Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya had'asa dasu ne haka??
Shikam godia ga Allah itace a kasance kullum a bakin su baffa da yiwa bayin Allah nan addu'a,,
haka baffa kad'do ya koma ya zauna wajen gadinsa yana cigaba da Sauraran 'yar qarmr rediyonsa yadan kishin gid'e da carbi hannunsa yana lazumi.
momy umaima ta jima tana fira da mama binte ummu hani kuwa dad'i kawai tsakeji ganin ynda mah dinta ta d'auki iyayenta da muhimmanci sosai take girmamasu kamar nata Alhalin suna qasa dasu km,, sakin jiki tayi tana daga kwance qafan mommonta idanun ta a lumshe tana jin farin ciki har ranta. batasan sanda barci yadauketa mai dadi ba a saman qafafun mamanta wanda rabon data kwanta haka a qafafun maman nata tayi barci tun suna garinsu,,
koda momy umaima ta tashi ciki ta shiga wajen momy ni'ima da sallamarta, wacce take zaune saman pray mat ta gama salla tana zaune tana addu'a,, samun waje momy umaima tayi daga kujerun falon ta zauna idanunta nakan momy ni'ima ganin yanda tasa gefen hijab tayi saurin goge qwallan data kucce mata daga idanu bayan shafa adduarta datayi,,
"subhanalla qawata miya faru haka? Kina hawaye? Cewar momy umaima tayi maganar cikin tausayi,, momy ni'ima tana son bude baki tayi magana amman ina ta kasa danjin da tayi wani gululun abu mai d'aci taji ya taso mata ya tsaya a maqoshinta, nan da nan taji wani kuka yazo mata ta duqan da fuskarta saman sallayar tana kuka mai girgiza jiki tana mai fad'in
"ya Ubangiji Allah ka bayyanar mun da yarona dan nabiyirrahmati ya Allah,,, kuka take dan jitake kamar lokacin ne aka sace mata jinjiranta mahabeer,,,saukowa momy umaima tayi daga kujerun ta zuqunna a gabanta ta d'ago da kanta ta d'ora bisa qafafunta tace "dan girman Allah qawata ki daina kuka haka kada ciwon ki ya
taso haka, kinsan mai hawan jini ba'ason aga yana shiga damuwa, tsagaita kukan nata momy ni'ima tayi cikin kyarmar murya tace"wlh qawata ni kaina bada son raina nake kukan nan ba,! wlh zuwan mun yakeyi bansan yanda zan fidda abin a raina ba wlh har baban boy naima alqawalin daina sa damuwa a raina amman dayake zuciya batada qashi wlh bansan sanda zuwan kukan ke iskeni ba saidai kawai injini ina yinsa!!""
taqarashe maganar cikin cigaba da share hawaye da farin hijab dinta.
"Kici gaba da haquri qawata dan Allah mudage dai addu'ar nan komi yayi tsanani maganin sa Allah kinjiko?,,,
nan momy umaima tayi ta dannarta harsaida taga tasaki jikinta sannan.
riqo hannunta momy ni'ima tayi tace
"nagode qawata sosai lallai kincika aminiya tagari banyi zaton raina zaimun sanyi ba saida kika mun tunasarwar nan ngd ngd,, bari na kawo miki abinsha",,
dan dai kawai momy umaima taqara farantawa momy ni'ima rai yasa ta miqe tace a'a mije can insha kinsan nima ai yar gida ce,, tare suka hau sama acan suka zauna suka ida firar sai bayan la'asar sannan momy ni'ima tarako momy umaima har wajensu ummu hani lokacin harta tashi tana linkewa mamanta kayanta dana baffa,, daga nan suka wuce gida. Suna shiga kuwa wata mota na sawo kai cikin gidan, basu tsaya ba suka wuce ciki suka zauna falo momy umaimah ta dauki remote ta kunna tv takoma ta zauna kan 3 seater tadubi ummu hani tace "ummu hani na jeki debomun dambun naman nan na jiya wanda kikaimum naji dadinsa sosai fa d'iyata,,gskia zuwa yanzu ban haufin diyata koda nakaita gidan miji ta iya kominta na irin kalolin girkinmu dana koyar dakesu ko ummu hani na?
Cikin kunya ummu hani tabar wajen da dan saurinta,,
da 'yar dariyar momy umaimah ta bita tace aranta "ina ruwan ummu na badai kunya ba,
sallama taji tana amsawa tareda duban qofa ganin hajia aina ce momyn hannat,
a gaba sai hannat din a baya, sakin fara'a momy umaimah tayi tace "ah hjy aina sannunku da zuwa, yawwa hajia umaimah, zama sukayi tareda qara sabuwan gaisawa momy umaimah tace kin rigamu shigowa knn da inata tunanin qoqartawa naje wajenki nai miki bangajiya,
nafita waje d'auko kaya"hjy aina tayi dariya tace "Kinjiki hajiya umaimah kayandama har sun qare na turamiki balance naki ma account tun jia kobakiji shigowarsa bane?"
"a'a naji bndai duba bane tukunna cewar momy umaimah din.
Hjy aina tace "kumamadai tayaya zakiyita yawo da wannan ciki haka Masha Allah ai kinyi nauyi harki iya zuwa wajena? ,, murmushi momy umaimah tayi tace "uhmm aikinsan anason excercise ga mai ciki sosai,
hjy aina tace "eh hakane dawata ya wannan kuma, yanzun wane watane kike haihuwa? wannan ne koko? dan muje mu sissiyowa baby kaya,, kafin momy umaimah tace wani abu saiga ummu hani ta fito daga cikin kitchen din hannunta daukeda plate na danbun naman wanda ta xubowa momy umaimah din ta shigo falon ta ajiye a gaban momy umaimah din tace "mah Gashi"
yawwa ummu hani na sannunki to, gaisheda hajiya aina ummu hani tayi wacce ta tsura mata ido taketa kallon ta, dan iya saninta dai batasan momy umaimah da wannan balarabiyan yarinyar ba cikin gidan nan .... amsawa tayi ta juya wajen hannat tace mata "sannu,, gani tayi hannat din ta daure fuska tana watsa mata harara a Kaikace,,, hakanan hannat taji tsani ganin aljanar yarinyar nan cikin gidan nan tasan yanda taketa wannan mugun zunzurutun kyawun mai dauke hankali ba abinda zai hana ta dinga yiwa mahabeer dinta feleqe dashi kuwa a cikin gidan , niko nace Allah sarki hannat kallon kitse kikewa rogo,,,ay ynda kikasan su sare junansu cikin gidanna haka sukeyiwa junsa kisan mummuqe bare har akaiga batun wani son burge d'ayan su.
Ita kuwa ummu hani ganin yanda wannan budurwar ke mata kallon ukku sisi yasata aranta cewa "tofa ikon rabbu πŸ€”,??,,, minayi miki ke kuma to? Inban manta ba wannan shine gani na biyu danai miki ban kuma yimiki wani laifin ba bare?!"
ba 6ata lokaci itama kuwa ummu hani ta mayar mata da irin kalan nata kallon ta miqe tsaye jin momy umaimah tace taje ga wayanta can sama a gudan dakinta taje ta d'auko mata. mafarin knn tabar wajen....
hannat ta bita da kallon mamaki...zuciyarta tace"lallaima,,!! wato wannan qaramar qaraman yarinyar har ta isa ta mayar mun da kallon rainin danai mata da tsana??!!,
qutawa tayi ta gyada kai gamida maida qaton glass din idanunta tana cigaba da cizon yatsa a 6oye.
sai lokacin ne momy umaimah tace ''aa hjy aina ba wannam watan nake haihuwar ba sai wata na gaba insha Allah".
hjy aina da magana ke faman cinta cike cikin bakinta ta dafa qafan momy umaimah tace
"keni ba wannan bama yanzun dai,, wannan buzuwar yarinyar hjy umaima a ina kika samota kuma? Nasanki da yaye yaye fa wlh,,
"wannan wacce tabar nn wai kike nufi hjy aina? cewar momy umaimah tana Murmushi.
"Eh ita nike nufi fa,,inji hjy aina din.
Murmushi momy umaimah tasakeyi tace ''wannan ai ummu hani knn, muna zaune tare da ita anan tana tayani aiki su kuma iyayenta suna nan gidan qawata nan maqotanmu hjy ni'ima matar alhaji Muhammad aminin nuree na suna tayasu aiki da kulada gida suma, kama haba hjy aina tayi tace
"ban fahimceki bafa sosai hajiya umaima ina kuka hadu da ita da itayenta kuma??
da zuciya day'a momy umaimah takwashe labarin komi ta fadawa hjy aina na ynda har su ummu hani da iyayenta suka hadu dasu kuma suka kasance a tare har ynxu.
kama baki hjy aina tayi sannan tace "amman wlh hajiya umaima banta6a sanin kinada qaramar kwanya ba sai a yau din nan, zuba mata idanuwa momy umaimah tayi tace "kamarya yaya hjy aina?? qaramar kwanya kuma dani kamar yaya kuma?
hjy aina tace "mm eh qaramar kwanya nace kamar yanda kikaji dai na fad'a,, haba haba hajiyata, kinsan kuwa yanda buzaye sukeda mugun sihiri kuwa? har kika iya ajiye wannan zuqeqiyar kyakkyawar yarinyar nan cikin gidan ki batareda tunanin komi ba?
baki tunanin zata iya tai miki siddabaru irin nasu ta koreki cikin gidan ta aure miki miji?
to wlh na rabaki marmaza marmaza ki kori buzuwar yarinyar tukun daga cikin gidanki tunkan ta zame miki qarfan qafa mai wuyar 6alluwa har sai an sare qafan sannan,,"!!!
karaff wannan maganganun na hjy aina sai a cikin kunnen ummu hani,, batace komiba ta ida isowa wajen ta miqawa momy umaimah wayan bata jira komi ba ta juya da sauri2 tayi cikin dakinta. hannat tabita da kallon shegiya qwamma kibar gidanma wlh inda bana uwa da uba bane ko hankali na yafi kwanciya.
da gudu ummu hani ta ida shiga dakinta ta fada bisa gado ta saki kuka mai zafi gamida cin rai,,
saida tayi kuka sosai sannan ta tashi zaune tare da sanya kanta cikin cinyoyin ta tace a fili "wacece ke wannan matar?? Ban sanki ba? ban taba ganin kiba sai a yau, gashi kinzo kina burin rushe mana farin cikinmu
Nidasu baffana na ganin mun samu kud'aden da za aiwa mamana aiki dasu ta samu lpia mu koma garinmu, yanzu in kika sa bayin Allahn nan suka koremu muka komsa garinmu to mimike dashi dazamu sayar mudawo a nemawa mamanmu lpia nata??!!!!!"
sake fashewa tayi da kuka snn taci gaba da magana cikin yarensu na buxaye da cewa "Allah kawomana d'auki kacece rayuwan mamana daga ciwon nan nata ka ida cika mana burunmu ka bata lpia, ya Ubangijinmu Allah ka temaka mana!"
tana maganar ne kanta na bisa cinyarta idanunta a runtse suke, kuma har ynxu hawaye basu bar sauko mata ba,,
Acan falo kuwa momy umaimah jin abinda hjy aina tace yasa sam 2 ta kasa magana tayi shiru sai idanuwa data zubawa hjy aina tana kallonta kamar wacce take son karanto wani abun muhimmi ne daga gareta mai matuqar muhimman cin gaske kuwa.....



*Xexen Fasaha*.

F.o.w.
[10/11, 2:47 PM] Xainab Documen: 🌊🌊🌊

*MAHABEER*!!!
🌊🌊🌊
Story and writing
by
Xayyneb πŸ’€πŸ’€

🌊🌊🌊🌊🌊

Fasaha online writers f. o. w.

*🌳imparting valuable knowledge and intertaiment is our concern*.🌳🀝🏻.

🌊🌊🌊🌊🌊
πŸ…Ώ3⃣6⃣
🌊🌊🌊
Momy umaimah tayi kusan minti 15 sai dai ta kalli hjy aina sai kuma ta kalli hannat harta kai ga sun fara tsarguwa da kallon nata garesu,,
hjy aina ce tayi qarfin halin sake cewa
"koko shawarar dana baki kina mata kokon to? inkina kokonto kibarshi kawai Allah baku zaman lpia keda 'yar aikin naki hajiya umaima"
yanayin yanda hjy aina ke maganar ne kaida ka kalleta kasan da biyu take mgnr,, dan a zatonta momy umaimah tuni tahau layin da takeson d'aurata ne. burinta ace momy umaimah takori yarinyar ita kuma tabita ta siyeta da kudi ta dinga neman kudi da ita dan taga yarinyar sosai-sosai girkakkiyace babu inda keda makusa ajikinta dole alhazawa suci uban dollers akan ta qarewar ma naira.
saidai abinda taji momy umaimah na cewa yasa taji abun kamar a mafarki dan bata taba tunanin jin hakan ba daga gareta,,
dubanta momy umaimah tayi sosai sannan tace
''yanzu hjy aina danna temaki bayin Allah shine qaramar kwanya ta wajaba kaina knn ashe?,,,,,,
yanzu hjy aina a misali ace rai yayi halinsa kuma ace baki da kowa a ckn garin nan kin tafi kin bar hannat shin zakiso ace tashiga quncin rayuwa na rashin kulawa daga Al'ummar Annabi?
yanzu hjy aina in miki mai gaba d'aya madai tukun inkece ke cikin halin rashi da yarinyar nan da iyayenta suke ciki kuma sai gashi Allah ya kawo miki mutanen da zasu temakawa rayuwar ki ta inganta yanzu zakiji dad'i kuwa? Shin hjy aina mutumin dayai nufin rabaki da inda kika samu kika ra6a a wannan lokacin shin maqiyi zaki kirasa ko masoyi,?!,
Hannat tayi karaf tace "momy maqiyi ne, wata uwar harara uwar ta aika mata da ita tareda danqara mata daquwa tace "uwaki 'yar banzar yarinya waya sakoki ne cikin batun?
Idan na sake na qara jin bakinki anan saina fasa miki shi kuwa yayijini shashashan yarinya kawai"
turo baki hannat tayi tana gunguni ta fiddo wayarta ta hau yin game abinta,, dud abinnan momy umaimah tana binsu da ido itakuwa batta fatan ace yau mahabeer zai auri wannan yarinyar dan kaida kaga idanunta sam babu d'igon kunya a cikinsu, misali ma gashi yanda takewa uwar tata wannan kallon daga magana,?!
tab???,, taff ta godewa Allah ma da mahabeer bawai wani attention nasa yake bawa yarinyar ba bare tsautsayi yakaisa ga auren 'yar mace.
wanda ta lura ynda hjy aina ke masifar son diyar nan tata to abin Allah kyauta koda anyi auren wani abu ya hadasu tsaf zata iya komi akai kuwa wnda hakan zai iya silar wargajewar zumuncin nasu to qwamma dai maganin kar ayi kar a soma.
jiyayi hjy aina tace
"shiknn kiyi haquri hajiya umaima da maganganun nawa kinsan zuciya da saqe saqe shiyasa na ga kamar hakan zai iya faruwa mafarin knn na tanka"",,
tayi maganar zuciyarta cikeda takaicin rashin samun ummu hani da batai ba ta shigo hannunta.
Ita kuwa momy umaimah tayi zaton har a ran hjy aina haqurin nata data bata babu komi aranta shiyasa cikin fara'a tace "hmm yawwa hjy aina nima nagode da fahimta na da kikayi kuma babu abinda zai faru sai alheri dan ummu hani yarinya ce mai tarbiyar gaske, kuma wlh koda ace mua'zzam saraki zaice yana sonta zan amince masa dan qwamma a auro maka wacce kasan halinta akan wacce bakasan nata ba,
"a'a daga nan dai, cewar hjy aina tana magana tana tada uban hancin nan nata sama.
danma butulci yasa ta kori baqin fatar fuskar nata da man coylean wnda muggan q'uraje na pumples kuma sukazo suka maye farin fuskar da asalin fatar da Allah yabata ta kushen.
murmushi Momy umaimah tayi ta canza maganar da cewa "gashi ko ruwa ban kawo muku ba munata fira"
tayi maganar tana cin dambun naman ta da small spon d'inta.
Miqewa hjy aina tayi tana fmn yafa gyalenta akai tace "a'a Wlh babu komi ynxu haka ma zamu wuce gidan hjy indo ne qawata zamuje gidan bikin diyar aminiyarta shine muka biyo tanan domun inga yanayin jikin naki kema",, momy umaimah tace "Allah sarki nakuwa gode hjy aina ku gaida gida,, "to gida zaiji kuma inaga nanda 2 days zan koma sake kawo wasu kayan dan wadancen sunqare inji 'yan kasuwan danake bawa su, komi knn dai zamuyi waya kanna tafin,,
"to shiknn hajiya aina Allah kaimu lokacin lpia,"
''Aminn"
har bakin mota momy umaimah ta rakasu sannan ta dawo falon ta zauna ta qwallawa ummu hani kira wacce ke kwance bisa gado tayi rub da ciki zuwa yanzu ta daina kukan sai ajiyar zuciya da take ta saki gamida sake kai kukanta ga Allah dan kareta daga sharren ire iren su hjy aina.
tashi tayi da sauri ta goggoge fuskarta ta fito daga d'akin ta iso har inda momy umaimah take ta zauna ta d'an saki murmushi kad'an tace"gani mah har baqin naki sun tafi?,, murmushin da ummu hani taga momy umaimah tayi yasata jin wani farinciki a ranta dan ga alama momin tata bata d'auki shawarar na aminiyar nata ba,momy umaimah tace "suntafi ummu, naji falon ba dad'i ni day'a shine na kiraki kizo muyi fira kinje kin qunshe d'aki ke mai tsoron mutane ko? Tayi maganar cikin murmushi,
'yar Murmushi ummu hani ta saki tace"laaa mah nadai bari ku gaisa ne shiyasa, girgiza kai momy umaimah tayi tace "suntafi ai,
Ni naji dad'i ma da mahabeer bai gidan wlh, zuba mata ido ummu hani tayi tace "sabida mi momy? Tace "saboda hannat wlh, nasan da tana nan har yanzun bawai son da take masa ne ke bnson ganiba ne a'a, ummu sam hannat tanada qarancin tarbiyya nikuma dud mai wannan halin gskia ban san inga yana huld'a dani bare wani nawa, mamanta tarigaya data sangartata sosai,,!
shiru Momy umaimah tayi tace "koda yake ma mubar zancen nan ummu zo kibani labarin garinku dan ina sha'awar al'adar bikin garinku ummu inga kunsa kayan nan naku baqaqe masu adon zanen zaruruwa a jiki tareda nad'in kanku kamar na gwadanki na mayafi nn wnda dashi ne naga ake muku ku amare,,
ki fad'amun yaya kuke hidimar bikinku ummu???,
tayi maganar cikin fara'a.
nan kuwa ummu hani ta saki jiki taita bawa momy umaimah labarin ynda ake shagulgilan nasu na aladar su cikin sanyintana murya,
saida momy umaimah tagama jin komi sannan tace ''kai amman gskia abubuwan naku dai daban burgewa aladar ku kam, musamman ynda kikace dukkan dangi ke taruwa wajen auren mnya da qananan ku.
yanzu dai mu ajiye wannan firan gefe najima inason in miki wata magana ummu hani, duban mah din tayi sannan ta maida kanta qasa tana d'anyin wani q'as q'as da yatsunta tace ''to mah tambayeni koma miye,, aranta tsoro take AllAh sa bawani abun taiwa mah ba dai,, jitayi momy umaima tace"a fannin addini Ummu kinada karatu tanan 6angaren kuwa?
in baki dashi kada kiji kunya ki fad'a mun dan ni mutum ce mai son ilimi zan saki makaranta yanda zaki karantu kinji ko ummu hani? ajiyar zuciya tasaki 6oyayyiya sannan ta d'ago ta dubi mah din tace "eh mah baffa na malamin addinin islamah ne, kuma nayi karatun litattafan addini da dama wajensa na sauke quranin Kareem da dama yanzu haka akwai hadda ta Q'uran inayi sosai itama,,, murmushin jin dad'i da farinciki momy umaima tasaki tareda kama baki cikin zolaya tace "aaa ikon Allah, ashe ni da malama Ummu hani nike zaune ban sani ba?, sanyayyar dariya ummu hani tasaki ta langwabe kai gefe tareda fad'in "kai mah,,,
"da gaske nk ummu kuma naji dad'i dakika kasance haziq'a haka gskia dud d'a namijin daya dace da 'yar nan tawa tofa babu shakka ya za6arwa yaransa uwa wacce manzon mu yayi umarnin da ita a aura, bareke ummu kin had'a komi ma wlh, kai masha Allah wlh,, ummu hani dai batace komi ba sai kanta data kwantar kan cinyar Momy umaimah,, ita dai haka take da son jin taushi kamar wata mage, jitayi momy umaima tace to batun boko fa kinyi ne shima,? "Eh mah nayi amman daga secondry school na tsaya,, "ok kina buqatar kici gaba to? Shiru ummu hani tayi tasan kota amince su baffa ba lallai ne su amince ba gskia inda bawai zama ne ya kawosu garin ba neman lpian mamanta ne. girgiza kai tayi tace "mah wanda nayi ma ya isa nasan su baffa bazasu barni bama nayi,
gyad'a kai momy umaima tayi tace "hakane kam kuma umarnin iyaye binsa abu ne mai kyau, "babu komi Allah ya albarkaci wanda kika samu d'in" "aminn mah,
mah sai yaushe ne annah zata dawo mana ne?, tayi maganar tana Murmushi har a ranta take missing na tsohuwar kirki annah,, momy umaima tace "nasan wannan satin mahabeer na zaije ya dawo da ita dan shima naji yana maganar tafiya daukotan next week.... sallamar wata matashiyar budurwa ce yasa su juyawa gamida amsa sallamar,, cikin fara'a momy umaimah tace "ah nabeela ce shigo shigo man, har qasa nabeela ta zauna ta gaisheda momy ta amsa cikin kulawa tace
"ya mamanki? nabeela tace "tanama gaisheki momy itace ma ta aikoni tace in gaisheki da jiki kafin ta shigo
(nabeela 'ya ce a wajen hjy asma'u maqotane suda momy umaimah, suna zumunci sosai,, wannan shekarar ne nabeela ta ida kammala karatunta ta dawo gida gaba day'a. nabeela yarinya ce mai kirki da son mutane sosai ta biyo halin mamanta asmau,, bazata wuce sa'ar ummu hani ba, ita kadaice wajen iyayenta a yanzu haka
Wanna knn).
Momy umaimah tace "Allah sarki ngd wlh sosai, ina ruwan hjy asma'u. Cikin fara'a nabeela ta dubi ummu hani tace "momy baq'uwa kukayi ne? Naga bansanta nan ba saidai yah mahabeer,
"eh nabeela matsayin d'iya na ke daukanta ta, sunanta ummu hani,, hannu ummu hani ta miqa wa nabeela sukayi musabiha cikin Murmushi wa junansu,,
Nabeela tace "Allah sarki momy nakoyi friend wlh dama zaman shiru a gida ya isheni zan dinga zuwa muku fira wajen ummu qawata,,
dariya momy umaimah tayi tace "hakane kam nima zanji dad'in qawance kuwa nabeela da ummu koba komi zaki dinga sata fitowa cikin jama'a kin ganta nan kamar mai tsoron mutane haka take, Murmushi ummu tayi tace ''kai mah,, "eh man Ummu hani haka kike fa gskia na fad'a,, dariya nabeela tayi tajawo hannunta suka miqe tsaye tace momy zamuje gidanmu da qawata ummu na nunawa momyna ita,, momy umaimah tace "babu damuwa nabeela kuje sai kun dawo to,
haka nabeela taja hannun ummu suka fice cikin farin ciki. ita kanta ummu hani lokaci day'a taji nabeela ta kwanta mata arai sosai sosai kamar 2
mi.
Momyn nabeela hjy asma'u da taga ummu itama ta yaba da ita,, sun jima tare sannan nabeela ta rako ummu gida itama ta koma nasu gidan,
haka ta kasance kullum sai nabeela taje wajen ummu sunyi fira, lokaci guda sabo yashiga tsakanin ummu hani da nabeela sosai kamar irinma wad'anda suka jima da sanin junansu daman can, takai ta kawo harsu baffa da momy ni'ima sunsan da qawancen su ummu hani da nabeela, kuma nabeela ta fahimci wacece ummu hani a gidan, dudda Momy umaimah bata fito filii ta nuna cewa 'yar aikinta bane a farkon had'uwansu saidai ita data fahimta daga baya. zuwa yanzu barci kadai ke rabasu dan sun shaq'u sosan gaske.
6angaren mahabrer kuwa tunda ya koma office ya rage zaman gidan sosai inba weekend ba shima inya shige daki ya dauki laptop dinsa yahau bazai sake fitowa wajeba saita kama mafarin knn ma suka daina haduwa da ummu inda itama yanzun data gama aiki suke shigewa shashin Momy umaimah itada nabeela suyita fira abinsu,,
satin bikin mukhtar ya kama wato yau takama alhamis da Misalin qarfe 8 na dare yagama shirinsa cikin hadadden shigarsa ta farin boyel sai sheqi yake, ya kawo hulansa q'ube read colour ya d'ora ta a kansa ta zauna sosai gwanin kyau, wnda hakan yaqara qawata kyakkyawar fuskarsa, sajen nan nasa kwantacce yasha gyara yayi wani luf -luf yas -yas saman fuskarsa zuwa qasan ha6arsa,
bash dake zaune gefen bed dinsa yace "huhh!! kai gifted billaheel Azeem za'ayi zaton kaine angon ay,,, kaganka kuwa? yanda ka had'e tsaf kanata faman tashin qamshi kamar wanda yashiga cikin perfumes yayi wanka?,,
mahabeer farin watch dinsa ya dauka ya daura bisa lallausar farar fatar hannunsa wacce ke cikeda gargasa sannan ya dago ya dubi bash yace "pleass is ko bash, mutafi ko?
dan kasan bansan african time tunkan ango yafara danno mana Kira kagane ai? Miqewa tsaye bash yayi yace "hakane mutumina muje kawai tom" saukowa sukayi falon gidan nan suka iske momy umaimah tana karanta littafin addu'oen ta yayin da ummu hani da nabeela suke zaune qasan carpet suna buga game daga zaunen da suke, cikin computer d'in nabeelan da tazo da ita, har wajen Momy umaimah mahabeer ya qarasa ya runguneta ta baya ya bata sumba a goshinta yace "cheap momy na zamu wuce mu sai mun dawo,,
"to mahabeer na sai kun dawo bashir ka gaisheda ango mukhtar,
"to momyn mu zaiji sosai,
wani ihu su ummu hani sukayi na q'ara saboda game over din da zuma game din nasu ya basu wanda sai lokacin nema mahabeer ya lura dasu awajen ma , tsoki yaja mai qarfin gaske wanda hakan yasa ummu hani saurin ankarewa dashi a wajen ta d'ago kai tareda zuba masa fararen idanunta shima kuwa ya sauke mata nasa idanun gamida cika mata idanuwa da harara da kalar kallon sa gareta na wulaqanci, Murmushi kawai tayi abinta cikin halin ko in kula irin nata data tayi masan, a hakan ma koda tazo janye fuskarta garesa saida ta d'an wani murgud'a masa baki itama sannan tabisa da hararar itama tareda sake maida kanta wajen game d'insu sukaci gaba da buga abinsu,, nabeela kuwa daman sanin kota gaidashi ba amsawa zai yiba shiyasa ta shafawa kanta lpia bata sake tankawa ba tun byn gaisheda bash datayi kuwa.
Koda sukazo fita tanan wajensu inda suke zaune mahabeer suka biyo, da gayya yasa cover shoes d'insa ya takewa ummu hani babban d'an yatsa na qafanta yabi ta kansa ya wuce, bash kuwa ya gansa ashe tym din. wata uwar q'ara ummu hani ta q'wallara kuwa ba shiri.....shi kuwa ida ficewarsa sukayi ko kallonta ma baiba bare yanuna ko yasan shine yayi mata aika aikar.
"Subhanalla ummu hani lpia???!, cewar momy umaimah, nabeela kuwa baiwar Allah dutta rud'e ta riq'e ummu tana fad'in ''sister na minene

Please Login or Register in order to submit comment