Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wayau sosai,
Koda suka koma gida lokacin day'a saura saida dady mua'zzam ya kirayo abokinsa mr johson yaji ko suna tareda mahabeer din amman sai yaji wayar tasa shima switchoff dole ya haqura ya barwa gobe haka suka kwanta zuciyoyinsu sai saqe saqe suke.
mahabeer kuwa suna komawa gida mikel ya wuce side dinsu shi kuma tundaga waje yake qwalawa ummu hani kiran nasa da cewar "feader na? feader na gani na dawo I'm back kina inane? Ina kika shige,,? Jin shuru yasashi kwanciya nan falon ya fiddo wayarsa yana dannawa danga tunanunsa ko wani abu takeyi a ciki jin shirun yayi yawa yasashi ajiye wayar ya miqe tsaye tareda haura saman dakin yana cewa feader nahhhhhh?? kin boye da yawa fa,, lokacin bada magungunan nan nawa yayi please kizo ,,,jin babu motsin komi a dakin yasashi leqa katifarta nanma bai gnta ba har toliet ya shiga ya dudda ba nan ma yaga wayamm tsaye yayi tareda dafe qugu da hannayensa yace "ah to ina ta shige ne kuma haka? saurin sauqa qasa yayi dan zuciyarsa ta basa wataqil tana kichen ne ma,, turus yayi ganin bata nan nanfa ya fito ya dinga qwalla mata kira shiru kakeji,, zubewa yayi bisa kujera yana tunanin to ina taje haka?,, wayarsa ya fiddo cikin aljihu ya kira number ta taita ringing baiji an d'aga ba,, tsoki yaja ya ce feader kin fiye saka waya silent why aita kira baki sani ba,, zuciyar sa yaji tace kaje side dinsi sera may be ta shiga ne can,, hakan kuwa ya miqe kai tsaye ya nufi bangaren su sera yana shiga kuwa yayi karo da sera zata fito ya danja gefe ya dubeta yace "sera sister na tana cik kuwa??
zuba masa idanun ta sera tayi sannan tace wace "sisteer naka kuma datun d'azun naga naga tabar gidan nan jaye da akwati tana kuka??
wata mummunan faduwa gabnsa ya yanke yayi cikin tsananin mamaki yace "kuka kuma miya faru da ita,, ware hannayenta sera tayi tace i don't know nazata ko kaine ma kai mata wani abun,, a guje mahabeer yabar wajen ya koma cikin gida yana qara kwalla mata kira yaji shiru zubewa yayi qasa ya dafe kansa idanunsa tuni sun fara ja cikin tsananin damuwa yake cewa "ina yarinyar nn ne ta shiga,, kaddai cikin garinan taje wani wuri, kuma tana kukafa akace??!!,, zumbur ya miqe tsaye tareda daukar key din mota dan gani yayi zama kam sam bai gansa ba. cikin birnin London yaita zagawa lungu da saqo ko zaiga umnu hani amman ina har saida akayi magrib da isha'e yana yawon neman ta cikin mota saqo da lungu kuwa.
daqyar yasamu yayi salla sanna ya dasa neman ta amman shiru kakeji,,, wata zuciyar tace toka koma gida my be takoma gida yanzun kaje ka duba,,, ransa a b'ace yace
"kin wahalar dani ummu hani miyasa zakije wani gu bada sani naba?? "!!!!!
qarfe 11 dai dai ya shiga falon gidan ya hau sama nanma shiru bata nan, nnnfa hankalin sa ya qara yin wani mummunan tashi a lokacin ne ya tabbatarwa kansa ummu hani wani abu yasameta a inda taje to ina taje?? wata zuciyar tace masa 6acewa tayi knn,, dafe kansa yayi nan da nn jijiyoyin kansa suka taso rudu rudu idanunsa sunyi jajir yana tunanin inda zai je nmta a qasar nn, zumbur yatashi ya fuce ya higi motarsa ya fuce kai tsaye gidajen television d redio ya nufa yaita bada sanarwa haka yaita yawo a titi kamar marar hankali zautacce,
sai ukun dare sannan ya dawo gida gaba day'a nutsuwa ta kucce masa sam takasa masa,, alwala yaje yayo yaita sallolin nafulfuli tareda kai kukansa ga Allah saida yayi asuba sannan yarigaya da yayanke shawarar bugawa gida ya fad'awa su dady batun kosasa a add'ua nan ya lalubo wayar tasa ya kunnata ko gani bayyayi sosai ma sakamakon wani zafi da idanunsa ke masa wnda damn indai ransa ya b'aci hakan shine alamun kukansa,, yana fara ringing day'a biyu yaji dasyn ya d'aga yana fad'in "Alhamdulilla sojana,, miyake faruwa wai naga ummu hani a gida tazo kuma inata kiran wayarka yaqi shiga?? a razane mahabeer ya miqe tsaye yace "whatttt dady tazo gida fa kace? Eh tazo yanzunnan ma haka asibiti zamuje dan acan ta kwana ba lpia dan haka komi kkyi ka ajiyesa kazo gida yau yau,,, ai baima bari dadyn nasa ya gama maganar ba ya latse wayar nan yahau shiri ko wanka baiba yayi parking kayansu ya hada komi da komi ya bude briefcase dunsa can qasa ya fiddo viza dinsu wanda ya karbo jia ya tsaida drop ko sallama baiwasu mr Joseph ba sai filin jirgi nan aka gama masa komi da komi ya shiga jirgi dud a rude ba'a jimaba jirgi ya d'aga dasu,, qarfe 11:22 suka sauka a airport drop yadauka zuwa anguwarsu basu jimaba suka iso nan ya sallami dan drop din yayi cikin gida kamar zai tashi sama dan sauri yana fad'in ''dady momy ina ummu hani din miya faru da ita dan Allah?!
jin anyi masa mgn daga baya yasa shi saurun juyowa wannan kurtun soja mai gadin gidan nasu shine yashigo falon yake fad'a masa suna asibi yan gidan,, bai tsaya tambayar wane hospital bane dan yasan itane suke zuwa nursing home da gudu ya fito ya figi mota ya fice daga gidan kamar mai tafiya saman iska,, da temakon doctor lurwan ya fado dakinda aka kwantar da ummu din sam shi baiga momy umaima dake zaune nesa kadan da gadon ummu dinba tana karanta littafin hisnul Muslim garkuwar musulmai, yayinda annah take can gefe d'aya tana zaune tana lazumi bayan gama sallar walhar ta datai,, ganin oxygen a hancin umnu hani tuni ya qaraso wajen a gigice ya durqushe gaban gadon yana kyarmar jiki ya dora kansa a gadon yana faman danne xuciyarsa da hannayensa kamar zata fito yekeji dan *tashin hankali*,, dubnta yake kwance kamar gawa wani tsabar tausayin ta ya mamaye masa zuciya ya kifa knsa a cinyoyinta yanata sabbatu yana fad'in "kitashi feader na please ina tsoron ace kada akan lalurar ciwo na ne yasa kika gudo kika barni????!!!! pleassssssss ummu wake up wake... Uppppppppp dan girman Allah ki tashi haka ki ganni nima na ganki zanje in nemo ma kaina magani na samu sauqi sosai,, insha Allah nai alqawarin zame miki gwarzo namiji ba marar lafiya wacce hatta kaisa garasa qarfin gaba dazai hucewa matarsa takaici ba kamar sauran maza ba, kitashi dan alah wlh xn nem mgni in warke ummu miyi rayuwarmu cikin jin dadi harki haifamun yarahh nima...... sambato kawai yake wasu zafafan hawaye yaji sun biyo kuncinsa abinda bai tab'a yiba wato kuka tunda Allan daya kawosa duniya kuwa,, amman wai yau shine yake zubarwa hausa fulani woman hawayen shi??? akan mace qwara daya? !! ta6666 shi kam dai ma bai damuba dan yayi hawayen shide din tsoronsa kada ace umnu hani tagajida lalurarsa ta gudo gida ne ta fadawa su dady dansu rabasu tunano hkn daya qarayi ne ya sashi qara zaucewa da sambatu yana sake fad'in """wlh zanje insamo maganin ummu zuqunnewa yayi a wajen tareda sake danne zuciyarsa datake sake qara masa wani iriyar addababben zafin numfashi kawai yake saki,
momy umaimah da anna kuwa tuni jikinsu yayi sanyi da tsananin tausayin yaran,, wato daman wannan matsalar dayake fad'a ynxun yasa ummu hani din dawowa gida sbd baida lafiyan gaba? abinda kowanensu yake saqawa a ransa knn,
a hankali momy umaimah ta qaraso ta dafa kansa tareda zuqunnawa a gabansa,,, da sauri ya gado kainsa da jajayen idanunsa kamar an watsa masa tasshi a cikinsu, ganin wacce ke gabnsa tana fidda hawaye itama hakan yasashi saurin rarrafawa ya fada jikinta yana cigaba da surutansa da cewa momy.. mo.. momy ummu kitadimin da ita kinga ance in ansanyawa mutum oxygen basu tashi a rayuwa,,, wlh momy zan mutu nima inta mutu momy na plasss kitasar mun ummu hawaye kawai yake bulbulo masa a fuska lokacin,,, rungume kansa momy umaima tayi cikin tausayin kansu tuni suka dinga fiddo hawaye a tare annah ce ta taso daga wajenda tagama sallar ta nufosu itama knn saiga...



*Xexen Fasaha*
f.o.w.
[10/11, 2:49 PM] Xainab Documen: 🌊🌊🌊

*MAHABEER*!!!
🌊🌊🌊
Story and writing
by
Xayyneb πŸ’€πŸ’€

🌊🌊🌊🌊🌊

Fasaha online writers f. o. w.

*🌳impacting valuable knowledge and Entertainment is our concern🌳*.
🌊🌊🌊🌊🌊
πŸ…Ώ5⃣0⃣
🌊🌊🌊
Annah ce ta taso daga wajen data gama sallar tata ta nufosu kenn saiga dady mua'zzam sunzo shida dady Muhammad da momy ni'ima sun shigo tareda sllma, suka zauna bayan sunwa su annah yamai jiki,
jigum sukayi suna kallon ummu dake a kwance ido rufe sai shi mahabeer kuma da keta faman sakin ajiyar zuciya yana jikin momy still,, dady mua'zzam ne ya matsa tareda d'agosa suka miq'e tsaye ya dubesa yace "haba sojana ya zaka tashi hankalin ka kan qaddarrarriyar qaddarar da Allah ya nufemu da ita tuntuni kayi ehm? kaga kayi haquri a halin yanzu Ummu hani addu'ar mu kawai take buq'ata bakomi ba, bakazo ka tasata gaba kana kuka ba kayi haquri insha allahu matarka zata samu sauqi kaji ko?,, saddar da kansa q'asa mahabeer yayi yana goge jiqaqiyar fuskarsa yana cigaba da ske ajiyar zuciya nan da nan yaji take masa duka fat! fat! fat!.
dady Muhammad yace "haquri zakayi mahabeer zata tashi insha Allah,,, cikin wata kad'uwar muryarsa yace "to dady na daina,amman nan d'ina ke mun beating sosai shiyasa ,yayi maganar yana nuna musu saitin zuciyar tasa da hannunsa,
Dady muhammad ya dafa kafadarsa bayan ya taso daga inda yace "sorry kadinga addu'a kaji ko? Insha Allah zai bari" a hankali ya dagawa dadyn kansa alamun to. momy ni'ima kuwa tana gefen momy umaimah takasa bawa mahabeer baki ita kam kamar ma tayi kuka takeji tsabar tausayin dake ratsata nasu,
zaunar da mahbeer dady mua'zzam yayi ya dubesa sosai yace
"amman yaya akayi ka bari matarka ta tafo tunda london ita kad'ai haka? annah tace "yawwa nima kam abinda niketa son naji kn,,,, d'agowa da kansa daga saman qasan mahabeer yayi ya dubi dadyn nasa yace "wlh ban san ta tafoba dady naje raka su bash airport ina dawowa naga bata gida,,....!! kasa ida maganar yayi yasa hannayensa ya rufe fuskarsa yanajin wani d'aci d'aci daga can cikin maqoshin sa sosai. dady mua'zzam yayi shiru sai dady Muhammad ne yace
"k to gaskia dawani abu kam,, annah tace "hakane mudai ajiye maganar har Allah yabawa ita ummu hani din lpia in-yaso maji komi daga gareta na dalalin tafowar nata hakan.
shiru sukayi daga nn doctor lurwan ya shigo ya qara dubata sosai sannan yaqara tabbatar musu da insha Allah zata farko nan bada jimawa ba dan alamun hakan sun nuna daga jikinta daga jikin na'urar oxygen d'in nata,, sunyi murna sosai dajin hakan kuma. mahabeer kuwa duqar dakai yayi dan kawai jiyake inama za'a d'ibi lafiyar dake jikinsa asawa ummu kota samu lpia itama,, shi abinda ke matuqar ma daure masa kai yanda akayi ta baro gidan nasu kma harta iya kawo knta nan gida tomi yafaru haka ne lokaci daya?
anya kuwa umnu tana d lapiyar brain? tambayar da wata zuciyarsa tai masa knn,, saurin girgiza kansa yayi tareda runtse danunsa a can cikin zuciyarsa yace "noooo ummu lpia nata lau danni bntaba ganin akasin hakan daga gareta ba,,,, wata zuciyar tace "to inba hakan bane kuma miya faru??
hakanan yaji kuma gabansa ya buga batareda yasan dalilin ba kuma,, jiyayi bakinsa yana motsawa a hankali yanaiwa ummu add'uar samun lpia,,, s dady Muhammad sai bayan la'asar sannan suka tafi annah ta dubi mahaber daya sa ummu hani a gaba ko matsawa baison yi dn rayuwarsu ta baya kawai yake tunanowa na tun farkon had'uwarsu har kawo rayuwarsu ta london annah yaji tasa hannunta ta tab'osa yayi saurin dauke idanunsa afuskar ummuhani da sukayi jajaye ya saukeso a kan annah,, annah tace "yakamata kaje kayi la'asar kaima kaga har 5 na niyyar yi,, jiyayi bakinsa ma kansa yai masa nauyi daman abinka da marar son fiye mgn shiyasa kawai ya tashi ya fice daga room din. momy umaima ta bisa da wani iriyar kallo cikin tsananin tausayawa dan tana lura dashi tun zuwan nasa bai iya qoqarin sa komi ckn bakinsa ba hr ynzu,
annah ta dubeta tace "amman kuma umaimatu shin ke a maganganun da yaron nan yayi na gameda lalurarsa ke baki fahimci komi a ciki ba?? gu
irgiza kai momy umaima tayi tana kallon ummu dake kwance tace ''a'a wlh annah ban fahimci komi ba wani abu ne? tagumi annah tayi tareda q'ara d'ora hannunta q'asan habarta fuskarta na kallon qasa sannan ta fara magana da cewa "niko dai gskia tabbas iriyar wannan matsalar ta mahabeer har tasa na tuno mai gida na Allah ya jiqansa da rahma lokacin yana raye ya tab'a samun ainahin iriyan cutar sanyin nan irinta yaron nan,,
a lokacin shima ya shiga damuwa na ganin kamar yana zaluntata ne yana qwarata ata wannan fannin,,to ni kuma alkunya tasa nike gwada masa babu komi dudda kuwa ina q'waruwa d'in nima sabida rashin qarfinsa ta wannan fannin to cikin ikon Allah da Allah yanufa qarshen matsalar tazo sai yaje ya fadawa kakarsa lalumo itama Allah ya jiqanta da rahma nanta zo har gida taita mana fad'a akanmi zamu zauna da babban laluri irin wannan bamu fad'a ba an nemo magani ba inda Allah yace tashi in temaka bawa?, nan mukayi shiru babu wanda yai mgn sai bayan ta fita ne na nuna miyasa yaje ya gaya mata hakan sai "yace bazan iya zaunawa ina cutar dake ba qwamma in fadawa ita din kaka wataqil ko Allah zaisa mu samu mafita,, shiru nayi kawai danni kunya ma yasa naji mgnr dayakai batun nan ga magabata,,
in fad'a miki umaimatu washe gari ina girki na tuwon amalo da rana saiga kaka lalumo ta shigo hannunta daukeda wata baqar leda nan na shimfida mata tabarma tsakar gida muka zauna naga ta kwance kullin ledar nan tafara fiddo wasu ganyayyaki na gargajiya ta ajiyesu qasan tabarmar ta dubeni tace "umaimah kinga wannan itace ake kira da *alyara* wannan kuma sunansa *cindazugun* sai wannan kuma shine *sassaqen zogale* wannan shi kuma
*sassaqen lalle* sai kuma wannan 'yar jan kanwar itama kin ganta ko? Na "ce eh kaka na ganta" tace "yawwa to nasan kunada jar dawa to zaki wanke jar dawar nan saiki shanyata ta bushe sai kisa 'yar citta cikinta kibada shagon eshay a niqo miki ita in an niqota ki tankad'eta tass to garin ne zaki dinga d'ibarsa kina damawa da ruwan magun gunannan da kika dafa kina bawa mai gidanki yana sha, sai kuma wannan man zaitun ne da kuma man kanamfari dana tafarnuwa dana hulba sai wannan d'an miski shima zaki hadesu waje daya in yazo ki basa kice injini ya dinga shafasu a gabansa to komi zaiyi sauqi insha Allah, ke koda ace mace mai fama da lalurar sanyi tayi hakan zata samu lpia da yardar mai sama'u"
niko shiru nayi ina kunya nai ma kaka lalimo godia haka kaka lalimo ta tafi, cikin ikon allah ba'a qulla wata daya ba da fara amfanin sa da magungunan nsa nan wlh ya warke sumul lpia kamar dama can da lafiyar sa a jiki har Allah yasa muka samu rabon mua'zzam dayake Ubangiji Allah yasa mai gidan nawa alhj saraki bamai yawancin kwana bane saiya rasu kuma yabarni da dumbin alhinin rabuwa da mutumin kirki gwarzo mai tsayuwar daka akan iyalinsa,,,
annah na kaiwa nn ta fara share wasu hawayen dan famin ciwon nata data famo na tunowa da maigidan nata saraki,
sannan tasake dubn momy umaima tace "zanwa mahabeer irin wannan had'in magungunan shima insha Allah kuwa da yardar mai! sama'u zai samu lpia ya dawo cikakken namiji shima kamar kowane namiji, dan da hr na sarai cikin satin nan zanje gida katsina amman nafasa sai ummu hani tasamu lpia sannan sosai" momy umaima taji dadin hakan kuwa itama,
suna gama sallar magrib lokacin dady mua'zzam yadawo suna dan taba magana sama yayinda mahabeer shida momyn suna zaune gefen ummu wato sun sakata tsakiya su kuma babu mai cewa komi tsakaninsu gwamma momy umaima wani lokacin ma tana dan magantuwa a maganar su annah,, qara ware idanunsa mahabeer yayi dake kan fuskar ummu hani daya zuba mata idanun nasa tuntuni yana kallon ta batareda yayi qi
oqarin janyewa bakuwa, gani yayi ta fara motsa idanunta qasa qasa zuwa can yaga ta budesu tarr tana kallon sama da sauri ya matso gareta yana qwalawa su momy umaima kira cikin rawar murya ta murna da cewa "momy mm... annah dady ummu ta farko,..! aida sauri suma suka qaraso wajen lokacin ummu harta samu ta miqe zaune da taimakon mahabeer din daya dagota da hannayensa,,
su annah hamdala kawai sukeyi cikin tsanani murna.
sai fmn sannu suke mata ita kuwa sai binsu take da idanunta, ahankali tayi qoqarin sa hannunta danta zare oxygen din dake fuskar nata mahabeer kuwa yayi saurin riqo hannunta yasaka idanunsa cikin nata tareda gurgiza mata kansa alamun a'a kartayi saurin yin hakan,wani kallota watsa masa cikin qarfin hali kuwa ta fuzge hannunta daga cikin nasa sannan ta koma ta kwanta tareda lumshe idanunta, sam mahabeer bai damu ba akan qwace hannu ta datai shi asali ma yadauki hakan ne abisa abunda ke damunta na ciwon datayi qoqarin cirewa shi kuma ya dakatas da itan, cikin Jin dadin farfadowar nata dady mua'zzam ya je yakirawo doctor lurwan suka dawo dakin tare,, cikin sauri doctor lurwan yaqara duddubata yaga komi normal hatta numfashinta yadawo lpia lau mafarin knn daya janye mata oxygen din tareda sake qara daura mata drip na ruwa ya tsira wasu alluran magunguna a ciki sannan ya juyo ya dubi dady mua'zzam yace "Alhamdulilla alhj komi normal ynxu nasa mata qarin ruwan nema danta samu qarin qarfin jikin nata dan zuwa gobe ma insha Allah muna sa ran ko iya sallamarta ma,
''Allah shisa to doctor cewar su dady mua'zzam din,,, da doctor lurwan zai fita kuwa saida ya dan saci kallon ummu hani da wannan nataccen kallon nasa sam ita batasan ma yana yiba danta runtse idanunta gam kamar mai barci, mahabeer ne kawai ya lura da kallon dayake matan yakuwa danqara masa harara na lamun nan ba kalar wajen wasan yara bane kama kanka da gabanka, aiko da sauri doctor lurwan kuwa yaqarashe ida ficewa daga room din, da wata iriyar harara mahabeer ya bisa tareda jan wani dan siririn tsoki, ahanka yace "banzan sakaran mutum kawani zubawa feadeer wasu ido mtsssss,, su annah sunzata ummu hani bacci takoma shiyasa suka tashi jin ana kiran sallar isha'e sukaje sukayi salla suna add'uar godia ga Allah ,, har suka gama kuwa bata tashi ba,hr lokacin mahaber basu dawo ba shida dady daga sallar suma kuma, jin anyi sallama an shigo ne ya sasu amsawa momyn nabeela ce ta shigo dakin itada nabeelar suka gaisa bayan sun zauna momyn nabeela tace "Allah sarki ummi ciwo lokaci day'a?! annah tace "wlh kuwa asma'u haka alamurran Ubangiji suke ay, momy umaimah tace "jiki kam aima yayi kyau bisaga jia kam ay zamce Alhamdulilla gobe ma muke saran sallama,, momyn nabeela tace " masha Allah Allah qara sauqi,, aminn suka amsa nabeela kuwa tana cen ta zauna kusada ummu sai kallon tausayi take mata dan ita dud a tuninunta ko kwai kwan ciki ne ke damun qawar tata,,
momy umaimah tace "ah nabeela anzo ganin goda ne?, cikin kunyar Murmushi nabeela tace "eh momy,, murmushi momyn nabeela tayi tace "uhmm kin ganta nan yau kwananta 1 wai mijin yatafi fuddo kayakkinsa na business can tayfot shine tace masa wai tsoron zama take ita daya mafarin knn tadawo gida koda na kiraki d'azun kikace mun kuna nan hospital dataji ummu ce b lpia datun lokacin zata tafo saida nai mata mgn sannan ta haqura muka zo tare yanzun din,, murmushi momy umaimah tayi tace "uhmm qawayen knn,, yar dariya momyn nabeela tayi tace uhmm aikuwa dai nima yau kwana na ukku daga dawowa daga garinmu jos,, annah tace "Allah sarki anje ganin gida knn? Momyn nabeela tace "a'a ma annah qanwata ce tasamu matsala ta iskokai wlh basu fad'an naje dubata ba sai lokacin, alhalin ciwon yakusan wata da samuwa a jikinta ashe ms, "Allah shi bata lpia" cewar momy umaimah da annah, momyn nabeela tasaki ajiyar zuciya tace "aminn ,annah wlh mutane babu tsoron allah kwata kwata a rayuwarsu ashe ciwon nan babu wanda yayi mata turensa cikin yardar allah sai abokiyar zamanta, kuma wlh annah lami lapia suke zaune katsam sai wataran ita aishan qanwata tana zaune saiga bilkisu ta shigo dakinta wato ita abokiyar zaman nata din, suna fira cikin firar ne tabugi cikin aishan cikin dabara take ce mata wai cikin halittu na jinsi miyafi bata tsoro? sai aishan tace kamar wane hallitu knn bilkisu? sai ita bilkesun ke cewa haka dai halittu na qananun halitta irinsu mage kusu d.s.,sai aisha tace oh allah sarki ai ni wlh kam bilkesu banjin tsoron komi sama da qadangare musamman ma iriyar manyan nan wlh saina iya suma dan tsoro (dan allah yan uwa bakowane mutum zaice ka fad'a masa mikakejiwa tsoroba kai kuma ka fad'a masa dan za'a iya cutar dakai da abin kamar yanda ya faru ga aysha qanwar momyn nabeela, dan duniyar nan mutanen cikinta kawai ke 6atata allah dai shi tsare dukkan kullihin musulmi aminn)
aikuwa ba'ayi kwana biyu ba dayin wannan maganar ba a tsakaninsu ba, aisha tana zuqunne bayan gida ta duqa saiga wani tsanwan qadangare ya tafo da gudu gunta,, kanta yunqura ta miqe a razane harya shige mata qasanta tace wlh annah aisha tace tayi saurin riqosa danta mnta dawani tsoro ita lokacin kawai sai rabin qugun jikin qadangare nan ya cire ya tsaya a hannunta kingin ya ida shige mata rabin ma saita nemesa ta rasa aiko saita fara hauka gadan gadan tun daga lokacin kuwa, kai abu dai yaqici yaqi yaqi cinyewa tsawon satika to dayake babanmu babban mlmin addini ne shine yadunga yimata magani karatu ruqiyya babu arziqi baqin aljanin nn ya bayyana jikinta sannan yace abokiyar zamanta ce tasa yazo gareta dan ita bata haihuwa sai ita aishan keyi amman dan allah kada akashesa zai fita, yana barin jikinta kuwa ta samu sauqi kamar ba ita ba,, sai akaga bayan sati daya iriyar ciwon yadawo kan ita bilkesun taita hauka da sabbatu tana qoqarin cire kayanta sai tonawa kanta asiri take ashe damn ta jima tana bin aishsn ta qarqashin qasa ta gaza sakamakon yawan addu'ar samun tsari da takeyi tagaza cimmata sai ynzu da allah ya qaddara abin yazo tana haila babu damar taba kurani babba bare tayi karatu,,, wlh annah in taqaice muku yanzun haka bilkesu tana gidan mahaukata wato cn sakaturum an rufeta dan babu wani sauran hankali a gareta kwata kwata, to kunji abinda ya faru kam,
salati momy umaima da annah kawai sukeyi dan abun baqaramin razanasu yayi ba hatta ummu dake jinsu saida abun ya shigeta annah tace "Allah Ubangiji ya qara katangemu daga masu wannan mummunan kalar halayyar, "amin" suka amsa jiki a sanyaye,
tashi ummu hani tayi zaune tana goge hawayen fuskarta da sauri nabeela ta rungume tana fadun "sannun sister komi zakiji sauqinsa da yardar Allah,,
sam kasa magana ummu hani tai sai ma wasu sabbin hawayen datake sharewa saida annah tasa baki sannan tasamu ta bar kukan ta koma na zuci ajiyar zuciya kawai take saki,, dazasu tafi har bakin qofa momy umaima ta taka musu sannan suka sauka zasu shiga motarsu knn saiga motarsu hjy aina tayi parking dayake basu fitoba daga motar shiyasa momyn nabeela bata fahimci su waye a ciki ba, suka shiga motarsu suka wuce,, a cikin mota kuwa hjy aina ta juya ta dubi hannat tace "to tabbacciya kindaiji da kunnenki abinda boka zalimu yace daya bamu wannan maganin, da kunnenki yace yau da yabamu wannan maganin ranar sa'a ce kowa yabawa magani yau saitayi tasirin abinda akeso, kuma baza'a qara samun irin wanna sa'ar ba sai anyi tsawon shekaru kuma yaqara maimaita mana muddin ummu

Please Login or Register in order to submit comment