Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dasan kifi shiyasa.
tsoka day'a ta dauka sannan ta yi musu saida safe ta shiga can cikin gidan a falo ta samesu nan ta gaisheda alhj Muhammad da momy ni'ima sannan ta koma can gefen momy ni'ima ta zauna.
sun dan jima suna fira a tsakanin abokan sannan da suka tashi tafowa sukayo musu rakiya suma har bakin gate momy ni'ima tace
"hjia umaima imsha Allah gobe zan shigo ganin dan nawa,, to shiknn hajia ni'ima Allah shi kaimu lpia.
a haka suka bar gidan suka koma nasu.
Annah da dady mua'zzam suka wuce room dinsu yayinda momy umaima tace "ummu wannan dakin da kike shine naki kinji ko?
gyada kai ummu tayi tace "to mah"
Yawwa ummu na to kije ki kwanciyar ki sai da safe ko?
"to momy Allah tashemu lpia"
"Ameen ummu.
a dakin kuwa ummu ta jima tana sake kallon tsaruwar sa da kyansa, ba wani abu bane mai tarkace a cikinsa ba iyaka gado ne mai lulube da tattausan beedshet akai, sai durowas da mirow harda dan qaramin deep freezar sai kuma can 6angaren toilet dake gefe.
kwanciyar ta tayi tareda lumshe idanun ta ciwon mahabeer ne kawai ke ranta a lokacin tasan sam baida kirki mutumin nan tarasa ya zata kaya tsakanin su inya warke, anya kuwa zai barta kamar yanda mah din tace kuwa???
qara gyara kwanciyar ta tayi tareda sake lumshe idanun ta tanata irin tunanin nata a haka barci yayi gaba da ita cikeda mafarkai ciki kuwa harda na mutimin nata.
tsawon sati 2 mahabeer yana Yana gida baije ko ina ba yana jinyar qafarsa yayinda ummu keyin kaffa kaffa dadud wata hanya da tasan zata hadasu,,yayinda kullum hannat tana manne da gidan,,
Kullum Ummu saita je ganin mamanta da baffanta in ta gama ayyukan ta,,,
yau ta kama juma'a ne ummu ta gama girkinta da momy umaima tace tayi mata jefin dan wake dan Yau jikin nata ya motsa batajin dadinsa sosai gashi dady mua'zzam bainan yaje dubai annah kuma tana dakin ta tana hutawa.
lokacin ta koma dakinta tayo wanka ta shirya cikin kayan da momy umaima ta bata jia wato wannan riga da wandon fakistan din sai rawa sukeyi kuwa a jikinta.
babu wani make up a fuskarta shiyasa fuskar tayi fiyau abinta gwanin sha'awa.
parking gashin ta tayi gefen kanta sannan ta dauki mayafin kayan ta nada sa akanta nan da nan ummu tasake fitowa da usulin kyanta babu wanda zaiga ummu bai ji buqatuwar cewa ta zama mallakin sa ba.
fitowa tayi tashiga kichen ta dauko abincin momy umaima ta nufi dakinta tayi sallama ta shiga ganin bata nan ne yasata tunanin kotana wajen annah mafarin knn ta juya ta koma dakin annah dun, anan tasamesu zaune suna fira, har cikin ran ummu taji dadin ganin yanda mah din tasamu lpia ba kamar d'azun ba.
zama tayi tana 'yar dariya dariya ta murna bayan ta gaida annah tace "mah gashi na gama danwaken da kikace"
"kai ummu nagode fa sosai naji dadin ganin dan waken nan yanzu yanda niketa jin kwadayin nan dan na zata ma sai dare zaki yi mana"
Murmushi ummu tayi tace "annah kin iya cin dan wake ma kuwa?
tayi maganar a tsokane dan itama yanzu ta saki jikinta ta mayar da annah kakarta,,,
"lalala ummu karkice zaki biyewa mahabeer na fa kuna tsokanar mun uwa"
cewar momy umaima tana dariya itama,, annah cikin raha tace "rabu dasu umaimatu,,zanyi maganin sune a gidan nan ay, hijira zanyi gobe in koma katsina sainaga wanda zasu tsokana,,fiddo fararen idanunta ummu tayi tareda ruqo hannayen annah cikin kalar murmushin ta tace
"wasa nike anna zanje na kawo miki kema naki yanzu ay, dariya momy umaima tayi ita da annah kawai har ransu qaunar yarinyar kullum take qara shigarsu,,
anna tace "aa ni bnjin yunwa ynzu nagama cin abinci"
Marairaicewa ummu tayi tace
"to amman in ajiye miki ko annah zakici anjima?
cikin Murmushi annah ta shafa kan ummu tace zanci ummu allah dai shi miki albarka yanda kike dad'ad'a mana kina samu farin ciki a kullum,,ameen cewar momy umaima dataketa saka danwakenta a baki tana ci harda lumshe idanun ta tosshin yasha yajin daddawa da magi d.s sai qamshi yake.
"Annah mah zanje wajen su baffa in gaishesu,, cewar ummu hani tana mai miqewa tsaye,,
Momy umaima tace "to shiknn sai kin dawo annah ta qara da cewa "ki kuma gaishesu qwarai2"
tana fita ta koma dakinta ta zura plate shoes dinta ta tsaya gaban mirow tana kallon kanta Murmushi tayi tasan in su baffa suka ganta haka tasan zasuji dad'i sunsan cewa hankalin ta na kwance ba kamar sanda suka shiga damuwar nan ba lokacin da suke nemn mafaka.
dan siririn Murmushi tayi jin gyalenta ya dan zame daga baya sabida santsin gashin kan nata yasa tasa dogayen fararen yatsunta ta fiddo jelinayen gashin kanta guda 2 dogayen gaske baqi qirin dashi gashin sai shining yake.
ta gaban goshinta ta sakosu har saman q'irjinta suka hau suna yawo,,
maido da gyalen tayi ta yafa sa bisa kan nata sannan ta koma kichen ta d'auki kular abincin su baffa din tanufi waje.
dayake momy umaima tace in zatayi musu girki ta dinga girkawa dasu baffan nata dudda acan suma ana kai musun nasu in momy ni'ima tayi, hakan da momy umaima tace ba qaramin dad'i ummu taji ba, a rayuwa burinta shine taga komi ta samu ko taci to suma iyayen ta susamu hakan shine cikar farin cikinta.
daga nesa ta hangosa ta wajen swimming pool din wajen inda yar bukkar nan take yana zaune bisa kujera ya dora qafan sa guda biyun a bisa tebir din tsakiyan wajen,, hannunsa riqeda viju milk yana tsotsa ,,
batasan dai su waye kusa dashi zaune ba, ga alama dai abokansa ne mazan,,
rasa yanda zatayi ta wuce ta wajen tayi dan dole saita hanyar da suken ne zata fita.
ta jima tsaye a wajen datai taga lokaci na neman qure mata yasa kawai ta yanko tikitin shahada tayo hanyar wajen nasu,,tun daga nesa ya zuba mata idanunsa yau tsawon sati 2 knn rabon daya yarinyar dudda burin da yaci nason ganin nata akan qudurin nasa,,
tunani yake sonyi akan wane irin kalar hukunci ne waima ya kamata yayi mata danya huce haushin sa akanta amman kuma zuciyar sa taqi basa daman yin hakan ta hanyar shagaltuwa da yayi da bin yarinyar da kallo batareda ya ankara ba,,, ganin ta kusa isowane kusa dasu itama akayi sa'a ta dago idanunta nan da nan suka had'a idanu cikin sauri ya fara maido nutsuwarsa cikin jikinsa ya yamutsa fuskarsa cikin daure fuskarsa tamm tam saida ya danqaro mata wani zafaffen kallo wanda ya haddasa wa ummu wani iriyar faduwan gaba ba shiri shikuma yasake binta dawani banzan kallo na raini yana binta da wata hararar sannan ya janye idanunsa daga cikin nata yana sakin tsoki ya maida viju milk dinsa cikin saman lips dinsa yaci gaba da tsotsar abinsa.
mukhatar cikin rawar jiki da da kyarmar baki ya tabo bash da Masud da imran yace
"kai kutttttt,,, wowww gayu kun kalli kyakkyawar halittar dake tunkaromu kuwa a halin yanzu?,
anya ba aljana bace takeson budemin ido inyi *gamdakatar* da ita kuwa ba a yammacin nan?, dubn inda mukhtar din yake nuna musu ne sukayi suna bin wajen da idanuwa suma,,,,
babu wanda zuciyar sa bata girgiza ba da ganin yarinyar ba a cikinsu suma, nan da nan suka hau murtsuka idanusu suna tunanin anya kuwa ba Ubangiji Allah ne yasa yaci dasu da rabon yin mafarki daga day'a daga cikin matan hurul ayni ba kuwa?
ji sukayi gaba day'a jikinsu yai musu sanyi a lokacin musamman mukhatar uban zalama lokacin daya tabbatar da cewa Lallaikm wannan mutum ce bil'adama abin hakitta.
cikin qunar rai mahabeer yasa hannu ya daki table din gabansu hatta sauran milk din da cups dake akai saida suka rigizazo qasa suka watse,,
da sauri suka maido hankalin su jikinsu shikuwa sai masifa yake tsattsaga musu da cewa "haba miye haka kukeyi dan Allah kuma mukhtar?? Kun wani kun sanyawa yarinyar mutane idanu dud salon dai kujanyo mana raini kuma? Yayi maganar ransa a matuqar 6ace wanda shi kansa baisan yaya hakan ta kasance ba,,
dai dai lokacin ta ida giftawa ta wuce ta gefensu cikin d'ari d'arin da takeyi gameda mahabeer din,,
saida ta wuce ne harta qulewa sannan suka maido hankalin su jikinsu lokaci day'a.
sauke ajiyar zuciya mukhtar yayi yace
"kamm bala'encan.. waiii zillaziya... duban mahabeer yayi yace
"gifted daga wane duniya gidan nan naku ya samo mun mata ya kawomun har gida dan Allah fada mun gifted??
bash yace "kaji dan iska namamajo kakai maryam din ina?? saura kwana 3 fa a daura muku aure,,?
"to dan yana saura kwana 3 in aureta ban iya fasawa ne kukega akan wannan zazzafar? kai kokuma in auresu duka ai addini ya yardar mun🤷🏽‍♂ ko? "
Wlh kunji ma na rantse zan iya barin auren maryam Dan wannan zata ishi mutum komi basai ya qara wata ba, yayi maganar yana sake zuqo hayaqin tabarsa.
Bash yace ''kaji dan iska kanata surutai ma kasani ko matar aure ce,,??
Mukhatar yace "ohhhshet..!!! daina mun fatar hakan dakuwa ba cutu wlh kajini da dan iska mugun bakinka ya koma maka to"
dammm!!!!!,,,,,, mahabeer yaji gaban sa ya amsa da maganar da yaji bash yace wai may be itan matar aure ce.
girgiza kai yakeyi samun kansa yayi a fili yana furta kalmar "noooooo mukhtar noo mukhtar,,, dukansu da kallo suka bisa shikuwa hannunsa yake kallo ganin yanda jini ke dan diga sakamakon cups din daya doka d'azun da hannun nasa harta kaiga ya yanke dan shi saima lokacin ya ankara da yankewar tasa. runtse idanuwan sa yayi gaam yayinda ya ciro farin hankicerf dinsa daga aljihun sa yafara qoqarin daure wajen dan jinin ya tsaya.....


*Xexen Fasaha*
[10/11, 2:47 PM] Xainab Documen: 🌊🌊🌊

*MAHABEER*!!!
🌊🌊🌊
Story and writing
by
Xayyneb 💤💤

🌊🌊🌊🌊🌊

Fasaha online writers f. o. w.

🌊🌊🌊🌊🌊
🅿2⃣9⃣
🌊🌊🌊
*A* hankali jinin ya fara tsayawa cak daga zubowar da yakeyi daga tafin hannun nasa.
Bash ne ya ida daure masa hannun da hankicerf din sannan yace
"garin yaya haka kuma gifted daga magana kuma?
idanunsa mahabeer ya dago ya duresa bisa na mukhtar ya banka masa wata harara,,, dariya mukhtar ya kwashe da ita sannan yace"gifted kaifa kana mana yabin wlh,, ya bani na tambayeka ba amman kanamun hararar haka? Ka harari bash d'in mana nikega ai zaifi ko? ,,,
Masu'd yace "plzzz mu dawo kan batun waccen fine babyn din guys koko ba haka ba,,, imran yace "Wlh kuwa friends kamar kasan abinda nike shirin fad'a knn ka rigani furtawa"
Mukhtar cikin zuqar tabarsa da yake sakeyi daga kishin giden da yake kan kujerar yace
"miye had'inku da da ita da kuka nacewa vatunta haka? Bakuka nayi shiru ba ne ni? Ina jiran gifted ya dawo dai dai ne daga yankan da yasha na dora masa tambayar ta daga inda na dora,,, bash yace "dalla mutane kuyi mana a hankali mana bakuganin irin jinin da ya gama zubarwa ne eye?
Mukhtar yace "hannu ke bada amsa koko bare kace hannun nasa da ya gama zubar jinin zai fama sa eye?
mahabeer gaba day'a ji yake surutun nasu na hawan masa kai dan haka cikin zafin zuciya yace "dan Allah ya isa haka,, dubiyana dai kukazo yi ko?
ya dubi su mukhtar din inka dauke bash dake gefensa wnda dama shi yasan baya cikin wnda mahabeer din kewa wannan tambayar,, dan da mukhtar din da Masud da imran dud halin su day'a na mugun son matan tsiya jarababbune na gasken gaske indai akan fannin mata ne ecpecially kyawawa ma.
masud yace "korar mu xakayi ne?
Imran yace ''ga alama dai kam hakan yake nufi,,,.
Mukatar yace "bari kaji gifted billahil axeem bazan bar wajen nan ba saika Fadamun wacece wannan yarinyar wacce ta gittamu ynxu ta wuce,,ya qara da cewa club zanje hakan na tsara amman zuwa na nan wajen ka da kuma arba da wannan lafiyayyar babyn da nayi ya rusa mun dud wani budget nawa Wlh, dan haka rufin asirinka indai kanason mu barka ka sarara shine kawai kai mana bayanin ta mlm"
Bash yace
''tirrr da kai mukhtar,, wlh kai dai mugun mayen mata ne dan air kawai, badai ka laso wajen dadin ba"
"kamace mun komi ni bazan da muba in dai zan samu amsata tofa hakan yayi"
cewar mukhtar din da yake sa cover shoes din qafarsa yana murje bindin sigarin da ya gama zuqarta ya yar a qasan wajen.
"plxxx gifted fada musu kawai ka wuce wajen kasan mayun mata ne su"
hade girar sama data qasa mahabeer din yayi tareda cewa"qyalesu bash barcin suna 'yan iska miye abin wani firgici da ganin yarinyar? da wani birgewa ga wasu matan hausawan marassa kamun kai???? balle ma ita wannan da tazo mana a matsayin 'yar aikin momy na s cikin gida face,,, tana aiki ana biyanta salary shine kukewa qwaqqafin tanbayr dai ko?
toga amsar nan kun samu saiku tashi ku qara gaba haka nan ko 'yan culub?
basu mukhtar da yafadawa cewa yarinyar 'yar aiki ce a gidan hatta bash saida yayi matuqar al'ajabi na mamakin ganin wannan kyakkyawar yarinyar wai house girl??????
wacce kamarta dai hakan ya kamata ace tana gidan wani dan shahararren dan kasuwan kokuma mai mulki ko sarauta tana aure amman gata available a matsayin 'yar aiki a gidan babban atrajirin dan kasuwa mua'zzam saraki tana bauta??????
"ta666 ikon Allah knn"
Cewar bash d'in yana mai sauke ajiyar zuciya.
Mukhatar kuwa baki ya saki shidasu Masud sai da qyar mukhtar ya bude baki yace "kutttt,,, anya kuwa???? to indai haka ne daga wace qasar taxo ne? dan da gani chief baby din nan ba zubin nan bane dagani zafinta zaiyi yawa Wlh ta hadu ta ko'ina k...
miqewa tsaye mahabeer yayi tareda jan wani kalar mugun tsoki yabar wajen bayan ya miqawa bash hannu sunyi hannu yayi shigewarsa cikin gida,, ya tsani irin firarrakun nan
da mukhtar keyi marassa kan gado haka,,,
dole su mukhtar sukabar gidan suma zuciyoyinsu amman cike suke da hasko zuqeqiyar babyn nan kuwa....
bash kuwa bayan mahabeer yabi zuwa cikin gidan shima.....
Ummu hani kuwa saida su baffa suka matsa mata akan ta koma gida haka, da yake lokacin anyi sallan magrib ma sannan ta dawo gidan anan falo ta gamu da momy umaimah da jug riqe a hannunta tana ganin shigowarta tace "yawwa ummu kin dawo ko? " cikin Murmushi tace "eh mah su baffa na gaisheki,,"allah sarki ina amsawa,,, jug din hannunta ummu ta amsa sannan tace "kawo nakai kichen din mah, aa barshi ummu kije ki huta yau kinsha aiki ay"
"hmmm momy aikin ai babu yawa ma kmr ynda kike gani,,
"hmm haka dai kikace ummu,, amm gobe insha Allah zamuje dake kasuwa na siya miki kayan sawa daga nan mu wuce wajen tailor domin yaga side dinki n ynda dinkin zai kasance,
Kije kinkwanta ynxu ummu saida safe"
"to mah ngd sosai Allah qara lpia cewar ummu kanta na sunkuye,, jitakeyi kamar zatayi kuka batasan wane irin so mutanen gidannan ke nuna mata haka? Kull wata zuciyar tace kin manta da amakson (maq'iyi) dinki dake cikin gidan nan,,runtse idanunta tayi sannan ta bude su tace ''to mah na tafi Allah tashemu lpian,,"
"ameeen ummu,, "
Momy ta wuce kichen dan ajiye jug din tana fitowa itama tayi dakinta dake fuskantar na annah.
yayinda ummu ta nufi dakinta taxo wucewa ta dai dai wajen wani room wnda yake kallon na dady mua'zzam knn taji an sha gabanta har ta tsorata ma ta fara ja da baya, dan ita haqiqanin gskia ma bata ta6a tsammanin da wani mahaluqi wajen ba jin ynda wajen ke tsit sai qarar esinan dake round wajen.
qara gyara zaman mayafin jikinta tayi zuwa saman kanta ganin ynda yake binta da wani kallon raini yana ta6e pink libs dinsa yana yamutsa fuskarsa kamar dole akai masa tsayawa wajen alhalin ya fito yin alwalar sallar isha'e ne ya gantan.
Sake had'e baqaqen cikakkun girarsa yayi gabda juna yana mai zura hannayensa a aljihun jeans dinsa duka guda biyun yana tun karo inda take.
tunkarotan da taga Yanayi ne ya sata jada baya baya tana waiwayen bayanta gudun kada taci qasa zuciyarta kuwa fad'i takeyi
"na banu wayyo momma na baffa,,, nasan daman bazai barni ba wlh wnn amakson din.
Jifffff taji ta fad'a a cikin wata kujera dake gefen wajen da taken a tsaye tana qoqarin yunqurawa ne tatashi taji yasa qafafunsa wanda takalmnsa a lokacin sun kasance masu irin tsirar mutum dinnan ne a qafanka muddin ka kuskure aka taka ka dasu,,,
Tosu ne fa yasa qafafun nasa ya danne fararen qafafunta dasu tin tin qarfinsa yanada tsayen hankalin sa kwance yakama hannayensa duka biyun ya had'e su cikin qirjinsa.
Wani irin azabar zafine taji lokaci day'a ya ratsa mata kwanya bazato ba tsammani kuwa,,
da qarfi ta saki wata wahalalliyar tsuwa amman saboda muryarta dama can haka take silently shiyasa tsuwar nata data saki bai karade falon ba na qasa iyakarsa anan inda suke wato falon saman benen wnda shine inka gangare daga falon ka qara sauka qasa sai dakin ummu din.
Zumbur tayi ta miqe tsaye a gbnsa tana son guduwa amman ta kasa dole ta koma saman kujar ta fad'a da bayanta ta koma matsar kwalla kawai da suke zurarowa daga fararen idanunta hatta eye lashes nata saida suka soma jiqewa a lokacin suma da lemar hawayen nata.
bata haqura ba a karo na 2 ma ta sake miqewa abinda ya faru da ita a first round shine ya qara samunta a second round,, wannan karon baffaaaaa na kawai take kira,,, dan tanajin tsananin azabar zafin dake shigar qafafunta kamar zasu 6are haka take jinsu,,,
ba shiri tasa hannayenta tana ture qafafunsa daga kan nata tana bubbugasu da qarfi tare da fad'in "ka dagamyn qafafu na amakson zafi wayyo dan Allah ka tadamun qafa na..... sai hawaye sharrrrrrr suka ci gaba da bubbulowa daga idanunta na tsabar azabar radsdin dake ratsa mata qwalwan kanta dud bayan second.
fuskarta takama matsawa da qarfi tana rungume jikinta tunaninta kota samu relief na sauqin axabar da mahabeer ke d'ura mata ta cikin qafafunta amman ina,,,, dole ta koma kan gashin kanta dayake sake a waje wnda azaba tasa tuni mayafin datasa ta rufe kan nata dashi yayi qasa tuni tulin gashin kanta data duqunqune ya warware ya sulalo gaba dayan jikinta tasa hsnnayenta akai tana tamqe gashin Tana burgima a cikin kujerar tana fiddo zafafan hawaye,, Allah kawai take kira a lokacin ya kawo mata d'auki daga wannan mugun maqetacin,,,,
dubn watch din hsnnunsa yayi ya dubeta Yana mata wani kallon rashin tausayi irin ko a jikinsa dinnan sannan ya girgiza kai tareda gyada kafadunsa yana wani turo baki yana tabesa yace"wlh da sauran tym yarinya dan kokacin sauka na baiyiba akanki,saura 4 munts, dan kisan ma da sanin yanda kika nemi nakastamun qafa harna kwanta jinya kema sai kin dan dana hakan,
dan kin ganni nan bazan lazimci yafiya ba ga dud wanda yanemi rabani da jindadina ba na lpia na dai dai da second day'a, da gangan koda bada gangan ba
Saifa mahalicci na wlh,,,,amman badai mutum abun halitta ba irinki ma stupid 'yar qauye masu yawon bara da kwana bisa atiti buzaye, wataqil ma dis vgn ne ke ma ko?
Mutane na miki kallon budurwa,
an gama barar da mutuncin wajen kwanan hanya dan a samu na abunci mtssss mima zanyi da hausa fulani Allah sawaqa ahaka kuke mafi yawancinku baku iya komin kuba wnda zaisa ku burge mutum sai dai baqanta masa mtsss yasake sakin wani sabon tsokin..
Shiru ya danyi sannan ya dasa da fad'in "munafika kawai sumimi kasau kullum kina lullube da fuska saina yanke wannan hancin naki inga ta rashin kunya ...,,
yana maganar ne cikin cije lips dinsa tareda qara sakar mata nauyin sa a saman qafafun nata,, gabaki daya muryan ta ya dishe baiwan Allah ummu hani,, ko kukan ma ta daina sai ruwan hawayen kawai dole ta sulalo da qugunta qasa ta sa hannayenta ta rungume qafafunsa katamau tana bubbugasu iya qarfin harda cizawa da 'yan mini minin haqoranta ta jikinta sai kyarma yake,,,,,
a zuciyarta yau kam ta sake gazgata mugunta ta wannan amakson din nata lallai ta sake tabbatarwa da cewa dud gidan nan Ko kuma ma tace dud duniyar nan batada cikakken maqiyi nan kuwa daya zarta sa,, gashi ranta har wani zafi zafi takejin Yana qara yi mata na munanan kalamen da yake jifanta dasu,,
Shikuwa ynda kasan ma ba'a jikin qafafunsa take hknba haka yaji shiyasa ko motsawa baiba yana tsaye abinsa fuskar nan murtuk babu sassauci.
saida yaga lokacin ya ida sannan ya janye qafafunsa
akan natan yayi gaba abinsa yana fad'in
"gobe ma in halinki kiqara zubda abu inzo in zame na fadi wlh sai na miki mafiyin abinda kika samu ynxu buxuwa kawai dake 'yar qauye..
sulalewa tayi ta kwanta a wajen rungume da qafafunta tana shafawa jin yanda sukayi tudu ne na kumburi yasa ta sake fashewa da kuka ta kama burgima a wajen tana fad'in "wlh amakson (maqiyi) kasan da sanin cewa bazaka shani basille ba ni dakai
*da sauran kallo*
A gidan nan chief amakson wayyo momma na baffa na kuzo kuga ummun ku a yanda take rayuwa da shugaban mamuguntan duniya a gidan aikinta.. "
a haka dai da qyar ta samu ta dinga yin rarrafe a qasan tayils din wajen harta gangara zuwa dakinta ta baje anan tsakiyar dakin tana maida numfashi sama sama....


*Xexen Fasaha*
[10/11, 2:47 PM] Xainab Documen: 🌊🌊🌊

*MAHABEER*!!!
🌊🌊🌊
Story and writing
by
Xayyneb 💤💤

🌊🌊🌊🌊🌊

Fasaha online writers f. o. w.

🌊🌊🌊🌊🌊
🅿3⃣0⃣
🌊🌊🌊
saida ta dan samu sauqi sauqin zugin qafar nata sannan ta samu ta koma bisa gadon ta kwanta tana mai goge qwallan fuskarta cikin sauke ajiyar zuciya.
a fili tace "ko siyoni yayi sai haka da wannan rashin qaunar da yake nunamun kamar wacce ta zamo maqiyarsa tun usulin farko,,, ni dama ban taimaka masa ba lokacin daya nemi in taimaka masan da ba'a kawo kamar yanzu ba.
wata zuciyar taji tana ce mata "kul da fad'in dama dinki akan taimakon mutum ummu hani,, yanzu ba gashi silan hakan ya haifar da alheri ba a tsakani? inda gashi ta silan hakan Allah ya kawo ku inda zaku samu abinda kuke da burin samu na aikin mommanki na hanyar albashin da iyayen naki zasu dinga samu ba kumz?
har asamu kudin sukai iyakar gejin da akace mukun ku kawo??? wannan shine ake nufi da alheri danqone yaddashi baya ka tsincesa a gaba a dud ta yanda yazo maka kayisa.
to dan haka ki daure kada ki nuna gajiyawarki akan wannan amakson din naki dake gidan nan kada kiyi tunanin cewa kibar gidan sabo dashi kada kiyi haka dan zaiji dadine shi,,,
a'a kedai kawai kiyi duba ga ciwon mamanki kiyi ta haquri akan abinda ya kawoku garesu har Allah ya kawo iyakar barinku garin nasu sai kiga kuma wazaiwa?
murmushin takaici tayo tana mai cigaba da share hawayen fuskar nata sannan tace
"zan dauki shawaran zuciya na amman fa kasani bawai na qyaleka bane amakson Allah saina rama....tayi mgnr cikin rawa rawan muryan ta na mai kuka,,, taci gaba da fadin "danma kabar ganin wai ina shiru shiru dogon zance ne ke bnda ra'ayin yinsa ne saita kama"
kamin cin mutunci iya son ranka ko???
Uhmmm,,, kwanciya tayi sosai bayan tayi add'ua ta kwantan amman zuciyar ta cike take da tunanin tawane hnya

Please Login or Register in order to submit comment