Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

waye, cikin waye, yadda aka samu cikin duk yana ciki" Abu-turab ya miƙe daga zaunan da yake ya shiga zagaye haɗaɗɗan parlourn nashi fuskarsa tayi jajir. "Ok, meet me at my house" yana faɗin haka ya kashe kiran. Tafiya kaɗan ce ta ƙara su da su cikin gidan Abu-turab wanda yake zaune tare da iyayensa, sojoji birjik ta ko'ina daka nuna rashin gaskiya zaka ji maza akan ka. Girman gidan ya zarce tunani, motoci kala-kala na kamfani daban-daban.
Ko a jerin masu kuɗi ba kowa zaka samu da wannan haɗaɗɗan gidan ba, gida ne 200by 200 iya compound na gidan zai ja hankalinka balle ciki. Kasancewar ba wanda bai san Hammad ya sa ba wani wahala ya nufi cikin gidan, a Main parlour ya samu Mama na sakkowa daga bene ya yi murmushi ya ce
"Sannu da gida Mama" kallonsa kawai take fuskarta kwance da annuri amma kana ganin sanyin jikinta kasan akwai damuwa, kyakkyawar dattijowa mai nutsuwa da sanin ya kamata,ga ilimi na iya zama da ko wanne mutum ga kyakkyawar mu'amala. "Na ɗauka mun yi laifi yau ne" cewar Mama bayan ta zauna.
"Laifi kuma Mama?" Ta dubesa kafin ta ɗauke kai ta ce "Naga babu ko mai kama da kai, hala wani aikin ka ke" ya shafa kai yana rusunawa ya ce.
"Haka ne kam, ina Yake?"
Ta ɗaga kai zuwa part ɗin dama da yake upstairs ta ce. "Ina son tambayarka dama, meke damun shi? Tunda ya shiga part ɗin sa bayan ya dawo bai fito ba, hatta wajan art ɗin da yake shiga yau shiru, lunch ma bai ci ba na kira phohe number sa na gida a kashe" ta tsare shi da idanu ya ce "Akwai wata tattaunawar sirri da yake da ita, maybe shi ne yake duba muhimman abu kasancewar tattaunawar sai 12 na dare"
Ta jinjina kai tare da faɗin "Allah ya taimaka, kasan ƴar rigimarsa ta hanani sakat ita dai Abbi" Hammad ya yi dariya sosai ya ce "Jiddatul-khairi ai ya saba mata ne" kafin Mama tayi magana sai gata ta fito da gudu ta faɗa jikin Hammad ta ce "Uncle, Abbina" ya ɗauketa ya shiga hawa upstairs yana faɗin
"Daughter me, bari muje muga Abbi sai muje siyan chocolate ko?" Tayi murmushi dimples ɗinta soka loma tana ta masa surutu har suka isa haɗaɗɗan part ɗin da kana ganinsa kasan Gov. Abu-turab Alƙasim ne a ciki. Hannu Hammad ya saka cikin wani screen dake ƙofar nan take ta fito da bayanan Hammad a hankali kuma ƙofar ta buɗe.
Jidda ta ƙwace daga hannun Hammad tayi cikin parlourn da gudu tana kiran sunan Abbi, yana zaune saman kujera daman alrdy ya san da zuwan Hammad ɗin, kayan shan iska ne a jikinsa fara Armless da black ɗin 3 gauter.
Hannunsa ɗaya riƙe da Black tea wanda aka sanya masa zuma a ciki, news yake kallo har Jidda ta faɗa jikinsa hankalinsa baya tare da shi. "Abbina"
Ya ware idanunsa idanunsa da suke a ɗan lumshe ya dubeta "First love" sunan da yake faɗa mata kenan, duk da kasancewarta ƴar shi guda ɗaya. "Abbi"
Ya juya bayan ya gyara mata zama a cinyarsa tare da kallon Hammad yana son ya ji wanne labari ne da shi wanda yake da alaƙa da Majeederh.
"Your Excellency barka da yammaci" jinjina kai kawai Abu-turab ya yi.
"Ga wannan wasiƙar, idan ka karanta sai ka ɗauki matakin daya kamata akai, ita kuma zamu nemota In sha Allah" hannu ya sa ya amshi wasiƙar tare da warewa zuciyarsa na harbawa, bai san mene ya sanya duk abinda ya shafi Malama Majeederh ya ke jinsa har ƙasan zuciyarsa ba, barci ya ƙauracewa idanunsa, ga ciwon kan dake ƙoƙarin kwantar da shi.
Duk Yadda ya so ya daure da riƙe kansa ya kasa ya miƙe tsaye da sauri yana ware idanunsa akan paper ɗin, tsoro,fargaba damuwa da kuma firgicin rashin sanin makomarsa wajan Majeederh ya taro ya haɗe masa waje guda.
Ya sanya hannu ya share zufar daya yanko masa, lokaci ɗaya ya hargitse wani zazzaɓi na neman kawo masa farmaki.
"Your Excellency, lafiya dai?" Ba tare daya kalli Hammad ba ya ce
"Ham...mad" "Yes, Your Excellency"
Ya juya gabaɗaya fuska a haɗe ya ce "Tun yaushe nake baka labarinta?"
Kai tsaye ya ce "Shekaru wajan biyar, tun ranar daka halarci musabaƙar da aka yi ta ƙasa"
Abu-turab ya jinjina kai, Elxty 5yrs kenan, a wannan musaɓar ya ji muryar Majeederh, muryar data sanya masa dafin so a zuciya ta zautar da duk wani tunaninsa, ya wanzu cikin muradinta a zuciyarsa, shi kansa ba zai iya sanin abinda ya sanya bai tun kare ta da wannan maganar ba, samun Majeederh Abdul'aziz Khan a garin nan ba wahala zai masa ba. "Har abada Majeederh kada ta san da wannan wasiƙar" da mamaki fal fuskar Hammad ya ce "Your Excellency amma kamar ba a kyauta mata ba, wannan wasiƙar ita zata fitar da ita daga zargi, kuma ita ce zata gane waye ya aikata mata haka" Abu-turab ya koma ya zauna kawo yanzu yasan Bp nasa tuni ya hau cikin kamilalliyyar muryarsa mai tsafta ya ce "Me ka ke nufi?"
"Ba mu yi mata adalci ba" cewar Hammad.
"So baya buƙatar adalci, kansa kawai ya sani, ayi hakkan ya tsaya ni da kai" Hammad ya kalli Abu-turab yana girmama yadda yaso kansa a fili sbd soyayya,idan har son gaskiya ne ba zai taɓa bari Majeederh taci gaba da zama da zargi akanta ba. "Shikenan, Your Excellency. Maganar meeting naka an gama shirya tattaunawar a guest house ɗinka, da kai da Deputy Governor, Secretary to the state of Government, Chief of staff" hannu bibbiyu Abu-turab ya riƙe kansa kana ya jinjinawa Hammad kai ganin yanayinsa ya sa Hammad cewa "yana da kyau ka huta haka, Jidda zo muje" ta maƙale ka faɗa jikin Abu-turab.
"Abbi baya jin daɗi" Abu-turab ya ware idanuna ya ce "Go"
Ta kwaɓe fuska cikin zafin zuciya ya ce "I said Go Hawwa'u Abu-turab Alƙasim!" Tsawar ta gigita mata lissafi ta fashe da kuka tana ƙanƙame Hammad ta ce
"Uncle" ya ɗauketa yana girgiza yana mamakin sauyawar Abu-turab lokaci ɗaya.
Dukkan abinda ya faru akan idanun Malama Majeederh Abdul'aziz Khan ya wakana, kasancewar bata fahimta kusan tunaninta duk ya jirkice ƙwaƙwalwarta na gab da fara daina aiki yasa bata fahimci su waye ba, motsi kaɗan zata ƙanƙame jaririnta kamar zata bayar da shi ciki, wani zubin kuma tayi ta surutu ita ɗaya sbd tarin abubuwan da suka cunkushe mata, yunwa ba a maganarta jikinta ya fara tashi sbd jini da rashin wanka.. bata shagala azkar, istigifari da addu'ar neman samun sauƙi wajan Ubangiji bai bar bakinta ba.
Washe gari Abbu ne zaune a parlour da Mami sai Ruma da Raihana wanda aka kira su daga gidan mazajen su, sai kuma Aaliyyah dake zaune tamkar marainiyya Idanunta a kumbure ko gani ba tayi sosai, sai Uncle Isma'il da Uncle Bello. "Yanzu har a ranka kana jin kayi daidai?" Abbu ya dubi yayan nasa ya ce "Majeederh dai ni na haifeta, ni na samar da cikinta na kuma raineta, kuma na dawo na ce bani da haɗi da ita don haka a bar wannan maganar" Uncle Isma'il ya ce "An barta, amma ka bani mamaki a matsayinka na Uba kuma dattijon ƙwarai har ka iya shafawa idanunka toka ka ce wai ka sallamawa duniya Majeederh, sbd kawai kada sunan family da naka ya ɓaci? Familyn bazan sunanka ɗin banza, da rayuwar mace kamar Majeederh ta ɓaci ba gwara duka sunayenmu su ɓaci ba, wata rana dalilinta sunan namu ya samu ɗaukakar damu kanmu ba muyi zato ba, mai ya sanya mu iyaye idanunmu ya kan rufe idan tsautsayi ya samu yaranmu? Yanzu Majeederh ko tana sane wannan abun ya faru ba zaka iya yi mata uzurin akan rashin auren da take da shi ya ja mata wannan ƙadsarar ba? Ita ɗiya macace duk runtsi duk jimawa dole ta ɓukaci ɗa namiji wata rana" Uncle Isma'il ya girgiza kai sbd tsabar takaici ya ce "taya ƙasa zata gyaru bayan mu da kanmu bamu gyara zamantakewar data yaranmu ba, fine ka kori Majeederh zan nemota na riƙeta a wajena....,"
"Yin hakan zai ja mana babban kuskure yaya, duk wanda zai so ta bayana yake bi, don haka a barni kawai" Abbu ya tari numfashi Uncle Isma'il da faɗin hakan. Uncle Isma'il da ransa ya fara ɓaci ya ce "Zan taimaketa kamar yadda take taimakon addinin Musulunci, bawai sbd data kasance ƴarka ba Abdul'aziz Khan" Abbu rai ɓace shi ma ya ce "Kana iya yin haka amma daga ranar babu ni ba kai, ka cire ni matsayin ƙaninka, ka yanke mu'amala ta dakai" murmushi sosai Uncle Isma'il ya yi wanda ya fi kuka ciwo yana girgiza kai ya ce "In sha Allah, idan kero na yawo zabo na yawo tabbas za a gamo Majeederh zata baka mamaki" Aaliyyah dake kuka sosai ta ce "Abbu don Allah ka bawa Yaa Nura dama ya kawo kuɗin aurena, na ga ji da zaman gidan nan na tsani komai dake cikinsa" kai tsaye Mami ta ce "Fitowa za kiyi ki ce kin tsanemu, aure kuma dole sai kin kammala makaranta daman ke ɗaya ki ka rage cikin gidan.." sai a lokacin Uncle Bello ya ce "Aaliyyah aure ki ke so?" Duk kawaicin Aaliyyah ta shanye ta ce "Eh, Uncle"
"Ki faɗawa Nura ya zo ya saman a gida nan da sati mai zuwa In sha Allah zaki bar wannan gidan" yana faɗin haka ya miƙe tsaye ya kalli Uncle Isma'il ya kalli Abbu ya ce "Yaya taso muje, Allah ya bada ladan zumunci Sunan family kuma a rubuta a gaban ƙoshi ana yawo da shi"
Suka fice tare da barin gidan,Abbu ya nufi part ɗin sa zuciya babu daɗi shi kam Majeederh ta zame masa annoba, Aaliyyah ta shige nata bedroom ɗin tana zuwa ta ɗauki wayarta ta kunna network ta shiga facebook inda labarin Majeederh da Bar Aliyu Sufyan Alhassan yake ta trending a media. Ko photon Majeederh ta gani da gudu take skipping ta shige sbd tsaron zagi da mugun alkaba'in da ake mata, tana cikin dubawa taci karo da wani posting photon Majeederh ne sanye da abaya fara mai kyau fuskarta rufe hannunta riƙe da loudspeaker. An yi rubutu a saman photon tare da saka.

*She's Innocent*
_Malama Majeederh Abdul'aziz Khan babbar malamar musulunci da muke da ita a wannan jiha, wacce ta samu damar zama zaƙaƙura wajan lashe musabaƙar Alkur'ani ta ƙasa, ita kuma ta ƙara jawo kima da martabar jiharmu, wacce take taimakon marayu, marasa gata take nutsuwar da matan aure akan darajar da aure yake da shi, duk da kasancewarta budurwa. Abin tambayar shin ta cancanci haka kowa? Kai da ka ke zaginta ko ki ke zaginta kina da tabbaci akan abinda ya faru, ko kina da hujja? Ko labarin ƙazan kurege aka baki har kike ɗorawa tare da aibatar ƴar jama'a, ta haifi wasun ku da yawa, ta fiki ilimi tunani da sanin ya kamata, ta fika kusanci da mahalicci amma kazo media ko sallar kirki a rana baka yi ka ɓuge da zagin babbar Malama? Ashe muna rayuwa da dabbobi bamu sani ba? Ko masu aikata zina sai an same su turbi da taɓarya tare da shaidu 4 sannan za a ɗauki mataki. MALAMA MAJEEDERH ABDUL'AZIZ KHAN SHE'S INNOCENT I STAND BY HER SIDE._

#Mrs No name

Wani murmushin jin daɗi Aaliyyah tayi 5 minutes da yin posting ɗin amma comments wajan 1k hakan ya tabbatar mata da Mrs no name yana da followers kuma babban mutum ne tunda har ya iya ɓoye sunan shi, kai tsaye profile ta shiga ya rufe komai da komai ko message ba za a iya yi masa ba, dole sai dai tayi magana ta comment section.
Har aka kwana aka tashi Bar Aliyu Sufyan Alhassan bai farka daga suman da ya yi ba, hankalin Hajia ya tashi tana da Papi tare da Almustapha, hatta korar da aka yi masa wajan aiki bai sani ba.
Misalin 8 na dare wahala tayi wahala jikin jaririn ya yi zafi kamar wuta, a yanzu ji take ko jama'ar gari za su kasheta babu abin da zai hanata fita ta nemi ruwan da zata bawa babyn nata, ta miƙe da ƙyar kusan gabaɗaya kayan jikinta sun ɓaci tana bin gefen hanya harta isa wani wajan da ake siyar da tsire kanta ƙasa tayi sallama, gabaɗaya mutanen da wajan suka dubeta wani ya ce "Baiwar Allah lafiya?" Ta jima kafin ta ce "Ruwa nake nema, zan bawa yarona" wani saurayi ya dinga kallonta kafin ya miƙe tsaye ya ce "Mene na rufe fuskar?" Ta ɗauke kai cikin sa a ya gano rabin fuskarta da jaririn hannun da ƙarfi ya ce "Masiƙa la'ananniyya mazinaciyya ku je feta ita ce Malama Majeederh" yana faɗin hakan ya sauke mata wani dutse a ƙoshinta ji ka ke tauu!! Nan take ya fashe jini ya dinga zuba, kafin ka ce me mutane sun cika kowa ya ɗakko duwatsu suka fara jifanta ta ko'ina ta durƙoshe ta rungume jaririn da jikinta, jama'a sunfi ashirin idan wannan ya jefa mata dutse aka sai Wannan ya jefa mata a baya...


Na'ima Sulaiman Shu'aibu
Nimcy sarauta
08119237616*🌈MIJIN MALAMA🌈*


Nimcyluv Sarauta
_*Follow my account👇🏾*_
https://www.arewabooks.com/u/nimcyluv

African Queen products
Sabulun matsi
Garin matsi
Humra
Turaren wuta
Maganin Infection
Ga number wayata...08130269641


*5.......*
Ta ko'ina suke jifa mata duwatsun jikin ƙaramin lokacin suka farfasa mata jiki. Wani saurayi wanda kana ganinsa kasan criminal ne yana da dakakkiyar zuciya ya ɗauki wani dutse tare da faɗin. "Fasiƙa, mazinaciyya, duk yadda akai kema ba ƴar halak ba ce, shi yasa tsayin shekaru talatin da biyar ki ka sa yin aure kina bin mazan aure da samari" yana faɗin haka ya sakar mata dutse a goshinta nan take ya fashe jini ya wanke mata fuska,ta fara gani dishi. Sunayen Allah take kira da neman ɗaukinsa, tsoro ya kamata jin babyn nata ya daina motsi da kukan da yake fatan ɗaya Allah ya sanya jifan bai same shi ba, balle ya yi sanadin mutuwarsa.
"To, wai me muke jira ne? daga ita jar jaririn mu sanya musu fetur a ƙona mazinaciyya mai ci da musulunci, a kuma ƙone mugun iri!"
Wani wanda yake da ɗan hankali ya ce "Amma kana ganin ba muyi kuskure ba? Ai ba jifeta ya dace ayi ba, tunda ba matar aure ba ce, budurwa ce bulala ne ya dace da ita" cewarsa.
Saurayin ya ce "A to mene martabarta da matar aure? Ai auren ne ba tayi niyya ba shi ya sa take ta gantali ta shiga rigar addinin musulunci ta ci zarafin Musulunci da musulmai, ita fa yankata ya dace ayi"
Kafin kowa ya sake magana hasken wata dalleliyyar mota ya haske wajan duk da irin fitilar da suke kan hanya.
Gabaɗaya suka kalla motar mai ƙirar Mercedes-AMG G63 Ash colour, slowly yake driving har ya ƙara su wajan, ta cikin motar yake ƙare mata kallo ganinta durƙoshe har yanzu ko motsi ba tayi, ya ja idanunsa ya lumshe wani abu ya daki zuciyarsa zafi da raɗaɗi yake ji sosai abinda yake ji tsayin shekaru ya ƙara yawa a ƙirjinsa. Ya fesar da numfashi tare da sanya hannu ya ɗan danne gefen zuciyarsa, gently ya gyara Bluetooth na kunnenshi speaking calmly ya ce.
"Meet me at my house right now" Yana faɗa ya ɗauki face mars ya sanya tare da ɗaukan Glasses ya saka a idanunsa, cikin tarin nutsuwarsa da kamewarshi wacce ta riga ta zauna a jikinsa musamman yanzu da izzar mulki ke ɗawainiyya da shi. Ya fito daga motar fuskarsa haɗe duk da babu wanda ya san waye, bai kula kowa ba ya nufeta tare da sanya hannu zai kama nata a firgice ta ɗago idanunta tare da girgiza kai cikin wata murya mai rauni da tausayi ta ce
"Kuyi mini komai, ban taɓa jikina" "ji banza shashasha, uwar mene ya yi saura a jikin banda najasa...,"
Marin da aka sauke masa ne ya sanya ya yi shiru da bakinsa domin har tsakiyar kansa ya ji marin shatin yatsun His Excellency ya fito raɗau a fuskar.
Ya ƙara kai hannu zai riƙe nata hannun domin taimaka mata tayi saurin ɗauke hannu kamar bai son magana murya can ƙasa ya ce "Please Hawwa'u, akwai jama'a"
Ta girgiza kai numfashinta na fita da ƙyar ya ƙara rusunawa shi kansa kamar wanda ya yi jinya ya ce "Haba Jiddo" ganin da gaske take ya sanya ya tattara ƙarfinsa waje guda tare da sunkutar ta gabaɗaya har jaririn sai cikin mota, ya kwantar da ita a baya ya sanya hannu ya zare jaririn tare da ɗaukarsa ya nufi ɓangaren diver. Yana shiga ya yi wa motar key da hannu ɗaya ya fara driving cikin sauri ɗaya hannun kuma ya rungume jaririn, keɓantaccen gidansa ya nufa da ita direct.
Wani tsohuwo ya ce
"To ba ga irinta ba, ɗaya daga cikin kwarton abokin alfashar nata ya zo ya ɗauketa, ai ni duk wani ɗan shege na daina tausyainsa tunda ana sane ake haifarsa"
Haka suka dinga surutu, suna faɗin duk wata mace mai irin shekarun Majeederh wacce ba tayi aure ba to kawai iskanci take tana aikata zina.
Lokacin da His Excellency Abu-turab ya isa gidansa P.a ɗinsa na tsaye yana jiran zuwansa, Hammad ya nufi Abu-turab wanda yake ɗauke da jaririn yana zuwa ya miƙawa Hammad jaririn shi kuma ya koma wajan motar, lokacin Majeederh ta gama sumewa jikinta ya ɗauki zafi sosai a ransa yake istigifari kafin ya tattara ya ɗauketa cak, sanin halin Abu-turab yasa tuni Hammad ya shige ciki da jaririn wani ɓangare ya nufa da ita ya kwantar kan bed, bai tsaya jan aji ba ya samu ruwan zafi da showel ya danna duk inda aka fasa mata tare da yi mata allurar kashe zafi data barci, ya yi mata dressing yana yi yana ɗauke kansa, raunin jikinta bai hana shi ganin asalin kyanta ba, asalin kyawun Fulanin Usul. Zuciyarsa kamar tayi tsalle ta fito ya razana da kyanta sosai shi ya sa ko Hammad bai bawa damar shigowa ba sai da ya gama komai ya sanya mata driving tana ta barcin wahala.
After ya gama ya duba babyn. A hankali ya fito yana dafe kansa sbd ciwon da yake masa yana zuwa ya faɗa saman kujera idanunsa rufe. "Amma yana da kyau ka huta Your Excellency" ya ware Idanu tare da tsiyaya black tea a cup sai da ya shanye ya ce
"P.a, kana tsaya iya aikin ka" "Am sorry sir, bayan p.a you're my best friend hakƙina ne na faɗa gaskiya kuma na kula da kai, idan kana son hakƙin Majeederh tana bawan Allan nan kada ya kama mu yana da kyau a bata wasiƙar ta karanta" ɓacin rai wanda Hammad bai taɓa gani ba ya bayyana kan fuskar Abu-turab, idanunsa da suke a ri ne ya ware akan P.a cikin kakkausar murya ya ce
"Kasan me hakan ke nufi?" Ya shiga kaɗa ƙafa a duk sanda ransa ya ɓaci kafin can ya ce
"She never choice me, ba zata taɓa zaɓata a matsayin miji ba, she most go back to him ba zata gane shekarun da nayu ina jiranta ba" ya miƙe yana kai kawo
"Sunanta na sanya jinina, sunanta na sakawa ƴata Jiddo, ko sunan mahaifiyata ban sanya ba sai nata, shi kaɗai ya isa yasa ka gane, zan iya adalci a mulkina al'ummata, amma ba zan iya adalci akan soyayyar Malama Majeederh Abdul'aziz Khan ba, duk hanyar da zan bi na raba ta da kowa zan yi"
Hammad zai magana Abu-turab ya daka masa tsawa ya ce
"Get out" dole ya fita amma shi a ransa ya san babban kuskure ne su riƙe wasiƙar nan.
"Ya Allah!" Abu-turab ya furta yana ɗaukan gorar ruwa mai sanyi, sai da ya shanye tas kafin ya yi cilli da Robber.
Babyn daman yana wajan wata maid yana ta barci ya ji ruwan zafi da kaya masu kyau ga madara da aka bashi sai numfashi yake saukewa.
Yadda Majeederh ta kwana kan gado haka ya kwana a parlour, lokaci zuwa lokaci yana zuwa a cikin daren sai da ya sanya mata drip uku kansa cewar ruwan na tafiya da sauri. Kiran sallar Subhi ya sa ya nufi bedroom ɗinsa farar singlet ɗin jikinsa ya cire ya sakarwa kansa shower ruwa na saukar masa, alwala ya yi ya shirya cikin ash ɗin jallabiya masallacin dake gefen gidansa ya shiga lokacin ana kuraye kirayen Assalatu....
Assalatun ya yi daidai da farkawar Bar Aliyu Sufyan Alhassan a gadon asibiti ya motsa a hankali yana dafe kansa dake masa ciwo kamar ya rabe gida biyu, dishi dishi ya fara gani kafin ganinsa ya daidaita idanunsa ya sauka akan Hajia ta ce "Zakina, sannu ka ji" ya yi ta kallonta kafin ya juya ya kalli Papa shi ma ya ce "Sannu Haydar, ya jikin?"
"Ba sauƙi Papa" Papa ya ce "Meke maka ciwo?"
Ya mutsa fuska ya yi yana rufe Idanu "Meke damunka? Almustapha kira Dr"
"Babu abinda zai iya"
Almustapha ya ja tsaki ya ce "To ai kun ji, shi fa sam baya tausyain kansa ina can gidana tare da matata ku kirani wai jikinsa ya tashi kamar shi kaɗai kuka haifa? Mene abin so a wajan wata Majeederh tsohuwar ko me?" Aliyu kamar zai kuka ya kalli Hajia ya ce
"Kin ganshi ko?" Hajiya ta ce "Ka fita idanuna Almustapha, kabar mini yaro ya ji da abinda ke damunsa" "I love her"
Cewar Aliyu. "Kayi haƙuri zaka sameta idan rabonka ce" Almustapha kamar ya shaƙe Aliyu haka yake ji ya ƙara yin tsaki ya ce
"Gashi nan an sallame ka daga court ɗin da ka ke aiki, sai ka zauna zaman kashe wando kana jiran wata" Zaki ya kwaɓe fuska ya ce "In sha Allah sai Allah ya ɗora maka son wacce bata son ka" Dariya sosai Almustapha ya yi kafin ya ce
"Ai matata ƴar Aljanna ce ta wada tani da komai na kwanciyar hankali to me zai sanya na fara tunanin yi mata kishiya?"
Sai a lokacin Papa ya shiga dramar ya ce
"Shi ma tashi matar ai ƴar Aljanna ce" "Barshi Papa idan ya cika ya zo ya dauki Latifa ya sata a wuta, matar taka duk raguwar mai"
Yana faɗin haka ya juya zuwa ga Hajiya tare da ɗora kansa a cinyarta ya ce "Hajia zuciyata babu daɗi ki taimaka mini" ta shiga lallashinsa ta ce "Yanzu yana da kyau ka shaidawa duniya baka da haɗi da ɗan gidan Majeederh, after that sai ka fara shirin nemanta ko?" Ya kalli mahaifiyar tasa sosai sai bai ce komai ba. Misalin 12 na rana lokacin an sallami Aliyu zuwa gida yana zaune ya faɗa sosai kamar wanda ya yi jinyar shekara kamar daga sama ta faɗo bai kalleta ba, ƙamshin turarenta kawai ya ji ya fahimta "Ya jikin?" A gajarce ya ce "lfy" ta zauna ta ce
"Amma ka fasa aurenta?" Ya dubeta ya ce "Ita wa?" Kai tsaye ta ce "Waccar Mazinaciyyar mana" ya yi murmushin kawai bai ce komai ba ta ce "Magana nake kayi shiru" ya juya gabaɗaya tare da saka hannu ya riƙe fuskarta ya ce "Kina son rabauta ko Wife? Me ya sa ki kewa mijinki haka?" Ta ce "Idan har zaka ƙara aure zaka iya ganin fiye da haka" ya sake ta yana kwanciya jikin kujera ya ce
"Sai dai idan bana raye, Latifa Omar ke baki tausayina ne? Sai fa Majeederh zata zo gidanki ki ke gyarawa, tsafta zero, kwalliyya zero, girki zero, mu'amalar aure zero, aikin ki kawai ki sani, yanzu mene ribarki don ki aibata mijinki? yaran da zaki haifa sune abin zai zamewa tabo not me or Majeederh" ta miƙe tsaye ta ce "Divorce me"
"Never, ki jira zama tare da sweetheart" baƙin ciki ya cika mata zuciya ya zari key car tabar gidan ya bita da kallo.
Tunda ta farka daga nauyayyen barcin ko tari ba tayi ba, tsoran ta buɗe idanu taga su waye akanta take, bata so ta samu ɗauki ba ta so ace mutuwa ce ta risketa.
Mama dake zaune ta zabga tagumi ta ce "Baiwar Allah kenan, Allah ya saka miki" ta goge hawayen Idanunta Hammad ya ce
"Kamar ta farka ai" Mama ta ce "Ato gwara ta tashi ai, ga ɗan yana ta kuka gwanin tausayi" a hankali ta buɗe Idanunta ba tare data kalli kowa ba sai gefe guda, yadda take ji zaka ɗauka kuka za tai ta rusawa amma idanunta a ƙafe komai na tunaninta ya sabunta hanyar da zata bi ta zama cikakkiyar karuwa kawai take nema.
"Sannu Malama, Sannu kin ji" sai a lokacin ta juya ta kalli Mama tana jinjina kai. Gently ta mayar da Idanunta ta rufe daidai shigowarsa

Please Login or Register in order to submit comment