Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

auren kawai" Uncle Isma'il ya dubi His Excellency, duba na tsanaki.
"Matsayin auren fa?" His Excellency ya ce "Zan sanya a rufe ko wacce tashar mota, data jirgin ƙasa, zuwa na sama, dana ruwa, zan zuba jami'an tsaro a kama shi zuwa gidan yari, ita kuma sai a akai mini ita gidana"
"Kada ka tsauwala, gaggawa aikin shaiɗan Your Excellency" ya ƙara girgiza kai ya ce "Majeederh ba auren sadaƙa za mu yi mata ba, tana da daraja sosai ƙaddara ce kawai ta faɗa mata, yadda aka juya mata baya ni ba zan bari ba" cikin girmamawa His Excellency Abu-turab ya dubi Uncle Isma'il kamar zai rusuna ya ce
"Afuwan bana nufin haka, ka fahimci ni, ka dubi halin da nake ciki Uncle"
Mahaifin Aliyu Sufyan ya numfasa ya ce
"Ita mace allura ce a cikin ruwa, mai rabo ka ɗauka, ina tunanin abar maganar zuwa sanda wannan ɗin zai dawo da ita" "Mahaukaci ne fa, zai iya aikata abinda ya furta" cewar Abuturab.
Murmushi kawai Uncle Bello ya yi, domin ya fahimci hutar son Majeederh a cikin idanun His Excellency.
Sun sha bamban da Abraham, shi a fili yake nuna maitar shi wanda yake sawa ayi tunani jikin Majeederh da kyanta ke fisgar shi tare da ingiza shi zuwa tubalin da bashi kenan ba.
Shiru ya biyo bayan maganar ta su ko wanne akwai abinda yake saƙawa a ran shi. Abu-turab ya kasa jurewa hankalinsa yana can kan Jiddo, zuciya ke raya masa yanzu ga su can ɗan iska yaron can mai idanu a tsakiyar kai yana yi mata tijara da keta mata haddi, ya samu damar da shi baya tunanin zai samu musamman da bai hango soyayyar shi a zuciyar Malama Majeederh ba.
"No, i can't take it"
"Me za ka yi?" Inji Uncle Isma'il. "Zan nuna masa ni ke mulkarshi, zan yi amfani da ƙarfin iko, na manta waye ni, na ajjiya matsayina akan samun Malama Majeederh amma wani na can da ita" "Ba zai cutar da ita ba" cewar Uncle Isma'il.
"Zai aikata abinda ya ce, ai Mahaukaci ne"
"Depression ne"
"Ba su da mara ba, abin da ke gidan ƙaura shi ne a Goje, ka bani dama ka kuma share mini fage"
Sai a lokacin Haseenatou ta yi murmushi mai ciwo ta ce "Abin mamaki baya ƙarewa, raƙumin dawa ya ga na gida,ko a labaran Hikaya, da film da littafan hausa ban taɓa ji ko ganin yadda ake rurrumar auren mace mara tsafta wacce ta haihu ba aure ba sai yanzu" Daga Mama har Abu-turab kallon Haseenatou su ke. "Yes, duk soyayya ta rufe ku,kun makance kun kasa ganin gaskiya na tabbatar da a hayyacinku ku ke ko da kuɗi aka haɗaku ba zaku taɓa sha'awar aurenta ba, to yanzu baku da mara da wanda su ke turo" ta faɗa rai ɓace domin har ranta bata ƙaunar auren Abu-turab da Majeederh.
Ta yi ƙwafa ta ce
"Abin da sake an bawa mai kaza kai" Sona da ke tsaye ta riƙe ƙugu ta ce
"Abin nema ya samu, matar dan doka ta haifi ɓarawo, ka dai ki ce halin dangin miji ne ya motsa miki?" Kamar Sona na karantar zuciyar Haseenatou, bata da burin daya shige irin Abu-turab ya auri ƴar uwar shi Intisar ta gyara tsaiwa tana kallon Sona ta ce "Aikin banza talaka ya girmi sarki, ina abun yake? Ai da tsohuwar zuma ake magana"
"Hankaka mai da ɗan wani naka, na aza cewa kan ki ki kewa farauta, to ai ke kin yi kaɗan kuma Anti Jeederh dashen Allah ce, murucin kan dutse bai fito ba sai daya shirya, kuma ƙaddara bata bar kan kowa ba" har huci Sona ta ke don masifa ta ƙara watsawa Haseenatou harara ta ce
"Hannu ɗaya baya ɗaukan jinka, kin yi kaɗan a wannan wasan kina iya komawa ki samo nagartattun ƴan wasa sai a fafata kuma....,"
"Stop it" Uncle Bello ya faɗa yana nunawa Sona hanyar shiga cikin gida ya ce "Ƴar banza uwar magana,ba ki ɗauka a ƙasa ba" murmushi kawai Uncle Isma'il ya yi domin surutun ƴar ta shi a yau ya yi rana.
Almustapha shi ma ya ji daɗin bayanin Haseenatou, Ubangiji ya sa Aliyu zaki ba zai taɓa samun Malama Majeederh ba har abada.
Musty ya kada baki ya ce
"Idan kaga kare yana sunsuna takalmi ɗauka zai, ba bu rami mai ya kawo rami Allah dai ya kyauta" Hajia ta watsa masa harara. Duk abinda ake Abbu yana ciki bai fito ba, baƙin ciki kamar zuciyarsa zata fito wai yau ƴar shi ta lalace? Take ƙoƙarin lalata masa family?.
Ganin yadda duk a kayi shiru kowa yana jimanta al'amarin a ran shi. Uncle Bello ya ce "Ina tunanin mu bar wannan maganar, zamu ƙara zama idan komai ya daidaita"
"Ba zai dawo da ita ba" cewar Abu-turab. Uncle Isma'il ya ce "Zai dawo da ita, da hannun daya ɗauketa ka sanya cewa wacce ta haifeka ba zata cutar da kai ba, to Abraham ba zai taɓa iya cutar da Maminsa ba"
His Excellency ya dubi Uncle Isma'il, ganin kamar shi ne babba kuma waliyyin Malama Majeederh, ya ce.
"Ka bani dama, ka yi mini alfarma a ɗaura auren nan" daga baƙin ƙofa Abbu dake fitowa ya ce
"Ni na ce ka auri Majeederh, kuma yanzu na ce kada ka aureta domin zata ɓata maka iri, kuma sam bata dace da kai ba" Abu-turab ya ce "Don't say that Abbu, kayiwa mata uzuri, kuma ka nasan ita alheri ce a gareni" murmushi kawai Abbu ya yi kana ya ce
"Allah ya taimaka, ko mene ya faru ka kuka da kan ka" yana faɗin haka ya nufi motarshi, Mami na bin bayansa suka shige ya ja ya rufe. Uncle ganin Abu-turab ya kafe ya ce "Ka je, zuwa dare sai ka zo mu yi magana"
"Thank you" "It's my pleasure Your Excellency sauka lafiya" Haseenatou kamar zuciyarta tayi bindiga haka ta shige fuuuu! Ta nufi mota shi na motarshi ya shiga ɗaya daga cikin motocinsa Chevrolet Silverado. Ash colour, dake tafiyar sirri ce ya sa baya buƙatar motar gidan Gwamnati hatta P.a ɗinsa Hammad bai taho da shi ba.
Hajia da Papi tare da Almustapha suka ta fi suma gidan ya rage daga Uncle Isma'il sai Uncle Bello da Yaran da suke cikin gidan.
Sosai Abraham ya take giyar motar gudu yake ba tare da ganin abin da yake gabansa ba, idanunsa sun yi jajur ta jikin madubin motar ya hango Aliyu dake biye da su. Ya cije leɓe yana girgiza kai a fili ya ce
"Fouk You, zan kashe ka" ya ƙara sanya giyar motar shi ma Aliyu ya ƙara gudu cikin sauri Abraham ya yi reverse kamar zai tsaya hakan ya sanya motar shi ta daki da Aliyu ya ƙara yin baya da motar ta sake hankaɗe ta Aliyu kamar zata kifa. Duk yadda ta so share shi ta kame kanta ta kasa ganin da gaske kisan kai ya ke son yi akan Idanunta a gabanta "Meke damunka, zaka kashe shi fa"
"And so f****** what?" Ya faɗa yana kallonta, sosai tayi mmkin ganin yadda idanunsa su ka yi bata taɓa ganin hakan ba sai ranar da haura cikin gidan su kowa na barci.
Gudu yake sosai tuni ya hankaɗe motar Aliyu,ta firgita ba kanta take ji ba ɗanta take ji ta runtse Idanunta cikin wata kalar murya ta ce "Stop the car, right there" ya yi mata banza. Hannu ɗaya ya sanya ya ɓalle bottle na rigar jininsa da ta yi masa nauyi bai saba saka kaya irin haka ba, yana cire rigar ya cilla ta gidan baya, ya rage sai singlet fara rabin faffaɗan ƙirjinsa a buɗe. Ga Brest ɗin shi kamar wata ma ce jikinsa duk a murmurɗe naman dake arms ɗin shi sai rawa yake. Ya kai giyar motar ƙarshe. "Stop, ka saurara"
Ya yi banza da ita, domin ya fara losing mind ɗinsa. Da ƙarfi tana ƙanƙame jikinta ganin sun nufi wani rami ta ce
"Don't, listen to me Little" Cak! Ya tsayar da motar dab da ramin tare da kifa kansa a kan sitiyarin motar ya shiga fitar da numfashi mai zafi yana dafe kansa da yake jin kamar zai rabe biyu.
Yadda zuciyarta ke harbawa haka ta shi take harbawa, ta rasa me zata ce masa, ta san kuma ba zai taɓa cewa komai ba. Sun ɗauki wasu daƙiƙo zuwa mintinu ni kafin ya ɗaga kan shi. ba tare daya kalleta ba cikin turanci ya ce
"Ki shirya mutuwa!"
"Wait!" Ta faɗa ya harɗe hannu a ƙirji girman kai biyu sun haɗu, Majeederh ji da kai da nuna isa musamman da take ganin da auren wuri tayi da tuni ta haifi kamar Abraham. Ya sauke numfashi zuciyarsa tayi masa nauyi without looking at her ya ce
"Why!" "Shi ne tsarina"
"Liar" ya furta ya gyara zama sosai tare da juyawa ya kalleta ya ce
"Na ce ki jirani, na jima da bada saƙon haka, mene na cin mutumci haka?" Ta daure ta ce
"Na sha bamban da tsarin ka, You too young"
Kalmar daya tsana ta ce masa wai shi yaro ne. Ya jima yana kallonta.
"You're my Child, my little boy you're can be my husband har abada, bana son ka, bana ƙaunar ganinka zai dauma a haka ki babu aure, ka ruguza mini rayuwa"
"Child?" Ya yi murmushi kawai tare da sanya hannunsa ya ɗauki Khalil dake barci, ya yi ta kallon yaron cikin so da ƙauna idan ka ɗauke iyayensa da Majeederh babu abinda yake ƙauna sama da Ibrahimul-khalil. A hankali ya yi kissing na sa kana ya kwantar da shi a gidan baya. "Child?"
Ya sake maimaita kana ya ce "Me zan yi wanda zaki daina kirana da haka?" "Babu har abada"
Cikin zafin nama ya sanya hannunsa tare da fincikota ta faɗa saman shi ya riƙe ta sosai hannunsa ta riƙe idanunta rufe sosai a hankali ya sunkuya ya manna kan shi a wuyanta cikin nutsuwa ya sauke mata laɓɓansa. Al'amarin da ta jisa har tsakiyar kanta, jikinta ya ɗauka gargasar jikin suka mimmiƙe, He just hug her so tight murya a rauna ce ya ce.
"I want you know that if can't be close to you. I settle for the ghost of you. I miss you more than life, And if you can't be next to me, your memory is ecstasy
I miss you more than life"
Shi kansa bai san kalaman na fito masa ba, kuma ya yi alƙawarin ba zai ƙara nuna yana son wani abu daga jikinta ba, yana son ta san ba jikinta ne ya dame shi ba.
"Let go of me"
"Promise me, ba zaki aure ban zan Governor can ba, na rantse da Jesus zan kashe shi" ya zameta daga jikinsa tare da tallafo fuskarta ya ɗora tasa akai ya ce
"I love you, i so much loves you Malumana, ki yafe mini na biki na tuba ban sakewa" ya ƙare maganar yana ƙara riƙe ta da kyau. Wani irin kunya ce ta kamata ranta ya ɓaci ganin yadda ƙaramin yaro ɗan cikinta yake ƙoƙarin sauya mata lissafi tare da kai duniyyarta zuwa inda ba tayi tsammani ba. Hakan baya rasa na saba da rashin sabo, ba wai yanzu ya fara ba amma a kullum sabo yake zame mata. Ta zisge jikinta tare da ɗaga hannu zata zabga masa mari ya yi sauri riƙe hannunta.
"Ya zama last time da zaki mareni, wancan na jure sbd you're my mother,and now zaki zaki matana i can't take it anymore" yana faɗin haka ya sake ta ransa ɓace tare da yiwa motar key, yanzu ne zai ɗauki mataki akan abubuwan da suke faruwa, yanzu ne zai koma ga mahaifinsa ƙilan hakan zai bashi damar mallakar Maluma. Kai tsaye gida ya koma, tunda suka ɗauki hanya babu wanda ya yi magana Malama Majeederh zuciyarta fal tunanin halin da Barrister Aliyu Sufyan Alhassan yake ciki.
Manyan motoci Majeederh ta gani a harabar gidan Uncle Isma'il, hakan bai ƙara bata mamaki ba sai da taga P.a ɗin Abu-turab Hammad kenan, ga kuma wani Dattijon mutum sai shugaban jam'iyya. Uncle Isma'il da Uncle Bello zuciyarta sai bugawa take ta buɗe ƙofa ta fito, Abraham Daniel David ya fito daga shi sai wandon kayan dake jikinsa, ya rungume Ibrahimul-khalil. A hankali P.a ya ɗago kai ya kalli Malama Majeederh tsoro ya kamata ganin yadda idanun Hammad suka kumbura tare da yin jaa alamar ya ci kuka son ran shi. Uncle Bello ya miƙe tsaye tare da ƙara sawa wajan Majeederh ya miƙa mata envelope da abu mai nauyi a ciki. Muryarsa na nuna zallar tausayi da kuma nuna nemon taimakon rai ya ce "Congratulations Majeederh,an ɗaura aurenki da Governor Abu-turab Alƙasim yanzu....


MIJIN MALAMA
Littafin kuɗi ne
Book 1 and 2
1kne 0811923761612
Jiri ta ji yana ɗibanta, kanta na juyawa zuciyarta tayi mata nauyi, wani abu ya tsaya mata a ƙahon zuciya, al'amarin daya kusan haifar mata da ɗaukewar numfashi na wasu daƙiƙo. Ta tsaya cak ta zama kamar wata statue, kallon Uncle Isma'il kawai take tana ƙara son jin gaskiyar abinda yake faruwa. Ganin kamar bata hayyacinta ya sanya Uncle Bello dake tsaye gabanta ya sanya hannu ya kama nata cikin nutsuwa da tattausan harshe ya ce "Shiga ciki, domin igiyar aure ke zagaye da ke yanzu" Abraham was spaceless kalma ɗaya ya iya ganewa shi ne “Aure”
Wannan dalilin ya sanya gurbataccen tunaninsa da rashin cikakkiyar sanin zallar Hausa ya sa tunaninsa ya yi ƙaura daga fahimtar abinda Uncle Bello yake faɗa.
"Uncle?" Ya furta cikin wata murya wacce zai wahala ka fahimci me ya sauya masa murya. Uncle Bello bai iya kallon Abraham ba ya juya yana faɗin. "Alhaji Isma'il talk to him" Uncle Isma'il ya ce "In sha Allah"
Yana faɗin haka ya ja hannun Malama Majeederh zuwa cikin gidan Uncle Isma'il, Abraham yana tsaye yana bin kowa da jirkitattun idanunsa wanda azabar abinda zuciyarsa ke ciki ne ya haifar da sauyawar launin su, ya ƙara rungume kyakkyawan Ɗan shi Ibrahimul-khalil wanda ya yi luff a ƙirjinsa yana barci kamar ya samu bayan Majeederh.
Ganin Uncle Bello ya shiga ciki da Malama Majeederh ya sa Abraham ya bi bayan su In his footsteps, like a full-fledged Muslim. Irin tafiyar nan ta cikakkun musulmai.
Bayan tafiyar su, cikin kamala da nuna isa irin na Uba da nuna bar martabar ƴar shi g dangin miji Uncle Isma'il.
"Allahamdulillah, da farko zan fara da yiwa His Excellency addu'a Allah ya bashi lafiya ya kuma tashi kafaɗonsa albarkacin Ubangiji" suka amsa da "Amin"
"Na biyu, ina son ku fahimta muna so da ƙaunar ƴarmu kuma zamu amsheta da hannu bibbiyu a duk sa'ilin da ƙaddara ta faɗa mata, abin nufi bi ma'ana bamu baku auren Hawwa'u a sbd ta rasa mijin aure ba, duk da ƙaddara ta kifta tare da yin kutse a cikin nagartacciyyr rayuwarta ba hana masu neman aurenta zuwa garemu da buƙatar su ta yin hakan ba, duba da shekarun baya duk yadda take a kame a nutse amma babu wanda ya taɓa furta kalmar “so” a gareta balle maganar aure ya shiga, kana taga Allah yana nasa, tayi imani hakan ƙaddara ne mu duka mun yi, sai gashi a yanzu daya kamata ta rasa mijin aure sai kuma maneman suke ƙoƙarin yi mata yawa, kaga babu mai yin haka banda Al-hakkamu sarki kowa da komai, mai juya ƙaddara zuwa abu mai kyau, mai jarabtar bawansa da jarraba mai wahala" Uncle Isma'il ya da kata kana ya kalli Shugaban Jam'iyya wanda yake tamkar Uba ga His Excellency Abu-turab. Ya ce
"Ina fatan wannan dalilin ba zai zama hujjar da za a gorantawa Majeederh ba, ba zai zama tubalin da za a gina shi a gidan aurenta har a hanata sakewa ba, Shi ne ya ganta ya kuma amince zai aureta a hakan nan, wanda har yake ƙoƙarin jefa rayuwar shi cikin garari, ina da tabbacin ba za a taɓa samun matsala daga Hawwa'u ba, haƙurin ta ya shige yadda kuke tunani, tana da zurfin ciki" Dattijon ya numfasa ya ce "Haka Uba na gari ya kamata ya kasance, kuma mun amshi amana zamu riƙe babu abinda zai sameta domin da ɗa da dukiya na Allah ne, ƙaddara kuma kamar riga ce zata iya faɗawa kan kowa, kada ka damu zanwa His Excellency magana da zarar jikinsa ya samu"
"To, madallah madallah dai" cewar Uncle Isma'il.
Ya juya zuwa ga P.a Hammad "Hammad kai abokin Abu-turab ne na ƙwarai, kasan halayyar shi mai kyau da akasin haka, ba ina doubting akan shi ba ne, ina son sanin mene halinsa wanda ya dace ace ko wane Uba ya sani a matsayin wanda zai bada aure?"
Hammad ya yi shiru kai a kai a ƙasa. "Ka ji tsoran Allah, a maganar aure ba wasa ba batun kuɗi da mulki babu wanda bashi da zuciyar da zata iya kai shi zuwa wani bigirin na sauyin hali, faɗa mini gaskiya" Ya ɗago kai tare da zubawa Uncle Isma'il idanu kafin ya ce.
"No!, actually no, he's innocent bashi da matsala" Uncle Isma'il ya yi murmushi ya ce "Allhamdulillah" shugaban Jam'iyya da Dattijon su kayi godiya sosai, tare da nuna farin ciki na auren Malama Majeederh Abdul'aziz Khan, da Governor Abu-turab Alƙasim. Sai Hammad motoci suka shiga kai tsaye kuma Government house sukai.
Tsaye Ya samu matar shi Hajiya Luba sai masifa take,ya ja ya tsaya tare da yin shiru yana son jin wannan masifar ta mece. "Fisabilillahi duk kin cika kunnen jama'a? Hala ke da Sona ne?"
"A'a, ni da Uban Sona da Jawaad ne, yanzu abinda ku ka aikata ya yi daidai kenan? Kamar kuna neman kai da Majeederh sai a ɗaura mata aure sama taka without her permission? Meke damunka tana da iko na zaɓawa kanta wanda take so take ƙauna kuma ai a bari ko yaye yaron tayi?" Uncle Isma'il ya ce "Tab ɗin, wannan masifar taki bata da gurbi yanzu, zuciyar fulani ta motsa kyaci kanki to" ta yi saurin tarar shi da
"Muci kan mu tare dai, naga alama shi His Excellency ɗin ka kewa baƙin cikin gyaran Fulanin Gombe, yadda ka susu ce a kaina ka ke takaicin ya ji haka?" Ya hangame baki tare da riƙe haɓa ya ce "Haba ko da na ji, cewa zaki Soyayyar da nake miki ba banza ba, to maza maza karya asirin da ki kaiwa zuciyata ina buƙatar ƙarin aure" ta maka masa harara irin ta wasan miji da mata sam bata ji daɗin hawan ƙawarar da su ka yi wa rayuwar Majeederh ba. Tana buƙatar hutu da nutsuwa tana buƙatar sanin waye zai so ta, so na gaskiya waye ba zai gorantawa ƙaddararta ba. Uncle Isma'il bai tsaya da maganar ba ya ce "Ki ji tsoron Allah Hajiya Luba, ashe shi ya sa kullum ki ke zaune daram a zuciyata, shi ya sa kullum nake ganinki tamkar alawa mai tsinke a leda, Oh! Ni Alhaji Isma'il Khan, Allah na tuba ka yafe mini ina da arziƙin yin mata huɗu amma sharrin matan fulanin Gombe ya hana"
Duk yadda Hajiya Luba ta haɗe rai bai hanata yin murmushi ba ta ce "Stop kidding me, ban ji daɗi ba, ban ji daɗi ba kuma still ban ji daɗi ba, yarinyata nada gata a bari ayi mata auren gata mana? Kuma batun ta tare yau babu shi" Uncle Isma'il dariya yake sosai he's so friendly
"To me ƴa, ai sai dai ayi haƙuri aikin gama ya gama kada ki manta daman ita ba mai son bidi'a ba ce, ki yi haƙuri ko wacce mace darajarta ɗakin mijinta, a yanzu babu abinda Hawwa'u take buƙata irin aure ta zama cikakkiyar matar aure, damar data rasa a baya ita ta samu yanzu, ki dubi Allah ki yafe mini amma ki janye batun cewa sai tayi yaye ai daman ba shayar da shi take ba" Hajiya Luba ta ce "Idan daɗin baki ne ba daga nan ba"
"Da shi na siye zuciyar ƴar mutan Gombe" su kai dariya ya bata side hug ta zaro ido waje irin ya haka?. A tsaye ya samu Abraham wanda ya kasa zama har yanzu yana riƙe da Ibrahimul-khalil, haka kawai zuciyarsa ke faɗa masa something bad was gonna happen to him, babban damuwar shi yadda a karo na biyu daya hango tashin hankali akan fuskar Maluma Jee. Gabaɗaya Uncle Isma'il ya mance da Abraham gabansa ya faɗi, musamman daya tuna shi Abraham bai san ƙaddara ba balle ya yarda ya kuma yi Imani da ita, cikakken mabiyin addinin Yesu ne na Injila. Ga Grandpa ɗin shi cikakken Pasto ne, zuciyar su a gurɓace take. Ya nisa tun kafin ya yi magana ya ji saukar muryar Abraham ya ce
"What's going on? Uncle?" "Nothing"
"Malumana, she's crying" "She most" Abraham ya ware idanu yana ƙara rungume babyn a ƙirjinsa yana jin tamkar ya tsaga jikinsa ya mayar da shi sbd tsananin son da yake masa. Ganin kallon tuhumar da yake masa ya sa Uncle Isma'il ya haɗe rai, ya ce "Ba zamu shirya da kai ba, kuma ita Maminka ba dole tayi kuka ba acikin jama'a akan idanun manyan mutane dana mahaifinta ka sanya hannunka ka ɗauke ta? Sbd kai baka jin nauyin aikata abin kunya daman ka saba, ka ji ma da sanin bakwai jituwa da mahaifinta yadda ka mayar masa gida kamar wani muzuru duk sanda kayi niyya sai dai ka haura, to a hir ɗinka ba zan zuba idanun hakan ba, ko da wasa na sake ganinka inda Majeederh take sai na saɓa maka, banda abin kunya ba taci kashi da fitsarinka ta goyaka a bayanta ta yi maka wanka amma sbd....,"
“..... She's not my mother” Unclu ya ce "Ba shakka" Abraham ya zube gaban Uncle kansa a durƙoshe ya ce cikin turanci "Na maka al'ƙawari sauya, zan zama yadda addininku yake son ya zama"
"It is too late to cry, Abraham" Abraham ya ɗaga gajiyayyun idanunsa kamar wanda ya sha ya yi tatul da basara ya ce "You're kidding me, right?" Uncle ya yi shiru Abraham ya ƙanƙame Ibrahimul-khalil yana jin tamkar shi ya rage masa a rayuwa, daman tuntuni ya haƙura da mahaifina. Tausayinsa ya kama Uncle Isma'il ya ce "Kawo a kai mata ɗan?"
“.... No! Uncle help me kayi saving rayuwata, I love Mulumana, and am ready to convert to Islam ba zan ƙara taɓa Jeena ba sai ta zama halak a gareni" ya faɗa cikin turanci. Gabaɗaya ya rasa me zai ce.
"Ok, I'll think about that" zan yi tunani akan hakan. Ya ƙara da "Kai mata babyn, ask her forgiveness sai ka je ka fara tunani idan kana son musulunta da gaske"
Ya miƙe cikin takunsa na isa kai ka ce cikakken Muslim ne yadda yake tafiya, yana tafiya arms ɗinsa na motsawa yana yin jikinsa har Mmk yake bawa Uncle Isma'il, ya yi kusan ukun Abuturab baƙar fatar jikinsa irin wacce ake so ɗin nan, so romantic and classic. Abraham is always stronger when he has Majeederh by his side, knocking ya yi ya daɗe kafin ya sanya hannu ya tura cikin kamo kalman da suka rage masa na Hausa ya ce "Salamu... Alayk" tana zaune saman kujera cikin abayar dake cikinta tun safe ta zura hannunta a tsakanin cinyoyinta sai girgiza ƙafa take slowly slowly, fuskarta tayi jajir kamar wacce ta ji ciwo haka ke tabbatar da ranta. " I can't believe this" Abraham said quietly. Da sauri ya ajjiye Ibrahimul-khalil ya zube gabanta tayi saurin ɗauke kai, girman Abraham tsoro yake bata, musamman idan ta tuna sanda yake yaro yana binta yana Mamina, gashi da son jiki da taurin kai baya jin magana bashi da tsoro. Ya jima da sanin rauninta ya san me sanyata magana ya san abinda zai sanya ta ji sanyi a ranta, but she hate him yana ganin ƙiyayyarsa a ƙwayar Idanunta. Ya rasa ta ina zai fara sbd sometimes bai wani iya rarrashi ba, One thing daya iya idan zai rarrashi mutum shi ne ya rungume shi, he just give a tight hug ɗin nan. Gently ya miƙe daga tsugunen da ya ke tare da fara zagaya ɗakin yana nutsa hannunsa cikin hargitsatsiyyar sumar kan shi. Da sauri ya yi kamar zai fita sai kuma ya sanya ƙafa da ƙarfi ya rufe ƙofar bedroom ɗin Majeederh tare da zura key ɗin cikin wandon shi....



MIJIN MALAMA na kuɗi ki biya ki karanta....If you read for free🤷🏾‍♀️🤷🏾‍♀️🤷🏾‍♀️🤷🏾‍♀️0811923761613
Abraham ya zubawa Maminsa Malama Majeederh narkakkun idanunsa, a hankali ya ƙara tura hannunsa cikin sumar kansa cikin huci ya sa ƙafa ya daki frame ɗin gadon ya ce "Ki daina" ya furta yana ƙara

Please Login or Register in order to submit comment