Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

"Me ta yi maka da zaka jefe ta da wannan maganar Ajlaal Sultaan? Da zaka wulaƙanta ta?" Ya watsa hannu irin ko a jikinsa ya ce "I don't know what comes over me, amma na ji kamar bata yi mini ba, ina bala'in son mace mai tsayawa akan nasara wacce bata yarda da faɗuwa ba, Sorry Nigeria" Ya yi gaba
"Meke damun Ajlaal?" Ƙhulud ta furta tana binsa da kallo ganin yadda yake tafiya kamar bai so. Majeederh kasa motsi ta yi maganganun Ajlaal suka zauna daram a zuciyarta tare da yi mata amsa kuwwa! Ta ji jarumta ya zo mata, komai na kanta ya dawo fresh, Ƙhulud za ta yi magana Majeederh ta girgiza kai tana ɗan yi murmushi "Babu komai"
Majeederh ta faɗa a taushashe tana nufar wani corridor, duk abinda yake faruwa akan idanun Captain Alpha daya jingina yana kuma jin komai deep down na zuciyarsa godiya yakewa Ajlaal yasan Majeederh ta tsani ace bata da ilimi ko a jefata da kalmar _“Kasawa”_ Ya yi murmushi kawai yana ɗauke kansa gefe guda. Majeederh ta buɗe bottle water mai sanyi ta shanye tas, a hankali ta shiga safa da marwa idanunta rufe, idan ta ja numfashi sai ta sauke. Tana tsaye Wani malami ya ce "Ki nutsu, tunda kin fahimci weakness na ki sai ki kiyaye kallon mutane, mu je lokaci ya yi" Ta jinjina kai har yanzu idanunta rufe yana gaba tana binsa a baya. Cikar da hall ɗin ya yi har yafi na baya, kanta a ƙasa ta nemi wajan zamanta a hankali girgiza cinyarta idanunta rufe. Rabin jama'ar wajan idanunsa yana kanta mamakin yadda sauran ɗaliban aka rufesu malamai da jagororin ƙasar su, ita kuma ba kowa. Ɗaya bayan ɗaya aka fara gabatar da final round babu ƙasar data tsallake sai da suka sha gyara, gyara kuma na ban mamaki har aka zagayo kan Majeederh. Ta runtse idanu jin computer na gabanta ya yi ƙara kafin ta ji computer ta ce. "الله"
"Ma hukumu?" Ma'ana hukuncin kalmar Allahu.
Ta sauke ajjiyar zuciya a taushashe cikin sanyin murya mai daɗi ta ce
"Tafkimun laámun ismul jalala" Computer ta nuna blue alamar “Mumtaz" ta yi daidai aka ci-gaba da yi mata tambayoyi na Alkur'ani kafin daga bisani aja mata aya
“Allah taziru waá zirataán uƙƙurrah" Ba sunan sura ba number aya kawai ita ce zatai tunanin wacce surah ce. Ta yi shiru ta rufe Idanunta tare da dunƙule hannu exlty yadda take yi idan tana haddar Alkur'ani.
Ajlaal dake hakimce saman kyakkyawar kujera ya zubawa Majeederh Idanu, haka Aliyu da shigowar shi kenan sai Alpha daya kasa Kallonta, matashin saurayi kuma ƙanƙame jikinsa ya yi waje guda.... Daga can ƙasa Nijeriya gabaɗaya Khan family ne zaune a babban parlourn gidan Uncle Isma'il, sun tisa plasma a gaba tsoro ya cika zuciyar kowa musamman Abbu. Ba iya Khan family ba duk wani gida idan ka shiga kallon musaɓar suke live, wanda basu da t.v a rediyo suke saurara. Abbu ya saka hannu ya share zufar data gangaro masa, ya kasa zama waje guda ya gama tsara plan ɗin yadda zai yi da duk wata kyauta da kuɗin da Majeederh ta samu, amma da alama yarinyar baƙin ciki take masa yana da tabbacin ta iya mugunta ce kawai. Ba zai iya zama ya ji wannan abun ba ya nufi hanyar fita daga parlourn daidai nan ya ji sautin saukar muryarta a cikin kunnenshi wacce ta wadatu da zallar ƙira'a Tajwid mukarijil hurum, ta fitar da komai da karatun Alkur'ani yake buƙata ta saka komai cikin muhallinta. Cak Abbu ya tsaya yana washe baki farin ciki fal zuciyarsa. Uncle Isma'il, Uncle Isma'il Bello, Maman Alpha, Anti, Mami, Aaliyyah, Ruma, Raihana, Widad, Innati... E.t.c suka sanya kabbara.
Wata ɓoyayyiyar ajjiyar zuciya Ajlaal Sultaan ya sauke yana tasbihi a ransa, Aliyu ya yi ƙasa da kansa hall ɗin tsit sautin ƙira'arta ne kawai yake tashi har computer ta tsayar da ita alamun lokaci ya yi. Lokacin daya shiga cikin kundin dairy ɗin Majeederh Abdul'aziz Khan, ta kasa tashi a hankali ta durƙoshe a wajan jikinta na ɓari rawa da ƙyarma wani irin raunataccen kuka ya ƙwace mata lokacin da alƙalai suka tabbatar da Malama Majeederh Abdul'aziz Khan! Matsayin wacce ta zama Gwarzuwa a jerin ɗalibai sama da 100 wanda yake nufin Nigeria ta ƙwace kambon tarihi daga hannun Ƙasar Misira wanda sune su kai na ɗaya a shekarar data gabata. Shugaban ƙasar Nijeriya riƙe kai ya yi ashe kafin ya sauka da rabon a teniwarsa uwa Nigeria zata amsa wannan kambon? Sauran gwamnoni suka miƙe lokaci guda hadda gwamnan Kano suka shiga ɗaga hannu da kabbara, da sarkin Misira dana Saudiyya Sarki Sultaan suka nufi inda Majeederh Abdul'aziz Khan take durƙoshe, Zaytoon ta saka hannu ta ɗagota tare da jawota ta rungume tana cewa
"Allahu Akbar, Allahu Akbar, Allahu Akbar ma sha Allah" Majeederh daman waje take nema domin ta kasa believing na nasarar data samu, ta ƙanƙame Zaytoon tana sakin wani mahaukacin kuka, She just wished that her parents were here to see her suga nasarar data samu, musamman Abbu burinsa ya fara cika. Ƴan jaridu gidan t.v da rediyo sukai kan Majeederh ɗaukarta suke ta ko'ina, lokacin da aka ɗauki wata farar hula ta silver aka saka mata tare da ɗaukan wani abu mai kama da Award na zallar tagulla aka bata wanda ya biyo ta hannun Sarki Sultaan, yin duniya ta cire liƙab ɗin taƙi haka aka dinga yi mata photo wanda kai tsaye ake watsa su a duniya, wasu mahaukatan kuɗi aka bata wanda ita kanta ba zata ce ga adadin su domin hankalinta baya kai tunaninta yana ga mahaifinta. Aka rataya mata sarƙa gold daga nan aka dinga mata kyauta wannan gwamna ya ce ya bata kaza wannan ya ce ya bata kaza, Shugaban ƙasar Nijeriya har yanzu kasa tantance me zai bata matsayin kyauta, duk abinda ya yi tunani sai yaga ya yi kaɗan. Kyautar kujerar Umara data hajji aka bata sarkin Makka ya ƙara bata kyautar kujerar hajji. Kana aka dinga photo lokacin da aka sanya mata albarka bata san mene ya faru ba, Majeederh ta samu kanta da wani irin jin girma wani abu mai girma ya hau kanta daga nan taro ya watse sai walimar da za ayi da daddare. Ƙhulud ta rungume Majeederh tana kuka murmushi kawai Majeederh ta yi tare da bubbuga bayanta a hankali ta ce "Ina mijinki?"
"Yana wajan takawa" cewar Ƙhulud, Majeederh ta ce "Rakani" Da sauri Ƙhulud ta kama hannun Majeederh suka isa wajan Ajlaal na tsaya rungume da Zaytoon da yake tsokanarta Majeederh ta tsaya kanta a ƙasa Zaytoon ta ce
"Ba dai ita ce wacce kike bani labari ba?"
“.... Ita ce Grandma”
"Ma sha Allah, na yi farin ciki ina alfahari dake da ƙasarku" Murmushi Majeederh ta yi ta ce "Na gode Mama" Zaytoon ta ce "Laa, wacce irin Mama bayan zan iya jika dake?" Ta yi murmushi kawai Ajlaal dai yana lafe da bayan Zaytoon ya kasa Kallon Majeederh ya ji ta ce "Thank you"
"For?" Ajlaal ya tambaya yana gyara tsaiwa ta ce "Kai ne ka ƙarfafa mini qiwwa na kasa mance kalmar Daƙiƙiya" Ajlaal ya ɗan shafa gemunsa ya ce "Congratulations"
Yana faɗin hakan ya bar wajan. Bayan sun fito tana ƙoƙarin shiga mota domin komawa gidansu ta ji ance "Hawwa'u"
Cak ta tsaya ta kasa tuna inda ta ji muryar ta juya, yana tsaye hannunsa zube cikin Aljihu sanye da wani tissue ɗin farin yadi ƙal da shi ta yi murmushi ta ce "Aliyu"
Ya yi jim domin bai ɗauka ta san sunan shi ba ya ce "Congratulations Hawwa'u ko wani zai nuna mini farin ciki ina tunanin bayan Abbu ne" Kafin Majeederh ta yi magana aka ce "A sbd kai ne wa?" Majeederh ta ware idanu ganin Captain Alpha bakinta na rawa ta ce "Yaya?" Ya ware mata idanu ya ce "Me kike? Yana da kyau ki huta" Ta ce "Ayya yau ai bana iya bacci, Aliyu baka da lafiya?" Aliyu dai bai ce komai ba sai kafeta da idanu da yake ya ce "Congratulations once again, take this matsayin nawa gift ɗin" Ya dubi hannunsa ta box ne ɗan ƙarami ta ce "No thank you, hakan ma ma gode sosai" Calmly ya taka har inda take ya ce "Please, ki amsa kamar yadda kika amshi ta kowa" Tana ƙoƙarin amsa Alpha ya karɓa ya ce "Mun gode, let's go" Majeederh bata ji daɗi ba amma haka ta daure ta ce "Jazakallah-bil khair, ina Latifa Omar? Kun yi aure hala?" Ta faɗa cikin muryarta wacce ta juye bai amsata ba ya juya kawai tare da barin wajan. Majeederh ta shiga mota Alpha ya shiga baya kusa da ita, driver ya ja suna tafe ya buɗe box ɗin wani ɗan ƙaramin ring ne mai kyau sosai, sai wani farin tissue da akai rubuta cikin good handwritten a hankali ya fara karantawa da sauri kuma ya tura tissue ɗin cikin aljihu ya maida ring ɗin yana tafe baki. Har Magriba Majeederh na tare da yayanta Alpha sosai tayi farin ciki, har akai walima. Ƙarfe 12 na dare ta buɗe wayarta message kamar hauka musamman daga wajan Aaliyah da Anti cikin sauri ta dinga dubawa ko za taga na Abbu domin tasan he's the first person da zai cnrgt nata amma har ta gama dubawa babu nasa jikinta ya yi sanyi a hankali ta danna number Abbu ringing ɗin farko ya ɗaga ta ce "Assalamu alaiyka Ya Abbu" Abbu ya ce "Majeederh na ji labarin irin kuɗaɗen da kika samu, da na yi lissafi sun haura miliyan 20 banda kujerar makkan " Sosai abin ya bata mamaki ta ɗauka zai farin ciki ya sanya mata albarka kan nasarar data samu amma sai ta ji babu batun hakan a bakinsa maganar kuɗi kawai yake? Ta yi murmushi mai ciwo ta ce "Ban san nawa bane Abbu, amma dai da yawa" Abbu ya ce "To da kyau ai tuni na lissafa, a hakanma banda kuɗin albashinki" Ta jinjina kai idanunta cike da hawaye wanda ya fara sakkowa saman fuskarta ta ce "Abbu ka shirya tafiya aikin hajji, ni ma zani Uncle Isma'il da Mami su je Umara" Abbu ya yi zumbur ya miƙe daga zaune ta cikin wayar ya ce "Ashe Majeederh baki da hankali baki da wayo?" Muryarta na rawa sosai ta ce "Me na yi Abbu? Ka yi haƙuri don Allah" Ya ce "Daga ni harke har su Uncle Isma'il ɗin da ita Asaben babu mai zuwa ko nan da airport balle aikin hajji, siyar da su za ayi a haɗe kan kuɗin tas" Majeederh ta ware Idanu while hawaye na zuba a fuskarta ta rufe bakinta ta kasa cewa komai "Hawwa'u?" Muryarta na rawa ta ce "Na'am Abbu?" Ya ce "Kuka zaki akan na ce haka? Shikenan riƙe kuɗaɗenki" Da sauri ta girgiza kai tana zubewa saman gwiwoyinta jikinta na rawa ta ce "Ka yafe mini Abbu wlh ba kuka nake ba, idan kukanne ma na farin ciki nake, na bar maka kuɗin halak makal ko biyar ba zan ɗauka ba, amma don girman Allah Abbu ko kai ɗaya ne ka je aikin hajjin idan ya so sai a siyar da sauran"
Abbu ya girgiza kai ya ce
"A'a ai tas za a siyar da su, nan gaba sai ki sama mini kuɗin da zan je aikin hajjin hakan ya fi ko?" Ta jinjina kanta ita gabaɗaya ba ruwanta da kuɗin ba shi take buƙata ba burinta kawai ta ji ya ce "Majeederh Allah ya yi miki Albarka" Wannan kalmar ita kawai take buƙatar ji, babu uwar da zata sanya mata albarka uban kuma bai damu ba. Abbu ya ce "To sai anjima aci gaba da ƙoƙarin adana kuɗi banda ɓarnatarwa" Kafin ta yi magana ya kashe wayar, sakin wayar ta yi tare da durƙoshewa ta shiga rera kuka kamar ranta zai fita tana buƙatar sanya albarka ko sau ɗaya ne idanunta ya kumbura sosai da ƙyar ta iya kiran Uncle Isma'il ya yi mata addu'a haka Uncle Bello ta kira Anti da Mama kana ta kira Mami sai Aaliyyah ji tayi duniyar ta yi mata zafi komai ya jirkice mata bacci ya ƙauracewa idanunta...... Majeederh ta tattara komai ta ajjiye waje guda karatu take sosai, shaƙuwa sukai sosai da Ƙhulud Arzaan Ajlaal kuma basu taɓa magana ba tun ranar, duk wata sai ta turawa Abbu kuɗi bata san me yake da su ba, Majeederh kullum cikin azumi take ta rame sai ɗan jiki fatarta ya goge sosai, zamanta da Ƙhulud ya ƙara sawa ta zama wayayyiya sosai rashin magana ya ninka nata, tun a lokacin da Abbu ya ja mata kunne ta cire batun aure a ranta, tun tana sha'awar yi har ta fice mata a rai, ta sanyawa ranta ba zata taɓa yin aure ba, duba da cewa tun a lokacin babu wanda ya ƙara cewa yana sonta, a shekarar ƙarshe ta zanna jarrabawa mai kyau ta samu first class tayi farin ciki sosai ta zama cikakkiyar Malamar addinin Muslunci ga tarin magoya baya da take da shi a facebook ta fara faɗakarwa akan maza da mata kamar yadda taga Fauziyya d sulaiman tana yi....

*After 8 year's.... Nigeria*
Aminu Kano airport...30
*After 8 year's.... Nigeria*
Misalin ƙarfe 6 na yamma jirgin sama na Emirates ya sauka a fili tashi da saukar jirgi na Aminu Kano airport, mai ɗauke ɗaliban ƙasar wanda suka kammala karatun su na scholarship da gwamnatin baya ta samar musu. Ɗalibai ne suka ta sakkowa maza da mata ko wanne fuskarsa ɗauke da wani irin farin ciki bayan shekaru takwas yau sun dawo ga iyayensu. "I couldn't believe Aunt Jeederh would come back from Egypt today" cewar Aaliyyah daga gefe aka ce "Me ya sa?" Ta kalleta "Haka nan" Aaliyah ta bawa Widad amsa. Ko wanne banza idanu yake yaga ta ina Malama Majeederh zata fito... Jawaad ɗan gidan Anti da Uncle Isma'il ya ce "Finally" Jin hakan yasa gabaɗaya suka kalli direction ɗin jirgin inda ake sakkowa. A hankali take sakkowa kanta a ƙasa tana sanye da wata Abaya ruwan sararin samaniya wacce akaiwa feshin dutsuna na masu ruwan huda, tayi rolling kanta da vail sai liƙab ɗin data sanya a fuska da wani sirrin farin photochromic ɗin Glasses a Idanunta. Hannunta ɗaya yana jan ƙatuwar trolley ɗinta ɗaya kuma riƙe da hand bag a nutse take sakkowa, lokacin data sakko ta tsaya cak ta lumshe idanu sbd wani daɗi daya ratsa, farin ciki ya wanzu a zuciyarta. Da ace tana da iko kuma zata iya da buɗe fuska za ta yi ta shaƙi ƙamshin iskar ƙasarta wacce rabonta da ita shekara takwas kenan, tun tana shekara ashirin a duniya yanzu kuma tana dab da cika shekaru talatin domin kaɗan ne ya rage mata 28 take yanzu going to 29 tunda end of the year suka kammala Final exm.
"Ma sha Allah" Majeederh ta furta cikin lallausar murya. A hankali ta shiga rarraba idanu taga ko akwai wanda ya zo tafiya da ita, domin komai ya sauya mata. Ihu ta ji an kurma tare da ƙanƙameta ana faɗin "Wlcm back Anti Jeederh" Majeederh ta ware idanunta akan Aaliyah cike da mamakin ganin yadda ta girma sosai ta yi murmushi tana hugging nata back.
"Sannu da dawowa ƙasa Nigeria" Widad ta furta murmushi kawai Jeederh take sbd tsantsar farin ciki. A hankali ta ɗaga kanta sai a lokacin taga tarin jama'ar da suka zo tafiya da ita, Anti, Ruma da Raihana sai Jawaad da Uncle Isma'il da Innati. Ta dinga ware idanu ko za taga Abbu amma babu shi sai jikinta ya yi sanyi. Tana zuwa Ta faɗa jikin Anti ta ce "Na yi kewa Anti"
"Mu ma mun yi rashin yarinyar arziƙi barka da dawowa" A hankali ta dinga bin kowa tana bashi hug Uncle Isma'il ya shafa kan Majeederh ya ce "Kin zama abin alfahari, Ubangiji ya baki zuri'a masu hali irin naki" Majeederh ta kalli Uncle Isma'il a ranta tana maimaita kalamar "Zuri'a" Ganin motoci har guda huɗu duk na familynsu ya bawa Majeederh mmki musamman da taga Ruma ta shiga wata kuma matsayin driver, motar Uncle Isma'il ta shiga ita da Anti a baya sauranma duk suka shiga mota, On their way back home, Majeederh kept looking at the road, everything has changed for her since she went to Egypt until now, eight years after returning. Ta ɗan ware idanu ta ce "Yaushe akai wannan a Government house?" Anti ta ce "Mefa?" Ta nuna musu roundabout Uncle Isma'il ya ce "Bayan tafiyarki da shekaru biyu, gwamanti data sauka" Ta jinjina kai Calmly ta ce
"Amma kamar ba hanyar gida ba, ko ni ce na manta?" Anti ta yi murmushi ta ce "Daman kam za a sha tambaya, nan ai hanyar Lodge Road ne bari mu ƙarasa za kiga komai" Murmushi kawai Majeederh ta yi tana jin sauƙi a ranta ganinta kusa da ƴan uwa shi ya sa bakin nata ya buɗe a taushashe ta ce
"Uncle yanzu ya yanayin garin yake, waye Governor da mataimaki?" Uncle Isma'il ya ce "Engineer Dr. Muhseen Bagayya" Ta yi saurin cewa "A'a ai daman shi ne Governor har lokacin dana bar ƙasar" Uncle Isma'il ya ce "Yes, ai shekara takwas ya yi yanzu ake ƙoƙarin yin zaɓe duk sun tashi hankali"
"Kenan wanne jam'iyyu ne?" Uncle Isma'il ya ce
"Yaushe Hawwa'u ta zama Talkative ne? zamanta a Egypt?" Murmushi kawai ta yi Anti ta ce "A'a ka barta ta tambaya ai ta zama maƙowa, kuma tana da ikon sani ai" Majeederh bata ƙara cewa komai ba har suka isa Lodge Road suka isa street ɗin da zai kai su har gida, Majeederh ta waro idanu waje ganin sun nufi wani tamfatsetsen gida mai mugun kyau, ta kasa ɗauke Idanunta daga gidan domin kaf unguwar babu na biyun gidan, gida ne iya gida 200by 200. Uncle Isma'il ya danna horn gatekeeper ya miƙe da sauri yana buɗe musu, shi kansa jikinsa rawa yake yau zai ga Malama Majeederh Abdul'aziz Khan! Mamaki bai gama sakin Majeederh ba idanunta ya sauka akan wasu lafiyayyiyun motoci na alfarma har guda huɗu a rumfar ajjiye motoci. Parking Uncle Isma'il ya yi yana fitowa Anti ta buɗe ta fito, a hankali Majeederh ta fito tana lumshe idanunta tare da bin cikin compound ɗin da kallo, a hankali kuma sauran motocin suka shigo. Aaliyyah ta kalli yadda Majeederh ke kallon komai ta ce
"Mamaki ko?" Ta jinjina kai Aaliyah ta ce "Ai zaki sha labari" Gabaɗaya suka shiga gidan a Main parlour suka zauna ita dai Majeederh kallon komai take cike da mamaki. "Ya kamata a cire mana liƙab ɗin" In ji Ruma murmushi ta yi ta cire liƙab ɗin, Gabaɗaya suka tsora mata idanu ta waro nata ta ce "Lafiya?"
"Wallahi baki da maraba da Balarabiya Anti Jeederh kin ga mahaukacin kyan da ki kai, sa maza hatsari a titi" Majeederh ta ce "Kyau ya zama Annoba idan har za ai accident" Suka saki dariya Mami ta ce "A bar mini ƴa ta huta haka nan, ta ci abinci" Innati ta ce "Azaba ji munari nabi abinci da gudu ba wando" Aaliyah ta fasa ihu ta ce "Rufa mana asiri ki saka wando" Innati ta ƙanƙance idanu ta ce "Da ubanki kike mara zuciyar nan, mai yawa ƙasa ƙasa yawan kasuwanci, ƴar banza da idanu fiƙi-fiƙi kamar malafar kwaɗo" Aaliyah ta murguɗa baki ta ce "Bani da lokacinki, Allah ya sa kiga fatalwa yau" Tsit Innati ta yi bata sakewa cewa komai ba. Anti ta sassauta murya ta ce "Majeederh jeki wanka ki sallah kici abinci" Ta marairaice fuska ta ce "To ban san ina zan shiga ba" Ruma ta ce "Zaman house ya dawo kenan" Ba wanda ya kalleta Aaliyah taiwa Majeederh jagora zuwa wani part mai kyau sosai da tsari With so much surprise ya dinga kallon komai kana ta cire kaya ta shiga bathroom a hankali ta saukewa kanta shower tana sauke numfashi, ta ɗaura alwala wata duguwar riga mai sauƙin nauyi ta saka, ta saka hijabi bayan tayi sallah ta ɗauki vail tare da rolling kanta kana ta nufi main parlour duk suna zaune saman dining area ta ƙarasa tare da jan kujera ta zauna. Spoon ɗin kawai take juyawa ta kasa cin abincin can dai ta runtse idanu ta ɗan ci kaɗan. Innati ta ce "Shi ya sa kike kamar kazar matsiyata firit a fige ba tsiya ba arziƙi, tirrr" Hira aka dinga yi har su Anti suka yi sallama tare da komawa gida.

Misalin 12:30 na dare Majeederh da Aaliyyah na zaune saman gado Aaliyah ta ce "Bayan tafiyarki babu jimawa Abbu ya ce za a rushe wancan gidan namu a yi sabo, ya ce kuɗi ya samu sama da miliyan biyar, ni dai ban ce komai ba ban kuma nemi sani ba, sbd i don't have any business with that, kuma ubanwa ya bani ikon tambayar inda ya samu kuɗin ma? Muka tattara gabaɗaya muka koma Gidan Uncle Isma'il Mami Kuma da Ruma suka tafi can dangin Mami, ba a ɗauki lokaci ba aka gina gida haɗaɗɗe aka dinga surutu a unguwa ina Abbu ya samu kuɗi shi ba sana'a ba?? Ya yi burus dai a lokacin akai bikin Ruma da Imran sai Raihana......,"
"Amma na gansu gida?" Majeederh ta katse Aaliyah da faɗin hakan ta ce "I have no idea, amma idan suka zo gida sai su yi wata gudu wai mazajan nasu basa gari" Majeederh bata ce komai ba, Aaliyah ta ɗora da cewa "Daga nan kuma Abbu ya buɗe shago a kantin kwari ya zuba kaya da yara masu kula da komai, ya ɗinka sutturu kamar yaƙi, lokacin da kika samu nasara a Misira da bayan wata huɗu ya ce gabaɗaya tashi za mu yi daga gidan nan zamu koma Lodge Road, haka muka koma bamu da wani option, shekarunki uku da tafiya akai bikin Anti Latifa" Majeederh ta waro idanu waje cike da mamaki sosai kafin ta yi magana Aaliyah ta ce "Wallahi anyi bikin bayan jinyar da Yaya Aliyu ya yi a ƙasar waje tsayin shekaru biyu, to bayan ya dawo akai bikin" Majeederh ta sauke numfashi ta ce "Ikon Allah, ina aka kaita?"...... "Gata nan kusa damu, ita ce neighbor namu fa" Majeederh kamar ƙaramar yarinya tai zuru ta ce "How?" Aaliyah ta ce "Good, bamu san mene ya faru ba daman akwai gida kusa damu dake duk kusan gidan haya ne na masu kuɗi kawai sai mu kaga ana fara gyara, daga nan ne Latifa take cewa Aliyu ne ya ce nan zai zauna yafi kusa da wajan aikinsa, ana yin bikin ya ta tare, amma a ranar auren ana ɗaura auren Aliyu ya tafi Cairo ƙaro karatu maganar da nake jiya ya dawo cikin dare" A gajarce Majeederh ta ce "Allah ya sa albarka, ke fa?" Aaliyah ta zaro idanu ta ce "Tab ai nayi al'ƙawari sai kin yi aure zan yi" Majeederh bata ce komai ba ta yi shiru da sauri ta ce "Abbu bai dawo ba?" Ta ce "Kai ai tun 7 ya shigo gida, baku gaisa ba?" Majeederh ta yi shiru kawai.
"Na manta ban faɗa miki ba" Aaliyah ta gyara zama ta ce "Bro Alpha an ƙara masa matsayi daga Captain zuwa General" Majeederh ta ce "Ma sha Allah, Allah ya riƙa" Daga nan Aaliyah ta nufi ɗakinta ba don ta so ba.
A hankali Majeederh ta miƙe tsaye tare da ɗaukan hijabi hankalinta yana kan Abbu shi kawai take son gani, taga ya mahaifin nata yake? Kai tsaye part ɗin da aka nuna mata aka ce shi ne nashi ta nufa, sosai part ɗin ya haɗu iya haɗuwa gashi parlourn farko ta gansa buɗe da dinga kallon komai cike da sha'awa da mmki, ganin baya parlourn ta shiga wata ƙofa da zai kai ta ɗaya parlourn wanda daga shi sai bedroom, ta tsaya cak tare da yin knocking ta ɗauki good 10 minutes tana knocking kafin cikin faɗa aka ce "Who is there?"
"Majeederh ce, Abbu"
Abbu ya maimaita "Majeederh?" Ta ce "Eh" muryarta duk rawa take gefe guda kuma farin ciki take zata saka mahaifinta a Idanunta can ta ji ya ce "To ya akai?" Sosai tambayar ta bata mamaki da tsoro ta ce "A'a daman tunda na dawo ban ganka ba, ina ta duba ka ina so mu gaisa" Daga cikin parlourn Abbu yana

Please Login or Register in order to submit comment