Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

d'in shi d'aya yanata barci abinsa lpia.
Tashin hnkali ya ziyarci zuciyar umaimah a lokacin dataji abinda mutumin Ke fad'a na zai rabata da MAHABEER d'in ta in iyayensa sunzo karbar abinsu, Wanda takeji duk duniya batajin akwai abinda zaisa ta iya rabuwa dashi dan a shirye take data bada ranta fansa ga jaririn...



XayynebπŸ’€πŸ’€.
[10/11, 2:44 PM] Xainab Documen: 🌊🌊🌊

*MAHABEER*!!!
🌊🌊🌊
Story and writing
by
Xayyneb πŸ’€

🌊🌊🌊🌊🌊

Fasaha online writers f. o. w.

🌊🌊🌊🌊🌊
πŸ…Ώ3⃣
🌊🌊🌊
*Q* ara ware idanunta umaimah tayi kan hoton tana kallon mamar shi mahabeer d'in, wnda kowa ya gnta kuwa yasan tabbas itace dai mamarsa sbd kamarsu d'aya sak,
Sannan ga kuma ita wannan dattijuwar matar da akace ita ta kawosa a gefen mamar MAHABEER d'in suna dariya aka d'auki photon. Maganar da taji mu'azzam sarakin na cewa ne yasa hankalinta dawowa wajen kacokam!
"To shiknn mlm mukhtar bakomi, Allah shi kaimu lokacin da rai da lpia kuma,
ay kasan shi cika alq'awali abune muhimmin gaske a dukkan rayuwar d'an Adam."
Nan mu'azzam sarakin dai ya cike file d'in da shi mlm mukhtar d'in ya basa ya ciken,
da kuma dai sauran abubuwan daya kamata yayin duk yayi su lokacin gaba d'aya,
Sannan da zasu tafi kuma ya cikasu da kyaututtuka suda kingin marayun gidan,
A lokacin kuma suka kamo hnya suka dawo gida.
Suna shiga falon gidan kuwa umaimah tayi saurin kar6ar yaron daga hannun Annah tana murmushin murna ta shige d'aki dashi ta goyeshi ram a bayanta ta fito falo tana zagayawa dashi,
shi kuwa sai mutsu mutsu yake yana q'oqarin tura hannunsa a baki ga alama mamansa yake son sha bai ishesa ba.
Annah kuwa sai binta da murmushi kawai take yi,
Sannan Annah d'in ta d'auko wayanta tafara gayawa 'yan uwa da abokan arziq'i haihuwar,
nan da nan kuwa akaita kiran iyayen jaririn ana musu murna sukuma suna amshewa cikin farin ciki.
Ranar kamar umaimah ta zuba ruwa a q'asa tasha Dan murna,
nan mu'azzam ya kirawo family doctor d'in su yace yana so ya siyo masa madarar da yasan ana bawa jinjirai in ruwan nono yaq'i biyawa.
Ba'a d'au tsawon lokaci ba sai gashi kuwa doctor d'in ya kawo madarar katan katan.
shima yai mamakin ganin jinjirin nasu.
Amman kuma da suka fad'a masa abinda suke fad'awa sauran sai ya yarda shima, duba da shi kansa ma yajima rabon sa da garin sai kwanan nan ya dawo sakamakon canjin wajen aiki daya samu.
Nan aka had'awa baby milk d'insa,
ita ya wuni sha abinsa.
Washe Gari kuwa abokanan umaimah sukaita zuwa ganin jinjirin kowa ya gnsa sai yayi santin yaron matuq'a.
'Yan katsina suma tun ranar suka fara durowa gidan haihuwar har zuwa ranar suna inda akasha shagali na kece raini kusan sati ana shagalin kuwa bai q'are ba,
Hatta abokanan mu'azzam saraki sukan zo takanas dan ganin jinjirin tareda ajiye masa kyaututtuka masu nauyin gaske.
Gskia kam baby yasamu dukiya ta ban mamaki, shiyasa babansa mu'azzam saraki ya bud'e masa account kawai yana zuba masa kyautarsa daya samu.
Kullum Annah tana tare da MAHABEER itama bacci kawai ke maidata d'akinta dan tana matuq'ar son sa itama sosai.
Haka suke rainon d'an nasu cikin farin ciki har yau gashi yayi wata 6 zuwa lokacin harya karya qafarsa wato ya fara rarrafawa knn abinsa gwanin sha'awa.
A lokacin ne Annah ta koma katsina cike da kewar MAHABEER.
Amman tun zuwan MAHABEER gidan Annah bata d'aukar tsawon lokaci bata zoba gidan d'an nata ba kamar da ba da zasuyi ta fama da ita ma akan tazo sai ta q'iya wai a cewarta jikin tsufa ciwo baison tafiye tafiye...
Shima MAHABEER ya fara sanin Annah shiyasa daya ganta tazo gidan har wani murna yake da zullon son ta d'aukesa Dan ya tantanceta a yanzun shima sosai.
Kullum kyansa q'ara fitowa yake na sak jinin larabawa....
'Yan magana sunce shekara bata gadon shekara yau har MAHABEER ya cika shekara 5,
A lokacin har an sanyasa nusry one a school.
Akwana a tashi har gashi ya gama nusry t primary har ya shiga secondary lokacin.
Allah yai masa brain shiyasa yai suna a school d'in su kowa a frnds d'insa zakaji suna fad'in
Gifted MAHABEER.
Tun su umaimah na zullumin yau ko gobe za'a zo d'aukar MAHABEER har suka daina dn ganin an Shari wad'annan shekarun haka Amman kuma shiru kukeji .
Kulawa kuwa ta fannin iyayensa kullum sai abinda yaci gaba kuwa takai yanzun in dai ya samu Hutu shida kansa yake matsawa dadynsa yakaisa katsina wajen Annah Hutu.
Haka zasu tafi kuwa su kaisa shida momynsa umaimah....

Haka lokaci yaketa tafiya kwanaki na zama shekara har gashi yau MAHABEER yayi degree d'insa da masters degree yagama duka.
A lokacin kuma ne
Ya zama wani irin murd'adden mutum q'arfaffa, wato irin giant d'innan ne,
ya ida riked'ewa ya zama hands some guy wani muskilin mutum naq'in q'arin kansa, d'an shekara 29.
A cikin satinne kuma mu'azzam saraki ya tursasa masa fara zuwa office d'insa dashi yayi murabus a kan kujerarsa ya d'ora MAHABEER akai a cewarsa yanzu ba kamar daba, ayyukan zasuyi masa yawa, q'wamma ya tsaya kan fita q'asashen wajen sa yana fiddo da kayan business d'insa abun zai zamo masa da sauq'i hatta al'amurran gidajen man sa da motocinsa na company dinsa ya damqa ragamar komi ga MAHABEER d'in,
Giant man knn,
nera kamar tai masa kuka ga kyaun usuli,...
'Yan mata kuwa komin nacensu garesa jin kansa da isarsa bazai ta6a iya bari ya d'aga kai ya dubesu ba, muddin bashine yaso ba dan Karin kansa ba.
**
Yau dai a matuq'ar gajiye MAHABEER ya dawo gida,
Parking motarsa yayi sannan ya sa6o labcote d'insa da brife case d'insa, fuskar nan a had'e ya tura q'ofar falon nasu ya shiga.
Ganin saman q'ofar dak'in ammi d'insa a rufe ya tabbatar masa da tana hospital d'in datace masa zataje ganin diyar q'awarta nahnah.
D'akin sa ya wuce ya tulla kayan hannun nasa kan gado sannan ya cire kayan jikinsa ya d'aura towel iya q'ugunsa ya shige toilet.
Yana fitowa kuwa yaji phone d'insa ta fara ringing a d'an duban harara ya kallo wayar dan baison wani Abu ya gitto ynxu ya damesa a ynda yakejin ya gajinnan over,
Wayar ya d'auko ya duba ganin sunan bash ne yasa shi d'an sakin fuskarsa kad'an shima, sannan ya d'aga yace
"yadai bash kun dawo ne?
Daga can bangaren bash yace
"kai gifted wlh mukhtar d'an iska ne,
yau rabon iv d'in nan na bikinsa da mu kaje nida mas'ud ba q'aramar wahalar damu yayi ba harda imran,
tun safe fa sai ynxun ana magrib muka dawo gida ,
Kai kai kai huhhh,!
Rabon iv ko masifa,
Shiyasa Nace masa
wlh gobe weekend dole ka fito dan a ida rabon nan dakai kaima kaji ynda abun yake inda gobe shine last day na rabon iv d'in.
Ta6e lips yayi yace
"ba inda zanje guys dan kuma sani,
Ni gobe ma KT zanje na dauko Annah ta,
Da sauri bash yace
"kai Dan Allah gifted?
You seriously?
Indai haka ne nima zanje kuwa ka jirani zan zo to muje dan nayi missing Annah wlh a lot nima, Amman Allah sadai ba jirgi zamu hauba?
Dan na sanka kamar tsuntsu kake wajen yawo a Sama."
ta6e lips ya sakeyi yi dan gajiya da yayi d mgnr sannan yace "don't mind bash,
a motor zamu indai zaka, but kuma wlh karkamun iskan cinka na lates African time, dan by ten i think zamu wuce ma ok?."
"OK babu ji ay gifted"
Cewar bash d'in.
Ajiye wayar yayi ya ida goge sauran leman ruwan jikinsa da towel d'in kansa, sannan ya murza sansanyen cream lotions d'insa ya fiddo wata baq'ar Riga irin ta shan iska mai gajeran hannu,
inda ta bayyana masa kwantaccen gashin jikinsa lu6 lu6 gwanin sha'awa. sannan ya zura tree quater d'insa blue shi kuma, fita yayi izuwa kan dining table nan ya iske fried rice wacce Tasha kayan q'amshi, baje baje take da kifi sosai, dama haka yake son ganin fried rice, shiyasa abinda Momy d'insa tafi girka masa knn dan tasan shine choice cook nashi a rayuwa.
Sam baya wasa da cikinsa shiyasa daya zauna sosai yaci abincin sannan yaje yai brush ya nufi wajen games d'insa inda yake motsa jiki nan wajen harabar gidan,
qaton d'aki ne babu abinda ke cikinsa sai kayan exercise a ciki manya da q'ananu an zube su a cikinsa.
Yakai one hour yana exercise a wajaje daban daban na wurin, yayi gudu ya d'aga q'arfe q'aton gaske da hannayen mabanbanta, yayi ta rubda ciki, yayi ta duq'e,
shiyasa lokaci d'aya wani irin mugun gumi ya jiq'esa sharkaf kamar Wanda ya fito cikin ruwa dudda esin dake wajen Sama da guda 5 kuma.
Saida yaji ya gamsu yaji dud wata sauran gajiyar daya kwaso ta ware sannan ya fito yana share zufa a saman fuskarsa da jikinsa da farin towel d'insa,
Nan ya fito ya koma cikin swimming pool yayi iyo nan ma sosai son ransa sannan ya koma d'akin sa ya canzo wasu q'ananun kayan farin jeans da farar Riga mai gajeran hannu Wanda ta bayyana Masa shatin murd'a murd'an qarfin arms d'insa na maji qarfin qarfaffen namijin gsk, yazari keys d'in motar sa ya fito yana shirin shiga motarsa knn yaga shigowr motar mamynsa a gidan.
Da sauri ya nufi wajen cikin takunsa a sassarfa na son ganin momyn tasa.
Amman lokaci d'aya ya tsaya cak dan ganin wacce suke tare da ita a gefenta.
Tuni ya q'ara d'aure d'aurarriyar fuskarsa katamau.
ita kuwa Hannat sai wani fari take masa da idanunta tana karye karye,
Wani dogon tsoki yaja yayi kamar bai gama momyn ba yana shirin kwana ya shige motarsa yaji momyn tasa tace
''ah MAHABEER_? baka ga momyn taka bane ba? ba welcome ba komi alhalin da katafo kuma saika juya?
A hankali ya juyo ya sauke zafafan idanunsa a....




XayynebπŸ’€πŸ’€
🌊🌊🌊

*MAHABEER*!!!
🌊🌊🌊
Story and writing
by
Xayyneb πŸ’€πŸ’€

🌊🌊🌊🌊🌊

Fasaha online writers f. o. w.

🌊🌊🌊🌊🌊
πŸ…Ώ4⃣
🌊🌊🌊
*A* hankali ya juyo ya sauke zafafan idanunsa a fuskar Hannat a wulaq'anci,
na kallon raini.
duk a cikin lokaci q'anqani yayi hakan, Ita kuwa momyn tasa ma bata lura dashi da abinda yakeyi ba lokacin ta juya danta d'auko jikkarta daga cikin motar tata data barota.
Isa yayi wajen momyn ya amshi jikkar hannun nata yace
"welcome Momy''
Dubansa tayi a wasance tace masa
"MAHABEER bazan amsa ba inda kana ganina kayi kamar baka ganni ba kana shirin ficewar ka ko?
"oh Momy I say sorry please,,,,,!
wani abune ya d'auken hankalina shiyasa"
Pleassss my mom kinyi haqurin ko ynxun?"
Ya q'arshe maganar yana langwa6ar da kansa tareda amsar jikkar hannun nata ya hada da hannayen sa alamun sorry.
Murmushi tayi tace
"To shiknn naji,
Amman da kake shirin fita haka da sauri ina zuwa?
Dan da alama yanzun ka dawo office ko hutawa baka samu kayi ba amman kuma kake shirin ficewa?''
Shafa kwantacciyar sumar kansa yayi ya d'an turo baki kad'an sannan ya manna mata jikkar ta ga hannunta yace
"yeah momy na, yanzun nan zan dawo Momy ba wani jimawa zanyi ba bye bye Momy".
da sauri ya juya ya shige motarsa ya bata wuta ya fice daga arear wajen, dan bai son ganin nataccen kallon da hannat take masa.
Hannat da kallo ta bisa tana fatan ace yau gashi dai MAHABEER ya zama mallakinta. data gama morewa quruciyar ta kuwa na mallakar wannan giant man d'in mai raunana zuciyar 'ya macen data sake tayi arba dashi ko a shirye koba a shirye ba.
Hasali ita fa bata San MAHABEER ba sai cikin satinnan data zo Hutu wajen momynta daga gidan babanta. dayake basu tare da baban nata ynxun. kuma ita momyn tata aminiyar mom d'in MAHABEER d'in CE tarema suke business d'in su.
a ranar da tazo ta iske momyn nata na shirin zuwa gidan su shine ta biyota a yinin ranar da sukayi a gidan su MAHABEER d'in har yayi dai dai da lokacin dawowarsa office anan ta gansa lokaci d'aya ta rikice da ganin halittar kyaun nasa mafarin knn kwana ukun nan da zuwanta kd wajen mamar tata tofa kullum saita zo gidan tun safe bata komawa sai ya dawo ta gansa sannan take samun lisilaman q'arfin gwiwar komawar ta gida.
Tun bai lura da manufarta a kansa har takai ga ya lura ta hanyar alamomin datake nuna masa a aikace hakan yasa Sam ko ganin ta tazo gidan bai ra'ayi, Dan a rayuwa ya tsani macen da take ballagazar da kanta da taga namiji, shiyasa Sam shi baida ra'ayin yin soyayya da yarinyar Hausa Fulani dan ganin su yake duk d'aya ba kamun kai.
Shiyasa yake daurewa yana d'an kula blessing towmy firind dinsa wacce take matuqar qaunarsa kamar ta mutu kuwa.
tun da suna cikin school ma take nace dashi har kuma yanzun da suka qare karatun, dan wani lokacin ma har gida take zuwa nemansa.
Jiki sanyaye hannat tabi momy cikin gidan bayan taga shigewar motar sa waje a guje.
Ita kanta tasan dai MAHABEER bata kanshi sam3.
Zama tayi kan one seater ta sauke nannauyar ajiyar zuciya tana tsinewa *so* a zuciyar ta daya kaita inda bata da galihu a muhallin wajen.
haka ta wuni gidan har dare yayi bataji dawowar saba,
dolenta kuwa badan taso ba ta haqura da taga babu sarki sai Allah har goma saura dole ta takira drever d'in su yazo suka tafi gida.

*Niger state*.
A yankin buzaye na asali a wata mazauna cikin wata Anguwa da ake kiranta darul Islam.
Yankine mai lumana da kwanciyar hnkali a cikinsa a koda yaushe 'yan uwa buxayen nan zaka gansu suna tattalin junan su, ga kuma kiwonsu da sukeyi gwananin sha'awa. ta kowane fanni rayiwarsu nai musu dad'i matuqa gaya sukeji.
Sai dai kuma babban abinda ya damu shugaban adalin yankin wato mlm kad'do shine rashin lafiyar mai d'akinsa binte, wacce yau a samu sauq'i gobe a koma jinya.
Dud wani jiq'e jiq'e da sukasan yana maganin Irin ciwon sunyi sa Amman sauq'i sai wajen mai duka.
Kamar yau ma haka ya baro q'ofar gida ya shigo gida jikinsa a sanyaye yake jinsa.
sakamakon kiran sa da *Ummu hani* tayi, wato babbar yarsa 'yar kimanin 18 years.
dan yazo yaga yanda ciwon Maman nata yake hawa da sauka a lokacin.
Zama yayi gefen bukkar tasu dake tsakar gida wacce ita binte d'in ke kwance idanunta na kallo sama.
sai cije baki takeyi tana motse motse da jikinta, dan ita kadai tasan irin azabar da zuciyarta ke mata a lokacin. ta kama ciki ta dafe gadaqam.
Zama yayi gefenta yana mai furta
"Assha!
sannu binte ciwom ne kuma ya taso da rana tsaka?
Ya Allah!
Ubangji Allah ya kawo afuwan miki wannan ciwo,,"!
Cikin xubar hawaye da matsanantan kyawawan fararen idanunta tace "Ameeen Baffa,
Dubanta yayi jin muryarta na rawa rawa yace
"haba ummu hani na?
bazaki daina kuka kan ciwon nan da Allah ya saukowa naman kiba knn ko?
Jinya lada ce fa,
tana kankare zunubbai haka kika karanta a cikin littatafan addinin Dana koyar dake kuma kinsan hakan, Amman danmi zaki dinga zubda mata hawaye Ummu hani?
Cikin 6oyayyar muryanta mai rawan kuka kuka, da maganar buzanci itama ta fara mayas masa da maganar muryarta na cigaba da kyarma tace "Baffa na daina to kayi haquri"
Girgiza kai yayi yace ''kullum na kamaki kina kuka haka kike cewa nayi haquri Ummu hani, Amman kuma dai hakan bazai sa kiqi qara kukan naki ba da zarar jikin nata ya motsa ba''
Shiru tayi bata qara cewa komi ba ganin Baffa d'in ya tashi ya shiga dakinsa ya fito da jiqon maganin da ake bawa mamar tata dud in ciwon ya tazoo mata haka da zafi...




XayynebπŸ’€πŸ’€πŸ’πŸ»β€β™€
[10/11, 2:44 PM] Xainab Documen: 🌊🌊🌊

*MAHABEER*!!!
🌊🌊🌊
Story and writing
by
Xayyneb πŸ’€πŸ’€

🌊🌊🌊🌊🌊

Fasaha online writers f. o. w.

🌊🌊🌊🌊🌊
πŸ…Ώ5⃣
🌊🌊🌊
*Z* ama yayi a inda ya tashi yana mai furta "bismillahe ya Allah"
da sauri Ummu hani ta matso tasa hannayenta biyu ta d'ago mamar tata ta zauna gefenta ita kuma,
tareda rungumeta a 6arin jikinta na dama, a haka baba kad'do ya d'ora mata qwaryan maganin a bakinta. binte ta fara sha har iyakan gejin da ake shan maganin.
Komawa tayi ta kwanta ta rufe idanunta.
Minti 5 da shan maganin nata taji
d'an zuwa isowar sauq'i a lokacin, taji zuciyar ta d'an lafa mata, hatta kuma da yawun ta dake tsinkewa a bakinta na kamar zatayi amai na dud in ciwon zuciyar ya motsa mata to yanzun taji ya lafa mata mafarin knn ta daina motse motsen ciwon, numfashinta ya fara dawowa dai dai.
Lura da haka da Ummu hani tayi da baffanta yasa su jin dad'i a ransu.
Da sauri Ummu hanin ta shige jikin Maman nata tana dariya mai tartare da murmushi Amman Sam takasa furta ko *A*.
Murmushi kad'do yayi shima sannan ya q'ara duban tilon 'yar tasu d'aya mai tsananin tarbiyya da girmama na gaba, ga ilimi dan tasan hadissai da dama gashi kuma tuni ta sauke q'urani wajen sauka 5,
dan a yanzu ma tana hadda ne ta kusan izu 52 ma,
Sannan ta fannin boko ma da yake lokacin an bud'e musu makarantan frimary da secondary a q'arqarar tasu Suma basai anje can birnin nasu yamai bama,
inda yanzu dai ilimi yazaga ko ina cikin duniya bawai sai za6a66en waje ba kawai.
A yanzu haka ma ta kammala frimary ta shiga secondary aji 5 knn take a yanzun.
Allah yai mata q'walwa sosai sosai kuma.
dayake dama dud makarancin q'urani babu wani karatu a duniya dazai layance masa yafi qarfin sa,
speak koyaya kai mata mgn dashi zataji kuma zata mayar ma sai dai in bataga damar mayar maka ba to wannan kuma fa.
Sai dai a ganinsa babbar matsalar da yake ganin ta addabi 'yar tasa shine rashin mgn, dud In kai mata mgn tofa kan ta maidoma amsarta zata d'au tsawon lokaci kuwa.
zakayi tsammani ma bataji ba.
Hatta su knsu iyayenta d'in sunma Riga sun saba da wannan halayyar nata gaba d'aya.
Sun lura hakan datake yi bawai sa kanta bane a'a abin a jinin jikinta yake tun mafarin farko.
Ita koda ace zata wuni tun daga wayuwar gari zuwa dare batai mgn ba hkn bazai ta6@ damun taba. d'abiarta ce hkn ita knta tasani kuma,
ta shiga jikinta sosai tun tashin ta haka tk shiyasa mutane ke mata kallon miskilar mace ta qin q'arawa.
amman in taso dan kanta taga dama takanyi magana jefi jefi ba laifi,
a nutse take komin ta a sanyaye haka habitat nata yake ita.
Sake dubnta kad'do yayi yaga ta shirya cikin uniform d'inta na makaranta yace
"Ya yau ne bazakije naku tehare
(wajen karatu)
D'in naku ba Ummu hani?
Tashi tayi ta je ta d'auko wata jikkar buhu q'arama.
wato irin ta 'yan makarantar nan mai dogon hannu.
da littafin ta wnda baifi 7 ba a ciki sai abin rubutun ta sannan ta dawo ta duq'a gefensa tace
"Baffa na shirya ma ay,
na tafi to saina dawo"
"Yawwa tabarat
(d'iyata) ta kaina, Allah shi kiyaye kinji?"
Saida ta q'ara kallon fuskar mamanta taga ta samu yin bacci sannan ta miq'e tsaye tace "Ameeen Baffa."
Daga haka ta wuce ta tafi.
Tana fita ta shiga gidan q'anen baffanta mai suna baffa indeh, tana shiga ta iske q'awar tata nahee wato 'yarsa.
tana shan fura wacce tasha nono kindirmo tayi haske sosai furan gwanin sha'awa.
Sam Ummu hani batayi niyyar zama ba amman ganin 'yar gidan nata kuma sabon damu
(fura da nono),
yasa ta zauna ta d'auki d'ayan ludayen furar ta soma sha itama.
Nahee ta dubeta tace "Ummu hani
Yau nazata ai ba zamuje tehare bane? dan naga har rana ta d'aga.''
Saida ta shanye furan dake cikin bakinta sannan ta dago fararen idanunta dasika dawo normal izuwa yanzun sakamakon ganin umman tata ta dawo lpia hnkalin ta ya kwanta.
ta dube nahee tace
Timiditen(qawata)
Mizai hana kuwa?
Kawai dai nayi kulawa ne da mama ne shiyasa na makara gun biyowa miki"
tana gama fadan hakan ta tashi tsaye.
tashi tayi tsaye itama naheen.
lokacin nahee ta maida furan d'aka mamar nahee ta fito daga d'aka ta bawa nahee naira 20 Ummu hani ma 20 kamar ynda ta sabar musu kullum. anan Ummu hani ta gaisheta suka wuce suka nufi waje.
Sukayi hanyar makarantar.
nahee nata mata zuba ita kuwa sai dai tayi gum...
dan inta bata masa tofa wata amsar bata samuwa,,, shiyasa dole nahee ta gaji da surutun nata tayi shiru ta koma masife Ummu hani tana cewa
"Ay dama gaskiar sahee datake cewa Dan kinga kinada kyawu shiyasa kike mana yanga mtss😏.
Muma ay munada kalan namu kyan ehe,,
Jin har lokacin Ummu hani taqi tankawa yasa tace
"Timiditen Nayima shiru bazan q'ara tanka kiba nima inda abun naki nima yau ya motso a kaina.
ummu hani kuwa ko a jikinta saima murmushi datayi kawai ta q'ara gyara zaman jikkarta a kafad'anta tana mai q'ara gyara farar safar hannunta irin ta garinsu mai raga raga d'in nan.
a haka har suka isa tehare d'in nasu....




XayynebπŸ’€πŸ’€πŸ’πŸ»β€β™€
[10/11, 2:44 PM] Xainab Documen: 🌊🌊🌊

*MAHABEER*!!!
🌊🌊🌊
Story and writing
by
Xayyneb πŸ’€πŸ’€

🌊🌊🌊🌊🌊

Fasaha online writers f. o. w.

🌊🌊🌊🌊🌊
πŸ…Ώ6⃣
🌊🌊🌊
MAHABEER kuwa sai wajen irin q'arfe goma saura na dare d'in nan ya dawo.
Yana shigowa kuwa falon gidan ya iske mu'azzam saraki da momyn tasa kan dining table Suna dinner.
isowa yayi gun nasu tareda Zama a gudn d'ayan kujeran datai saura kusa da mom, ya gaishesu kowane y amsa cikin kulawa.
mu'azzam saraki ya dubesa sosai yace
"Yadai my boy?
i hope dai komi na tafiyar maka lpia game da alamurran office naka ko?".
langwa6e kai yayi tareda d'orasa a cinyar momyn tasa datafi kusa dashi sannanyace "yeah dady, everything it's normal,
amman fa akwai wahala nikeji dady sosai har dayawa fa, dunbnsa dadyn yayi tareda murmushi sannan ya Girgiza yayi yace "dole zakaji haka my boy ay daman, amman kada kadamu i think next in ka saba zakaji komi lpia nina fad'a ma hakan my boy na ka riqe hakan"
d'an murmushi yasa ke yi sannan suka miq'awa juna hannu suka hade sa tareda girgiza hannayen nasu🀝🏻(sun saba duk in sun had'u sai sunyi hakan)
MAHABEER yace
"Ok my dady baji to.''
Yana maganar ne yana hamma alamun barci na binsa dudda yunwar dayake ji kuwa.
Momy tace "ah MAHABEER na?
kanajin barci Kuma shine baka dawo gida da wuri ba kuma?
dan ko saboda ka samu isasshen barci inda ga tafiya da zakayi katsina gobe Kuma?
q'ara lafe kansa yayi a kan laps d'inta sannan can cikin muryan barci yace
"to Momy but... but..I am very very hungry now fa."!
Mu'azzam saraki murmushi kawai yakeyi musu,
ya kad'a kai ya miq'e tsaye yana fad'in "kada na biye muku inason kallon N.T.A., yanzum dan naga alamum umaimah kullum baby kike son maida wannan zabgegen d'an saurayin naki,
kuyi tayi Allah bada saa to".
Ba umaimah kad'ai ba abin da shi ogan mu'azzam sarakin ya fad'a ya bata dariya ba hatta Shi uban garin Wanda ake maganar domin sa saida ya murmusa a lokacin.
koror d'an barcin dake neman haiq'e masa yayi ya miq'e zaune yana 'yar sakin dariyar ciki ciki ta abinda ya farun ba tareda yace uffan ba dai,
jiyayi momyn tasa tana cewa dadyn nasa.
"haba nuree muna fira ina ganinka Kaida d'ana Kuma inajin dad'i shine zaka tashi abinka ka barmu Kuma plssssss!!?
Ta q'arashe yanayin maganar da alamun shagawa6a a cikin ta.
Har a zuciyar MAHABEER yana matuq'ar son irin soyayayyar iyayen nasa da suke gwadawa juna har yanzun,
tun daga lokacin quriciyarsu na matuqar burgewa.
shi dai a rayuwa yana son mace wacce ta iya soyayya matuq'a.
Amman yana tunanin samun bahaushiyar yarinya wacce zatayo irin halin momyn sa wa dadynsa yanzu ba abune mai yiwuwa ba sam3.
shiyasa yaji baida ra'ayin irin auren bahaushiya,
dan jiyake qwamma kiristan Wanda sune yasan sun q'ware a ta iya soyayya,
in yaso saiya sa ta musulunta suyi auren,
dan a cewarsa Hausa Fulani woman shiririta kawai sukeyi bawai soyayya ba,
Yare sunfi iyawa.
(Niko nace anya kuwa dai hakane MAHABEER???πŸ€”)
gaya shi d'in yanda yakejin kansa yasan d'an love ne sosai, be jin zai iya jurewa d'ari d'arin matarsa muddim suna tare yana sonta kuma, tofa zai d'orata ne a setin harkar burinsa, ynda rayuwar auren sa zatayi masa ynda ya tsara ta.
Yana son mace mai shagwaba wacce ta iyata sosai shiyasa yake d'an looking blessing tommy d'insa dan tana d'an kamantawa dud da ba full take yin taba kamar ynda yake buqatan.
amman dai ba laifi tana q'oqartawa yi d'in.
inda tasan hakan na matuqar burge tunanin sa shiyasa komi na rayuwa bai qyashin yi Mata daga 100k Har zuwa abinda yai Sama yi mata yakeyi danshi mutum ne mai hannun alheri.
sak halin babansa ya d'auko wato mu'azzam saraki. dan sau tari ma wani lokacin shi yake turowa bada sadaq'oqi a wuraren daya saba basu.
dan har yanzu a tsawon shekarun nan bawai dena bayarwa yayi ba, shiyasa kullum kuwa arziqin sa qara ha6aka yake yi Kuma sosai sosai.
Shafa kansa da Momy tayi shiyasa ya sauke sanyayyen numfashi ya maido hankalinsa wajen.
Yaga dadyn nasa ma har ya shige side d'insa da leader shp a hannunsa.
"Mi kakeso kaci to saina Sama?
Abinda tace masa knn tana dubnsa tana murmushi.
Yatsina fuskarsa yayi a lang@6e yabi kayan abincin dake wajen da

Please Login or Register in order to submit comment