Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

maka n gudu daga Rushia zuwa Naija" Jin shiru yasa Abraham ɗago kansa ya kalli Majeederh ganinta ya yi ta tura kanta tsakanin cinyoyinta ya dinga kallonta ya ce "Jee" Ta jima kana ta ɗago kanta a rikice ya durƙoshe gabanta ganin fuskarta ta rine ta yi jajur ya ce "Am sorry Maa, Na tuba" Sosai take Mamakin yadda Little bai manta komai nata ba, wato ya fahimci ranta a ɓace a hankali ta ce "Wajan wa ka ke nan?" "My Grandpa, shi ne Pasto na church" Gabanta ya faɗi ƙirjinta dinga ɗagawa da gaske Little ɗinta Christa ne? Wani ya sauya masa addini ko daman can shi ne ba musulmi bane? Ta ce "Full name?"
"Abraham Denial David" Ta runtse Idanunta tare da yin jikin kujera ta ce "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un!" Ta dinga maimaitawa hankali tashe. "I hate my father"
Bata kula da maganar Father ɗin ba ta ce "Your mother where's?" Ya kwaɓe fuska yana ɗan ɗage mata gira bai ce komai ba. "Ka yarda kai Bad boy ne?" Ya jinjina kai ya ce "Yhhhh" "Kai Mahaukaci ne?" Nan ma ya ce "Eh" Ta dinga kallonsa cike da tausayawa kana ta miƙe tsaye shi ma ya miƙe Ta ce "Jeka gida" Ya marairaice mata ya ce "Jee zan bika, I will sleep with you today, Mami, I miss you so much" Ta kalle shi bata ce komai ba har ta nufi wajan motar ta, yana ta mamaki Maminsa tayi kuɗi ko me? Ganin zata shiga mota ya ce "Kawo key ɗin, I'll drop you" Frm head to toe ta kalle shi tana harɗe hannu a ƙirji ta ce "Wani ɗan kwanini da kai ina ka iya driving?" Kasancewar da Hausa tayi maganar sai bai fahimta ya kalleta da kasalallun idanunsa yana riƙe da murfin motar ya ce "Me?" Da Turanci ta ce "Idan zaka iya Hausa ka iya Little ban iya surutu da turanci dama dai larabci ne" ba tare daya fahimta ya ce "Ohk" A hankali ya zuba hannunsa a aljihu yana kame fuska ya ce "Let me drive you and drop you off at home" Ta ce "Wai kai yaushe kaga ɗan ƙaramin yaro yana driving? Kawai ka zubar dani lallai yaron nan" Ta faɗa cikin turanci sbd bata son wani surutun kuma. Wani irin Expression Abraham ke kallon Mamin tasa, a ransa yana ƙara maimaita kalmar yaro Ta ce "Kabari ka ƙara girma da wayo ka san halin kanka zuwa matakin aure" Calmly ya ce "Ohk" Yana tsaye harta fice daga cikin makamatar yamma lis, ya dinga kallon ƙofar kana ya cire hannunsa ɗaya daga aljihu ya dinga hargitse sumar shi. Gang team ɗin suka dinga dariya Taj yadda riƙe ciki ya ce "Gaskiya Mamin nan taka ta rainka da yawa, wai kai ne yaro?" John ya ce "Da kana kula babies wata rana ta ganka da wata a kwance manne kamar chewing gum ai ba zata ce maka yaro ba" Joshua ya ce "Wai kabari ka ƙara wayo sai ka yi driving nata, Goodness!" Abraham kallon su kawai yake. Taj ya ce "Amma seriously i like ur mother classes one Educated women, amma mene wannan a fuskarta? Naso ganinta" John ya ce "Amma dai ƴar rainin hankali ce wai kai ne yaro?" Gadan-gadan Abraham ya yi kan John tare da shaƙe masa wuya kamar wanda ke ƙoƙarin kashe shi "Am sorry Bad boy, sorry" Sai dai Numfashin John ya fara sama kana ya sake shi yana pointing nasa da hannu ya ce "Ko Grandpa ba zan ƙyalle ba akan Malumana Mamina, Jeena balle kai" Yana faɗin hakan ya shige motarsa ya mance kalmar yaro ya nufi gida wajan Grandpa cike da farin ciki yaga Mamainsa..... Wani irin kwara amai Aliyu yake kamar kayan cikinsa zai fita lokaci ɗaya ya fita hayyacinsa, Latifa ta dinga masa sannu ko kulata bai ba, da ƙyar ya wanke bakinsa a sink yana mai da numfashi ya fita parlourn daya zage ya gyara shi, zubewa ya yi saman kujera yana ƙaro gudun A.c Latifa ta ce "Wai lafiya? Mene ya saka amai?" Ya yi mata banza daga ƙarshe ya miƙe zai bar parlourn ta ce "Please Aliyu what's going on? Muje hospital" Ya kalleta kawai ta ce "Please Sweetheart" Ya girgiza kai ya ce "Kyankyaso cikin abincina Latifa? Kyankyaso dai na cikin toilet ki haɗe kika dafa abinci da shi, Innalillahi wa'inna ilahir raji'un!" Ya dafe kansa yama rasa me zai ce Ta ce "Kayi haƙuri ban san yaushe ya shiga ba" Da ƙarfi ya ce "Haƙuri haƙuri, I'm tired of your behavior, I feel sorry for you" Yana faɗin hakan ya fice daga gidan bakiɗaya he need to see a doctor ji yake kamar komai na cikinsa zai zube. Cikin dare Latifa na bacci ta ji an jawota ta yi saurin buɗe idanu tare da kunna switch haske ya bayyana, Suka haɗa idanu da Aliyu ta ce "Lafiya?" Da mamaki ya ce "Are you exlty questioning me?" Ta yi shiru ya ce "Ke ba matata ba ce?" Ta haɗe fuska ta ce "Yanzu mene?" Ya miƙe tare da jingina da frame ɗin gadon ya ce "Why are you answering my questions with a question?" Ta ce "Naga ai dare lokacin da ko wanne mai rai yake hutawa yana bacci gajiya, 1/24 idanun Mutum biyu" Ya jinjina kai ya ce "Ko?" Ta ce "Wallahi fa, mu kwanta mu yi bacci" A hankali ya ce "To" Yana faɗin hakan ya miƙe tsaye yana jin mararsa kamar zata cire saboda azabar ciwo haka ya raya dare ido biyu tar sai asuba ya yi wanka tare da nufar masallaci a hankali suka haɗu da Abbu suka gaisa... Misalin 9:00 na safe Majeederh na bacci sbd jiya ba tayi baccin kirki ba tunanin yadda zata sauya Little kawai take ya dawo musulmi kamar ita da sauran jama'a, gefe guda kuma maganganun Uncle Bello da ya zo har gida ya yi mata ta tas akan taƙi tana yawo ta gaggauta fito da miji suka taro sukai mata tsaye a zuciya wanda ya hanata bacci sai asuba. tashin da Aaliyah ke mata a gigice ne ya sanya ta buɗe idanu Aaliyah ta ce "Anti Jeederh ki tashi" Ta kalli Aaliyah alamar "Lafiya?" A ruɗe hankali tashe ta ce "Wallahi Wani ne ya zo yana ta kwalla kira wai Mami, Malumana, hadda Jee" Majeederh tar ta buɗe idanu ta ce "Tun yaushe?" Ta ce "Tun Ɗazo fa, am sure Abbu bai ji ba da tuni ya fito" Jikin Majeederh duk rawa yake gashi kayan bacci ne jikinta ta ɗako hijabi ta saka ta ce "Shi da waye?" Ta ce "Shi kaɗai" Ta yi gaba bata saka Liƙab ba, gabaɗaya shap ɗin jikinta juyawa yake sbd ɗan saurin da take, Aaliyah ta rufa mata baya, tana zuwa compound idanunta ya sauka akan shi daga shi sai armless white colour sa gajeren wando gargasa duk kwance a fatar jikinsa gashin kansa a hargitse sai surar jikinsa da ƙarfafan maza ta bayyana, daga nan idanunta ya sauka akan wasu dalla dallan mahaukan matoci a ƙofar gate ɗin su daga waje, kafin ta yi magana taga ya kama katanga ya diro cikin gidan nasu tana ƙoƙarin juyawa tana girgiza masa kai amma ina tuni yayo kanta idanunsa cikin nata yanzu zuwa ya rungumeta sai gabaɗaya ta shige jikinsa duk girmanta hadda empty space daidai nan Abbu da Mami suka fito compound ɗin...


Allah ya nuna mana Monday Lafiya..... Wanda ba zai jira ba mu haɗu Arewabooks


MIJIN MALAMA na kuɗi ne dan Allah ki biya kafin ki karata ki kuma sauke nauyi.... 08119237616A tsorace take bin shadow ɗinsa da kallo, kasancewarta mai mugun ji da kanta girman kai da kame kanta cike da tarin nutsuwa da kamala ya sanya kai tsaye ba zaka fahimci girman tashin hankalin da take ciki ba. So take ta samu zarafin buɗe baki, ta tambaye why he's here? But she couldn't. Ta ruɗe sosai ta can cikin zuciyarta dalilin rashin kayan arziƙin dake jikinta, ɗan ta ne, amma tasan bashi da ikon ganin wani sashe na jikinta. "Little, why are you here? and why did you turn off the light?" Ta ji shiru ba amsa, sai shadow kawai idanunta suke gane mata. Ƙoƙarin Miƙewa take ta kasa sbd wani irin masifaffen ciwon kan dake nema juya gurɓata mata tunaninta,ji take kamar kan zai rabe biyu, ga zazzaɓin daya gama cinye mata kuzarin jikinta, a hankali ta koma ta kwanta tare da ɗora kanta a frame ɗin gadon ta curkuɗe jikinta da white duvet ɗin dake shimfiɗe saman royal bed ɗinta na turkey. "Ok fita a ɗakina idan ba za ka yi magana ba" Majeederh ta faɗa so calmly ba hayaniya a muryar sai raunin dake son bayyana, still bai magana ba, sai hasken da taga ya mamaye bedroom ɗin lokaci ɗaya, ta sauke ajjiyar kana ta juya side ɗin da take tunanin yana wajan, haɗa idanu sukai da shi yana zaune saman ƙatuwar kujerar dake ɗan nesa da bed ɗin kaɗan, ya saka hannunsa guda ɗaya cikin tsakiyar kansa ya birkitata, sumar ta cukurkuɗe har gaban goshinsa idanunsa sun yi wasu mahaukatan jaa, fuska ɗaure tamau. "How are you feeling now?" Ya jima yana kallonta kafin a takaice ya ce "Lafiya ina" Majeederh ta tsaya kallon ikon Allah jikinsa duk bandeji amma wai lafiya yake? Sbd taurin kai da zafin zuciya ta ce "Come, muga jikin" Ya yi mata shiru yama ɗauke kansa daga direction ɗinta. Ta ɗan saki fuska ta ce "Common baby, zo nan yaro ne" Ya juya a ɗan hargitse yana kallonta sai kuma ya ɓata fuska sosai cikin gadara ya ce "Stop calling me boy, am not"
"Oh sure? Shekararka nawa?" Kamar ba zai bata amsa ba ya ɗan lumshe jiƙaƙƙun idanuna ya buɗe a takaice ya ce "16" Majeederh ta gwalo fararen Idanunta waje, kamar ruwa ya kwanta a ciki dan haske. A hankali ta shiga ƙarewa Abraham kallo, idan aka ce namiji daya amsa sunansa to ana nufin Abraham Daniel David. Wata iriyar suffa Ubangiji ya wadata masa a jiki, zagayayyar fuska ce da shi wacce aka cewa Round face, yana da kwantaccen saje mai yalwa baƙi siɗik da shi, wanda ya taho har gemunsa ya haɗe waje guda. Ɓata lokaci ne tsayawa description na how handsome he's, The first look she gave him. Ganin yadda ya kafeta da idanu ya sa ta hararesa cikin ƙarfin hali ta ce "Yafi na goyaka a bayan nan nawa kamar yadda na saba, meye wani 16yrd na ɗauka ma zaka ce 50" Shi dai bai ce mata komai ba, kallonta kawai yake ta ƙara ɓata fuska ta ce "To mu da a garin nan kake ma, wallahi ina faɗa maka yanzu za a maka kaciya, idan ba a maka ba kuma ka faɗa na kai ka, I want my child to grow up very well" Dake da turanci duka take maganar yasa ba wani big wahala na fahimtar Abinda take cewa ga Abraham. Ya saka ya shafa sumar kansa yana son yin murmushi ko yaya ne amma he couldn't speaking calmly ya ce "Na zo ki duba?" Ta ce "What?" Nan ma dai ya jima kafin ya bata amsa da "Anyi kacin ka ba ai ba" Majeederh ta yi shiru tana mai da numfashi domin ita har bata bata jin ba daidai ta faɗa ba. "Yaushe ka zo why are you here?" Ya miƙe tsaye yana nufar window ɗin bedroom ɗin nata ya ce "Since 12 at night, Maa check your hand" Baki sake take kallon, kenan tsayin awa nawa yakai zaune yana kallonta tana bacci? Ta juya sai a lokacin ta lura hannunta dake manne da audiga ta ƙara ganin robber na drip daya ƙare da shocked ta ce "Are you a doctor?"
"Yhh, I am" Da mamaki ta ce "But me kake zuwa yi B.u.k a Department na politics Democracy? Yaushe ka zama doctor a ƙarancin shekarunka you're too young da zama likita, likitan me?" Ta girgiza kai ta ce "Kayi yaro da yawa Baby, ban ma yarda da karatunka ba" Ta juya ta kalle shi taga yana tsaye harɗe da hannu ya zuba mata Idanu, idanunsa har yafi baya rinewa. "Zo nan ɗan yaro na" Majeederh ta sake faɗa, domin idan tana ganinsa komai na zuciyarta yayewa yake, sosai take son ɗanta kamar ko wacce uwa. Da sassarfa ya ƙarasa inda take tare da zube ƙafafuwansa a ƙasa ya ɗora kansa a cinyarta da wata kalar murya ya ce "Ki daina ce mini yaro Mami, am not a child" Dariya ta so kamata tayi shiru ta ce "To idan ba yaro bane kai mene? You're just 16 fa haba Khalil" Abraham ya ƙare haɗa fuska tare da zuba idanunsa cikin nata sun ɗauki daƙiƙo suna kallon tsakiyar idanun juna ya ce "Ni ba yaro bane" Majeederh ta ce "Ni dai a wajena kai yaro ne,kaje can inda kake firgitarwa da ƙaton jikinka, amma ni bai fi na goyeka ba" Gani tayi da gaske yake baya so gabaɗaya Annurin fuskar Abraham ya ɗauke kamar an watsa wuta Ya ce "Ohk" Ta share ta ce "Ɓangaren me ka karanta? Ba dai kayi mini allura ba" Ya ce "No! Yanzu zan miki"
Nan da nan ta haɗe fuska itama ta ce "To wallahi na ji sauƙi ma, lafiya ta lou dan ka ji" Ya miƙe cikin wata tafiya ta masu izza da ji da mahaukan kuɗi ya nufi wajan bed side table ya ɗauki wata injection yana zuƙar ruwan ciki, a hankali yake kuma lumshe idanu yana jin kamar kansa zai rabe biyu, Majeederh ta ruɗe domin babu abinda ta tsana sama da injection ta ce "Zo ka fice mini daga ɗaki, Allahamdulillah na ji sauƙi sosai" Bai kulata baz domin a maganarta ba kana jin masharsharar zazzaɓi, gabanta ya faɗi ganin ya nufu inda take tama mance daga ita sai under wear ta miƙe jiri na kwasarta ta nufi har bathroom, tako ɗaya ya yi ya saka hannu ya riƙo ta. "Wayoo Son Allah ban so, kayi mini mutuwa zan yi" Ji ta yi ya saketa, ta sauke numfashi.
"Am sorry Mami" Ta fahimci haƙurin na mene ta ce "Go and ask my father's forgiveness,not me Khalil, shi ka yiwa laifi ba ni ba, da al'adarmu ta ko akwai bambancin, ka je ka bashi haƙuri" Ya matsa kusa da ita tare da sunkuyar da kansa ya ce "I am sorry, Jee" Sai ta ji tausayinsa shi akaiwa laifi shi za a bawa haƙuri,amma yana da kyau yasan muhimmacin bada haƙuri akan kuskure. Kafin ta sake magana ta ji ya ɗan shige jikinta ya marairaice ya ce "Ka yi haƙuri Jee" Majeederh ta ce "Ok, i for give you, but in one condition" Bai ce mata komai ya shiru akan kafaɗarta ta ce "Bana son sunan nan bad boy, bana son zafin zuciyar nan naka Khalil tun kana ɗan 3yrs kake da zafin zuciya har yanzu nothing changes about that, bana son ƙatuwar sarƙar nan wannan team ɗin ban so idan har ka yarda am your mother, kuma.....," Cak! Ta tsaya tare da yin ƙara tana ƙanƙame Abraham jikinta na rawa da ɓari sbd shigar tsinin allura da ta ji a jikinta, tsabar tashin hankali da zafin da ta ji numfashinta kusan ɗaukewa ya yi, kamar yarinyar goye haka Majeederh ta saki wani irin raunataccen kuka bakinta na rawa tana kallon Abraham ta ce "Amma ba na ce na ji sauƙi ba, ni Maminka ka yi wa Allura..." Ta kasa magana sai kuka kamar ta kwanta a ƙasa ta yi ta kuka haka take ji ganin idanunsa kawai ya hanata, tunda aka haifeta ba a taɓa yi mata allura ba sai ta saka drip itama da ƙyar, Abraham ya saka hannu ya kama kunnensa ya ce "Am sorry, ban sakewa" Tana shassheƙa ta ce "Da ƙyar wajan bai kumbura ba, ina ji ma ƙafar cirewa za ta yi" Ya ɗan shafa kansa Calmly ya ce "To bari a lailaya" Kafin ya kafaɗu ta miƙe da sauri zata shige bathroom sai kuma ta saka sbd dishi dishi data fara gani kanta ya shiga juyawa, allurar ta fara aiki a jikinta a hankali tayi baya zata faɗi ya yi sauri ƙarasawa ta faɗa saman chest ɗinsa. Sukutar ta ya yi har zuwa saman bed ya kwantar da ita ya ja mata duvet tare da rufeta ya ƙaro gudun A.c Jin ta riƙe hannunsa sosai bakinta na motsawa ya sanya Abraham zama gefen gadon ya ɗora kunnensa a bakinta a hankali ya ji ta na cewa "Stay with me son, Abbu bai so na ya tsane ni ba wanda ya tsana a duniya sama dani, tayaya zan fito da miji a kwana biyu? Good 31yrs bani da farin ciki sai yanzu dana ganka, my son are still alive kada ka barni, Abbu ya tsane ni" Zame kansa ya yi yana jin maybe ya kashe Abbu kawai, Aure? Miji? Sati biyu?" Sune abubuwan da bai gane ba ya jima zaune yana jinta tana surutu a hankali bacci ya ɗauketa kuma ya taɓa wuyanta ya ji ba fever ya sauka.... Washegari wajejen 8 na safe kiran Uncle Isma'il ya farkar da ita daga bacci ta miƙa hannu da ƙyar ta ɗauki wayar tana kaiwa kunne ta ce "Assalamu alaika, barka da safiya Uncle" Cikin sakin fuska ta wayar ya amsa mata da "Allhamdulillah Hawwa'u" Ta yi jim can ta ji ya ce "Hawwa'u da gaske yaron nan ɗan rainonki ne?" ɓoyayyiyar ajjiyar zuciya ta sauke tana jin nutsuwa jin maganar Little ta ce "Shi ne Uncle" Uncle ya kalli Anti ya ce "Ikon Allah, mene sunan shi?" Ta ce "Khalil" Uncle ya ƙara cewa "Oh, Ibrahim-Khalil kenan? Amma kin san ba Muslim bane?" Ta jinjina kai ta ce "Eh" Ya ce "Good, ki bashi address na gidana anjima ya zo ya saman" Ta yi shiru ita yanzu ina zata sake ganinsa ma? Uncle Isma'il ya ce "Kin ji ko?" A hankali ta ce "Bani da Digits nasa, kuma Abbu ya hanani fita" Uncle Isma'il ya ce "Akan me kuma? Aikin naki fa?" Ta ce "Wai na fito da miji immediately cikin 2days" Cikin ɓacin rai Uncle Isma'il ya ce "To ya garƙame ki a gida tayaya zaki samu mijin? Ko akwai wanda kuke dating da shi ne?" Cike da takaici da ɗacin rai ta girgiza kai ta ce "A'a" Uncle ya ce "Kina kina gida a garƙamen zaki samu mijin aure? Ko shi ne zai nemo miki mijin ne eh?" Uncle Isma'il ya saki tsaki ya ce "Abdul'aziz baya kyautawa kansa kuma kema baki kyautawa kanki ba, ai ba mijin aure kika rasa ba" Yana faɗin hakan ya kashe wayar rai ɓace. Majeederh ta kifa kanta akan pillow tana jin zuciyarta kamar tayi bindiga damuwa ta mata yawa, ita yanzu ina zata samu mijin aure? Waye zai aureta? Wama take da shi ita wallahi bata taɓa soyayya bama bata san ya take ba, daɗinta da wahalar cikinta duka bata sani ba, amma zo da nufin yaudararta babu wanda ya taɓa, ita ko gurgu ko tsoho ne ya zo da nufin aurenta wallahi da gudu zata amince masa ta gaji over gajiya rayuwarta a jirkice take gabaɗaya, ƙaddarar rayuwa ta sanya ta ciki tsaka mai wuya, rana zafi inuwa ƙona, a dangi a goranta mata rashin aure, a gidan da aka haifeta wanda take jin tana da ƴanci nan ma haka, few people suke supporting nata always. Miƙewa ta yi da nufin shiga bathroom idanunta ya sauka akan Card ɗinsa wanda da gayya ya ajjiye ta dauki card ɗin dake ta sheƙi taga an rubuta Dr. Abraham Denial David, so da gaske dai likita ne shi? How? Ita kam ta raina shekarunsa da zama likita, number ta gani uku ta ƙasashe daban-daban ta dubi ta Nigeria taga ganta special one domin kusan duk digit ɗin 1 ne. Ta saka number ta yi saving da _Son My world_
Kira ta yi lokacin Abraham na zaune cikin garden na gidan su idanunsa kwance a saman tsuntsayen da suke yawo wajan, a hankali yake kaɗa ƙafarsa wacce take cikin ruwa hannunsu riƙe da coke yana sha da kuma shisha gabansa. Wani cool ring tone ya shiga tashi kai tsaye ya fahimci me kira, tun ɗazo Gang team ke kiransa amma yaƙi ɗagawa, ya ɗaga kiran yana mannawa a kunne yana jin sanda ta sauke ajjiyar zuciya ta ce "Uncle Isma'il na kiranka, check your inbox za kaga address ɗin gidan nasa" Tana faɗin hakan ta kashe kiran yasan haushin Allura ne dai bata shige ba. Ya cije lip's yana shafa sumar ƙirjinsa yana gani ta yi mata Dm na address ɗin gidan a hankali cikin ƙasa da murya kamar shi ma da kansa bai son jin maganar shi ya ce
"Mamina mai tsoran allura"..... Innati ta ƙanƙance idanunta tana kallon Mami zuwanta gidan kenan ita da Maman Alpha sbd acan Innati take da zama ta dubeta ta ce "Ke baki isa ba, bana buƙatar lalatacciyar munafukar gaisuwarki, mijinki nake nema maza kira shi" Mami ta ce "Kiyi haƙuri Innati" Innati ta yi shiru ta juya wajan Maman Alpha ta ce "Ai ka ji tsiyar da Maryama ce uban me zai sanya tayi shiru? Kin zo kin jaɓe kamar kayan wanki" Maman Alpha dai ta yi shiru babu jimawa Abbu ya fito cikin wata dakakkiyar shadda shampo sai ɗaukan idanu take ya tsuguna ya ce "Sannu da zuwa Innati, anzo lafiya?" Innati ta yi mitsi mitsi da idanu ta ce "Kai bayan son zuciya ta hakƙin lafiyayyiyar ƴarka mai zuciya mai kyau, hadda bakin uwa ke binka Audil azizu" Abbu ya ce "Subuhanallahi me na yi?" Kamar zata dage shi ta ce "Me kowa na ce kayi? Cewa na yi bari na zo na ji wanne marar tsoran Allan ne yake rusawa yarinya farin cikinta? A wanne dalilin ka hanata fita aiki? Kuma da zaka karkace ɗuwawu bayan ta tara maka arziƙi ka ce cikin kwana biyu ta nemo mijin aure, ita ƴar bori ce ko aiki da ruhainai da zasu bata mijin aure?" Abbu ya ce "Ni Majeederh ta tarawa arziƙi? Duk faɗi tashin da nake har Ubangiji ya dafa mini? Kuma sbd kare mutuncin kanta na ce ta fito da mijin aure, shekaru 31 banda ita wa kike gani a family bashi da Aure? Sai fa Sona da Aaliyyah, ka kaf area ɗin nan namu babu mai shekarunta sai dai kullum ta yi wanka ta saka kaya ta shiga mota ta tafi aiki? Ba batun aure a ranta ta mayar da kanta tamkar namiji sbd gogagawa da take da su ta zama kamar wata feminist sai dai ta bawa wasu shawarar zama gidan miji da yadda za su yi haƙuri da rayuwar aure amma ita tana zaune gabanmu tana haɗa kafaɗa da uwarta?" Innati ta ce "Ka gama?" Ya yi shiru ta gyara zama tana saka hannu a ƙirji ta fito da yagulallen nono duk a bushe ta ce "Me ya wannan Audil azizu?" Ya saurin cewa "Don Allah Innati ki yi haƙuri Please" Ta girgiza kai ta ce "Ni fa ƴar banza ce, shiru dai kawai nake bance komai ba, idan kana jin kai ka haifi Kululu to ni kuma ni na haifeka ina umartarka daka gaggauta janye sharaɗin ka akan ta, ko kawai na saki nonon ya faɗi ƙasa kasan me hakan ke nufi" Abbu ya ce "In sha Allah" Ta ce "Maza kirata, ai ba wani yaƙunanne bane ya tara arziƙin gidan" Abbu ya ce "Asabe kirata" Mami ta miƙe tare da nufar part ɗin Majeederh not too long suka dawo tare, ta yi wanka ta shirya cikin wata designer ɗin Abaya mai kyau da tsada tayi rolling kanta kyanta ya bayyana idanunta ya faɗa kamar Balarabiya. Malama Majeederh Abdul'aziz Khan! Ta tsuguna ta gaida Maman Alpha da Innati da kuma Abbu bai amsa ba ya ce "Ki koma aiki" Innati ta ce "A'a daman waye ya sanya ta fara aikin ba kai ba, cewa za ka yi ka janye maganar miji ta nemo a nutse ba tashin hankali" Ya faɗi yadda ta ce Majeederh ta ce "Na gode Abbu" Fita ya yi Innati ta bisa da idanu ta ce "Yanzu ma jin kansa yake wani ɗan iskan

Please Login or Register in order to submit comment