Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ɗaya da sunan kulawa da bashi tarbiyya ba, mace ɗaya ta fara ƙoƙarin saita shi da ganin ya dawo hanya ita ce wacce yake kira da Mami, ur daughter Malamar nan" Uncle Isma'il ya ce "To ya akai ya dawo gare ku bayan ya ɓata? Tunda mun zauna da shi shekaru 2" Grandpa ya ƙara yin murmushi ya ce "His father, shi zuba private Investigators everywhere domin hankalinsa ya dawo kan shi, cikin sa a kuma aka same shi daga nan ya ɗauke shi zuwa wata ƙasar" Mamaki fal ya cika Uncle Isma'il sbd yasan cikin dare aka nemi Abraham aka rasa. "Waye mahaifin nasa? Yanzu yana ina? Me yasa kuma basa tare" Grandpa ya ce "You can ask him by yourself" Uncle Isma'il ya jinjina kansa kana ya yi murmushi ya ce "Yanzu ga abinda jikan naka yake ƙoƙarin rikituwa, kana ganin zai iya musulunta" Grandpa ya jima yana kallon Uncle Isma'il kafin ya ce "Har abada, ku gaggauta yiwa yarinyarku aure, idan kuma zaku bashi aurenta haka to, kai ko zaku bashi mahaifinsa ba zai taɓa yarda y auri musulma ba kuma ba wacce ta girme masa ai tayi tsofa da yawa gsky" Ran Uncle Isma'il ya fara ɓaci sosai kafin ya ce "Kai kake ganin tsofanta, bamu zamu gaggauta mata aure ba ku ne zaku jawa naku ɗan kunne akan ya fita harkar yarinyarmu ko kuma duk abinda ya same shi shikenan, ko hukuma ta rabamu da shi" Miƙewa Grandpa ya yi da sanda a hannu irin tsofaffin attajiran nan masu arziƙin gaske ba muna kuɗi ba ya ce "Hukuma? Waya faɗa maka Abraham na tsoran hukuma bayan shi ne hukumar kansa? Abraham babu wanda ya taɓa zama ya ce masa wannan abinda kake ba daidai bane ga wanda ya kamata ka yi, Abraham ko yini guda ya yi bai kai abinci bakinsa ba babu wanda zai ce masa ɗauki abinci kaci, irin wannan wanda bai san bambancin fari da baƙi be kake tunanin zai fahimci wani ya daina kula muku ƴa?" Grandpa ya girgiza kai kawai kafin ya ce "Sbd karamcinta ya sa nace kuyi nesa da ita daga idanunsa, Abraham ne yaro ne mai naci da taurin kai, tun yana ƙarami idan yana son abu kansa yake bugawa a ƙasa ba zau taɓa bari ba sai an bashi, Have a good day!" Yana faɗin haka ya fice daga cikin Parlourn ya nufi compound da sauri driver ya buɗe masa bayan mota ya shiga.
Anti dake shirya Lunch ta kalli Uncle Isma'il ta ce
"Ya akai kai jarumin namiji?" Ya nemi waje ya zauna tare da rufe idanu ya yi shiru. Ganin yanayinsa ya sa ta nemi ruwa mai sanyi a cup ta miƙa masa tana zama kusa da shi, bai musa ba ya amshi ruwa ya sha sosai yana sauke numfashi. Ganin bai ce komai ba itama Anti ta yi shiru da bakinta, har ya je sallar Asr ya dawo ya zauna cikin iyalansa idanunsa akan Jawaad ya kasa cewa komai, tunani fal ya sa yana sanya Jawaad matsayin Abraham taya zan iya sanwaltar da rayuwar ɗan shi ya bawa duniya ajjiyar shi? Ba dole ya kan gare ba. "Abba" Jawaad ya kira sunan Uncle Isma'il ganin kallon da yake masa kafin ya ce "Abba ruwa zan baka?" Ya girgiza kai kawai ya ce "Allah ya yi maka albarka Jawaad" Ya ce "Amin Abba" Sona ta ce
"Jawaad kaɗai Abba?" Ya haɗe rai ya ce "Sona dake da Jawaad waye babba?" A hankali ta ce "Shi ne" Ya ce "To ya zama last day da zan ji bakin ki ya ce Jawaad ki bi bakin Majaufiarki na Fulanin Gombe ki ce Hamma, ko ki ce Brother da turanci ko Yaya da Hausa" A hankali ta ce "Am sorry Abba" Ya ce "Bashi haƙuri" Ta kalli Jawaad ta ce "Am sorry Yaya" Jawaad ya yi murmushi ya ce "No bad my dear" Bayan sun kammala cin abinci Uncle Isma'il ya zayyane wa Anti yadda sukai da Grandpa. Anti ta yi shiru zuciyarta fal tausayin rayuwar Abraham ta ce "No wonder sweetheart, ka duba Abraham sosai wallahi kallo ɗaya nayi masa nasan babu kulawar uwa a tare da shi ita kuma ya yi missing, duk lalacewar yaro idan har a gaban mahaifiyarsa yake wlh zai samu nutsuwa da sauƙi wani abu, shi yasa a kullum muke addu'a Ubangiji ya bamu tsayin rai mai amfani mu rayu tare da yaranmu" Ta girgiza kai ta ce "I felt sorry for the boy, his life is full of challenges, wallahi ya bani tausayi yanzu da babarsa na duniya taya zai dinga garari? Ba sai dai su shiga duniyar tare ba?" Uncle Isma'il ya ce "Ƙaddara" Wani irin kuka Anti ta rushe da shi ta ce "Wallahi tallahi na ji gwara ɗana ya mutu ya barni da ace na mutum na barshi ban san wacce kalar rayuwa zai yi ba, ban san waye zai kula da shi ba, Innalillahi wa'inna ilahir raji'un Ubangiji kayi mana tsayin rai mu rayuwa da yaranmu cikin kulawa da amincinka ya Rahamanu ya Rahimu" Uncle Isma'il ya ce "Ke fa daman haka kike babu dama ki ji abu sai kuka haba" Ta girgiza kai kawai wani kukan na kwace mata ta ce "Yallaɓai baza ka gane ba, don Allah ka jawo Abraham jikinka plx" Ya yi shiru for good 3 minutes kafin ya ce "I'll think about that dear" Abraham na kwance saman 3 sitter a haɗaɗɗan parlourn shi kwana uku kenan cif babu inda yaje, duk ya fita daga cikin hayyacinsa. Taj ya kalle shi ya ce "Wani ya yi mini maganar zanen gida da kukai da shi, gashi har time ya shige" Abraham ya yi shiru idanunsa buɗe yana kallon sama alama ya lula duniyar tunani. Taj ya ce "Ina ta magana?" Sai a lokacin ya ce "Ka tura masa kuɗin shi ba zan ba" Taj ya ce "Nawa ne kuɗin?" Shortly ya ce "3M" Joshua ya girgiza kai ya ce "A'a ba za a mayar ba, a bashi haƙuri zuwa wani week ɗin kafin nan sai ka yi" Taj ya ce "Ya ce a mayar kuma daman shi zai aiki tunda ba zai ba bashi kenan ba?" John ya ce "Taj kada a mayar plx mu yi tunanin wani abun" Duk sukai shiru. John ya ce "Kunga news guy's?" Taj ya ce "What news? What's happening in the world?" A hankali ya ce "Wai President ɗin Germany aka kaiwa hari za a kashe shi" Da wani irin Mamaki Taj ya ce "Kashe kuma? President ɗin guda? Kuma a hospital?" Join ya ce "Daman wai jinya yake fa bashi da cikakkiyar lafiya, to a hospital ɗin akai attempting kashe shi amma ya kuɓuta, irin haka dole akwai haɗin bakin wani na kusa shi" Taj ya saci kallon Abraham da idanunsa ke lumshe yana jin duk abubuwan da suke cewa ya ce "Ayya! Shi bashi da ɗa ne wai?" A hankali Abraham ya miƙe ba tare daya kalli kowa ba ya nufi cikin part ɗinsa ya kwanta saman bed, haka kawai ya ji bashi da nutsuwa gabansa sai faɗuwa yake, ya runtse idanunsa sosai a hankali ya ce "Daddy"
Majeederh ta kalli Latifa a sanyaye ta ce "Yanzu Latifa ya zan yi? Wanne irin baƙin jini ne irin wannan? Kamar wata mujiya" Latifa ta girgiza kai ta ce "Ki daina cewa haka komai lokaci ne, ƙaddara ce kuma tana da nata lokacin" Ta goge hawayenta tare da yin shiru a hankali ta ce "Surutun jama'a ya fara damuna ana son mini sharri" Cike da tausayawa Latifa ta ce "Duk yadda kake kare kanka ba zaka taɓa hana jama'a faɗar abinda su kai niyya ba, wani ma bai san waye kai ba labari kawai zai ji yaje ya ɗorar ba zaki taɓa yiwa kowa daidai ba rayuwa kawai ki tsarkake zuciyarki" Latifa ta ce "To yanzu da Uncle ya kira Abraham gidan nan parlourn Abbu me zai masa?" Ta girgiza ta kasa cewa komai. Uncle Isma'il ya kalli Abraham ya ce "Khalil me ya kawo ka bedroom ɗin Mamin take few days ago?" A hankali ya ce "Matata dai not Mami" Uncle Isma'il ya jinjina kai ya ce "Ohk me ya kawo ka?" Ba tare da damuwar komai ba ya ce "Just to see her, sai kissing ɗinta da na yi" Uncle Isma'il ya saki baki dan ya san da gaske anyi hakan tunda har ya faɗa don baya ƙarya. Abbu ya runtse idanunsa sosai yana jin kamar zuciyarsa ta fita. Uncle Isma'il ya ce "kiss fa kace Ibrahim?" Abraham ya ɗan kalli Uncle I sai kuma ya kwaɓe fuska ya ce "A small kiss, kaɗan na yi fa" Uncle Isma'il ya ce "Tab ɗin" Uncle Bello shi abin dry ya bashi yana kallon Abraham cike da birgewa ganin baya ƙarya ko kaɗan kuma hakan alamar mutum mai nagarta ce wanda zai iya riƙe amana ta komai. Uncle Isma'il ya ce "Khalil ka san me kake cewa?" Ya ɗan watsa kafaɗa cikin turanci ya ce "Exlty, kwana biyu bata kulani Uncle I ka barni naje ko ɗan hugging nata na yi da kiss ɗin sai nayi ta ganinta a baccina" Kallonsa kawai suke, Abbu kuma ji yake kamar ya shaƙe Abraham Uncle Isma'il ya lura magana ce sosai a bakin Abraham wacce ya jima bai ba dan haka ya ce "Ya akai to yanzu?" Abraham ya gyara zama idanunsa sun yi jajur yana riƙe hannun Uncle Isma'il ya ce "Uncle I Mamina muguwa ce, bata so na ta hana ni sakat a bacci sai na dinga jin kamar gani kwance da ita" Wani irin hawaye ya zubu masa a cikin idanunsa masu zafi wanda rabon da ya yi kuka har ya manta ya ce "Uncle ka aura mini Mami idan na mata ciki zai sanya sunanka ka barni naje wajanta yanzu na yi mata small kiss.......


Jama'a ya Ibada? Allah ya bada lada ayi addu'a sosai Allah ya hurewa kowa kuɗi ya biya Mijin Malama ya sauke nauyi..... Hakƙi ba wasa bane. 08119237616




*Aunty Zee MOM MUJAHID KATSINA*
*08162859027*

*INGANTACCEN MAGANIN SANYI MAI WANKO DUK WANI DATTIN MARA SANYIN KASHI CIWON BAYA CIWON KAFA JIN ZAFI YAYIN MU AMALAR AURATAYYA FITAR FARIN RUWA MAI WARI KAIKAYIN GABA TUSAR GABA WARIN GABA KURAJEN GABA KURAJEN JIKI KAIKAYIN JIKI RASHIN HAIHUWA BASUR MAI TSIRO CIKIN IKON ALLAH ZAIMAGANCE MAKI/MAKA ZAKIJI DADIN MAGANIN SANYINNAN SOSAI A BANGAREN GYARAN AURE BA A MAGANA DAN ZAI SAUKAR MAKI DA NI IMA ZAKI JI SHA AWA KODA SHA AWARKI TA DAUKE ZATA DAWO KIJI KE KIKE MARMARIN ABAR KEDAI KINEMI AUNTY ZEE MOM MUJAHID KATSINA*
4k


*MAGANIN GYARAN NONO MAI TADA KOMADAR NONO DA DUK WATA TAMOWA TA* *JIKINKI NONUWA ZASU CIKO SOSAI ANMA BANCE ZASU TSAYABA WANNAN MAGANI ANGWADA ANDACE HANZARTA KI MALLAKI NAKI YAR UWA 8K*
*TAREDA MAGANIN CIRE TUMBI DUK INDA KIKAI KAMAR KIN KUSA HAIHUWA AITA TAMBAYAR KI WATA NAWA IDAN KINSHIGA MATE KIZAMA KAMAR BABARSU DAN ALLAH KIZO KIJARABA 7k *INA AIKAYA KOWANI GARI DA YARDAR ALLAH INBAKI SHIRYA BA KIBARI KI SHIRYA SAI KUNZO NAGODE KAYAN* *AUNTY ZEE MOM MUJAHID KATSINA*
*KI TUNTUBENI A WANNAN LAYIN*
*08162859027*Wani lafiyayyen mari Abbu ya sauke Abraham a fuska yana huci tare da cewa "Who the hell do you think you are? Akan idanuna kake cewa a barka kaje ka sumbaci ƴar cikina? Sbd ka tabbatar mana kai mahaukaci ne baka san addini ba ko? Yanzu kai ko musulunci ne How do you think I will welcome you to marry my daughter, I will never let you marry Majeederh as long as I am alive in this world even if you are a Muslim, balle kuma ƙaton arne wanda babu ɗigon imani tunani a ransa" Uncle Isma'il ya ce
"Alhaji Abdul'aziz wannan ba mafita bace, kamar kana ƙara tunzura shi ne wlh,This is not the way to solve this problem, take heart please" Abbu ya girgiza kai ya ce
"Ba zan iya zama takaici ya tarwatsa mini zuciyata ba Isma'ila, Majeederh ta zame mini masifa da bala'i a cikin zuri'a kamar ita kaɗai na haifa? Ina sane fa time to time yake hauro mini gida kamar ɓaraho ya shigewa ɗakinta, tunaninta itama ban sani ba" Uncle Bello ya buɗe baki da mamaki bai ce komai ba ya juya ya kalli Abraham ya ce "Khalil, Majeederh kake so? Zaka iya kula da ita? Zaka iya musulunta?...," Abbu ya yanke maganar Uncle Bello da faɗin "Me ya sa kuke mini haka ne wai? To idan baku yarda ba, bari na ƙara maimaitawa wlh wlh wlh tallahi ko wannan shegen yaron zai musulunta ba zan taɓa lamumce masa auren Majeederh ba, kai na rantse da Allah da Majeederh ta auri yaron nan gwara ta zama duk abinda take son zama, gwara ta dauma babu aure har ƙarshen rayuwarta, gwara ta zubar mini da shegu na dinga ganinsu da dai ace wannan yaron ya aureta, i hate him for no reason, don Allah ku saka shi ya fice mini daga cikin parlour" A hankali Uncle Isma'il ya ce "Khalil" Abraham bai ɗago kai ba, balle ya kalli Uncle Isma'il bai ma san me suke tattaunawa ba tunda da Hausa suke magana, yadda yake jin ihun Abbu ya san faɗa yake, zuciyarsa kawai yake kaiwa nesa da tuna al'ƙawarin da ya yiwa Majeederh. Uncle Isma'il ya ƙara cewa "Khalil je waje ka jira ni" Ya ɗaga kansa ya kalle shi calmly ya ce "Na je gun je?"
"A'a, ka je waje ka jirani itama tana can gidana ai" Miƙewa kawai ya yi jiki a sanyaye ya fice daga cikin parlourn ya jima tsaye yana kallon part ɗinta da yake a rufe yana jin kamar tana ciki musamman da ya ji zuciyarsa na bugawa da ƙarfi, tuna Uncle Isma'il kuma ya ce bata nan yasa ya nufi compound na gidan. Yana tsaye jingine da motarshi idanunsa rufe ya ji ance "Aa yau Little ne a gidan namu?" Jin muryar Aaliyyah ya sanya ya buɗe idanunsa tare da zuba mata a hankali ya ce "Baki iya gaisuwa ba?" Aaliyyah ta zare ido tana riƙe haɓa ta ce "Wa zan gaisar? Kai? Tab ka tuna sanda muke goyaka ne a baya muke maka wanka" Ya haɗe fuska tamau idanunsa ya ƙara yin ja kamar ba zai magana ba sai kuma ya ce "Kee!" Aaliyyah ta ce "A'a ba wani batun kee, sbd kaga ka zama ƙato kamar samudawan farko? Daga yau Anti zaka dinga ce mini" Bai kulata ba sai kuma da sauri ya ce "Ko jee ba taɓa ganin jikina ba, balle ke yarinya" Ta riƙe haɓa ta ce "Yarinya?" Ya yi mata banza yana kallon motar Uncle Isma'il ta ce "Bari na ƙarasa na gaji sosai" Ya jinjina kai ta ce "Ka gama secondary school?" Ya wani irin kallonta sai kuma ya ce "A'a" Ta yi Murmushi ta ce "Ka dage ka gama sai ka fara zuwa University school ɗin da nake Yusuf Mai tama" Silently ya ce "Ohk" Sbd at this time bai ma san me zai ce mata ba, kuma darajar jinin Majeederh dake yawo a jikinta ya sanya yake conversing da ita. Yana kallo ta shige ciki. Uncle Bello ya kalli Abbu ya ce "Amma har ranka baka ji kunya da ka ce wai kana kallo Khalil yake shigewa part ɗin Majeederh? Ba tare da taking any action ba, kuma kana ji a ranka kai uba na gari ne ko? Ka bada gudunmawa mai tarin yawa a rayuwar Majeederh yanzu kuma kana son bawa ƴar cikinka laifi?" Ya girgiza kai Uncle Isma'il ya ce "Alhji Abdul'aziz Please faɗa mini tun daga kan haihuwar Majeederh kawo yanzu da tayi growing up ta mallaki tunaninta sau nawa cikin dare ka taɓa tashi ka duba ɗakinta kaga yadda take kwana, ka duba kaga akwai problem da zamanta ita ɗaya a ɗaki ko babu? To mace bata taɓa girma a gaban iyayenta muddin ba aure tayi ta nufi gidan mijinta ba, yadda duniya ta lalace Majeederh ko maza take kawowa cikin gidanka take kwana da su ba zaka taɓa sani ba, tunda baka bincike yanzu ma da Khalil ke zuwa dalili ne ya sanya ka fahimci yana zuwa sbd ka saka idanunka akan shi, haka son shi. Yadda zamani ya lalace da waya ma kadai zai iya sawa yarinya ta lalace ta dinga aikata ba daidai ba a ɗakinta tunda tana ganin ita kaɗai take kwana take tashi, waya kuma babu mai binka mata balle asan me take, Alhj Abdul'aziz till now da kake wannan harbin iskar baka taɓa zama ka ji mene problem ɗin ƴarka ba, baka taɓa zama ka ji wanne hali take ciki ba, babu mai bata shawara akan rayuwarta kama gdy Allah ya baka yarinya ta gari wlh, amma ka iya zama ka buɗe baki kace wai yaro yana shiga cikin bedroom ɗin Majeederh bayan baka taɓa tsawatar masa ba, idan zaka tashi ka kula da rayuwar yaranka fine" Uncle Bello ya sauke numfashi ya ce "Muma fata muke mu rabu da Abraham lafiya a samu Majeederh tayi aure shikenan dole ya haƙura, amma kana surutun banza da iska kasan kaifin bakin uba akan yaransa? Baka gudun bakinka ya kamata haka kurum kaja mata masifa? Bama wannan ba kana da wanda zaka bawa aurenta ne?" Calmly Abbu ya ce "Still searching" Ya ce "Allah ya kyauta ni zan shige" Uncle Isma'il ya miƙe ya ce tafiya zan ni ma. Fitowa sukai a tare suka bar Abbu zaune dafe da kansa dake juya masa. Suna fitowa Compound Raihana na shigowa ita da wani yaƙunannen mutum jikinsa duk dauɗa talakan ƙarshe mai fama da halin rayuwa. Bayan ta gaishe su Uncle Bello ya ce "Wannan fa?"
Ta ɗan shafa kanta ta ce "Tasi'u sunansa" Ya ƙara cewa "Who's he?" Ta ce "Shi ne wanda mukai magana ya amince zai auri Majeederh, na kawo shi Abbu ya gansa" Uncle's ɗin suka dinga kallon Tasi'u kafin Uncle B ya ce "Ok neman kai aka ce miki ake da ita?" Ta ɗan shafa kai ta ce "Daman naga har yanzu ba tayi aure bane, kuma tana ta yawo a gari har ana mana gori wai iskanci take....," Wani ba hangon mari ta ji an sauke mata nan take hancinta ya fashe, aka ƙara sauke mata wani. Da sauri Uncle Isma'il ya ce "Khalil mene haka?" Huci kawai Abraham yake bai ma san akan me ake magana ba, sunan Majeederh kawai ya fahimta. Ya juya kan Tasi'u sai gashi ya saki fitsari a wando yana cewa "Wallahi ƙarya take ni Mahaukaci ne ba wani aure da za a mini" Sai kuma ya kwasa da gudu ya fice daga cikin gidan. Raihana ma ta miƙe tai waje da gudu tuni gefen fuskarta ya kumbura bata taɓa jin zafin mari irin wannan ba wanda ya gigita ta lokaci ɗaya. Abraham ya shiga motarshi ya fice da gudu tare da nufar gidan Grandpa. "Wannan yaron zuciya ne dashi" Uncle Bello ya ce "I like him, da musulmi ne babu abinda zai hana ni aura masa Majeederh wlh, ko zata dinga goya shi a baya dan ƙanƙantar shekarunsa" Uncle Isma'il ya ce "Ko waye ya faɗa mata namiji na yin kaɗan? Kuma ma age is just a number sanda zata fara ƙaunar mijinta ba wanda ya sani" Murmushi kawai Uncle Bello ya yi ya ce "Exlty, kaga a 9mnts ka samu jika" Ya ce "Ko shakka babu a wannan zafin naman na shi".... Bayan kwana biyar Majeederh na zaune duk ta rame ta kalli Latifa sai ta ji kamar ta faɗa mata Abraham na shigo mata bedroom cikin dare amma ta ji tsoron kada tayi mata wata fassarar Kullum abin na damunta ta rasa yadda za ta yi, bata da ƙarfin qiwwar tunkarar Abbu da wannan maganar hakan ya sanya bata da wani mafita kullum addu'a take Ubangiji ya ɗauki ranta ta huta da wannan halin da take ciki. "Ni laifinki nake gani, ga Aliyu ki aura wlh da tuni kin haihu da shi a sanda na yi miki wannan maganar amma kin ƙi" Majeederh ta girgiza kai ta ce "Ina jin kamar bani da rabon farin ciki a wannan duniyar Latifa, bani da gata na ko wacce mace na sare banda na san hukuncin wanda ya kashe kansa wlh da rataye kai na zan yi na huta, an kasa fahimta ba babu wanda ya gane halin da nake ciki, Abraham ya takura ni duk inda zani ya sani da ace na san ina ne dangin mahaifiyata wlh da can zan tafi maybe su za su iya fahimtar yadda nake ji a zuciyata, akwai mutanen da Ubangiji yake ƙaddara musu abubuwa wanda basu da rabo a duniya sai a lahira jikina yana bani ina ɗaya daga cikinsu" Hawaye ne ya kawo a idanun Latifa ta ce "Stop saying that dear, Ubangiji ya fi kowa sanin halin da kike ciki, In sha Allah watarana sai labari zaki zama abar kwatance, zaki farin ciki, zaki dariya sooner or later" Majeederh ta runtse Idanunta ba tare da ta ce komai ba. Gabaɗaya ƙaddara ce ke zagaye da rayuwarta tasan idan ta cika mumina dole tayi accepting na destiny ɗinta har zuwa lokacin mutuwar ta. Ƙilan rabonta na Aljanna yana jiranta. Aliyu dake sauraran su tun ɗazo ya sakko daga upstairs da sauri Majeederh ta rufe fuskarta da liƙab. Ya nemi waje ya zauna Latifa ta ce "Sweetheart ya zazzaɓi?" A hankali ya ce "Allhamd" Majeederh ta ce "Sannu Aliyu" Ya buɗe idanunsa zuciyarsa na harabawa jin ta kira sunansa ya dai kalleta bai ce komai ba. Can ya ce "Ki yi haƙuri da rayuwa, kada ki sare kuma ki yarda Allah ke yi shi kuma zai miki, ki tsarkake zuciyarki, ki miƙa lamuranki ga Ubangiji ki ci-gaba da addu'a watarana zai amsa, babu ɗan adam ɗin da bashi da damuwa ko ƙalubale Hawwa'u naki ne kawai ya fito fili" Miƙewa tayi tsaye ta ce "Thank you" Ya ɗauke idanunsa duk suka bita da kallo harta fice daga cikin Parlourn. Latifa ta ce "Sweetheart dan ka auri Majeederh" Da wani kalar yanayi ya kalleta ya ce "how many times zan ce miki bana son wannan maganar? Eh? Ni na taɓa ce miki ina son ta ne?" Ta ce "Sbd Allah, watarana zaka so ta, she's a darling ita abar so ce" Ya ce "Bana son ta" Da sauri Majeederh ta bar wajan tana rufe Idanunta domin daman tsaye tayi tana mai da numfashi sai kuma ta ji suna maganar. Latifa ta miƙe tsaye tare da barin wajan, Aliyu ya riƙe saitin zuciyarsa a hankali ya ce "Hauwwau, u're my destiny"
Majeederh na zaune zuru ita ɗaya lokaci lokaci take kallon ƙofa, a hankali ta miƙe ta zura hijabi ko wanka ba tayi ba ta nufi part ɗin Mami ta sameta ta shirya zata nufi part ɗin Abbu "Majeederh ya dai?" Kanta a ƙasa ta ce "Mami zan kwanta part ɗinki" Da mamaki ta ce "Me ya sa samu naki?" Ta ce "Tsoro nake ji" Ta dinga kallonta kafin ta ce "Ok ni zani wajan Abbunku ki kwanta ki zare key ɗin, kin ci abinci?" Ta ce "Bana jin yunwa" Mami ta ce "Wanne irin bakya jin yunwa? Da safe na haka kika ce fa, ki tabbatar ko tea kin sha kafin ki kwanta" Ta jinjina kai kana ta shige part ɗin Mami, da mamaki take kallon Ruma sai bata kulata ba Ruma ta ce "Ki ce yau mai kwanan gida ne, ana ta tsofa a gida dai" Majeederh bata ce komai ba. Ruma ta ce "Allah sarki ɗan haɗa mini tea plx ban jin daɗi" Majeederh ta juya ta kalleta ta ce "Ashe ba zaki sha ba" Ruma ta miƙe tana kallon Majeederh ta ce "Ina magana kina magana? Wake ja da matar aure baki san yanzu gaba nake dake...." Wasu tagwayen maruka Majeederh ta saukewa Ruma har sai da taga wuta ta nunata da yatsa ta ce "Ki iya bakin ki, stay in your limit da aure irin naki gwara ban ba, idan iskanci zan yi kinsan me lasisi zan yi" Ruma ta buɗe baki za ta yi magana ta ce "Uffan kika ce sai na haɗa miki jini da majina a nan" Ta yi tsit tana zare idanunta. Duguwar Majeederh ta zauna tana duba wayarta

Please Login or Register in order to submit comment