gabaɗaya hakan tsarin waye? TSARIN ALLAH, Ubangiji ke da ikon ƙaddara kuma shi ne wanda masarrafar rayuwarmu ke hannunsa, ya haliccemu domin bauta masa dayin biyya da iyaye duk mutumin da ya cika haka bazai taɓa tuzarta ba, ƙaddara shuɗaɗɗiyya ce, ba za'a taɓa hana zuciya ƙuntata ba, domin baka da ikon yin haka amma akwai mataki na kare kai, Majeederh ki yarda Allah ke tsara duk abinda zai faru, Mu so wanda ya ke son mu shi ne soyayya, mu so Mutum ya so me shi ne dacewa a soyayya, mun so abu babu damuwa maybe abin ya dace aso shi saboda nagartar da yake da ita, rasa abinda zuciyar mu ke so, bashi yake nufin rasa rayuwarmu ba, watakila rabonmu na ta wani wajan yana jiranmu, idan soyayya na gudunm ƙauna ta har abada tana can wata duniya idanu rufe tana nemanmu, faɗuwa a soyayya nuni na cewa hakan ba alheri bane a ranmu, ba laifi bane don munyi kuka idan an yaudaremu, babbar asara ce ka komawa wanda ya guje ka ko ya yaudareka, hakan na alƙinta mana mun rasa wani abu a baya inma mu rayuwa inma mutum mu rayu da sanin Ubangiji ke zana komai cikin tsaftaccen allon lauhil mahfuz, yi kuka Majeederh akan farin ciki kada ki yi kuka akan baƙin ciki...." Anti ta yi shiru kana a hankali cikin rauni tausayi da fargaba ta ce "Ba a ɗaura aurenki da Alpha ba, domin ya gudu bisa ra'ayinsa na ƙin auren wanda Ubangiji ne kaɗai ya san dalili" Da wani irin Expression Majeederh take kallon Anti, kallon da sai da hantar cikinta ta motsa, gabanta ta faɗi domin bata taɓa ganin rikiɗewar idanu lokaci ɗaya irin na Majeederh ba, ƙarar tsayawar abu a wuyan Majeederh yasa Anti taɓata ta ce "Majeederh ki yi haƙuri ki yi haƙuri, ban san yaushe ne hakan ta faru ba, ban san mene ya sauyawa Alpha ra'ayi ba, amma nasan yana son ki ina ganin hakan acikin idanunsa, rabonki yana wani tsagin rabo mai girma rabon da zai bawa kowa mamaki,ki yi haƙuri da rayuwa Majeederh" Maimakon kuka sai taga Majeederh ta saki Murmushi, murmushi mai kyau wanda bata taɓa ganin irinsa a fuskarta ba, irin wanda dashi gwara kayi kuka irin sa yafi kuka ciwo a zuciya hakan na nufin Mutum yana cikin halin da kuka ya yi masa kaɗan. Ta miƙe tsaye ta ce "Zani gida"
"Majeederh are you okay?" Ta ce "In sha Allah" A hankali ta ce "Kiyi haƙuri ki miƙa lamuranki ga Ubangiji please" Ta ƙara yin murmushi ta ce "Ba komai, bani hijabi da liƙab ɗin Sona" Ba zata iya tsayar da ita ba, akan Idanunta ta saka hijabin da liƙab ɗin tare da amsar kuɗin napep wajan Anti ganin haka yasa Anti ƙwalawa Aaliyyah kira ta ce "Maza jeki ku tafi akwai matsala" Jefa ƙafafuwanta kawai take without knowing ina take takawa, da gudu kuma Aaliyyah ta cimmata ta tsare mai napep ta ce masa Lodge Road..... Misalin 8 na dare wani irin ciwon kai ya kama Majeederh har bata iya gani sosai ga jiri da ƙyar ta miƙe ta nufi part ɗin Abbu da yake kiranta tana zuwa ta zube a ƙasa wajan ƙafafuwansa ta kasa cewa komai. Ya dubeta ya ce "Kin kyauta"
Da sauri ta kalle shi tana son tambayar mai tayi sai kuma tayi sbd nauyin da harshenta ya yi mata wanda ya tilasta mata kame bakin. Ya gyara zama da kyau ya ce "Kin tuzartani cikin dangi Majeederh,kin kunyatani kin cin mutuncin shekaruna, akan namiji? Yanzu me gari ya waya? Kin barwa kanki abin gori kin bar mini nima koma babu komai tarihi zai kafo akan Alpha ya gudu saboda baya ƙaunar aurenki" Ya girgiza kai ya ce "Majeederh kin yarda ni mahaifin ne?" Da sauri ta ce "Wallahi Abbu ban taɓa kokwanto hakan ba" Ya miƙe tsaye tare da ɗakko Alkur'ani mai girma daman yana da alwala ya ɗora hannunsa akan Alqur'ani izzu sittin ya ce "Wallahi wallahi Allah Majeederh ni ne ubanki mahaifinki, wanda jinina ke yawo a jijiyoyinki, na rantse da Allah ni ne mahaifinki ni Alhaji Abdul'aziz Khan" Ta dinga girgiza kai babu hawaye ko ɗaya a Idanunta ta ce "Don Allah Abbu ka bari" Ya kalleta ya ce "Amma ni ina tunanin kamar an sauya mini ɗiyata, kamar ke ɗin ba Majeederh ta bace"A rikice ta ce "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un, Ya Allah wallahi bana gane komai ko fahimta" Ya zauna ya ce "Kin kasa bani abinda nake so nake buri Majeederh, na rasa yadda zan yi dake kin kasa rufa mini asiri, Hawwa'u aure fa ba dole bane tunda zaki iya riƙe kanki, kuma ni na san jinkiri ne kawai kika mijinki nan zuwa ki taimaka mini, ni mahaifinki ne" Majeederh ta ce "Ka yafe mini, ba sake cewa ina son kowa ba shi na don Yayana ne ai kaga ma bai aurenin ba shikenan sai na fara neman aiki" Abbu ya saki kuka wiwi yana cewa "Faɗa kawai kike Majeederh ki je kawai nama haƙura kiyi aurenki kawai kuma na yafe" A rikice, rikicewar da ko sanda aka faɗa mata Alpha ya gudu ya fasa aurenta ba ta yi ba ta riƙe ƙafar Abbu ta ce
"Nayi asara Abbu, rayuwata ta halaka na shiga uku akaina kake zubar da hawaye mai yasa zaka ja mini azabar Ubangiji Abbu Innalillahi wa'inna ilahir raji'un Abbu kuka kake a kaina??" Ganin yadda halinta ya tashi ƙarara yasa ya ƙara rushewa da kuka tashin hankali ya bayyana akan Majeederh amma ko ɗison hawaye babu a fuskarta zuciyarta ta ƙafe ta ce "Na tuba, wallahi na tuba gobe zan nemi aiki zan fara nayi maka al'ƙawarin wadataka da abinda kake so iya kacin iyawata, za ka yi alfahari dani Addu'arka da albarka ka nake nema kawai" Ya share waye ya ce "Da gaske zaki aikin?" Ta ce "Na yi alƙawari" Ya sauke ɓoyayyiyar ajjiyar zuciya ya ce "Kin cika ƴa, na gode ƙwarai Allah ya yi miki Albarka" Ta miƙe da ƙyar zata fita ya ce "Ga mata nan da yawa na garari duka babu aure, shi fa auren nan lokaci ne kiyi ta azumi" A wannan lokacin bata fahimtar komai, dishi dishi take gani ga jiri ga kuma haki da ƙyar ta lalubi hanya ta nufi part ɗin tana ta faɗi wanwarsa a tsakiyar ɗakin babu numfashi..... Bayan kwana bakwai da faruwar komai Latifa na driving fitowar su kenan daga B.u.k sun shiga duba wani ita da Majeederh, ganin ta ɗauke hanya ya sanya Majeederh ɗago kai a hankali tare da zubawa titin idanun sai dai bata ce komai ba, ta maida idanunta ta rufe mamakinta kuma bai shige ganin yadda Latifa take wani Mahaukacin driving ba. A hankali ta ce "Kee" Murmushi kawai Latifa ta yi cikin sauri ta ce "Ina da hankali ba kashe mu zan ba, nasan adadin giyar dana saka ban shige limit ba" Ta juya ta kalli Majeederh suka haɗa idanu ta ɗaga mata gira ta ce
"Afuwa Malamarmu zan shiga Tahir Quest Palace ne" A gajarce Majeederh ta ce "Hotel?" Latifa ta ce "Eh, Abu zan amsa ai" Majeederh ta yi shiru tana tunani me zai sanya ita kowa ta shiga hotel? Ai hakan babban zunubi ne, kayi ta ganin kartin maza ba zata iya wannan mummunan saɓon ba. Bata ce komai suna zuwa gate ɗin shiga Majeederh ta ce "Wait"
"Like how? Kamarya na tsaya?" Ta ya motsa fuska ta cikin liƙab ta ce "Amai nake ji" Jin hakan yasa Latifa tsayawa Majeederh ta fito da ƙafafuwanta daga cikin motar tana fitowa ta ce "Shiga,ki saman nan" Girgiza kai kawai Latifa ta yi taja motar a 150 ta shige cikin Hotel.... Tana tsaye bakin Hotel ɗin ta ji an ce "Malama Majeederh me kike a nan?" Da sauri ta ɗago kanta ganin ɗan unguwarsu yasa tayi saurin jan jikinta baya daidai nan mai napep ya tsaya ta shiga, saurayin ya dinga mamakin ganinta a bakin hotel. Har sama da awa guda Latifa bata fito ba, can sai ga motar ta ganin babu Majeederh ya sanya ta kirata a waya ta ce "Kina ina ne?" A taƙaice ta ce "Gida"
"Gida kuma? Au tafiya ki kai" Ta ce "Kamar uzurinki babba ne, ni kuma ina jina Uncomfortable a wajan" Kafin ta yi magana Majeederh ta kashe wayar. Lokacin da Latifa ta isa gida ta samu Aliyu tsaye a balcony sanye da wata farar singlet sai gajeren wando hannunsa riƙe da coke yana sha, kallo ɗaya ya yi mata ya ɗauke kai, ta ƙarasa inda yake tana murmushi ta ce "Sweetheart harka dawo?" Bai ce komai ba. Ta saka hannu ta karɓe coke ɗin hannunsa tana sha ta ce "Am sorry"
"For...?" Aliyu ya tambaya yana zuba mata narkakkun idanunsa. A hankali ta ce "Da daɗewa, na raka Majeederh meeting ne a Tahir Quest Palace" Ya dinga kallonta sai kuma ya ce "Ohk" ta zauna a cinyarsa ta ce "Me kake yi kai ɗaya?" Ya haɗe fuska sosai ya ce "Ɗaga ni" Ta ɗaga shi ya dinga kallonta up to toe kana ya ce "Exlty, tun jiya kayan nan ke jinki kenan baki wanka ba?" Ta yi shiru ya miƙe tsaye tare bi ta gefenta ya shige ciki, yana zuwa ya haura sama not too long ya fito cikin tattausan voyel fari tas sumarsa kwance luf hannunsa zube cikin Aljihu ganinsa haka ta ce "Ina zaka?" Ya dinga kallon parlourn kamar na mahaukata sai warin yawu yake, Aliyu ya rasa me ma zai ce can ya ce "Ki tabbatar kin gyara gidan nan, Hajia na hanya" Yana faɗin hakan ya fice, ya ɗauki good 20 minutes kafin ya shigo yana fitowa daga mota ya nufi cikin gida, yadda yabar parlourn tun jiya haka yake ya ajiye takeaway ɗin hannunsa cikin ɓacin rai ya nufi bedroom ɗinta yana toshe hanci, ganinta ya yi durƙoshe jini na zuba ta ƙasanta a rikice ya nufeta yana faɗin "Wife lafiya badai cikin ne ya sake zubewa ba?" Cikin mawuyacin hali ta ce "Aliyu shikenan yanzu ma mun rasa shi, na rasa babyna Aliyu cikin ya zube" Gabaɗaya Aliyu ya rikice tashi ƙaddarar kenan ya ce "Taya kika san ya zube? Wife kada ki tarwatsa mini zuciya" Da ƙyar ta ce "Wallahi ya zube" Bai magana ba ya sunkuceta zuwa mota, suna zuwa likita ya tabbatar ya zube Aliyu har kuka ya yi domin wannan shi ne karo na uku.... Majeederh na zaune tana shigar da bayananta domin ta samu offer a B.u.k za tana koyarwa, da kuma gidan t.v akan yiwa mata wa'azi musamman da Ramadan ke gabatuwa. Mami ce ta fito fuskarta ɗauke da murmushi ta ce "Yawwa Majeederh shirya yanzu ki je gidan Amani ƴar wajan Hajiya Nusaiberh haihu tayi kuma

Please Login or Register in order to submit comment